MALIKA MALIK CHAPTER 3 BY JANAFTY

MALIKA MALIK CHAPTER 3 BY JANAFTY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

“”Bai waiwayi Malika ba sai da tayi Shekara hudu aduniya,ammh duk bayan watan Duniya yana Turamata over 5k abankin madam dora domin hidimarta,shiko bashi wannan kasar bashi wannan duk domin yaga mafarkinsa ya tabbata,itako Malika tatashi hannun Kafurai ne,bata taba zaton tana da Sirkin kamshin musulunci ba.

Madam Dora ita ta sanyata amkaranta,kuma mkrantan ma,na Turawa,shiyasa tun malika na yar karama dabi’unta da kuma hallayanta yakoma na Turawa,domin a iya wannan Shekarun batataba sallah ba,domin madam dora bata koyamata ba toh masulmace ita,balle ta koyar da ita,wanda yakamata yazauna ya koyar da ita neman Duniya ya Rufemai ido,banda zuwa coci da karatun,bibble bata koyamata komai,domin tayi alqawarin bazata bar Diyar Juliyat ta subuce mata ba, ko kafin mahaifinta ya karbeta ta riga da ta gama tusamata duk wani akidansu.

Shiko Abdulmalik duk wani soyayyah da tanadi wa malika yake yinshi domin yana matsanancin sonta da kuma tsausayinta na yarda bata taba shan Nonon uwa ba,sai dai madara,kuma bata rayu da mahaifiyarta ba,Shiyasa ya dauki son Duniya ya doramata yakan samu lokaci yazo,domin yanzu yabar england yana kasar spain yana aiki da wani kamfanin sarrafa agogon Fata na maza da mata,gida kuwa sai dai yayi musu sakon kudi ko ya kirasu ta waya bai samun sararin zuwa.

Sai da aka kirasa aka sanar dashi Innaro ta rasu kana yaje Nageria lokacin kuma Malika tagama primary sch ,t yaso ya taho da ita,ammh madam Dora taki yarda ta dinga kawomai uzurin cewa Ga mkrantar ta,kar yatafi da ita karatun ta yatsaya,ita kuma bata so yatafi da ita ne yan”uwanshi su Farga Da Abunda ke Faruwa su riketa yaki dawo da ita,ta haka ta ribaceshi ya tafi ya barta,sai dai yaje ya sanar dasu da baki,babu wanda yanuna wani damuwa domin lokacin Abdulmalik shine Sarkin gidan sakamakon yana da kudi yanzu so babu mai ce mai baiyi Daidai ba.

Bai dawo ba sai Da ya bada kudadade sosai wanda zai bude wani kamfanin sarrafa atamfofi akano,domin yanzu Abdulmalik yana da hannayen Jari da yawa akamfanoni da dama,shiyasa yake da kyakyawan alaka da Turawa sakamakon yasan harkan kasuwancin da yadda zai habaka kamfani ya shahara lokaci kadan ba”a Rufe Shekara ba *DAN KASUWA INVESTEMENT* ajahar kano, ya kammallah kuma kafin lokaci kadan ya shahara ako”ina aka sanshi kafin arufe shekara biyu Alhaji Abdulmalik ya mallaki manya kamfanoni masu yawa agida Nageria,kama daga na sarrafa takalma,dana Sarrfa kayan yara maza dana mata,harda na taliya,sai kuma na Tumatur,bayan gidajen man dayake dasu wanda ya bude su da sunan *MALIKA MALIK PETROLEUM NIG LIMITED* Ako wata wata jaha afalin Nageria in kaje zaka ga brach dinsu,hatta a malumfashi bai san iyakarsa ba.

Bai tashi karban Malika ba sai da tagama Secondry sch dinta a england lokacin tana da shekara 18 Aduniya duk inda girma da budurci yake to Malika tagama mallakanshi,ammh kallon Farko zakayimata ka shaida da mahaifiyarta take kama,don tafi kama da baturiya Fiye da jinsu hausa Fulani,duk da baban inda yazo yana kokarin nusar da malika cewa itafa ba irin dangin mamanta bane ita musulmace,toh zata jishi ne kawai ko ya takuramata tayi sallah na ganin idonshi ne kawai yana tafiya zata watsar takama harkan gabanta,tun tana karama ta iya zuwa party da club clubs gashi ta koyo banzan dabi”,an yayan Turawa na Shigar banza bata kunyar Fitar da tsiraicinta waje,gashi ,ammh wannan kwakwalwar ta mahaifinta tayi gadonshi wajen kokari da himma,Abunda yasa malika tadawo hannunshi saboda mutuwar madam Dora ce,yasa bayan anyi Shagalin binneta ya karbo malika tadawo hannunta wanda bai wani samu matsala da sauran yan”uwan mahaifiyarta ba,Tunda ya cikasu da kudi kuma yayi musu alqawarin kawota duk bayan wani Tsawon lokaci.

A Canada Malika tahada digirinta na Farko akan Accounting daganan ta Wuce kasar America a babban birninta US tahada digirinta na biyu,bata dawo ba sai ta  Hada takardan  Phd dinta,lokacin shekaru biyu da suka Wuce mahaifinta yagama cin moriyar Turawa suma sunci nashi yasa ya tararra yakoma gida akatsina ya gina wani tamfatsetsen gida mai kama da aljannar Duniya,kuma yayi aure da matarsa Hajiya Binta,yar”uwansa ce suka manna masa,saboda kudinsa,duk da ita Binta bata sonshi,dayake bazawarace,mijinta ya rasu ya barta da Diya daya mace JODA wacce bazata wuce Shekara 22 da biyu ba, ammh dole ta hakura Tunda kowa na Son daula ,uwa uba kuma tasamu jin dadin Rayuwa,domin shi ya kaita makka,kuma suna zuwa yawon duniya duk bayan wata daya bayan ya saka Joda a mkranta ,yanzu haka tana Final year dinta ne Barrau dikko dake zaria tana karantar SB NURSING.

Tun zuwanta gidan Ta fahimci daga yar har uban babu mai tarbiya da ilimi gabadaya jahilci na dawainiya dasu ranar da suka fara kaima Malika ziyara a US sai da ta zubar da kwallah yadda ta ganta da irin Shigarta da yadda ta maida rayuwarta wlh ko wasu Turawan Sun fita kyan gani,gashi ya shagwabata ya sangarta baya iya mata Fada,yanzu sai takama kuka tana hargowa,shikuma baya son bacin ranta Shiyasa duk Abunda tagama dama shi takeyi,gashi Tun tana karama kudi sun batata komai take bukata aikwai Shi bata taba neman wani abu tarasa,tun dataji lbrin mahaifinta yayi aure,taji tsani matar tukan ta ganta,sai gashi sun hadu banda harara babu Abunda ya shiga tsakaninsu,sai ma ita Hajiya binta ne Alhaji Abdulmalik ya umarta data gaishe da ita Malikan saboda lalacewa,koda suka dawo gida,ta nemi gayamai gaskiya game da yadda yabari Rayuwar malika ta lalace tana ya”mace,ammh sai yaki bata dama yace ta kyaleta taji dadin Rayuwarta Allah yaba mahaifinta Dukiya mai yawa so Dole tayi Abunda taga dama.,Tundaga Ranar Hajiya binta takawo ido ta sanya musu bata kara saka Musu baki ba, Ba kome zasuyi tasani akwai ranar kin Dillanci.

Bayan tagama karatunta dakyar Alhaji malik yashawo kan malika tadawo Nageria da zama saboda kula da kamfoninsa,saboda malika yarinyace mai kokari,she is very talent and smart,gata da wayau da kuma lura,shiyasa lokaci kadan Alhaji malik yasakarmata duka ragaman Kamfoninsa,domin ya Fahimci tafishi iya gudanar da komai,shi sai dai yana gida suyi waya agudanar da komai ita kuma malika taje ta tabbatar,kowani taro za’,ayi,daga gida Nageria zuwa kasashen waje duk malika ke Zuwa ta gabatar da kowani ragama,shiyasa kafin lokaci kadan Tayi suna Aduniya don Aduniya inda kafarta bai taka ba kadan ne,kuma babu wanda baisan Rashin tarbiya da rashin mutumci irin na Diyar Abdulmalik Dankasuwa ba,abokansa sunsha zuwa suna kokarin mai nasiha ammh duk sai ya toshe kunni,daga kuma ranar ya yanke alaka da mutum,masu kwadayi kuwa sunsha kawo tallah da tushen hada ya’yansu aure da Malika ammh yaki bin mganarsu domin malika yanzu ba aure bane agabanta batama sanshi ba,domim bayan dawowarta dakyar da yaki yarabata da karatun Bibble,dakyar kuma ya ke sata tana sallah ammh wani lokacin,sai tazo kwanciya take hadawa,tana Tura bakin ita an takurata tafison Rayuwar england taje coci taje Club,tayi yawo yarda taga dama,ammh dawowarta Nageria,yasa duk tazama atakure ga wani takuran wai sai ta dinga sallah,ita wlh bazata iya ba,mganar dressing dinta kuwa Shi baya ganin aibun hakan,domin rashin saka dankwalinta yasamo na
sabane da tashin datayi cikin Turawa shibaya ganin hakan awani mtsala Tunda shima ba ilimin addin yake dashi ba.

Shiya samomata masu kula da ita mata har guda biyu mrry da Dose,sai excort dinta harsu ashirin masu take mata baya,in zata Fita kamar wata yar Shugaban kasa yadda combain yake biye da ita,ko kafin kace kwabo Alhaji Abdulmalik Dankasuwa yashahara kuma yayi Fice Aduniya bayan tarin dukiyan dayake dashi,ga kuma manyan hannayen jarin daya ke dashi akamfanonin kasashen ketare,inda malika take kula da Shige da Fitar komai,saboda hakanema yasa tayi karatu akan ilimin na”ura domin ta saukakama kanta wasu al”amuran rayuwa ta yau da kullun Tunda komai na business din mahaifinta ita ke kula dashi.

Sau daya tataba zuwa malumfashi,ammh sai da tayi danasani saboda gabadaya garin bai mata ba,kama daga yadda aka dinga kallonta kamar anga wata bakuwar hallita,saboda yanayin shigarta uwa uba babu kallabi akanta sai gashinta data daureshi ta baya ta bazoshi,ba mutanen garin ba hatta dangin Abdulmalik ranar sunyi tir da Dabi’un Malika da suka mata mgana tayi musu Rashin mutumci ta zagesu tas tayi tahowarta,da suka kira mahaifinta suka sanar dashi sai ya goyi bayan yarsa yakuma ce ko suzo subata hakuri ko kuma ya cire hannunshi akansu,sanin da sukayi in ya cire hannunshi akansu sun bani sun lalace don basu da kamarsa yasa sukayi mota guda suka zo suka ba ma Malika hakuri wanda sai da baban yasa baki kana tace ta hakura,Tunda ga lokacin kowa yake kiyayewa saboda ita bata ganin kowa da daraja sai mahaifinta bandashi kowa zata iya takashi saboda kudi,tana ganin Duk wani mikamin Duniyan nan bashi da wani amfani in ba kudi ba.

Malika ta zarce Duk Tunanin mai karatu ba yarinya bace shekaranta 27 Aduniya ammh in ka ganta sai kace yar Shakara 20 ce saboda yadda ta mori jiki,babu gidan Talabijin da gidan Jaridun da ba”ayi hira da ita ba,shiyasa sunanta yafi na mahaifinta shahara aduniya,malika ko abinci bataci da kanta bata akeyi ko wanka sai anyi mata saboda gata komai da kuka sani yimata ake,saboda tace matukar kudi na mganin komai to zasu mata mganin dukkan mtsalanta,Dawowarta Nageria basa ta rage zuwa clubs da party wani lokacin sai tsakiyar dare take dawowa  Akullum Alhaji Abdulmaleek Dankasuwa yana takaichin hallayar Malika musaaman ma n zuwa club da party,ammh bashi da yarda zaiyi da ita,don baya iya tsawarta mata ba, kana tana da wayau bata da yarda ko kadan,ko ma”aikatan ta da excort din ta bata yarda dasu ba,tana ankare dasu kuma tana bibiyan dukkan motsinsu.

Abu dayane batayi Shine Zina,Malika bata yarda Akala tashiga tsakaninta dawani Namiji ba,sai dai in ta kasuwanci ko kuma abota,shima tun barowanta US rabonta da abota da Namiji,kuma tun alokacin ne da Sunan Abota take yarda tayi kiss da mutum sai dan Abunda ba”a rasa ba,ammh bata yarda wani yaketa mata budurci ba,saboda tana da bala”in wayon tsiya shiko mahaifinta tunda ya samu ya yakiceta da zuwa coci da karanta bible hankalinshi ya kwanta,sauran abubuwan datake kuma ko Abun na damunshi bai iya mata mgana Saboda yadda yake matukar sonta da kaunarta,so daya yataba kwantatan yimata Fadan ta rika sanya kayan hausawa,kuma ta dinga mutumta Hajiya binta, da malika tayi Fushi sai dai kawai yasamu waya kan cewa tana England takoma wajen dangin mamanta hankalinshi yatashi sai da yaje da kanshi dakyar da lallashi ta yarda zata dawo ammh da sharadin bazai kara takuramata ba,dole ya yarda da haka saboda yana Tsoron kada watarana Malika tayi Ridda takoma Kafura,duk ko ayanzu marabanta da kafurci ne kadan ne,banda sallah bata wani Abu na bautar Ubangijinta.

itama sallar ba da kyau takeyi ba,ko Fatiha banajin tagama iyawa Saboda lalace babu Abunda tasaka agaba sai Duniya tanaYin duk Abunda tagama dama,ko dabi”ar Tubewa zindir wasu matan nayi miki wanka,Ai dabi”ar yayan Turawa ne wadanda basu san addini ba,ammah kome malika ta zama Aduniya sanadin yana wuyan mahaifinta domin Tun farkom gina Ginshikin samunta bai bi yarda Addinin mu ya tsara ba,koda aka umarceka ka auri Ahlul baiti bai chanchanci bayan haihuwar malika ya mikama Turawa rikon yarsa ba kuma yana sane da cewa sudin ba musulmai bane,taya zasu so malika ta koyi addininshi,shiyasa suka koyar da ita duk dabi”unsu da addininsu saboda ko gaba kada ta barsu.

Ranar da suka hadu da Saleem har ta mareshi ta dawo Daga kaduna ne,wani party ne na ya”yan manya marasa jin mgana da”aka Shirya to daya daga cikinsu Friend dinta ne,Tun suna US shiya gayyaceta taje,shine da zasu dawo sukayi dare har su Saleem suka taremata motoci,Tun sadda Abun yafaru batakara Tuna wani hallita ba balle ta damu da Furucinsa na sai ya rama, ita tana ganin Shirmene da yarinta da kuma talauci da rashin nayi ke damunshi yasa,tun awajen ta tararrashi ta watsar ta cigaba da harkan gabanta,duk a iya tsawon wannan Shekarun babu Abunda ya ragu na Hallayar malika saima Abunda ya karu,Hajiya binta ko bacin kashin da bata gani har marinta malika tatabayi,ammh Alhaji malik bai dauki mataki ba,ita da banza Duk dayane,kallonsu kawai take tana jiyema Alhaji Ranar da zaiyi nadamar Turban daya dora Tilon yarsa akanshi.

Tsakanin Malika da Joda ko basu da wani kyawawan alaqa,duk da ba sosai sukayi haduwa ba,wani lokacin in Malika na gida Malumfashi Joda ke Tafiya saboda ita yarinya ce mai hankali da gudun zuciya ga natsuwa,gata bata hayaniya,itakadai sai ta Shige daki tana kuka,in taga cin kashin da malika kema mahaifiyarta.

Abun na damunta ammh bata da yarda zatayi sai hakuri saboda ko ita bata da bakin mgana, Saboda akwai lokacin da Makila tama Amminta rashin kunya,sao tayima malikan mgana,shikenan ta juyowa ta kasheta da mari,ta kuma sanya su Peter suka Dauketa chak suka Fita da ita daga gidan,tace kuma zamanta yakare agidan,sai dai Hajiya binta ta bita wajen tabata kudin mota tace ta tafi malumfashi Abun yamata bakinciki,sosai datatafi malumfashi tadade wajen Dangin babanta kafin ta dawo,shima saboda Ammin nata ne,ammh daga Alhaji Abdulmalik din har Malika ba wanda ya nemeta,sai ma goyon bayanta da yayi lokacin da hajiya binta ke sanar dashi Abunda tayima jodan,tabe baki yayi yace tayi Daidai Domin tana da iko da gidan Ubanta,Shiyasa Tundaga lokacin ta kiyayi kanta da malika.

Iyakarta da malika sannu daga haka wata mgana batataba Shiga tsakaninsu ba,sai suyi kwanaki agidan ammh wlh ko zasu hadu sau goma ne ba wacce zatama wata mgana,ita malika tana ganin tafi karfin joda,saboda gidan mahaifinta take zaune,kuma take ci tasha tayi Sutura daga Dukiyar ubanta,to tana ganin tafi karfinta tsakaninta da ita kamar nisan kasa da sama, ne.

Itako Joda tana kiyayewa ne Tun Abunda yafaru Amminta tajamata kunni sosai kan Malika,shiyasa tafita harkarta in taga damane ta gaisheta randa bata ra”ayi kuma tayi kamar bata ganta ba.

*CIGABAN LABARI*

_Washegari_

Saleem Tun bayan da suka dawo sallar Asuba da Abbi da ya marwan bai yarda ya kara haduwa dakowa ba,ko masallacin ana sallame sallah yayi Wuf ya Fito,saboda kada ya marwan ya tareshi da wata mgana,don bai shirya amsama kowa tambayanshi ahalin yanzu ba,sai ya aiwatar da gudirinsa akan Malika 

Yana dawowa ya Shirya domin komawa bakin aiki,ada yaso yabari sai gobe monday,ammh don gujema Fuskartar wasu barazanq mussaman ga Ya marwa da Ummi,shiyasa ya Shirya komawa batare da ya sanar da kowa ba.

Karfe 7:00am na Safe ya Fito daga Dakinsa yana sanye da Uniform dinsa,sai wayarsa da makullin motarsa,Falon Tsit babu motsin kowa sai Ashura mai goge  goge ce kadai afalon tana share share,sama sama ya amsa gaisuwanta ya nufi koridon da zai sadashi da dakin Hajiya babba,domin itace kadai hope dinshi ayanzu.

Koda ya Shiga dakin nata,tana zaune akan darduma tana laziminta na safe,domin a akidar hajiya in tayi sallar asuba bata tashi awajen sai  Rana ta Fito.

Tana jin sallamarsa ta dago tana kallonsa,saboda yadda uniform din suka amsheshi ko ita sai da yayi ma kw
arjini sosai,mirmishi ya sakarmata kafin ya karisa gabanta ya zauna bayan ya cire takalmansa daga bakin kofar dakin,yana Fadin”Hajiya barkanmu da Safiya..?

Shafa addu”anta tayi kafin tace”Muntashi lafiya? sai ina naganga cikin Shiri kamar wanda akace gawani dan fashi chan? Dan mirmishi yayi kafin yace”Kaji hajiya,yo mu ai basai mun jira ance ga Dan fashi ba,mu da kanmu muke Fita nemansu,Tunda kinsan bazasu kawo kansu ba..”

gyada kai tayi tana Fadin”Hakane kuma toh Allah yayi jagora..”Da Amin ya amsa kafin yace”Hajiya zan Wuce,nazo ne nayi miki tuni kan mganarmu ta jiya,wlh am serious don Allah ki matsama Abbi yaje yanemanin Aurenta plz..”Kai tsaye hajiya tace”Ina zanyi sanya,ai dolensa nema yaje,Abunda muke ta nema kuma Allah yakawo to me zamu jira?karka damu insha Allahu zaka aureta Tunda na lura kana sonta..”

Dan cije baki yayi baiyi mgana ba,saima Kallon agogon fatan dake hannunsa yake,kafin ya mike yana Fadin”Zan Tafi hajiyata,nidai kiman kokari kome ke nan,zamu waya..”bata tashi ba tace”Toh Allah ya tsare…”Da Amin ya amsa kafin ya Fice.

Daga Dakin Hajiya ko Dakinsa bai koma ba,yayi waje,motarsa ya Fada yamata key yana zuba hon,da hanzari maigadi yazo ya budemai get yana mai Fatan isa lafiya,babu wanda yasan Tafiyarshi agidan sai hajiya,shiyasa har sai da  akazo breafast ne,aka Farga saleem bashi agidan lokacin da Marwan ke tsiyan yasan Abunda yayi yaki Fitowa Hajiya ce tace”,Wa..? Salihu ai ya dade da isa zamfara yanzu…”ba su kadai ba hatta da Ummi sai da Abun na Saleem yafara bata mamaki babu dai wanda yace kanzil kowa ya barsa da Abun Tunda ganin Shikanshi mai gidan bai ba mganar wani muhimmanci ba.

shiko Abbi yaki bada Fuska ne saboda kada sumai wata mgana mussaman Ummi wacce Tun daren jiya taso tatadamai Tsiyarta yaki bata Fuskar yin hakan,data fara zencen ita bata yarda ba,kuma shima kada yabiyema Saleem,haryanzu yaro ne baisan inda ke mai ciwo ba,ammh ita bazata bari Akawo mata wannan Tsinanniyar yarinyar amtsayin Suruka ba ko alama.

  Shikanshi Abbi ya Shiga dogon Tunani game da bukatar Saleem,duk shima yana da lbrin yarinyar kaf bamai dadi bane,toh ammh yayi Duba zuwa ga wani Abu,duk wanda yayi sanadiyar Shirriyan wani Shima yana da lada,sai dai kuma kafin ya je wajen Mahaifinta sai ya kira Saleem ya tabbatarmai ba saboda Dukiyan mahaifinta yakoson aurenta ba,duk yana da Shaida sosai kan tarbiyan ya”yansa,.

Baya da Haufi kan Saleem domin yafi Shakuwa dashi fiye da marwan,wanda baima yi karatunsa a nageria ba,kuma yana da masaniyar Jarumi ne na karshe,wanda zai iya tankwasa ko wacce mace indai tana karkarshinsa ne,kuma aure ba haramun bane,sunnar ma”aiki ne kuma Dukkansu akanshi sukazo Duniya,shiyasa batare da shawara dakowa ba ya yanke zai kai ma Alhaji malik ziyaran Farko tun bayan kammallah jami”ar Dan Fodiyo basu kara samu zama sosai ba,sai dai haduwa sama sama,wanda bayan yazama IGP sun hadu sau biyu wajen taro wanda shima agayyaceshi ne yaje suka hadu,suka gaisa duk da kowa yana da nombar kowa,ammh basa mgana awaya,saboda yanayin aiyukan kowannensu.

Monday*

monday Tushen aiki ko bature na tsoronta,Tun safe Abbi ya Shirya bai sanar da kowa ga inda zashi ba,ko Ummi bai sanar da ita ba,saboda tana Fushi dashi Tun safe ma ta Fice zuwa babbar kotun data ke aiki A higher suprime court Abuja.

Karfe 10:00am na Safe suka dau hanyar katsina dagashi sai Direbanshi,Wanda marwan yaso ya tukosa,ammh ya dakatar dashi saboda bayason kowa yasan inda zashi.

kokafin 12 da wani abu,suna kofar gidan Alhaji Abdulmalik Dankasuwa dasuka zuba hon cikin motarsa kirar vibe2k19,Da megadin ya leko sai da yatambayesu,ko suna da ganawa dashi Alhaji Abdulmalik din ne? amsa Abbi yabashi da cewa “A’a baisan da zuwanshi ba,ammh asanar dashi wani tsohon abokinsa ne daga gombe…”

  Koda Alhaji Abdulmalik yaji  Haka Abun yabashi mamaki,don baitaba kawowa Cewa Kabir kumo bane,sai ya bada Umarnin abarsu su shigo,koda suka shigo cikin babban Falon gidanshi na kasa,aka sauke Abbi wanda yaji kayan alfarma kamar baza”a mutu ba,ko kafin kace kwabo ancika gabansa da kayan lashe lashe da shaye shaye.

Yafi minti goma zaune kafin Alhaji Abdulmalik ya Shigo sanye da shadda gezner fara riga da wando,Abbi zaune yabama kofar Shigowa Falon daga cikin gida baya,shiyasa har Alhaji Abdulmalik ya kariso yana Fadin”Barka da zuwa…”

  Juyowa Abbi yayi yana mirmishi yace”Yauwa….”Yafada yana mai kayatattacen mirmishi,Sake baki Alhaji Abdulmalik yayi,kafin ya rike bakinsa yana Fadin”Kabir kumo…? Yafada yana nuna shi,shima Abbi nunasa yayi yana Fadin”Na”am Abdulmalik Sa”ad..”

yafada Fuskarsa da yalwa da Fara”a Rumgume juna sukayi suna mai murnan ganin juna kafin su saki juna mamaki bai bar Alhaji Abdulmalik ba,kara rike hannunsa yayi yana Fadin”Am very Suprise dana ganka agidana kabir,alhalin ni yakamata na fara kawomaka ziyara? garin  yaya haka IGP guda yana yawo babu wasu masu tsoron lafiyanshi..? yafada yana dariya.

Kafadansa Abbi yadaka yana Fadin”karka damu kanka Abdulmalik,gashi na nafara zuwa,mganar zuwa da Masu tsorona kuma,ni na dakatar dasu saboda bani son kowa yasan nazo ne,so nake ka ganni amtsayin Kabir kumo dina ba IGP Ba..”Dariya suka saka kafin su koma su zauna Alhaji Abdulmalik na Fadin”Am so happy wlh..Ya hanya..?

Nan suka shiga gaisawa,sai kuma hirar yaushe gamo tatashi,dakuma tambayan iyalai,nan Abbi ke sanar dashi ya”yansa Uku maza biyu mace daya,Shikuma ya sanar dashi Yarsa dayace aduniyan nan,yana ta bashi kadan daga cikin nasarorin Daya samu atafiyar shi kasar England.

Alhaji Abdulmalik dakanshi ya shiga cikin gida yakira Hajiya binta tazo suka gaisa da Abbi,wanda suka gaisa cikin sakin Fuska,kafin takoma ciki,nan da Alhaji Abdulmalik ya Umarci Da a shirya Abinci mai rai da lafiya ga Amininsa Kabir kumo,wanda suka baje suna ta hiran yaushe gamo,suna Tuna rayuwarsu ta mkranta suna Dariya Abun gwanin ban sha”awa.

Malika bata Fito daga dakinta ba sai around 2 na rana koda ta Fito tana sanye da wani damammen wando pencil,wanda ya Fitar da duka suran cinyoyinta,rigar jikinta kuwa bata da hannu,wanda dakyar ta Rufemata cibi saboda rashin tsawo,kanta babu dankwali dama bata saba sawa ba,sai gashinta wanda ta daureshi daga tsakiya da band,ta saki jelan yana Mata yawo abayanta,Ear phone akunnenta wacce take jin waka da faskekiyar wayarta.

Dakin Daddynta tashiga ta iske baya cike,da sassarfa ta sauko Falo tana kwalama Hajiya kira,tana kichen suna aiki da Atika,ta Fito tana amsawa karo sukaci da ita tana Fadin”Hajiya ina Daddyna..? na dubasa dakinsa baya ciki..? ta Fada tana Wani yamusta fuska,tana mele baki wanda yaji wani pick din jambaki.

Kallonta tayi daga sama har kasa kafin ta kada kai tace”Yana Falon bakinsa na kasa,yayi bako ne..”kada kai Malika tayi batare datayi mgana ba Tanufi hanyar Falon tana tafe Gabadaya Hip dinta suna kadawa kamar wata karuwa baki Hajiya ta rike kafin ta bita da sauri ta rikota tana Fadin”A”a malika don Allah karki je ahaka kikoma ki Suturta jikinki don Allah…”

Wani kallo tayi mata kafin ta waigo tana Fadin”Found of corection Hajiya,in Suturta jikina fa kika ce? yanzu ina yawo Tsirara ne..? tafada cikin mamaki tana bin kanta da kallo.

Hajiya binta tayi saurin cewa”Bance kina tsiraraba,nufiba kije ki sanyo ko dogowar riga ki Rufe wannan kayan don Allah…”,Tsaki malika taja tana Fadin”,excuse me Hajiya..”Tafada tana zare hannunta dake kafandanta ta wuce tana wani kada kai kamar wata kadangaruwa.

Fadowa kawai tayi Falon babu sallama,sai dai Alhaji Abdulmalik yaji kikam ta Fadomai ajiki ta Rumgumesa bayan ta sakarmai kiss agoshi tace”Daddylove i miss u…”

Tunda Alhaji Abdulmalik yake da Malika bai taba jin kunyar Hallayarta da banzan Dabi”arta ba irin na yau,duk kunya Abbi ta kamasa,wanda yayi kasake yana binsu da kallon mamaki 


Mirmishin dole ya saki yana riko hannunta yace”Me too my Sweetbby,kin tashi lafiya..? baki tawani mele kafin tace”Fine Daddy…”Tafada tana kara gyara zama bisa cinyarsa idonta kur ana Abbi ammh baisa ta gaisheshi ba,duk ta  ganeshi tana ganinshi albarai amtsayin IGP na Nageria gabadaya ammh ko agefen gyalenta,duk atunanin yazo maula ne wajen mahaifita tunda haka take kallon kowa.

Alhaji Abdulmalik ne yace”Aermmm Sweetbby baki gaida bako na ba? Shima Abbanki ne,tsohon abokina ne,tare mukayi gwagwarmaya dashi a jami”ar Sokoto yanzu kuma Kinga yadda Allah ya maidashi shine inspector general of police na kasa gabadaya…”,idonta kur akanshi kafin ta dauki Farin hannunta ta mikamai Tana Fadin”Hy….”

Ai ba Abbi ba,har Alhaji Abdulmalik yaji ya muzanta da Abunda malika tayi kunyar Duniya duk ta kamashi,shiko Abbi mamaki tare da al”ajabi sun kamashi,lokaci guda kuma tsausayi suka bashi daga uban har yar domin zahirin gaskiya rayuwarsu na cikin tabewa.

Mirmishi ya sakarmata bai mikamata hannun ba yace”kina lafiya…”,Kai tadaga kafin tace”Fine….Same….”Tafada kafin ta mike tana Fadin”Daddynlove let me go, Zanje nayi breafsat sai ka shigo…”Dagahaka ta juya tana Tafiya Ko”ina na jikinta na rawa mussaman ma hip dinta,da hanzari Abbi ya kauda kai yana Ta’awizi aransa ayayinda Alhaji Abdulmalik ya sadda kai kasa yana jin wani iri aranshi.

Abbi ne ya kaunda Shuru da jansa da wata hira shiyasa yadan saki sai da yaga haka kafin yace mai”Wannan itace malikar..? da kai ya amsa mai kafin yace”Yes itace,my dota ina alfahari da ita,domin acikin kaso mafi yawa daga Dukiyata samuwarta ya samo asali ne daga jajircewarta…”Jinjina kai Abbi yayi kafin yace”,Gaskiya ne kenan ita ke Lura da komai yanzu,kai kana gida kenan..”Girgiza kai yayi kafin yace”Eh gaskiya kusan komai ita ke zuwa ta gabatar takuma tabbatar,wani lokacin sai akirani ta waya mu jadadda bayani,ammh gaskiya yanzu ragamar komai na hannunta don jiya tadawo daga london ma,kan mganar wani kamfani danike da hannu jari dasu..”

Shuru Abbi yana jinjina kai kafin ya kalleshi kai tsaye yace”To kana shirin aurar da ita kuwa Abdulmalik…? Kuri yayimai da ido yana kallonsa gabansa na Faduwa,ajiyar zuciya ya sauke kafin yace”Ban taba sanar da wani wannan mganar ba sai kai kumo,wlh inason malika tayi aure saboda cikar mutucinta,ammh mtsala dayane Malika ,banta ganinta dawani Namiji da sunan suna soyayyah ba,kai infact ma nataba mata mganar aure nace yakamata tayi aure,sai ta sanar dani ita Batasan ma miye aure ba,ta,zauna karkashin wani ? to indai hakane har abada bazatayi aure ba,Abun na damuna sosai kumo narasa yadda zanyi ne..”Yafada muryansa ta chanza kamar yayi kuka.

Riko hannunsa Abbi yayi yana Fadin”Meyasa? ai batafi karfinka ba,in ka Tursasa mata dolenta tabi Tunda kana matsayin mahaifinta,ammh cigaba da rayuwa haka Bazai yuyu ba,domin Duk ranar daka mutu wlh sai Allah tambayeka game da kiwon da kayima yarka..”Shuru yayi kafin yace”Bana iya Tursasa babby tayi abu,saboda ban son Abunda zai mata mata rai,zan dai gwada lallashinta,toh in ma ta yarda ina miji,nifa tsoro nakeji yanzu samarin zamanin nan duk ba don Allah suke aure ba,sai domin hannun jari,kuma samun Tsayayye jarumi wanda zai tankwasa Malika abu ne mai Wuya koni mahaifinta bana iya tankwasata toh balle wani..”Yafada cikin zafin rai,ashe Abun na damunsa bai iya Fadane.

Ajiyar zuciya Abbi ya sauke aransa yana Fadin”An zo wajen…”gyara zama yayi kafin yace”indai wannan ne baka da damuwa,in ka yarda ina so zan neman ma Da’n wajena aurenta,i know My son very well zai iya Zama da ita harma daga karshe zamansu yabamu mamaki..”(Ya sanar dashi hakane saboda bayaso yace Saleem ne yace yana son Malikan,wanda dole zai zargi wani abu..)

Kallonsa Alhaji Abdulmalik yayi bakinsa duka abude saboda Farinciki gefe daya kuma fargaba yakara damke hannunsa yana Fadin”Da gaske kake kumo..?,Gyada kai Abbi yayi kafin yace”Da gaske nake indai ka amince sai mai tattauna mganar…”Rumgumesa kawai Alhaji Abdulmalik yayi yanajin kamar yayi kwallah yace”Ngd ngd…Kabir kumo,hakika ba iya abota kakesona dashi ba,kai masoyin gaskiya ne,Tun lokacin muna mkranrta tare dakai,naji kunya lokacin da kaga irin rashin tarbiyan da Malika ta maka,ammh duk da haka bakaji komai ba,kakeson hadata da Danka wanda ko da banganshi ba,nasan yatara abubuwa dama kumo,sanin da nayi maka mai tarbiya da ilimi da hangen nesa nasani cewa bazaka bar zuru”arka haka,hakika kai abokina ne na nagari,ni kaina ina son Malika ta chanza kumo,ammh ya zanyi domin Na bar Shiri Tun rani,dana barta hannun dangin mahaifiyarta ta girma,duk shi yakara maidata haka..”Yafada yana sharbe kwallah kafin ya dago yana kallon Abbi.

Mirmishi yayimai yana Fadin”Babu komai wlh,dama ita rayuwa haka tagada,ammh kaima danaga kuskuren data dawo wajenka bai kamata ka sakarmata ba Abdulmalik,ita Diya mace ba”a barinta haka ko Da namiji  ya fandare balle mace,macen ma wacce ka sakarmata komai sai yadda tagama takeyi…”gyada kai yayi kafin yace”Ko baka Fada ba i know iz my mistake,bana bari wani ya sanar dani haka kabir saboda bani son Abunda zai dagamin hankali,kai ne mutum na farko dake sanar dani kai tsaye nayi ba daidai ba na gyara hakika nagodema Allah daya hadani dakai,yanzu kabar mganar komai ahannuna komai ke akwai zamu mganata ta waya buh yanzu in ka koma ka Turomin yaron wajen naka sai muyi mgana..

Hannun Abbi yabashi suka sarke yana Fadin”Masha Allahu,to ai bakomai zan sanar dashi insha Allahu…”Yafada yana bayyanar da murnansa,nan suka cigaba da tattauna al”amarin Alhaji Abdulmalik nata sanar dashi damuwarsa game da wasu dabi”un Malika bai iya boyemai komai ba,hatta ayadda abagaren addinin bata san komai ba,batayi iya komai na rayuwa ba,gazuwa club da Party ga rashin salla akan lokaci,Bata son komai sai rayuwar gata da jin dadi,yana Fadamai yana kwallah domin iya shekaru daya dauka da wannan takaichi bashi da wanda sai sanarmawa saboda duk Abunda malika tazama ayau Shine silan komai,Hakuri Abbi yayi tabashi yana sanar dashi insha Allahu zata gyaru.

Sai gashi Abbi bai baro katsina ba sai da sukayi sallar la”asar kana suka dauko hanya kamar karsu rabu,hakika Alhaji Abdulmalik yaji dadin zuwa Abbi da duk abubuwan dasuka tattauna,yanzu Fargabansa daya da kuma Tunaninsa taya zai Tunkari malika da wannan mganar,domin yasani ko giyan wake yasha bai da ikon sanar da ita komai,gabadaya ya Shiga Rudani yakasa samun mafita,kuma bayaji zai iya hakura zuru”ar kabir kumo kamili da dattako ya Wuce Malika domin bayan shi din,ba uban da zaiji hallaya tare da Abun Tir game da malika kuma ya amince Dansa ya aureta,wannan sai uba na gari,da Amini na gari.

Shiko Abbi har suka kai Abuja zuciyarsa na harbawa,yana so ya gano mai Saleem yagani wajen wannan yarinyar da zaice anema masa aurensa,shi dai bai hango wani quality wajenta ba,illah tarin munin dabi”unta,ada ya karaya ammh kuma sai ya duba da ya amince saleem ya auretama wani jihadi ne babba,toh ammh Abu daya yake son sani wani dalili ne ya sanya Saleem ke son aurenta? in har Abunda zuciyarsa ke zargi ne,to bazai lamunta ba,sai da ko yakira Alhaji Abdulmalik yabashi hakuri,ammh bazai yarda ayi Abunda daga baya zaiji kunya ba,da girmansa da komai..

    *****************

Kwance yake akan makeken royal bed dinsa wanda yaji Shimfudun alfarma,katon bedroom ne mai dauke da gado,sai dressing mirror,sai wani katon wardrope wanda ya cinye rabin dakin akallon Farko zaka Fahimci ma mallakin dakin baison hayaniya da tarkace,domin daga kayansa dake sagale a hanger,sai jerin takalamsa kama daga sawu ciki,zuwa budaddu wanda suke jire bisa wani Stool mai Fadi da Tsawo.

Dakin malale yake da wani Cafet mai taushi da Santsi bayan kuma daga Fentin dakin har kalan Funutures din ash and black ne.komai dai ya tsaru kamar ba dakin Namiji ba,saboda yadda komai yake atsare.

Mamallakin Dakin yana kan gadon kwance dagashi sai bakin dogon wando,jikinsa babu Riga,gabadaya Fafaffada
n kirjinsa wanda ke cike da gargasa,ya bayyana awaje,Mike yake sambal bayan duka idanuwansa suna sama suna kallon Rufin dakin,yayin da duka hannuwansa ya Sagale su abayan keyanshi yayi matashi dasu.

yayi zurfi cikin Tunaninsa kafin karar wayarsa ya Dawo dashi,da hannu ya sa yajawo wayar wanda ke kan Stool din gadon,sunan daya gani ne yasashi sakin Siririn tsaki Afili ya Furta..”Kai Dis man,in maye ne in yakama mutum wlh sai ya ga bayansa haba..”

Yafada irin Abun ya ishesa Din nan, dankawafar da wayar yayi yana tsaki bayan naga sunan mai kiran *FRIEND* ne da manyan baki,Idanuwansa ya kankance aransa yana Jin in ya hadu da saleema sai yaci ubanta,Bakin yarinyarnan kamar sikat,saboda rariya jikinta narawa komai akayi agida sai ta kira sadiq ta sanarmai kamar wata Sakarya,Abunda ya lura dashi daga shi har ita Tsofaffun munafukai.

Tun jiya daya dawo Sadiq keta kiran wayarsa yana kin Dauka,domin yasan Tatsuniyar gizo bata wuce ta koki,Mganar malika ne yake so yamai,shikuma haryanzu bai shirya Amsa wata tambaya ba,ko kuma ya budi baki yayi bayani Abunda ke gabansa kawai Sai ya rama ne,shiyasa yake ganin kiran yana kin dauka.

Wayar nasa ne takara dauka Tsuwa wannan karon dogon tsaki yaja ya mike daga kwance ya dauki wayar yayi niyyar ya dagane ya danna mai ashar sai yaga sunan Abbi na yawo asaman Sreen din wayar tasa,jikinsa na rawa ya daga kiran yana Fadin”Barka da Safiya Abbi.?

Dagachan bangaren Abbi ya amsa da cewa”Lafiya lau Acp,ya aikin? ya karba da”Alhadulilallah Abbi ya gida dasu Ummi…? Abbi yace”Gida dukkansu suna lafiya,jiya kuma sai ka tafi ba sallama ko? Kunya takamasa sai ya kama sosa bayan keyanshi yana yar dariya yarasa tacewa,yar dariya Abbi yayi irin nasu na manya kafin yace”Mu bar wannan mganar,yanzu dai dalilin kiranka danayi dama juz na tambayeka tsakaninka ga Allah ne,Shin meye dalilinka nason Auren Diyar Alhaji Abdulmalik Dan kasuwa..?

Gaban Saleem ya Fadi nan da nan zufa tashiga ketomai ta ko”ina azahirin gaskiya bazai iya sanar da Abbi dalilinsa na Son auren malika ba,kuma bazai iya sanar dashi don Allah yakeson aurenta,kada Allah yakamashi da laifin karya,gashi Abbi ya daureshi da cewa ya sanar dashi tsakaninsa da Allah.

Kame kame yafarayi Muryansa na Rawa Abbi ya katsesa da cewa,”Kaga Ka natsu ni ba ina Turke ka bane naji dalilinka,ni Abu dayane nakeson ji,Allah yasa ba zargin danike akan ka bane,..? Saleem ya aro baki dakyar yace”Abbi wani zargi kake akaina..?

Kai tsaye Abbi yace”Ina tsoron ko saboda kudin mahaifinta kakeson auren ta..?Ajiyar zuciya ta kwacema saleem ya saukarya yana jin wani sanyi aransa kai tsaye yace!Wlh Abbi Waye Allah..? shine Shugaban halittun duka Duniya ko? Toh Tallahi ba saboda kudin mahaifinta bane,haba Abbi kafi kowa saninmu,mu har wani kudi ne zai Rufemana ido,me muka nema muka rasa agidan Duniya..”

Mirmishi Abbi ya saki kafin yace”Alhamdulillah,Naji dadin jin haka,dama Fargaba na daya kada wannan ne dalilinka daga baya azo ana jin kunya,Masha Allah jiya naje katsina na hadu da mahaifinta,dayake munada kyakyawan alaqa dashi na sanar dashi komai,kuma shima ya nuna murnansa kuma yayi na”am da mganarka..”

Washe baki Saleem yayi kafin yace”Nagode Abbi Allah kara girma…”Abbi ya Murmusa yana Fadin”Ameen,ammh yanzu yace yana son ganinka,so in kasamu lokaci sai kaje ku gana ko? gyada kai yayi yana Fadin”To shikenan Abbi babu damuwa ko gobe ne sai naje ya ganni..”Abbi ya jinjina kai yana Fadin”To babu mtsala zan kirasa na sanar dashi zuwanka,kai kuma zan Turamaka nombarsa kaji ko..”Amsawa yayi da cewa,”Naji Abbi Allah ya biya bukata ngd sosai…”Daga haka sukayi sallama.

Saleem ya tashi da sauri ya daka tsalle yana Fadin”Game din ya kusa karewa fa…”Malika malik ganin nan zuwa gareki..”Yafada yana wani Cije baki bayan ya datse lebenshi na kasa,yana wani juyi kamar wani zakin daya dade bai ga abinci ba.

___________________

Shiko Abbi koda yadawo koda wasa bai sanar da kowa Abunda yake Faruwa ba,kama bakinshi yayi ya tsuke yana jiran Saleem yaje katsina ya dawo komai kenan daga baya kowa yaji,ko Hajiya data matsamai sanar da ita yayi sunyi waya da Alhaji Abdulmalik ya sanar dashi baya gari ammh da zarar ya dawo zai sanar dashi,toh dahaka ya kashe bakin Hajiya.

Itako Ummi bata kara marmarin karamai mganar ba,yasani ta sakamai ido ne taga iya gudun Ruwanshi,shiko yafi kowa karantarta tana da saukin kai,koman Turjiyanta kan Abu,da zarar ya tankwasata tana tankwasuwa,saboda yadda suke da Fahimtar juna,shiyasa bai damu da shariyanta ba,kuma mganar gaskiya duk wata uwa tagari bazata so Danta ya hada Zama ko Aure da Malika ba, domin kwata kwata bata cika sharudan zama mace tagari ba,Marwan ko Tun ranar litinin din yakoma,shi bai wani damu ba,don yana daukan mganar Saleem amatsayin Shirme ne kawai.

Shiko Alhaji Abdulmalik Ranar bai iya Runtswa ba saboda damuwa da Tunanin mafita,duk Farkawar da Hajiya binta zatayi sai ta ganshi zaune ya jingina da gado idonshi biyu ya Shiga zurfin Tunani,in ta tambayeshi yace mata bakomai takoma ta kwanta Kawai,Farkawanta uku tana ganinshi cikin wannan Halin,Na karshen ne tatashi tashiga tiolet ta wanko Fuska tazo ta zauna kusa da kafafunsa tana Fadin”Haba Alhaji,wai meke Damunka ne,Tun dazu  dana farka sai na ganka zaune ka zabga Tagumi,kuma na tambayeka kace bakomai,Bakomai ne zaka kasa barci Fisabillah…? 

Tafada cikin kulawa Tana kallonsa,kur da ido,ajiyar zuciya ya sauke yana Sauko da kafafunsa kan lallausan Cafet din dake malale abedroom din,Dukar dakai yayi yana Jin Damuwa tayimai yawa,yana da bukatar Abokin shawara,Kuma yanzu bashi da kowa akusa dashi sai Binta,dalilin daya sanya ya dago yana kallonta kafin yace”Binta akaro na Farko Tun bayan aurenmu zan sanar dake damuwata ina Fatan zaki bani shawara don Allah..?

Gyada mai kai tayi tana Fadin”insha Allahu Alhaji,dama amfanin zaman tare kenan…”Kada kai yayi kafin ya shiga zayyanamata yadda sukayi da IGO KUMO,har zuwa karshe ya karishe da Fadin”Ya kike ganin za”ayi Binta wlh ina tsoron sanar da Sweetbby wannan al”amarin bansan da wani Fuska zata kalli Abun ba infact ma ni banison Abunda zai bata ranta ,ammh mganar gaskiya inason Malika ta auri Dan wajen Kabir kumo,ko don samu ingantattacen tarbiyan dani mahaifinta na gaza bata…”Yafada cikin Raunin murya.

Hajiya tayimai zuru tana kallonsa cike da mamaki kafin tace”Tabdijam babban mgana Alhaji,ammh azahirin gaskiya najima malika murna,domin ko ba komai Aure wani Nau”i ne na Bautan Ubangiji,da kuma Fatan Rabauta ranar gobe kiyama,ammh kuma wani hanzari ba gudu ba Alhaji a yadda ka bata yarinyarnan bana jin ko kai dakake mahaifinta zata saurareka balle kuma wani,…”Tafada tana jinjina Abun.

Dafe kanshi yayi yana Fadin”Shine babban damuwana,Binta yanzu menene mafita..? Ajiyar zuciya ta saka kafin tace”Mafita dayane Alhaji,sai dai aboye wannan mganar kada asanar da malika sai bayan an daura auren kana,koda zatayi borinta na dan lokaci ne Tunda anrigaya da an Daura auren..”

Kallonta yake yana jinjina kai alamun gamsuwa da shawaranta yace”Shawara mai kyau Binta,kinga yadda ma Tafiye Tafiyen kamfafoninnan suka gabato zata kashashe biyu ina jin kwanannan,Allah barshi sai ansanya lokacin bikin daidai lokacin da zata dawo…”Hajiya binta tace”hakan ma yayi Alhaji Allah dai ya Shigemana gaba…Da Ameen ya amsa kafin ya cigaba da sanar da ita sauran Shirinsa ammh zai ijeye komai sai yaron yazo su Tattauna.

   

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *