MALIKA MALIK CHAPTER 15 BY JANAFTY

MALIKA MALIK CHAPTER 15 BY JANAFTY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Shigowar Su Malika ne ya dakatar da Saleem daga,d’aga hannun dayayi zai Naushi Bakin Zahra,wacce ta Sulale kasa tana kuka hannunta Rufe da bakinta tana makyarkyarta.

Malika ko Wajen Ayda ta nufa cikin Rawan jiki ta dauketa tana jijjigata batama kai ga Zarafin mgana ba,Taji muryan Saleem cikin wani yanayi yana Fadin”Why..? Zahra me nayi miki..? Me malika ta tsare miki..? Wani alhaKi Yar jaririya Ayda tayi miki da kikeson kasheta.?.”Atare joda da Malika suka kwalolo ido suna bin Zahra da kallo Wacce ke girgiza kai tana kuka take Fadin

  “Wlh batamin komai,Sharrin Shedan ne,ammh ni ko kuda Bazan iya kashewa ba..”Tafada tana gunjin kuka tana daga hannuwanta,Saleem bai iya mata mgana ba,sai da Numfashinsa ya koma daidai kafin yace”Hakane bakomai,Allah nagani ban Aureki da Wata Zuciya ba zahra,nayi kokarin ki zama mace tagari hakan ya gagara Daga karshema Saboda bakin kishinki kamaki nayi kina neman kashe yar Jaririyar Allah Wacce bata ji ba bata gani ba,ammh ngode ma Allah daya Toni asirinki Tunkafin ki aikata Abunda kika niyya,kije bazan hada ki da hukuma ba,ammh zan Sallameki daga Rayuwata sallama ta har Abada,Saboda haka kije na Sakeki saki biyu kuma Tsakani dake Zahra Allah ya isa,bazan taba yafe..Miki ba..”Yafada kamar kwalla zata zubomai Shiyasa ya Fice Daga dakin da Sauri yana Share hanci.

Itako Zahra zaman yan bori ta karayi akasa tana kuka hannunta biyu bisa kai tana kururuwa tare da kuka alokaci daya tana Fadin”Wayyo Allah na..!Kaicho na ni Zahra na kashe Aurena dakaina..”Take Fada tana kuka mai hade da Nadama mai karfi,Malika da joda dake tsaye agabanta suka daskare atsaye suna binta da kallon mamaki mai cike da tsoro.

Zahra ta rarrafa zara riko Kafar malika,ita kuma tayi Saurin yin baya tana girgiza kai Wasu hawayen Tsausayin kanta dana Yarta na kamata,kara rumgume Ayda tayi tana Fadin”Ban taba Zaton zafin kishinki akaina har yakai kiyi Tunanin kashe Jaririyar da batasan komai ba,haba Zahra me kika Dauki Duniya ne,duk Abunda Zaman lafiya da hakuri bai baki ba,Wlh tallah akasinsa bazai taba baki ba,Meya Rufe miki ido?Dukiya.?ko ko Shikanshi Mijin..? Wanda duka Zaki Mutu ki barsu anan Duniya kije lahira ki girbi Abunda kika Shuka..,Hakika kin bani mamaki Zahra,ammh kuma ngd ma Allah daya Tsaremin Ayda baki riga kin aiwatar da mugun Nufinki akanta,babu Abunda zence miki,tunda kin riga da knga karshenki..”Tafada tana kuka kafin ta sakai ta Fice daga dakin Zahra na kururuwan Kiran Sunanta.

Joda ta Shiga Tafa hannu tana fadin”Innalillahi ni joda na Shiga Aljannah,ammh dai kinyi Asara wlh,yanzu ke Zahra ina miki kallon mara hankali Ashe kallon biri nake miki kina min na ayaba,Toh Allah ya Shiryeka yasa wannan Ya zameki Darasi knga dai karshen Wanda yaja da ikon Allah don Malika da Saleem haduwar Allah ce bata ta mutum ba..”Tafada kafin tajamata dogon Tsaki ta Fice,

Nan Zahra ta kara Faduwa tana kuka harda birgima Nadama Tare da danasani suka Shigeta lokaci Daya tana Danasanin meyasa ta biyema Sharrin Zuciya Dana Shedan,gashi ya kaita ya baro,yanzu me zatacema iyayenta a auren da ko Shekara bai yi ba..? Bazata iya bude baki ta Furta irin Abubuwan Data aikata Saboda Tasan Halin Abba da momi suma bazasu mata da Wasa Ba.

