MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 27

MATACCIYAR RAYUWA 
CHAPTER 27
daure kai, k0 tun tsawon yaushe ya maidata?” 
“koma yaushe ne shi ya sani, bari yazo ya bani takardar Falmata, gwara na maidawa mahaifinta diyarsu tun ciwon zuciya bai kama musu ‘yaba, shi kuma yaje ya yi ta zama dasu Kumatu, babu ni babu shi har abada!” 
Hajiya Babba tace “Don Allah ki daina fadin wadannan maganganun, domin muddin Falmata ta rabu da Mukhtar a yanzu burin su Kumatu ya cika, za kuma su cika bdki da ganin malaman tsubbunsu suka basu nasara, gwara dai a dage da rokon Allah kawai”. 
Da kyar Hajiya babba ta samu ta shawo kanta akan a kirawo Mukhtar :aji ta bakinsa, sannan a tsananta sanarwa da Allah har Ya kawo Karshen abin. 
Yana ta shirin tafiya OfiS, Fatila ana ta taya shi shiri, wayarsa ta kama Kara. Ya mika hannu ya dauka. Gabansa ya yanke ya fadi ganin lambar Hajiyarsa, gaba daya sai Fatila ta hade rai domin ta ga sunan mai kiran wayartashi,hanka1inta ya tashi kamar tace kada ya daga kiran 
Ya kara wayar a kunnensa da ladabi yace
“Hajiya an tashi 1afiya,yanzu nake shirin 
Nazo
Hashim ya katse masa maganar yana fadin“Ba hajiya bace, nine Yaya Malam, amma Hajiyan ce tace a sanar da kai kazo gida yanzu yanzu tana son ganinka”. , 
Gabansa ya kara faduwa yace“Lafiya daiko ?” ‘ 
Hashim yaji kamar yace, kai ka san wannan, amma sai ya dake domin yasan duk abin da yayan nasa yayi bai isa yayi masa rashin kunya 
ba. Yace ‘lafiya lau, idan kazo kaji k0 menc ne”. Ya kashe wayar. 
Mukhtar ya kashe wayar shi ma jikinsa sanyi kalau. Fatila ta tsare shi da ido, “Wai laflya naga gaba daya yanayinka ya sanya?” 
Ya yi saurin’ wayancewa yana fadin, “Lafiya kalau bari .na flta Hajiya tana nemana a can babban gida, Allah dai ya sanya ba wani munafukin ne ya sanar dasu komenki ba. Nafi son sai an dan kwana biyu na sanar dasu da kaina” 
Kafin ta kaiga ccwa wani abu ya fice da hanzari. Ta bi shi da kallo cike da zancen zuci, shin me ya dace ta yi ne? Sai ta dauko wayarta ta ‘sanar da mahaiflyarta abin dake faruwa. 
Shi kam da hanzari ya isa gida, lokacin Hajiya maria na zaune ta cika fam, 
domin tuni Hashim ya gudu don kada a huce a kansa. 
Ya isa ya durkusa yana gaishe da ita cikin girmamawa, jikinsa da sanyi don ganin yadda ta hade rai. 
Bata amsaba sai hannu data miqamasa tana fadin, “Bani takardar sakin Falmata”. 
Ya waro ido waje tamkar wanda sanarwan mutuwa ya riska,shi da kyar ya iya daurewa yace Hajiya kin ji abin da kika fadi kuwa?” 
Ta kuma fusata, tace“Ban sani ba ai kasan nayi hauka ne irin wanda kayi, azzalumi mai cutar da diyar mutane. Wallahi Mukhtar kaji tsoron gamonka da Ubangiji”. 
Sai a sannan ya gano laifin da ya aikata, babu dar a jikinsa yace
“Hajiya tace miki bana kwana a gidan ne k0? Amma ba ta gaya miki laifin data keyi ba, wallahi Hajiya kije gidan zaki tabbatar da duk wanda ya kwana a ciki sai dai a dauki gawarsa da safe ya kumbura saboda wari‘. Wata irin kazanta ta koyo yanzu k0 kusa daje ta tsaya sai kin ji wannan warin”. ‘ 
Hajiya ta kalle shi da tsananin mamaki. ‘ta kula maganar da yake fadi hakan take har cikin ransa, take ta gano asirin jaba k0 mushen jaki akayima Falmata, basu gano ba amma da yake tana kufule da shi taci gaba da fad’a. 
“Da ka san haka ne ai sai ka sauwake mata. ka huta tunda baka da uwa balle uba a duniya k0 wani dangi da zaka iya sanarwa da abin da kake ciki”. Ya kwantar da kai cikin sigar rarrshi, yace
“Ki yi hakuri Hajiya, tabbas nasan nayi laifi…” 
Ta doka masa tsawa, “Kada ka kuma kallona ko kirana a matsayin mahaifiyarka daga yau babu ni babu kai, na zareka daga cikin ‘ya‘yana, kaje su Kumatu sun ishe ka rayuwa…” 
Muryar tata ta fara rawa kamar zata yi kuka, tayi shiru tare da kawar da kai gefe guda. 
Hankalinsa yayi kololuwar tashi, tabbas yau ya kai mahaifiyar tasa karshe, idan ta sallama shi ya shiga uku. Ya kara kwantar da kansa ya fara bata hakuri, amma ba ta saurare shi ba 
Daga karshc ma ta fatattake shi da kada ya kuma zuwa inda ta ke
Yana fita ta kirawo Malam Nura wani almajirin mijinsu neda ya shahara akan harkar ilimin addini matuka, sunansa yaje ko’ ina a 
 duniya. Da hanzari’ ya je gidan, domin bai manta d’umbin alkhairin mutan gidan, bayan sun gaisa ta sanar dashi duk abin da ke faruwa cike da bacin rai. Ya yi shiru yana nazari, can yace
tabbas akwai alamomi na sammu a ciki, amma abin da za a yi yanzu ki shirya kije gida“, duk yanayin da kika tadda gidan sai ki sanar dani, ni kuma zanzo”. 
. Da haka suka rabu yana fita ta yafa gyalenta ta nufi gidan Falmata tare da Hashim dake can dakinsa na gidan yana jiran abin da zai faru. 
‘Sun tadda Falmata baiwar Allah tana ta gyaran gida wanda yake Kamshi, k0 gaisawa ba su yiba Hajiya ta kira wayar Malam Nura tace
“Malam gani a gidan baya ga kamshi ban ji komai ba. Tabbas shi kadai yake jin warin nan”. 
Malam Nura yace “Gani nan zuwa, amma abin da nake bukata maza a fito da kayan gidan 
gaba daya, idan kun kammala ku sanar dani zanzo da kaina yanzu”. 
Hajiya ta amsa da, “To”. 
Sannan ta sake kiran waya gida tace da Hajiya Babba saurayin dake cikin gidan yazo
tana son ganinsa a gidan Mukhtar. Kan kace kwabo sai ga mutum uku sun iso, lokacin ta sanya Jidda da Hashim sun fara fita da kayan gidan, ita da Falmata da Muhammad suna can bayan gidan tana ta yiwa Falmata fada kamar zata rufe ta da duka ita dai Falmata hakuri taketa bayarwa tana zubda hawaye, da ace yadda surukarta ke sonta haka mijinta ma ke sonta tabbas da ta more a rayuwa, sai dai an sami akasi su ke son zaman su ‘ ba shi ba. ‘ 
Kafin karfe daya sun flto da komai na gidan aka sanar da Malam Nura ya iso gidan da ruwan addu’a ya dinga yarfawa bayan an share gidan tas, bar wasu layu da wasu cire-ciren abu mai kama da bishiya aka tidda, bandaki ne kadai ba a yarfawa ruwan addu’a ba, suka koma can bayan gidan suka shim‘flda tabarma, a nan suka ci abinci da yake gurin akwai inuwa, sai‘ da gidan ya bushe gaba daya sannan aka maida kayan, Malam Nura tuni ya tafl ya bai wa Falmata Karin wasu addu’o’i akan wanda ta keyi, domin ta yi masa bayanin wanda ta keyi. 
Hajiya da jama’arta ba su sami barin gidan nan ba sai bayan sallar magriba, lokacin an maida komai zannuwan dake shimfide a gadajen duk an kulle ta tafi dasu, tace da falmata idan yazo gidan yadda suka yi ta sanar da ita. 
Shi kam malam Mukhtar yau kasa komai yayi a ofis dinsa, sai zancen zuci tabbas ya san illar fushin iyaye ga ‘ya’ya, shike sanar da wasu ma, sai dai shi ya rasa abin da ya sanya kullum yake saBawa mahaifiyarsa, har sai da yayi kuka yana rokon Allah Ya yafe masa, ya kuma yi alkawarin yau zai kwana a gidan Falnata k0 da zai mutu ne kuwa, in dai shi ne laifin da ya aikata mahaifiyarsa tayi fushi haka da shi, ta daina. Don ya san in dai ba ta daina fushi da shi ba ya shiga uku, don haka ana tashi daga ofis kai tsaye gidan Falmata ya wuce. . 
Duk da sai daya Bata lokaci a OflS ya kai har dare domin ya dan sami nutsuwa a ransa. 
‘ ‘ ” Suna zaune a falo suna kallonsu ita da  jidda . . suka jiyo ana kwankwasa kofa, k0 kusa basu kawo malam bane, domin ta sanshi sai dai ya tsaya cikin mota ya kirata don haka Jidda ce ta mike tana t’ambayar waye? Tana bude kofa sai ta ga malam _ tsaye‘kyam, kirjinta ya buga cike da mamaki, tace, “Sannu da zuwa”. Ta mike da sauri babu k0 waige ta nufl sashinta. 
Falmata kam daga kai tayi da niyyar 
tambayar Jidda lafiya, sai ta hango mutum tsaye a dokin kofa, ta mike tsaye a firgice kamar wacce aka tsirawa allura, shi kam tsaye yayi a bakin kofar yana shakar iskar gidan daya. tsana, sai dai ga mamakinsa yau kam babu wani wan’ k0 hamamin da yake ji sam, falmata ta isa da sauri bakinta yana rawa tace, “Sannu da zuwa”. 
Ya kalleta sau daya yace, “Yanwa”. 
Ta mika hannu ta amshi jakarsa amma sai ya wuce ciki ya barta tsaye, duk da hakan taji dadib yadda ya shiga din tabi shi da sauri sai dai kafin taje ya datse kofar dakinsa. Ta yi tsaye cike da fargaba kamar ta buga sai ta ga rashin dacewar hakan, don haka ta koma ta zauna taci gaba da kaIlon da sam hankalinta ba ya kansa. 
Ta jima a zaune har ta fara gyangyadi amma ba taji ya bude kofar dakin nasa ba, dole ta hakura ta dauki Muhammad dake bacci akan kujera, suka nufi daki. Ranar kam sai da ta yi sallah ta yi godiya ga Allah da Ya sanya mijinta ya dawo kwana a gidanta. 
Fatila kam tunda yamma tayi mijinta bai dawo ba, kuma bai kirata ba ta sha jinin jikinta, domin tasan zuwansa gidansu ba alkhairi ba ne, sai dai tunda dare ya yi hankalinta ya kuma tashi
 bakin cikinta saya kada aoe yana gidan Falmata 
Ai kuwa sanda ta bincika aka sanar da ita yana can din, gashi duk ya kashe wayoyinsa. 
Malam yana shiga dakinsa ruwa ya watsa ya kashe wayoyinsa ya haye gado nan da nan wani bacci mai dadi wanda ya jima bai yi ba ya dauke shi, rabonda yayi bacci irin wannan harya manta
F atila kwana ta yi tana kuka da buge-buge, don kaninta da ta tura ya gano mata k0 yana can gidan ya tabbatar mata da yaga motarsa a gidan, hakan ya sanya ta tabbatar yana can din, wato aikin da suka yiwa gidan ya karye kenan, domin boka ya tabbatar musu shida Kara kwana a gidan har abada ko da gawarsa aka kai gidan sai ta yi tsalle ta fice sai kuma ga shi da ransa ya kwana, (Allah Ya fusu ke nan). 
Da sassafe Falmata ta fara shirya masa kari, tayi sa’a kuwa Muhammad yana ta baccinsa, abin da ya bata mamaki da sanya ta jin dadi bai wuoe gapin yaci abincin da tayi ba sosai tamkar wanda ya kwana da yunwa, koda yake da yunwar ma ya kwana tunda bai ci abinci ba ya kwanta, ya kuma ‘ amsa gaisuwarta har da cewa, ta jeta dauki Muhammd . a daki yana kuka Tana ta sauri
shirya Muhammad din ta fito ta tadda ya flce, k0 dai hakan aka tsaya ta godewa Allah. 
Can kuwa kiran Hajiya ya shigo ta dauka tana. dariya tana fadin hello Hajiya tana ji dani wallahi”. 
Suna gama gaisawa tace“Ya ya?” 
Ta yi murmushi tace “Hajiya a gidan Ya kwana har yai karin kumallo ma, yanzu ya fita daga gidan”. 
Farin ciki ya cika Hajiya, tace“Ki gaya min gaskiya fa, idan kika min karya ni da kene falmata”. 
. Ta cw Wallahi da gaske Hajiya, ta tambayi Jidda da Hashim ma”. . Da haka suka yi sallama ran Hajiya yayi wasai. 
Tun daga wannan ranar ya koma rabon kwana, idan ya yi kwana biyu a can yayi a nan ‘ duk da sun‘ sha dumburwa da tashin hankali da Fatila, sai da taga babu Sarki sai Allah sannan ta hakura taci gaba da kulle-kullenta don ta tabbatar ko zata rasa ranta sai Mukhtar ya rabu da Falmata, taci gaba da yin rayuwarta ita kadai. 
Shi kam Mukhta: idan akwai abin dake damunsa bai wuce fushin da mahaiflyarsa keyi da shi ba, duk yadda yaso rarrashi da ba ta hakuri abin ya faskar, ya hada ta da duk wanda zai iya shi ma a banza, sai da ya yiwa Abbagana waya ya sanar da shi halin da ake ciki sannan ta hakura amma duk da haka bata sakar masa fuska sosai, sai dai tana sanya ido a gidansa sosai. 
*** *** 
Sai dai wani’ abu da kowa bai sani’ ba sai Falmata duk tsawon zaman da sukeyi Malam bai taba kwana a dakinta ko ya ,kusanceta ba, ga shi hqr,an kusa shekara guda, yakan yi mata duk wani abu da ya dace miji ya yiwa matarsa na biyan bujatar zahiri har dasu hira, amma ya kasa kusantarta sam, sai ya dinga ganinta tamkar kaninsa Hashim, babu wani abu da yake ba shi sha’awa game da ita sam. 
Wannan kuma yana daga cikin mugun aikinsu Fatila Wanda b’ai karya ba, Fatila kuma ta fuskanci hakan duk da bai taBa sanar da ita ba daga yadda kullum idan ya dawo gidanta yake
yin kamar ita kadai ce matarsa. 
Tabbas abin yana damun Falmata, domin ita din ba karfe ba ce ba tana son ta ji mijinta a jikinta, shekara daya kuma ai ba wata daya bace. Lokuta da dama idan dare ya tsala son mijinta ya juyo mata sai ta tashi ta kama kuka, ko ta yi ta sallah, daga ‘karshe ,ta yanke shawarar binsa dakinsa. 
Wajen jarfe sha daya na dare ne ta shirya. Muhammad da yayi wayo an kusa yaye shi ma, ta nufi dakin mijin nata cikin wasu kayan bacci masu matukar kyau da d‘aukar hankali, wanda duk lafiyayyen namjin da yaga mace a cikinsa sai ta burge shi. ‘ ‘ 
Ta kwankwasa kofar dakin nasa gabanta yana faduwa, domin ta tabbatar bai yi bacci ba daga ciki ta jiyo muryarsa yana fadin. 
“Waye ne? Shigo”. 
Ta san yasan babu mai zuwa dakinsa a wannan lokacin idan ba ita din ba, ta tura kofar gabanta naci gaba da bugu. Yana kan kwamfuta ta girke yana ta aiki tunda shi agogo ne sarkin aiki, ta shiga da sallama ya amsa ba tare da ya kalle ta ba; 
Ta dan tsaya tana kallonsa taga bai kalle ta ba, sai ta wuce a hankali ta kwantar da Mdhammad a gadon.ta sami guri ta zauna. . 
Kusan minti goma suna haka,..can ya juyo ya kalleta, ya kalli Muhammad, mamaki ya bayyana a kan fuskarsa matuka, ya kalle ta yana fadin. 
“Laf1ya kika kawo mini danki dakina?” 
. Abin tamkar .shirin dirama wai danta yace ma, wato shi ba dansa babe kenan? Ya jima yana yi mata abubuwa tana shanyewa,. Amma _yau sai ta tsinci kanta da kasa hakurin zuciyarta 
ta kekashe tace “Wai kawo shi nayi yau ya dand’ana dadin 
mahaifinsa da bai sani ba ita da kanta ta yi mamakin yadda tayi karfln halin fadin wannan maganar. 
‘ Ai kamar jira yake sai cewa ya yi. OK rashin kunya kika shigo kiyi mini kwnan Ko ku hanani bacci keda d‘anki shin daman na taba ce miki ba dana bane balle har ki shigo kiyi mini rashin kunya?” 
Ta yi narai-narai da ido kamar zata fasa kuka. saita  dake ta kwantar da murya tace
“Malam ba rashin kunya bane, idan ba ka sani . ba ka sani, ni da Muhammad muna bukatar kulawarka, muna kwana kullum da kewarka’ don Allah idan munyi maka laifl ne ka yi hakuri”; 
Ai kamar ta watsa masa ruwan dalma, sai ya mike ya fara masifa da fadar maganganu. 
“Kinga ban gayyace ki ba, ba kuma na sha’awar kwananku a cikin dakina, ban dake sokuwa ce kin taBa ganin inda mace ke bin namiji yana yakice ta? To yau na gaya miki na . gaji, idan kuma kinga zaki je ki kai Karar tawa ne bismillah”. 
Idonta ya kankance tama rasa abin da zata ce da yake ba rashin kunyar ta iya ba, sai kawai ta fashe da kuka mai tsanani, domin ba tasan me zata ce ba. 
Ya doka mata tsawa, “Ban nemi ki min kukan munafunci ba ki dauki danki ki bar mini dakina‘malama, kin katse mini aikina”. 
Ta sungumi Muhammad tayi waje tana ci gaba da kuka. Ya bita da kallo sai kuma yaji tsananin tausayinta ya rufe shi, bai san daliliq da ya sanya yake mata haka ba, sam ya kasa iya rike kanshi da zai iya yanzu kamata yayi yaje ya bata
hakuri, amma sai yaga ba zai iya ba, sai zama Yayi a gefen gadonsa ya dafe kansa cike da takaici. 
Hmm anan muka kawo karshen MATACCIYAR RAYUWA BOOK 📚3 
Mu gamu a littafi na 4 kuma na karshe. 
Domin ci gaba da sauraran wannan qayataccen littafin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *