MARWAN CHAPTER B
Ilahirin jikin Umma rawa yake ta kuma riƙe Abba tsam kamar zai gudu, cikin ɗaga murya ya fara karanto ayatulkursiyyu yana kaiwa ƙarshe zai ɗakko wata ayar ya dire sannu ahankali sukaji wannan girgizar ta fara lafawa, Maryam ce ta kalli Abba tace, ” Abba ina zuwa zan ƙarasa gurinsa ” jiki ba ƙwari Abba yace, ” ina tsoron karya haɗaku gaba ɗaya ya cutar daku saboda nasan Maryam tana da raunin ibada ” ita ɗinma tasan sarai halin Yanzulak sai dai bazata karaya ba saboda karta karyarwa da su Umma gwiwa, cikin nuna gwarin gwiwa tace, ” babu Abinda xai faru damu da taimakon Allah ” tana gama magana ta tashi ta keta ta jikin bango ta ɓace, daga Umma har Abba kowanne zuciyarsa babu daɗi ga hankulansu gaba ɗaya ya tashi, jigum sukayi aka rasa mai bakin magana sai dai kowa da abinda yake saƙawa cikin zuciyarsa.+
Marwan jin Abba na niyyar ƙonashi yasa da sauri ya tashi daga saman rufin gidan wata irin muguwar tsanarsa ta kuma ɗarsuwa azuciyarsa musamman da yaji duk irin bayanin da Maryam tayi masa kuma da karɓar addinin su Abba da tayi, yana tashi bai sauka a ko’ina ba sai cen tsakiyar da’irar fadarsu yanayinsa ba walwala ya sauka, duk fadawan gurun sunsha jinin jikinsu musamman da suka san gari banza ma Yanxulak bashi da daɗi bare kuma antaɓoshi, tunda suka ga dirarsa suke masa barka da sauka babu wand ya tankawa kai tsaye cen ƙarshen fada ya zarce kowa na ganin wucewarsa yasha jinin jikinsa saboda sun san sarai ba abu mai daɗi ne yake kaishi cen ba, babu ko neman iso haka yasa kai ya danna cikin wata ƙatuwar ƙofa, bai zarce ko ina ba sai gurin Kakanninsu na ɓangaren Uba fuska babu walwala ya rissina ya gaidasu sannan ya zauna yana jera musu bayani, ” misasatbinsa bi Jalbalsikabu wadribakinsahu misasu kalbasali munbatu girbaki harbinsaku kilasminsas finsatu mumdasgifam Falzuka “( yakai mai martaba Jalbalsikagu bana fatan ɓulluwar wata matsala acikin masarautar nan amma wannan karan Falzuka ta kaini bango ) kallansa suka yi da kyau sannan kakansa ya tambayeshi, ” mirsaduskinda kilbasu tahrasbinsa kilasim Yanxulak? ” ( bama fatan jin tarxoma acikin dangin nan amma meye ya haɗaku Yanxulak? ) duk abinda yake faruwa tsakaninsa da Maryam ya kwashe ya sanar musu da tura Falzuka da yayi sai kuma kawo masa tsaiko da take ƙoƙarin yi, gaba ɗaya sun saurari bayanansa kakansu Jalbalsikagu na shirin yin magana sukaji shigowar Maryam itama fuskar nan tata atsuke take babu walwala, sai da ta rissina duk ta gaishesu cikin girmamawa sannan ta nemi guri itama ta zauna, Jalbalsikagu ne ya fara magana, ” Falzuka mimsadufit kalbisrakat limansubatul kalbanxinsa munsa tafkad hinzaxin laimansu winfasanun, wargar Yanzulak kimbarimsat ifsanai ganfasudanki? ” ( Falzuka nasan abinda ke tafe da ɗan uwanki kema shi ke tafe dake, amma Yanzulak baka ganin akwai ƙalubalen da zaka fiskanta tunda ba jinsinmu bace? ) duk yanda kakansa yaso nuna masa illar hakan fir Marwan ya ƙeƙashe ƙasa ya nuna shi ba wanda ya isa ya raba shi da Maryam dukda dai kakannasu bai nuna goyon bayansa akan kowanne ɓangare ba, Falzuƙa tashi tayi ta fice daga gurin bayan fitarta kakansu Jalbalsikagu ya tambayi Marwan, ” warginkasu lalisfatun kirazu Maryam kinsatu bindastinkahu ” ( a ina ka ajiye matar taka Maryam na ɗauka masarauta zaka kawo ta) ” Marwan ko kaɗan baiso gayawa kakan nashi ba amma ganin Falzuka ta fice yasa yace masa, ” gaibatslak finsatu minraki DULBARYAZIMMU ” ( tana cen cikin kogon dutsen Durbaryazimmu ) Falzuka dake jin duk hirar tasu cikin murmushi ta maimaita sunan da Marwan ya faɗa ta wuce gaba abinta.
Maryam na barin fada bata sauka a ko’ina ba sai cikin kogon dutsen da Marwan ya gayawa Jalbalsikagu, lokacin da ta shiga ta jima tana dube-dube neman Maryam amma bata ganta ba, har ta fara sarewa agefe ɗaya kuma ga fargabar kar Yanzulak ya dawo ya sameta aciki, faɗawa tayi cikin wata ƙorama dake cikin kogon dutsen tana faɗawa ta samu Maryam zaune guri ɗaya, Maryam ɗin Abba na ganin mai siffarta tsoro ne ya kamata atunaninta wannan wace ta taɓa tsoratata ce, duk yanda Maryam taso ta tafi da Maryam ɗin Abba abun ya faskara saboda irin matakan tsaron da Marwan yasa agurin, tunowa tayi da Auzubillahi mishshaiɗanirrajim da Abba ya koya mata aykuwa tana ambata, ta tofa wa gurin cikin ikon Allah ta saɓi Maryam a kafaɗarta cikin sa’a ta fice daga cikin kogon dutsen. Wani irin shock Marwan yaji take gabansa ya yanke ya faɗi tunowa yayi da fitar Faizuka, ko sallama baiyiwa su Jalbalsikagu ya tashi ya fice daga gurin, da gudun gaske yake lulawa ta cikin gajimare, yana zuwa bai sauka a ko’ina sai cikin kogon dutsen da ya ajiye Maryam, tun bai ƙarasa ciki ba ya hangi gefen ƙoramar naci da wuta, cikin wata irin sufa ya faɗa ciki amma ga mamakinsa sai gani yayi gurin wayam babu Maryam babu alamarta, wata irin ƙara kwarma harsai da gaba ɗaya nahiyar ta ɗauka cikin ƙaraji yake faɗin, ” Maryaaaaaaammm ” amsa kuwwar bata tsaya iya inda yake ba harsai da ta ƙarasa wajen da su Maryam suke, cikin matsanincin faɗuwar gaba Maryam aljana ta kuma ƙara kaimi tana tsoron kar Marwan ya cimmusu, cikin tsananin ɓacin rai Marwan yayi wata irim girgiza atake ya rabe gida huɗu kowanne Marwan da hanyar da yabi ta gabas, yamma, kudu da arewa aƙoƙarinsa na cimma burin kamo Falzuka da Maryam, cikin ikon Allah su Maryam suna daf da ƙarasowa hartaxo daidai saman gidan tana niyyar sauka taji saukar wani irin bahaggon duka atsakar kanta, jiki asake ta saki Maryam ita ɗinma faɗuwa tayi yaraff tana jan numfashi da ƙyar kanta na wani irin azabar zafi.+
Tun bayan fitar Maryam su Abba na zaune gani yayi shirun bazai kaisu ko’ina ba, tashi yayi ya ɗauko Mp dinku ya saka karatun Alkur’ani tun daga suratul baƙara, wannan karatun shi ne yasa suka farajin nutsuwa azuciyarsu, saboda wani irin tsoro ne ya addabesu ya mamaye zuciyarsu cikin ikon Allah sannu a ahankali suka fara jin komai na warware musu, Abba wayarsa ya ɗauka ya kira ƴan uwansa ya sanar musu da duk halin da suke ciki, cikin damuwa suka ce masa suna nan tafe zasu zo.
Abba na zaune gaba ɗaya abun duniya ya isheshi da ƙarfin gaske yaji ƙarar faɗuwar abu, ta maza yayi ya leƙo ta window ganin Maryam da Maryam kwance yasa shi farin ciki abangare ɗaya kuma yana jin tsoron halin da suke ciki, jiki a sanyaye yasa ƙafa ya fito Umma na daga window tana leƙensa, rasa gane Maryam ɗinsa yayi aciki ahankali yaga Maryam aljana jikinta na tsagewa tana motsi da ƙyar, dago da kanta tayi agalabaice tace wa Abba, ” Abba ga Maryam nan na dawo muku da ita ayanxu bani da wani ƙarfi da zan iya cigaba da taimaka muku dashi, ku kula da ita sosai saboda Yanzulak ya wuce duk inda kuke tunani yana iyayin komai akan Maryam karku kuma sakacin da zai samu damar ɗauketa, Yanzulak ya nakastani bansani ba nida ku ko zamu kuma haɗuwa saboda nasan sai ya ɗauki fansa akaina tunda na wargaza masa shirinsa, ku yafemun idan akwai abinda nayi muku nasan muddin na bar gurin nan abu ne mai wuyar gaske idan bai gama wargaza rayuwa ta ba ” ba Abba ba hatta Umma dake jikin window hawayene ya ciko idanunta cikin jimami da rashin jin daɗin abinda ya faru da Maryam Abba yace, ” karki damu mu baki mana komai ba kuma shigowarki cikin rayuwarmu alkairi ce, amma ki sani mutuwa da rayuwa duk suna hannun Allah Marwan bai isa ya miki abinda Allah bai miki ba, inasan ki riƙe addu’o’in dana koya miki da kyau, wallahi ba shi ba ko dubunsa ne suka taru akanki babu abinda zasu iya aikata miki, daga ƙarshe ina miki godiya bisa ga saida rayuwarki da kikayi akanmu Allah ya ɗoramu akan wannan baƙin mugun azzalumin mu kawo ƙarshen rayuwarsa ” Abba ya ƙarasa maganar yana zubda kwallah, har cikin zuciyarsa jin ƙaunar Maryam aljana yake, ji yake kamar tashi Maryam ɗin ce take magana, ana cikin haka su Baba Ibrahim suka yi sallama jiki ba ƙwari Abba ya amsa musu ganin halin da Maryam ɗin Abba take ciki yasa kowa jikinsa yayi sanyi, saboda asume take batamasan mai yake faruwa ba, gefe suka ja suka tsaya kowa yana ta’ajibi cikin zuciyarsa, Maryam ce ta kalli Abba tace, ” Abba zan wuce inbarku haka Inafatan Allah ya ƙaddara saduwarmu inasan ka dinga mun Addu’a kamar yanda zaka yiwa taka Maryam ɗin ” Abba da tausayin Maryam ya gama rufeshi cikin sanyin jiki yace, ” na miki alƙawari Maryam bazan daina miki Addu’a ba harsai ranar da bana numfashi, kema jinki nake har cikin zuciyata tamkar Maryam ɗin dana haifa, kuma insha Allahu babu abinda zai faru dake sai alheri nima ina miki fatan alheri ” ya ƙarasa maganar hawaye na zubo masa, ita ɗinma hawaye takeyi jiki a sake ta yunƙura ta tashi tana layi da ɗan ɗingishi ta keta ta jikin bango ta wuce, Umma ma hawayen ta goge lokaci ɗaya taji ta daina tsoron Maryam ɗin wata irin ƙaunarta taji na ratsa cikin jikinta.
Da mamaki su Baba Ibrahim suka bi Abba da kallo suna leƙensa musamman da suka ga wani guri yake kallo daban yana surutai yana ambatar sunan Maryam, bayan yayi sallama da Maryam Baba Idirs ne ya kalleshi yace, ” kai Umaru wai surutan me kakeyi haka ne? Ko kaima sun fara taɓa ka ne tunda muka shigo muka sameka kanata surutai kai kaɗai alhalin ga halin da yarinya take ciki ” Abba ne ya kallesu sannan ya zayyane musu da wacce yake magana da abinda ya sameta ta sanadiyyarsu, sosai suma suka tausaya mata suna mata fatan samun lafiya, Baba Jamilu ne yace, ” Yanxu ba surutu zamu zauna ba sai mu wuce mu kaita gurin masu ruƙiyya ina ganin hakan yafi ay ” gaba ɗaya da shawararsa suka amince da farko Umma fir cewa tai bazata zauna agida ita kaɗai ba kar wani abun ya sameta, sai da suka dinga mata wa’azi da nasiha sannan ta kuma samun nutsuwa ta yarda suka ɗauki Maryam suka sa amota, kai tsaye MUNAUWARA ISLAMIC CENTER suka wuce da ita cikin karramawa aka karɓi Maryam aka shiga da ita wani ɗan madaidaicin ɗaki.
Abinda ya dakatar da Marwan daga ɗauke Maryam yaso lokacin da bigi Maryam aljana akai ya samu damar ɗauke Maryam, amma jin wani irin azababben zafi na shiga jikinsa yasa ya dakata yaja baya har suka faɗa tsakar gidan, duk yanda ya dinga so ya leƙo koda ta ƙarƙashin ƙasa yaɗauke Maryam ne abun ya faskara yana tunkarar gidan wuta ke lasar jikinsa saboda karatun kur’anin da Abba ya kunna, jin zasu tafi da Maryam wani guri yasa yaji daɗi atunaninsa ta nan zai samu damar ɗauketa, amma ina Baba Idris shi ya kuma kunna karatu awayarsa har suka ƙarasa cen.
Mlm Abdurrahaman shi ne malamin da yake yiwa duk wani wanda aka kai ruƙiyya gurin sai kuma yaran sa biyyar da suke taimaka masa, bayan shigar da Maryam ɗakin da ƴan mintuna ya shiga ɗakin hannunsa ɗauke da wani ruwan magani ajarkaLokacin da ya shiga ɗakin Maryam na sume bata san ma waye akanta ba, daga gun da take kwance ya samu ruwan dake cikin jarkar ya zuba ahannunsa, da bismillah abakinsa ya fara yayyafa mata har a fuskarta, ahankali ta fara mutsu-mutsu tana motsi ganin haka yasa Mlm Abdurrahman yayi a’uziya sannan yafara karatu yana cikin yi mata karatu wani yaronsa ya shigo da kaskon wuta anzuba habbatussauda aciki lokaci ɗaya hayaƙin ya tirniƙe ɗakin, bayan ɗan lokaci kaɗan fita yayi da kaskon saboda kar hayaƙin yayi yawa har wannan lokaci Mlm bai tsagaita da karatun ba kuma har lokacin Maryam bata yi magana ba sai dai ja ta baya da takeyi tana ƙoƙarin guduwa, ya shafe kusan minti talatin akanta amma fir taƙi tayi magana, leƙawa yayi yasa aka kawo masa wani ruwan addu’a acikin wata jarka haɗe da wani turare aciki wata ƴar kwalba, bismillah yayi ya fara ɗiban ruwan yana watsa mata sannan ya shammace ya shafa turaren ahannunsa yana shafe mata shi afuska da kanta, wata irin ƙara ta kwallar mai ƙarfin gaske, lokaci ɗaya jikin ta ya fara wata irin karkarwa, Mlm na ganin haka ya fara tambayarta, ” wanene ko kuma wacece? ” awahale Marwan ya fara magana, ” gasmundadu kilbansika wartafansiku mankasu ” ( ni ne ka daina karatun nan mai kake so inyi maka amma ka daina kona ni) ” Malam tsawa ya buga masa yace, ” Hausa nake san kayi mana ba wannan yaren ba ” Marwan sauke wahallan numfashi yayi yace, ” nace maka nine ɗan sarkin masarautar GADBASGAJI mai kake so dani? ” Malam yace masa, ” Mai yasa ka shiga jikin baiwar Allah nan har ka aureta bayan kasan ba jinsinka bace? ” Marwan jim yayi yaƙiyin magana, ganin haka yasa Malam ya cigaba da karatu haɗe da watsa masa wannan ruwan na hannunsa, cikin ƙaraji Marwan yace, ” dan Allah kayi hakuri zanyi magana ” Malam yace, ” inda kasan da Allah ayda baka cuci yarinyar mutane da iyayenta ba, muna jinka maiyasa ka shiga jikinta har ka aureta? ” Ajiyar zuciya Marwan ya sauke sannan yace, ” Na shiga jikinta ne tun shekaru goma sha shida baya da suka wuce alokacin tun batafi shekara uku ba aduniya, amma bansamu gurbin zama ajikinta ba saida ta fara zama budurwa lokacin zatayi shekara goma zuwa sha ɗaya aduniya ” shiru Marwan yayi yana sauke numfashi da ƙyar.+
Malam ne yace, ” a ina ka samu damar shiga jikin nata kuma garin yaya ka samu har ka aure ta? ” Marwan ya cigaba da magana, ” tana shekara sha ɗaya na shiga jikinta amma aurenta ba haka nan na aureta ba Mahaifiyarta da kanta ita tabani aurenta da bakina da nata ta gaya mun haka kuma har sadaki na ɗauka na bawa Mahaifiyarta ta karɓe”.
jinjina kai Malam yayi yace, ” kai ka taɓa ganin inda akayi aure tsakanin aljani da mutum banda zalinci da shiga haƙƙi ba? ” Marwa babu ko kunya yace, ” gashi mu munyi kuma harda rabo a tsakani ” Malam cikin jin haushi yace mai zaka fita daga jikinta ko sai na ƙone ka ” Marwan yace, ” gaskiya Malam bazan fita ba hasalima duk duniya banga wanda ya isa yasa ni inrabu da Maryam ba aure ne na nema anbani kuma har sadaki na biya meye aibuna? ” Malam naji haka bai kuma tankawa Marwan ba haka ya cigaba da karatu ba ƙaƙƙautawa, tun Marwan na dakewa har takai ga ya ya fara ihu yana neman agaji, bayan Malam ya tsagaita da karatun muryace yaji ta sauya kamar ta dattijai, cikin halin dattako dattijon kakan nasu ya fara yiwa Malam magana, ” Salamu alaikum malam barkanka da wannan lokacin ” Malam amsa masa yayi da, ” wa’alakas Salam dawa nake magana? ” Dattijon ne yace, ” kana magana da kakan Yanxulak wato Jalbalsikagu wanda a jinsinku yana nufin Ibrahim khalil, naji duk abinda yake faruwa tsakaninku da jikana amma ina neman masa afuwa kayi hakuri karka ƙoneshi ” Malam cikin mamaki yace’ ” kar inƙonashi inbarshi ya cigaba da cutar da ƴar mutane? ” Ibrahim khaleel ya amsa, ” ba nufina kenan ba ina nufin ka bani ƴar dama inasan nayi magana dashi akan ya janye bakarsa game da yarinyar nan dan Allah dan Annabi kamun wannan Alfarmar ” jim kaɗan Malam yayi sannan yace, ” yaci darajar Allah da Annabi Muhammad S.A.W da ka haɗani dashi zan baku zuwa nan da anjima muddin naji bai ƙyale yarinyar nan ba babu abinda zai hana imƙoneshi, sai ku dinga haɗa mutane da Allah da Annabi kamar kunsan darajarsu ” aɗan hassale kakansu Marwan yace, ” Dan Allah dakata ban nemi alfarma gurinka dan kaci zarafina ba kana ganin bil adam ne kawai suke cikin addinin musulunci ko kana ganin mu bamusan Allah da Manzan sa ba? akwai mu da dama da mukafi wasu daga cikin bil adam ɗinku riƙo da addini, ni nan da ka ganni cikakken musulmi ne haka iyayena da kakanni na matata ce ba musulma ba sai wasu daga cikin zuriyata da Allah ya nufa basu da rabon shiga wannan addinin, dan Allah kudaina mana kuɗin goro kuna mana kallan marasa adalci ” Malam amsa ya bashi, ” na fahimceka kuma na karɓi uzurunka ina sauraonku zuwa nan da anjima ” Ibrahim khaleel ya amsa da, ” Nagode insha Allah zaka same ni mai cika maka alƙwari ” yana gama faɗin haka Maryam ta yanke jiki ta faɗi tana sauke numfashi da ƙyar.
_WASA FARIN GIRKI_🤣
Kallan gurin take yi gaba ɗaya kanta ya juye da idanu take bin Malam da kallo lokaci ɗaya kuma Marwan ne ya faɗo mata azuciya, da sauri ta fara ja da baya atunaninta shi ne ya sauya kamanni, ahankali Malam ya fara takowa inda take yana furta mata, ” sannu ” ƙin amsawa tayi sai binsa take yi da mugun kallo ganin halin da take ciki na tsoro yasa Malam ya juya ya fice daga ɗakin, duk abinda yake faruwa su Abba na daga jikin wani ɗan window suna kallan ikon Allah, gaba ɗaya ta’ajibi ne ya cika su jin kalaman da Marwan yake furtawa, bayan Malam ya fito bayan sa suka bi, sai da ya zauna sannan yace musu, ” da alama aljanin dake jikin yarinyar nan yan da taurin kai kuma zamuyi gwagwarmaya dashi, amma ya faɗi wasu maganganu da kaina ya kulle, saboda yace uwar yarinyar nan ita ta bashi aurenta da hannunta baki da baki, kuma wai har sadaki ya bata kaina ya kulle sosai duk da nasan akwai makirci irin na shaiɗanu, sukan ajiye kuɗi mutum bai sani ba ya ɗauka amma naji baice ajiye mata kuɗi yayi ba ” jinjina kai gaba ɗaya sukayi cikin tsinkewa da lamarin Marwan, baba Ibrahim ne yace, ” ikon Allah kenan Allah ƙadiran Allah manyasha’u yanxu Malam ya ake ciki ” Malam Abdurrahman bayani yayi musu tiryen-tiryen duk yanda sukayi da Marwan da kakansa, bayan ya gama musu bayanin yace, ” Yanxu kuna iya shiga gurinta saboda ayanda na lura har yanxu tana cikin damuwa da firgici, zan turo akawo mata ruwan shayin magani da ɗan abinci inzata iya ci ” Jikin su asanyaye gaba ɗaya suka wuce suka shiga cikin gurun da Maryam take.+
Maryam da dake zaune agefen gado tana jin sallamar su Abba a tsorace ta kai idanunta gurun, ganin su Abba yasa ta tashi da gudu ta tafi gurunsu cikin kuka ta faɗa jikin Abba tana kuka mai tsuma zuciya, shi kansa Abba daurewa yayi amma yana jin kukan Maryam yake har cikin zuciyarsa, sai da tayi mai isarta sannan ta fara magana, ” Abba dan Allah ku ɗauke ni mu tafi gida kar Marwan ya ƙara ɗauke ni, Abba Marwan ba Mutum bane shi ne ya saceni dan Allah Abba karku bari ya ƙara ɗaukata ” gaba ɗaya tausayinta ne ya kamasu, Baba Idris ne ya riƙo hannunta yace, ” karki damu ƴar baba bazai ƙara ɗaukeki ba insha Allah munzo gurin da za’a kawo ƙarshenshi ” Maryam daɗi taji har cikin zuciyarta afili gyaɗa musu kai tayi tana goge hawayenta, Huzaifa ne ya shigo da kofin tea ahannunsa miƙa musu yayi sannan ya juya bayan wani lokaci sai gashi da plate ɗin Abinci ya kuma kawo mata, ahankali ta fara kurba shayin tana cin abinci baifi cokali huɗu tayi ba tace ta ƙoshi, ruwan tea ɗin tasha sai alokacin taji daɗin cikinta.
Bayan wasu awanni Malam ne ya kuma dawowa kan Maryam da turare yana sake mata ruƙiyya wannan karan Ibrahim khaleel kakan Marwan ne ya bayyana, bayan sun gaisa ne Malam ya jefo masa tambaya, ” Malam Ibrahim ya kukayi da jikan naka shin zai bar jijin nata ko kuwa? ” gyaran Murya Kakan Marwan yayi sannan yace, ” akaro na biyu ina mai ƙara neman alfarma agurinka yakai wannan Malami mai adalci, har yanxu ina nan ina neman shawo kan yaron nan amma abun ya ta’azzara dan Allah ka ƙara min wannan alfamarmar zuwa nan da safiya indai gobe tayi yaron nan bai ƙyale yarinyar nan ba naji na yarda na lamince duk abinda zakuyi masa kuyi masa, idan ƙoneshi zakuyi ku ƙoneshi idan ma kasheahi zakuyi duk kuyi yanda zakuyi ” ba haka Malam yaso ba Amma ganin irin sigar da Kakan Marwan yaxo masa da ita cikin mutumci da girmamawa yasa Malam yace, ” Lallai wanna jikan naka yaci darajarka amma wallahi ba dan kai ba da babu abinda zai hana ingama dashi ayau ɗin nan, amma babu komai Allah ya kaimu yau da gobe duk ɗaya ne agurin Allah ” cikin jin daɗin Kakan Marwan yace, ” nagode ƙwarai da wannan karramawa taka gareni, kuma kasan ɗan yau ne ka haifeshi baka haifi halinsa ba kamar yanda kuke fama da yaranku na zamani muma haka muke fama dasu Allah dai ya shirya mana su bisa tafarkin addinin islama ” Malam murmushi yayi yace, ” Aameen, ashe kowanne jinsi suna da tsageru ƴan zamani? ” Kakan Marwan yace, ” sosai ma ay ƙarshen duniya ne yazo ” Malam yace, ” to Allah kyauta ina saurarenku zuwa nan da safiya ” Kakan Marwan yace, ” To Allah ya kaimu ” daga haka suka yi sallama gaba ɗaya.
Malam ne ya samu su Abba ya fara musu magana, ” har yanxu yaron yana kan bakarsa amma kakansa ya kuma neman alfarmarmu zuwa safiya, to kuma dan ina ganin mutumcin tsohon ne amma da tuni na gama da shi ” maganganun Malam ba ƙaramin faranta musu rai sukayi ba, da ɗan ƙwarin gwiwa atattare dasu suka ce, ” to ba komai Allah ya nuna mana goben lafiya ” Malam ya amsa da, ” Ameen ” da ƴar damuwa afuskar Abba ya kalli Malam yace, ” Malam yanzu zuwa safiyar bazai kuma dauke ta ba ko? ” Murmushi Malam yayi yace wa Abba, ” haba wane shi ƙaryarsa aytasha ƙarya dashi da duk zuri’asu inda zasu taru basu isa su ɗauketa agurin nan ba ” hankalin Abba ne ya kwanta sanna yace, ” to Alhamdulillah ” har zasu fita Malam ya kira su yace, ” Yauwa dama abinda nake san sanar daku, ku kira Mahaifiyar yarinyar nan ta zo ta zauna da ita ko kuma wata macen dai saboda jinyar mace dole sai mace ” cikin gamsuwa da Maganarsa suka amsa masa sannan suka fice daga gurinsa. Su Baba Idris ne suka zauna da Maryam Abba kai tsaye gida ya wuce lokacin da yaje Umma na tsakar gida azaune duk tayi firƙai-firƙai, tana jin sallamarsa da sauri ta tashi bako amsa sallamar ta fara jero masa tambayoyi, ” Malam ya ake ciki ta farfaɗo? ” ajiyar zuciya ya sauke yana jingina da bango sannan yace mata, ” ta farko, ki haɗa ƴan kayanki da nata ko kala bibbiyu ne saboda ba yau zasu sallameta ba ” Umma najin haka da sauri ta faɗa ɗaki gaba ɗaya jikinta yayi sanyi da lamarin Maryam, bata ɗauki lokaci ba ta fito tsaf cikin shiru, sallahun girkinsu ta barwa Mustafa su kansu yaran gaba ɗaya basa cikin walwala tunda suka ji matsalar da ƴar uwarsu take ciki, Umma da Abba hanyar Munauwara Islamic Center suka kama dake unguwar Briget bakin sabuwar kasuwa.
Umma ba ƙaramin daɗi taji ba musamman da ta samu Maryam ido biyu har tayi mata magana, cikin zuciyarta har taji ƴar nutsuwa, sai dai aɓangare guda kuma inta tuno da labarin da Abba ya bata na cewar wai itace tabawa Marwan auren Maryam, sai taji ta shiga cikin ruɗani da tashin hakali musamman da yace bazai fita daga jikin Maryam ba, afakaice Umma take goge hawaye gaba ɗaya jinta take wani iri.+
*WASHEGARI*
Kimanin ƙarfe 10:00 na safe Malam Abdurrahman ne ɗauke da wasu irin turarurruka da wasu jarkuna ahannunsa, sai yaransa dake ɗauke da kaskon turaren wuta da habbatussauda, da Sallama ya shiga cikin ɗakin lokacin tuni Abba ya ƙaraso shi da Umma suna zaune suna ɗan ɗebewa Maryam kewa, bayan sun gaisa Malam ya buƙaci da su fita su bashi guri amma idan suna da sha’awar gani suna iya tsayawa ta jikin window, ba musu suka tashi suka fice Abba da Umma kan bencin dake jikin window suka zauna, hayaƙin Habbatussauda ya farayi mata sannan ya miƙa mata roba ɗaya yace ta karɓa tasha, ba musu ta karba ta farasha bata jima ba da sauri ta cire robar abakinta tana huci, cikin zafin nama Malam ya karɓe robar sannan ya rufe, wani turaren kwalba ya ɗiga akan garwashi sannan yayi bismillah ya fara mata ruƙƙiya, tun baiyi nisa ba Maryam ta fara fita daga hayyacinta, Malam ya jima yana karatu ya kusa minti ashirin yana abu ɗaya amma ko gezau Maryam taƙi magana, cikin azama ya ƙara kaimi haɗe da yayyafa mata wani ruwan Addu’a dake cikin wani galan.
Cikin wani irin ƙaraji da kuwwa Marwan ya taƙarƙara ya ƙwalla wata irin ƙara saboda azabar da yaji, Malam ne ya fara tamabayarsa, ” yaya zaka fice daga jikin baiwar Allah nan ko sai na ƙoneka? ” Marwan dake sauke numfashi da ƙyar ya fara magana, ” ka tsaya ka saurareni Malam idan ka tilastani na fita daga jikin Maryam ba’amun adalci ba, saboda Maryam matata ce na ɗau tsawon shekaru ajikinta yanxu rana tsaka ace sai na rabu da ita? ” ahasaale Malam yace masa, ” ba hira nace kamun ba tambaya ɗaya nayi maka zaka fita ko bazaka fita ba? ” Marwan shiru yayi ganin haka yasa Malam ya cigaba da karatu ba ƙaƙƙautawa, sai da ya kumajin azaba sannan ya cigaba da cewa, ” ina da magana malam kamun rai inada magana ” jinkirtawa Malam yayi yace, ” inajinka ” Marwan ne ya cigaba da magana, ” Malam naji zan fita daga jikinta amma tana nan amatsayin matata tunda na riga na biya sadaki na ” cikin jin haushi Malam yace, ” gayamun sanda ka bada sadakin nata da kake ta ikirarin matarka ce har sadaki ka biya ” Marwan daɗi yaji da jin wannan maganar ta Malam, da ƙwarin gwiwa ya cigaba da cewa, ” Nagode da ka bani wannan damar Malam ” Malam cikin ƙaguwa yace, ” ina jinka.”
_” Bayan shekara goma sha shida baya, wata rana ranar laraba da daddare ina kwance ina hutawa saboda ranar acikin nishaɗi nake, sai gani nayi Maryam da Mahaifiyarta sun shigo banɗaki gurin da nake kwance, da sauri na matsa gefe na basu guri alokacin Maryam batafi shekara Uku ba, akan ido na Mahaifiyarta ta watsa mata ruwa dake lokacin, lokacin zafi ne alokacin sai yanayin hallitar yarinyar ya birgeni acikin zuciyata har nake cewa dama bil adam tun suna yaransu haka Allah yayi musu sura mai kyau, bayan sun fice sai nabi bayansu har Mahaifiyarta ta gama shiryata ta kwantar da ita kwanciyar bacci, cikin birgewa nabi gefe ina ƙarewa halittar yarinyar kallo kai daga ƙarshe ma sai nabi gefe nayi zama na abina, ina nan zaune sai mahaifinta yaxo lokacin da zai kwanta sai ji nai yana addu’a wani irin zafi mai hucin wuta na lasata azabure na tashi na fice daga ɗakin, wannan shine mafarin tsanar da naji na fara yiwa mahaifin Maryam arayuwata, duk yanda naso na kuma komawa ɗakin abun ya gagara akan dole na hakura har zuwa washegari, haka nan ma da safe da zata kuma mata wanka anan banɗaki muka kuma haɗuwa har ta gama mata wanka ta fice, to tun daga ranar sai ya zamana bani da gurin zama sai gidan su Maryam ina bibiyar duk lamarinta, amma idan mahaifinta na gida bana samun gurbin zama agurinta, ana cikin haka sai Mahaifinta ya yi tafiya ya koma gurin neman kuɗinsa, tunda ya tafi na sami dama nake kwanciyata agurin Maryam, kai da naji shaƙuwarmu ta kara yawa sai nake ɗauke ta idan dare yayi inbarwa mahaifiyarta jabunta, sai inkaita cen gidana dake cen duniyarmu, idan gari ya waye ta tashi daga bacci sai inzuba mata kayan more rayuwa na wasanni da zai ja hankalinta, inzauna inta kallanta tana wasanni cikin birgewa, gabda lokacin da Mahaifiyarta zata tashi sai na maida cen kafin wani daren._”Haka nake yi kullin har ya zame min jiki ba dare ba rana ina tare da Maryam, mun shaƙu da ita sosai saboda daga baya har bayyanar mata nake yi nayi ta jan ra’ayinta ina mata wasanni, sai ya zamana mun saba da ita idan ma na ɗauket ko ta tashi bata cika damuwa ba saboda ina ajiya mata kayan da zasu ja hanklinta, haka nayi tayi yau da daɗi gobe babu saboda duk lokacin da mahaifinta ya dawo gari tofa bani da sauran walwala, alokacin da ta fara wayo ta fara gane abubuwa kuma tayi baki sai na daina ɗaukanta na kuma daina buɗe mata ido, saboda nasan yau da gobe idan ta faɗawa iyayenta zasu ɗauki mataki, sai nake binta ta bayan fage ina bibiyar duk al’amuranta.”_
_” Tana ƙara zama budurwa kyau da ƙirar hallitarta na ƙara cika alokacin sai na sameni da jin wani irin kishinta, bana san naga wani mutum ɗaya ya raɓeta koda ba da kalmar soyayya bace, mafarin fara nisantani da Maryam dawowa mahaifinta kano da neman kuɗi, agaskiya ya kawo mun matsala Sosai saboda kusan kullin sai ya karanta suratul baƙara, nikuma banaso saboda hanani shigowa gidan yake gaba ɗaya, sai na zamana ina laɓe ina bibiyar lokacin da Maryam zata fita tana fita nake maƙale mata har taje inda zataje ta koma gida, sai dai idan islamiyya zataje ne bani da damar binta saboda cen ma kusan ƙonani suke idan naje, ahankali sai na fara cirewa maryam da mahaifiyarta ra’ayin karatun addini kwata-kwata duk da dama mahaifiyarta bata damu dashi ba, amma dake mahaifinta tsayayye ne sai abun bai yuwu ba, duk wannan abun da yake faruwa babu wanda ya sani daga cikinsu sai ni kaɗai nake kiɗana nake rawa ta, alokacin da ta cika shekara goma sha uku ta zama budurwa ba laifi sai wata irin soyayyarta ta shigeni mai tsananin gaske, sai nayi tunanin cewa mai yasa bazan aureta ba kawai, naso na aureta tun alokacin amma da kakana yaji abinda nake shirin aikatawa, sai yace mun muddin na aureta to babu ni babu sarauta, wannan dalilin ne yasa na jinkirta na haƙura. “_+
_” lokacin da ta cika shekara goma sha biyar wata rana ita da Mahaifiyarta da kannenta sun shirya zasuyi tafiya zuwa garin doguwa, ina ganin motar da suka shiga nima na rikiɗa zuwa surar matashin saurayi, kujerar baya su umma suka zauna kuma kujera uku suka ɗauka, ina zuwa nayi zamana agurin da ya rage, bayan zamana da wani ɗan lokaci sai motar ta cika, mun fara tafiya ba daɗewa sai kwandasta ya buƙaci afara bada kuɗin mota, inajin haka na zaro kuɗi na miƙa masa nace na biya mana harsu gaba ɗaya, Umma har ta miƙa kuɗi sai yace mata na biya musu tana jin haka sai ta fara mun godiya cikin jin daɗi, sannu ahankali muna tafiya nake ɗan jan Maryam da hira, ayanda na lura azahiri tana da kamun kai dan sam taƙi sakin jiki da ni muyi hira yanda nake so, na daɗe da sanin mahaifiyarta nada san abin duniya ganin ban samu fuska agurinta ba sai na zaro kuɗi ina tunanin alokacin dubu goma ne, na miƙawa mahaifiyarta nace mata gashi suyi tsaraba da murnarta ta karɓa tana ƙara jadadda mun godiyarta, wannan kuɗin dana bata sai ya buɗemun kofar hira tsakanina da Umma har take sanar dani zata je gaida iyayenta, nima sai na nuna mata kamar ziyara zankai gun wani abokina acen garin doguwa. “_
_” Muna cikin wannan hirar sai na jefo mata tambaya, ” nikuwa ina kamun yarinyar nan taki ko zaki bani aurenta? ” babu ko gezau Umma tace mun, ” mai zai hana indai kana so zan baka aurenta ” tsuke fuska naga Maryam tayi uffan dama bata tofa mana ba daga cikin hirarmu, har wani mutum dake kujerar gabanmu ya jiyo yace mun, ” Abokina kai ka shigo motar a sa’a gashi har ka tsinci dami a ka la” cikin murmushi nace masa, ” ay haka Allah yake ikonsa ” itama Umma dariyar tayi banda Maryam da kamar jin haushin hirar tamu take ji, cikin jindaɗi nace mata sai na kuma ce mata, ” amma fa ina biyan sadaki aure fa ya kamallah kin amince ? ” Umma batayi nazarin maganata ba kawai ta amince ta amsa nima kuma banyi wata-wata ba na zaro kuɗi dubu hamsin na miƙawa Umma, naso na biya yafi haka amma gudun kar zargi ya shiga tsakaninmu sai na bada dubu hamsin ɗin, Umma hannunta har rawa yake tasa hannu ta karɓe cikin jindaɗi tace, ” Saurayi gashi ko sunanka bamu sani ba? ” murmushi nayi nace, ” sunana Yarima “_” Cikin washe baki Umma tace, ” Yarima fa wannan ay sunan sarakai ne ” nima murmushi nayi nace mata, ” eh kowa haka yake cewa ” daga nan hira muka cigaba dayi har wasu daga cikin ƴan cikin motar suna ɗan sako mana baki, tafiya mukayi mai ɗan nisa har muka ƙarasa garin doguwa, kwandasta ne yayi shelar sanar da zuwanmu doguwa muna da ɗan yawan gaske muka dinga sauka, bayan saukarmu mutane kowa kama gabansa yayi cikin zolaya na kalli Maryam nace mata, ” To Amaryar sai anjima ” ko kallan gurin da nake batayi ba, da haka mukayi sallama da su Umma cikin kewar Maryam na tafi ina ƙarajin wani irin nishaɗi na ratsa zuciyata, tafiyarsu keda wuya na ɓace daga gurin na cigaba da binsu har cen cikin garinsu, koda Umma taje bata sanarwa da kowa inda ta samu kuɗinba hasalima bata gayawa kowa tana da kuɗi masu yawa ahannunta ba, sai bayan ta dawo gida ta killace su acen ƙasan kayanta sai ta shiga adashi sannu a hankali har ɗauka taxo ta kwasa, bayan ta ɗauka sai ta haɗa da wannan kuɗin dana bata taje cen garinsu ta sayi gonaki, wannan labarin da nake baka ko Mahaifin su Maryam bai sani ba saboda tun ahanya ta ja kunnenau ta tsoratar dasu akan kar wanda suka gayawa wani ya bata kuɗi.”_1
_” Ranar da abin nan ya faru wuni nayi cikin farinciko da jindaɗi, tun daga ranar sai na maida Maryam kamar matata haka zanje gurinta intana bacci inyi kwanciyata kusa da ita abina har ta kuma girma ta mallaki hankalin kanta, lokacin da ta zama budurwa sai ya zamana wani lokacin zama na kusa da ita ya ɗanyi ƙaranci saboda tana zuwa islamiyya karatun da takeyi sai yake nisantani da ita, da naga haka sai na sake salo na fara shiriritar da ita har nake sa mata mantuwa, tanan na kuma samun galaba har na sakankace da ita, tashin farko iyayena sukaji maganar aurena da Maryam alokacin tuni andaɗe da mun baiko da wata ƴar uwata Madishshila, ransu ne ya ɓaci sosai da jin abinda nayi ba tare da saninsu ba, wani ƙarin takaicin kuma da na bijire musu nace sam ni bazan auri Madrishshila ba saboda tamun tsufa kuma ni banida ra’ayin auren zumunci, ansha gwagwarmaya dani sosai akan auren Maryam tun suna fishi dani har suka sauko muka dawo da hulɗar da kowa kamar da, lokacin da Maryam ta ƙara zama budurwa wata rana sai naji Umma na yiwa Abba maganar nemarwa Maryam maganin farin jini saboda ita babu mutum ɗaya da ya taɓa zuwa gurinta da sunan yana santa, inajin haka sai nayi tunani kar daga neman maganin farin jini azo ace musu jinnu ne ya aureta, sai nayi farat na sake salo dan ina ganin idan nayi sake kamar lokacin tonuwar asirina ne yayi, dukda dai naji mahaifinta baiyi na’am da maganar ba.”_
_” Bayan maganar Umma da kwana biyu wata rana da daddare sai na rikiɗa na koma surar wani matashin saurayi daban ba wancen va, yaro na samu aƙofar gidansu na tura shi nace yaje yace ana sallama da Maryam, bayan shigarsa da wasu mintuna sai ya dawo yace tana zuwa, da sallama abakinta ta ƙaraso gurina cikin nutsuwa ta gaisheni sai dai gaba ɗaya yanayinta shi zai nuna maka cewa awannan fannin ita farin shiga ce, sannu ahankali na fara gabatar mata da kaina, ” da farko dai sunana MARWAN, Maryam nasan baki sanni ba ƙilama baki taɓa gani na ba, amma ni nasanki nasan nutsuwarki da kyawawan ɗabi’unki, hakan ne yasa na yaba da hankalinki naji ƙaunarki ta ɗarsu azuciyata, ina fatan zanji makamancin haka daga gareki? ” murmushi tayi tana rufe fuskarta cikin jin kunya tace, ” to amma ka bari nayi tunani tukunna ” nima murmushi nayi saboda komai na Maryam yana birgeni kallanta nayi nace, ” to ba komai na baki zuwa nan da gobe kiyi shawara ” aɗan hanzarce ta kalleni tace, ” kai gaskiya gobe yayi wuri ina laifinma jibi ” ina shirin bata amsa sai ga mahaifinta ya ƙaraso gurin, tsayuwarsa kawai da na gani sai da gabana ya faɗi, amma haka nayi ta maza na maze na russuna har ƙasa na gaisheshi, inajin alokacin da ya lura dani sosai zaiga tashin hankalin da na shiga amma dake bai daɗe agun ba na tabbata bazi gane ba, bayan shigar Abba gida Maryam kallona tayi tace, ” zan shiga gida Abba ya dawo ” ba musu haka mukayi sallama da ita ta wuce ciki nima nayi tafiyata.”_
Ajiyar zuciya Marwan ya sauke Malam ma dake tsaye yana ji daga gun Marwan shima ajiyar zuciyar ya sauke sannan yace, ” Lallai Marwan ka tabbata cikakken hatsabibi, ashe dama ka jima kana cutar da ƴar mutane da iyayenta, to ay naji Mahaifinta yace ka tura iyayenka har kuɗin aurenku sunkai ya abun yake? “
Jinjina kai Marwan yayi ya cigaba da cewa, _” Tabbas na tura iyaye na kuma da ƴan uwan Mahaifin Maryam suka ji maganar sun buƙaci suyi bincike, kuma sunyi saboda har unguwar da nace musu cen nake da iyaye na sunje.”__” Bayan zuwa na da kwana kwana biyu sai na ƙara komawa wannan karanma yaro na tura na sa Akamun sallama da ita, bayan wani lokaci sai ga Maryam ta fito cikon shiga ta mutumci sanye da hijabi, sallama tamun muka gaisa bayan mun gaisa na kalleta nace mata, ” Barka da dare Queen ina fatan na sameki lafiya? ” murmushi tayi akunyace tace, ” lafiya klau ” gyara tsayuwa ta nayi nace, ” ke nake saurare wane hukuncin kika yanke? ” cikin nutsuwa ta fara magana, ” ranna bayan na shiga gida mahaifina ya tambayeni waye kai kuma inane unguwarku, to na sanar dashi iya abinda na sani game da kai wanda ka sanar dani ” lokacin da ta ambaci sunan mahaifinta gabana sai da ya faɗi haka zalika naji ba daɗi sosai amma dan karta fahimci wani abu sai nayi yaƙe nace mata, ” aydama duk uba na gari zaiso yasan waye yake zuwa gurin ƴarsa kuma ya tarbiyyarsa take, amma kuma baki bani amsarki ba ” ɗan sunkuyar da kanta tayi ahankali tace, ” na amince ” kafeta nayi da ido nace, ” kin amince dame? ” shiru tayi tana murmushi saboda ta lura zolayarta nakeyi, daga nan hira muka taɓa bayan wani lokaci ta mukayi sallama ta koma gida, tun daga ranar soyayya ta ɗinke tsakaninmu da Maryam wanda ba ƙaramin jin daɗin hakan naji ba, sannu a hankali na siya mata waya da farko mahaifinta ƙin yarda yayi sai bayan wani lokaci ya amince, hidima dai-dai misali ina wa gidansu Maryam, da na lura Mahaifinya ba mai san adinga yawan bawa ƴarsa kuɗi bane nake yo shopping na cuko manyan ledoji idan zani zance inkaimusu, sai da na kai ruwa rana da Maryam sannan ta fara karɓa acewarta tsoro take kar Abba yayi faɗa, shi ma da yaga irin hidimar da nake musu saida ya taɓa samuna yamun magana yace ɗawainiyar da nake tayi yawa, hakan ne yasa na sassauta wani abun amma fa ban fasa ba, aykuwa nan da nan na mamaye zuciyar Umma tana matuƙar sona sosai fiye da yanda Abba yake sona.”_+
_” Mun ɗan ɗauki lokaci muna soyayyah wata rana kwatsam sai Maryam take cemun Mahaifinta yace baya san yawan zance idan da gaske nake na turo iyayena, banji ko ɗar ba saboda dama tuni na daɗe da shirya plan ɗin haka, cikin farin ciki na kalle ta nace, ” idan na koma zan sanar dasu sai su kawo kuɗin gaisuwa ” ita ma yanda na lura hakan da na faɗa ya faranta mata rai, da murmushi afuskarta ta amsa da, ” to ” Tun daga lokacin na fara yiwa Maryam ɗan abubuwan almara na ban mamaki dan wani lokacin har takance ni ɗan baiwa ne, da farko ta fara tsorata amma kuma tunda ta lura da niɗin maison barkwanci ne da zolaya sai ta ɗauki abun a baiwace da Allah ya bani, sai abunma ya daina damunta sautari zanyi abubuwa da dama amma dake ta saba ko ajikinta, bayan na koma gida sanar da Mai martaba shima na sanar dashi kar daga baya yaji abinda nayi yace baisani ba, amma ni tuni na daɗe baza fadawan mahaifina a unguwar da nacewa Maryam acen nake, gida na kama na sa su, su biyar aciki har ni na shida duk azuwan Mahifina da mahaifiyata sai kannena mata uku, hulɗa muke sosai da mutanen unguwar mun saba dasu sosai kuma kowa ya sanmu da ƙyawawan ɗabi’u, shiyasa ko da nace wa Maryam ta sanar da Mahaifinta za’a kawo kuɗi da yace zasuyi bincike banji ko ɗar ba, ƴan uwan mahaifinta su suka wuce kan gaba wajen bincike a unguwarmu kuma sun samu gamaassum shedoji, bayan kwana biyu da yin bincikensu sai Iyayena suka shirya su wajen shida suka kai kuɗi aka tattauna cikin mutumci da karamta juna, tun daga nan banida wata damuwa ko ɗar tsakanina da Mahaifin Maryam sai akace abari tayi Candy sai atsaida mana da ranar aure, ana shirye-shiryen sa mana rana tsautsayi yasa wata rana da naje zanje gurin Maryam na ɗauketa na kaita cen masarautar mu, saboda yawan damuna da iyayena sukeyi akan na kai musu ita su gani, ni nasan wannan abun da ya faru tsautsayi ne ko ince ƙaddara, saboda tun daga nan ne mafarin faruwar matsala tsakanina da Maryam danma nayi ƙoƙarin rufe bakinta amma dukda haka hakan bai yuwuba, Surunjeet ita na fara turawa azuwan jabun Maryam amma ita dake tana da zafin rai sai bata daɗe ba ta nemi ta bayyana kanta, bayan ta dawo gurunmu sai na tura Falzuka saboda duk cikinmu tafimu hakuri yarinya ce mai sanyi hali ga tausayi, gaba ɗayansu cousin sisters ɗina ne har ita Madrisshila saboda ni mu biyu ne kaɗai agun mahaifina da mahaifiyata daga ni sai ƙanwata Mazbeeta, ita Falzuka itace gaba ɗaya ta ɓata mun shirina ta wargaza mun duk wani ƙulli da nake shiryawa.”_
Dago da kai Marwan yayi yace, ” Malam kaji yanda akayi Maryam ta zama matata ” ajiyar zuciya Malam yayi sannan yace, ” lallai Marwan ko acikin shaɗanun Aljani kai na musamman ne, kai babban hatsabibi ne kuma azzalumi, najima banji mugun mayaudari irinka ba, wannan neman auren naka ay baya daga cikin tsari da koyar addinin musulunci, wai kai Marwan ma banda abinka yaushe rayuwa zata yuwu tsakanin mutum da aljan, ka saurareni da kyau ka jini kayi gaggawar fita daga jikin yarinyar nan idan ba haka ba wallahi sai na ƙone ka yanxun nan ” shiru Marwan yayi sai daga baya yace, ” Malam yanxu duk abubuwan dana gaya maka basu gamsar da kai ba? ” ahassalle Malam yace, ” babu wata hujja ko dalili da zaisa mu kyaleka ka cigaba da cutar da yarinya ” yana rufe baki Malam yayi a’uziya ya fara karatu, gaba ɗaya jikin Abba yayi sanyi Umma duk tayi fiƙi-fiƙi kamar tayiwa sarki ƙarya yasa akamota.Marwan banda kururuwa ba abinda yakeyi saboda azaba amma da Malam ya jinkirta ya tambayeshi zai ce shi fa sam baiga hanyar fita ba, sun shafe mintuna sun atir-tirka akan haka amma saboda taurin kai yaƙi fita, Malam ransa ba ƙaramin maci yayi ba ganin Marwan na niyyar ɓata masa lokaci, wani yaronsa yasa ya ɗauko masa wani turaren miski da ruwan addua ana kawo masa ya fara karanta suratul baƙara yana biyawa yana kwara masa wannan ruwan, daga gefe guda kuma turaren miski yaronsa take yarfa masa, jin wannan azabar tayi yawa yasa Marwan cikin ƙaraji ya fara neman taimako yana zai fita, saurarawa Malam yayi yace, ” Zaka fota ko bazaka fita ba? ” cikin galabaita yace, ” zan fita ” Malam ajiyar zuciya ya sauke yace, ” ta ina zaka fita? ” Marwan na fidda numfashi da ƙyar yace, ” ta ido zan fita ” Azabure Malam yace, ” bazaka fita ta ido ba ta baki zaka fita ” jim Marwan yayi yace sai dai infita ta Ƙafa ” Tsawa Malam ya daka masa yace, ” Bazaka fita ta ƙafa ba ta bakin dai zaja fita ” Marwan shiru yayi yana nazari, jin haka Malam ya zabura har zai fara karatu sai ya fara masa magana, ” dakata Malam karka ƙoneni zan fita ta bakin ” Malam ne yace, ” ina saurarenka ” shiru ne ya biyo baya bayan ɗan lokaci Maryam ce take ta zabga hamma bata jima ba bacci yayi awon gaba da ita, Sharce gumin fuskarsa Malam yayi afili yake faɗin, ” Alhamdulillah alakullihalal ” tashi yayi ya fito ya janyo ƙofar, su Abba mazauninsu kan benci inda suke, ganin fitowar Malam da sauri Abba ya kalleshi yana faɗin, ” sannu da aiki Malam Allah ya taimaka ” agajiye Malam ya amsa da, ” Ameen-Ameen ” wucewa gaba yayi su Umma na zaune gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi, suna nan zaune Sallamar su Baba Ibrahim sukaji bayan sun gaisa suke tambayar jikin Maryam, Umma zumu tayi tana sauraren taji abinda Abba zaice musu, shikuwa Abba dake cike da haushinta kallenta yayi adaƙile yace, ” Ki bamu guri zamu tattauna da ƴan uwana ” sum sum sum haka Umma ta tashi kamar wacce kwai ya fashewa aciki, tana tafe tana ɗan waige har ta ƙarasa ɗakin da Maryam take, Abba duk abinda ya faru tun daga farko har ƙarshe ya basu labari kowa jikinsa sanyi yayi, cikin haɗin baki gaba ɗaya suka furta, ” Allah ya sawaƙe amma abun babu daɗin ji ” suna nan zaune wani yaron Malam yaxo yake ce musu Malam yace bawan wani lokaci zai buƙaci ganinsu akwai, cikin kulawa suka amsa masa da, ” Allah ya kaimu.”+
Bayan wani lokaci Maryam ce ta farka gaba ɗaya jikinta banda tsami ba abinda yake mata kamar wacce akayiwa duka, bayan ta tashi Umma ce ke jero mata sannu ba adadi, jin maganar Umma yasa su Abba suka shiga ciki suna zuwa suka sameta zaune, Baba idris ne yaje ya sanarwa da Malam tashin Maryam tare suka taho bayan ya shigo sannu yayi mata yana kuma tambayarta ƙarfin jikinta, cikin sanyin jiki ta amsa masa da, ” jiki da sauƙi sosai ” cikin jin daɗin yanayin da ya ganta Malam yace, ” To Allah ƙara afuwa ” gaba ɗaya gurun suka amsa da Aameen, wanka ya fara cewa su sata tayi idan tayi wanka sai abata abinci taci ta ƙara hutawa, hakan kuwa sukayi bayan tayi wanka ruwan tea aka bata mai kaurin gaske, sha tayi sannan ta ɗan ci abinci bayan wani lokaci bacci ne ya kuma ɗaukanta, gaba ɗaya iyayen nata suna ciki farin ciki, ganin ta samu bacci yasa suka fice daga gurin suka basu guri ita da Umma.
Malam ne ya vuƴaci ganinsu Abba a office ɗinsa gaba ɗaya suka hallara agurin banda Umma kallansu yayi yace, ” ina Mahaifiyar yarinyar gaba ɗaya nake san tattaunawa da ku ” Abba najin haka ya tashi ya leƙa ta window ya kira Umma, tana jin haka gabanta ne ya yanke ya faɗi jiki ba ƙwari ta tashi ta shigo cikin office ɗin, cen gefen tabarma ta koma ta rakuɓe guri ɗaya ta zauna, kallansu Malam yayi sanna ya fara magana, “Assalamu alaikum yaku ƴan uwa masu albarka, maƙasudin zaman mu anan inaso inɗanyi wani tuni ko jan hankali garemu, Alahayyi-aleen muna yawan sakaki da addu’a wanda ta kasance takobin mumini ce, nasan basai na gaya muku abinda shi wancen shaiɗanin aljanin ya faɗa ba kunji da kunnuwanku, kuma kunji dalilin shigarta jikinta da inda ya ganta kuma har ya shiga jikinta, Annabin rahama ya koyar damu addu’o’i kala-kala babu abinda bamu da addu’arsa, amma saboda sakaci wani lokacin kuma rashin ilimin abin ne yasa muke watsi dasu, Banɗaki da kuke gani nan ne matattarar dukkannin taƙadiran aljanu masu cutar da mutane, musamman ku mata da Allah ya ƙwawata muku surarku, ya kamata mu farka mu gane cewar Azkar shi ne makami na yaƙar duk wani aljani mai niyyar cutar damu, kamar yanda na fuskanta kuma shi da kanshi ya faɗa ya nuna cewar, Mahaifin Maryam na kawo mishi matsala har yaso ya kasheshi amma cikin taimakon Allah da taimakon azkar ɗin da yakeyi sai bai samu galaba akansa ba, saɓanin mahaifiyarta da ita Maryam ɗin da tuni yayi galaba akansu saboda sakacinsu da addu’a, wanna babban darasine kuma izina ce garemu gaba ɗaya, amatsayinki na mahaifiyarta kece keda alhakin kula da duk wasu abubuwa kuma kece keda alhakin nuna mata abu mai kyau da mara kyau, bance Mahaifinta bashi da wannan hakkin ba amma idan mukayi duba da uzurin mahaifi dole wani abun uwa itace zata nazartar da yaranta duba da cewar itace take tare dasu yau da gobe.
Abu na gaba zanyi magana akai shi ne kwaɗayi ko ince san abun duniya, wanda ya zama gama duniya ga yawancin iyaye musamman iyaye mata, basai nace komai kunga yanda san zuciya ya taka muhimmiyar rawa wajen janyo wannan gagarumar matsalar, na tabbat wannan babban wa’azine dani daku baki ɗaya, Allah ya kuma shiga tsakanin nagari da mugu ” Malam na kaiwa nan gaba ɗaya suka amsa da, ” Ameen ” idan ka kalli kowa gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi musamman Umman da take ganin maganganun Malam kamar wata bulaliya ce yayi mata.
Malam ne ya cigaba da magana, ” Insha Allah gobe da safe zan sallameta idan naga yanda jikin nata ya ƙara kyau, sannan ita kanta akwai nasihohin da ya kamata aƙara jadadda mata da jan kunne, abu na ƙarshe da zance muku shi ne, ku dinga yawan kunna karatun alkur’ani da karantashi agidajenku musamman suratul baƙara, wannan babbar kariya da babu shaɗanin da ya isa ya tunkari gidan bare kuma ya nemi cutar daku, Allah ya kuma tsaremu ubangiji ya ƙara karemu baki ɗaya ” Cikin jin daɗin nasihar Malam suka amsa da, ” Aameen ” godiya suka yi masa sannan suka tashi suka fice daga cikin gurin kowa zuciyarsa fes.
Maryam ta jima sosai tana bacci bayan ta tashi jikin ta ne taji ƙwarinsa ba kamar farkon tashinta ba, Umma ce ta sata ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah sannan ta kuma shan ruwan tea, magunguna yaran Malam ya kawo musu sai da ya tsaya aka bawa Maryam sannan ya tafi, jikin Maryam yayi sauƙi sosai har hira suke da su Abba, ganin jikin nata yayi kyau yasa su baba Idris suka yiwa Abba sallama suka wuce gida.+
*WASHEGARI*
Malam bashi ya sallami su Maryam sai wajen bayan azahar, magunguna kala-kala haka ya haɗa musu bill ɗin kuɗin da yayi musu dubu sittin da biyar ne, atake ƴan uwan Abba suka biya ba ƙaramin daɗi Abba yaji ba saboda alokacin kuɗin jikinsa basu fi ɗari uku ba, dama aniyyarsa idan aka gaya masa kuɗin ya nemi rencen kuɗin agurinsu dukda yasan abu ne mai wuya su zura masa ido ya biya ba, godiya ya dinga jero musu saboda jin daɗin abinda sukayi masa, Baba Lawan ne ya kalli Abba Yace, ” Lallai Umar ka bani mamaki, yanxu saboda mun biya kuɗin jinyar Maryamu har kake wannan godiyar kanaso ka nuna mana kai kaɗai ne uban Maryam? Ko so kake ka nuna mana kaine dolenta? ” Kunyace ta kama Abba da jin maganar da yayan nasa ya faɗa, cikin girmamawa Abba yace, ” Dan Allah kuyi hakuri yaya wallahi ba manufata haka ba kuma…” katse shi Baba Lawan yayi da, ” idan ba haka bane menene? karka ƙara maimaita wannan shirmen naka ” cikin biyayya Abba yace, ” na kiyaye insha Allah Yaya ” su Umma da Abba gida suka wuce yayinta su Baba idris kowa ya kama gabansa, Maƙota ne keta shigowa zaryar duba Maryam dukda dai basu san maƙasudin rashin lafiyar ta ta ba, Hafsa ce dai tace musu ankwantar da Maryam bata da lafiya, gudun surutun mutane yasa Umma ta dinga ce musu typot ne ya ci ƙarfin Maryam har aka kwantarsu a asibiti.
Washegari Abba ne ya sa Umma da sauran yaran gaba ɗaya agaba yana musu nasiha ta tunatar dasu akan muhimmancin addu’a haka nan ya gargaɗi kunensu banda wasa da ibada, abu na ƙarshe daya kuma gargaɗarsu dashi shi ne yawan sauraren karatu da yin addu’a kafin shiga banɗaki, sannan ya shaidawa Umma cewar dole ne ya sanyata makarantar islamiyyar matan aure, babu ko gardama Umma tayi karaf ta amsa masa da, ” to Malam ” yaran ya sallama suka wuce ɗakinsu sannan ya kalli Umma kallo na tsanaki yace mata, ” Hajja kinbani kunya kuma kin bani mamaki, yanxu aduniya dama akwai wani abu da wani cen bare zai baki wanda har ni bazaki sanar dani ba? wai ma alokacin da aljanin nan ya baki kuɗin nan kin manta da aurenko ne ko dama da zaki fita ajiyeshi kikayi a gida? yanxu meye ribar ƙwaɗayi da san abin hannun mutane? wacce riba kika samu gonakin da kika siya sun yanke miki talauci ne? yanzu da ace ɗan yankan kai kika haɗu dashi fa? ke alokacin idonki ya rufe kinga kuɗi kika saki baki kike magana san ranki ko kaɗan bakya hangen gabanki ” jikin Umma sanyin yayi harda ƙwallar ta afuska sannan ta fara magana, ” Dan Allah Malam kayi hakuri ka yafemun wallahi kuskurene nayi kuma hakan bazata ƙara faruwa ba, kuma ni waɗannan gonakin ma wallahi banasansu na yafe abayarsu sadaka duniya da lahira ” jinjina kai Abba yayi sannan yace, ” Allah sa tuban da kikayi har cikin zuciyarki ne ba tuban muzuru ba, gonaki cen ke dasu ni babu ruwana aciki ” marairaicewa Umma ta ƙarayi sannan tace, ” Malam idan kace haka sai inga kamar baka yafe mun ba, dan Allah kayi hakuri Malam ” Abban da yaji daɗin wannan nadamar ta Umma yace, ” shikenan komai ya wuce Allah ya kiyaye gaba, gonaki zamuji matsayin kyautarsu amma sai na nemi fatawa agurin Malam Liman ” cikin jindaɗi Umma tace, ” duk yanda kayi Malam dai-dai ne ” Abba tashi yayi ya fice Umma kuma ta hau kiciniyar ƴan gyare-gyarenta da ba’a rasa ba.
Tun daga ranar rayuwar gidan Abba ta sauya gwanin sha’awa da birgewa, ko kaɗan basa wasa da ibada musamman Umma da ta fahimci kuskuren nata ne tun da farko, sai dai babban abinda yake damun Abba bai wuce na rashin kasuwarsa ta shago ba, tun abin baya damunsa har abun yayi tsamari, ganin irin halin daya faɗa yasa ƴan uwansa suka yanke shawarar Maidashi cikim kasuwancin su, Abba ba ƙaramin daɗi yaji ba kuma cikin ikon Allah, sai Allah yasa musu albarka alamuransu, bayan kamar wata takwas da fara kasuwancinsa ya sa gidansa akasuwa kuma bai ɗauki lokaci mai tsayi ba aka samu masu saye ya sayar musu, ya je cen tudun murtala cikin ƴan uwansa ya sayi gidansa madaidai ci mai ɗaki huɗu, abinsu gwanin sha’awa da birgewa kuma wannan karan zaman Umma da facalolinta gwanin sha’awa ba habaici bare tashin hankali, shekara na zagayowa Abba yayiwa Maryam duk wani abu da akewa ɗalibi dangane da neman Admission, kuma cikin ikon Allah, Allah yasa Maryam na ɗaya daga cikin ɗaliban da Sa’adatu Rimi Collage Of Education ta ɗauka, a ɓangaren digree program yayin da ta samu gurbi a English Department.
Safwan Muhammad Safwan matashin saurayi ne da bazai wuce shekara Ashirin da takwas zuwa talatin ba, asalinsa ɗan garin Rano ne sai dai iyayensa suna zaune acikin garin kano Unguwar Tarauni, Mahaifinsa Pro.Muhammad Safwan sananne kuma fitacce ne gidan su nada rufin asiri sosai dan baza’a kirasu da talakawa ba, Safwan su biyu ne kaɗai agurin Iyayensa daga shi sai ƙanwarsa mai suna Safiyyah, Safwan lectural ne a kwalejin ilimi ta sa’adatu rimi yayi karatunsa daga Primary zuwa secondary acikin garin kano, yayi digree ɗinsa da PHD ɗinsa a ƙasar waje bayan ya kammallah karatunsa ya dawo kasa nigeria. Abba nasiha sosai yayi wa Maryam lokacin da zata fara zuwa makaranta nasihar sa da ita sosai itace tasan ƙawayen da zatayi mu’amala dasu kuma ta nutsu tayi abinda ya kaita, sannan ta kiyaye kule-kulen samarin makaranta, saboda yawancinsu ba karatu ke kaisu ba saidai su shagaltar da ƴanmata ƙarshe su yaudaresu su ƙara gaba su barsu da yawan carry over harda su spell over ( _ta wani lectural mu yana idan kika biyewa gayun makaranta har Fly over sai kinyi_🤣) sosai nasihar Abba ta shigi Maryam, ta tsaya sosai bilhakki tana karatu ko kaɗan bata wasa, ƙawaye biyu tayi Nafisa da Khadija suma gani tayi nutsuwarsu taxo ɗaya shiyasa ma tasu taxo ɗaya har suka kulla ƙawayence, tafi-tafi lecture suke sosai har ta fara ɗaukan zafi karatu suke sosai saboda ƙaratowar exams, suna cikin wannan yanayin aka kafe musu time table, wannan ne ya ƙara musu ƙaimi ba dare ba rana Maryam ta tana karatu, ranar wata talata ranar ne suka yi final exams kowanne ɗalibin dake department ɗinsu sai farin ciki yake, bayan sun fito daga papper suka fara bankwana da junansu musamman manyan ƙawayenta Nafisa da Khadija, haka kowa ya tafi gida cike da kewar ɗan uwansa sauƙinta ma da waya suna yawan haɗuwa ta Whatsapp.
Bayan yin hutunsu da sati ɗaya Maryam ta haɗu da wani saurayi mai suna Abubakar, Abubakar ɗan nan kasan unguwarsu ne Mahaifinsa ma duk tare suka taso dasu Abba, Abubakar sana’ar ɗinkin mata yake ya ƙware sosai dan shaguna biyu gareshi duk yaransa ne aciki, Abubakar ya jima yana ƙaunar Maryam saidai tsoronsa ɗaya kar ya furta mata kalmar so ta wulakanta shi saboda yanda ya lura babu wani saurayi akaf layinsu da take shiga sabgarsa, wannan karanma shahada yayi ya aika akayi sallama da ita, lokacin da yaron ya shiga yin sallama sa Maryam Abba na gida yana cin abinci, ba Maryam ba hatta Abba sai da gabansa ya faɗi cikin ƙarfin hali yace wa yaron, ” kaje kace inji wa ” bayan wasu daƙiƙu sai ga yaron ya dawo yace, ” wai Abubakar ne ɗan gidan Mlm Isa Mai rini ” jin sunan da yaron ya faɗa yasa hankalin Abba ya ɗan kwanta, kallan yaron yayi yace, ” jekace tana zuwa ” bayan fitar yaron kallan Maryam yayi yace, ” kije sallamar da ake miki ki fiti da azkar abakinki ” Maryam ɗinma jikinta ba ƙwari ta ɗauki hijabinta ta fita, da sallama ta ƙarasa gurinsa shima cikin jindaɗin yanayin ta ya amsa mata, gaidashi tayi cikin girmamawa amasa mata yayi sannan ya gabatar mata da kansa, yayi mamakin yanda ta karɓeshi hannu bibbiyu hira suka taɓa daga nan yayi mata sallama.+
Washegari Abba zuciyar shi ce ke ta mishi wasi-wasi ganin hankalinsa yaƙi kwanciya yasa yaje har ƙofar gidan Mlm Isah yasa aka mai sallama da mahaifin Abubakar, bayan sun gaisa Abba sanar masa da zuwan Abubukar gurin Maryam, cikin farin ciki ya kalli Abba yace, ” ay ya sanar dani tun kafin yaje gurinta kuma nima yau ɗinnan dama nakesan zuwa gurinka cikin ikon Allah kai kuma sai ka rigani ” Abba sai yanxu hankalinsa ya kwanta cikin jindaɗi yace, naji daɗin wannan lamari Allah ya tabbatar mana da alheri” Mahaifin Abubakar ya amsa da Aameen ” hira suka sha sosai sannan Abba yayi masa sallama, bayan ya koma gida ya sanarwa da Umma duk yanda sukayi da Mlm Isa Mai rini, ita kanta Umma sai alokacin taji dama-dama hankalinta ya kwanta.
Tun daga ranar soyayya ce mai ƙarfi ta shiga tsakanin Maryam da Abubakar tun ƴan unguwa basu sani ba har aka fara fahimtar haka, murna da farin ciki gurin su Baba Ibrahim bata misaltuwa saboda tun sanda Maryam ta warke babu wani wanda ya ƙara zuwa gurin Maryam da sunan soyayya, suna cikin haka har hutunsu ya ƙare suka koma makaranta, su Khadija lura sukayi da halin da ƙawartasu ta faɗa na soyayyah duk yanda taso nuna musu ba haka bane tuni akayi walƙiya suka hangota, sannu ahankali lokaci ke miƙawa har suka cinye level one sukayi hutu, gabanin zasu shiga level two ne iyayen Abubakar suka kawo kuɗin gaisuwar aure da sa rana shekara guda, ba Maryam kaɗai aka karɓi kuɗinta ba harda ƴaƴan su Baba Jamilu ataƙaice dai kuɗin auren ƴan mata shida aka karɓa da sa rana, kowa sai taya wannan iyalai murna yake saboda abin farin ciki ne lokaci ɗaya unguwa ta karaɗe da maganar, sauran masu ƴaƴa mata sai sha’awa suke, farin cikin gurin Maryam da Abubakar baya musaltuwa, haka su Nafisa sun taya ta murna ƙwarai da wannan abun farin cikin.
A washegarin ranar da aka sanya ranar auren Maryam da asuba, gidan su Abubakar suka wayi gari da tsananin tashin hankali wanda ba ƙaramin girgiza al’umma yayi ba, abinda ya faru kuwa mahaifin Abubakar ya bubbuga ɗakinsa da asuba zasuje masallaci yaji shiru Abubakar bai yi magana ba, har yaje yayi alwala ya ƙara dawowa ya bubbuga masa ƙofa wannan karan ma shiru yaji, touchlight ɗin hannunsa ya kunna ya haska ɗakin nasa yana ƙwala masa ƙira, yana haskawa idanunsa sukayi tozali da mummunan gani, gawar Abubakar ya gani yashe akan katifa anmurɗe wuyansa fuskarsa ta koma ƙeyarsa, ƙeyarsa ta dawo fuska salati Mlm Isah ya rafka cikin gigicewa ya ƙarasa ɗakin yana rungumarsa yana fashewa da kuka mai tsuma zuciya, Mahaifiyarsa da take sallah azabure ta sallame ta fito tana shiga ɗakin taci karo da abinda Mlm isa ya gani, cikin tashin hankali ta fashe da kuka itama, kafin wayewar gari tuni labari ya karaɗe ko’ina tunda a masallaci aka sanar da jana’izarsa.