Gajiya Tayi da kukan ganin babu mafita yasa ta tashi ta Shiga hada kayanta amanyan akwatunanta,Sai da ta hada komai nata kana ta koma ta Zauna tana Sharan kwallah,sai ga Saleem ya Shigo saurin mikewa tayi tana mutseke ido zatayi mgana kenan ya Mikamata Farar Takarda hannunta da jikinta na Rawa ta mika hannu ta karba tana kallon Fuskarshi wanda ya kauda kai alamun bayason ganinta ma kwata kwata,Ta karba ya sakai ya Fice ya barta tana zubewa bisa gado Tana Tsiyayan Hawaye.

Zahra da kanta ta Dinga jidan akwatunta zuwa waje,megadi ne ya Fita ya samo mata mai Napep ta Shiga Zuwa Tasha inda ta hau motar Kano,har suka kai kano Zahra na kukan Nadama da kaicho da Rayuwarta haka Napep din data Shiga da Inda mota ta Sauketa zuwa,gida nan ma kuka tayi tayi,kuma haka ta Fadama Falon gidansu tana wannan kukan megadin gidansu ne ya Shigo da akwatunta yana Sanar da Momi Mai napep na waje yana jiran kudinsa

Momi da ke Falon ita da Nadira suka mike Arazane atare suka Tarbi Zahra suna Tambayanta lafiya bata iya mgana ba illah Takardan da Saleem ya bata ta zaro ta daga cikin karamar jakarta ta mikama Nadira,momi kuma na kokarin ciro kudi cikin pos dinta Dake kan kujeran daya Daga cikin wadanda sukama Falon kwanya 500 ta mikama megadi ammh Rabin Hankalinta naga farar Takardan Da Nadira ke warwarewa tafara karantawa abayyane kamar haka.

  _NI *SALEEM KABIR KUMO* Na kara karishe yanke igiya biyun daya Rage a tsakanina da *ZAHRA BUKAR MADA* Sakamakon munanan hallayata wanda in kuka Tambayeta zata Sanar daku da kanta,Ina Rokon Allah in azamana da Zahra na cutar da ita ko na Mintina daya na yarda ku iyayenta ko Rokarmata Allah ya Sakamata,in ko Azamana da ita Ita ta Cutar dani kuyatani Rokon Allah ya sakamin Akanta.._

                _* ACP S.K.Kumo.*._

Daga Nadira har Momin hannu Suka Dora bisa kai suna kiran Sunan Allah da Salati lokaci daya,itako Zahra kasa ta Sulale tana gunjin kuka Momi na kallonta cike da Tashin Allah..”Innalillahi Wa’inna alaihiraju’un Zahra garin ya haka ta Faru,yaushe Mijinki ya sakeki da zai ce ya karishe igiya biyun dake Tsakaninku,yaushe wannan Abun ya faru ammh mu bamu sani ba…? Tafada tana Rike haba cike da damuwa,Itako Zahra taki mgana banda kuka babu Abunda takeyi Haushi yakama Momi takai mata Duka tana Fadin”Don Ubanki bazaki mgana ba..? Mekika aikata har ya sakeki saki biyu lokaci daya,kuma a yadda yaron nan yayi Rubutu Zahra kece kika jama kanki Zawarci da yarintarki,Kinje kinyi Abunda kika kashe kanki kika kuma kashe mu iyayenka,Wlh baki kyautamana ba Zahra..”Take Fada tana kuka Nadira ce ta Rikota tana bata hakuri tana Share mata hawaye,itako zahra kukan ta take karama Volume Saboda bata da karfin gwiwa bada lbrin Abunda ya Faru 

