MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 17

MEYE ILLAR YAYA MATA
 CHAPTER 17
Aneesa ce ta shigo cikin d’aki tana Murna magajiya tace Yadai Aneesa? Aneesa tace kin San duk wani abu da faruk yakeyi ni nake sashi yayi, dan kawai ya mallaki dukiyar nan, gashi can yanzu suna mishi signing jin karan motsi yasa sukai saurin flta mama suka gani wacce take sauri kuma daka ganin saurin da take taji abunda suke fad’a, da sauri Aneesa ta Fara nufanta mama ta fara kokarin sauka zuwa ‘kasa aiko Aneesa ta turata ta Fara gangarawa zuwa kasa, Tana turata tayi sauri ta koma d’aki ita da magajiya, Bayan sun gama signing d’akin faruk din suka nufa suka bashi takardan yaji dad‘i Sosai tare da fad’in zai rikesu dakyau fira suka zauna suna tayi Jin kaman karan Abu ya fad’i ga kuma ihu da sukaji yasa suka fita da gudu, aiko suna fltowa suka hango mama a kasa jini na zuba ta kanta cikin tashin hankali suka nufeta duka sukai ‘kasa faruk ne ya dauketa aka sakata 3 mota suka nufi asibiti suna zuwa akai emergency da ita, kowa dake gidan yazo asibitin ciki harda Aneesa wacce bata bari sun ganta ba ta samu ta shige d’akin da aka kaita, likitoci ne tsaye akan mama suna dubata domin ta bugu a kanta Sosai, sunyi Sa’a numfashinta ya dawo dai dai amma duk da haka ba’a cire oxygen din ba, Dr ne suka fita Dr na fita Aneesa ta nufeta tana kokarin shage mata wuya jin ana bude kofar yasa ta koma ta boye da sauri, wanda dai dai lokacin mama ta bud’e ido kuma yayi dai dai da shugowar su ummi da sauran iyalan gidan, mama tana ganinsu ta Fara tambaya Ina Ibrahim? Kallon juna suka fara suna mamaki, jin haka Dr yace su fita ya dubata flta sukayi suna mamaki Jim kad’an Dr ya fito inda yake shaida musu tayi loosing memory dinta bazata iya tuna abunda ya faru da ‘Ita baya na shekara d’aya ba, ciki kuwa harda mutuwar d’anta dan haka Kar kuyi wani abu da zaku dinga tuna mata dan Idan tasan d’anta ya rasu komai zai iya faruwa saiku kiyaye, suka amsa da Toh jiki a sanyaye, Aneesa najin haka ta samu ta fita dakyar ta koma Gida cikin murna, mama da yamma aka sallameta dan babu inda yake mata ciwo su zainab ne sukai gaba Kafin su mama Su fito, gida suka nufa direct suna ta nocking kofar shiga aka ki budewa khairat ta Fara kiran Aneesa Aneesa kodai basa nan ne, sunyi wajan mimi Goma suna nocking Kafin Aneesa ta fito ta bud’e suna kokarin shiga Aneesa ta dakatar dasu tare da fad’in ina kuke kokarin shiga? Rahma tace gidan mu wannan wani irin tambaya ne haka? Aneesa tace gidanku a da ba amma banda yanzu dan haka yanzu gida nawa ne tunda na miji nane yanzu, kallon juna suka farayi cikin mamaki zarah tace Aneesa kin San abunda kike fad’a kuwa Aneesa tace inaga Kun kuramce amma Bari insa ku Fara ji, binta binta ta Fara kiran magajiya aiko magajiya daka sama ta Fara jefo musu akwatin kayansu matsawa sukayi dan Kar akwatin ya fad’o kansu, rahma tace Aneesa karki bari faruk ya ganki bazaki ji dad‘i ba, Aneesa ta kwashe da dariya tare da fad’in ku kalli can, faruk ta nuna musu wanda yake tsaye yana kallonsu, zainab tace faruk miye haka? Faruk shuru yayi ya kasa magana, ganin haka yasa aysha ta Fara magana tace Aneesa dan Allah kiyi hakuri yanzu za’a tawo da mama bama son tasan Mai ake ciki dan Allah, aneesa ta tabe baki tare da fad’in wannan damuwarku ce ba tawa ba, duka suka tsugunna suna ro’kanta amma ina kaman bada ita suke ba, tace in basu tashi sun bar wajan ba zata kira musu police, tashi sukayi dai dai lokacin mama suka karaso suka boye akwatinan su a baya, mama tace Mai kuke yi a waje? Aneesa tayi caraf tace mama muna jiran ku dawo ne mu tarbeku, mama tayi murmushi tace toh muje suka shiga ciki mama aka kaita d’akinta dan ta huta ana kaita Aneesa ta fito ta samesu a falo suna zaune akan kujera su duka, daka musu tsawa tayi Ummi da Amina suka bita da ido, Aneesa ta kalli ummi tace bani keys din duka gidan, ummi tace kaman ya? Aneesa tace saboda yanzu gidan nawa ne, ummi ta kalli su zainab wanda suma ita suke kallo, tace maike faruwa? Khairat tace hakane mum yanzu komai ba 
namu bane na faruk ne, Aneesa matsawa tayi kusa da ummi ta fisge keys din dake makale a wajan zaninta, tace zan barku ku zauna saboda mama in kuka saba ma umarnina zaku bar gidan nan sannan zan fad’a ma mama komai, ta kalli ummi tace ki kwashe kayanki dake d’akin alh Ibrahim domin nan zan koma da kwana ummi shuru tayi tana hawaye yau itace zata bar d’akin mijinta, rahma tace Aneesa kin San mai kike fad’a kuwa? D’akin Abba Din zaki koma? Dariya Aneesa tayi tace yes gida nane Ina da iko dako Ina, bari kuji in fad’a muku daka yau ku duka inda masu aiki suke kwana nan zaku koma sannan daka yau zan Kori masu aikin gidan nan dan banga amfanin zaman ku ba, zarah tace dakata Aneesa Mai kike nufi baki isa ki mayar damu bayinki ba, murmushi Aneesa tayi tace OK zan fad’a ma mama komai yanzu ta nufi hanyar d’akin mama da sauri aysha da khairat suka shiga gabanta tare da fad’in Mun amince da abunda kika tsara, dariya tayi tare da fadin good, maza aje Ayi min abincin dare nan da karfe 6 Ina son ganin komai a table, sannan a siyo min dodon kod’i Ayi min farfesun shi, haka suka amsa da Toh, kitchen suka nufa suka daura abincin dukansu kyamar dodon kod’i din suke domin basu taba ciba, gashi kuma yau suna dafawa, haka dai suka gama dafa abincin suka jera mata a dinning, Bayan sun gama jerawa Aneesa da magajiya suka zauna a table din, su kuma suka tsaya a ‘saye, ummi ta Fara zuba mata abincin sannan ta zuba ma magajiya zarah na zuba mata ruwa sai jin jifa sukai da plate din abinci a jikinsu duk ya bata su, aneesa cikin fad’a take fad’in wannan wani irin abinci ne mara test, haka ake girki babu Magi babu gishiri abinci salaf, Waye yayi wannan girkin? Ummi ce tayi girkin kuma aneesa ta Sani da gangan take tambayar amma ga mamakinta sai jin zainab tayi tana fadin nice nayi girkin, kallon zainab tayi cikin tsiwa da fad’a tace maza ku kwashe wannan ku cinye kuje ku dafa min wani yanzu yanzu domin yunwa nakeji, ke kuma zarah dauki yaro na ki bashi Madara yasha, zarah ta dauki yaron su kuma suka kwashe kayan abincin, basu dad’e ba suka gama dafa mata wani abincin, ci tayi tare da fad’in gwara wannan ta kalli magajiya tace binta ci mana, farida dake tsaye tana kallon ikon Allah tare da tunanin mai yasa faruk yama y’an uwanshi haka,ji tayi jiri na dibanta tazo zata fad’i faruk yayi sauri ya ri’keta Wanda lokacin yazo, cikin damuwa ya fara fad‘in farida lafiya kuwa, amma k0 gezau batayi ba, dan haka ya ciccibeta zuwa asibiti Aneesa kam dake zaune ba’kin ciki kaman zai kashe ta, zainab da khairat suka bi faruk asibiti sun bishi ne dan farida inda ba haka ba ko kallo bai ishesu ba suna zuwa gwajin Farko Dr yace ciki gareta harna wata biyu Faruk murna Sosai yake tare da gode ma Allah da yasa farida itama ta sami ciki, Suma su zainab sai murna suke, Dr yace amma ya kamata ta rage damuwa dan damuwa yayi mata yawa shi yasa harta fad’i in bata rage damuwa ba akwai matsala nan Dr Ya basu magani tare da bata shawarwari yanda zata dinga kula da kanta da cikin ta,faruk kam sai Washe baki yake, koda suka koma Gida suka fad’a musu nan suka fara murna Sosai, Aneesa kam kasa boye ba’kin cikinta tayi ta tashi ta haura Sama, basu ko damu da ita ba, 
Cikin zainab yana ta girma Sosai gashi kullum aiki suke kaman jakai babu ranan hutu, cikin masu aikin harda farida domin a wajansu take kwana yanzu dan a halin da ake ciki yanzu babu wanda ta tsana kaman faruk tare da takaicin shine uban d’anta, farida ce da ruwa ta dauko tana goge kan step tana dan hutawa dan bayanta yana ri’ke mata gashi ta gaji, faruk daya shigo gidan yaga yanda takeyi sai yaji wani iri, dan haka ya nufeta tare da fad’in farida bana hanaki wannan aikin ba karki manta fah yanzu bake d’aya bace, ko kallonshi batayi ba sai tashi da tayi ta nufi sama dan ta goge kofofln dakuna, binta yayi tare da ri’ke mata hannu yace farida bakya jina ne wai? Fincike hannunta tayi tare da fad’in karka kara taba ni, yace karki manta ni mijinki ne Ina da right inyI’ duk yanda naso, dan haka kibar wannan aikin kodan lafiyan d’ana dake jikinki, kallonshi tayi tace d’anka? Tunda nake a duniya ban taba takaicin wani abu ba sai yau, tabbas Ina ba’kin ciki daya kasance kaine uban d’ana ko y’ata, inaso daka yau ka sani koda na haiyu babu kai babu abunda na haifa domin bazan so d‘ana yasan kaine ubansa ba Ya gane mahaifinsa shine wanda ya cuci y’an uwansa ba, tana gama fad’in haka ta tafl ta barsa baki sake. Aneesa da magajiya ne zaune suna fira su zarah kuma nata faman goge goge zainab ce ta fito da cikinta da yayi girma tace khairat ina farida taje? Khairat tace Wlh ban sani ba kaman tana sama, zainab tace bata nan nan hankalinsu ya tashi suka fara dubata amma shuru bata nan, Aneesa kam ko kallo basu isheta ba, zarah ce ta kira faruk yana d’auka ta tambayeshi ko suna tare da Farida ne? Yace a’a maiya faru da ita? Tace tun dazu bata gida kuma bata fad’ama kowa inda zata ba, nan hankalin faruk ya tashi shima ya fara nemanta amma shuru Ummi tace masu zarah k0 za suje dubata? Aneesa ta daka musu tsawa tare da fad’in kuje kuyi min aiki yarinya ce ita da zaku damu mutane da ba’a ganta ba, duka sukai shuru suka ci gaba da aiki, faruk ne ya shigo gidan yana tambaya ta daw…. Bai gama rufe baki ba sai gata ta shigo cikin gidan, ummi tace ina kika je farida? Shuru tayi can tace na d’an flta ne, Aneesa dake zaune ta tabe baki, farida ta nufi faruk hannunta dauke da Littat”: da biro ta mi’ka mishi tare da fad’in ina son ka rubuta min saki na yanzu, wani irin kallon mamaki yake mata, ita kam Aneesa dake zaune wani irin dad‘i taji yana ratsata, tare da sakin wani lallausar murmushi, faruk yace kin San mai kike fad’a kuwa? Tace eh na sani Bana bukatar Inci gaba da zama da aurenka domin na kasa gane miye matsayi na a wajanka dan haka Ina son ka sauwake min in kuma ba haka ba zan zubar da cikin dake jiki na, faruk yace karki Fara karki kuskura, shikenan zan sakeki kaman yanda kika bukata amma da sharadi guda d’aya in kin amince shikenan,? Tace shradin miye? Yace zaki ci gaba da zama a gidan nan koda na sakeki, shuru tayi can tace na amince, ummi tace farida Mai kikeyi haka? Tace ummi dan Allah karku ce komai mi’ka ma faruk takardan da biro tayi inda ya fara rubutu, Aneesa kam ji take kaman ta tashi ta taka rawa, yana gama rubutun ya mi’ka mata tare da barin wajan, itama inda suke kwana ta nufa ta Fara kuka wanda ta rasa na miye murna ne ko ba’kin ciki haka tayi mai isarta ko takardan bata karanta ba ta saka cikin akwatin ta tare da rufewa aneesa kam duniya ta mata dad’i ita daya zata zama matar faruk yanzu sai dai abu d’aya yake damunta shine cikin da farida ke dauke dashi dan tasan muddin farida ta haihu akwai daru domin dai tasan d’an faruk ne kuma dole yaso d’ansa ko taki ko taso, d’an shuru tayi tana nazarin maiya kamata tayi …….. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *