G G.C UNITY COLLEGE*
Makaranta ce mai tarihi yana ɗaya daga cikin manyan makarantun da ke cikin garin Bauci kasancewar shine ɗaya tilo makarantar kwana wacce ta tara ɗalibai daga gabaɗaya yankunan Nigeria, kama daga arewa har kudu. Makarantar ta tara ɗalibai da dama saboda irin karatun da ake yi da tsayawar da malamai suke yi dan ganin sun samar wa ɗalibansu ilimi nagartacce.
A hankali ta buɗe idonta ta shaƙi iska mai ƙarfi, tsananin farin ciki ne ya kama zuciyarta saboda tsintar kanta a cikin makarantar. Kai tsaye wajen da ake Parker motoci Abba ta shiga ya yi parking, buɗe motar ya yi ya fito ita ma ta biyo bayan shi, kai tsaye admin block suka je, ɗan abubuwan da ba a rasawa aka yi, daga baya ya yi mata nasiha ya bata pocket money ya tafi, sai a lokacin ta ji zuciyarta ta tsinke, admin officer ɗin ne ya sa aka kira masa wata senior a cewar sa ita ce house captain ɗinsu.
“Deeja, ga Ummi nan a bata ɗaki a kuma sa ido a kanta”.
“To Daddy” abun da ta faɗa kenan ta fita ta kira wasu ga dukkan alamu juniors ne irinta, kayanta suka ɗebe tamkar ƴan dako suka tafi har cikin Hostel ɗin, a nan ne ta san tabbas bariki iyawa ce, duk da kasancewar rana ne hakan bai hana idonta ganin abubuwa wanda suka kauce hanya ba, babu kunya bare tsoron Allah, runtse idonta tayi tana mai Allah wadarai da irin shigar banzan da suke yi. A hanklai zuciyarta ya fara tsananta bugawa da sauri da sauri.
House captain room shine abun da ta gani an rubuta a saman ɗakin da ta shiga bin bayanta tayi itama a hankali ta sauƙe ajiyar zuciya ganin ɗakin ba mutane sai gadaje guda biyu(bonk) waɗanda suka sha shimfiɗa. Hamdala ta shiga yi wa Allah dan duk a tunaninta ta kauce ma faɗawa halaka irin na wasu watsatstsun data wuce a hanya.
Ajiye kayan suka yi suka fita, Sister Deeje ta ce ” a nan za ki zauna sai ki shirya kayanki a can”.
Tana gwada mata wajen ta fita. Zuba wa kayan ido tayi tana mai karanta wasiƙar jaki.
Kasancewar yamma tayi kuma weekend ne kafin ta kammala jera kayanta ta fara jiyo hayaniyar waɗanda suka dawo daga Arabic class, wata murya mai zaƙin sauraro ne ya daki dodon kunnenta.
“Allahumma Rabbi Salli Alah, Salli Alah, Muhammadun shugaban gaskiya, gaskiya, Balarabe ɗan balarabiya, rabiya, dominsa ne an kayo duniya, duniya, dominsa ne…” Bata kai ga ƙarasa maganar ba ta kutuntuma ashar.
“Kutumar jan durin uwa! Wata tsinanniyar ce mai bakin uwar ƴar gidan taƙi zama jikar asalamar ce ta ɗauke mun net ɗina dana shanya! Na rantse da Allah ko a dawo mun da shi ko nayi bura uba! Dan babu ƴar iskar da zan ragar mata yan kutumar….”
“Kai Zarah wai ke baki gajiya da danna ashar ne dan Allah? Yanzu fa kika gama ƙasida ko aya baki kai ba kin zo kina kutuntuma ashar kamar ƴar gidan maguzawa”.
“Hold on nature!” Ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. “Ba ruwanki da Ni ina faɗa miki ki daina shiga sabgata kin ƙi na rantse da Sarkin da yake busa mun numfashi zamu yi kutumar bura uba da ke, dan ni ba karamin abu ba ne a wajena na kwaɓe mu bugu”.
“Ai daga magana sai nawa ya zama mai zafi? Lallai kan! Ki sani ba da ni zaki yi ba dan ni nasan me nake yi” tana gama maganarta ta wuce ta barta tana ta kumfar baki”.
‘Cabɗijam! Wai dama haka ake yi? Mutun ya yi ta kutuntuma ashar kamar bai san zafin iyayensa ba? Kai gaskiya wannan yarinyar bata da ɗabi’a mai kyau in Dai haka take’ Ummi ke wannan zancen zucin fuskarta cike da al’ajabi gami da mamaki, bata taɓa zaton haka rayuwar makarantar take ba sai gashi a cikin mintuna ƙalilan ta fara karo da ɗabi’u marassa kyau.
Bokitinta ta ɗauka ta fita waje da niyyar zuwa deɓo ruwa dan ɗaura alwalan sallah magriba da tayi, saboda a hanyar shigowarsu ta ga wani burtsi (borehole) a gaban Hostel ɗin, kanta a ƙasa take tafiya a hankali tamkar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, ba tare da zato ko tsammani ba ta ji taci karo da mutum, wanda ya sata ɗagowa da sauri, kafin ta kai ga ganin wacce ta buge ta tsinkayi azababben mari a fuskarta, Wanda yasa ta jin sa tamkar sauƙar aradu.
“Dan kutumar durin uwar ki ke makauniya ce da zaki buge ni?” Maganar da tayi ne yasa Ni kallonta, da mamaki na sai naga gabaɗaya mutanen da ke wajen suna darewa wasu har ƙasa suke tsugunawa suke gaisheta kafin su wuce.
Bata kai ga bata amsa ba ta sake kife ga da wani wawan mari Wanda yafi na ɗazu ƙara. “Kutumar uwa wallahi ko ke kurma ce yau sai na ga uban da ya tsaya miki dan uban babanki”.
Finciko ta tayi tamkar kayan wanki tayi hanyar Hostel dinsu da ita, tun daga nesa ka fara jin “puya uba lallai yau lulu ta samu Nama”.
Zuciyar Ummi ce ta shiga wani irin bugawa a take taji cikinta ya yi wani irin murɗawa.
More comments more typing🤷🏼♀️
*MAKARANTAR KWANA*
~(Boarding school)~
_Bazan ɗauki zagi ko cin mutunci ba daga wajen kowa duk wanda ya mun tabbas ba zan bar shi ba_👌🏼
Page 2
Kneel down suka sa tayi a tsakiyar Hostel ɗin. Duk wanda yasan Lulu house yasan field ɗin yana da girma sosai.
Hawaye ne masu zafi suka fara zuba daga idon Ummi tun kafin ta a kai ga mata magana.
Kai tsaye ɗaki senoir tayi ta cire ɗan yalolon hijab ɗin da ta rufe jikinta da shi wani banza kayane a jikinta wanda baki ba zai iya faɗin munin shi ba.
“Keeee! Dan uban ki taso ki biyo ni ɗaki yau sai kin ci mai cin uwarki”.
‘Auzubillah’ shine abin da ta faɗa a cikin zuciyarta, a duniya ba abin da ta tsana kaman a zagi iyayenta sai gashi yau an zage ta tana gani babu abin da zata yi wanda ya wuce kuka kawai, jikinta a sanyaye ta tashi ta bita har zuwa ɗakin da ake kira da lackzirious. Babban ɗaki ne wanda ya tara mutane da yawa mafiya akasari shaiɗanu ne a ɗakin saboda yawan da suke da shi gashi idan har abu ya faru babu wanda zai baka hakuri sai dai su zuga juna.
Ana kaita suka yo kanta ba tare da tambayar abun da tayi ba.
“Dan ubanki shigo nan kwanan” wata da ke zaune a up bonk daga ita sai bra da gungun wando ta faɗa, jiki a sanyaye Ummi ta shiga kwanan durƙusawa har ƙasa tayi ta ce “ga Ni sister” dungurar kanta tayi da ƙafa tace “ƙasan gadon nan zaki shiga ki kamo mun ta macen sauro”.
Ido waje ta zato ta ce “sister yanzu dan Allah ta ina zan samo macen sauro?”.
“Au tambaya ta ma kenan kike yi? Ke!” A hasale ta durƙo daga kan gadon, ta kife ta da wani irin mari Wanda ya sata ganin taurari a idonta.
“Haba Social irin abun da kuke yin nan sam bai dace ba, yanzu fa idan aka tambaye ki me tayi aka kawo ta Hostel ɗin nan ma bazaki iya faɗa ba, amma kin hau ta da duka”.
“Ke Luba bana cike da iskanci kina ji ko, babu ruwanki da duk abin da zan yi, akan me ma zan tsaya tambayar abun da tayi kenan tsoronta nake ji ko me? Wannan ya zama na ƙarshe da zaki ƙara shiga sabgata idan kin ƙi kuma abun ba zai yi mana daɗi ba”.
A yadda take magana a masife kaɗai ya isa ya tabbatar maka da cewar ita ɗin ƴar bala’i ce domin wacce tayi katsalandar yi mata maganar ma juyawa tayi saboda sanin idan ta tsaya abun ba zai yi mata kyau ba.
Ganin hakan ne ya ƙara tsinkar da cikin Ummi, da kyar ta iya tattaro nutsuwarta ta haɗa shi a waje ɗaya tace, “dan Allah sister kiyi hakuri ni fa sabuwar zuwa ce yau ɗin nan aka kawo ni, wallahi ban san sharruɗan makarantar nan ba sam, daga yanzu zan kula, dan Allah ki barni naje nayi sallah”.
“Kin ci Sa’a kince Allah na kuma yi haƙuri saboda shi, karki kuskura ki ƙara abun da zai sa a kawo ki Hostel ɗin nan, dan haɗuwar mu ta biyu ba zai taɓa yi miki kyau ba”.
Godiya tayi mata ta fita jiki a sanyaye taje tayi sallahn magirba da isha’i a masallaci ta koma Hostel har zuwa lokacin babu kowa a dakin, anan ne zuciyarta ya cika da tunani ko dai sister Deeje ita kaɗai ce a ɗakin? Idan ma ita kaɗai ce ina take zuwa haka?.
‘kin ga Ummi ina raba ki daga zuwarki har zaki fara jeho ma kanki tambayoyi haka? Ko ma meye babu abin da ya shafe ki naki ido kawai’ zuciyarta ta bata shawara wanda ya sata saurin kawar da zancen ta haɗa abinci taci ta kwanta.
*BIMA HOUSE*
Bima Hostel Yana ɗaya daga cikin Hostel ɗin da mafi akasari junior ke zama, kuma ita ce ta kasance Hostel na ƙarshe daga cikin jerin hostels ɗin da ke cikin g.g.c (unity college) Bauchi daga shi sai masallaci a ta gabansa gefensa kuma ginin bango ne wanda zai sada ka da waje daga wajen kana iya jiyo ƙaran ababen hawa da suke zirga-zirga a cikin gari.
Dare ne mai cike da tarin ni’imomin Ubangiji kasancewar hunturu ya fara shigowa sanyi ake sosai wanda ya sa mafiya yawan mutanen da ke cikin Hostel ɗin yin Bacci idan ka cire tsirrai waɗanda, basa jin magana. Komai sanyi komai zafi sai sun aiwatar da rashin jin da suka saba kaman kodayaushe, sai kuma tsirrai waɗanda ke tare da masoyansu a wani ɓangaren.
Bam! Bam!! Bam!!! Sautin bugun ganga ne ya cika ilahirin Hostel ɗin wanda ya Bawa shaiɗanun da basu yi bacci ba daman fitowa da gudu wasu har tuntuɓe suke yi, idan ka tsaya ka ƙare musu kallo tabbas ba zaka iya banbance musulmai da Christian ba saboda yanayin shigar banzan da suna yi, wasu daga su sai vest da indies wasu kuma daga su sai guntun wando wanda bai ma sauƙa ba gabaɗaya dai abin babu kyan gani.
“Bujena bujena wayyo Allah bujena! Ran da ban ga buje ba sai na fi ruwa hauka”.
A razane Ummi ta tashi daga baccin da take yi saboda azababben ƙaran da ta ji ya bugi dodon kunnenta, lalube ta fara yi ganin duhu ya mamaye ɗakin, a ɗayan ɓangaren kuma, wani irin gurnani da nishi ta jiyo, ji tayi gabaɗaya jikinta ya sake tsoro gami da al’ajabi ne suka kamata, da sauri ta tashi tayi gadon da take jiyo ƙaran yaye raping ɗin da aka yi wa kwanan tayi, “subhanallah” abun da ta faɗa kenan da karfi gami da juyawa da baya.
DONLOAD BELOW ⬇️