Momi batayi sanya ba ta Daga waya ta kira Abban Zahra tace ya dawo gida yanzu ba lafiya,jin muryanta cikin wani yanayi yasa ya umarci Direba daya juyo dashi gida,dama yana hanyar Zuwa gidan Wani abokinsa ne,koda yadawo gidan nan ya iske bakin lbri wanda ya kusa saka Zuciyarsa bugawa,yayi tambayan Duniyan nan Zahra taki mgana sai kuka take,daga karshema tashi tayi ta Shige daki Nadira tabi bayanta,ganin haka yasa Abba ya kira Layin Saleem din ammh kuma wayarsa tana kashe,sai ya sauya alaqaan kiran Zuwa ga IGP KABIE KUMO,wanda Shi Abba ne ma ke Sanar dashi Abunda ya Faru don su basu da lbri,ammh yabashi hakuri da janjanta lamarin inda yace zai Nemi Saleem din yaji gaskiyan batu 

Abbi Ummi ya sanarmawa Abunda Bukar Mada ya kirasa ya sanar dashi kirji ta Dafe tana salallami,wayar Saleem tayi ta kira bata Shiga sai ta kira na Malika,bayan sun gaisa take Tambayanta ina Saleem,wanda lokacin yana dakinsa duk Wunin yau bai ci abinci ba  saboda
Damuwa da Nadamar Auren Zahra daya lullubeshi Malika tayi ban hakuri ammh yace ta rabu dashi bayason cin komai,Yana kwance akan gadonsa ta mikamasa wayar tana Sanar dashi Ummi na Son mgana dashi karban wayar yayi ya saka akunne alokaci daya yana gaida Ummi bata tsaya amsawa ba ta Shiga jeromai Tambayoyi kan Abunda Bukar Mada ya kira Abbi ya sanar dashi baiyi Nauyi baki ba ya sanar da Ummi duk Abunda ya Faru baki ta rike tana mamakin Zahra,Duk da Zahra tayi Abunda bai kamata ba,ammh Ummi tanuna Saleem yayi kuskuren yanke Hukunci cikin Fushi,ta kuma bashi Umarnin ya kira Mahaifin Zahra yamai bayani don daga mganarsa Zahra taki mgana,ya sanar da ita zai kirashi da Safe,da haka sukayi sallama tana Fadin Allah ya kyauta na gaba 

Koda ta Sanar da Abbi lbrin da Saleem ya bata tsaki yaja yana Sababin Yarinta kenan da Shigen Rawan kai irin na Saleem,ammh ina shi ina mata biyu,da lokacin da ya Rarito an hanashi ba hanuwa zaiyi ba,ammh yanzu wa gari ya waya..? Allah ya kyauta ammh sam basu da Tunani inda suna dashi da duk  haka bata Faru ba,shima Allah ya kyautan yayi toh babu wani gyara Tunda Saki ukun ya cika kemata sai Da Fatan Allah yasa yazama darasi garesu gabadayansu…  

  Hajiya Babba ko dataji Fada takamayi da saleem din wai meyasa bai bata kashin mutuwa ba kafin ya tarata,Shiko Ya marwan dama yace Daga ganin wannan amaryar ta Acp batajin mgama,Saleem ko sai Washegari ya kira Bukar Mada ya Warwaremai zare da abawa Tundaga Farko har karshe sai gashi Daga karshe Bukar Mada kebama Saleem Hakuri yace babu komai kanta tamawa,koda Hajiya Saratu momi taji batayi wani mamaki ba,don tasan wauta da sakarci irin na Zahra kuma ga Abunda Nadira tace ta kirata tana fada mata,duka Momi ta hada Fadan da kuma Takaichin Zahra ta Watsar illah ta Sanar da ita idai kan kishiya zata kare rayuwarta aiko Tana da Wahala don yanzu Rayuwa ta chanza ba lalle bane mazan yanzu su zauna dakai kai kadai ba,balle keda kika je kika tarar ammh har kina da kokarin Son ki kori ta ciki,wanna Shine kaikayi ya koma kan mashekiya.

*****************

Sai bayan kwana biyu kana Saleem ya warware,ranar monday ya Fita office,ammh adaren sunyi Tsiya da Malika kan tacemai ita daya nemi Shawaranta da bai saki Zahra ba,Wanman mganar Shiya batama Saleem Rai har ya Nunama Malika hakan,Dakyar ta bashi hakuri ya hakura ammh ada har ya dau Zafin da Cewa kila ko bata Sonshi ne,da har zata ce ya cigaba da zama da Zahra wacce bata son Jininsa toh aiko bata Sonshi karyan banza ne kawai.

Da Maman Abba Taji lbri sai da tayi Guda bayan ta juya Duwawau Tacema Malika ta tayata barka,domin Rabuwa da muguwar kishiya irin Zahra babban nasara ce,wanda zama dasu bala’i ne Tunda Zuciyarsu bata da kyau sam,Toh ita kanta Malika Tasan Zahra ba masoyiyarta bace,ammh sakin ne bai mata dadi ba,shiyasa ko da taga Saleem yasa anfitar da komai dake dakin Zahra an saka Sabbi tsoffin kuma yabama megadi yace yakai ma ilayanshi ya karba yana murna Hade da godiya,Sai merry ta koma tana kwana adakin,joda kuma bata dade ba takoma Katsina wajen Hajiya.

*****************

Yanzu gida ya rage daga Malika sai mijinta Saleem sabuwar Soyayyah mai dauke da Sabuwar Rayuwa mai cike da muradi da burgewa nan suka bajema juna yadda suke kaunar junansu,kowa yana kafa kafa da Dan’uwanshi bayason bacin Ransa,gefe daya kuma suna kula da yarsu Ayda wacce take kiba tana kuma kara girma da Wayau,gefe daya kuma Malika na ta Shiryen Shiryen Biki wanda Abun ya Hade mata gata wan mijinta ne,Gata kanwar amarya kuma kawa gareta,gata kuma ta wani bangaren tamkar Uwa take gareta Tunda komai na Shiryen Shiryen bikin Hajiya Binta ita ta sakarmawa Shiyasa koda yaushe cikin mgana Suke awaya don ganin yadda Abubuwan zasu tafi kan Tsari.

Shiryen Shiryen biki na cigaba da Wakana ta bangarori da Dama,kadama Uban gayyar yaji lbri yafi kowa Zumundin Aure Fiye da kowa shiyasa ya saki bakin aljihu ya sakarma Ummi kudi ta Aika Dubai akayo mata odar akwatuna da kuma kayan alfarma na gani na Fada,sai wanda ya gani akwati 10 cif aka Hadama Joda wanda kudin da”a ka narka kan kayan dake ciki ba kananan kudi bane.

   Bikin an Shirya Sosai ta bangaren Amarya da kuma bangaren Ango,bikin na Saura Sati biyu Hajiya Binta ta kira Malika awaya tana Sanar da ita Dangin Mahaifin joda sun aikota mata kan basu yarda Joda ta zauna awajenta ayi Taron biki ba,suna bukatar Yarsu ta dawo wajensu da zama har zuwa Ranar Daurin Aurenta,Daga yadda Hajiya Binta ke mgana zaka gane bataji dadin Zencen na Dangin Mahaifin joda ba,ammh sai malika ta shiga bata baki tana Nuna mata babu ta kyale Joda ta tafi bakomai aciki sai su tattara su Bita chan malumfashin bayan andaura Aure aka dauko amarya bashi kenan ba,Kalaman Malika su suka kwantarma da Hajiya da hankali Sukayi mganar da zasuyi kafin su yanke kiran.

Malika ita take Sanar da Saleem Abunda Dangin Joda sukace,bai damu ba yace hakan Shine Daidai Tunda gidan Wan mahaifinta Za”a Daura aure,daganan sai adauko amarya Zuwa Abuja basai ankara wahalan Zuwa Katsina ba,kafin ma Malika ta kira Ummi Ya marwan din yama su Ummi bayani kuma Suma sun gamsu,kuma Sunyi Na”am da hakan Tunda zai ma Fi sauki da ada sai ankoma ta katsina an Taho da Amarya… 

  

Biki na Saura kwana goma Ummi ta Shirya kai kayan Auren Marwan,tare da kwalayen minti dasu Sweet sai goro da tabarmu harda buhun Shinkafa da Su Taliya da makori da sauransu da kudi 100k na amarya da kawayenta sai kayatattu  katinan da’aka bugo mussaman Domin Amarya,koda Ummi ta nemi malika datazo Ana gobe Abuja ta kwana Washegari suyi sakko Zuwa katsina in Hajiya Binta tagani dagachan sai Su Wuce Malumfashi,Aiko da Malika ta Sanar da Saleem murje ido yayi ya bala Toka yace wa..? Shi ba dan iska bane da zai barta tayi wannan Doguwar Tafiya ga Ayda jaririya kawai taje ta kwaso mata mura,kana kuma uwa uba Shi tatafi ta barshi da wane,Wlh kada ma tasaka rai bazata ba,Tun Tarihin zaman Saleem da Malika wannan ne karo na Farko daya hanata Abu taji Ranta yabaci wanda tayi kokarin Danne Fushinta ammh kuma ya gagara sai da ta bayyanashi,saboda takaichi sai da tayi kwallah,Ammh Saleem ko ajikinsa,da Ummi ta kirasa sai yayi mata karya da Malikan batajin dadi ne,kuma Ayda ma Tana mura baza ta samu Zuwa ba,harga Allah Ummi ta yarda shiyasa ta kira yan kumo suka taho Suka Dumguma zuwa kai kaya.

Katsina Suka Fara Zuwa wajen Hajiya inda Taji dadin karan da’aka yi mata amtsayinta na Uwar diya,sai da suka ci abinci sukayi sallar azahar kana suka Damki hanyar Malumfashi,koda suka isa ba laifi sunga kara,dayake Ba Joda kadai za”a Aurar ba aiko yayanshi mata su uku joda ce cikon ta Hudunsu Tun Tarar da an kawo kayan Auren mutum biyu Aranar,suka Hada dana Joda cikon na ukun kenan,kuma Alhamdulillah Ciki duk Joda ce Tayi Zarrah,toh Pilot guda Wasa ne Dole akaga barin Naira,kunsan ance dama yanayin kayanku yanayin Tarbanku ne😂Toh su Ummi sunga karammawa sosai,sun kai suma kuma sun taho da Niki nikin Abun Arziki harda kudin Tukwaicinsu 40k aka basu Wanda Ummi ta nuna bazasu amsa ba ammh suka matsa musu suka karba ammh bayan Sun Nuna basu ji dadi ba.

  ******************

Malika ko tagama Fushinta na kwana Biyu Dole Ta Hakura,Ammh tayi damarar Cewa Tun ana Saura Sati daya biki zata biyama Hajiya su Wuce Malumfashi biki,saboda Joda bata da Wata kawa kuma yar’uwa abokiyar Shawararta irinta so tana bukatarta akusa da ita,Da Farkon mganarta Saleem bai dauka da Gaske take ba,shiyasa bai dau Abun Serious ba ya Fita batunta don bayajin zai iya Rabin Malika tayi Nesa dashi Domin ya riga daya saba Rayuwa da ita,ko kwana daya Sukayi Batare da juna ba ya Fita jin jiki 

Malika ita tama Joda waya kan Ta samu Wacce zata mata Dilka da Halawa da kuma kunshi,in tazo zata biyamata,mganar mgungunar mata kuwa Maman Abba ta Hada ma Joda masu kyau da inganci dama ta iya Su gumba ne,su Tsimi ne,su garin aya,Hadin Bawon kankana,daidai Sauransu harda kaza da yan Shila mai mgani Malika ta Sanya akama joda,yan Uwanta ma na Dangin babanta basu barsu h
aka ba,suna basu Wata gumba da’a ka hadota daga sokkoto suna Damata kamar Fura da Madarar Yoghourt ko Madaran gari,Hajiya na gefe ta barma Malika komai Tunda itace Uwar Diya,shi kanshi Marwan din Da ita yake waya,shiyasa Saleem yace Ana nuna masa Wariyar Launin Fata,sai da yaga Ya marwan ya kira Malika,chan anjima kuma yaga Ummi ta kirata ayi ta kuskus shiko bamai kiranshi,daya gayama Ummi haka Dariya tayimai batace komai ba Itako Malika gwalo ta Dingamai Tana Dariya,shiko yana girgiza yake Fadin lallema Yarinyarnan zaki Shigo hannu ne…”

****************

Biki na ragewa Saura Sati daya Tun Daren Jiya Malika ta Shirya kayanta tsab acikin akwatunanta guda biyu Wanda natane dana Ayda ta kuma Umarci Merry data Hada nata,don da ita Zata Tafi saboda kula da Ayda,shiko Saleem Sai da ya dawo da Daddare ne yaga kayan Malika tsab ashirye Abun ya bashi mamaki ganin har Washegari da Safe batamai mgana ba yasa shima ya Shareta yana so yaga iya gudun Ruwanta.

Yana cikin dakinsa yana kokarin Daura Tek tie dinsa Malika ta Shigo hannunta Rike da Waya,gefen Gado ta Zauna tana Fadin”Mallam yau zamu tafi harma na kira Direba daga gida nace yazo ya kwashemu..”ido kawai ya sakamata yana Daura Tek Tie dinshi bai mata mgana ba Sai da ya gama yana kokarin Saka coat dinshi ne yace mata”Zuwa ina..?Kuma da izinin wa..? Ya fada Fuskarsa ba Fara’a.

Jagale tayi tana kallonshi kafin tace”Bangane Zuwa ina ba Mallam..? Ka manta nayi maka mgana zan tafi katsina yau gobe mu Wuce malumfashi da Hajiya saboda Shiryen Shiryen biki..? Wayarsa yadaga yana Fadin”kuma sai nace miki toh na amince ko..? Ni azatona kawai kina mganarki ne..”Malika taji kwallar Sun Fara cikamata ido cikin Raunin murya tace”Mekaka nufi mallam..? Jakar brief case dinsa ya dauka yana Fadin”Kinfi sani ,so u better call d Driver ki sanar dashi kada yazo don inda kinga kinga bar gidan nan Toh ana gobe biki ne,bandama rashin Tunaniku na mata kitafi Tun yau nikuma sai kibarni na Zauna dawa,biki ba gobe ba ba kuma jibi Ba..”Yafada kanshi Tsaye yana nufar Wajen jerin Takalmansa  bayason kallonta kada Hawayen datakeyi ya bashi Tsausauyi 

Malika dataji Abun yayimata Wani iri mikewa tayi tana Share kwallar data subomata tana Fadin”Ammh mallam kada kamin haka Don Allah,daga hajiya har Joda suna bukatata,kuma in kayi la’akari ina nataba Zuwa nayi kwanaki banda lokacin dana gama wankan Jego,don Allah kada ka hanani zuwa…”Bai kalleta ba ya Zura takalminsa baki Sawu ciki ya mike yana Fadin”Meyasa kikeso ki Fara Abunda ba halinki bane malika..? Na riga na gama mgana bafa zaki Tafi yau ba fakat bani son yawan gaddama..”Daga haka ya Fice adakin yana daga wayarsa dake Neman agaji Tun dazu.

Wani kukan Takaichi ne ya kama Malika batasan sadda ta Fada bisa gado tana kuka ba,babu mai Rarrashinta Abunda yafi mata bakinciki meyasa Ranar datamai mgana bai ce bazata ba,sai da ya bari ta gama Shirya kayanta kuma ta saka rai atafiyar bayan ta kira Har Hajiya ta Sanar da ita yau tana Tafe,shine kuma zai hanata Zuwa kuka tayi sosai kafin ta dauki wayarta ta kira Hajiya muryanta a cunkushe tace kada Direba yazo bazata samu Zuwa ba yau..”Hajiya Binta yadda Taji muryan Malika tasan kila Saleem ne ya hanata sai bata damu ba,sai ma ta fara lallashin Malikan tana bata hakuri,Nuna mata tayi bakomai ammh kasan Ranta takaichin Abun yaki barinta.

Ranar Wuni Tayi kwance,banda salla babu Abunda ke Tada ita ko girki bata Dora ba Ranar Tea kadai tasha merry kuma complex tace ta Hada tasha,ita kanta Ayda yau tayi Rigima saboda bata,bata nono yadda yakamata ba,Sai wajen bayan mangariba kana Saleem ya Shigo gidan da merry ya cikaro Afalo tana jijjiga Ayda dake kuka,Amsarta yayi yana tambayan ina mamanta take..? Merry tace tana daki yau kamar batajin dadi ne,Tunda yaji haka yasan Dalili koda ya Shiga dakin nata tana kwance,da alamun yau kazanta ne tataahi don ko wanka bata sake ba,Tunda da kayan daya Fita ya barta daso yazo ya sameta,cike da mamaki yayi tsaye kanta yana Fadin”Malika…”Yakirata cikin muryan Amo dagowa tayi tana kallonshi batayi mgana ba,mamaki tabashi mamaki ammh sai ya shanye mamaki ta hanyar kara Rumgume Ayda wacce ke Saman kafadanshi yana lallashinta yace”Meye haka..? Kina ji Ayda Na kuka ammh bazaki Fito ki amsheta ki bata nono ba,mekike nufi da yin hakan..? Mai da kanta tayi ta kife bisa Filo bata tanka mishi ba,ganin haka yasa Ranshi ya baci sai kawai ya kada kai ya Fice Zuwa Falo bai kara Tankata ba.

Merry ya umarta ta kawomai madarar Ayda ta Sakamata Ruwan zafi ajikin Fidanta yana bata ta karba da Sauri tana ta Sha,daga gani tasha Yunwa,sai da koshi kana ta saki kan Fidan tana Wani maida Numfashi Tsausayinta yakamashi,Allah sarki yaro kenan,Rumgumeta yayi yana jin Bacin Rai game da Abunda Malika zata koya na wani banzan Hali,bata jima ba barci ya kwasheta nan ya mika merry ita shi kuma ya koma daki ya wanka ya Sauya kaya Zuwa jallabiya daganan ya Dauki mota ya Fice,sai da yayi sallar isha’i kana yaje yayo musu takeaway ya kawo musu,da kanshi yakaima Malika har daki bayan yabama merry nata Ya karbo Ayda Tunda yau matar gidan Tana Fushi dashi.

Babu Abunda ya kara batamai Rai da lamarin Malika illah rashin cin abinci uwa uba kuma taki bama Ayda nono,ko da Daddare bai raba makwanci da ita ba,ammh ita ta juyamai baya kuma bayan ta maida kanta ta wajen kafafunshi,babu Abunda ya tsana irin mace ta juyamai baya,shiyasa shima ya Futa batunta Shi yayi ta bama Ayda madara cikin Dare har ya samu ta yi barci koda Safe Shi yayi mata wanka ya Shiryata Shima yayi wanka ya Shirya,ko kallon barayin da Malika take baiyi ba kuma Fuskarshi tana Daure babu alamun Fara’a itako Malika haushinta daya Don me yasan ya bazata ba,ammh bai sanar da ita ba sai bayan ta Shirya..? Koda zai Fice ko tak bai ce mata ba ya sakai ya Fice bayan ya mikama Merry Ayda yace ta kula da ita ko kuka take kada ta kaima Malika ta dama madaranta ta bata tasha ta goyata karban ta tayi tana amsa da toh Sir.

Bayan Fitanshi ma Malika kuka tasha saboda ganin haryauma din bai ce mata komai,gashi joda ta kirata jiya tace mata bata samu tahowa ajiyan ba,ammh insha Allahu yau tana bisa hanya,ammh ta lura Mallam so yake Ta nunamai haryanzu malika malik din da bata Tafi ba,aiko sauranta kawai Ruwa ne ya daki babban Zakara Shiyasa ya ganta haka..

Har yatafi office da bacin Ran malika Shiyasa ko achan din Fuskarshi ba’a sake ba yana mamakin yaushe malika tadaina tsoronshi..? Yaushe kuma ta Rainashi haka..? ita kuwa tana kwance kiran Ummi ya Shigo wayarta bayan ta Dauka sun gaisa take tambayanta tana katsinan ne,Takaichi ne ya ciko malika ta sakama Ummi kuka tana Fadamata Abunda ya Faru,ran Ummi ya baci ta yanke kiran Ta kira Saleem yana dauka ta Rufeshi da Fada,Ta inda take Shiga batanan take Fita ba,daga karshe tace maza ya kira malika ya bata izinin tafiya bataso  iskanci,Saleem yaji zuciyarsa na Tafasa da zafi cikin bacin rai ya furta.”Haba Ummi biki sai kace hauka Yaufa saura kwana 6 in ta tattara tatafi ni kuma na zauna dawa..”Ummi taji Haushi ta kunduma mai zagi da cewa”Ka zauna da Uwarka mana,koda kafin ka Auri malikan da ita kake kwana..,.? Kai bani son Dogon zence kayi Abunda nace kawai mallam in kuma bazaka iya bane ka Sanar dani..”

Ranshi bace yace”Toh Ummi…”Daga haka ta yanke kiran tana Sababi ita kadai Abbi dake zaune gefe yana karanta Jarida ya dago yana Fadin”Aisha..”Aisha Shugaban matan Duniya,Kinga na haneki da Shiga lamarin yaran zamani kada Watarana kiji kunya atoh..”Tana kokarin Ficewa daga daki tacemai”Ba wani jin kunya Abbin Marwan,saleem din ne da ban Haushi wai kada ta barshi Shikadai,toh da dawa yake kwana..? Kaji wani iskanci..”Dariya Abbi kafin yace”Jiki da wata mgana nifa banga laifinshi ba,Ciwon Da Namiji ai na Da namiji ne so kona yi miki bayani bazaki gane ba..”Dariya Ummi tayi tana Fadin”Au hakane,toh shikenan Muma Ciwon ya mace na ya mace so ko nayi maka bayani bazaka gane ba..”Tafada tana tikar Dariya ta Fice daga bedroom din Abbi na tayata.

Bai kirata ba kamar yadda Ummi ta umarcesa sai dai ya Turamata s
ako kamar haka  _Kin kyauta Tunda ni ban isa nace Abu ba kiyi,shine kikeje kika Hadani da Ummi ko? bakomai Allah kiyaye hanya Bawan Allah bazai Wulakanta ba insha Allah.._  ya Rubuta mata ya Tura mata koda taga sakon duk kuma sai taji bata kyauta ba Nombarsa ta laluba ta kira,ammh har ta gama Ringing bai daga ba,ta sake kira ma Still bai daga ba,daga karshema latse kiran nata yayi ya kashe wayar gabadaya,Sai gashi Duk dokin Tafiyar ta Fita aranta taji da badon ta kira Hajiya tace ta turo mata Direba ba data hakura wlh,haka ta dinga gwada kiransa ammh wayarsa akashe har Direban yazo,dama aleady tun dazu ta soyamai miya da farar Shunkafa ta sakamai cikin fridge ta kuma soyamai Nama Shima ta ijiyemai kozai wahala kadan ne,Duk da tasan Mallam din nata akwai son jiki karshenta sai dai ya rinka Siyan abinci.

Bata Wuce ba sai da ta Shiga gidan Maman Abba ta karbi sakonta na kayan matan data bata kudi ta Hadama Joda sukayi sallama bayan sun Rabu akan Ranar biki insha Allah zata biyo Baban Abba Tunda zashi Daurin Aure,Malika tayi murna sosai suka rabu akan sai tazo,Merry ita ke Rike da Ayda Wacce tasha wata hadaddiyar Bulawus mai kyau da tsari ga gashin kanta an tajeshi har merry ta daure mata shi da band dayake Ta biyo gashin uwar tata.

Megadi shi ya taimakama Peter ya saka musu akwatunsu aboth din mota malika ta mai sallama kafin Su Fada mota su Fice daga gidan megadi na Daga musu hannu,sai da suka dau hanya kana Malika ta yanke shawarar Turama Saleem text sai ta Shiga wajen Rubuta sako acikin wayarta ta Rubutamai.

   _*Am so srry mallam Bani da laifi wajen Sanar da Ummi komai,Banso mu Rabu ta haka ba buh Allah ya huci Zuciyarka we are in our way,In ka koma gida nayi maka miya,da abinci ka Duba cikin fridge,harda Nama soyayye,Sai mun hadu achan..I love u..*_

Tagama Rutamai ta Turamai suka Cigaba da Tafiya bata ga Reply dinsa ba sai da suka Shiga katsina kana taga ya Rubuto mata  _Banso ban kuma gode ba,I swear zaki dawo ki tarar da Abunki.._  Daga haka bai kara komai ba,ita saima sakonshi yabata dariya ta Shareshi bata kara bi ta kanshi Ba.³¹

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *