MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 21
Windonsa ya yi shiru tsawon lokaci, ta rasa ko tunanin mai yake yi, sai dai ta bai wa kanta laifi, a ganinta tabbas ta yi masa wani abin da yake taba masa ransa, don haka a yau kam ta yi niyyar tunkararsa taji duk abin da ta yi masa dake Bata masa rai.
Ta yi kwalliyarta a cikin doguwar riga irin ta larabawan Moroko mai aiki sosai a kirjinta da hannayenta, kusan daman wad’annan su ne kayanta tun tana budurwa balle da ta ke da ciki yanzu, tanjin dadin amfani da su fiye da kowanne kaya.
Ba wata shaharan’iya kwalliya ta yi ba, amma ta cire barimar da ta sanya a hancinta ta G.L ta maida ‘ta gwal, don haka hancin nata sai ya Kara kyau da Kyalli, domin hujin hancin yana cikin abin dake qara mata kyau.
Yana kan tsakiyar gadonsa a zaune yana ta aiki da laptop ta shiga da sallama da siririyar muryarta. Bai dago kai ya kalle ta ba ya amsa a dakile, abin ya dan taBa mata zuciya, domin ta san a can baya da yaji sallamarta zai dago da sauri ya amsa cikin farin ciki. Wani lokacin harya kan tashi ya tarota ma amman dai ta dake ta
Karasa tsakiyar gadon da rarrafe tace
“Sannuda aiki malam”.
Bai, d‘ago ba har yanzu ya amsa da, “Yauwa”. Kawai ya ci gaba da aikinsa.
, Tabbas kamshin da ke fita daga jikinta yana ratsa shi har ya kan lumshe ido, amma miskilanci ya hana shi daga kai ya kalle ta balle ya nuna ya ji dadin abin.
Su kai shiru tsawon lokaci gabanta yana ta faduwa, tsoro duk ya baibaye ta, ba ta san ta inda za ta fara ba sam, idonta ya ciko da kwalla, a haka suka kwashi tsawon minti goma’ bai damu da zamanta a gurin ba balle har ya nuna yasan tana zaune. .
Ta daure ta tattaro dauriya da Kyar tana in’ ina, tace
“Idan babu damuwa daman’ ina son yin magana da kai”.
Ya gyara computer din ya tsareta da idonsa, wanda ke tsoratata wani lokacin idan ya tsare gida.
Gabanta kuwa ya ci gaba da faduwa, ta yi saurin sunkuyar da kanta tana fargabar abin da zai fito daga gunshi.
A niyyarshi ceW‘a zai bai da lokaci, domin aiki yake Amma yanayinta gaba daya sai ta ba shi tausayi, don haka ya daure yace. “Sai dai kada ki ja lokaci don. ina da abin yi, minti biyar ai ya ishe ki k0?” Da sauri tace, “Hakan ma yayi, na gode”. Ya; kuma tséreta da idanu wanda ya sanya ta kasa daga kai ta kalle shi, ya’ce, “Ina jinki ki , fadi abinda ya kawo ki”. a , Yanayin yadda yake maganar ke fadar mata da gaba, don babu wargi cikin muryar tasa. Tana wasa da yatsunta idonta har ya fara » zubda. Hawayen data taru tace“Daman naga kwana biyu kamar ka sauya ne, shi ne na ce bari na tambaye ka k0 wani laifin na yi maka”.
Ya kuma hade rai ya ce, “Ban gane na sauya ba, ci k0 sha k0 suturu na daina ba ki, k0 kuma daina kwana na yi a gidan k0 dakinki?”
Yanda ya furzo maganar ka san ransa a tsananin Bace yake, hakan ya sanya gab d‘aya ta firkice ta ras abin da zatace tabbas cikin abin daya lissafa babu daya wanda ya daina mata, amma ya daina walwala da sakin fuska, hatta kannensa sun fahimta
Ya daka mata tsawa, wacce har ta firgitata yana fadin.
“Kc nake saurare malama ki gaya mini mena rage ki cikin abin da na lissafa?”
Da shesshekar kuka tace, “Babu ko daya, amma daman… ai gani na yi kamar ka rage walwala da nishadi ga kuma…”
Ta yi shiru ta kasa karasawa saboda yadda ya tsare ta da idanunsa duk da ba ta daga kanta ta kalleshi ba. ,
Cikin kausasshiyar murya mai fidda zafin
sauti yace, “Kuma me? Ki fad‘a mana”. ‘ ‘Jin .ta yi shirun ya sanya shi ya kuma harzuqa ya fara banbami kamar dama jira yakeyi
“Kawai shi ke nan sai na shigo na yi ta miki dariya kamar wani mahaukaci k0 shashasha… Don Allah idan abin da ya kawo ki kenan zan ci gaba da aikina, please”.
Gaba. daya jikinta yai sanyi hankalinta ya yi mugun tashi yau ita malam kewa korar kare, idanunta suka ci ga‘ba da zubar da hawaye, lallai malam din nata ya“ sauya gaba daya, haka nan ta mike jikinta sanyi kalau ta nufi dakinta,
zuciyarta tana tafasa da ‘radadi
Bai k0 daga kai ya dubeta ba, ya ci gaba _ da aikinsa, domin sai ’ya tsinci kansa a cikin tsananin jin zafinta, da kalamanta, tamkar ta tunzura shi’ ransa ya dinga suya; gaba saya sai ya ji aikin ma ya fice daga ransa, don haka ya kashe laptop din ya dauki hularsa dake gefen gadon ya sanya ya dauki wayarsa da makullin motarsa ya fice
. . Falmata tana fita falo ta wuce ta yi tagumi cike da tunani, ta so shiga daki ta yi kuka k0 taji dadi, amma ta san tana shiga Jidda zata bi ta ta isheta da tambaya, don yanzu haka‘ tana wanka ne da ‘zarar ta dito zata fara nemanta, sai ‘ta san tana dakin malam sannan zata hakura ta zauna ta ci gaba da kallo don wannan shi ne lokacin kallo da hirarsu, don malam yakan yi aiki a irin wannan lokacin. ‘
Tana zaune ta jiyo alamar tafiyarsa gabanta’ ya ci gaba da faduwa har zuwa lokacin da ya bayyana a falon. A yadda ta ganshi ta san . shirin fita ya yi, da zata iya cewa zata yi ina kuma zai je, sai dai ba zata iya ba din, don haka cikin ladabi tace
“A dawo lafiya, Allah ya tsare”
Bai waigo ya kalle ta ba balle har ta sanya ran zai amsa ya bude kofa yayi ya fice abinsa.
Ta bi shi da kallo cike da Kunar zuciya, hawaye na ci gaba da gangarowa daga, idonta, to me ta yi wa bawan Allah nan da ta cancnci , wannan wulakancin? Tabbas wani lokaci hakuri , kan zama ciwo, domin da ace zata iya yau da babu inda zai fita kwata-kwata. Jin hargowar .’ fitowar Jidda ne ya sanya ta goge idonta da sauri ta fara kakalo murmushi. . ‘ Jidda ta iso da kaset a hannunta tana fadin,
“Anti Falmata kina dakin Yaya malam na je na amso mana fun din nan, da _ake ta tallansa UWARGIDA wanda marubuciyar nan da. nake bala’rin littattafanta Fauziyya D. Sulaiman ta rubuta.” . . Duk da ranta a Bace yake, sai da taji dadi domin sun jima suna jiran film din nan domin suna son su ga irin rubutun da Fauzan ta yiwa shirin, shin ya kai littafanta kyau da dadi k0 kuma bai kai shi ba, ko kuma rubutun fin din yafi littafin nata kyau.
Da doki tace, “Yauwa kanwata kunna
mana mu gani”.
Da hanzari Jidda ta fara kokarin sanya musu
Shi kam Mukhtar k0 da ya fita bai san inda za shi ba, shi dai kawai yaji zuciyarsa tana kuna da suya, sannan tana azalzalarsa ya bar gidan kawai. Yana fitowa kuwa ya ji sanyi a ransa, ya dinga zagaya titi kawai yana kalle-kalle, daga jarshe sai ya tsinci kansa da nufar gidan Fatila, kamar wanda ake ba shi umarni ya bude gidan ya shiga sam babu kowa.
Sai ya ji kewar gidan kawai ta kama shi, ya nufi dakin baccinsu ya tsaya tsawon lokaci yana karewa dakin kallo, sai ya nufi gadonsu ya kwanta yana kallon silin, ba zaice ga tunanin da yake y‘i ba, da farko haushin rashin kwashe kayan da iyayen Fatila basu yi ba yake ji, amma sai ya tsinci kansa yanzu da murba da ba su debe ba din. Haka ya dinga juyi a gadon har bacci ya dauke shi, domin ya sami tsananin nutsuwa, sai wajen sha biyu da kwata ya farka a firgice yana kallon agogo yaji gabansa ya fadi. Da suri ya tashi ya fice ya nufi gidan Falmata.
Su kam a can, tun bayan da flm din UWARGIDA ya kare suka fara tattauanawa a kansa cike da murna can kamar ance Falmata ta kalli agogo, sai ta ga sha daya da kwata na dare, duk sai hankalinta ya tashi, domin ta san mijinta bai taba kaiwa wannan lokacin a waje ba, idan ranar da zai kwana gidan Fatila ne tun takwas zai zo ya yi mata sallama ya tafi idan kuma ranar girkinta ne karfe takwas idan ya dawo ba ya fita sai dai idan ta kama, kuma idan ya fita din ba ya jimawa zai dawo, duk inda ya kai karfe goma zai dawo gida duk inda yaje kuwa. . ‘
. Cikin dabara da wayo tace da Jidda, “Ke bari naje na kwanta bacci na keji”.
Jidda ta kalle ta sai ta dan karanto halin da ta shiga, ta kalli agogo tace,,“Anti Falmata yau ina Yaya Malam ya shige ne har yanzu bai dawo ba, lafiya? K0 kiransa zaki yi a waya kiji?”
, Ta’ yi kokarin kakaro murmushi tana
fadin. “Lallai kallo ya dauke miki hankali, ai d‘azun ya yo waya muna kallo ya ce zai je wani guri zai dan jima”.
Jidda ta ce, “Auho, yanzu na ji magana nima bari naje na kwanta”. Ta nufi. akinta.
Falmata tayi shieu a falon cike da damuwa akan karyar da tayi ta dauki wayarta tana jujjuwa ko kiransa zatayi ta ji inda ya tafi?_ Gaskiya bai kamata ta kyale shi haka ba don haka ta fara neman wayar tashi, sai dai duk Wayoyin nasa a kulle ta ji su, don haka dole ta hakura ta nufi dakinta ta sake yin wanka da sauya kayan bacci ta kwanta gefen gado tana ta addu’o’i a cikin zuciyarta, Allah Ya sanya lafiya yake ba wani abu ne‘ ya tsaida shi ba. ‘
Sha biyu da rabi harda mintina ta ji alamar .shigowarshi cikin gidan, ta mike da azama tana lekensa ta windo, babu wani abu da ya same shi domin kalau yake har ya fito daga motar ya maida gidan ya kulle tana kallonsa.
‘ .Ta zauna a gefen gadonta ta yi shiru tana jiran .shigowarsa, sai dai tsawon lokaci ba ta ji-ba, har tai tunanin ko ya yi kwanciyarsa a dakinsa ne, ta san dai nan dakin nata yaje zuwa su kwanta, amma sai ta dakewa zuciyana kawai ta . kwama ta runtse idonta katamau, fatanta bacci ya dauke ta kawai take k0 ta huta, sai dai babu alamun bacci a idon nata, kai har ta gaji da jiran nasa ta yanke shawarar nufar dakin nasa ta ji ya shigo
Dakin nata da sallama.
‘Ta amsa murya da sanyi taga ya dan tsaya turus cikeda mamaki, mamakinsa b‘ai wuce tadda ita ido biyu ba har lokacin, kamar ya tambayi dalilinta na kin yin bacci, amma ya kasa kawai sai ya nufi gadon ya kwanta can nesa da-ita.
Idanunta suka dinga zubda hawayen tausayin kanta, da wannan sabuwar rayuwar da suka shiga ita da m_jin nata mutumin da karfe goma ya kai a waje ya dinga ba ta hakuri da kawo uzururirrika, amma yau ko kallo ma bata ishe shi ba har ya kai karfe daya na dare a waje.
Sautin numfashinshi taji alamar bacci ya d‘auke shi ta jiyo, ta tashi zaune ta kura masa ido, baccinshi ya ke lafiyar Allah bai da darnuwar komai. Ta duba agogo ta ga karfe d‘aya har da kusan minti hamsin da uku, kawai sai ta nufi bandaki don daura alwala ta yi sallah ta kuma sanar da Allah halin da take ciki.
******************
Su Fatila kam sun dage aiki suke yi matuka akan bayin Allah da ba su san da zamansu ba. Sunci nasara akan malam domin
duk ‘da dumbin ilimin da yake da shi bai da maida hankali akan addu’ar kariya da karya sammu kamar Falmata, don haka shi kam Sun fara tasiri a kansa, domin ko kallon Falmata ya yi sai yaji wani kunci da radad‘i a zuciyarsa, haka kawai yake jin haushinta, sai kuma yayi ta begen gidan Fatila kullum sai ya je duk daran Allah.
Sannu a hankali ma sai ya fara jin tunaninta a ransa, har yana ganin abin da ya yi sam bai kyauta ba, ‘amma dai bai ji yana ci gaba da sha’awar zama da ita ba sam
Falmata kam tana Kokari da shanye duk abin da yake mata, daman ta san aure ibada ne, don haka ta shirya samun aljanna ta nan ba ta taBa sanar da wani halin da ta ke ciki ba, ta yi alkawarin ma ba zata sanar ba. Jidda ce daman mai kula da wasu abubuwa nata to a satin ya kawowa Jidda admission latter ta N.C.E a nan inda yake koyarwa, wato Legal, don haka tuni har ta fara shirye-shiryen fara zuwa lecture domin ya gama mata komai, sai abin da ba a rasa ba da dole sai taje da kama.
Sati uku ma ta fara tafiya lwcturc don haka duk wasu abubuwa na gidan ba kulawa dasu takeba
kamar can baya.
Sati uku k’enan rabonta da awo, wanda ya dace ace sati biyu da suka wuce taje, domin . cikin ya shiga sati na talatin da bakwai don haka ta koma sati-sati k0 da ta tuna masa da maganar kai ta din sati biyun da ya wuce sai yace yana sane zai kaita abubuwa ne sukai masa yawa, amma har Satin yaci ya cinye bai kaita ba, wani satin ma ta kuma tuna masa nan ma cewa ya yi ._ yana da aiki ta yi hakuri.
Duk abin duniya -ya ishe ta, ga rashin bacci, ga ciwon kai, sannan’ ga kafarta ta yi ‘kumburi ‘har fuskarta don haka ta keson ta ga likita ya dubata don ya tabbatar da abin da ke damunta, amma sam ta kula shi k0 a jikinsa, duk wata kulawa da taga ana bai wa mai ciki sam ya daina bat sai dai taci kukanta ta more.
Yau kam ranar zuwan awon ne don haka tun da ta kammala girkin dare ta shirya da yake da daddane take zuwa awon saboda asibitin na kudi ne, ta zauna a falo tana jiranshi ya fito daga daki bayan ya kammala cin abinci ya shige dakinsa.
Ta kuma gaya masa maganar awon tunda safe yace Allah Ya kaimu,daren”. Don haka tasan yana sane. ‘
Can kuwa suna zaune suna kallo ana ta fada tsakanin Hashim da jidda tana dariya, amma rabin hankalinta yana kan kofar dakin nasa. Ya fito yana zabga kamshi, ranta ya yi fari domin ta san kai ta ya fito yi.
Ta mike da hanzari tana fadin, “Yaya na taho ne?”
Ya waiga yana mata wani duba, yace, “Ban gane ba, ki taho ina?’
Duk jikinta yai sanyi, su kansu Hashim da jidda ba suji dadin yadda ya amsa mata din ba, amma sai suka nuna kamar Ba su jiba, suka ci gaba da kallon talabijin din kawai.
Ta dan‘ waigo ta kalle su sannan ta ce dashi. . ‘ .
“A’a, daman maganar zuwa asibiti da ‘ muka yi da kai da safe kace na shirya za mu”.
Ya gade rai matuqa, “Amma tunda na dawo baki tuna min ba sai da kika ga na shirya zan fita? Gaskiya akwai wani guri mai muhimma‘nci da zani. amma tinda kin matsa da maganar zuwa asabitin ga kudi nan ki tari adaidaita sahu Jiddah sai ta raka ki” .
Ya zaro dubu daya sabuWa ya ajiye mata akan kujera, mamaki mai tsanani ya cikata, malam din da bai san k0 da rana ta hau motar haya ko’ina ne ya gwammace ya kaita, amma yanzu da daddare yace wai ta hau motar haya? Tsananin mamaki ya sanya ta kasa cewa komai, domin tana mamakin muhimmancin inda zai je da har yafi ya’ kai ta’asibiti a binciki lafiyarta bayan ta gaya masa halin da ta ke cilci.
Ya waiga ya kalle ta. jin ba tace masa
‘ komai ba, yace, “Yaya‘ naji kin yi shieu, k0 ba ki , yarda da abin da nace ba ne?”
Da sauri tacc, “A’a ba haka bane, a dawo .lafiya”_. . ‘
Ya sanya kai ya fice yana fadin, “Amin”.
. Ta koma kujerar ta zauna jikinta da sanyi qalau, tabbas banda tana son a duba ta sosai da ~ba zataje asibitin ba, amma ya ya ta iya, dole ta je din.
. .Tausayinta ya cika Jidda da Hashim duk .
Da basu zama a gidan sun kula da rayuwar gidan
gaba saya ta sauya, sam kosu ba ya sakar musu . fuska kamar can baya.
Hashim ne ya fara magana, “Anti kinsan
inda makullin motar can tasa Honda CiBic yake idan kin sani dauko kawai na kai ku, domin na san ba ita zai hau ba”.
Falmata tayi yake, tace Na san inda yake, amma bai dace mu hau ba tunda bai bada umarni a hau d‘inba, gwara mu tafi a wacce ya amince din”.
Hashim yace “Amma ai bai dacw akwai mota a gidan nan a ganki ata haya ba, kawai ki d’auko na kaiki din”. ‘ ‘. ‘
Ta mike tan fadin, “Lallai yaeo baka san sharuda da dokokin aure ba, ai a kan sabawa wannan umarnin ‘nasa sai Allah ya jarrabe mu da wata masifar, gwara dai mu bi umaeninsa kawai”.
Hashim ya yi dariya yana fadin, “Kai Anti Falmata yau ni ne yaron, kin san fa a lalace na baki shekaru sunfi bakwai k0 biyar k0?”
Sukayi. dariya gaba dayansu, Jidda na fadin, “To gyanbo sarkin son giema, sai kaje kai ta tara shekarun”.
Ya harare ta yana fadin, “Bani da lokacinki yarinya”. ‘
Ya kalli f‘almata, “To baei naje can babban gida na dauko mota sai na kai ki”.
Ta‘ kwantar da murya tace, “Ka yi hakuei‘ Hashim dare ya yi mana, wani satin sai ka dauko motar gid‘an ka kai ni” .
Ta kalli Jidda tace, “Taho mu tafi kada dare ya‘yi” .
Hashim yace, “Har dani fa za a tafi, ai ba zab yarda ku fita a wannan daren ba ko domin kada wasu su kalle mini amaryata”. Ya kalli jidda yana dariya, wacce ta dalla masa harara ta wuce da sauri ta dauko gyalenta.
Sunyi sa’a kuwa suna isa bakin titi suka
sami adaidaita. sahusuka je asibitin. ‘ Ba su jima ba wajen karfe tara da wani abu suka kammala suka juyo. Sai dai gurin komawa suka rasa mota, da kyar suka sami wata tasi, yacw shi ma sai dari takwas zai kai su. Haka suka hau don sun gaji da jira ga dare ya yi goma da wani abu suka isa
“A cikin gida a falo suka tadda shi ya cika fam, suna shiga ya kama fada wai sun dade me suka tsaya yi haka, duka awon minti nawa aké”yi?
‘Falmata kam shiru ta yi ta kasa cewa komai, domin fadan nasa ya yi yawa, Hashim ne
Hmmm please 🙏 idan har kunason wannan book din ya dinga zuwa muku kan lokaci ku dinga farantamin rai da ruwan comment abinda nake buqata kawai kenan