MASARAUTAR JORDAN BOOK 3 CHAPTER 4 BY MAI_DAMBU

MASARAUTAR JORDAN BOOK 3 CHAPTER 4 BY MAI_DAMBU

              Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sake bud’ar baki tayi zayi magana yace. “Allah Kiy) hakuri ki basht matar sa, munyi laifi dan ko maso ki fahimei abinda nake da tabbacin sa ba ganewa zaki, Allah ki bamu matar mu.”

Ya mai da al’amarin wasa, sosai sannan ya kara da cewa.

“Bari na miki wata magana wanda zai tabbatar miki SAFINAH tana tare da muinta, ba wai Zarginta nake ba, amma ina da Yakinin suna tare da juna, kirata kice mata ta kyauta miki da kika ce karta kirashi sai da takira shi, zak) ji abinda zata ce.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Shiru Ummi tayi kafin tace. “Alhaji ita tace da bazata kuma kiran shi ba, koda yazo a karba mata takardanta.”..

Duk yadda yaso ta fahimta taki sai ya zuba mata ido a ranshi yace. *Ba dai SAFINAH nace zata kunyataki*

kik Washe gari da wuri ta tashi bayan ta gama komai na al’adar gidan, sannan takira Safinah abinda ta fara cewa. “Wato SAFINAH da nace karki kira Ashraf sai da kika kira shi ko!? Ban isa dake ba? Namy) yafi iyaye ko?!” Www.bankinhausanovels.com.ng

“Ummi kiyi hakuri! Ablah ce take kuka sai na kata gurin Appanta.* Jikinta ne yay! masifar Sanyin. “Safinah wacce rin so kikewa Yaron nan ne da baki iya kame kanki daga gare shi.”

Kuka ne ya kwacewa SAFINAH, tace. *Ummina! Wallahi ban san tya adadin son da nake mishi ba, Ni dat bana iya jure nisanta kaina daga gare shi, zan iya hakura da komai ban da Son Ashu, Ummi kiyi hakurt bazan kuma kiran shi ba.”

Ajiyar zuciya Ummi ta sauke sannan tace. *Toh duk abinda kuke j’bi ku dauko hanya.”

“Ummi kiyi hakuri! Bazan kuma ba” Yadda tayi maganar sai ya kara kashewa Ummi jiki, tace. “Wata sati ina son ganinku a Abuja.”

“Toh Ummi naji! Amma Kiyt hakuri ba zan kuma ba.”

“Allah yayi miki albarka.” Haka suka yi Sallama da Ummi, kowanne su yana jin ba dad’, musamman Ummi da ta

shiga tsakani tay) kabe-kabe (_ )

kik Jordan …. Dama ita rayuwa dama ce Allah da ya bamu, domin kambamawa da kuma gwarzantawa, sannan suna tafiya akan hanya me matukar kayoyi da tarin fasasun kwalaben.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ita rayuwan nan ko anki ko anso turare bata da uwar da ta wucce kwalba, Yau ina Abu Zarri, ina Yasir bini Alhashmiyya, Ina Abdulla bini Alhashmiyya, Yau rayuwar da aka jingina ta domin wasu ta kare , ina kuma wanda ya jingina tashi rayuwar domin kansa, Duk wata dama da ake samu na rayuwa An bawa Ukshe, amadadin ya gyara sai ya kuma lalata komai, mutumin da duk abinda yake so ake mishi yau shine ake juya akalar rayuwarshi, abinc sai lokacin da ake bukatar yaci ake basu ba lokacin da shi yake bukata, wannan tta sirrin rayuwa, kay: amfani da Damarka kafin lokacin da zai subuce maka. Kwallar nadama ce ta sauko mishi, tunawa da yayi dukda tawaye da yake da ita, haka bas hana shi samun damar da za a kira shi wani a kasar ba, sai gashi garin son kai da son zuciya irinta dan Adam, yau Gashi ta kare mishi a gidan ajiye tsofi. Dan shi Uzaif ya manta dasht, sauran al umma yana kyautata 2aton sun manta da babin shi, rayuwa kenan kay: dai dai ya aka cika balle kuma bakayi dar dai ba,(_Shi yasa nake mamakin yadda kai baka kashe wutar gabanka ba, amma kana saka ran

kai zaka iya kashe wutar Wani, kowa yayi abinda yaga yayi mshi ra’ayina daban nas Mrs Jmoon daban, haka ma na Mrs G daban, sannan dukkan mu uku babu wanda zai ce wance zaki bi ra‘ayina, dan ke ba akan dai dat kika daura ra‘ayin ki, ba, duk wanda yake da huyar kare kanshi, kare da kudin shi, a wannan lokacin da zaran ka fadi gaskiya an kiraka da munafuki, idan kayi shiru akirana da Annamimi har kaj! a ranka kabar kowa ya tsula tstyar shi ko ba haka ba .)

Tura kekenshi yayi zuciyarshi a cunkushe, yaye ya amshi abincin da yake ci, har zai wucce yaji sanarwar da ake na sabon sarkin Jordan, Ammar sunkuyar da kar yay! cikin jin kaskanci, yau kujerar da yake hari gashi ta fita daga gidan da suke ta yakarta dan samun ta, yau gashi D’an Abu Zarrin da ya kashe shine akan mulkin da ko yaran shi baya kaunar so ambaci suna son zama sarakuna, kaicon Rayuwar da bata amfane shi da koma ba, sai bakin ctki da damuwa, saukar —hannu yay! a kafad‘arshi, ya d’ago kai yana kallon mutumin da ya dafa shi, goge fuskar shi yayi sannan yace.

“Kuka baya magani kuma baya goge bakin fentin da kayi, aikin alkhatri tare da tuba tsakanin bawa da Allah yana rage wasu abubuwan, idan kaji abinda na aikata kai kanka.”

Girgiza kai yayi cikin damuwa, sannan yace. “Wani alamanin sai Allah! Ka cigaba da niman gafara ”

Sun jima sosai suna tattaunawa, har Ukshe ke gaya mishi irin abinda ya aikata, shima ya kuma gaya mish irin nashi laifin, da yadda zasu yt tunanin me kyau.

kik
Www.bankinhausanovels.com.ng
Oman… Ghaniyu da kan shi ya isa da Nannah wacce ake turata a kan gadon marasa lafiya, zuwa cikin gidan Sarautar Oman. Jiyar da kai Mahaifin Natashah yayi, hawaye nazm zuba daga idanun shi, yau yar uwarsa wacce take da yawan alkhain itace me mugun laifi har haka, idan aka mikata ga kuliya hukuncin kisan kat za a yanke mata, amma sabida lalurar ciwo yasa sun barta da halinta yadda ta iya ha’inta dan cikinta babu wanda bazata cuta ba.

Dan haka suka mai da ita Asibiti aka cigaba da jinyar ta.

A can Jordan kuwa Yan uwan Zoyah suka juya mata baya, dan ta b’ata musu sunar kabilar su, tare da zubda musu da kimar su, sannan tayi dalilin da babu want Bahashmin da zai kuma auren Yar kabilar su ba, koda kuwa a k’ork’ora suka je balle kuma a musu tayin aurenta, sannan_ tasanya musu hyaba tsakaninsu da sauran kabilun babu su babu magana a cikin k‘asar baki d’aya, dan kowa yasan yadda ake kare mutumcin tare da kankaro darajar su, amma dare d’aya ta rusa musu mafarkinsu, tasan musu Jin tsoron shiga cikin masarautar Jordan, ta kuma rufe musu goben da sauran ga samun Mulkin jordan.

A da cikin izza da alfahari suke maidawa kowa magana cikin iko da d’agawa amma yau an way! basu da ikon haka gudun kar a musu gori.

Jigun jigun suka zauna kafin Abu Darda ya mike cikin damuwa yace.

“Yaku banu Hussain! A yau zan ajiye wakilcin kabilar mu, Ni Abu Darda na hakuri da wannan mukamin dan ina jin kunyar masarautar da kuma yadda zan fuskanci Al’ummar cikinta, musamman kabilar Hashimawa.”

Duk suka dukar da kansu kasa cikin damuwa, sannan ya cigaba da cewa. Www.bankinhausanovels.com.ng

“Da ina da yadda zan kakkare abinda Zoyah tay! da nayi haka, amma babu halin haka, shi yasa naga dacewar na hakura da wannan mukamin sannan zamu cire kanmu da shiga duk wani abu da ya shafi masarautar da sauransu ko ya kuka gani.”

Shiru ne ya gifta tsakanin magana da yayi, wani dattijo a cikin su me yawan shekaru ya mike cikin mutumtaka yace. “Ya shugabana Ni a nawa ganin ajiye mulki bazai karo mana darayar da aka zubda mana, kawai abinda ya dace. A tura da sakon ban hakuri da abinda ta aikata, sannan mu nemi jin want hukunci suka dauka abinsa laifin da aka musu.”

“Wannan maganar da Shah Nawaz yayi itace gaskiya. Ko ya kuka ce, kuyi magana wannan abun dan kare kimarmu ce.”

“Ghaiyyas kayi gaskiya haka ma Shah Nawaz yayi gaskiya, sauran Al’umman baku ce komai ba, muna son muyi abu da murya daya karku nuna gazawarku mana, mafita muke nima.”

Duk suka amince da yin mubaya’a da abinda suka tattaunawa akan bawa masarautar Jordan hakuri a bisa laifin da Yar su Kanwar su, ta aikata.

Wannan shine matsayar da suka cimma a zaman su na yau, Kuma haka ya yi musu dadi.

kee Ukraine… Www.bankinhausanovels.com.ng

Tunda muka idar da waya da Ummi, share kwalla nayi sannan na kalli Sophia wacce suke wata da Babanta Takaicin Ashraf ne ya kama Ni, na shiga niman number shi, yana dauka na mike na koma d’akin, na zauna a bakin gado cikin jin haushi nace mishi.

“Wannan wani irin hauka ne da zaka gayawa Ummina muna waya da kai, _kasan irin fadar da tayi min kuwa.”

“Wallahi ban gaya mata komai ba, Ni har yanzun ban mata maganar dawowarku ba, ina jiran

ta bani umanmni.”

A madadin na saurare shi, sai ma maida al’amarin ya girmama, haushi ne ya turnike shi cikin tsawa yace.. “Kee! SAFINAH Ni sa’an kine da zan rantse miki bamu yi haka da ita ba har ki karyatani, ina wasa dake. Toh na gaya mata ina waya so What sakarya kawai wacce bata san ciwon kanta ba har kin isa nayi na baki hakuri kina ce min nayi miki shiru, toh Kizo ki dake Ni wawuya kawai”

“Ashu! Ni ka zaga?°

“Kinga mu bar maganar haka, bana son tashin hankali, lafryar ki tta damuwata™ “Nace Ni ka zaga?”

Shiru yayi ya rasa yadda zai yi da Safinah a rayuwarsa, idan akwai abinda ke bashi matsala Safinah ce, dan yana da kwarin gwiwa akan komai na tayuwa idan tazo mushi amma SAFINAH kadai ce zata had’a mishi zafin da lokaci guda zai shiga zufa.

“Kinga SAFINAH mu fahime! juna mana Ni bana son muna rigima a gaban danginki, sai naji a raina suna dana sani bani Aurenki.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Dana sani na nawa kuma, wannan kaddararren Aurenka mara albarka.”

“Haba SAFINAH! Auren kike kwashewa albarka.” “Banzan aure na tsane ka, ka rabu dani, tunda babu wani abinda ya hadani da kai mugu me son kanshi.” “Innalillah! SAFINAH zagiba kike akan abinda bai kai haka ba, Haba SAFINAH, duk laifin da nayi ai naci Arzikin Fatimah,” “Baka ci Arzikin ba, kuma wallahi sai na gudu inda bazaku kuma gani na ba, tunda halinka had’ani da mahaifiyata mugu kawai.”

Kashe kiran nayi ina yan tsaki yafi a kirga, tsabar naji haushin kaina, da zagin da nay) mishi wallahi naji zafin amma ban san me yasa nake saurin jin zafin shi ba, kodan fadar da Ummu..uo Abuja… Shafa kanshi yayi cikin damuwa, sannan ya juya zai bar cikin gidan. Ido biyu suka yi da Khalil, shan jinin jikinshi yayi cikin nuna babu abinda ya faru, yace. “Ya dai? Kana son wani abu ne?!” “Gaskiyar nake son Sani! Didih tac: mutuncinta ba?!” “A’ah Khalil! Ba wani abu bane, dan ai mun saba haka, kuma zaka ga mun dai-daita kanmu.” Shiru Khalil yayi dan yayi alkawarin sai ya gayawa Ummin su. “Ai shikenan tunda kace ba komai, baka son a mata fada bayan abinda tayi ba dai dai bane” “Amma juya naji kana cewa kana son bike, bari nasaka a kawo maka.” Murmushi Khalil yayi wato shine Ashraf zai ma wayo, sai shima ya share tunda Ashraf ya nuna baya son maganar sai yaya bakin shi yayi shiru. Bayan sallah maganb, Khalil na zaune yana cin abincin dare a gaban Ummi, ya d’ago kai sannan yace.
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ummi Ya kamata kiyiwa Didi magana, domin ban tab’a ganin kinyiwa Abba magana mara dadi ba, amma yau naj! da kunne na. Sai magana take gaya mishi sht kuma sai bata hakuri amma bata fasa ba, yau ummi misali idan SAFINAH ta rasu, aka dauki Adda Batul ko Khalilah aka bash bazai amsheta ba, sabida bai ji dad’in yar Uwarsu ba, don Allah Ummi ki mata magana wallahi da kunnena naj! yana cewa shi baya son tana jan ngima a cikin danginta don Allah ki mata magana, wallahi nayi zafin abinda tay: mishi sai kace ba tarbiyyarki ba.”

Duk sai jikin Ummi yayi masifar sanyi, musamman yadda Khalil ke kalublantar. Har ya gama cin abincin ya bar falon Ummi bata bar gurin ba.. “Ghaniyu ka fahimce ni, na gaji da Halin SAFINAH, idan muka sami matsala da ita, a madadin ta mutuntani sai zagina. Haba Ghaniyu yaushe zanyi kima a idanunta, zan rabu da ita na kuma yi hakuri kafin Allah ya bani wacce bata fita ba.” Shiru yayi yana jin abinda Ghaniyu yake gaya mishi. Murmushi yayi sannan yace. “Ba dai SAFINAH ba, dan bata da sauki kawat zan hakura da (ta ne.” Kome Ghaniyu ya gaya mishi ya sanya hannu a goshinsa, tare da lumshe idanunshi Kafin yace. “Shi kenan, amma bazan cigaba da jin cin kashin da take min nan, wallahi Ghaniyu SAFINAH ta fice min a kai, sam bana sin kamar yadda nake ji da” Shiru yayi sannan yace. “Ba wai bana sonta bane kawai ta ficce min akai ne, wallahi da gaske nake ta renani sosai.” “Nagode sosai da shawarar da ka bani.” Kashe kiran yayi sannan ya ajtye wayar ya kalli bakin kofar da Khalil ya shigo, murmushi yayi sannan yace. “Shigo mana.” Zama yayi sannan ya kalli Ashraf yace. “Nasan bata kyauta ba, amma don Allah karka juya mata baya. Insha Allah bazata kuma don Allah.” Wani iri Ashraf yaji a ran shi, Anya Safinah tasan yadda yan uwanta suna sun zaman su kuwa. “Ba damuwa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *