MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 10

MATACCIYAR RAYUWA
BOOK2
CHAPTER 10
                                  A KANO 
Ya isa Kano cikin sa’a da kwanciyar hankali, yana isa ya yiwa Falmata waya yace ya isa lafiya. Kamar ta doka tsalle don murna, ta dinga yi wa Allah godiya da ya kai mata masoyinta kuma mijinta gida laflya. 
Gidansa ya wuce kai tsaye, maigadi ya bude masa Kofa yana masa sannu da zuwa. Ya amsa ya wuce ya ajiye motar gurin da yake ajiyeta. ~ . 
Fatila kam an ci kwalliya kamar za a filin rawa, domin tasanda zuwan nashi, sai dai bai shiga gidan ba gurin maigadin nasa ya amshi buta ya daura alwala jin tayar da sallar magruba a masallacin: layin nasu, ya nufi masallacin da sauri. 
Tun da ya dawo ta baibaye shi da iya yi da kissarta, wadda ke hana shi ganin aibunta. Ba ta d‘aga murya a gabansa balle ta yi fad‘a, ga shi kullum cikin yabon iyayensa da girmamasu take a gabansa, don haka idan ‘yan uwansa ko mahaifiyarsa suna korafi akanta, sai ya ga kawai don ba ta haihuwa ne suka tsangwame ta. 
Yana cin abinci tana ta ba shi labarai kala-kala yana dariya, domin ta kula yau cike yake da farin ciki. Amma a can Kasan zuciyarsa .yana tunanin ta yadda zai gaya mata maganar Falmata, don bai san yadda zata dauki maganar ba, har suka kwanta bacci yana dari-darin yadda zai sanar da ita. 
Washegari da safe sun sha hirarsu da Falmata a office  dinsa ta wayarsa, yau dai ya yi niyyar gaya wa Fatila duk yadda zata dauka kuwa. 
-Daga OflS kai tsaye gidansu ya wuce, bayan sun gaisa da sauran abokiyar zaman mahaifiyarsa ya wuce d‘akinta; tana zaune tana kallon tashoshin Larabawa ya shiga da sallama. Ta daga kai ta dube shi fuskarta a sake ba kamar yadda ta ke daure masa ba can baya. Ya sami guri ya zauna bayan ya durkusa ya gaishe ta. 
Cikin farin ciki ta ce, “Mutancn Maiduguri yaushe ka dawo ne? Tafiya babu sallama sai Isyaku ke gaya mini ka tafi Maiduguri da nake jajenka kwana biyu, yaya’ ka baro su lafiya k0?” 
Ya sosa Keya yana dariya, cike da kunya yace, “Lafiya lau suke, sunce a gaishe ku ma”. 
. “To, muna amsawa. Har yanzu ba ka yi maganar tariyar Falmatan bafa”. 
Ya gyara zama sannan yace, “Abin da ya kawo ni kenan, na sanar da su ranar asabar za,a je d‘aukarta, sai ku zabi wadanda zasu zan’turo da motoci idan kun gama kimtsawa” . 
Dadi ya cikata, tace, “Hakan ya yi kyau, a nan gidan naka zata zauna ne ko kuma ka tanadar mata gurin zama ne?” 
“A’a, a gidana da nake gini na can Janbulo zata zauna, ‘ai an kammala aikin ma, sai da na fara biyowa can sannan na yo nan, fenti kawai za a yi gobe insha Allahu”. 
“To ai shi ke nan, Allah Ya sanya albarka, amma kuma kasan ba ka yi mata kayan lefe ba, tunda auren babu shiri aka yi shi, yaya za ayi ke nan?” 
Cikin ladabi yace, “Ina sane, gobe wai da zan je gidan Hajiya Safiya na ba ta kudin ta siyo duk abin da ta ga ya dace, ranar da zata tare a tafi da kayan, ina ga ai hakan ya yi k0?” 
Ta cc, “Eh, ya yi Allah dai Ya kawo su laflya, amma ya ya maganar matarka, ka gaya mata kuwa?” 
Gabansa ya yanke ya fadi,.damuwa ta bayyana karara akan fuskarsa, amma sai ya dan dake ya ce, “A’ a, sai yau dai nake son sanar da ita insha Allahu”. 
Ta taBe baki, “Kai dai ka jiyo, amma ka sani bazan yarda a maida Falmata bora ba, dole ne ka tsaida adalci a tsakaninsu muddin kana son a zauna lafiya” . 
.Da sanyin murya ya‘ce, “Insha Allahu ba zaki ji komai ba sai alkhairi”. Ya mike tsaye, “Bari na wuce gida  na ga magriba tana kawo kai”. 
“To ka gaida mutanen gidan, Allah Ya tsare”. ‘ ; .. Ya amsa da .amin, sanda yake kokarin ficewa. Hajiya Mariya ta yi jagale cike da fargaba, tasan halin Fatila da uwarta za su iya yin komai akan Falmata, amma dai ta Allah ba tasu ba. Ta san Falmata ba ta sakaci da addu’a, 
duk abin da suka tura mata insha Allahu Allah 
zai kare ta. Da wannan tunanin ta sami nutsuwa. 
Sanda ya koma gida Fatila ba ta nan, ta tafi gidansu, don yau za a kawo kayan auren kanwarta Raliya don haka bayan ya watsa ruwa kai tsaye masallaci ya nufa. Har ya dawo ba ta dawo ba, da yake shi din ba bakon zafi ba ne, sai ya shiga kicin da kansa don ya nemarwa kansa abin da zai ci, indomie ya dafa da kwai, ya dawo falon yana ci yana kallo. 
Gaba daya kewar falmata da sonta suka taso masa, ya dinga murmushi shi kadai yana son yanayin shagwaBarta da sanyinta, don haka ya ga gwara ya kirawota k0 ya samu sanyi a cikin ransa, babu wani jinkiri ya kirata. 
Cikin siririyar muryarta ta yi sallama, jikinsa ya yi wani yarr ya haye doguwar kujera ya kwanta yana amsawa cike da nishadi a lokaci guda kuma yana rage sautin talabijin. 
Daga can Bangaren tace, “Malam yayata ba ta kusa ne k0? Na ga yanzu lokacinta ne ba nawa ba”. 
Ya yi dariya, yana fadin, “Au har kin raba muku lokaci? To yanzu ya za, ayi gashi
kishirwarki ta sanya na shiga lokacinta. Ina jin kamar na yi tsuntsu nazo kusa dake, na rungumi’ wannan tattausan jikin naki. na sumbaci dan karamin bakinki mai kama da atafa”. . 
Ta yi dariya cike da nishadi da jin dadi, tana cewa,_“Ni fa kunya nakeji, ka daina fadin haka mama”. 
Yace Au? Kunya k0? Ina ma ina kusa daje da kinga abin da zan miki karamar kunya ma wai me kikEyi ne yanzu Fatimatuna?” 
Ta sake yin dariya tana kallon dakin nata, tace, “Da dai lazimi nake yi. Yanzu kuma ina sauraron muryarka ne mai dadi
Ya yi dariya, “lye? Lallai yarinyar nan kin fara fitowa. To bakya tunanina kenan k0?” 
. “Ina yi mana, .ai kewarka ta sanya na kama karatu da lazimi ma”. 
Ya kuma yin dariya yana jin dadin kalamanta masu kama da busar sarewa, shaf ya sha’afa ya ma manta a inda yake, balle har ya yi tunanin abin da zaije yazo Ya dan lumshc ido yace
“To kin yi kokari, sauranki abu daya yanzu, kice ina sonka Mukhtat’, kinga sai na yi bacci cikin dadin rai k0?” 
Ta kama dariya cike da kunya, don ba zata iya fada ba. Ya ce Uhm, ina jinki k0…” Kamar an ce ya bude idonsa, sai ganin Fatila ya yi a kansa tana huci kamar mayunwacin Zaki, gabansa ya fadi gaba daya ya dimauce. Da sauri yace da Falmata“Shi kenan, zan kiraki an jima”. Bai jira jin abin da zata ce ba, ya kashe wayar. Mamaki ya cika falmata jin muryarsa gaba daya ta sauya, sai tunanin Fatila ya fado mata, k0 ita ce ta zo gurin ne? Tabbas idan dai saboda it ya kidime haka tana da aiki ja a gabanta, domin bashakka yana tsananin tsoronta. Ta zame ta kwanta jikinta ya yi sanyi qalau Shi kuwa ta maza ya yi, yace“Yaushe kika dawo banji shigowarki ba?” . ldanunta sun rune zuwa jawur, kamar Jan gauta. Tace, “Eh daman yaushe zaka san na dawo kana iskanci a waya, yanzu Mukhtar ba ka ji tsoron Allah ba kake magana da mace haka, kana cikin gidanka na aure, kowa yana kallonka kamar kamili, ashe kana can kana watsewarka da ‘yan mata…” . ‘ 
“Ke Fatila, kisan maganar da bakinki zai dinga fadi”. Ya katseta cikin tsawa kamar zai tsaga falon. Ya ci gaba, “Ta yaya zaki dinga gaya min irin wadannan maganganun masu zafi haka, kin sanni ba tun yau ba, babu matar da zan iya yiwa wadannan kalaman idan ba halaliyata ba, haba…” 
Ta waro ido waje cike da tsoro, gabanta yana bugawa da sauri-sauri, tace “Ban gane abin da kake nufi ba Mukhtar, kana son ka ce min ita wadda kake yiwa wayar halak dinka ce? Yaushe ka fara bada fatawar son rai ban sani ba?” 
Hawaye ya fara zarya a idonta, wani irin .masifaffen kishi ya tokare kirjinta, har da kyar ta ke zaro numfashinta, da ace wani neya ba ta labarin ya ganshi yana waya da wata lallai da ta karyatawa zatayi
Cikin karfin hali yace, “Ba wai fatawa Ce ta karya ba, sai dai ina son ki yi hakuri ki 
fahimta,’ wacce nake waya da ita Falmata matata ce kamar yadda kike matata”. 
“ What? Kada ka gaya min zancen banza wanda hankali ba zai dauka ba, kana son ka ce min bayan ni kana da wata matar? Shin cikin bacci aka daura muku aure, k0 kuma a duniyar wata ka aure ta? Ka dawo hayyacinka Mukhtar ka gane abin da kake fada don Allah”. Gaba daya jikinta rawa yake yi. 
Babu tsoro yanzu a idonsa, ya ce, “A duniyarmu ta mutane aka daura mana aure ba a duniyar wata k0 a mafarki ba. Sanda na tafi Maiduguri ziyarar aikin da na gaya miki, a sannan aka daura mini aure da Falmata diyar Abbana gana abokin mahaifina, ki yi hakuri ni kaina ban san da maganar auren ba, sai da naje aka ce an daura mini aure, a yau dama na yi niyyar gaya miki
Ganin bata ko Kifta ba ya sanya yayi zaton ko ta saduda ne, sai dai bai san shirun tsiya ta yi ba, ya matsa kusa da ita da zummar kamata ya rarrafa, sai dai yana taBata ta yi baya luuu ta fadi a sume. 
Da sauri’ ya durkusa a gabanta yana kiran sunanta, amma ina ko motsi ba ta yi  , tuni ya mike ya nufo firij ya dauko swan water mai sanyi ya yayyafa mata. 
, Ta yi wata sassanyar ajiyar zuciya, sannan ta bude idonta ta mike zaune a firgice tana kallonsa, don ta yi zaton mafarki ta keyi, tace masa, “Hubby wani mummunan mafarki na yi yanzu, kai mafarki babu kyau, wai ka yi aure a Maiduguri, da gaske ne k0?” 
Ya yi shiru ya ma rasa abin da zaice, bai taba ganin mace mai shegen kishin Fatila ba. Ganin ya yi shiru sai ta hango gyalenta da jakarta da takalminta da ta dawo da su daga unguwa, hakan ya tabbatar mata da lallai ba mafarki take yi ba gaske ne, sai kawai ta fashe da kuka tana fadin. 
“Da gaske ka yi aure a Maiduguri, tabbas ka cuce ni, ka ci amana ta, ka tabbatar na gama zama da kai, ,tabbas kai munafuki macuci azzalumi”. ‘ 
Ta mike ta yi dakinta kamar mahaukaciya, ya mike da sauri ya bita yana 
fadin, “Fatila ki saurare ni na gaya miki yadda aka yi auren nan, nima ba da son raina na yi ba”. 
Amma ina bata k0 waigo~ ba, ta banko kofar dakin nata har da sanya makulli. Ya yi tsaki cike da takaici, sannan ya wuce dakinsa yana fatan Allah Ya sanya abin ya tsaya iyakacin nan. 
Ita kam tana shiga daki tama rasa me zata yi, sai ta koma tsige kayan jikinta tana wurgi dasu kamar mahaukaciya, sai da tayi tumBur sannan ta kama zunduma ihu a dakin ita kadai tana zagaye dakin, hannunta bisa kanta. Sai can dabarar kiran mahaifiyarta ta fado mata, ta janyo wani zani ta daura sannan ta fara neman layin. wayar hajiya Kumatu mahaifiyarta. 
Bugu daya Hajiyar ta d‘auka, tana fadin “Hello Fatila ya ya aka yi, har kin isa gida?” 
Maimakon ta yi magana sai kawai ta ci gaba da ihu a waya tana kuka, hankalin Hajiya Kumatu ya tashi, ta mike tsaye a rude tana fadin, “Kc Fatila gaya min meke faruwa ne, 
kin bugo waya kina mini ihu, k0 mijin naki ne ya rasu?” 
Da kyar ta dan tsaida kuka tana fadin “Momy ai gwara ace mini mutuwa ya yi sai nafi jin sauqi da a sanar dani wannan mummunan labarin, wai fa aure ya yi ban sani ba…” 
“Aure kuma kan uban can, da gaske kike yi Fatila k0 kuma labarin karya aka zo aka gaya miki? Ni fa bana son kina dinga .yarda da wadannan labaran na karya, ai kin san an ce mama shi da aure k0 bayan ranki har abada k0?” 
Ta Kara fashewa da kuka tana fadin“Shi fa da kansa ya gaya mini ba labari aka ba ni ba, samunsa na yi yana hirar soyayya ma da matar tasa, kin san Mukhtar ba ya karya, ina ga tsinanniyar babar nan tasa ce ta hada wannan tuggun, tunda daman tace komai tsafina wai sai ta yiwa danta aure. To burinta ya cika Mommy na shiga uku, ina raye a gaban idona Mukhtar ke hirar soyayya da wata mace ai gwara ace na haukace na huta ma ni…” 
Kuka ta keyi kamar ranta zai fita daga jikinta. ‘ 
Ita kanta Hajiya Kumatun ta shiga matukar mamaki, to ya ya aka yi hakan ta faru, ko.da wasa ba ta ji maganar a layin ba, ga shi layinsu daya da gidan su Mukhtar din, to ko dai ba a sanya rana bane? Da kyar ta dan daure ta ce
“Kinga ki kwantar da hankalinki, sun yi nasarar daura masa aure da wata, amma na rantse da Allah basu isa ta tare a gidansa ba, balle har wata mu’amalar aure ta shiga tsakaninsu ba, da kanshi zai zo ya gaya miki ya sake ta muddin ina raye, idan kin ga Mukhtar ya zauna da wata mace sai dai idan bana numfashi ne a duniya, k0 ba na numfashi fatalwarmu ba zata kyale shi ya zauna lafiya ba”. 
Cikin kuka tace“Anya kuwa Momy ba cutarmu bokayen nan keyi ba, washegarin ‘ sanda ya dawo fa sai da naje gurin Barbushe na sanar da shi sauyin da yazo da shi, yace mini babu komai, har ya ba ni wasu magunguna na ‘ yi amfani da su, ashe tuni an daura auren ma ba tare da saninmu ba, ni fa abin har ya fara ba ni haushi da takaici fa”. 
Cikin kwantar da murya ta ce, “Kiji wani zanccn banza, ba don aikin nasu yana yin .kyau ba, da kin-isa ki aure shi ma balle har ki zauna a wannan gidan, ko kin manta da yadda aka yi auren ne ki daina fadin wannan maganar ma, ai daman dole a semi akasi kuma ba kin ce ‘yar Maiduguri diyar abokin babansa bace? Ai suma ba haka zasu zauna ba, ai nasan malam Abba Gana shegen malami ne, dole sai mun tashi tsaye, ki dai tanadi kudi, gobe zamu koma gurin Barbushe din”. 
Da kyar ta samu ta lallaba= diyar tata ta daina kuka, sai dai suna gama wayar ta kirawo kawarta Diyana. Ita kam ruwan ashar ta dinga ‘zubawa kamar famfo, ta kuma ce ita ma akwai wani’ boka sai sunje gurinshi, dole da ita za a yi tafiyar. 
Sai a sannan ta sami dan sauki a cikin zuciyarta, har ta kwanta a gado, sai dai kusan daren nan ba ta runtsa ba, ta Kagu gari ya waye ta nufi gurin bokayenta. 
Shi kuwa bawan Allah malam Mukhtar jira yake gari ya waye ya kuma zuwa ya lallasheta, don a ransa bai taBa kawowa Fatila 
tana bin bokaye da malamai ba saboda yadda ya yarda da ita. 
Don haka da safe yana kammala shiryawa ya nufi dakinta, abin daya -ba shi mamaki bai wuce ganinta tayi wanka ta shirya ba, duk da ba tayi wani make up ba amma bai yi zaton k0 wanka zata iya yi ba, Ya dan ji sanyi a cikin ransa, domin hakan yana nuna masa ta dan sauko ke nan. 
Ya isa ya zauna gefen gadon ya kwantar ‘ da kanshi ya shiga lallashinta, kamar zai zubda hawaye. Ta yi shiru kamar ta bari din, amma «cikin zuciyarta tafasa kawai ta keyi, ji take kamar ta shake shi ta kashe shi ta huta ma, ji ta ke yi ta tsaneshi matuka, amma dai ta taushi kanta ba ta tanka masa ba, burinta ya fita ita ma ta fice kawai. 
Ya jima yana surutunsa, sannam ya ficc jikinsa sanyi kalau, domin ta ba shi tausayi ainun, ganin yanda ta zabge dare daya. 
Tana jin tashin motarsa ta yagi  gyalenta da jakarta ta fice ita ma. Yana fita daga gidan ta nufi motarta ta shiga ita ma ta rufa masa baya 
zuciyarta tana tukuki kamar zata faso Kirjinta ta fito. 
A can gidan mahaifiyarta ta yada zango, ta tadda ta a shirye don haka ta mike kawai ta zari jaka, a kofar gida suka ci karo da Diyana adaidaita sahu ya sauketa suka dunguma suka wuce neman duniyarsu. 
Shi kam bawan Allah Doctor  Muktar daga nan gida kai tsaye ofis dinsa ya wuce, karfe biyu dai-dai ya tashi daga aiki ya wuce gidan yayarsa Hajiya Safiya. A kofar gida ya yi mata waya .ya isa, murna kamar ta goya shi domin da duk_ ‘yan ‘uwansa haushinsa suke ji akan rashin Kara aure, amma yanzu tunda ya yi aure suka sama masa lafiya. 
Bayan sun gaisa ta kalle shi tana dariya, tana fadin, “Ango kasha kamshi, dube ka sai wani kyallin goshi kake yi”. 
Ya tura hularsa keya yana sosa goshinsa, yana dariya, babu abin da yake burge shi a yanzu illa a yi masa zancen Falmata, yana jinta matuka a cikin ruhinsa. 
Hajiya Sahura ta dora da cewar, “Jiya Abba ya yi kirana, yake sanar dani maganar 
Fatila fa taqi yarda da kaddara shin me kuke tunanin zai iya biyo baya oya a buga sharhi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *