MAIRO
CHAPTER 5 KARSHE
Sai da Mairo ta tabbatar da sun gama gyare-gayarensu su tafi, sannan ta fito ta shiga kitchen.
Tana kare girkin ta kama ɗakin,
Sai goma dare Qasin ya dawo gidan kai tsaye ɗakinta ya nufa “Baby na kinga ni sai yanzu aiki ne ya rik’e ni”
Fuskarta shagwaɓa tayi “Amman kuma har dare kadai ko dan matar ka ta dawo ne?”
Kusa da ita ya zauna “Oh karki kawo wannan a ranki yanzu dai muje ki haɗa min ruwa nayi wanka sai mici abinci ko?”
Hannunta ya rik’a suka fice tare.
Bayan yayi wanka ya saka kayan bachi suka dawo parlor suka ci abinci sai dare-dare suke, ba k’aramin bachi ran Mansura yayi ba ganin ko ɗakinta bai leko ba.
Sun daɗe suna fira parlor saida dare ya tsala sannan suka nufi gurin bachi,
_Washe gari_ guraren 8 Mairo ta fito ɗakinta zaune ta tararda Mansura tana kallon k’ofar ɗakinta bata kula taba ta nufi kincin.
Aiko tana shiga Mansura ta rufa mata baya, a bakin kofa ta tsaya ta katsa mata tsawa “Ke uban mi zakiyi a kitchen ɗin?”
Juyowa Mairo tayi tana hararata “Uban ki zanyi kinsan ai yafi daɗi ci wai ke Mansura mi kike ɗaukar kanki ne?”
“Ke ni zaki faɗama wannan maganar? Ke nan fa gidana ne kuma Wallahi in baki bi a hankaliba sai na miki ɗan ba zan duka”
Taɓa hannu Mairo tayi “Amman naga ai da kunya ki kira kanki matar gida matar da bata san darajar mijinta mijin kullum cikin kuka yake da ita ke bari kiji na faɗa miki yanda nan gidan yake gidan mijinki haka nima yake gidan miji n babu banbanci dan haka ki fita idona kona gyara miki zama”
Hannu Mansura ta kai zata mare ta da sauri Mairo ta rike “Kinyi na ɗaya bazaki kara na biu ba kinyi kaɗan ki sake sakamin hannu a fuska ko wacan karon da kikayi na kyaleki saboda mijina ne”
Jefar da hannun nata tayi ta juya ta cigaba da aikinta.
Tsaye Mansura tayi tana mamaki da kuma jin tsoro dan gani take kamar ba Mairo ba,
Ruwan zafi Mairo ta ɗora sannan ta shiga feraye ɗankali. Har lokacin Mansura na tsaye tana kallonta,
Can ta matsa kusa da ita ta kai mata wani mugun shuri, tashi Mairo tay daga zaune ta dake ta wankeata fuska da mari biu ta janyo muciya ta buga mata ita a kafaɗa,
Da sauri tayi baya ta dafe kunci tana zaro ido “Maryam ni kika yima haka?”
Wani ya tsine hanci tayi “Kaɗan kenan daga abubuwan dana tanadar miki saibna gyara miki zama acikin gidan nan kuma ki fice ki bari guri ko yanzu na chaja miki halinta”
Kai ta gyaɗa “Ke wai gidan ubanki ne nan Wallahi zan halakaki”
“A’a ba gidan ubana bane amman inajin ke gidan naki uban ne ko ki fice ki bani guri ko Wallahi na miki wanka da ruwan zafi nan”
Tsaye tayi tana kallonta cike da tsoro saida taga ta nufi ruwan zafin sannan ta juya da sauri ta fice.
‘Dakinta da dawo ta zauna tana mamakin Mairo tabbas aljanune da ita haka zuciyar ke nasa mata dan daga ganin faɗan nan bana banza bane iskokinta ne ke son tasowa, haka ta dinga tunane-tunanenta tana naman hanyar da zata biyo mata.
Tana ficewa Mairo tayi k’wafa ta buga tsale “Yauwa yanzu kin fara gane karatun kenan ai nima yar issakar kaina ce”
Cigaba tayi da girkinta tana mai jindaɗin abinda tayi har ta gama sannan ta shiga tayi wanka ta shiga tada Qasin,
“Yaya tashi abincin yayi”
Janyo ta yayi ya rumgume “Toh bbyna”
Ya daɗe rumgume da ita sannan ya tashi ya shiga bathroom,
Bayan ya gama abinda zaiyi ya fito suka nufi dining, suna cikin karyawa ne Mansura ta fito daga & ɗakinta dan muryar su taji ya tabbatar mata da suna dining.
Har ta zauna Mairo harararta take. Plate taja da cup zata zuba ta bude kular k’wai zata zuba,
Nan Mairo ta tashi tsaye “Ke mi zakiyi?”
Banza ta mata ta cigaba da zubawan,
Kular k’wan Mairo ya janyo da k’arfi “Ai baki isa ba Wallahi indai zakice sai dai ki girka ni mijina kawai nake iya girkama abinda duk wata k’atanyar banza tayi kaɗan Wallahi”
Kallo Mairo Qasin yayi kamar yayi magana sai kuma yayi shiru ya cigaba da cin abincin,
Mansura ta Taɓe baki “Ni ba biye miki zanyi ba dan na fahimcin baki da hankali ba ki kuma da tarbiya”
Nan Qasin ya saka baki “Ke ya isheki haka ke idan na Maganar tarbiya har kina da bakin magana?”
Mamaki ne ya cika Mansura “Qasin ni kake faɗama haka saboda kayi sabuwar Amarya kan uba” ta faɗa tana gyaɗa kai.
Filas ɗin ruwan zafi Mairo ta buɗe tana faɗin “Yanzu zakiga rashin hankalin nawa”
A fuska ta watsa mata su kamin ta ankara ta k’ara watsa mata su har so uku, cikin hanzari Qasin ya rik’e yana “Maryam lafiyarki?”
Ita kuma ta faɗi tana ihu da murzar jiki.
“Wayyo Allah na shiga uku ta kashe ni wayyo Allah”
Nan ya saki Mairo ya nufe yana kiran sunanta, rik’a ta yayi ya tada ita ya nufi mota da ita.
Tsaye Mairo tayi tana kallonsu har suka fice sannan ta cikama bakinta iskan dan tasan tayi ɓaran-ɓarama.
Asibiti ya nufa da ita bayan an bata gado, ya kira a gidan su ya sanar.
Cikin yan mintuna mahaifiyarta ta iso tare da k’anenta biu, tambayarshi suka rik’ayi yadda abin ya faru bai faɗa musu gaskiya sai kawai yace ruwan zafi ne ta ɗauko sai ya watsar mata a fuska da jiki.
Sai da ka kira sallar Azahar sannan ya baro asibitin ya nufo gidan Momi, a masallacin dake kusa dasu ya tsaya yayi sallah sannan ya shiga ciki.
Tun daga yanayin Sallamar shi Momi ta gane akwai abinda yake faruwa bayan sun gaisa ta soma tambayarshi, “Ya akayi yau naga kamar ranka a ɓace?”
Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yace “Momi Maryam ce ta watsama Mansura ruwan zafi”
“Subhanalllahi garin yaya?”
Nan ya kwashe abunda ya faru ya faɗa mata.
Baki Momi ta rik’e “Da gaske Maryam ce tayi?”
“Itace Momi kuma ni irin masifar nan ce nake gudu kar wata rana suje suyi abinda yafi haka kuma”
“Ai maganin biri karen baguzawa abinda Maryam tayi Batayi dai-dai ba amman kuma hakan zai sa Mansura ta ɗan saurara mata”
Qasin ya gyaɗa kai “Ko kuma tace saita rama ba”
“Abinda nake so dakai indan taji sauk’i sai ka tarasu guri ɗaya kaja musu kunne”
“Toh Momi zanyi haka In’sha Allahu”
Sai da yaci abinci sannan ya bar gidan.
Mairo na zaune parlor ya shigo da sallama amsa mishi tayi tana kallon cikin idonshi, k’in yarda yayi ya haɗa ido da ita tana mishi sannu da zuwa ya amsa ya wuce dakinshi,
Da ido ta bishi har ya shige sannan ta zauna saman kujera tana sauke ajiyar zuciya. Duk sai raji ba daɗi. Ta kusan minti 30 a haka sannan ta tashi ta nufi ɗakin nashi.
“Assalamu alaikum” a sanyaye tayi sallama shi kuma ya amsa mata yana daga kishingiɗe tana dannar wayar shi,
Juyawa tayi zata koma nan ya ɗaga kai ya kirata “Maryam”
“Na’am” Juyowa tayi ta k’araso kusa da gadon shi idonta cike da hawaye.
Nan ya unk’ura ya tashi zaune “Mi akay?”
“Ba komai”
“Ba komai kike kuka?”
“Naga kana fushi danine”
“Kan mi zanyi fushi dake ni bana fushi dake amman abinda kikayi ban jidaɗi kuma baki kyauta ba”
“Amman ita ta kyauta data fasa min kai ko?”
Cike da shagwaɓa tayi maganar.
Murmushi yayi mata ya janyo ta ya zaunar saman k’afafunshi,
“Toh ramuwace kikayi kenan?”
“A’a nidai bance ba”
“Amman nasan nufi kenan naji yanzu kin rama ai shi kenan ko dan Allah karki sake kinji ku zauna lafiya nine za jindaɗi in kika min haka karki sake kulata”
Kai ta ɗaga mishi “Bazan sake ba amman sai idan ita bata min ba”
“Ba zata miki ba zanja mata kunne itama”
“Naji tashi muje kaci abinci”
Tashi yayi badan yana jin yunwa ba sai dan yana gudun yace baya ci tace mishi fushi yake da ita.
Zamansu su cigaba dayi na ma’aurata wani abu bi sake shiga tsakanin su,
*** *** *** ***
Mansura kin yarda tayi ta dawo gidan bayan an sallame ta daga asibiti danginta sai masifa suke ita kuma tace sai da ya zaɓa ko ita ko ita ko kuma ya raba musu gurin zama shi kuma yace ba zaiyi ko ɗaya ba Momi tace mishi ya samu musu ido idan ta gaji ita zata nemi dawowa,
*BAYAN WATA UKU*
Rufe yake da ido Mairo na gudu yana binta suna yar link’wa. Saman kujeara ta hau tayi tsaye tana taɓa bayan shi juyowa yayi cikin hanzari ya rike yana faɗin “Na kama” ita kuma ta fashe da dariya suka faɗi k’asa,
Wata razzanann ihu ta saki lokacin da kuiwar hannushi ta daketa a mara by mistake.
Da sauri ya buɗe idon yana tambayar ba’asi. kasa magana tayi sai kuka take tana rike ciki, nan ya shiga duba cikin. Jikin da yaganine ya katse mishi hanzari,
da sauri ya ɗaga ta amman ta kasa tsaye sai kuka take tana kiran Abban ta saman kujera ya zaunar da ita ya nufi ɗaki, riga yasa ya ɗauko keys ya dawo parlor a guje ya ɗauke ta ya nufi mota da ita.
Story continues below
Asibiti mafi kusa ya nufa da ita yana isa ka wuce da ita Emergency,
Shi kuma ya kasa zaune ya kasa tsaye sai safa da marwa yake a bakin kofar. Can Momi ta faɗo mishi a rai da sauri ya taɓa aljihu shi da niyar ɗaukar waya yaji babu komai dan ba’a cikin shiri ya fito ba,
juyawa yayi da sauri ya koma gurin da aka tana da dan parking din Motocin Asibitin da na mutane ya shiga tashi motar ya ɗauki hanyar gidan Momi.
Hankali a tashi ya shigo yana kiranta.
Da sauri ta fito daga kitchen “Gani nan Qasin lafiya”
“Momi Maryam ce na kai Asibiti yanzu”
“Lafiya miya sameta?”
Kasa faɗa mata ainihim abu yayi sai kawai yace “Ruwa suka zuba a kasa shine tana takawa sai ta faɗi jini ya dinga mata zuba”
“Inna lillahi wainna ilaihi raji’un wace Asibitin ka kaita?”
“Momi saka hijab ɗinki muje a Special Rahama hospital na kaita yanzu suka shiga da ita Emergency”
Kitchen ɗin Momi ta koma ta kashe gas ta ɗauko Hijab ɗinta suka fice.
Gudu ya rik’ayi sosai cikin yan mintuna suka iso Asibitin direct Emergency ya nufa.
Koda ya isa har likitan ya fito daga ciki yana tsaye waje yana magana da wata Nurse. Qasin yace “Yauwa gama likitan daya karɓe ta can”
Gurin shi suka nufa ko k’arasawa basu yi kusa dashi ba Momi ta shiga tambayarshi “Likita ya jikin wadda aka kawo?”
Kallon Momi yayi ya ɗan murmushi “Kune iyayenta? yanzu nake tambayar wadda ya kawota”
“Mune muka kawota ya jikin nata?” Qasin ya tambaya
“Da sauki bachi take yanzu muje office ɗina akwai maganar da nake sonyi da kai”
Shine a gaba suna biye har ya isa office ɗin gurin zama ya nuna musu bayan ya zauna ya ɗauko wata takarda yayi rubuce-rubuce ya mika mishi “Wannan maganin za’a siyo mata kuma ina son sanin abinda ya faru da ita har ya janyo zubar jinin nan nata?”
K’arya da yayi ma Momi ita yayi ma likitan yana noce-noce da kai.
Likitan yace “Toh kunci sa’a da cikin bai zube gaba daya ba amman dai yayi zuba dan haka kawanakin haihuwar ta zai karu kamin ta haihu”
Bakin Qasin sake yana kallon likitan dan bai fahimci inda ya dosa ba,
Momi cikin rashin fahimta tace “Dr mi kake nufi ciki ne da ita ko mi?”
“Eh tana da ciki baku sani bane? 3 months amman yanzu ya koma 2 saboda zubar da yayi”
“Dr da gaske?”
“Ya no doubt zaka iya zuwa wani Asibitin ka bincika idan baka yarda ba”
Baki Qasin ya rufe ya lashe ido yana sauke wani nauyayen ajiyar zuciya. Can ya tashi tsaye ya yaba likitan baya ya rumgume hannayenshi yana murmushi,
Momi kuma ta ɗaga hannu sama tayi yima Allah godiya. Likitan dai sai kallonsu yake yana murmushi. Momi ce tayi ma likitan godiya shi kuma ya ɗauki takardar maganin suka fice.
A hankalin ta fara motsa hannunta har ta buɗe idonta,
Qasin ta fara yin karo dashi yana zaune kusa da ita yana murmushin da duk wadda ya gani yasan daga zuciyashi yake. Hannu yakai ha shafa kanta “Babyna kin tashi?“
Kuka ta rik’a k’ok’arin k’ak’arowa “Ina Momi?”
“Tazo ta duba ki sai kuma tace bari taje ta girka miki abinci”
Shiru tayi bata sake cewa komai ba. Nan yaja yatsanta yana murzawa “Maryam albishirinki?”
Kallonshi tayi “Mi akayi?”
“Mi zaki ban idan na faɗa miki?”
Kuka tasa mishi “Nidai kawai ka faɗa min”
Ido ya sakar mata yana murmushi har sai da tayi kukan da gaske sannan ya shiga share mata hawaye yana faɗin “Likita yace kina ɗauke da juna biu kina da ciki”
Tashi tayi zaune “K’arya ne”
Qasin ya ɗan sha kunu ya lak’aci kuncinta “Toh wa yake yin k’aryar?”
“Likita mana”
“Toh bari na kirashi kiji daman ai yace idan kika tashi na kirashi”
Bai jira cewarta ba ya tashi ya fice.
Bayan wasu yan mintuna ya shigo tare da likitan suna dariya,
“Sannu ko ya jikin naki yanzu?”
“Da sauki”
Qasin ya zauna kusa da ita “Likita wai har yanzu bata yarda tana da ciki ba”
Dariya yayi “Saboda mi ni har yanzu mamaki kuke bani ace wai bakusan tana ɗauke da ciki ba har na tsawon lokaci haka”
“Toh bata wata alama na masu ciki balle na gane tunda bata amai bata rashin lafiya ba wani”
“Eh ai ba duk cikine yake saka amai ba wani sai ciki ya tsofa wani sai yakai tsakiya wani tun yana farkon shiga kai wani ma har ta haihu ita abin yazo mata da sauki ne shiyasa amman ko tofar da yawun nan batayi ne ko kwaɗayi? Kuma baka lura da lokutan period ɗinta ba?”
“Bata tofar da yawu gaskiya sai dai kwaɗayi da maganar period kuma ni duk ban ɗauka cikin ne ba”
Murmushi likitan yayi ya shiga duba “Akwai wani abin da kike ji yanzu?”
Kai ta girgiza “Babu wai da gaske ciki ne?”
“Ciki ne mana nan da wasu watanin saiki haifo mana baby boy ko girl koma biu ko uku”
Shiru tayi kamar mai tunani ta ɗora hannu saman cikin, nan Dr ya shiga faɗa ma Qasin wasu abubuwan daya dace tayi ko kar tayi da kuma wa yanda zata ci, ya dade yana mishi bayani sannan ya fice.
Story continues below
***, *** ***
Kwananta biu Asibitin aka sallame ta bayan likitan yasa ya buɗe mata file ɗin awo,
Momi k’in yarda tayi su koma gida sai wai abubuwa zasu mata yawa tun shi namiji ne ba zama yake ba k’ara ta ɗan kwana biu gurinta sannan.
Qasin ba dan yana so ba sai dan ganin ta nace akan hakan dole tasa ya sai kyali ta dawo gurin Momi da zama, ta kusan wata biu gurin Momi baya aikin komai sai dai taci tasha sai bachi da kuma kallo Momi ta dinga shagwaɓata kamar gareta farau ciki.
Sai da Qasin yayi kamar yanayi sannan Momi ta samu wata yar tsohuwa ta haɗa su wai ta rik’a kama mata aiki, da kuma lurarda ita wasu abubuwan da ya kamata ta sani.
Aɓangaren Mansura tunda labarin ya sameta ta shiga damuwa da nadama kullum cikin kuka take tana dana sanin abinda tayi,
**** **** ****
Wani yanayi Qasin ya sami kanshi wadda bai taɓa mafarkin samun haka ba wai yau gashi shida matarshi suna rainon ciki,
Kula yake da cikin sosai yana Shagwaɓata da tarairaiyarta hakan yasa abu kaɗan sai tasa mishi kuka shi kuma duk yabi ya rikece. Cikinta na wata shida yasa ta shirya shi da ita suka je k’auye gaida Gwaggo,
Aiko kamar ta haɗeye Mairo dan murna dan rabonta da ita tun tana Amarya ga kuma cikin da taga jikinta dan Qasin hana Momi yayi ta faɗa, aiko murna gurin Gwaggo ba’a magana ta rasa inda zata saka Mairo. Duk inda dangi suke na kusa sai da Gwaggo ta kai ta duk da ita Mairo ba hakan taso ba wai ita kunya take ji,
Kwananta biu can ran na uku Qasin ya zo ya ɗauke ta abubuwan su na k’auye Gwaggo ta haɗa mata bayan tayi mata tsabar daddawa da miyar kuka, da guro. Da kayayyakin k’walama na k’auye.
*** ***** **** ****
Ganin babu Sarki sai Allah yasa dole Mansura ta nemi dawowa gidanta,
Bai hana taba amman kuma bai bari ta dawo gidan ba dan ganin yake wata fitinar ce zata sake haddasuwa idan ta dawo tunda yasan halinta da kishi kuma Mairo da ciki komai zai iya faru hakan yasa ya ware mata ɗaya daga cikin gidajenshi ta tare can duk da ba hakan yaso ba dan wasu ganin suke raba mata kesa yara su tashi ba haɗin kai ko kuma su rik’a k’iyayyar junansu,
Wasa-wasa cikinta ya tasarma wata na takwas. Sam Qasin baya yarda tayi wasa da awo dan yasan muhimmancin zuwa awo ga mace mai ciki yana hana faruwar wasu abubuwan yana kuma taimakawa mace ta sami saukin haihuwa.
kullum Qasin cikin zolayar yake wai yan biu zata haifa duk da likita ya tabbatar musu da ɗa ɗayane a cikinta,
Itan babu abinda ta tsana irin wannan maganar dan ɗan ɗaya ma tunanin take yadda zata haifoshi.
*** **** ***** ******
Duk zaune suke k’asan carpet suna kallon Tv. Ita kuma sai faman nishi take tana cin gauta,
Hannu yakai ya shafa cikinta “Wannan cikin Akwaishi da ciye-ciye koda yake daman ance yan biu haka suke”
B’ata fuska tayi “Ka fara ko nace maka nidai bana so”
“Toh ko baki so idan Allah ya nufa sai kin haifa baki ga cikin kullum k’ara girma yake ba?”
“Ai Dr yace ɗa ɗaya ne”
“Toh likita Allah ne? Abinda Allah yaga dama yake sanar dasu kuma so nawa akayi haka kinga an haifi ba abinda suka ce ba? Kedai kawai kice Allah ya sauke ki lafiya”
“Amin amman nidai ɗaya zan haifa”
Murmushi kawai yayi ya cigaba da kallon yana shafa cikinta.
Kwantowa tayi saman jikinshi “Yaya” a hankali ta kira sunan shi
“Na’am K’anwata”
“Ya maganar tafiyarka tana nan?”
“Tana nan amman idan kin barni ba kince bakison naje ba?”
“Toh baza ni ba”
“Toh kayan da naga kasa a boot ɗazun fa?”
Murmushi yayi “Wanine ya rok’eni tufafi shine na saka a mota idan zan fita sai na biya na kai mishi”
“Amman kuma ka saka a jakar da kake tafiya da ita?”
“Eh har jakar zan bashi”
“Da gaske?”
“Eh mana ba kince kar naje ba amman fa abubuwa zasu wuce ni da yawa kinga tunda kika zamu cikin nan duk wani abun da zai kaini nesa bana zuwa wannan ma dan naga yana da muhimmanci ne dan kuɗi zamu samu ba kaɗan ba kuma kinga zamu haɗu da wasu turawa ne idan sun mana interview munci sai su saman hannu mu fara wata kwangila a South Africa”
“A’a nidai bana so ka bari har wani lokacin ai duk gun da arzikinka yake sai ka ci”
Kwantar da ita ya ya k’arayi “Ai a zani ba tunda kince bakiso amman dai da kin Amince da yafi”
“A’a ban Amince ba”
“Ok My Queen”
Dariya tayi shima yayi murmushi ya rumgume ta,
Sun daɗe parlor sai da yaga ta fara jin bachi sannan ya tashi suka shiga Bedroom.
Story continues below
*WASHE GARI*
Tun da sukayi sallar A’suba suka sake komawa bachi. Mairo bata farka ba sai 9 da rabi. Ta daɗe zaune saman gadon sannan ta sauko tana wani abu da jiki kamar wadda ke mata ciyo,
Sai da ta shiga bathroom tayi fitsari sannan ta nufi parlor sanye da doguwar rigar bachi kanta ba ɗankwali,
Murmushi ya rik’a sakar mata har ta k’arasa kusa dashi tana kallon dining room. “Baba Ladi bata k’are haɗa breakfast ɗin bane?”
“Ta kare mana acici ke nake jira ki tashi muci”
Sai a lokacin ta kalleshi “Good morning”
Ta faɗa tana shafa kanshi tana murmushi
Kiss yayi mata a cikin “Morning my babies how was your night?”
Dariya tayi taja mishi kunne. Nan ya tashi tsaye yana faɗin “Muje nayi miki brush muci abinci”
Hannunta yaja suka koma ɗakin.
*11:5am* Suka gama breakfast cikin dabara Qasin ya zare jiki ya shiga ɗakin shi yayi wanka, yana fitowa ya tararda Mairo zaune saman gadonshi tana kallon k’ofar bathroom ɗin.
Murmushi ya sakar mata “My babies”
“Ina zaka je?”
Zaunawa yayi kusa da ita yana tsane jikinshi da tawul “Bana faɗa miki tun shekaranjiya ba ina da ɗaurin Aure?”
“Eh amman ai K’arfe biu kace za’ayi”
“Inason na biya gurin Momi ne kamin lokacin yayi dan kusa da sune”
“Da gaske?”
Fuskarta ya rik’a ya goga mata hancin shi “A’a da k’arya”
Murmushi tayi “Na shirya ka kaini gurin Momi sai ka wuce? Tun da kace zaja biya”
Shiru yayi har na wani lokacin sannan yace “Eh jeki shirya”
Da dariya ta tashi ta fice.
Tare suka tafi gidan Momi yana yin parking yayi saurin riganta shiga parlor, koda ta shiga bata tararda kowa ba kujera ta samu ta zauna taba kiran Momi.
Kitchen Momi ta fito tare da Qasin tana murmushi “Oyoyo Maryam yau gidan mu?”
“Eh Momi ina kwana?”
Zaunawa tayi tana faɗin “Wuni dai ko ai sha biu ta wuce yanzu ya gidan?”
“Lafiya kalau ina su Usman?”
“Yana makaranta jiya ko Siraj ya turo mana hoton matar da zai Aura”
Mairo tace “Eh muma ya turo mana Momi kyakkyawa da ita fara”
“Eh yace yana nan zuwa a shirya zuwa gaida iyayenta”
Qasin yace “Wai Momi yar Abuja ce?”
“Eh yace acan take ita da iyayenta”
“amman yayi dacen mata gaskiya” fadar Mairo.
Momi tace “Ai ko ita tayi dacen miji dan ɗaya nima ba baya ba”
Duk dariya sukayi Qasin ya shafa kanshi “Nikan bari naje ina son biyawa wani guri”
Momi ta kalleshi “Ok Allah ya tsare”
“Amin”
Da ido Mairo ta bishi har ya fice. Sannan taji ya kira ta,
“Na’am” amsawa tayi ta tashi ta nufi k’ofar, tsaye tayi bakin k’ofar tana faɗin “Gani”
Hannu yasa ya janyota ya rufe k’ofar.
“Baki ce Allah ya tsare ba”
“Toh Allah ya tsare duk abinda aka ci ka kawo min”
Dariya yayi “Toh an gama Hajiya ta”
Nan ya matso kusa da ita sosai yasa bakinshi cikin nata ya soma kissing.
Sun daɗe haka sannan ya cire bakinshi yana sauke ajiyar zuciya ya ɗora goshinshi saman nata ya lumshe ido,
Can ya ɗauke kanshi yana murmushi “Sai na dawo biebes na I LOVE YOU”
“I love you too Allah ya tsare”
Murmushi yayi mata as respond ya nufi gurin motarshi,
Har ya fice hannu take ɗaga mishi yaba dago mata. Saida Mai gadin ta rufe gate sannan ta juya ta koma cikin parlor.
shigowanta yasa Momi ta kalleta tana murmushi “Allah ya saukeki lafiya Maryam wannan ciki sai kace yan biu”
“Haka yaya yake cewa shiyasa ko wani aikin kirki bana iyawa” ta faɗa tana k’ok’arin zaunawa,
“Ai dole yanzu ma ba dan kar Ladi tace an barta ita ka ɗai ba da sai kiyi zamanki har ya dawo”
“Ai sai ya dawo zamuje”
“A’a yace da maraice yayi na turaki gida kar na bari dare yayi”
Kallon Momi tayi “Momi ba ɗaurin Auren zaije ba?”
Murmushi Momi tayi
“Yaje kaduna amman yace kar a faɗa miki sai ya tafi”
Nan da nan gashin jikinta ya tashi idonta suka cika da kwallah kan kace kwabo har hawaye sun fara mata zuba,
Momi tace “Toh ai ba dade wa zaiyi ba kwana biu zaiyi ya dawo”
Kuka ta sama Momi sosai “Niko Wallahi ba zan koma ba sai ranar daya dawo ko shekara zaiyi”
“Toh gaki ga guri ai indai zamane ita Ladi anjima sai Nura yaje ya faɗa mata taje gida har ki dawo daga nan sai ya biyo miki da kayanki”
Duk da hakan ta daɗe tana kuka Sannan ta share hawayen ta cire hijab ɗinta,
Momi ta tashi ta ɗauko mata fruits.
*** **** *****
Tunda ya tafi kullum cikin kiranta yake kirn safe daban na rana daban na dare ma daban.
Ranar da zai dawo Mairo ta tashi da wani irin matsanaicin ciyon kai da zazzaɓi wuni tayi kwance breakfast ma dak’er tayi bata fito ɗakin ba saida Momi ta kare shirya ma Qasin komai da tasan zai buk’ata dan ya faɗa mata nan zai sauka,
Abinci kusan kala uku Momi ta shirya mishi sannan taje tayi wanka. Mairo ma wankan tayi ta shirya cikin wani les Sky Blue bata yi makeup ba powder kawai ta shafa sai mai a leɓe ta dawo parlor ta zauna. Fuskarta babu walwala,
Zaune tayi a parlor har kusan biyar na yamma. akai-akai take duba wayarta dake saman hannun kujera kamar mai jiran kira gaban sai faɗuwa yake, Guraren biyar da rabi ta samu kanta ciki wani yanayi kamar ta fasa kuka. Sai juye-juye take tana sauke ajiyar zuciya.
“Amman yaya ya daɗe bai iso ba ko bai taso da wuri bane” a fili ta furta tana kallon k’ofar ɗakin Momi,
Wata zuciyar na nuna mata ta kira shi sai kuma taji ba zata iyaba.
Tana haka taji Parking ɗin mota da k’arfi ta zabura tana kallon k’ofa bugun gabanta ya k’aru,
Usman ne ya shigo hawaye na mashi zuba, suna haɗa ido yayi saurin sadda kanshi yana share hawayen.
Zaro ido Mairo tayi nata idon suka cika da k’wallah “Lafiya Usman miya faru?” ta tambaya muryar ta na rawa.
“Ba komai ina Momi?”
Kasa bashi amsa tayi ta k’ura mishi ido tana son karantar abinda yake ɓoye mata,
Fitowar Momi ce tasa ta daga kai tana kallon upstairs. Hawayen da ta gani a fuskar Usman su ta sake gani shinfiɗe a fuskar Momi,
Rawa jikinta ya shigayi ta fara wani wahalallen numfashi, kamar haɗin baki wayarta tayi ringing.
Da sauri ta kalli wayar tana haɗe yawu,
Cikin hanzari Usman ya kai hannu ya ɗauke wayar ya kashe.
K’ara zaro ido Mairo tayi hawaye suka shiga mata zuba kamar an koro su, Momi na da fata ta saki wata irin razananniyar kara ta faɗi zaune dafe da ciki.
Da sauri Momi ta kamata wani irin rik’o Mairo tayi ma Momi da k’arfi tana wasu zafafan hawaye “Momi ya rasu ko? Yaya ya rasu?”
“Ba rasuwa yayi accident ya samu a hanyar shi ta dawowa”
Usman ne ya bata amsa dan Momi in banda kuka babu abinda take.
Kai ta girgiza “A’a nasani ɓoye min ne kuke ya rasu na shiga uku na bani na lalace”
Bakinta Momi ta tushe tana girgiza mata kai,
Sun dade a haka kowane su sai kuka yake Usman ne yayi k’arfin halin yace “Momi kuka bayayi addu’a zakiyi bari naje Asibitin na gani”
Momi na k’ok’arin tashi Mairo ta rigata “Zan bika Usman”
“A’a Maryam ki zauna gida har na dawo” Momi ce take maganar cikin kuka,
“A’a Momi dan Allah ki barni naje koda gawarshi ce na gani babu wani abinda zaku ɓoye min na riga naji komai dan Allah Momi karki hana ni”
Shiru Momi tayi kamar mai tunani sannan ta nufi upstairs ta ɗauko hijab ɗinta dana Mairo ta fito. Momi da kanta tasa mata hijab ɗin sannan ta sama kanta suka fice.
Suna isa Asibitin suka nufi gurin da wata Nurse ta nuna musu, tsaye sukayi bakin k’ofar cirko-cirko kowanne fuskarsa da hawaye in banda Usman da yake k’ok’arin danne kuka,
Likitoci uku ne akan shi suna aiki bashi taimakon gaggawa. Sunyi awa uku a ɗakin suna abu ɗaya dak’er suka sami numfashinshi ya tsaya dai-dai yadda ake buk’ata, sannan suka cigaba da duba sassan jikinshi, Ko a hakan ma sun daɗe sannan suka fito.
Da sauri Momi ta tare su “Dr yana da rai yuwa?”
Ido Dr ya sakar mata sannan ya kalli Usman ya sake kallonta ba tare da yayi magana ba. Momi cikin kuka tace “Dr ka faɗa mana kawai ni uwar shi ce wannan k’anen shine wacan kuma matarshi ka faɗa mana kawai”
Ajiyar zuciya ya sauke yace “Mama ki kwantar da hankalinki bai mutu ba ya daiji mummunan rauni ne babu kariya aciki amman dai awazonshi sun samu matsala wadda ya haddasa murdewar jiyojinshi”
Kuka Mairo tasa “Dr kawai kace mana ya mutu”
Nan ya kalleta “Bai mutu ba nan da wasu awanin zai farka har magana zaku iya yi dashi amman ba zai iya tashi ba ko cin abinci ya haɗe har sai an mishi aiki”
Usman ya faɗi zaune dafe da kai yana “Inna lillahi wainna ilaihi raji’un”
Momi ma durkuashewa tayi tana kuka, Mairo kan hawayen tsaya mata sukayi k’ofar ɗakin kawai take kallo,
_ni kuma na kasa ganewa shin farincikin ance yana raye ne ya hana mata kuka ko kuwa dan ance ya samu matsala ne bakin cikin ya hanata kuka_.?
A hankalin ta jingina jikinta jikin ginar dake bayanta ta sulale k’asa zaune ta rafka tagumi,
Daker Usman ya lallaɓa Momi ta tashi daga inda take ta zauna saman kujera,
Nan ya zauna kusa da ita yana bata hak’uri.
Kiran sallar I’sha ice tasa kowanne su ya tuna da bai yi magariba. Da sauri Usman ya tashi “Momi bari naje nayi Sallah”
Kiran shi tayi ya juyo tace ya bata wayarshi ba musu ya mik’a mata ya fice,
Wata number tasa ana ɗauka ta fda mata wasu abubuwa da za’a dauko mata. Bayan ta ashe wayar ta kalli Mairo tace “Zaki wani abu?”
Kallonta kawai Mairo tayi ta kauda kai ba tare data bata amsa ba,
Zirga-zirga yan’uwan da abokin arziki da suke kusa suka rik’ayi Asibitin duk da likita bai ba kowa damar shiga ba, sai dai su yima Momi da Mairo sannu su tafi.
Guraren 3 da rabi likitan ya sake shiga ɗakin bayan wasu yan mintuna ya fito ya kora Usman dake zaune saman kujera a hankali dan a zaton shi su Momi sunyi bachi ganin duk sun zaburo yasa ya ɗaga musu hannu “No kuyi zamanku shi kawai nake buk’atar yazo”
Da sauri Usman ya tashi ya nufe shi. Shi kuma ya k’arasa buɗe mishi kofar suka shiga tare.
Maida k’ofar Dr yayi ya rufe sannan ya kalli Usman yace “Ya farka baya buk’atar hayaniya shiyasa na kiraka kai ka ɗai dan nasan su zasu iya sa mishi kuka har wani abu ya faru”
Usman ya rike shi “Da gaske Dr”
“Gashi can zaka iya zuwa ka ganshi sai dai ba zai iya magana ba sai nan da awa biu”
Cikin sauri ya k’arasa gaban dagon yana kallon Qasin shima shi yake kallo kowanne idonshi cike da hawaye.
A hankalin Usman ya kira sunanshi cikin muryar kuka “Yaya” nan Dr ya tari numfashi shi “Na fada maka baya son hayaniya ciyinshi zai iya karuwa idan ka tada mishi hankali dn haka ina son ka zauna dashi ne kawai har lokacin da zaiyi magana kar kuma ka barsu su shiga har sai na bada izini”
Kai kawai Usman ya ɗaga mushi yaja kujera ya zauna,
Shi kuma Dr ya juya ya fice.
Momi na ganin ya fito ta tareshi “Dr ko ya mutu ne?”
Murmushi ya ɗanyi “A’a bai mutu ba ɗanki fa shida wata matsala idan ba wannan matsalar dana faɗa miki ba”
“Toh yanzu Dr babu wani abu da zaku iyaye ku shawo kan wannan matsalar?”
“Za’a iya mana za’a iya yi mishi aiki sai dai aikin da hatsari sosai kuma Dr ɗaya ne ya k’ware sosai akan wannan matsalar duk Nijeriya shine Dr Siraj kuma yanzu an mayar da shi Abuja da aiki sai idan transfer za’ayi muku kuje can Abuja ko kuma na ku fitar dashi waje gaba ɗaya gun da k’wararrun suka da yawa dan a ganina fitar dashi wajen yafi”
Rufe baki Momi tayi hawaye suka zubo mata, hak’uri Dr ya bata sannan yasa kai ya fice.
Story continues below
***
Sai da awa biyu ta cika cif sannan Qasin ya lumshe ido ya haɗeye yawu har lokacin Usman kallonshi yake yana hawaye,
A wahale ya soma magana “Ina Momi”
B’ari jikin Usman ya shigayi cikin rawar murya ya bashi amsa, “Tana waje Yaya ya jikin naka?”
“Maryam tayi kuka ko?”
“A’a batayi ba”
“Karkamin karya Usman”
“Tayi yaya ita da Momi duk sunyi”
Har lokacin idonshi a rufe yake yana maganar duk da turo k’ofar da Momi tayi ta shigo baisa ya buɗe ido ba sai hawaye kawai suke mashi zuba,
Cikin muryar kuka Momi ta kira sunan shi “Qasin… “
Ya dade kamin yayi magana “Momi kibar kukan nan bana son kina kukan nan koda na mutu”
“Bazan iya ba Qasin bazan iya juye ganin halin da kake ciki ba banyi kuka ba kaima kanka ai kukan kake”
A hankalin ya buɗe ido ya kalleta “Momi ina kukane saboda ni kadai nasan abinda nake ji sannan ina tunanin yadda rayuwarku zata kasan idan bani”
Cikin kuka Momi tace “Ba zaka mutu ka bar muba Qasin kada Allah ya nuna min san wannan ranar ina raye”
“Ina Mansura ina Maryam?”
“Mansura tana can kwance tun da labarin ya sameta ta faɗi ana mata k’arin ruwa Maryam kuma tana nan waje zaune”
Usman ne ya bashi amsa
Ya ɗan daɗe kamin yace “Kira min ita” da sauri Momi ta juya sai da Usman yayi kamar ya dakatar da ita akan abinda Dr yace sai kuma yaji ba zai iya ba,
Da sauri-sauri gudu-gudu Mairo ta shigo ɗakin ta k’araso kusa da gadon shi “Sannu Yaya sannu” Abinda ta ringa furtawa kenan tana wani yawo da ido kamar firgitacciya.
Cikinta ya k’urawa ido sannan ya kalleta ya sakar mata murmushin k’arfin hali tare da kiran sunanta “Maryam”
Da sauri ta amsa “Na’am Yaya Allah ya baka sauki tashi kafaɗarka” Hannu takai tana taɓa shi,
“Amin amman dan Allah kubar kukan bana son kuna min kuka koda na mutu”
Kai ta girgiza “A’a bazaka mutu ba Yaya baza mutu ba idan ka mutu nima mutuwar zanyi”
“Ba zaki mutu ba nine dai zan mutu ke zaki rayune keda abinda kika haifa cikin jindaɗi”
“Taya kake tunanin zamu yi rayuwar jindaɗi nida abinda na haifa idan baka raye kunci ne kawai zai mamaye mu dan Allah ka dai na wannan maganar bazaka mutu ba”
“Mutuwa wajibi ce Maryam dole ne sai mun mutu shiyasa ake son a rik’a tuna ta a kowane lokaci”
Rushewa Mairo tayi da kuka mai k’arfi ta rike gadon da yake kwance. Hakan ya haddasa shigowar likitocin da sauri.
Faɗa sosai ɗayan likitan yayi ma Usman sannan duk suka sawo su waje,
Kuka sosai Mairo keyi wadda har saida ya haddasa mata ciyo a kasan mararta,
***
Ana sauke Sallar A’suba Siraj ya diro cikin Asibitin, Momi na ganin shi ta tsaye da sauri tana kallon shi har ya iso. Fuskarshi cike da tashin hankali yace “Momi ya jikin nashi?”
“Yana ciki bazan ce maka ba sauki ba tunda yana magana amman yana cikin mawuyacin hali”
Kai Siraj ya ɗaga wadda hakan yasa ya hango Mairo dake kwance saman carpet dafe da ciki idonshi cike daf da hawaye,
Da sauri ya share hawayen ya kara matsowa kusa da Momi ta yadda Mairo bazataji Abinda yake faɗa ba yace “Momi mi yasa kika sanar da ita miyasa kuka zo da ita har a Asibiti ba a sanar da mace mai ciki irin wannan tashin hankali”
“Nima ba a son raina ta sani ba” Haka kawai Momi tace mishi ta cigaba da kukanta.
Hannayenshi yasa aljihu ya sake ajiyar zuciya sannan ya nufi k’ofar ɗakin,
Tsaye yayi yana kallonshi bayan ya maida k’ofar ya rufe kamin ya k’arasa kusa dashi ya kira sunanshi “Yaya ya jikin naka?”
Daker ya masa mishi “Alhamdulillahi Siraj ka iso?”
“Eh mi kake ji yanzu?”
Bai bashi amsa ba sai kawai yace “Siraj Please ka kula da Momi sosai da kuma Abinda Mairo zata haifa nasan zasu iya shiga wani hali idan ba kowa kusa dasu musamman Momi”
Kallon rashin fahimta Siraj yayi mishi “Mi kake magana akai ne
?”
“Siraj bana jin zan tashi daga ciyon nan inajin ajalina yana kusa dani”
“Waya baka tabbacin ba zaka tashi ba?”
“Babu nine naji a jikina”
“Zafin ciyone kuma In’sha Allahu zaka warka”
“Nidai inason ka kula da Momi Siraj karka barta ta shiga damuwa”
Siraj zai sake yin magana yaji an turo k’ofar ɗakin, hakan yasa shi juyawa yana kallon Mansura da wata mata ke rike da ita, daga jiya zuwa yau kawai tayi wata irin rama idonta yayi bak’i kamar ba ita ba,
Har kusa da gadon matar ta kawota, ita kuma ta fashe da kuka tana kallon Qasin “Ina ni Allah ya ɗorawa wannan ba kai ba ina son ka Qasin sosai”
Cikin sanyin murya yace “Na sani Mansura shiyasa naso nayi rayuwa ta jindaɗi tare da ke naso naga jininki”
Durkushewa tayi gaban gadon tana kuka “Hakika na cutar dakai Qasin duk wani hakki da yake akaina naka banayi kana son haihuwa amman na dinga shan magani akan kar ka ɓata min rai ka kyale ni har mahaifa ta lalace ta yadda bazan iya haihuwar ba yanzu”
“Ba amfanin yin wannan maganar a yanzu ni dai Abinda nake so dake shine kada ki cutar da abinda Maryam zata haifa dan Allah”
“Duk abinda Maryam zata gaifa Qasin jininka ne bazan taɓa cutar dashi ba zan nuna mishi so kamar ɗan ciki na zamu bashi kyakkyawar tarbiya ba zamu sake faɗa nida Maryam ba zamu zauna a gida ɗaya zan rike kamar k’anwata nayi maka alkawari”
“Ba tashi zanyi ba Mansura dan haka babu anfanin yin wannan maganar kawai dai inason ki kula da abinda Maryam zata haifa kamar naki”
Kai ta girgiza tana wani irin hawaye “Bazan iya rayuwa ba kai ba Qasin ka sani”
“Na sani amman daga yanzu zaki soma”
Cikin kuka mai k’arfi tace “A’a Qasin ba zaka mutu ka barni ba ba zamu rabu da juna ba”
Nan Siraj ya kalli matar ake rike da ita itama tana kukan yace “Fitar da ita waje Please yana cikin zafin ciyo yanzu”
Ba musu ta kamata tana kukan suka fice.
Tashi shima yayi ya fice yan nashi hawaye,
Jinginawa yayibjikin k’ofar yana kallon Mairo dake kwance dafe da ciki bayan ya fito,
Can ya k’arasa kusa da ita yana kllonta rabon daya sata a idonshi tun ba’a ɗaura mata Aure da Qasin ba dan duk zuwan da yake yi sai dai yace yana gaisheta amman bai taɓa yarda sun haɗu ba koda sau ɗaya,
Tana kallonshi ta fashe da kuka “Siraj Yaya” Abinda ya furta kenan tana rike da mararta. Nan ya kalli Momi yace “Ko nakuda take ne?”
“A’a ba watan haihuwar ta bane cikinta wata takwas ne”
Nurses Siraj ya kwalama kira cikin hanzari suka iso ya nuna musu ita,
Bayan sun ɗauke ta yaje ya kira wata Dr mace dan ta kula da ita.
Baifi minti biyar zuwa shida da barin gurin ba Yarima ya iso, kana ganin shi shima zakasan hankalinshi a tashe yake. Kallo kawai yayi ma su Momi a atsayin gaisuwa dan yadda ya gansu cirko-cirko bai iya yi musu magana ba sai kawai ya tura k’ofar ɗakin ya shiga,
“Sannu friend Allah ya baka lafiya” Abinda yake faɗa kenan yana k’ok’arin k’arasawa kusa dashi.
“Yarima…” A hankalin Qasin ya kira suna shi. Amsawa yayi tare da jan kujera ya zauna “Na’am ya jikin naka?”
“Wata alfarma nake rik’o a gareka”
“Alfarma kuma Qasin kamar ta me?”
Ya dade kamin yace “Nasan ka tsaneni Yarima amman ina rokonka dan Allah kada k’iyayyar da kake min ta shafi Maryam ko abinda zata haifa Please”
Murmushi Yarima yayi idonshi cike da hawaye yace “I hate you no more Qasin banyi maka tsanar da har zai iyasa na cutar da iyalinka ba kuma duk wannan ma abaya ne na maka alkawari babu abunda zai sake shiga tsakanin mu”
“Yes babu kan tunda zan mutu zan tafiyata na bar duniyar”
Kafadarshi Yarima ya dafa “Zaka tashi Qasin zamu sake zama abokai kamar lokacin da muna k’anana”
“Bazan tashi ba Yarima i feel it” Idonshi cike da hawaye yayi maganar,
Hannu Yarima yasa ya toshe bakinshi ya lumshe ido. Suna haka Siraj ya shigo wata Nurse na bayanshi rike da akwatin magani,
Tun daga bakin kofa yace ma Yarima “Ka tashi ka fice yana cikin zafin ciyo yanzu baya buk’atar kowa kusa dashi”
Sai da ya buɗe ido ya sake kallon Qasin sannan ya tashi ya fice.
Sirinji Siraj ya ɗauka ya shiga ɗura mishi allura, yana faɗin “Ya kamata ka samu bachi yanzu”
“Karka min alurar nan Siraj”
“Dole ne ayi maka ita Yaya kana buk’atar hutu”
“Baka tsoron idan kayi min wannan alurar nayi ta bachin da bazan farka ba”
Tsayawa Siraj yayi cak. Sannan ya lankwashe alurar har ta sokar mishi hannu, da sauri Nurse ɗin ta aje abinda ke hannunta ta rik’e hannun shi tana faɗin “Calm down Dr”
Bai kulata ba ya shiga faɗa da Qasin idonshi cike da kwallah “Irin wa yannan kalaman naka ne suka haddasa matar nakuda ba lokacin haihuwar taba wadda hakan kan iya haddasa mutuwar abinda zata haifa ko kuma ita kanta, miyasa kake irin haka ne Yaya?”
“Siraj ba ko wane bawa bane idan zai mutu yake samun irin damar dana samu ta aiwatarda wasu abubuwan da halshen bakina ba”
Gufanawa Siraj yayi gaban gadon kamar mai rokon gafara yana kuka “Dan Allah kabar irin wannan maganar Yaya i don’t want to lose you”
“Of course you haka to” A wahale yake maganar,
“Taya kake tunanin ɗan’uwanka zai rayu idan ba kai a kusa dashi?”
“Ka dawo da aikinka a nan Siraj dan idan ka cigaba da zama Abuja abin zai yima Momi yawa”
Gefen rigarshi Siraj yasa ya share hawayenshi ya tashi ya fice.
*** *** ***
Two hours Mairo tayi tana nak’uda cikin ikon Allah Allah ya kawo mata sauki ta santalo kyakkyawan ɗanta,
Nan wasu Nurses suka hau gyara ta ita kuma Dr ta shiga cigaba da yi mata abubuwan da akeyi ma macce bayan cire ɗa.
Saida suka gyara shi tsaf sannan wata Nurse ɗin ta fita karɓa kayan jariri,
Bayan sun saka mishi kayan suka naɗeshi cikin tawul suka fito dashi suka mik’ama Momi dake kuka tare da dariya.
Mansura ce ta riga kowa karɓar shi ta manna mishi kiss a goshi sannan ta nufi hanyar da zata kai gurin da ɗakin Qasin yake,
A hankalin ta tura k’ofar ɗakin ta shiga Momi na bayanta kowanne fuskarsa da hawaye. Kusa da gadon ta tsaya tana nuna mishi jaririn “Maryam ta sauka Qasin mun samu ɗa”
Yana kallon yaron ya lumshe ido hawaye suka gangaro mishi suka shiga cikin kunnen shi sai numfashinshi ya fara rawa.
Taimakon gaggawa likitocin suka shiga bashi cikin taimakon Allah numfashin nashi ya dawo dai-dai,
Su Momi na tsaye waje cirko-cirko likitocin suka fito. Jiki na rawa Momi ta shiga tambayar ɗayan likitan “Yana da rai kuwa?”
Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan yace “Yana da rai amman abinda kukayi kasada ne babban dan ba’a nunawa marar lafiya abinda zai tada mishi hankali irin haka”
“Alhamdulillahi” Mansura ce tayi godiyar tana share hawaye, Doc yace “Daga yanzu kada wadda ya sake shiga ɗakin sai da izinin Dr”
Kai Momi ta gyaɗa dai-dai lokacin Siraj ya iso yana faɗin “Ance numfashinshi ya ɗauke?”
“Eh amman ya dawo yanzu komai na tafiya dai-dai” Dr ne ya bashi amsa
Kanshi ya shafa yayi ma Allah godiya Dr ya kalleshi yace “Dr Siraj kayi mishi tiyatar yanzu kaiwa dan akwai jijiyar da take taushe mashi numfashi kaga idan akayi komai zai zama dai-dai”
Siraj ya nisa yace “Nima haka nake tunani dan idan ace sai ya warke za’ayi toh kamar wani sabon ciyon ne kuma”
“Good haka nake nufi kuma kaga idan zai warke zai warke gaba ɗaya ne ba sai yayi jinya biu ba”
“Haka za’ayi amman sai naga tafiyar numfashinshi tukuna sai naga yadda abin yayi”
“Okey haka yayi amman karka sake bari wani ya shiga ɗakin koda Momi ce” Ya faɗa yana murmushi.
Kai Siraj ya kaɗa mishi yana kallon Momi sannan ya nufi ɗakin,
Saida Siraj ya ɗauki awa biu yana ganin tafiyar numfashinshi sannan yasa aka shirya mishi komai ya shiga ɗakin tiyata dashi,
Awarshi hudu ɗakin tiyarta har da yan muntuna sannan ya fito tare da wasu manyan likitoci, saida ya shiga wani ɗakin ya cire kayan daya fito dasu daga ɗakin tiyatar sannan ya nufo gurin su Momi.
A fuskarashi Momi ta karanci abinda ke bakinshi, da murmushi ya k’arasa yana kallon Momi da ita murmushin take idonta da hawaye.
“Anyi nasara Momi babu sauran kuka sai dai ayi adduu Allah ya bashi sauki”
Godema Allah Momi ta dinga ita da Mansura da sauran yan uwa da suke gurin,
Murmushi Siraj yayi ya nufi k’ofar ɗakin da aka chanja ma Qasin, a nan ya tararda Yarima tsaye hannayenshi sanye cikin aljihu,
Uffan Siraj bai ce mishi ba sai ma kauda kai da kuma yayi, murmusawa Yarima yayi ya mik’a mishi hannu yana faɗin “Congratulations Siraj”
Hannun nashi Siraj ya kalla sannan ya kalleshi “Banyi zato wannan daga gareka ba so tell me minene sirrin?”
Murmushi Yarima ya sakeyi yace “Babu komai Siraj kuma bana so ka sake daukata cikin makiyan Qasin no more”
Fuskarshi Siraj ya k’urawa ido nan Yarima ya k’araso kusa dashi ya dafashi “Siraj abinda ya samu Qasin ya karantar dani abubuwa da yawa just look at him da ace mutuwa yayi da yayi kyakkyawar cikawa kowa yana kuka da rashin shi ni kaina ban taba jiya n abinda naji game Qasin ba irin wadda na daga jiya zuwa yau,
Siraj Qasin yana da farin jini gurin kowa ba kuma komai ya jawo mishi wannan ba face kyakkyawar mu’amala da kowa”
Sukuku Siraj yayi yana kallonshi kamin yace “Yarima kaine da kanka kake wannan maganar?”
“Nine Siraj ina nadamar abinda nayi ma Qasin da ace ya mutu da bansa ya duniya da mutane zasu kalleni ba bansan abinda zan fadawa ubangijina ba”
Ajiyar zuciya Siraj ya sauke yace “Idan har da gaske kayi nadama ba afurincika kawai za’a gani ba a aikace za’a gani Yarima zanfi kowa jindaɗi idan ka zubarda duk wani mummunan hali nake ka chanja rayuwarka ka maida kanka ba kowa ba,
Mulki fa ba ya dawwama kamar yadda sarauta bata dawwwama dole ne ka barsu ko su barka shin idan da tunani mutuwa miya zau kawo girman kai da ɗagawa baka fi kowa ba a gurin Allah kuma babu wadda ya fika sai wadda yafi wani tsoron Allah,
idan har da gaske ne toh zanfi kowa farin ciki da haka”
Yarima yace “Inason ka zubarda duk wani kallo da kake mi na marar kyau hali ko kuma wadda zai iya cutar da kai ina son mu koma normal bida Qasin”
Murmushi Siraj yayi “Nima zanso haka sai dai har yanzu gani nake kamar ba Yariman dana sani bane”
Murmushi kawai yayi ya juya yasa hannun shi aljihu ya nufi kofar da zata fitar dashi daga gurin gaba ɗaya,
Da ido Siraj ya bishi har ya fice,
Kai tsaye gida ya nufa gurin hajiya,
Parlor ya sameta kishingiɗe ita da bak’inta suna fira, tana ganin shi ta zaune yana kallon shi.
‘Daya bayan ɗaya ga bisu duk sai da ya gaishe su, sannan ya nufi cikin ɗakin,
Ba Hajiya ba har ba har su saida sukayi mamakin abinda yau Yarima yayi musu abinda bai tanaɓa.
Tashi Hajiya tayi ta tufa mishi baya zuciyarta cike da tambayoyi ta shiga ɗakin,
Yana ganinta ya sakar mata murmushi “Hajiya ta?”
“Na’am Yusuf”
Sai ta zauna sannan tace “Ka chanja Yarima fiye da yadda nake tsammani ka fara zama yadda nake mafarkin zaka zama”
“Yafiyarki nake nema nasan na ɓata miki da yawa”
Kai ta girgiza mishi tana murmushi “So nawa kake so nace na yafe maka Yusuf? Na faɗa maka nida Mai Martaba tuni muka yafe maka babu sauran ɓacin ranka cikin ranmu”
Dukawa yayi har k’asa yace “Hajiya ina neman wata alfarma agareku?”
“Ka faɗi ko minene zanyi maka shi Yarima”
“So nake ku zaɓa min matar Aure keda Mai Martaba”
Wani irin daɗi Momi taji sai kawai idonta suka cika da kwallah.
“Na gode Yusuf Allah yayi maka albarka zamu zaɓa maka matar data dace da kai In’sha Allahu”
Tashi yayi tsaye ya rumgume ta ya lumshe ido.
*Wannan kenan*
***
Ranar da Mairo ta cika sati ɗaya da haihuwa yaro yaci suna Yusuf sunan Yarima akayi mishi lak’ani da little Yarima sosai Yarima ya jindaɗi karku so ganin irin kayan da yayima jariri da uwar shi,
Aɓangaren su Momi basai na faɗa muku irin kayan barka da ta zuba ita da mutanenta ba dan kusan hausawa sunce abu namu…..
Su Gwaggo kan bana cewa komai dan nasu farin cikin baya faɗuwa,
*** *** ***
Ciyo ne yake zuwa nan take amman Lafiya sannu-sannu take Shiga haka Qasin ya cigaba da jinya yana samu kyakkyawar kulawa daga ɓangaren mtanshin da kuma Momi, Yarima da Hajiya ma ba baya ba kusan kullum sai yajs Asibitin har ya samu sauki aka sallame shi,
Ranar daya dawo gida Mansura da Mairo kamar su zuba ruwa k’asa su sha dan murnar, anan gasa ta shiga tsakaninsu kowace ta rik’a k’ok’arin ganin ta kyautata mishi kuma suka haɗa kansu kamar babu abinda ya taɓa shiga tsakanin su,
Bayan wata hudu da sallamar Qasin daga Asibiti aka ɗaura Auren Yarima da Amaryar da Hajiya ta zaɓa mishi yar wani tsohon kwannan katsina,
An zubarda nera tsayawa faɗa muku irin shagulgulan da akayi a biki ɓata lokacine, manyan mutane suka halarci bikin ta ko ina.
***
Bikin shi da wata biu akayi na na Siraj da Amaryar shi a Abuja akayi komai can ne Mansura ta ziyarci wata Asibiti mai zaman kanta dan a duba mata lafiyar mahaifarta.
Duk wani bincike da ya dace saida likitocin sukayi sannan suka tabbatar mata da bazata iya ɗaukar ciki ba dan mahaifarta ta lalace sosai ta yadda bazata iya rikon ciki ba,
Bakin ciki Mansura tayi sosai tayi dana Sanin abinda tayi.
***
Little Yarima nada shekara da wata biyar Mairo ga sake samu ciki. Murna gurin Momi da Qasin ba’a magana, Qasin kamar ya haɗe ta dan farin ciki.
Cikin jindaɗi ta kwanciyar hankali tayi fa rainon cikinta har ya girma ta haifo yan biu duk mata, aiko lokacin ne Qasin yace bata ga komai ba indai so da kauna ne yanzu na fara nuna mata shi.
Mairo tayi sani fari tayi bulbul gwanin shawa’awa Mansura ma ba bayab dan duk wani bacin rai nata aje shi tayi gefe suka rika juna ita da mairo kamar ba kiyashi ba ba zaka gansu kace wani abu ya taba shiga tsakanin su ba,
Aɓangaren Yarima ma ba shida wata matsala shida matarshi farin ciki ne da jindaɗi kawai a gidan duk wani hali nashi marar kyau ya zubar suka koma shi da Qasin kamar AMINNAN JUNA, Momi tafi kowa farin cikin ganin halin da su Qasin da Yarima suke yanzu,
Ita da hajiya suka koma kamar yadda suke da komai normal.
Suka shiga wata sabuwar rayuwa mai cike da jindaɗi.
TAMMAT BIHAMDILLAH!
Oh Allah hope for your mercy. Do not leave me for myself. Correct all of my affairs for me.
Anan na kawo karshen wannan littafin mai suna MAIRO kurakuran dake ciki Allah ka yafe min yar karamar faɗakarwa dake ciki Allah yasa mu anfana da ita, duk da ba a nan naso na tsayawa amman ku kuka hanani kashe Qasin 🤷🏿♀.