Makaranta duniya chapter11

Makaranta duniya

            Chapter 11

wannan sifarba. Saidai bani da abin yi, face ince na danka wa ‘Allah’wannan al’amarin. ‘
Domin shi kadai yasan dalilin‘da yasa ya saukar min da wannan jarabawar, kuma ina rokon daya nufeni da cinyewa”. Ya mike ya bar ofishin, ba ‘tare‘da Alhaji Bara’u ya iya koda mutsi ba.
Mintuci barkatai sun shude, bayan shigowarsa ofishinsa, yana‘tsaye jikin taga batareda yasan ma yake tunaniba. Amma a hakikanin lamari. Alhaji Bara’u kawai ke daure masa kai. “Sannu da zuwa Alhaji”. Kalaman ne-sukadawo da‘hankalinsa jikinsa.
Ya juya ya dubi mai magana. ‘Masinjansa ne tsaye “Malam ilya”. Ya amsa “Ranka ‘ya dade, ya iyali, ya wajen mai jiki?” Yace “Alhamdulillahi!” Yace “Allah ya‘ kara sauki”.“.Amin
Ya juya zai fita. Alhajin yasa baki ya kira shi ya dawo “Don Allah kaje wajen‘Sakatare ka amso min files
dinnan na shekaran jiya da kakai masa To ranka ya ‘
dade”. Ya fita da sauri. Kafin ya dawo. Al‘hajin ya tattara
duk wasu takardu muhimamaiwaje daya. Yana cikin ware nasa komatsan. ‘Masinja ya. dawo ya: mika .masa sakan. “Yauwa an-gaisheka. Ah! Malam ilya”. ” . “Ranka ya dade”. ‘Ya dube shi’ da kayau. Yace “Ka san komai yayi farku,’zai yi karshe. sabuda haka nakeson  gaya maka karshen zamana a wannan offis din ya
So ina fatan zamu yafi juna, koda wani ya sabi wani bisa kuskure, kasan zaman tare
Malam ilyA ya wangame baki.‘Yace “Ci-gaba aka samu ranka ya dade? Kai madalla-madalla. Allah ya taimake ka Yallabai, sai dai kuma mu ne zamuyi rashi, ga koshi ga kwannan yunwa”. Alhajin yayi dan murmushi. ‘ – Yace “Ba haka bane; aikaga (oditor‘s) daga
Lagos? To bincikene yazo kaina, wanda nake ganin zaiyi wuya na haure shi. Ina ma kowa fatan alheri ‘tare da’fatan zakaci-gaba da rike amanar‘ aikin ka, kamar yadda ka saba’Jikin Malani Iliya ya mutu murus! Ya dauki salatin Manzo’tare dayiwa Allah tasbihi. Sannan Yace Ban yarda ba ranka ya dade, kowane irin bincike’ne wannan. a akwai sharri da munafunci a ciki, kuma da yardar Allah zasu ji kuya Allah‘ yana tare da mai gaskiya”.
‘ Ya numfasa yace “Haka ne, kana‘iyatafiya. na gode”. Ya jima tsaye yana jinjina‘ kai. Ya juya hannunsa kame da ‘bakinsa yana fadin “Allah ka rabamu da sharrin mutum da aljan. Wannan wane irin zalunci ne?” harya bude’kofa, ya sake juyuwa.
Yace “ranka ya dade kar ka damu. Allah bazai ‘ kyale duk mai hannu a cikin Wannan maganaba”. Yace
“Allah ya yarda’Malam lliya, nagode”.~
Yace “Na gode Alheji Belarabe. amma karka manta. na shige ban daukaba. bata fidda barawo”.
“ karkace haka Yellabai. kowa yasan irin yaddah kake  kamanta geskiyela Sennan tsawon zamana a wannen campanyn ban tabajin an kakamaka DA wani laifi ba
Har yenzu akwi damar da zamu nuna  cawe babu hannunka a wannan lamarin wasu ne kawai suke make maqarqashiya
. Yece “Kalamankela bazasu zama hujje-ba a gaban gwomnati. Rashin kamani da wani lefi a can baya  zai wankeni daga wannan lamarinba
’ Anin bukata kawai itece addu”a.don samun saukin lamerin”. Sakataran ye sauke numfashi  Yace “Allah na nan kuma zamu yi make addu”a
Yace “Na gode Alheji Balarabe. Aci=gaba da gudanar de aiki yadda ya kelamata Kona dawo ofiis dinnan. koban dawnoba ine rokon kada ka tsere gelaskiye
Yace “inshe-Allhu alhaj  Yace “’Shi kenen ka koma bakin aiki Ni zan wuce in fare duba jikin Baba, sannan in wuce inde eke
neman mu Ya mike yayi masa fatan alheri. ya fita .
Hajiya Suwain na kicin ta dukufa girke-girken da take son kaiwa su gwagg a asibiti. Tsayuwar motar Alhaji taji, ta dauki hankalinta, cikin ranta take fadin‘
“Taf! Har Alhaji ya dawo ban~ gama komai ba?”
‘ Ta juya miya ta fito falo da sauri, ta tarbeshi. Wai harkA dawo ne?”
Tasa hannu ta karbi takardun daya shigo dasu. yayin da yake cewa “Baki shirya ba kenan”.~ Tace “Ai’kaika sai yara sun dawn. Miya ma nakeyi wa Gwaggo . .
Ya zauna a kujera ya cire hularsa ya‘ aje gefe, ya dubeta. “Ai kuwa kin kyauta da ki kayi mata miyar’. Ina: Babana’?” “Ya koma barci tun da nayi masa wanka”. Yace.
Da kyau’Ta wuce dakinsa, don aje takardun. Ta fito kai tsaye kicin ta sake shiga ta juyu miyarta, ta dawu ta sameshi ido runtsé, fuskarsa na kallon silin. Ta kare masa kallo,’ta dan kada kai kafin ta zauna a hankali ‘gefensa. “Alhaji
Ya bude ido da sauri ya dubeta. Ta karasanyaya. murya tace “cuta ba mutuwa bace Alhaji, da yardar
Allah Baba zai tashi. Kayi hakuri ka kwantar da hankalinka
‘ Ya aje numfashi a‘hankali.-Yace “Akwai matsala Suwaiba”. Hannunta a kirji ta tambaya‘ “Matsala? Inna- ‘LiIlahi’wa-lnna-llaihir—Raji’tjn! A ina Alhaji?” YaCe”A  ofis, Suwaiba’ na fada tarkon da Allah ne kadai zai‘iya
dani”. A firgice ta kara matsoshi. “Meya faru Alhaji?” ‘
Yace”Aina gaya miki (oditors) zasu zo yau. Ashe bincike ne na musamman aka’ turosu akan wani janerata da aka ‘kama za’a fita da shi kwatano. Janareton da aka kai Fanbeguwa ne, don basu wutan lantar’ki kuma= bahban gaske ne, kudinsa sun tasarwa miliyan goma”.
Idanuwanta ‘suka kara yo waje, ta maimaita “Goma? Tokai menene naka a ciki Alhaji? Na tabbata ba: ”
zasu kamaka da laifin komaiba”. Ya kada kai,_yana
dubanta; “Haka kike zato Suwaiba, ‘amma hannuna dumu-dumu aka samu a ciki”: “Ban ganeba Alhaji?”
Yace ‘Nima ban gane komai ‘ba Suwaiba ban. kuma San yadda akayi ba amma ga takardu zahiri Sun nuna sa hannu na. Ma’ana da amincawa ta aka fita da
Injin  wani abin mamaki, wai nida kaina na bada cin hanci akaiwa (oditor‘s) din .” Yace “Miyarki na konewa, ga qauri can inaji ta mike cike da mamaki cikin azama ta fada kicin din, ta sa hannu ta murda (Gas cooker)  ta dawo da’sauri ko motsa ‘miyar’ batayiba. Ta zauna ta  sake zubo masa ido. . .
Yace “Kin yar’da ba’a mafar‘ki bane, tunda naji kaurin miyar ki’?” ldanuwanta suka jirkita, a raunane. Tace“ “alhaji ban yarda daya‘ daga cikin wadannan
abuubuwa zai fito daga gareka ba. Ya kamata a zur’fafa bincike a gano wadanda suka ce ka’aikesu da cin hanci”.

Yace “Ai ba’a boya sukeba. Mr. Balagune da llhaji Bara’u ne”. Fuskarta ta kara tsananta cikin mamaki “Alhaji wa’?” Ya yi dan murmushi.
Yana “Ni kaina ban yarda ba Suwaiba. Da ace labari aka gaya min, duk rantsuwar’ mutum ba zan aminceba. Saidai ya zama dole in yarda, tunda a gaba na suka sake maimaitawa”. ‘
Jitayi kamar, numfashinta zai dauke, shi yasata kara dafe kirjinta; kwalla- suka cika idanu’wanta. Ta fara‘ salati tare da tasbihi ga Allah. “Alhaji Bara’u?”,Ta sake maimaitawa. “To yanzu ya ake ciki da maganar?”
Yace “Zamu kai kan mu ofishin bincike,ne sai kuma abinda Allah yayi. Shi yasa na dawo in shaida . miki. ldan mun sami fitowa DA wuri, zaki ganni na dawo’
ldan kuma basu bariba, zan turo Magaji-Yazo ya kaiku ‘Zariyar’ ku dubu jikin Baba; Amma karki gayawa gwoggo komai, kar tashin hankalin yayi mata yawa”.
Tuni hawaye suka tsunke mata, fadi take. “Amma mutum butulu ne. mutum, mugun icce ne Alhaji.- sakamakon mu kenan a wajan Alhaji Bar’a’u?” Yakai hannunsa bisa kafadar ta.
“Natsu ki kwantar da hankalinki Suwaiba. Shi mai gaskiya, ai yana tare da Allah. Kuma ita duniya. ai
makaranta ce, baka ganewa, sai‘ darasin ya
bayyana muraran a idonka, kaganshi. Sharrin zuciya ne
kawai ya debi Alhaji Bara’u ya aikata wannan danyen aikin. Na tabbata sai yayi nadama tunda ba’a ci‘ribar abin ba”. ‘
Baki na rawa ta amshe. “Ai alhakin ka ba zai bari suci riba ba Alhaji, sannan da yardar Allah ba zasuyi nasara a kanka ba, wanan wane irin zalunci ne da aikin son zuciya? Wane irin mugun butulci ne kuma?”
Ta kara sarkewa cikin kuka. Hankalin ‘Alhaji Abdul-Rasheed ya kara tashi, ya dan kada kai‘ YaCe “Ki daina kuka haka Suwaiha, al’amarin nan, addu’a kadai . yake bukata. Ni yanzu abinda yafi damuna shine‘ jikin Baba, sosai hankalina ke kansa.
Ya ka‘mata ace yanzu ina tare dashi, saboda Baba yanacikin wani hali mai dagula’ lissafi. Ki share . fuskarki, kuma ki tattaro’dukkan natsuwar ki, domin banason yarannan su fahimci kamai tukuna …… ”
“Wane yara Alhaji? Kana nufin’ su Nasiru? Ba‘ zan boye maka ba, yadda na ke ganin ubansu bakikkirin! Haka na tsani zamansu cikin gidan nan”; .Ya numfasa
yana kallonta. “Laifin wani, ai baya shafar Wani
Suwaiba, “Yana shafa Alhéji, kuban korisu Nasiru‘a 
gidan nanba. UbanSu zaisa, ko kuma sauyin fuska ta ya
koresu. Ba zan iya jure abinda‘suka yi makaba Alhaji.
don sun zalunceka, duk wanda ya taba ka kuwa. har  abada hana ganin farin sa Alhaji”.
Ya koma kan kujera ya jingina, ransa ya dada baci. Ya tsani maganganun Hajiya Suwaiba gaskiya ce. amma rama mugunta da alheri koyine na Manzon tsira. Ya numfasa. Yace “duk nasan haka Suwaiba.
Sai dai ina so ki kasance wanda Allah yake so kuma yace yana tare dashi har kullum, watau masu hakuri. Musa ido muga karshen wannan kura data taso
Sannan mu jira mu ga wane mataki Alhaji Bara’u zai dauka na nade tabarmar kunyarsa? Ina fatan kin fahimce ni? Kuma za kiyi ‘aiki da shawarata”;
Ta share fuska da gefen zani. Tace “Naji Alhaji. Allah ya kubutar da kai, su kuma yayi masu yadda sukayi maka”. .
Yace “Amin. Ni zan koma, ki tabbatar da kin gama miyar nan, don, nayi farin-cikin jin céwa kinawa gwaggo miyar. Ki tsaida hankalinki waje daya, saboda banason kowa ya fahimci wani abu, kinji?” Tace “lnsha- Allahu zaka; sameni da cika umarninka. Allah’ya jishe mu alkhairi”.
Ya mike yana fadin. “Amin summa amin”. Ya maida hularsa bisa kansa, yayi waje tana binsa a baya har gaban mota. Magaji ya taso ya gaisheta, sanan suka wuce ba tare da sun kara cawa juna komai ba.
Ta dawo gida a sukwane ta nemi kujera ta zauna, hannu biyu bisa kuncinta. Kawai hawaye ne shar-shar! Suka tsunke mata. Tsawon lokacin bata san meke damuntaba. Kukan kadai take ta faman yi, sannan ta
tuna da kalamansa.
Nan da nan ta mike ta shiga bayi, ta wanke fuska ‘
ta koma kicin taci-gaba da girke-girken ta. tana yi tana
yiwa Allah tasbihi, don hakane kadai zai sa ta sami
salama cikin ranta.
Karfe daya daidai samarin uku suka tsero daga makaranta, babsu tsaya yin (Lesson) ba. Sukayi sallama, ta amsa tana daga inda take zaune bisa kujera, hannunta a kunci. Zumbur! , ,
Ya’diru .da murnarsa yana fadin “Yaya! yaya Kai tsaye Nasiru ya nufa ya cafe shi. “Imam Yusuf! Ya gida? Ya Mamanmu?”,
Ya nunata da hannu, yana dariya. Yace “Gata nan”. Suka karasa tare. “Sannu Mamanmu”. Ta amsa fuskarta babu walwala sosai. ‘
“Baban bai shigoba ko?” Inji Suleman. Tace “Bai shigoba, na dai san yana hanya”. “Bari mu shirya kafin ya iso”. Suka wuce dakinsu ba tareda ta amsa ba.
Imam yana biyedasu har suka gama kintsawa,sukafito
cin abinci. Hajiya Suwaiba na ~nan zaune hannu a kunci.
Suleman da Khalid suka wuce ta. Nasiru yaja ya tSaya.‘
ya kare mata kallo sannan ya dan rage tsawonsa. Yace “Mamanmu”-
Ta dube shi a natse.‘ idanuwanta duk sun kada saboda damuwa. Cikin taushin murya ya tambaya. “Lafiya kuwa Mamanmu? Fuskarki babu walwala tunda muka shigo
Ta dan numfasa. Tace “Babu komai, ciwon kai naketa fama dashi tun safe”. Yace “Ayya!-Sannu, amma kinsha magani ko?” Tace“Nasha. Kaje kuci abinci, bari inyi sallah kafin ya dawo”. Ta mike, sauran na mata sannu. Ta amsa ta shige dakinta. Tayi alWala, ta yi sallah, ta daga hannu. sama ta roki Allah sauki da taimakonsa.
Har karfe biyu babu labarin Alhaji. Hankalin Hajiya SuWaiba ya kara tashi, zuciyarta ta rasa dukkan natsuwa. Ta saka wannan, ta saka’wancan ita kadai cikin daki bisa sallaya.
Wani lokacin idanuwanta suyi taf! Da hawaya, amma tayi kokari ta- shanyesu. Biyu da kwata‘taji tsayuwar mota, tayi wuf! Ta mike tayo waje. Tana isowa ’ tsakar’ falo. Magaji na sallama. ‘ .
Gabanta ya yanke ya fadi, kanta yayi dum! Yana hada wani sauti maras dadin ji. Cikin sanyin jiki ta amsa masa, haka shima a sanyaye yake ‘fadin “lnji ‘Alhaji wai idan kun-shirya kuzo in kaiku Zariyan”.
Ta hadiyi miyau da kyar. Tace “Bazai sami zuwa banE?” Yace “Basu gama abinda sukeyi bane, amma Yace in gaya miki ki kwanatar da hankalinki, lafiya lau yake”.
Ta ajiye numfashi da karfi.‘ Tace “Shi kenan’ :
bari mu fito”. Yayi waje, ita kuma ta buga kofar samarin‘
ta tura ta shiga, duk suna gyangyadin‘ barci ya tafi dasu, har da dan autan nasu. . Ta bubbuga kofar‘ da karfi, kawa ya buda ido,
suka dubeta “Ku tashi mu tafi”. “Yazo?” Tace’ “Da .
Magaji zamu tafi, har yanzu (oditurs)’din .basu tafi bane”. Tayi waje, ta bar su suna gyare-gyaren fuska.
gwaggo na zauna gaban gadon tanayi masa’
fiffita. Magaji ya jagorancesu zuwa dakin. yana dauke da wasu kayyayakin a hannunsa. Ta mike zuru har suka karaso- wajan, suka zagaye shi ana ta gaishe-gaishe. “da alama jiki ya yi kyau, tunda aka cira (oxygen) din?” .
. lnji Hajiya Suwaiba. Gwaggo “Alhamdulillahi! Tun sha biyun rana aka cire, har munyi magana, yana‘ tambaya ta Alhaji, nace masa nan, ya “kwana da kyarma ya tafi ofis. Yana ina ne?”
Tace”Bai sami dawowaba, saboda basu gama da bakin nasubane. Amma nasan komai dare ya gama dasu zai taho, don shima hankalinsa nanan”. ,.
“To Allah ya kawoshi lafiya”. Ta jawo kayan da suka .kawo. ta mika mata. “ga miya gwaggo,
ga wadannan biredin. Wannan kular .kuma farar shinkafa ce Ina Mairo ne?” _ Tace “Ta je gida yin wanka. Sannu. Suwaiba
Allah yayi albarka”. “Amin”. Suka yi shiru suna ta kallon Baba Liman, yana barci. Bai farka ba, sai gab da magariba, suna shirin tafiya; Kowa ya juya gareshi, yanagaishe shi. ‘
Daqar yake iya, amsawa, saboda har yanzu
‘numfaShinsa baya SaUka Yadda ya kamata. “Ina AbdulRHShEd; Suwaiba?” Ta kara matsoshi. Tace‘
yana office baba amman yace daga  da yardar Allah”zaizo ya dubaka komin dare. Murya dishe yace ki gaya masa karya biyo dare, yabari sai gobe in ‘ ranmu yakai. Kinji”. Tace, ‘
“To Baba, Allah ya kara lafiya. yasa kaffara ce”; “Amin Suwaiba, ina takwara na?” Inna Mairo ta matso dashi a hannunta. Tace “Gashi nan Baba, tsuro yakeji ya
.ganka a kwance”.
Ya miko hannu a hankali yarike nasa, ya yi zuru yana kallonsa. Maganar Hajiya Suwaiba ce ta dawo da hankalinsa garesa. “Bari mu wuceBaba kar dare ya yi
‘ mana a hanya”. Yace “Ya kamata. Sannunku ’na gode, na-
‘ gode”.
_ Ya dubi samarin duk jikinsu yayi’sanyi. baSU ko’iYa magana. Yace kunata kallon  ko? Kar’ ma kusa “ran cin gumba”. kowannensu yayi mUrmUShi
Suleman yace “Mudai bamu ceba, likitocine mu
tsayawa mukai muga tukunyar (Oxygen) nawa zaka zuke”.’ ‘ Sukayi ‘yar dariya. Baba Liman ya bisu da kallo Hajiya
Suwaiba tace “Mu tafi ko?” ‘
Duk suka sallame shi, suka yi waje. Hajiya Suwaiba kE baye.  taga lokacin da’Baba ya kirata da karma; “Me kakeso Baba?” Yace.
Bana- bukatar komai Suwaiba. Zan aike kine Wajen” mijjinki. Ki gaya masa Allah ya yi masa alharka; sannan karya kuskura ya biya hanya cikin dare. Kin ji?”
Bata san me yasa idanuwanta suka kawo kwallaba. Tace “Insha—Allahu zan gaya masa”, ‘
Yace‘Karki manta sakonnan Suwaiba,” ki gaya masa yana tare ‘da albarkata, saboda *haka ‘yayi zamansa. Sai Allah ya nuna mana goba”,
“Ma‘zaisa na mantawannan habban sako Baha’? Tamkar a kunnen Alhajin ka fadi maganar nan da yardar Allah”. Ya dan numfasa. Yace ‘Allah ya sauke ku lafiya“. “Amin Baba, Allah ya kara laliya”. Ta Wuce, yayin .da yaka amsawa.
Suna tafe, .zuciyarta na sake-sake kuma tana mata kuna kwarai da gaske. shi yasa bata iya magana da kowaba, har’Allah ya kawosu gida lafiya. A zatonta 2asu iske Alhaji a gidan amma basu iske shi ba .
Take nan ta juya kan Magaji taci-gaba “Don Allah
muje ka kaini wajan’Alhaji”.,
samarin‘suka bude gida ‘suka shiga, tare da Imam dake sharar barci Gasu nan ga su nan har ofis din bincike. Sai dai an kulle. domin dare yayi.
lta Hajiya Suwaiba bata tu’na cewa dare yayi ba za’a sami ma’aikatar a budeba Hake suka dawo zuciyarta cunkushe, tana faman tambayar Magaji. “To ina Alhaji ya nufa? Ko sun kama sune?” ,
Magaji’ ya sauke numfashi, ya-dan kada kai. Yace “Nima alamarin ,nan yana ban mamaki Hajiya, gaskiya Mai.gida yana bukatar addu’a, don makiya‘sun shirya masa sharrin su”. ‘ ‘ ‘
Ta runtse ido, tana sauke nUmfashi, kafin. Tace “tabbas haka ne. Kuma Allah zai tona asirinsu. baza suyi nasaraba da yardar Allah. Matsala ta yanzu, in san halin da yake ciki”; Magaji yace”Toko’ yabi motar’ haya ne?” “Kana nufin mun sha bamban?” Yace “Haka nake nufi”. Ta dan yi shiru, tana kokwantu mai yawa.
Sallolinta ta idar’ tana zaune bisa sallaya hannayen ta biyu, ta zabga tagumi, can kasan zuciyarta kuwa itakadai ta san yadda takejinta. Nasiru ya turo kofar tare da sallama. baiji _ta amsa ba:
Dan haka-ya shigo yana kara maimaitawa Sallamarshi har’ ya iso gabanta. ya_tsugunna Mamanmu”. Ta dubeshi a firgice. Tace “Ya dawo ne?
Yace.”Wa?” “Alhajin”. Ya kada,kai, yana “Bai dawaba”. Ta sauke numfashi ta kauda kai gefe, tana tasbihi cikin ranta.‘ Ya zura’ mata idnojim, ka na ya tambaya. ‘Tun da muka dawo makaranta, na lura kaman kina cikin damuwa Mamanmu. Me yake damunki ne?” tace Babu komai Nasiru, jiki nane bana jin dadinSa”. Yace”.Ayya, kinsHa magani  Tacé “Nasha”. Yace-“Allah ya sawwake”.”’” ‘ ‘ Amin, kun ci abinci?” Yakada kai. Tace “Toku ‘ je ciki ku zuba, akwai komai a kuloli”.- Ya mike ‘yana fadin. “To”. Ya fice ya bar Hajiya Suwaiba taci-gaba’da ‘ tunaninta. Duk da cewa hutulcin da Alhaji Bara’u yayi masu. ‘ ’ ‘ Yasa tana jin haushin‘ yaransa amman Nasiru ya. ‘ burgeta, kuma ya gwada dan hankalinsa, tunda ya lura tana cikin damuwa. Daran nan batayi barci ba. haka kuma bata kai lomar abinci bakinta ba. . Karf‘é bakwai tana cikin kicin, ta tsinka yi muryar Imam yana buga kofar Alhajin yana kira “Baba! babal!” : Ta fito da saur’i ta’nufi gunsa. “Imam ka tashi ne?” ‘ , Ya’ dube ta Yace “Baba zani” Ya ‘juya yaci- gaba da kwankwasaWa, har’ yana fadi da’bakinSa “Kwan- kwan’, Baba!” Hankali tashe tasa hanu ta dauke shi. Tace “Babanka haya nan Imam…..-..”
Ta murda kofar. suka shiga, “Ka gani? Baba baya “nan. muje a wanke baki. ka sha Tea”. Suka fito yana yan surutai. A tsakar falo ta yi kicibis da Sulaman yana . “Ina .kwana Mamanmu?” Ta amsa lafiya lau”. Ya kama hannun Imam. _ ‘
“Kai tsoho. yaka kwana?” Bakinsa har’ kunne. Yace.“ “Lafiya lau”. Kamar yadda yaji Mamansu tace  ta wuce Suleman, yaSake tambaya. “Yau saura kwana uku ziyarar’ su Murja ko Mamanmu?”
Nan da nan haushe ya kumata,« ta watso masa . wani irin mugun kallo. Tace “Ban saniba”. Nan take shima ya sauya fuska; jikinsa lakwas‘. Amma kafin yace” wani abu. ta bar wajen. , ,
Ya jima tsaya, Sannan ya biyota’dakin. Tana cikin bayi, tana shafa man wanke baki akan bUrosh. Ya tsaya jikin kufar ya tambaya. ‘ .
“Meya faru Mamanmu?” Rai bane ta dube shi. “Kai baka~ damu da komaiba; sai abinda ya shafeka. Kana sane Babanka bai kwana gida ba, amma ba ka damu ka tambaye shiba.‘sai ziyarar Murja! Murjar me?” ‘
gabansa ya‘ kara faduwa, a raunane. Yace “Ai na ‘ zaci daga ofis ya wuce Zariya ne gano jikin Baba”.Fadar hakan yasa jikinta ya mutu, har ta yi nadamar fadan da tayi masa. Ta dan numfasa. Tace. ‘ ‘ .
“Haka ne, jeka ku kar’ya, karku makara”. Yace “Me yasa ki kai min fada Mamanmu?” Tace “Haushi ka bani, aiko ka’na zaton akwai inda Babanka ya kwana, ya kamata ka tambayeni shi. Wannan shine zai tabbatar min daka damu da shi”. ’
Ya gyara tsayuwa, duk da ransa ya dan sosu, bai nuna mataba. Yace “Amma dai Mamanmu kin razanani Wallahi na zaci wani laifi Murja ta yi miki, kika gwasile ’ maganarta”. Tace “Batayimin komai ba, in banda abinka, ina zan ganta harda zatayi min laifi? Kawai fushinka nE ya shafeta. Jeka karya
Ya juya fuska cunkushe, don Mamansu tai bala’in bashi haushi. Ta rakashi da’kallo harya. fice. Ta tabe baki. Tace a ranta “Hmm …… Yaro man kaza, zan ga . yadda‘za’ayi wannan abu”.
Ta juya bayi ta wanke wa‘imam baki, ta shiryoshi ta fito dashi falo don shima’ya karya. Duk suna bisa tebur suka gaisheta, sannan su biyun sUka témbaya. a ‘ “Baba ya wuce Zariya ,ne Mamanmu?” Tambayar ta sanyaya ranta, amma bata kai ga basu amsa ba. Magaji~ ya shigo da sallamarsa
Don  haka ta kwashi sauri ta nuFI kofar, ta bude tana amsawa “Magaji”. “Na’am Hajiya, ina kwana?” “Lafin lau”. Yace “Dana fito yanzu na sake komawa inda su Alhaji suke na bincika,’gaskiya akwai magana Hajiya”
‘Jikinta ya dauki rawa ta fito’sosai, suka tsaya a koridon. “Me yafaru Magaji?” Yace”An gaya min su
Alhaji na hadikwata. saboda Alhaji Bar’a’u ya gudu, watau shi baije ofishin ba. kamar yadda’aka bukacesu, shi yasa aka ce a tsare su, kar’ suma su gudun”.
Take nan duhu ya lulluba idanuwanta, ta dafe
kirji. Tace “Shi kenan ta faru, ta kare Kai. “Inna-Lillahi’wa-lnna-llaihir-Raji’un! Yanzu menene abinyi Magaji’?” Yace “Ki kwantar da hankalinki Hajiya. Allah yana tare da Alhaji, don yafi kowa sanin zaluntarsa akayi. lnsha-Allahu. bazai wulakanta shiba. kuma gaskiya zata bayyana; Mu taya shi da addu’a
kawai”. . ‘ ldanuwa taf da kwalla. Tace “Kana ganin za’a barni in ganshi a hedikwatar?” Yace “Ban tabbatar ba. amma idan na ajesu Sulaman makaranta, zan koma in ci-gaba da bincikawa, duk yaclda akayi, zan dawo in gaya miki”.’Tace “To shikenan, ina jiranka”. Ta dawo cikin falon, kai. ‘tsaye daki ta wuce, samarin suka rakata da kallo. ” ‘ ‘ ‘ BaYi ta shige ta kulle, kuka ya kubce mata. Tayi shi sosai, ta share hawaya, tasa ruWa ta wanka fuskarta, ta-barwa Allah al’amar’in. Tana fitowa tsakar daki. ta
tsinkayi muryoyin samarin na fadin. .
Mun wuce Mamanmu?” daga ciki ta amsa “Ku dawo lafiya”. Tayita zama cikin daki. ta kasa tabuka komai
a cikin gidan. sai addu’a da rokon Allah daya kawo masu daukinsa.
Karfe guma Magaji ya dawo mata da bayanin ba za’a ga Alhaji ba, har sai an kama Alhaji Bara’u. Jikinta ya gama mutuwa, yinin nan kaf! Bata san inda zata tsoma rantaba. ‘ Karfe biyu su Suleman suka dawo makaranta, sannan ta tuna babu abinda za suci. Tana kwance bisa doguwar kujera. Nasiru ya zuba mata’ ido “Har yanzu jikin ne Mamanmu?” Tace “.‘Wallahi kuwa, yau ko abinci ban girka-‘ maku ‘ba”. cikin tausayi Khalid yace “Wayyo, sannu Mamanmu; bari in ajiye jaka, in shiga kicin din ko Taliya‘  in dafa mana”. Tace “To”. Suleman’ yayi dan guntun tsaki, ya wuce yana ” fadin “Yau jagwalgwalo kawai za muci”..Suka bi bayan sa, suna bashi amsa. “Baka ‘da tausayi ne? Bata da lafiyar neza tayi ‘girki?’ Ta dan kada kai. Tace “Lallai Sulemati baida hankali;, ” Yana shiga daki. Ruf! Da‘ciki yayi bisa gado, sauran suka cire rigunansu Suka fito’ da singileti a- ‘ suka fada, kicin don dafa Taliyan fara. Saboda. . akwai miya. Dadinta kenan. Hajiya Suwaiba bata rabuwa ‘ da‘ miya, koda yaushe Shigarsu kicin din keda wuya. kamar’ daga sama _sallamar  Hajiya Aliyaa ta sawo kai cikin falon. Hajiya
“suwaiba ta mike tsaye tana kallonta. ta ma rasa wace irin
tarba za tayi mata?
lta kanta Hajiya Aliyaar babu annuri bisa fuskar‘ta ‘da kayar ta iyA yin karfin hali tace “Aliyaa ce? Sannu da zuwa. Babu walwala ta ‘amsa daga tsaye. “Ki zauna mana .
Kai tsaye tace “Ba zama nazoyiba Hajiya Suwaiba. na zone intafi da ’yayana, tunda abin haka ya zama, ai dama idan baka mutuba, baka gama ganin abin’ ’ mamakiba. To hankalin Alhaji Abdul-Rasheed ya kwanta‘.
an kama Baban Mansur, sauran magana yasa a harbe shi Don Allah kar a bar Shi‘da rai” . Jin muryar’ ta, yasa su Nasiru suka fitu daga
kicin, yayin da Hajiya Suwaiba ke fadin. “Ban yi mamaki ba Aliyaa, kuma kalamanki basu girgiza niba, don babu abinda zanji mai tsananin muni a’kunnena fiye da. wanda na jijiya! Kuma ke da a wautarki, kina zaton mijinki zai shane? Har abada Wallahi, domin Allah baya barin azzalumil aya ta farko kenan Ubangiji ya fara nuna maku”.
Tace “Rufe ‘min baki. Akwai azzalumi.macuci._ irin Abdul-Rasheed? Ka ‘shirya cuta, ka daUki’wanda bai jiba, bai gani ba ka manna masa….,.”
“Au. haka ya gaya miki? To ai gaskiya zatai halinta, da yardar Allah nan bada dadewaba, duniya‘za tanuna azzalumi, butulu a tsakaninsu”: ‘

www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *