MALIKA MALIK CHAPTER 14 BY JANAFTY
Yana Nunata da yatsa cikin Fushi ya Furta”Ashe haka kike Zahra bansani ba,agidan Uban wa na gayamiki zan saki Malika in ta haihu..? Yaushe na taba tattauna wannan mganar dake don Ubanki..? Yafada yana kwalalo mata ido,..
Daga Zahran har Saleema atare jikinsu ya Fara rawa,Zahra na Dafe da kunci lokaci daya hawaye suka wanke mata Fuska ganin irin Tozarcin da Saleem yayi mata agaban kishiya da yan”uwanta harda zaginta,ganin haka yasa ta jajige Razanarta ta mike ga kanta tana Fadin”Eh mana kazo da borin kunyama Tunda kaga gaban matarkace? in ba kai ka gayamin ba wazai Fadamin ba,ko kasheni zakayi bazan Fasa fadan kai ka gayamin baka Son Malika ba, Baka kaunarta,kai cemin ma kayi baka Kaunar mai kaunar….”Jikake Tim..”!Zahra ta Fadi akasa,wanda Saleem yasa kafanshi ya kwasheta zuwa kasa,kafin ya fara kokarin kwancen belt din wandon Jeans din dake jikinsa cikin Zafin rai da Zuciya yake Fadin.
“Ba malika ne baniso ba,kece bantaba kauna ba Zahra,kuma yau zan tabbatar miki da cewa Na tsaneki…!..”Yafada yana kwanto belt din Malika ce ta mikama Joda Ayda ta isa gareshi tana Riko hannunshi take Fadin”Plz mallam A’a kada kafara ba mutumcinka bane,juz leave her,ka barta da Halinta..”Fizge hannunshi yayi har sai da Malika ta kusa Faduwa ko,sai da tayi da gaske,ta iya tsayuwa bisa kafafunta dakyau.
Bai Saurari Malika ba,ya shiga Tsulama Zahra belt din ba ji,ba gani yana Fadin”Zaki fadamin waya gayamiki kokuwa haryanzu kina kan bakanki..”Yake Fada yana Shimfidamata belt din ta ko’ina,Itako Tun tana Dauriya Harta Saki baki tana ihu da kuka,Joda ko sai dariya take ranta yayi mata Dadi,Malika ce idanuwanta ya cika da kwallah don ita bata saba ganin Tashin Hankali ba,Wajen goggo Hadiza ta nufa Tana jan hannunta take Fadin”Goggo don Allah ki saka baki,kiba mallam Hakuri don Allah ya bar dukannta..”Goggo Hadiza tace”Ki rabu dashi Yanzu ko nayi mai mgana baji zai yi ba,kema kiyi Shuru da Bakinki..”
Dole Malika tayi Shuru tana Raba ido itako Saleema jikinta ne yakara Daukan mazari saboda tsoro ta Rakube jikin bango tana rawan sanyi da makyaryarta tana Tsoron kada Zahra taji duka tace abakinta taji,ai tasan yau kwananta ya kare,itako Zahra ganin zai mata illah ne yasa ta Rike belt din da hannuwanta duka biyu tana kuka take Fadin”Wlh ba kai ka Fadamin ba,zan Fada…!Zan Fada wlh…”Take Fada tana kuka kamar wacce ake zare Ranta,.
Idanuwanshi Jawur,yace mata”Ki yi hanzari sanar dani wani munafikin algumgumin ne ya sanar dake wannan mganar,har kike jifan Matata uwar ya’ya da ita,ki sanar dani Wanene ko wacece…? Ya Fada cikin Tsawa Zahra na Sosa gefen kunnenta inda Belt ya sameta,😂kallon Saleema take wacce ke girgiza mata kai alamar karta Fada,ganin haka yasa Saleem ya Ware ido yana kallon Saleema yana Fadin”Au kece Don Ubanki…”?Yafada cikin Tsawa da Tambaya yana nuna ta da belt din dake hannunshi.
Saleema ta fara ja da baya tana mannewa jikin bango take Fadin”A…A
..A’a Bani bace fa…”Take Fada har idonta ya ciko da kwallah,ganin haka yasa Zahra tayi Saurin Cewa”Wlh ita ta Fadamin,ita ma tace Wai bakason Malikan wai..Wai…Wai…Kuma..” wai Kuma me..? Ya katseta cikin Tsawa yana kwalolo mata ido,ganin haka yasa Zahra tace”Wai ba don Allah ka maida Malika dakinta ba,sai don kudin mahaifinta,,(Karya ta karama Saleema,don so take yarda aka jifgeta toh ayima Saleema mafiyinshi domin duk Abunda ya Faru itace Sila.)
Baki Saleem yakama cike da bakinciki da mamaki yake bin Saleema da wani mugun kallo,itako jin Abunda Zahra ta Fada yasa tafara mgana tana hawaye “Wlh karya takemin Yaya,ban gayamata haka ba,sharri ta kullamin wlh Allah..”Tafada tana kara matse jikinta,nan ko Zahra tahau Rantse rantse tana Fadin Saleema ta gayamata,sai kaji tashin zencen Zahra bata rage duk makircin da Saleema ke kitsamata ba harda karya ta kara,saboda tana so aci uban Saleema dakyau sosai,Zahra harda Sanar dashi Saleema tazo ne,don su hadu su Fitar da malika daga gidan..”
Ba Saleem kadai ba hatta Su joda sai suka rike baki suna mamakin Saleema,shiko Saleem nufarta yayi yana mirmishin takaichi yake Fadin”Saleema kanwata..Hmmm,umh…”Yake Fada yana Nufota ganin haka yasa ta nemi guduwa taku daya yayi ya Rikota,Ai sai ta zame tana so tana bashi hakuri tana kuka,wuyan Rigar Atamfanta dama ya riko,ai bai tsayawa wasa ba ya Shiga tafkan Saleema kamar Allah ya aikoshi,Malika tayi kokarin Cetonta,ammh saboda yadda Ranshi ya baci ko gani bayayi har sai daya sameta ahannu tayi baya tana sosa wajen,Ganin haka yasa joda tace”Don Allah Anty malika ki bari yaci ubanta,ai wlh tayi Abun duka haba,dan’uwanta Fa..”Goggo Hadiza bata yi mgana ba sai da taga ya kai Saleema kwance yana duka kafin ya hadasu ita da Zahra ya cigaba da tafkansu atare,dkyar ya saurari goggo Hadiza ta karbi belt din dake hannunshi ammh bayan ta bari sun lallasu,domin sun jiki kowannensu jikinsu duk shatin belt ya kwanta kuka suke kamar ransu zai Fita.
Yana huci da Numfarfashi yake Fadin”Saleema,Zahra dukkanku Babu Abunda zence muku sai nagode da sakayyar ku gareni,kunyi ikirarin zaku kori Malika daga gidan daku kukazo kuka tarar da ita,to Alhamdulilah kafin ku koreta ku bari ku Farayin gaba,Zahra wlh nayi nadamar Aurenki saboda haka kije na SAKEKI SAKI DAYA,…”Malika ta kwalalo ido,goggo Hadiza ko Fadi take”Assha Ashha..Saleem hukunci yayi Tsauri..”
Hannu ya daga yana Fadin”goggo kibarni,wlh aurenta ya Fice daga kaina,dama kuma kadarrace ta sani aurenta bawai don ina jinta acikin zuciyata ba..”Yafada yana huci Zahra ko hannun ta daura bisa kai tana Fadin”Wayyo Allah na Shiga uku ni Zahra Fatima,don Allah honey kamin rai kada ka rabu dani..”Take Fada tana kuka,tsaki yaja kafin yace”Dallah Rufema mutane baki sakarya Wawiya kawai,ke har kina da bakin yima malika gori akan bana Sonta,kin ma san miye so,Toh bari na gayamuku Abunda banta gayama kowa ba,ko gabanki kike wankewa kibani wlh bazaki kamo mtsayin malika acikin Raina ba,in kince zaki kishi da ita,sai dai ki mutu wlh don bazaki taba samun mtsayin data samu ba,saboda haka ki tararra ina inaki kibarmin gida ki koma gidanku ki kuma Sanar da iyayenki wajen Gudirin koran kishiyane Reshe ya juye da mujiya,ke kuma…”Yace yana nuna Saleema da hannu.
“Kin kyauta in kuma nuna min Cewa kedin kin Fita Dabam acikin ya’yan Ummi da Abbi,shegiya mai Fuskar alade ki rasa inda zaki zo kiyi munafuncinko da gulma sai gidan Dan”uwanki harkina bada goyon bayan ayima matar dan”uwanki wulakanci Saboda mugun Halinki,baki Tunanin kema wata rana gidan wani zaki,ko don kina ganin Sadiq bai da kanwa baki Tunanin yana da ya’yan yan’uwa..? kema za’ayi miki haka? ya zakiji? ko kuma ayima yar da zaki Haifa zaki so..? Amsan ita ce A’a ammh kuma kike kokarin cima wata Zarafi agidan Mijinta,wlh Saleema Tir da munanan Halinki kema ki tararra kayanki ki barmin gida yanzu ba sai anjuma,kuma yanzu zan kira Ummi da Abbi na sanar dasu Abunda kika aikata,in kin koma chan ma kikara amsan hukuncinki,Dabba kawai wacce batasan
nata ba..”Yafada yana Shureta da kafa kafin ya juya afusace ya Shige dakin yana banko kofa Ranshi bace kamar Zuciyarsa zata Fito waje.
Malika ce tabi bayanshi Da Sauri tana zuwa jikin kofa tajita akulle gam,baya ta dawo tana Dafe kai,Joda ko dake Rike da Ayda cikin Towel,ta fara Dariya kamar cikinta zai kulle,Zahra da Saleema da suka ji jiki,suka bita da kallo idanuwansu jajir,kowacce Fuskarta ta chanza Saboda Wuya,Saleema ta fara Ture Zahra wacce ke kan Kafadanta tana kuka,dagowa Zahra tayi tana kallonta cikin bacin Rai take Fadin”Allah ya isa tsakani na dake Saleema,gashinan wajen zugani na Raba Malika da honey ni kin kashemin Aure..”Tsaki Saleema taja Tana mikewa dakyar take Fadin”Allah ya isa ta biki munafuka,daman chan da ra”ayinki na ganki da baki da mugun Nufi akanta dana kawo Shawaran ai ba Dole nayi miki ba ko? Tafada tana mata wani Wulakantattacen kallo,ganin haka yasa Zahra dingisawa ta mike tana cakumo wuyan Zahra tana kuka take Fadin”kece ai munafuka Komin mugun Nufina inda ban samu goyin bayanki ba,da bazan iya yi ni kadai ba,Ammh saboda rainin wayau bayan kin kashemin aure,shine kike Fadamin mgaanar banza,Ran Saleema ya baci ta kalli Zahra tana Fadin”Sakarni don uwarki…”Baki Zahra ta rike tana Fadin”Lalala..Har da zagin Uwata,to anki asakeki din don uwarki kema,Tunda uwa batafi uwa ba..”Jin haka yasa Saleema ta Fizge riganta daga hannun Zahra tana Fadin”Andai ji kunya wlh,Ni sai yanzu nake nadamar biyemiki Domin Tun Farko na gane ke Shashashace..”Tafada tana hararanta kafin ta Shige dakin Zahra tana Sosa bayanta inda belt din ya Shigeta dakyau
Kukan kura Zahra tayi tabi bayanta tana Fadin”Kutumar ubanchan To Fitomin daga daki..”Daga cikin dakin Saleema ke bata amsa da Cewa “Dakin ki ko dakin Yaya Saleem,don ko banza ni ina da gado agidan ko yau ya Saleem ya Fadi ya mutu,ke fa.? Saki ne fa akanki kinga ko baki da wani iko da dakin nan..”Nan suka Shiga suna zagin junansu da cin mutumci,Malika ta rike bakwai aranta tana Fadin”Lalle Zamanta zamafara yasa ta Fara karatun Duniya,Joda ko goggo Hadiza daki suka koma suna fadin Allah Shi kyauta,dama Ramin karya kurarrene,kuma dama haduwar abota indai ta munafunce bata karfo,kuma indai tatashi Rabewa bata rabewar arziki.
Haka kowacce ta Fito dauke da katon akwatinta da mayafinta bisa kai,har suka Fice daga gidan suna tsiya taku da tona ma juna asiri suna zage zage kamar zasu daki juna,koda suka isa tasha suna tare,kuma da Saleema ta hau motar Abuja,itama Zahra nan ta Shigo nan Saleema ta kalleta tana Fadin”Ke mara Mutumci ina zaki danaga kin Shiga motar Abuja..”?
Zahra bata tankata ba Sai da taja mata wani dogon Tsaki kafin tace”Kina da son bata bakikin,aikwai inda zani wanda ya Wuce gidan iyayen Mijina,chan zani muje kowa ya maimata Abunda ya aikata nabama Ummi hakuri na Roketa ta Roki Honey ya maidani dakina,don ni dai ko giyan wake nasha bazan koma gida ba..”Baki Saleema ta bude kafin tace”Bazan taba bari ki koma gidan Ya Saleem ba Zahra,domin dama chan baki dace da yayana ba Malikar dai itace ajinsa…”Baki Zahra ta mele kafin tace”Daga baya kenan,wai anyi Sadaka da karuwa,kanki kuma akeji yanzu..”Tafada tana juyama mata keya,har mota tatashi suna Tsiya har sai da wata mata dake ciki ta musu mgana kana suka Saurara.
Shiko Saleem dama yana Shiga dakinsa Bayan ya kulle kansa,bai kira Ummi ba sai da fushinsa ya Fara sauka kana ya kira Ummi yana gayamata Abunda ke Faruwa kamar yayi kwallah,Ummi da Ranta ya gama baci da jin Abunda Zahra ta aikata kuma Abun haushi harda Diyarta Saleema cikin Fushi da takaichi tace”Ina Fatan kaci uban Shegiya ka barta kwance ko,…?”Yace”Nadai mata hukunci Ummi buh ita Zahran na Saketa gaskiya Ummi,bazan iya zama da ita ba wlh..”tsaki Ummi taja kafin tace”To waya kwasota ai ni dama Tun ranar dana Fara ganin idon yarinyarnan nasan akwai zence,Allah ya kyauta in ta yi hankali sai kadawo da Matarka..”Shuru kawai yayima Sukaci gaba da mgana,nan yake Tambayanta Abbi don yace ya kira Nombarshi bata,nan take sanar dashi yana meeting da Shugaban kasa,sun dade suna mgana da Ummi kafin kowanne ya yanke kiran.
Da Ummi take Fadama Hajiya Abunda ya Faru mamaki da Haushin Saleema ya kamata,tayi ta sababi ita kadai,harta Fadin bari kabirun ya dawo azo ayi mganar aurenta kawai Da Yaron nan Sadiq,tun bata da mutumci,Zuwa yammah kuwa sai ga Zahra da Saleema sun Diro,Ummi takaichi kamar ya kasheta,ganin yadda Zahran ke kukan munafunci,ko dayake bata ga laifin Zahra ba,babu babban mai laifin irin Saleema,Ummi tayi Fada kamar ta daketa,haka Hajiya babba Ta nuna mata abunda tayi Rashin kishin kanta ne,domin har Abada Saleem dan”uwanta ne,Dakin dai Saleeman Zahra ta sauka,ammh ko mgana basu ma juna,Ummi tace ta jirata zuwa gobe suyi mgana da Abbi,Abbi koda yadawo Ummi ta sanar Shuru yayi yana maimaita Sunan Saleema,Ummi ya sa ta kira masa Saleeman yayi mata Fafata yaci Mutumcinta sosai kuma yace maza ta Shirya kayanta a Asibitin Mallam Aminu kano zatayi Housemanship dinta,Saleema tayi kuka da Nadamar dama bata aikata Abunda ta aikata ba hakuri tayi tabama Abbi,ammh yace wlh chan zata,kuma mganar aurensu da Sadiq kwananan zata tashi,bazai zura mata ido tana bin gidan Dan”uwanta tana Assasa rashin zaman lafiya atsakanin matanshi ba.
Ummi ko datayimai mganar yasa baki Saleem ya maida Zahra dakinta,kiyawa Abbi yayi yace mata dama Tun mganar Auren Zahra ya yayi alqawarin bazai kara shiga Sha”anin gidan Saleem,ta barshi shima magidancine,kuma hukunci da yayanke Shine Daidai gareta,ganin haka yasa Ummi ta nemi izininshi gobe in ta dawo daga court don tana da wata Shari’a zata saka Zahra agaba ta maidata Zamfara,Tunda ta nuna tayi Nadama,Bai damu ba yace adawo lafiya.
**************
Saleem bai saki Fuskarshi ba sai da gari ya waye kana ya fara warwarewa,ammh itama malikan tasha Fada,Akan meyasa in Zahra tayimata wani Abun bata sanar dashi,toh meye amfanin ta amtsayinta na Uwargida,kuma yayimata Fushin yadda ta nemi ta yarda da kalaman Zahra na cewa zai saketa,ya sanar da ita in har zai saketa ai ba Tsoronta yakeji ba dabai Fadamata ba,Ita dai Malika nata ban hakuri da kuma mai alqawarin insha Allahu haka bazata kara Faruwa ba,bai saki ba Fuska Sosai don Ranar ko breafast baiyi ba ya Fice zuwa wajen aiki,Ranta duk ba Dadi don bata son wannan Saleem din nata tafison Abu Ayda na yanzu yafi dadin zama da Dadin Sha’ani.
Dukkansu basu san da Zuwan Ummi ba,sai gashi wajen karfe 1 sai ga Ummi da Direba tazo tare Da Zahra,haka Malika ke rawan jikin Tarban Ummi,ita kuma tana Fadin tazo ta zauna jego take,Sai bayan su gaggaisa ne da Malika da goggo Hadiza da Joda,Tunda tazo Ayda na rike a hannunta Zahra na gefe ta rabe kamar wata mutuniyar kirki da akwatunta agabanta,Ummi ce ta tambayi Saleem,Malika tace yana wajen aiki,waya Ummi ta Fito dashi ta kirashi tace yazo gata agidanshi tana jiransa yanzu zata Tafi ne,bai jima ba sai gashi yazo Fuskarshi ta kara Dinkewane lokacin daya cikaro da Zahra,cogewa yayi yaki zama yana Fadin”Ummi dama wannan munafukar gida taje,ke Abuja nan ne gidanku da zaki tafka hauka miji ya sakeki kuma kije chan.? ya Fada yana kallon Zahra cike da Tsana.
Ummi ce ta dakatar dashi Da Fadin”Saleem zo ka zauna bani son Shanshancin naka..”Jin haka yasa yazo yazauna akasa akusa da ita yana gaisheta,ganin haka sai Malika tatashi zata Shiga ciki,sai Ummi ta kirata ta dawo ta Umarceta data zauna domin mganar ta Shafesu dukkansu ne,dama Joda da goggo Hadiza tunda suka gaisa da Ummi suka koma daki,Kafin Ummi tafara mgana sai data fara Rokon malika gafara bisa Abunda Salema da Zahra suka aikata gareta,Kusan Malikar Taku da Sanyin Hali nan da nan ta yafe musu dama bata Rikesu ba,Ummi taji dadin haka harsai da Ta nuna afuskarta,Bangaren Saleem kuwa sai da Ummi ta Fitomai a uwa sak kana ya yarda ya yafema Zahra har ya maidata dakinta,ammh ya gayama Ummi da Sharadi wlh tallahi last chance ya bata in takara duka Sakin biyu zai cikasa mata,Nan Ummi ta yarda bayan ta sa Zahra ta duka tabama Saleem hakuri,shi kuma yace bazai hakura sai inda Ta Roki malika
ta yafemata tukunnah,don ita suka batamawa,Dole Zahra tabama Malika hakuri ba don Ranta yaso ba,sai don Tsira da Aurenta datake matukar So,malika batayi gaddama ba tace ita bata taba kallonta da wani Abu ba,taje ta Yafemata,Ummi taji dadi sosai nan ta tarasu tana ta yi musu Nasihan zama lafiya da Hakuri da juna,kafin daga karshe tayi ta sakama Malika da Saleem albarka tana bayyana yadda suke alfahari dasu.
Ummi bata tafi ba sai datayi la’asar ammh kafin tatafi sai da takara jan kunnam Zahra sosai,ta nuna mata taji kuma insha Allahu itama zata zama mace tagari kamar Malika,Ummi kuma dazata tafi ta Shiga har dakin Malika ta damkama wani Abu abakar leda tace zata kirata awaya ta mata bayani karba Malika tayi tana ma Ummi godiya,Dole Ummi ta ijye Ayda wacce take nanike da ita Tunda tazo ammh tadaukan ma Abbi sabuwar Amayarshi hotuna,don ta kara Nunamai yadda Ayda takara girma,har bakin mota suka rakata ita da malika suna dagamata hannu har motarsu ta Fice Daga get din gidan.
Suna tsaye Saleem ya juya zai koma cikin gida Malika ta riko hannunshi tana kallonshi bai kalleta ba,sai ma wani hade rai dayakeyi,Matse hannunshi tayi tana Fadin”Maraba da Uwa ta gari gaakiya Ummi tayi Abunda kowacce uwa ta dace tayi,naji dadin yadda ta dawo da Zahra dama harga Allah banji dadin Hukuncin daka yanke ba..”Wani kallo yayi mata kafin ya Rike hannun data Rike shi dashi yana Fadin”Uhm ke murna ma kikeyi ko? kinsa me,ma Umarni zan baki ba Shawara ba,ni nasan zahra ba Tuban gaskiya tayi ba,duk Randa ta sake Miki gori ko wata mganar banza ki daki bakinta sai yayi jini kafin ni nazo nayi mata mai dalili..”Baki ta rike tana yar dariya tace”Wane ni? Ka Rufamin Asiri ,Insha Allahuma bazata kara ba.”Jinjina kai yayi kafin sufara Taku zuwa cikin gida,.
Mirmishi Malika keyi kafin tace”Mallam yaushe zamu dora daga karatunmu..”Bai kalleta ba yace”Duk Ranar da Ummi Ayda ta Shirya toh Abu Ayda Shima ashirye yake..”Dariya tayi tana kallonshi kafin tace”Na tambayeka…? Yana kallonta ya dagamata kai,Idanuwanta na cikin nashi tace”Da gaske ne,Abunda ka Fadama Saleema da Zahra..? Gira ya dagamata kafin yace”Me…? bata Dauke idanuwanta akanshi ba tace”Kana SONA….? Sun dade suna kallon Juna cike da wani yanayi kafin shi ya lumshe ido ya bude yana Fadin”Nan ba wajen da zamuyi wannan mganar bane kibari kigama wannan jegon Tukunnah..”Yafada yana jan karan hancinta,batayi mgana ba,illah kanta data aza bisa kafadanshi,shikuma ya sako da hannunshi guda daya ya Rumgumeta yana Sakin Ajiyar Zuciya,ji yake kamar ya maidata cikinshi saboda yadda Zuciyarsa ke bugawa Saboda ita.
Saleema ko kwana biyu takara Abbi ya Tarkatata ta koma Kano cikin Asibiti inda zatayi Housemanship dinta,Saleema taji kunya Sosai saboda harda ya marwan Sai da ya kirata ya mata Fatata,ya zageta kamar ya fito ta wayar yaci ubanta haka yakeji,Kuka ta sakaimai tana bashi hakuri,yace bashi zata ba Hakuri ba,Malika da Saleem zata bama hakuri,haka ko akayi Ummi ta Turamata Nombar Malika ta kirata ta bata Hakuri malika tace ta yafemata wlh.
Shiko Uban gayyar sai da ta kwana2 tana kiranshi bai dauka ba,sai ana uku kana ya dauka,Saleema na kuka tana bashi hakuri tare da alqawarin tayi Nadama kuma bazata kara ba,Bai hakura ba sai da ta sanar dashi takira Malika ta bata hakuri kana ya hakura har sukayi mgana tace tana kano,Nasiha yayi mata na ta maida hankali kan karatu kafin suyi sallama,shiko Sadiq dayaji lbri wajen Ya marwan Takakkiya yayima Saleema har kano ya nuna mata tayi Wauta,Saleema dai Tashiga uku kowa ganin laifinta yake,Nadama ko tayishi ba adadin Tayi Nadamar Abunda ta aikata,daga karshe Goge Nombar Zahran tayi acikin wayarta ma gabadaya ta maida hankalinta kan Abunda ya kawota.
*******************
*AFTER SOME DAYS*
Zahra ta chanza kamar ba ita ba,yanzu babu Rawan kan nan ko kadan,domin shikanshi Saleem din bai Fara kulata da cin abincinta ba,sai da ya tabbatar da Nadamarta kana,kuma ya saka mata Dokan dole da Safe ta rinka zuwa tana gaida Malika don Tana gaba da ita.
Toh Babu laifi Duk batasaki jikinta ba,ammh zata bita har daki ta gaisheta ta dauki Ayda ta mata wasa,ta gaida Goggo Hadiza tayi Fito,joda ma sukan gaisa in suka hadu,ammh ba sosai ba don ita Joda har yanzu gani take Zahra nada Sauran wani Abu Ranta,domin ko Fuskarta ka kallah zaka ga bata Fara’a Sosai.
Malika bata tsaya wasa ba tacigaba da karatunta wajen Malaminta ,gefe daya ga kuma girkin datakoyo domin Tunkafin ta haihu dama ta iya wasu,saboda Shiga kichen din datakeyi tana ganin yadda Joda keyi,Shiyasa ta zage Damtse kafin Joda tatafi ta samu ta koyi wanin Abu,kuma ba laifi tana da kwalkwala komai daukeshi takeyi,Ga kuma Shirin Akushi da Rufi na Arewa baya Wuceta shima tana karuwa dashi sosai,Maman Abba bata son da wannan kalmar zata gode mata ba,domin taba Rayuwarta dukkan wata gudummuwa,shiyasa ta hadamata Turamen Atamfa masu kyau da Tsada guda biyar da Kuma kudi gefe daya ga Naman suna data dibanta da yawa wanda dama su sukayi wahalanshi harta mutanen Kumo da Malumfashi sai da aka aika musu dashi,harda yan group din Malika malik paid da kuma Hafnan and Janaf paid group suma kowa ya samu kasonshi😂,Maman Abba kin karba tayi Sai da goggo Hadiza ta saka baki kana ta karba tana godiya sosai.
****************
Ana Saura kwana biyu Malika tayi arba’in Sai ga wayar Hajiya binta ta kira Saleem da kanta inda take sanar dashi Ranar Asabar mai zuwa alkalin alkalai mai ci ayanzu zai raba gadon Dukiyar Daddy so duka Manajojin kamfanoninsa dana gidajen mansa anyi musu waya zasu tararra komai suzo dashi harda Mrs suzan wanda suke Da Rubutattacen komai na hannayen Jarin Da daddy ke dashi akasashen ketare so za’a hadu Ranar asabar din domin saukema Daddy Nauyi kuma malika ita kadaice yar’shi kwara daya daya mallaka,shine zasu zo shi da ita,da sauran yan’uwanshi da suka rage daga Malumfashi domin gani da ido..
Da Saleem ya gayama Malika ranar Mutuwar Daddy takara tasoma Malika tayi ta kuka Yana lallashinta,Dakyar ya samu tayi Shuru,dama kuma Abun yazo adaidai domin goggo Hadiza zata koma malunfashi itama Joda zata tafi,shiyasa suka Shirya Tafiya alokaci daya Malika da Joda da goggo Hadiza Tun Ranar Jumma’a Tasaka Direba yazo daga gida ya daukesu ya kaisu katsina Shikuma Saleem sai gobe zai zo Saboda Ranar yana da meeting,Ammh yama joda da goggo Hadiza sha tara na arziki suka karba suna godiya.
Rabon Malika da gidansu Tun bayan Tafiyarta lokacin Rasuwar Daddy,lokacin data Shiga gidan sai da tayi kuka domin tana ganin kamar Daddy zai Fito yace”Bbyna…”Ammh kuma Daddy yatafi Tafiya ta har Abada,Hajiya ta dauke Ayda tana cillata sama tana Bangala mata Dariya,ita mamakin girma Ayda take kamar wata diyar Turawa,Goggo Hadiza tace ta samu Nono mai kyau ne Shiyasa,Malika ko tazo da kayanta dayawa Tunda Mallam yace zata kwana biyu har Abuja zata gidansu ta kwana biyu kafin takoma Zamfara,shiyasa harda guzurin mganin matan da Ummi ta kawomata tazo dashi domin tafara amfani dashi,don Ummi ta kirata ta mata bayanin gumba ce,da kuma garin aya wanda zata dinga damashi da madara,sai wata hadin zuma wacce zata dinga shanta ita kadai,Ranar Malika sai da tayi hawaye taji aduniya ai batayi maraici ba,balle goggo Hadiza ma bata barta haka ba,kayan Fruit din duk matsa mata sha,take tana da kuma Shan Abu mai Romo romo,ita kanta goggo da Hajiya Sunji dadin yadda Saleem ya yarda zai bar Malika ta kwana biyu in yazo gobe saboda su samu lokacin yimata gyaran da basu yi mata ba lokacin Aurenta.
Dose da mery ko nanan Gidansu Malika suna taya hajiya aikace aikace,Suma sunyi murna da ganin Malika,haka suke rigen rigen daukan Ayda har suna Fada,malika ko na musu Dariya cike da Nishadi
****************
Zahra ko tana ganin Su Malika sun Tafi ta Fito Falo ta Fada kan kujera tana Fadin”Gida yazama nawa ni kadai,hakama miji yazama nawa nikadai,ammh da wannan matar ta gaje komai,wlh bantaba kaunar Malika ba,kuma bazan taba k
aunarta ba..,Kawai nayi lambo ne abubuwa su yi sauki kafin na Fito da wani sabon salon..”
_Akwai wan lbri dake Tsungulina,Lbrin ba irin Salon da kuka sani bane,Salo ne da zai karkata kan wani al’amari dake cimin Tuwo akwarya na Yadda Mata take mallake Miji ta rabashi da kowa nashi ciki harda Uwar data Haifeshi..? Bayan ta rabashi da kowa nashi,sai yakoma nata da ita yan’uwanta..? Shin yaya Abun zai kasance..,..? Sai kun yi jimarin bina sannu a hankali mun gama malika da aminci in Allah yaso,sai mu Dora cikin wannan Lbrin nawa wanda zai zo da Sabon salo…_
“”Saleem sai washegari da Safe yazo,inda aka hadu aka Raba gadon Tarin Dukiyar Daddy,wanda Malika ta samu kaso mafi rinjaye da tsoka domin kusan rabi da kwatan Dukiyar natane,Hajiya ma ta samu nata kason,Sakamakon Dady bashi da uwa ba Uba,kuma ba wani dan’uwa da suke Daki daya ko kuma yan Uba duka Babu wanda zai iya gadanshi bayan Malika da hajiya,sai kuma cikin kawunan Daddy akwai wadanda suka Shigo cikin magada.
Anan Hajiya take Sanar da Malika cewa Zata koma Malumfashi ita Joda,tunda gidan da suke ciki malika ta gajeshi,ai nan da nan Malika tace batasan wannan Zencen ba,Tace Har Abada hajiya bazata bar gidan ba,zata cigaba da zama tare dasu merry ita zata cigaba da biyansu,kana manajojin Kamfanonin Malika tayi mgana dasu Tace su Cigaba da gudanar da komai sai lokaci bayan lokaci zasu dinga mgana ta waya,hannayen Jarin Daddy na kasashen ketare kuwa an Dawo dasu ne an rabasu,tsabar kudin da Malika ta mallaka banda kamfanoni bata san iyaka ba,shiyasa kuma bada cigiyar Filaye inda tace tana so agina islamiya,da masallaci,domin sadakatul jariya zuwa ga Daddy.
Hakika wannan bayanin nata ta saka Farinciki azuciyar kowa,mussaman Mijinta Saleem wanda Farincikinsa yakasa boyuwa har sai da ya bayyana mata,bai koma Zamfara ba aranar sai awashegari ammh yammah nayi yace Malika ta Shirya tazo suje yawon bude ido😂Tako cakare ita da Ayda Suna Fita bai su zame ko’ina ba sai gidansu wanda Daddy ya basu,Allah sarki megadi na nan da wani wanda yake kula da gidan,komai yana nan amuhallinsa babu Abunda ya chanza.
Malika tasha mamakin ganin hatta cikin dakunan tsaf tsaf,ashe Hajiya ta kansa merry da Dose suzo su gyara lokaci bayan lokaci,basuyi masauki ako’ina ba,sai akan gadon Da Saleem ya karbi budurcin Malika haka ya Rumgumeta kam idanuwansa alumshe yake Tambayanta..”Kin Tuna wannan gadon Ummu Ayda..”Cikin kasala ta dagamai kai bai bata zarafin mgana yace”Toh wannan gadon shi yakafa miki tarihin zama azuciyata wanda baki Fita ba,kuma bazaki Fita ba har Duniya ta tashi..”Kuramai ido tayi cike da mamaki tana kallonshi bai bata xarafin mgana ba,sai da ya tsotse lebunanta kafin ya hada dogayen hamcinsu waje daya yana Fadin’Tun Ranar dana aikata miki wannan Abun,ban kara Sukuni ba,tunda lokacin Ashe sonki ya Shigeni sai nake dauka Tsausayinki nakeji sai daga baya na Fahimci na Fada acikin kogin sonki wanda baida iyaka,Wlh Malika zuciyata tanayin Xafi matukar na ganki cikin damuwa,kukanki tamkar zubowar dalma daga zuciyata,Bata miki rai kuwa tamkar Nima an batamin ne,Bana samun sukunin zuciyata sai naji gangar jikina ta hadu danaki..Yau na Na sanar dake Abunda na boye miki I SO MUCH LOVE U MALIKA…”Ya Fadamata idanuwansa na chanza launi.
