MAKIRCI KO ASIRI
CHAPTER 3
Sha d’aya da rabi (11:30pm) suka shigo gida, ratsowa sukayi cikin parlour yana rungume da ita, basu lura da wanda take zaune ba jin maganar da sukayi, yasa suka tsaya..
“Sannunku da dawowa”
Ramlah ta fad’a tare da k’arasowa gabansu
“Yauwa”
Mufeedah ta fad’a tare da tab’e baki shiko Imran inda take bai kalla ba sai guntun tsakin da ya saki…+
Murmushin takaici Ramlah tayi ta k’arasa gaban Imran kallonshi tayi sama da k’asa duk ya canja ba Imran d’in da tasani da bane, mai tausanta mai san ganinta cikin farin ciki mai san ganinta kusa dashi yau shine ya tsaneta ya tsani ganinta kusa dashi, wasu hawaye taji zasu zubo mata tayi saurin mai dasu tare da jin wani k’arfi da ya taso mata dan yau ko yane sai ta karb’i yancinta…
“Lafiya kikazo gabana kikaman tsaye”
Cewar Imran yana cika ya batsewa
D’agowa tayi ta kalleshi tace
“Yanzu abinda kayi ka kyauta? Baka gudun Allah yaman sakayya ko ka manta yau aiki nane? Ka d’auketa kafita da ita mikake nufi da hakan? Abinci na maka amma ko inda yake baka kalla ba sai jifana da kayi da k’ana nan maganganu dami wannan kucakar tafini? Wallahi bata fini da komai ba ka kalleta ka kalleni wallahi nafita komai dubi kanta kagani gashin doki ne fa bisa kanta”
D’an kwalinta ta warware ta girgiza kanta gashin ta ya zubo har gadon baya juyi tayi tace
“Ka kalleni ka kalleta dami ta fini, ko baka fad’a ba nasan kasan nafita da komai…”
Tsaye yayi ya daskare ya kasa koda motsa hannunshi ne…
Ihu Mufeedah ta saki tayi kan Ramlah, d’aga hannu tayi zata mareta rik’e hannun tayi tace
“Kada ki soma gigin wannan mummunan hannun naki zai tab’a fuskata, duk abinda zai man zan d’auka saboda miji nane Aljanna nake nema wajenshi amma ke baki isa kice zaki d’ora hannunki kaina ba duk randa ko kikayi gigin aikata haka wallahi sai kinyi danasani…”
Tana gama fad’an haka ta jefar da hannun Mufeedah….
Kallonshi tayi sama da k’asa tace
“Ka guji had’uwarka da Allah duk randa hakkina dana yaranka ya tashi kamaka wallahi sai ka tsani kanka…”
Tana fad’in haka tayi gaba, ji tayi ya fizgota da k’arfi sai da ta fad’a k’irjinshi….
“Ubanwa kike gayama magana?”
D’agowa tayi ta kalleshi tace
“Ba magana na gaya makaba na tunatar da kaine dan naga kamar ka manta miye adalci shiyasa nake tunatar da kai dan kasan mi kake ciki tun kafin lokaci ya k’ure ma…”
D’aga hannu yayi zai mareta, da sauri ta kalleshi tace
“Kada kasake wannan kuskuren na cewa zaka mareni, kada kaga ka mareni ban cema komai ba amma duk randa ka sake wannan mistake d’in sai ka gane kurenka..”
Tana fad’in haka ta fizge tayi d’akin yaranta…..
Ihu Mufeedah keyi tana zagin Ramlah ita ko bata juyo ba bare tasan da ita take..
Tsaye yayi kamar an dasa shi mamaki cike da ranshi tun da yake da Ramlah bata tab’a mashi gardama ba amma yau gashi ta tsaya gabanshi ta k’are mashi cin mutunci….
Harara Mufeedah ta watsa mashi tace
“Burinka ya cika matarka taman cin mutunci amma ka kasa d’aukar mataki”
“Kiyi hak’uri baby zanyi maganinta”
Tsawa ta daka mashi tace
“Rufe man baki kafin ka d’auki mataki ni zan d’auka..”
Tana fad’an haka ta ruga d’akinta binta yayi yana kira kafin ya k’arasa ta shige d’akin tare da rufe k’ofar ba yanda ya iya dole ya juya ya nufi d’akinshi cike da k’unar rai….
Tana shiga d’akin yaranta, ganin su kwance suna bacci, hawayen da suka gangaro mata ta goge, adu’a ta masu kana ta juya ta nufi d’akinta tana kai bakin k’ofa..
“Ammi”
Dasauri ta juyo ganin Haneefa da alamun ba bacci takeyi ba..
Dawowa tayi tace
“Miya hanaki bacci?”
“Taya zanyi bacci iyayena na cikin wani hali”
“Amma Haneefa kinsan fa dare yayi 12 fa kuma gobe kuna da makaranta”
Murmushi tayi tace
“Nasani Ammi, a yanzu ne ya kamata mukaima Allah kukanmu ba mu kwanta muna bacci ba..”
D’aga kanta tayi dan tasan gaskiya d’iyarta ta fad’a
Mik’ewa Haneefa tayi ta nufi toilet tana kai bakin kewaye ta juyo ta dubi Ramlah tace
“Ammi ki tashi kije ki gana da mahaliccinmu kinsan irin wannan lokacin da kanshi yake saukowa yana cewa ina masu neman biyan buk’ata in biya masu…”
Tana fad’in haka ta shige ban d’aki, kwarin guiwa Ramlah taji ta tashi ta nufi d’akinta tana shiga itama Alwalla tayi tazo ta tada sallah…
K’arfe bakwai dai dai tagama shirya yaranta suka mata sallama suka wuce school….
D’akinta ta shige tana shiga ta wuce toilet ta dad’e tana wanka kana ta fito…
Tsintar kanta tayi da sha’awar yin kwalliya ta b’ata lokaci wajen yin kwalliya tana gamawa ta wuce wardrobe, red super ta d’auko doguwar riga, ta saka rigar d’is ta zauna jikinta ta kafa d’aurin d’an kwali kai kace gwargwaro ne ta nad’a, feshe jikinta tayi da turararuka kala kala, ga sanyin AC, sai ya bada wani k’amshi mai sanyaya zuciya….
Kanta ta kalla a madubi murmushi ta saki wanda ita kanta tasan tayi kyau, (Nikaina sai da na firgita ganin kyan da tayi sai kace wata balaraba…), parlour ta nufa tana isa ta zauna kan 1seater ta d’aura k’afa d’aya kan d’aya tana kallon MBC Bollywood….
+
K’arfe tara ya fito cikin shirin shi na tafiya office dai dai Mufeedah itama ta fito daga d’akinta murmushi ya sakar mata yace
“Good morning baby”
Inda yake bata kalla ba bare yasa ran zata amsa..
Yana d’agowa suka had’a ido da Ramlah, murmushi ta sakar mashi kauda kanshi yayi amma a ranshi yana yaba kyan da tayi
“Ina kwana”
Muryanta ta katse mashi tunanin da yakeyi
A tak’aice ya bata amsa da
“Lafiya”
Kallonta Mufeedah tayi, saida ta kusa fad’uwa ganin irin kyan da Ramlah tayi, kanta ta duba gani tayi Ramlah tafita komai ta mata tazara nesa ba kusa ba ji tayi kamar ta d’aura hannu bisa kai tasa ihu saboda takaici, harara ta bankama Ramlah tayi tsoki ta koma d’akinta…
“Your breakfast is ready”
Ya tsinkayo muryan Ramlah, bai tanka mata ba ya nufi dainning table, k’arasawa tayi dan tayi serving d’inshi, soyayyen dankali ne sai tea ta had’a mashi wanda yasha kayan yaji..
Tura mashi tayi gabanshi tace
“Ranka yadade gashi nan nasan kayi missing abinci na.”
Tana fad’an haka ta kashe mashi ido tare da sakin murmushi, harara ya wurga mata tare da tsoki ya fara cin abinci, yana gamawa yayi hamdala, ya mik’e ya nufi d’akin Mufeefah…
Da sallama ya shiga d’akin, zaune take bakin gado tayi tagumi, bata amsa ba haka ba kuma ta d’ago ba..
Takowa yayi yazo gabanta hannunta ya cire, kwacewa tayi ta buga mashi tsoki..
Jawota yayi ya had’ata da k’irjinshi, kuka ta sakar mashi , gaba d’aya hankalinshi ya tashi
“Minene Baby kinsan bansan ganin kukanki..”
Hawaye ta share tace
“Kana gani jiya matarka taciman mutunci amma ka gagara rama man..”
Bayanta ya dunga bubbugawa yana bata hak’uri shi kanshi ya rasa ya akayi ya kasa hukunta Ramlah jiya da dare…
Hak’uri ya dinga bata da kyar ya samu tayi shiru, wasanni ta fara mashi daga nan komai ya canja…
Wanka ya fito yana tsane kanshi, hararta yayi yace
“Idan kikasa aka koran aiki yau sai kisan ya zakiyi damu..”
Dariya tayi tace
“Bama mai korarka..”
Shiryawa yayi ya fito dan wucewa aiki tare suka fito shida Mufeedah tana manne a k’irjinshi, parlour suka tarda Ramlah zaune tana jiran fitowarshi, wucewa sukayi inda take bai kalla ba, itako Mufeedah sai shigewa take jikinshi tana cewa
“Baby Allah kamar mu koma nifa ban gaji ba..”
Ta kalli inda Ramlah take ta kashe mata ido tana murmushin mugunta..
Hancinta yaja yace
“Idan na biye maki yau baki barina fita…”
Ramlah ji tayi kamar ta fashe da kuka, wannan wane irin bala’i ne haka aikinta ne fa amma yaje ya nemi wata, kukan dake neman kubce mata ta maidasu dan bata san Mufeedah ta gane halin da take ciki tayi dariya..
Murmushi ta k’ak’aro tace
“Harka fito?”
“Eh”
Ya bata amsa a tak’aice…
Kallon Mufeedah yayi yace
“Baby sai nadawo ko?”
Rungumeshi tayi tace
“Ka kabiyoman da shawarma”
“An gama”
Yace mata ya juya ya tafi..
Yakai bakin k’ofar fita parlour ya juyo muryanta tana cewa
“Allah ya kiyaye hanya ya baka sa’a ya had’aka da alkairin da ke cikin wannan ranar sharrin dake cikinta Allah ya nisanta ka dashi, ka tabbata halak d’inka zaka kawo mana idan baka samo ba ka dawo zamu hak’ura..”
Juyowa yayi ya kalleta, murmushi ta sakar mashi
“Nagode”
Yafad’a a hankali yana fad’a ya juya ya fice…
Juyawar da zatayi taga Mufeedah zata zuba abinci, dasauri ta k’arasa wajen ta d’auke warmer din tace
“Akanmi zaki tab’aman abinci?”
D’agowa Mufeedah tayi ta watsa mata harara tace
“Bangane ba?”
“Bazaki gane ba ai”
“Naga abinci kuma inajin yunwa mi zai hana bazan ciba..”
Dariya Ramlah tayi tace
“To naga bake na dafa mawa ba mijina na dafa mawa akanmi zakici”
Iya k’ulewa Mufeedah ta k’ule tace
“Kiban abinci inci”
“Bazan bada ba aikema macece ki shiga ki dafa da kanki”
Zagi ta maka mata tace
“Miye amfaninki gidan dama dan ki dafa mana abinci zakiban ko kuwa”
Shek’ek’e Ramla ta kalleta tace
“Bazan bada ba idan kin isa kizo ki karb’a”
Tana fad’an haka ra juya ta tafi, zagi Mufeedah ta dinga jifar Ramlah dashi, ko juyowa ba tayi ba bare ta tanka ta..
Haka ta k’araci masifarta taja k’afa ta koma d’aki dan yunwa takeji sosai…Yan team din Ramlah I hope kun shirya ganin yanda zata ida kasancewa tsakanin Ramlah da Mufeedah ‘yar ruwan zafi, kowa zaiyi winning, Mufeen nasan dai ke kadai ce Team din Takwararki amma bari inbi bayanki muzama mu biyu lolzz..
Tana shiga d’aki ta fara kai kawo cikin d’akin dan yau Ramlah ta mata abinda sai ta wulakanta ta wallahi dan taga ta d’aga mata k’afa shine harta samu wuri haka yau ita take gaya ma magana ta hana abinci…
Dogon tsaki taja ta zauna gefen gado tagumi tayi tana sak’awa da warwarewa numfashi taja tare da sakin wata irin dariya tace
“Yau zaki raina kanki Ramlah saina sa an k’ask’antar dake kinsan ba bakin komai kike ba..”
Tana gama fad’in haka ta tashi taja k’afa ta nufi k’ofa dan yunwar da takeji idan ta zauna zata iya illatata gara ta mik’e ko tea ne ta hada…
Bakin kitchen suka had’u da Ramlah, ban kad’arta tayi inda take Ramlah bata kalla ba ta girgiza kai ta wuce, tsoki tayi tace
“Mutum idan ya isa ya tanka mana”
Kallonta Ramlah tayi shek’ek’e tace
“Ai idan kare na haushi shi kad’ai baka biye mashi…”
D’aga hannu tayi zata mare ta, rik’e hannun tayi tace
“Ko amafarki kada ki fara wannan gangancin dan duk randa hannunki yakai jikina na maki alkawarin asibiti zaki kwana….”
Tana fad’an haka ta jefar da hannunta tayi gaba..
Ji tayi kamar ta fashe da kuka irin cin mutuncin da Ramlah ta ke mata ya fara isanta gashi boka ya gagara yi mata komai, tsaki taja ta shiga kitchen warmers din ta fara budewa taga ko da abinci babu komai cikinsu harma an wankesu, ba yanda ta iya illa ta had’a tea kawai…
Tea tahada mai kauri taje daining ta d’auki bread ta nufi d’akinta. Tana shan tea tana kitsa makirci da zata had’ama Ramlah wajen mijinta….Inda tasha tea nan tabar cup din da sauran bread ta koma kan gado, wayarta ta jawo ta kira Lash, ringing biyu Lash ta dauka..
“Hello Lash”
Banji mi Lash tace ba, ajiyan zuciya tayi tace “Lash akwai matsala fa komai na niyar kwance man” nan ta kwashe komai ta gaya mata..
D’ayan b’angaren Lash tace
“To ko boka zamu canja?”
Tsoki tayi tace
“Ba abinda boka zai mana tun da boka na kan tudu ya kasa to babu wanda zai man wannan aikin illa ma suci kudina..”
“To yanzu ya kenan?” Cewa Lash
Ajiyan zuciya tayi tace
“Karki damu nasan mizanyi”
Tana gama fadan haka ta kashe wayar bata jira taji mi Lash zata ce mata ba ta yarda wayan bisa gado ta kwanta rigingine tana tunanin miza tama Ramlah…+
Kitchen ta fito dan ta shirya lunch dan yaranta 2:00pm suke dawowa daga school, jellof rice tayi sai ferfesun kayan ciki, kafin kicemi k’amshi ya cika gidan, tana gama abinci ta kwashesu cikin warmers takai d’akinta dan tayi alk’awarin ta gama dafa abinci Mufeedah taci idan bazata iya dafawa ba da kanta ta bari…
Jin k’amshi ya cika mata ciki taji wata kasallar yunwa ta taso mata dan tasan tea ba abinda zai mata, mik’ewa tayi ta nufi kitchen dan yunwa takeji sosai, da saurinta ta isa kitchen ta bud’e tukunya ganin tuk’unyar wayam ba komai sai k’anzo k’anzo ji tayi kamar ta d’ora hannu bisa kai ta rushe da kuka dan takaici..
Dakyar take jan k’afafuwanta tayi d’akin Ramlah, bako sallama ta banka mata d’aki, zaune take tana kallo tana cin abinci, wasu miyau Mufeedah ta had’iye dan dagajin k’amshi, abincin zaiyi dadi. Inda take Ramlah bata kalla ba balle tasan akwai mutum wajen…
“Ina abinci na?”
Banza tayi ta kyaleta kamar ba da ita take magana ba.
“Ramlah Ina abincina?”
Sai sannan ta d’ago ta kalleta tace
“Ajiyan abinci kikaban?”
Itama kallonta tayi ta ya mutsa fuska tace
“Wanda kika dafa..”
Dariya Ramlah tayi ta kalleta sama da k’asa tace
“Ban dafa dake ba”
“Saboda mi?”
“Saboda ba Yar aikinki nake?, beside haka aka koya maki gidanku shiga d’akin mutane ba sallama? Ko dayake ba laifinki bane ba islamiyya ce ba’a je ba, bama wannan ba ay mace kike kema kuma aure kikeyi mizai hana bazaki shiga kitchen ki dafa da kanki ba? Ko kuma ance maki ni yar aikinki ce, ko dan in dafa maki abinci nake zaune gidan, zaman aure nakeyi kamar yanda kikeyi, dan haka idan zaki dafa abinci da kanki ki dafa kici idan bazaki dafa ba wallahi nagama baki abinci kin iya kwanciya da miji amma baki iya dafa abinci ba, to nima bazan kara dafawa ba idan kinga nayi abinci gidannan nawane da ‘ya’yana sai kuma mijina…”
Tana gama fad’an haka ta cigaba da cin abincinta..
Ji tayi kamar ta fashe da kuka dan Ramlah ta gama da ita, da kyar taja k’afafuwanta ta nufi d’akinta dan idan ta k’ara minti d’aya d’akin Ramlah sai tayi kuka wanda kuma aganinta raini ne….
Tana fita Ramlah ta bita da harara ta cigaba da cin abincinta hankali kwance….
D’aki ta koma tana shiga ta fad’a kan gado, rigingine tayi tana kallon silin, wulakancin da Ramlah ta mata ya dawo mata, dole ta d’auki mataki sai tama Ramlah illah., haka ta cigaba da surutunta ita kadai….
K’arfe biyu da minti goma yaranta suka shigo gida, da sallamarsu, ganin ba kowa parlour yasa suka wuce d’akin Amminsu, dan yanzu zaman parlour ba kullum akeyinshi ba sab’anin da. Da kullum suna parlour tare da iyayensu cikin k’auna da aminci…
“Assalamu Alaikum”
Cewar Haneefa dake gaba..
Amsawa tayi da
“Amin wa’alaikum salam “
Shiga sukayi cikin d’akin, da fara’a ta tarbesu
“Har kun dawo?”
“Eh Ammi”
Suka bata amsa, ware masu hannuwa tayi suka k’arasa wajenta ta had’asu duka ta rungume, Banda Haneefa da tayi tsaye tana kallonsu….
“Kallonta tayi tace
“Princess baki zuwa ki hugging Ammi?”
Dariya tayi tace
“Wad’annan sojojin naki sun makaleki Ina zan iya zuwa”
Dariya sukayi tace
“Come on princess zoki hugging Ammi..”
K’arasawa tayi wajenta ta had’asu duka ta rungume, tana k’arajin k’aunar yaranta a cikin ranta…
STORY CONTINUES BELOW
Takai minti biyar rungume dasu kana ta sakesu, kallonsu tayi tace
“Kuje ku cire unifoam kuzo kuci abinci”
“A d’aki zamu ci abincin?”
Cewar Haneefa, d’aga mata kai tayi, alamar
“eh”
Ba musu suka nufi d’akinsu, jim kad’an suka dawo d’akinta da sallama, suna shiga suka samu wuri suka zauna. Warmers ta d’auko ta bud’e da kanta tayi serving d’insu kowane ta tura mashi gabanshi..
“Ammi miyasa zamuci abinci a d’aki yau?”
Cewar Haneef,
murmushi tayi tace
“Kawai inasan yau muci abinci a d’aki ne ko bakuso mu koma parlour?”
Da sauri Mukhtar yace
“Munaso Ammi ki barmu nan..”
Shafa kanshi tayi tana murmushi, ita dai Haneefa ba tace komai ba illa abincinta da take ci.. suna gama cin abinci Mukhtar ya kwashe plate d’in ya kai kitchen.
“Ammi tun d’azu nake fad’uwar gaba”
Haneef ya fad’a cikin damuwa, kallonshi tayi cikin kulawa, jawoshi tayi jikinta tace
“Ka dinga karanta innalillahi wa’inna ilahir raj’un in shaa Allah zai daina”…
D’aga mata kai yayi alamar to, hira ta dinga jansu dashi, har lokacin islamiyya yayi, kallonsu tayi tace
“Kuje kuyi shirin Islamiyya”
Ba musu suka mik’e suka nufi d’akinsu dan shiryawa….
Cikin shirinsu na islammiya suka fito, daidai itama ta fito daga d’aki.
“Har kun shirya?”
“Eh”
Suka bata amsa.
Tace “to kuje kada ku makara, Allah ya bada sa’a ku maida hankali kunji…”
Amsawa sukayi da “Ameen”…
Banda Haneef da kwatakwata bai ciki walwala, hannunshi ta kamo tace
“Soja nah ya dai?”
Tab’e baki yayi kamar zaiyi kuka Ammi wani abu mummuna zai faru dani”
Da sauri ta rufe mashi baki tace
“Pls stop saying that Haneef nothing will happen to you (bari fad’in haka Haneef ba abinda zai faru da kai)” fad’uwan gaba ne kuma in shaa Allah zai daina…
D’aga mata kai yayi, “Haneefa Kuje, pls take care of them for me (Haneefa ki kularman dasu)”
“In shaa Allah l’ll..”
Kama hannunsu Haneefa tayi suka tafi, yakai bakin k’ofa ya dawo da sauri ji tayi an rungumeta ta baya, juyowa tayi taga Haneef k’arfin hali tayi ta duk’a tace
“Soja yadai?”
K’ura mata ido yayi yana kallonta, sai da ta girgizashi kana ya dawo hayyacinshi…
“Haneef mike damunka?”
Rungumeta yayi yace
“I love you so much Ammi”
Ita ma k’ank’ameshi tayi tace
“Love you more Haneef”
Sakinta yayi ya juya ya tafi, yakai bakin k’ofa ya juyo ya d’aga mata hannu, itama hannun ta d’aga mashi yana fita ta sauke hannunta tare da share kwallan da suka zubo mata? Hannu ta d’aga tana adu’a wajen Allah kan ya kare mata yaranta duk inda suke….
D’aki ta koma jiki ba kwari duk tausan d’anta ya kamata, komawa tayi kan gado ta kwanta lum tana tunanin halin da yaronta yake ciki dan tunda ta haifeshi bata tab’a ganinshi cikin wannan halin ba, da kyar ta samu tayi sallah ta koma kan gado ta kwanta dan yau ko abincin dare batajin zata iya idan sun dawo ko indomie ce ta dafa masu….
6:00pm
K’aran tsayawar motar Imran taji, gabanta ne ya yanke ya fad’i tuna yanda sukayi da Mufeedah yau tayi tasan Allah kadai yasan irin sharrin da zata mata yau….
Shigowa yayi yana kwalama Mufeedah kira, itako tana jinshi taki amsawa sai ma kuka da ta fashe dashi, d’akinta ya k’arasa yana kiranta, ganin tana kuka yasa hankalinshi ya tashi, da sauri ya k’arasa inda take…
“Lafiya?”
Ya tambayeta tare da jawota jikinshi, tureshi tayi tace
“Ka kyaleni”
A rud’e ya kalleta yace
“Miyafaru? Please tell me”
Kuka ta fashe dashi hankalinshi idan yayi dubu ya tashi, lalashinta ya fara dan in akwai abinda ya tsana kukan Mufeedah ne…..
Da kyar ya samu tayi shiru yace
“Miyafaru?”
“Kana fita Ramlah tafara zagina tana zagar man iyaye wai ni karuwa ce, kaima sai da kagama lalata dani kana ka aureni ay kaima dan iskane irina babu abinda bakasha babu matan banzan da baka bi, ta tara yaranta tana gaya masu suna man dariya, wani kukan munafuncin ta fashe dashi, mik’ewa yayi tsaye yana huci kamar zaki har wani bak’i bak’i yake gani gabanshi, haka ya fita yana hard’e k’afafuwa…
“Ramlah! Ramlah!! Ramlah!!!”
Tun daga d’akin Mufeedah yake kwala mata kira, gabanta ne yaci gaba da fad’uwa dan tasan dama za’ayi haka, fitowa tayi da sauri inda yake tsaye, kafin tayi magana taji saukar Mari? Marinta yake ta ko Ina sai da yaga takai k’asa kana ya cire belt ya fara dukanta dashi…..
Dukanta yake ta ko Ina tun tana Iya kuka har yakai bata kuka, tsaye tayi ta hard’e hannu tana kallonshi tana murmushi…
Shigowa yayi da sallama yana kiran Ammi, da gudu ya k’araso ganin Imran na dukanta, kamashi yayi
“Yana Daddy ka daina dukanta mita maka?”
Wurgi yayi dashi ya cigaba da dukanta, tashi yayi zai koma Mufeedah ta kamashi ta je far dashi bisa tiles kanshi ya bugu, daidai shigowar Haneefa da Mukhtar wata irin k’ara yayi daga nan bai sake motsi ba, da gudu Haneefa ta k’arasa wajenshi tana kiran
“Haneef”
Jin k’arar da tayi yasa ta ingijeshi ta nufi inda Haneef yake kwance kanshi ya fashe, kuka ta saki sosai tana jinjigashi, dagoshi tayi ta rungume tana kiranshi ganin bai motsi yasa ta d’aukeshi su Haneefah suka bi bayanta suna kuka….
Hanyar fita tayi maigadi na tambayarta bata tsaya bashi amsa ba ta fice tana fita tayi sa’a mini jeep (napep) ta aje wasu fad’a wa tayi tace Alheri clinic zaka kaimu…
Mai napep yaja suka tafi kuka takeyi sosai suma su Haneefa kuka sukeyi, gani tayi kamar mai napep din bai gudu tace
“Malam dan Allah ka kai motar ka k’arshe kada yarona ya mutu..”
Tausayi ta bashi dan tunda suka fito yaga halin da suke ciki, gudu yake amma bata gani saboda rud’e take……
Suna isa bata bari ya ida tsayawa ba ta fito, ganin haka shima bai jira kar b’an kud’inshi ba ya wuce. Da gudu ta fad’a cikin asibitin tana kiran nurse, wata nurse ce ta tashi ta karb’i Haneef tayi emergency dashi….
Tazo shiga aka hanata, fashewa tayi da kuka ganin tana kuka ya saka Haneefa da Mukhtar kuka, rungumesu tayi ta cigaba da kuka kamar ranta zai fita………Ganin kukan da suke ba abinda zai masu yasa ta kama yaranta ta zaunar dasu, “Ammi ya Hafeen ba zai mutu ya barmu ba ko?” Cewar Mukhtar, hawaye ta share tace
“In shaa Allah zai tashi bazai mutu ya barmu ba….”
Jawo Haneefa tayi jikinta tace
“Princess kuka bazaiyi magani ba please stop crying adua zaki dingayi in shaa Allah he will be olryt okay?”
Hawaye ta share tace
“Ammi na tsanesu I hate dem both wallahi ta kashe man k’ani l’ll kill her nima..”
Rufe mata baki tayi “please stop saying dat Haneefa ita bata isa ta kashe Haneef ba sai dai idan kwananshi sun kare, kuma ki daina cewa kin tsanesu bare ta kaiki da cewa sai kin kasheta I kwn it’s hurt amma muyi hakuri, duk abinda Imran yayi ba yanda zakiyi mahaifinki ne ita kuma matar shi ce dole ki bata respect kamar yanda zaki bani, kuyi hakuri nasan Imran bai mana adalci amma ba laifinshi bane kunsan irin sanda yake mana dan haka duk abinda kuka ga yana faruwa ba laifinshi bane kedai kawai keep praying, in shaa Allah komai zai koma daidai….”
Haka ta cigaba da lallashin Haneefa tana bata baki…
Bayan awa guda aka fito da Haneef daga emergency, yana cikin gadon asibiti kanshi d’aure da bandage tashi sukayi da sauri suka nufi inda suke, “doctor ya jikinshi?” Cewar Ramlah, murmushi doctor yayi yace
“Dasauki yanzu za akaishi d’aki,”
“Alhamdulillah” gaba d’ayansu suka fada..,
“kece mamarshi?”
“Eh nice “
“Kisameni office inasan magana dake”
Bai jira amsawarta ba yayi gaba….+
Kallon Haneefa tayi tace
“Bari naje yanzu zan dawo”
“Daga mata kai tayi, hanyar da taga doctor yabi ita ta nufa, da sallama ta shiga office d’in d’agowa yayi ya kalleta
“Have a seat”
Ba musu ta samu wuri ta zauna. Rubuce rubuce yayi yakai minti goma kafin ya d’ago ya kalleta, har ta k’osa da zaman da takeyi
“Ke kika haifeshi?”
Maganarshi taji cikin kwanyar kanta, d’agowa tayi ta kalleshi tace
“Eh ni nahaifeshi”
“Ina babanshi?”
“Bai nan yayi tafiya”
Haka kawai ta tsinci kanta da mashi karya wanda ita kanta bata san dalilin yinta ba….
“Garinya akai yaronki ya fad’i haka?”
Gabanta ne ya fad’i dan bata san mi zatace ba ko zata gaya mashi kishiryata ne ta mashi haka no bazan iya ba zaiga sakaci na kuma kamar na tona asirin gidan mijinane …
“Toilet ya shiga kawai sai dai naji karanshi, Ina shiga na ganshi kwance kanshi ya fashe nafi ganinta ga faduwa yayi”
Haka kawai ta tsinci kanta da gaya mashi haka…
Kallonta yayi ido cikin ido, Har sai da gabanta ya fad’i “kodai ya gane k’arya na mashi?”
“Wani irin sakaci ne iyaye kukeyi yanzu d’anki yaji ciwo irin haka baki san tak’amaimai abinda yaji mashi ciwo ba? Shin ko kin manta yaranki amanane Allah ya baki? Amma kike sakaci dasu haka, well ba wa’azi zan maki ba, yaronki kanshi ya bugu sosai dan har jini sun taru amma munyi aiki mun cire kuma zai samu sauki in shaa Allah yanzu dai mun bashi gado Sai ya warware sosai zamu sallameshi….”
Kanta duk’e yake tunda ya fara magana, sai da ya gama ta d’ago tace
“Nagode likita in shaa Allah bazan karayin wasa da lafiyan yarana ba zan kula dasu sosai…”
Murmushi yayi yace
“Zaki iya tafiya..”
Sallama ta mashi ta tashi jiki sanye ta fita, inda ta barsu Haneefa nan ta iskesu kamasu tayi suka nufa d’akin da aka kwantar da Haneef, tura k’ofan sukayi suka shiga, bakaji motsin komai sai k’aran AC, gaban gadonshi suka k’arasa kwance yake yana fitar da numfashi daya bayan daya, kanshi ta dafa
“Allah ya baka lafiya Haneef forgive ur Daddy kaji?”
Hannunta ta janye ta share hawayen da suka gangaro mata, Haneefa ta kalla tace
“Bari naje gida na d’auko abinda muke bukata”
“To Ammi saikin dawo”
“Take care of your self nd my pikin kinji ko?”
“In shaa Allah Ammi”
Peck ta ma Haneef a kunci tace
“Get well soon my Baby”, kamar yaji mi tace yayi murmushi, “princess sai nadawo” tana fad’an haka ta fita daga d’akin…..
STORY CONTINUES BELOW
K’arasawa wajen gadonshi Haneefa tayi ta k’ura mashi ido, hawaye suka zubo mata Mukhtar ne ya matso kusa da ita yace
“Adda Haneefa stop crying please”
Hawaye ta share ta rungume Mukhar
“Karka damu nadaina kuka” d’agowa yayi ya share mata hawaye daga nan babu wanda ya kara magana….
Tana shiga gidan babu kowa parlour haka ta shige d’akinta ta d’auki abinda zata buk’ata taje d’akin yaranta kowa ta d’aukar mashi abun buk’ata takai mota, dawowa tayi ta d’auki wayarta da ATM card dinta ta saka a hand bag ta fito ta rufe d’akinta, harta kai k’ofar fita ta dawo tabi wani corridor, ta shiga d’akin Imran, sallama tayi ba’a amsa ba, shiga tayi cikin d’akin zaune yake ya had’a kai da hannuwa, kallo ta k’are mashi duk ya fita hayyacinshi sai kace ba Imran d’inta ba d’an gayu kamili Maiji da kanshi…
“An kwantar da Haneef asibiti”
Abinda ta iya fad’a kenan d’agowa yayi ya kalleta baice komai ba, itama kuma batayi expecting zaice wani abuba…
Juyawa tayi zata tafi, “wane asibiti yake?”
Abinda taji yace kenan
“Alheri clinic “
Ta bashi amsa a tak’aice
“Allah ya bashi lafiya”
“Amin”
Ta saka kai ta fita, tana fita maigadi ya taso yace
“Hajiya lafiya?”
Murmushi tayi tace
“Haneef ne ba lafiya amma yanzu da sauki”
“Allah ya bashi lafiya”
“Amin”
“Yana wane asibitin?”
“Alheri clinic”
“Allah ya sawak’e”
“Bud’eman gate Baba”
Ba musu ya wangale mata gate wuta ta ba motarta ta fita daga haraban gidan, d’aga mata hannu mai gadi yayi har saida yaga k’ulewarta kana ya rufe gate d’in ya koma bakin aikin shi……
Tafiya take tana tunani tabbas sai ta d’auki mataki dan idan ta kyale Mufeedah sai ta gama illata mata yara kuma da alama Imran bazai d’auki mataki ba, da haka harta iso asibiti, d’akin da Haneef yake ta nufa, sallama tayi ta shiga, zaune suke babu mai ma wani magana, murmushi k’arfin hali ta masu tace
“Yara na yadai?”
Mukhtar ne yace
“Bakomai Ammi”
“Princess are sure ba abinda ke damunku?”
Sai sannan tayi magana tace
“Ammi ba abinda ke damunmu sai ciwon Haneef”
K’arasawa tayi wajensu tace
“Karki damu in shaa Allah Haneef zai warke”
“Ammi idan ya Haneef ya warke karmu koma gidan Daddy please “
Jawoshi tayi tace
“Can zamu koma”
“Saboda mi?”
“Saboda babu inda yafiye mana nan nanne gidanmu gidan mahaifinku nikuma gidan mijinane dan haka bamu da inda yafi nan kaji ko?”
D’aga kanshi yayi alamar yaji…..
Wayanta ta zaro ta kira Ahmad ringing biyu ya d’auka
“Hello Ahmad Ina wuni”
“Lafiya lau Ramlah ya kuke dasu princess?”
“Lafiya lau muke dama zan gaya maka Haneef baida lafiya muna kwance asibiti”
“Subahannallah miyasa meshi?”
“Maganar na da tsawo sai kazo”
“Okay to in shaa Allah nan da minti talatin zanzo wane asibiti ne?”
“Alheri clinic” ta bashi amsa
“To shikenan in shaa Allah gani nan zuwa…..
*************
Wayan ta ne yayi k’ara tana dubawa taga Ahmad d’auka tayi,
“gani na shigo”
“Okay muna room3 private room”
Kashe wayan yayi dan yanama kusa da d’akin, sallama yayi ya shigo, da gudu Mukhtar ya k’arasa wajenshi yace
“Uncle Ahmad ya Haneef kanshi ya fashe, kuma Anty Mufeedah ce ta jefar dashi sai da kanshi ya fashe.”
Kallon Ramlah yayi yana neman k’arin bayani, kamo hannun Mukhtar tayi tace
“Princess kuje daga waje kinji”
Hannunshi Haneefa ta kama suka fita waje….
“Ina wuni?”
“Lafiya lau “
Ya bata amsa a tak’aice, “maganar da Mukhtar ya gayaman gaskia ne?”
D’aga kanta tayi alamar “Eh”
“Garinya haka ta faru inashi Imran din yake?”
“Yana nan”
“Yana na?” Cikin tsoro ya sake tambayarta
“Eh yana nan” ta bashi amsa, Ramlah mike faruwa daku? Karki b’oyeman komai ki fad’aman komai…
Wuri ta samu ta zauna ta share hawaye da suka gangaro mata, tun bayan Auren Imran da Mufeedah………. nan ta kwashe komai ta gaya mashi babu abinda ta rage mashi, gumi ne ya karyo mashi
“Innalillahi wa’inna ilaihir raj’un” kawai yake ta maimaitawa….
Gaban gadon Haneef ya k’arasa kanshi ya Shafa yace
“Allah ya baka lafiya my boy”
Yana fad’an haka ya juya ya fita, sai da yakai bakin k’ofa kana ya juyo ya kalleta yace
“Zanje in dawo”
Bai jira amsarta ba yayi gaba….
Yana fita babu inda ya wuce sai gidan Imran, horn ya dingayi kamar zai b’alle gate d’in gidan da gudu mai gadi ya wangale mashi gate, cinna kan motarshi yayi cikin haraban gidan, bai ida ko parking ba ya fito yayi hanyar shiga cikin gidan, tunda ga bakin k’ofa yake kwalama Imran kira, Har ya shiga parlour, da sauri Imran ya fito d’akinshi dan gane muryan waye ke kiranshi, itama fitowa tayi dan taga wakema mijinta wannan kiran…
“Ahmad lafiya kuwa?”
Cewar Imran da ya k’araso inda yake, kallonshi Ahmad yayi sama da k’asa yace
“Kai zan tambaya lafiyarka kasan mi kake yi kuwa? Kasan wutar da ka kunna ma gidanka da kanka?”
“Ban fahimci mi kake nufi ba fa”
“Ina zaka fahimta an juya maka kwakwalwa sai da nace karkayi auren nan ba alkairi baneba ka dage Sai kayi gashi nan irin abinda ka aura. Wallahi kaji tsoron Allah Imran kasan mi kake ciki saboda sai Allah ya tambayeka irin rik’on da kama iyalanka, yanzu Haneef na asibiti kuma matarka ce silar komai amma banganka asibiti ba kuma banga ka d’auki wani mataki ba, Anya hakkin yaran nan da mamarsu bazai tambayeka ba..”
Harara ya wurga mata yace
“Ke kuma kiyi duk abinda kika iya lokacin kine kuma zakiyi nadama a lokacin da wuri ya k’ure maki.” Yana gama fad’an haka ya juya ya tafi, harara ta bishi dashi tace
“Zanyi maganinka kaima daga kaina kagama shishigi gidan wasu…..
Asibiti
Kanshi ya dafe yana k’ok’arin yin kuka da gudu suka k’arasa wajenshi, kamashi Ammi tayi tana mashi sannu,
“Bari naje na kira likita”
Cewar Ammi dake k’ok’arin fita, hannunta ya rik’e gama, a hankali ya fara bud’e idanshi, fes ya ajiye idonshi kan Ammi, murmushi ta mashi, shima murmushin yayi, juyawa yayi ya kalli su Haneefa dake gefenshi, suma murmushi ya masu..
“Bari naje na kira doctor “
Girgiza kai yayi
“Ki barshi Ammi naji sauk’i, ki zauna dani bansan kiyi nisa dani..”
Kujera ta jawo ta zauna, tayi ta gumi d’ayan hannun na rik’e da hannun Haneef, cire mata tagumi yayi yace
“Ammi bakin ce tagumi ba kyau ba?”
“Eh ba kyau my boy”
“To miyasa kikayi?”
“Bakomai nadaina”
Girgiza kanshi yayi, ya k’ura mata ido.
“Ammi”
D’agowa tayi ta dubeshi jikinta duk ya mutu,
“Yadai?”
“Ammi forgive me please kaina zafi yakeman”
“Haneef please ka daina karyaman zuciya in shaa Allah zakaji sauki.”
Juyawa yayi ya kalli Haneefa yace
“Adda forgive me, zan tafi in barku ki kulaman da Ammi da my little bro, i knw its difficult amma nasan zaki iya ki cigaba da taya Ammi da adu’a komai zaizo maku dasauki, nd finally kice ma daddy ya yafeman, naso in ganshi, amma baizo ba,”
gaba d’ayansu kuka suke, “Ammi stop crying”
Kamo Mukhtar yayi yace
“Lil bro bazanyi doguwan rayuwa tare daku ba amma kasani ina k’aunarku, zan barku cikin k’unci a yanzu amma gaba zakuyi dariya.”
Fad’awa Haneefa tayi jikinshi tana kuka, d’agota yayi yace
“Kidaina kuka Adda nasanki da juriya please stop crying be strong, be strong for me kinji” d’aga mashi kai tayi, d’agowa yayi a hankali ya mata peck, “take care of my Ammi nd my lil bro” hannunshi ya kai kan fuskan Ramlah yace ki daina kuka kinji, now bless me kinji” d’agowa tayi ta share hawayenta tace
“Allah shi maka albarka”
Amsawa yayi da amin, peck yama kowa a kunci ya koma ya kwanta tare da had’a hannuwansu cikin nashi…..
Ji tayi wurin yayi shiru, da sauri ta d’ago ta kalli inda yake, hannunta ta kai kan k’irjinshi idan ba mafarki take ba Haneef bai numfashi, jijjigashi ta farayi tana kiran sunan shi amma ina Allah yayi nashi ikon kan Haneef fashewa tayi da kuka mai tsuma rai, kuka takeyi Haneefa ma kuka takeyi,
“Ammi mi yasamu Ya Haneef “
Cewar Mukhtar da bai fahimci komai ba, kamoshi tayi tace
“Haneef he’s gone, he’s gone forever” daidai shigowar Imran da Ahmad.
“What?”
Gaba d’aya suka juya ganin jin muryan waye, da sauri ya k’araso inda Haneef yake kwance yayi zai tab’ashi.
“Don’t touch him, don’t touch my son komi ya sameshi kune sila, now matarka ta kasheman yaro sai ku zuba ruwa k’asa kusha, amma kasani bazan tab’a yafe maka ba kaida matarka.”
Kanshi k’asa ya kasa magana ya kuma rasa abinda ke damunshi, yasan dai wani abu na damushi amma shi kanshi baisan ko miye ba…
“Calm down Ramlah yanzu ba lokacin da zamuyi magana baneba nan bari inje in sami doctor” Cewar Ahmad, fita yayi dan kiran likita…..
Yana fita ta d’ora kanta jikin Haneef tana kuka, gaba d’aya yaran kuka sukeyi, babu mai lallashin wani, tsaye yake kamar gunki ya kasa motsi zuciyanshi wani irin zafi yake mashi, duk da yasan yanzu yaran basu gabanshi, amma ya ji mutuwa Haneef saboda yaron ya shiga ranshi sosai..
Ahmad ne ya dawo da sallama yana gaba doctor na biye dashi, gaban gadon doctor ya k’araso gwaje gwaje yayi yakai minti goma yana gwaje gwaje, daga k’arshe da ya d’ago yace
“Sai dai muyi hak’uri Allah ya karb’i abunshi.”
Kuka ne ya kufce mata, ta k’arasa wajen gadon Haneef da gudu tana kuka,
“Haneef katashi dan Allah ka tashi munasanka ni dasu Adda dan Allah Haneef ka tashi”
Babu wanda baiyi kuka ba, harta likitan saida yayi kwalla.
Haneefa ce ta k’arasa wajenta ta kamo ta tace
“Ammi kiyi hak’uri Haneef ya tafi ya barmu adu’a zamu dinga mashi amma kinsan bazai dawo ba da ana mutuwa a dawo da babu wanda zai bari nashi ya mutu bai maidoshi ba, ki godema Allah ya ronki ya rasu yana neman yafiyarki dama gashi yaro bai balaga ba kiyi ta wakkali Allah bazai barki haka ba sai kinga sakamakonki nan gaba, kima gode ma Allah ya rasu ya huta da wannan rayuwan da muke ciki…”
Sakin baki likita yayi yana kallonta “dama akwai yara masu irin wannan baiwar? Lallai kowa da baiwar da Allah ya mashi..” ciki zuciya yake wannan tunani…
“Likita muje office kabamu bill d’inmu mutafi dashi dan yau za’a mashi sutura gobe in shaa Allah akaishi gidanshi..”
Ahmad ne ke fad’ama likita haka, fita likita yayi Ahmad ya bishi baya dan yayi clearing komai, su tafi gida da gawan Haneef. Saida Ahmad ya gama da asibiti ya biya bill d’in da aka mashi yadawo d’akin inda ya tarda wasu nurse sun shirya Haneef d’aukarshi akayi aka sashi mota, suka nufi gida……
***********
Abinda ya faru, Ahmad na fita daga cikin gidan, Imran ya biyoshi baya, harya tada mota zai tafi, yaji an bud’e gaban mota an shiga, bai tanka mashi ba ya ja mota yabar haraban gidan, saida ya tabbatar da ya hau titi, ya juyo ya kalli Imran, kauda kanshi yayi yace
” Ina zan kaika? Danni asibiti zan koma”
“Nima asibitin zani, inasan in ganshi inga halin da yake ciki..”
Juyowa Ahmad yayi ya kalleshi daga nan ya kauda kanshi bai k’ara mashi magana ba har suka iso asibiti……
************
Daidai bakin gate d’in gidan Imran, Ahmad yayi horn maigadi ya lek’o ganin motan Ahmad ne yasa ya koma da sauri ya bud’e masu gate, shiga yayi cikin gidan ya samu wuri yayi parking, suna fitowa mai gadi na k’arasowa
“Hajiya ya jikin Haneef? Ko an sallameshi ne?”
Ya fad’a yana kallon Ramlah, gaba tayi dan bata iya bashi amsa…
Ahmad ne ya bashi amsa da
“Allah yayi ma Haneef rasuwa”
Tun kafin ya ida Baba maigadi ya fara salati yana sharan kwalla, gaba d’ayansu sukayi cikin gida banda Baba maigadi da aka bari tsaye yana hawaye….
Suna shiga Ramlah ta saka hannu ta amsheshi daga wajen Ahmad tayi d’akinta dashi, zaune suke parlour Ahmad da Imran sunyi jugum jugum, babu mai ma wani magana. Da karairaya ta fito parlour bako sallama ta samu wuri kusa da Imran ta zauna, hannunshi ta zare daga tagumi tace
“Baby kadawo kenan? Wai inama kaje?”
“Asibiti naje”
Ya bata amsa.
“Aww hakane fa ya mai jikin?”
D’agowa yayi jiki ba kwari yace
“Yarasu”
Tab’e baki tayi tace
“Allah ya jikan nusulmi”
Amsawa yayi da
“Ameen”
Duk abinda ya faru idon Ahmad na kasu wani mamakine ya rufe shi,
“Anya matar nan kuwa tasan Allah? Duk abinda yafaru ita ce sila amma yanzu kalli yanda ta nuna abun bai dameta ba, zanyi maganinki…”
Cikin zuciya yake maganarshi, tana d’agowa suka had’a ido da Ahmad, wata harara ya watsa mata sai da gabanta ya fad’i…
Tashi tayi tace
“Baby natafi in kwanta sai ka taho”
Tana fad’in haka ta juya ta nufi d’akinta, Imran na d’agowa idanuwansu suka had’u waje guda shida Ahmad, harara Ahmad ya wurga mashi..
“Katashi kaje d’akin Ramlah ku zauna da gawan, ni zan zauna nan”
“Bazan iya zuwa ni kad’ai ba please muje tare sai mu kwana da gawan ita idan yaso sai ta tafi d’aki da yaran..”
“Akanmi zamu rabata da d’anta sai dai kai ku zauna tare da ita” marairaice mashi yayi yace
“Ban iya zama da ita kusa dani”
“Why?”
“I hate her, na tsaneta na tsani na ganta kusa dani duk idan tazo kusa dani daurewa nakeyi, wallahi bazan iya zama kusa da ita ba har mu kwana zan iya mutuwa nima..” Galala Ahmad ya saki baki yana kallonshi, dan tabbas baccin yasan waye Imran da sai yace shaye shayen zamani yafara, amma wannan ko ba’a fad’a ba kasan bayin kanshi bane ba, saboda irin san da Imran ke ma Ramlah kowa yana mamaki amma yanzu yana fad’in ya tsaneta….
Banza Ahmad yayi dashi, kamar ba dashi yake magana ba, kwanciya yayi bisa kujeran da yake zaune yayi, shima Imran d’in kwanciya yayi, alamun bazaije d’akin Ramlah shi kad’ai ba….
Ganin da gaske yake Ahmad ya mik’e yace
“Muje”
Ba musu kuwa yabi bayanshi, da sallama suka shiga d’akin zaune take k’asa ta kunna karatun qur’ani, ta d’aura kan Mukhtar bisa ciyarta da alama yayi bacci, Haneefa na gefenta tayi tagumi…
“Ramlah kuje d’akinsu Haneefa kubarmu zamu kwana da gawan”
Ta bud’a baki zatayi magana yace
“Ah ah karki man gardama kiyi yanda nace baki ganin Mukhtar yayi bacci kuje can d’in mu muna nan..”
Ba yanda ta iya dole ta tashi ta d’auki Mukhtar taja hannun Haneefa sukabar d’akin…..
****
Tana shiga d’aki fad’awa tayi kan gado tana murna, wayarta ta jawo ta danna kira, har wayan ta tsinke ba’a d’auka ba, k’ara dailling number tayi, saida ta kusa tsinkewa kana aka d’auka.
“Hello Mufeedah lafiya kike kirana cikin dare haka?”
Murmushi tayi tace
“Kiyi hak’uri Lash Ban iya bari sai da safe ban maki albishir ba.”
“Miyafaru? Ina jinki”
“Haneef ya rasu”
“Wane Haneef?”
“Yaron Ramlah mana.”
“Miyafaru? Gayaman dan nasan koma miye kece sila.”
Dariya tayi sosai tace
“Kamar kin sani.” Nan ta kwashe komai ta gaya mata, shewa sukayi gaba d’aya,. “Gaskia Mufeedah baki da kyau”
Ajiyan zuciya tayi tace
“Ay dama nace ni zanyi komai da kaina, sai dai bashi naso ya mutu ba wannan marar kunyar yarinyar naso ta mutu, dan Haneef ya d’an shiga raina…
Dariya Lash tayi tace
“Itama bani kokonto zaki gama da ita soon.” Dariya suka saka, haka suka cigaba da hira kamar wani abu bai faru ba daga k’arshe sukayi sallama kowa ya kwanta…..
9:00am
K’arfe tara daidai aka shirya Haneef dan kaishi gidanshi na gaskia. Fitowa akayi dashi za’a tafi dashi, tashi Ramlah tayi ta rik’e gawan tana kuka ganin haka yasa Haneefa kuka ita da Mukhtar duk wanda ke parlour babu wanda baiyi kuka ba, sai Mufeedah dake latse latsen waya…..
Dak’yar aka janye Ramlah daga jikin Haneef, tanaji tana gani aka wuce da Haneef makwancinshi na gaskia, ana fita dashi ta fad’i k’asa sumamma, da gudu mutane sukayi kanta, ruwa aka dinga yayyafa mata dakyar aka samu ta farfad’o. Tana farfad’owa ta had’a Haneefa da Mukhtar ta rungume tana kuka, babu wanda bai masu kuka ba, duk rashin imaninka sai kayi kuka……
Haka aka cigaba da zaman karb’an gaisuwan Haneef, duk wanda yasan Ramlah da ya ganta yanzu sai yaga canji, wasu suna zaton mutuwar Haneef ce ta mayarda ita haka…
Bayan sadakan bakwai, Ahmad ne zaune parlourn Imran, gaba d’aya ya tara Imran da Ramlah dan yanasan magana dasu, kallon Imran yayi yace
“Ina matarka?”
“Taje unguwa”
Ya bashi amsa. Ajiyan zuciya yayi yace
“Dama maganar da zanyi bata shafeta ba, zanyi magana ne akan kai da Ramlah da irin zaman da kukeyi…”
Kallon Imran yayi yace
“Da kai zan fara saboda kaine namiji kuma ikon gidanka yana hannunka, gaskia nayi mamakin irin sakacin da kayi akan iyalenka idan wani yace zakayi haka wallahi ni zan fara k’aryatawa amma gashi bawani yabani labari ba ni nagani yanda ka maida gidanka, duk da ba laifinka amma akwai sakaci ka kuma san ba ruwan Allah sai ya kama ka da laifin daka aikata, a gabanka matarka ta zama silar rasa d’anka amma baka d’auki mataki ba kuma nasan bazaka d’auka ba bance kuma ka d’auka ba dan nasan bazaka d’auka ba, amma duk bawani abu ya jawo maka haka ba rashin dagewa da azkar, numfasawa yayi, ya cigaba kaji tsoron Allah ka dawo hayyacinka kayi adalci tsakanin matanka iyakar shawara da zan baka kenan…”
Ramlah ya kalla yace
“Nasan ba amaki adalci ba amma ki dubi irin sanda mijinki yake maki ke da yaranki a da dakuma juyawar da ya maku yanzu kinsan ba laifinshi baneba kiyi hak’uri ki dage da ibada in shaa Allah komai zai koma kamar ba’ayi ba, kuma kiyi hak’uri da d’aukan mataki akan rasuwan Haneef kibar ma Allah ya saka maki karki manta Haneef bazai wuce ranan ba kawai dai Mufeedah ta zama sila, kiyi hak’uri nasan kinayi to ki k’ara akan wanda kikeyi…”+
Kanta k’asa tace
“In shaa Allah zan cigaba da adua kuma nabar maganar”
“Alhamdulillah”
Abinda Ahmad ya furta kenan, kallon Imran yayi ko zaiyi magana amma baiyi ba kuma da alamu bashi da niyar yin magana, girgiza kanshi Ahmad yayi yace
“Akwai wani malami daura da akaman maganarshi adu’a yakeyi in shaa Allah zanje wajenshi zuwa jibi komi zaizo k’arshe..”
“Allah shi yarda”
Cewar Ramlah., sallama ta yima Ahmad ta tashi ta koma d’aki, kallon Imran yayi yace
“Ranka ya dade zan wuce gida”
Tashi yayi dan ya rakashi, suna isa k’ofar fita parlour sukaci karo da Mufeedah ta dawo, kallonta Ahmad yayi sama da k’asa, ya wurga mata harara. Gabanta ya fad’i ta rasa dalilin da yasa da taganshi take fad’uwan gaba, rab’asu tayi ta wuce.
Imran ne ya washe baki
“Baby sannu da dawowa”
Inda yake bata kalla ba bare yasa ran zata amsa maahi. Tab’e baki Ahmad yayi ya wuce, suna fita haraban gidan, Ahmad ya dubeshi yace
“Yanzu haka matarka ke fita Imran? Wani irin freedom kaba yarinyar nan? Kalli yanda ta fita riga da wando ne fa jikinta amma kabarta ta fita haka anya Imran kwakwalwanka bai tabu ba?”.
B’ata fuska yayi dan baisan maganar. Murmushin takaici Ahmad yayi yace
“Na tab’a maka yar gwal ko? Shiyasa kake b’ata fuska?”
Shiru yayi bai bashi amsa ba, shima bai k’ara cewa komai ba ya isa gaban motarshi, ya shiga ya tada mota yabar haraban gidan ba tare da ya kalli inda Imran yake ba….
Komawa yayi cikin gida, d’akin Mufeedah ya nufa, yana zuwa ya murd’a k’ofa, cikin rashin sa’a kulle ya tarda k’ofan, buga k’ofan yakeyi amma tak’i bud’e wa haka ya hak’ura ya koma d’akinshi….
BAYAN KWANA BIYU
Ahmad ne ya shigo cikin gidan da sallama ba kowa parlour, waya ya zaro ya kira Ramlah bugu biyu ta d’auka.
“Gani parlour”
Abinda yace kenan ya kashe waya, daga kitchen ta fito rik’e da flask d’in ruwan zafi.
“Ashe kina kitchen?”
Murmushi tayi tare da gaidashi, amsawa yayi fuska sake yace
“Ina Imran d’in?”
“Yana d’akin Mufeedah”
Tabashi amsa, waya ya zaro ya kira sai da ta kusa tsinkewa kana aka d’auka.
“Ina parlour”
Yana fad’in haka ya kashe wayarshi, Jim kad’an sai gashi ya fito, da fara’a suka gaisa, inda Ramlah take bai kalla ba inda sabo ta riga da ta saba…
“Ramlah zanje daura kamar yanda na gaya maku dan haka shiyasa nazo In sanar daku.”
Haka kawai taji gabanta ya fad’i, jikinta sanyaye tace
“Allah ya maidoka lafiya”
Ta juya ta nufi d’akinta, amsawa yayi da
“Ameen”
Hannun Imran yaja suka fita, saida suka isa bakin mota yace
Imran zan tafi kuma kasani tafiyan nan zanyi ta ne dan kai, inajin jikina ba dad’i amma daurewa zanyi in tafi saboda nasa raina da wannan tafiyan kuma inasan ka koma Imran d’inka na da, Ina san ka saka wannan a zuciyar ka Ramlah bata da kowa saini ni kad’ai na rage mata gashi nima zan tafi ba lallai baneba in dawo inasan kaman alk’awarin duk runtsi bazaka rabu da Ramlah ba, a lokacin da na barku Ramlah bata da kowa sai kai inaso kayi hak’uri ka rik’eta matsayin mata kuma matsayin k’anwa, dan nasan ko bayan raina watarana sai gaskia tayi halinta sai ka koma Imran d’inka na da, kaman alk’awarin zaka rik’e Ramlah da yaranta…”
Jiki sanyaye ya d’ago ya kalleshi yace
“Na maka alk’awarin bazan rabu dasu ba zan zauna dasu duk da a yanzu babu wanda nafi tsana irinsu amma zan zauna dasu, kuma zakaje lafiya kadawo lafiya..”
Hawayen dake mak’ale kan fuskan Imran suka gangaro, rungume juna sukayi sun kai minti biyar kana suka saki juna, shiga mota Ahmad yayi ya tada, lek’owa yayi ta window yace
“Kace ma Princess, koda ban dawo ba ta cigaba daga inda na tsaya I know zata iya, I trust her…”
D’aga mashi kai yayi alamar “to”, motarshi yama wuta ya bar haraban gidan, d’aga mashi hannu Imran ya dingayi har sai da yaga ya bar gidan kana ya sauke hannunshi ya koma cikin gida, jikinshi duk babu kwari……
Haka Ahmad ya hau hanyar daura sai fatan Allah ya kaishi lafiya ya mai doshi lafiya…
FLASH BACK
Imran Sadeeq haiffen d’an katsina ne, a unguwar saulawa, maihaifiyar Imran ta haifi mata biyar amma babu wanda ya tsaya, suna da shekara uku suke fara wasu k’uraje daga nan sai su mutu, tun da tasamu cikin Imran take rok’on Allah yasa ya tsaya harta haifeshi bata daina rok’on Allah cikin Imran na da wata biyar mahaifinshin ya kwanta ya rasu sanadiyar rashin lafiya da yayi, Imran har ya girma ya wuce shekarun da yaranta ke mutuwa, San duniya ta d’aukeshi ta d’aura akan Imran amma duk da haka bata fasa bashi tarbiya ba, kuma ta bashi ilimin boko da na Allah. K’awancen Ahmad da Imran ya samo a saline tun suna yara unguwa d’aya suke, haka makaranta d’aya sukayi tun daga primary har zuwa jami’a dake cikin garin katsina…
Ahmad d’an k’anin baban Ramlah ne Alhaji Habeebu, iyayenshi sun rasu sanadiyar gobara da sukayi cikin dare lokacin Ahmad yana gidan yayan babanshi, a lokacin baisan mutuwa ba shiyasa mutuwar bata dameshi ba. Bayan rasuwan iyayenshi gaba d’aya rik’onshi ya koma wajen yayan babanshi, ba abinda ya nema ya rasa na rayuwa shiyasa bai San minene maraici ba…
Suna aji hud’u primary school shida Imran, Aisha matar Alhaji Habeebu ta haifi d’iyarta kyakyawa, wadda taci suna Ramlah tunda Imran ya ga Ramlah yace ya samu mata, duk idan ya dawo daga makaranta yana nan mak’ale da Ramlah bacci kawai ke rabashi da ita, shak’uwa mai k’arfi ta shiga tsakanin Ramlah da Imran ko hannun wa take da taga Imran ta dinga kuka kenan sai an sauke ta ta tafi wajenshi. haka Ramlah ta taso cikin so da k’auna kowa santa yake saboda Ramlah nada shiga rai, duk abinda Imran ya samo ramlah yake kawo mawa. tana girma shak’uwa na k’ara shiga tsakanin ta da Imran….
Imran na aji biyu jami’a lokacin Ramlah na ss2 lokacin gaba d’aya komai na budurwa ya gama fito mata, gakuma samari da suke kawo Mata hari, ganin haka yasa hankalin Imran ya tashi, samun Ahmad yayi ciki damuwa shi dai zai gaya ma Ramlah yana santa, dan gani ya keyi kamar za’a kwace mashi ita. Dariya Ahmad yayi har yana kama ciki yace
“Ai sai da nace ka gaya mata kace kafisan sai ta gama makaranta to yanzu ay gashi nan kanaji kana gani zata zama rabon wani..”
Bugu ya kai mashi Ahmad ya goce yana dariya.
“Ramlah ta wace ni kad’ai babu wanda ya isa ya mallaketa sai ni dan haka kasa a ranka yau zan gaya mata abinda ke cikin zuciya”
Dafashi Imran yayi yace
“Abinda ya kamata kayi kenan dan haka ina bayan ka d’ari bisa d’ari..”
Rungume juna sukayi suna dariya cikin so da k’auna…..
*********
Kwance take d’aki wayarta tayi ringing, yi tayi kamar bazata d’auka ba sai da wayan ya kusa tsinkewa kana ta d’auka ganin wanda ke kiranta ne yasa ta fad’ad’a murmushin ta d’auka tayi cikin shagwab’a tace
“Ya Imran Ina ka shige duk yau banga ka ba?”
Wani irin murmushi ya saki wanda shi kad’ai yasan fassaranshi yace
“Yi hak’uri angel mun fita ne da Ahmad amma after magrib zamu dawo so ki shirya ina da maganan da zan gaya maki..”
Bai jira mi tace ba ya kashe wayanshi, kan gado ta fad’a tare da sakin murmushi mai tarin ma’ana kala kala ita kanta tasan idan tana tare da Imran Wani irin yanayi take tsintar kanta dashi, wanda ita kanta batasa ma’anar shiba kawai ta barshi akan shak’uwa dake tsaninsu ne. Haka ta dinga juyi bisa gado tana murmushi da haka har bacci yayi gaba da ita…..