Kamkameshi Malika tayi tana hawaye Da dariya lokaci daya,Kanta takara tusawa bisa kirjinsa tana Fadin”Bani da bakin mika godiyata gareka,domin asanadin Abun ka min akan gadon nan,ya chanza rayuwata na dawo malika datace na dawo mace kamar kowa,har Abada kai Abun alfahari na ne,Duk Abunda kamin bai hana zuciyata ta Fada tarkon sonka,Ina Sonka Abbu Ayda fiye da Yadda nakeson kaina..”Tafada tana dago kanshi bakinta takai kan nashi Tafara tsotsan lebenshi cike da kwarewa shima kan nata ya rike da hannu bibbiyu ya mikamata harshensshi tana cigaba da Kissing dinshi kamar Allah ya aikota shiko gabadaya jikinsa da hannuwanshi rawa suke saboda yadda Malika ke Tafiyarshi dashi cikin Kwarewa.
Ayda ko na gefe tana barci,iyayenta ko sun gama rikita juna,cikin xafi zafi Suka raba kansu da kayan jikinsu suna kara Shafa sassan jikin junasu cike da So da kauna,Awannan daren Darene mai cike da tarihi wanda Malika da Saleem bazasu manta dashi ba,darene daya kunshi tarihi kala kala,sun gudanar da wata rayuwa mai tsayawa azuciyr masoya,haka Saleem ya kwana yana jadaddama Malika kalmar yana Sonta,tagani kuma ta yaba domin ya nunamata a aikace haka Saleem ya tasata lasheta daga sama har kasa,itakuwa ta jiyar dashi madaran dadin daya Kasa controlling kanshi tasha Surutai sai da tagaji Ta rufemai baki.
Washegari da Safe tare sukayi wanka su kama Yarsu Ayda kowannensu anan ya chanza kaya Tunda dama Daddy ya siyasu komai,kamar karsu bar gidan haka suke ji,shiyasa Saleem yace zai nemi Transfer adawo dashi Katsina sai su tararra su dawo nan,Malika ko taji dadin haka sosai,sai da suka koma gida yayi Sallama dasu hajiya kana ya Sallame Malika kafin yakama hanyar komawa Zamfara cike da kewar matarsa da soyayyar yarsa Ayda..
***************
Zahra yanzu ta Sadda kai kasa ne,in kuka ga yadda takema Saleem ladabi da biyayyah sai kun yi mamaki baya mgana kanta na sama sai akasa,kuma kullum cikin makircin tambayanshi take yaushe malika zata dawo..? Tayi kewaar Ayda sosai,sai da yayi mirmishin jin dadin Zahra ta zama mutum yace Suna tafe insha Allah.
Ganin haka yasa Saleem ya sakarma Sosai suna baje Soyayyarsu domin Ta nuna itama tana kaunar Malika da Abunda ta haifa baisan ta munafuncin bane,gashi taci riba domin Saleem yanzu yana kokarin bata lokacinsa sosai suna shan love wanda ko lokacin amarcinsu basu sake da juna haka ba.
************
Malika ko sati daya tayi A katsina ta Wuce Malumfashi tayi kwana uku wanda babu Shakka dangin mahaifinta sukaji dadin ganinta ta zaga dangin sosai wanda dama tare da Joda sukaje,dagachan suka Wuce Abuja,Ummi da Abbi kamar su goyata haka suka dinga dawainiya dasu,Ayda ko suna zuwa Abbi ya amsheta suna sama wajensa,Saboda dadin zama agidan Ummi sati daya cur Malika ta kwashe,ada har tana da niyyar karawa Saleem ya kirata awaya yace in takara bada yawunshi ba ta dawo don wlh ya gaji kewarshi zata illatashi,Aiko da Ummi sukaji zata koma aiko tace batasan wannan Zencen ba,sai taje kumo ta dawo kafin ta koma,Ransa baiyi dadi ba da Ummi ta kirashi tana Sanar dashi sai Malika taje kumo ta dawo kana,bashi da yarda zaiyi dole ya hakuri suka tattara suka Tafi kumo duka gidan harda Hajiya,kwana daya sukayi suka dawo Ita kanta Malikan kwana Daya ta kara Direba ya kwasheta ita da Merry Tunda Joda Tun a malumfashi ta barta,shiyasa hajiya tace tazo da merry saboda ta dinga taimakamata da Renon Ayda in ita kuma tana wasu ayyukan,ammh sai da ta kira Saleem ta nemi izininshi baiyi gaddama ba ya amince,Malika bata yi kasa agwiwa ba tazo da System dinta wanda rabin kasuwancin mahafinta keciki,tazo dashi saboda tana so ta Tuntubi Saleem in zai barta ta dinga gudanar da komai tana gida basai taje ba,Tund Gabadaya babu Abunda bata sani akan kasuwancin ba.
Saukan yammah sukayi so Saleem baya gida sai Zahra wacce tayi kiba kamar ba ita ba,tadai Fito tayi musu sannu da zuwa daganan tayi komawarta daki Ranta bakikirin Da dawowar Malika wanda ta sani yanzu duk Jin dadin data samu zai rage ne,haka ko akayi don Ranar ko takanta ma Saleem bai bi Tunda ya dawo yana nanike da Malika,Tunda suka Shige daki basu Fito ba Sai Washegari wanda hakan ya kona ma Zahra rai kamar tayi Bindiga saboda kishin Malika balle yanzu dataga tafi da kyau da iya tsara kwalliya komai na Malika mai kyau shiyasa komai ta saka yake mata kyau,bata kwalliya sosai ammh kuma duk kayan data sanya sai sun amsheta,balle Ranar girkinta yazo bata wasa da duk Abunda ya Shafi mijinta,Komai zatayi sa cikin lokaci ne,bangaren girki kuwa Malika bata da mtsala domin ko gane wani Abu ne batayi ba,zata dauki wayarta tayi browsing taga yadda komai yake ta kuma yishi yadda yakamata..
Zumuncinsu da Maman Abba ko y
akara kullewa ita ke kara koyamata wasu dabarun zama da miji ammh ita malika Tuni ta samu key din Rayuwar Saleem ahannunshi,Bata mai gaddama kan Abunda ya haneta,koda tana son Abun nan da Zarar yace “A’a to ta barshi har gaban Abada,kuma ko Fuska bazata nuna taji haushi ba,Abu na Biyu bata Raina Abunda yake mata ita da yarta komiye in ya Siyo mata zata karba ta Gode masa sosai yadda kasan ba’a taba mata makamanciyar kyauta irinta ba,Duk da ko tarin Dukiyar da Allah yayi mata bata Raina Abunda mijinta yayi mata,sai Abu na uku Tarbiya Malika bata tsalleki mganarsa tana girmamashi tare da ganin Darajarsa in yace ga hanya tabi nan take saka kai babu gardama gata da Sanin wayewar Duniyar Tafiyar da miji cikin sauki,toh tana da iliminta daidai Gwargwardo to wadannan hallayar ta Kara sace Zuciyar Saleem wanda ko mgana tayi Shima bai iya tsallaketa,kuma yake Fifitata akan kowa duk da yana kokarin kwatatan Adalci Atsakaninsu da Zahra,ammh bata ganin kullum cikin kishi take da kyashi akan Malika da yarta..
Mganar kula da kamfafoninta da suka zama mallakinta kuwa Tun kafin tayimai mganar ya Tuntubeta ya kuma bata dama ta rika gudanar da Komai acikin gida,Tunda ga Na’ura mai kwakwalwa ga waya,Shima yayi mata alqawarin bata dukkan gudummuwanshi Murna wajen Malika ba”a mgana dama ita tana son kasuwanci sosai nan da nan ko tacigaba daga inda ta tsaya rabonta da wani Kamfanin daddyta Tun kafin Aurenta da Saleem,yanzu kuma saboda karfin gwiwanshi da Soyayyarshi gareta ta fara Dawowa Ainihin Malika malik dinta,ammh wannan ba Wacce kuka sani abaya bane,ta yanzu She very smart and Educated both na addini dana boko.
Sai ya koma in tana kan Na’ura Merry ke kula da Ayda,ko in tana kichen tana girki Ranar ko da bata da aiki Shikenan ammh merry ta taimakamata sosai Duk da ma Aydan bata da Rigima sosai,Abu daya Fara Tunzura Zahra Shine Soyayyar da Saleem ya kwashe kaso mai yawa yamikama Ayda wanda ko ita matarsa baya Sonta haka,Ko malika kedashi ko ita kedashi yana Nanike da Shegiyar yarinyarnan baya ijiyeta sai dare ya tsala lokacin kwalliyar datayimai Duk tagama goge kanta Saboda Haushi ma tafiyarta dakinta take tayi kwanciyarta sai sanda yagaji da kanshi ya maidama uwarta kana zai zo ya kwanta,wani zubin har ta Fita girki baya Nemanta Saboda daya dawo bashi da Hutu jikinsa na Rawa zai karbeta da ita zaici abinci wanka ne kadai ya ijiyeta in zai Shiga,wannan Abun yanzu Shike damun Zahra sai ma tatarra tsanarta kacokan kan Ayda wacce batafi wata uku Aduniya ba,in ko ya ijiyeta ya Shiga wanka haka Zahra zata dinga Dungurin yarinyar tana hararanta sai taji motsin zai Fito sai ta dauketa tana lallashi kamar gaske,shiko ganin haka sai yaji dadi har yana cemata in taga Malika na aiki ta rinka zuwa tana daukan yafi merry wacce ba musulma ta dinga wahala da ita,sai ta nuna kamar ta Allah harda cemin tana matukar Son Ayda kamar Ranta,shiko har Ga Zuciyarsa yace mata tabari Malika ta sake haihuwa sai su bata,Wani bakin ciki ya cika mata rai wato Malika ne zai karama ciki ta haihu ba ita ba ko? Tundaga lokacin ta dauki damaarar Azabtar da Ayda matukar ta Shigo hannunta,musamman take karbanta ahannun merry ta Shigo da ita daki ta dinga saka yarinya kuka tana mganarinta tana zaginta,sai gaji da kuka zata maidama Merry ita kuma ta kaima Malika ta bata nono,Wanda zatayi ta mamakin ganin Ayda haka duk tasha kuka Fuskarta tayi jajir,ita da bata da Rigima ko ta tambayi merry sai tace Anty Zahra ce ta karbeta,jin haka yasa Malika bata Shigo da wani Tunani zatayi Saurin kauda Shedan daga Zuciyarta.
*****************
Bayan Sati biyu Zahra ta samu waya daga kano cewa An kwantar da momi Hajiya Saratu a asibiti,Dole suka Shirya tafiya harda Malika sukaje suka dubata,ammh su sai ka dawo Saleem yace Zahra ta zauna ta kwana biyu Tunda dama bata taba zuwa ba,ammh afuskar Zahra ya Fahimci bata ji dadin Cewar da yayi zai barta ba,haka ta bata rai har suka Tafi,ita kuma ba komai ne yamata bakinciki ba,sai yadda zata bar Malika da mijinta su kadai agida shine kishi ya Turniketa taji kanon ya Fita aranta,itako la’akari da Momi dake kwance ba lafiya batayi ba,A’a ita hankalinta na gida,Shiyasa Adaddafe tayi kwana hudu ta dawo sai dai suka ganta kwatsam,Saleem yayi mamaki Domin Sati daya yace tayi daya tambaayeta ba’asi sai tace Ai momin ce taji sauki Ita tacema ta taho gidan Mijinta,alhalin ko achan cema Momi tayi ita da Nadira Cewa Saleem ne yace kwana uku yabata ta dawo gida,Abba najin haka ya hadota da Direba ya maidota Zamfara.²⁸