MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 4
Tunda Dr ya shiga dakin operation din bai fito ba suna ciki shida wasu Dr’s din, Alh Ibrahim daya shiga mugun damuwa kallon mama yayi tare da fadin mama wannan wahalan da take sha Nasan namiji ne zata haifa tunda bata taba haka ba, mama tace insha Allah muyi mata addu’a dai Allah yasa Ayi aikin a Sa’a yarjar fitilar dake manne a kofar dakin tiyata din shine ya tsaya alaman an gama kenan, da sauri Alh Ibrahim ya nufl Dr din Dan yaga sun fito, cikin damuwa yace Dr ya ake ciki? Dr yace an cire mata mahaifa sannan ita da baby dinta suna lafiya, cikin zakuwa da sonjin mai aka samu yace Dr maita haifa? Dr yace baby girl, Idan aka kaita dakin hutu zaku iya shiga Dr na fadin haka Ya wuce, Alh Ibrahim kam gaba daya kasa magana yayi domin a halin da yakejin kanshi bayajin zai iya furta wata kalma, idonshi ne ya kada yayija, lallai Nayi kuskure dana yarda da wannan matar zata iya bani d’a namiji Nayi kuskuren yarda da ita gashi yanzu bata da mahaifar da zata kara haiyuwa flta yayi daka asibitin mama na kallonshi bata ce komai ba dan a halin da yake ciki yanzu baya bukatarjin maganan kowa yana bukatar a barshi ya huta, koda ya fita mota ya shiga abu daya ya furta ma driver shine muje Gida, tunda ya fadi haka bai kara magana ba sai zuciyarshi dake mishi zugi da radadi.
Saida ummi tayi wajan awa daya Kafin aka fito da ita zuwa dakin hutu duk wannan Abun da ake ummi bata farka ba dan anyi mata alluran bacci Kafin a fara aikin saida za‘a gyara matajiki ne ta dan bude ido Bayan an gama ta koma bacci, mama itama kam dauriya kawai take shiga dakin da aka Kai ummi tayi wajan baby din ta nufa yarinyar yar karama da ita, Dan tsaki mama tayi tare da fadin jibeta karama amma duk ta wahalar da mamanta, ummi kam bacci take abunta yarinyar ce ta tsala ihu wanda yasa mama daukanta tana
Toh dawa zata bar ummi? Tana cikin wannan tunanin ne taji qunjin kukan ummi da sauri ta nufeta tare da fadin yaya kike kuka? Ummi tace mama na kasa na kasa bama mijina abunda yake so, wannan ma mace na haifa bana miji ba, mai yasa haka ke faruwa Dani shikenan bani ba farin ciki har abada, na taso ba tare da iyayena ba ban San dangina ba duk a tunani na Idan Nayi aure duk wani fargaba ko kadaici ya barni har abada, ashe ba haka bane zanso ace mijina ya amshi y’ay’a matan da Allah ya bashi domin bai San wani irin baiwa ke garesu ba, zanso ya gane cewa duk abunda Allah yaba mutum Toh shine mafi alkhairi a garesa, bawai son zuciyan mub…… Mama tace ya isa haka kubra Ya isa haka mi’ka mata yarinyar mama tayi tare da fadin ina son duk wani abu da d’ana yake so abu daya ne bazan goya mishi baya ba shine rashin gaskiya, amma a wannan maganan yana da gaskiya bari kiji in fada miki wani abu, mijina Kafin ya rasu Ibrahim shine yaci gaba da harkanshi daka karshe yace ya bashi company dinshi halak malak duk da haka munajin dadi yana Gida yana hutawa d’ansa kuma yana can yana kula da kasuwanci inda bamu haifi namiji ba fah? Waye zai yi mana wannan Abun ita hindatu tana gidan mijinta tana zaman aure bamu da iko da ita sai abunda mijinta yace amma shiko Ibrahim muna da iko dashi, Dan haka shima yana bukatar d’a namiji kaman kowa yana bukatar mai taimaka mishi, tana zuwa nan tayi shuru jin kukan ummi ya tsananta yasa mama barin dakin da sauri, Bayan fitan mama mota ta shiga driver yaja tayi Gida dan taga a wani hali d’an nata yake ciki, koda ta isa Gida a falo ta ganshi zaune yana hawaye, nufanshi tayi da sauri tare da fadin Ibrahim
dagowa yayi ya kalleta nufanshi tayi tace kayi hakuri Ibrahim insha Allah zaka samu d’a namiji kaman yanda kake bukata zan nema maka wata matar da zata baka d‘a namiji Nayi maka alkawari, cikin jin dadi yace dagaske mama? Tace eh dagaske nake Ibrahim kwanciya yayi akanjikinta yana mai jin dadi idonshi ya rufe akan son d’a namiji baya gani baya tuna Allah ne mai bayarwa sai yake gani kaman ummi ce mai badawa kuma itace ta hanashi d‘a namiji dan haka gaba daya yanzu babu komai cikin rashi sai tsananta.
Ummi tana zaune da yarta suna samun kulawa wajan Dr Sosai mama ce kawai take zuwa dubata, tayi wajan kwana shida a hspt ba’a sallameta ba saboda anaso Aga yanayinjikin nata kwananta goma aka sallameta anyi majaririya huduba da khairat, wannan karan ummi bata da kudin siyan rago dama ba taron suna takeyi ba ba’a yanka ma khairat rago ba haka ummi taci gaba da kula da y’ay’anta a yanzu ta Fara sabawa da shareta din da mijinta yake Dan haka ta cire komai a ranta duk da tana boye bakin cikin da take fama dashi, babu babban bakin ciki kaman yau ace mijinka yajuya maka baya kaida y’ay’anka
ummi tana matukar kokari wajan boye damuwarta.
Mama ta nemo ma alhaji Ibrahim mata mai suna Amina, wata rana mama taje kasuwa jiri ya dibeta zata fadi Amina tayi saurin riketa da yake babu nisa gidan da Amina take yasa takai mama can wacce takejin jiri Bayan ta kaita ta bata ruwa tasha tare da bata abinci mama taci taji ta dawo normal, tayi ma Amina godiya tare da tambaya ke daya kike zaune a gidan nan? Amina tace a’a nida yayana da matarshi, mama tace eyya amma nagode Sosai nace in ba zaki damu ba akwai wanda kike so? Amina ta dan rufe ido alaman kunya tare da girgiza ma mama Kai tace a’a banda kowa, mama tace zaki iya auran d‘ana? Cikin jin kunya tace eh, mama taji dadi Sosai tare da fadin shikenan gobe zansa azo wajan yayanki saiki fada mishi Amina ta amsa da Toh sannan mama ta wuce har mota Amina ta rakata sannan ta dawo Gida, mama bata dade da taflya ba yayan Amina ya shigo da gudu ta nufeshi tana fadin saleh mun kusa fita talauci zamu zama masu kudi, yace kaman ya? Labarin yanda sukai da mama ta fada mishi tare da fadin Nasan Labarin gidan mai gidan yana da kudi Sosai yana da burin samun d’a namiji amma ita matarshi mata take haiyuwa Kaga Idan na shiga gidan Na samu d’a namiji sai abunda nace, dariya saleh ya saki tare da fadin wow wow wow gaskiya kanwata kanki naja, ni kuma Na miki alkawarin komai zai faru sai kin haifi d’a namiji Kinga komai ya zama namu zamu zama masu arziki Kai Wlh harna ganni cikin katuwar mota gani a kwance a daki ina bacci ga AC a kunne dariya Amina ta saki tare da fadin Toh gobe zasu zo Kardai kayi abunda za suji sun fasa yace karki damu ni saleh Na miki alkawarin shiga gidan alhaji Ibrahim tako wani hali lndai ni yayanki ne Toh dole sai ya aureki kuma dole ki haifi d’a namiji wannan alkawari ne.
Kaman yanda mama tace hakan ko akayi Washe gari akaje neman auren Amina inda yayanta saleh ya amince kuma baiyi wani abu da za’a gane son kudinsu a fili ba, nan take aka bada sadaki inda magabatan Alh Ibrahim suka bukaci a daura auren ranan juma‘a saleh yace Kai Anya hakan zai yihu kuwa, mufa talakawa ne Ina zamu iya hidiman biki nan da kwana bakwai, daya daka cikin magabatan Ibrahim yace karka damu basai kunyi komai ba alhaji Ibrahim yace shi zaiyi komai dan haka ku amince kawai, saleh yace Ayi haka kuwa? Sukace karka samu damuwa burin mu shine Allah ya basu zaman lafiya saleh ya amsa da Ameen, Bayan sun tafi amina ta shigo dakin da sauri tana murna ganin kudi dumus masu uban yawa yasa takai musu cafka amma Kafin ta dauka saleh ya kwashe bata fuska tayi tare da fadin ka bani kudin mana, yace Ina amina wannan nawa ne Dan haka kibar cewa in baki, tace amma ba sadaki na bane? Yace shine keda zaki fara samu da yawa ai kyabar min wannan, tace naji amma kadan ban wani abu, tsaki yayi tare da ciro duba biyu ya bata kallonshi tayi galala yace in baki so bani, amsa tayi dan tasan halinsa, matarshi ya kwadama kira tare da jefa mata Dari biyar yace aje a siyo komai na abinci Ayi mai dadi yau tace toh tare da dauka ta fita.
Yau Friday aka daura auren Amina da alhaji Ibrahim, Bayan an daura aure da daddare kaman yanda al’ada yake aka Kai Amara cikin makeken gidan Alh Ibrahim, ummi kam sai jin guda tayi da hayaniyan mutane Koba ta tambaya ba tasan mijinta ne Ya kara aure dan haka take ta kuka a daki domin yanzu ta tabbatar baya kaunarta tunda gashi aure ya kara ba tare da saninta ba tana cikin kuka zarah ta shigo itama kukan tasa ganin yarinyar na kuka yasa ummi yin shuru tare da goge ma zarah hawayen nata itama, zarah tace ummi Abba ya kara aure yanzu ya daina sonki,ummi mai yasa Abba ya tsanemu kodai muba yaranshi bane ….. Da sauri ummi ta toshe mata baki tace ku yaranshi ne Kar in karajin kin furta wannan Kalman daga yau Kinji na fada miki, cikin kuka ta daga kai tare da fadin insha Allah ummi Kema ki daina kuka,murmushi ummi tayi tare da tambayan Ina su aysha? Tace suna daki suna bacci, ummi tace toh Kema tashi kije ki kwanta, tace toh tare da fita Bayan fitan zarah ummi taci gaba da kukanta saida tayi mai isarta sannan bacci barawo yayi gaba da ita.
Amina tana mulki a gidan Alh Ibrahim iya son ranta domin duk wani kulawa tana samu, saleh yana ta mata maganan akan shima yana son Ya dawo gidan Dan ya gaji da zama a gidanshi tace mishi Ya bari ba yanzu ba in lokaci yayi zata sa ya dawo, kwanci tashi ba wuya amina aka sami ciki, zo kuga murna wajan mama da Alh Ibrahim amina bata aikin komai yayin da ummi ta zama kaman yar aikin gidan Alh Ibrahim baya kulata, komai Amina sai abunda tace, wata rana su zarah suna wasa harda khairat da take dan tafiya wani kwaro ya shige ma khairat ido, tasa kuka da sauri zarah ta dauketa sukai ciki wajan ummi idon Kafin kace me harya dan kumbura, ummi tace zarah maiya sami idonta? Tace ummi suna wasa dasu aysha kawai tasa kuka, Jin kukan khairat din ya tsananta yasa ummi fita da sauri zuwa falo inda ta Sami su Amina da mama da sauri mama tace suje asibiti cikin masu zuwan harda amina ana zuwa akai emergency da khairat wacce take ta kuka, Dr Ya dauki lokaci Kafun ya flto inda yace su sameshi office, Bayan sun shiga office din ya fara musu idonta ya samu matsala dole sai an bata glass Indai anaso ta dinga gani,ummi babu abunda take sai kuka amina ce ta iya cewa a yanka mata Toh hakan akayi aka bata na yara, ummi tana kuka tana fadin abubuwa Kala Kala daka wannan sai wancan Allah ka bani ikon cin wannan jarabawan, gidan suka koma suna zuwa suka Tarar da Alh Ibrahim yana ganinsu Ya fara fada Wai dan mai yasa amina zata bisu in cikinta ya sami matsala fah, ummi najin haka ta wuce ciki ita da yarta shi bama ta matsalan yarsa bane damuwanshi cikin dabai zo duniya bane ya damu dashi, ummi kuka take Sosai inda zarah ta labe ta wajan window tana kallon ummi babu komai cikin zuciyar zarah sai tsanar mahaifinta.
A kwana a tashi babu wuya cikin amina ya cika wata tara harma ya Dan gota yau tunda amina ta tashi take tajin ciwon baya Abun dai taga bana karewa bane ta fadama Alh |brahim nan da nan ya dawo Gida suka nufl asibiti suna zuwa akace haiyuwa ne, Gida ya koma dan a kwaso kayan haiyuwa sannan su dawo da mama, Kaf‘ln ya dawo harta haiyu inda itama matar saleh aka kawota haiyuwa Dan asibiti daya suke zuwa amma ita da Abun dake cikinta duk sun rasu koda suka dawo saleh ne zaune yana ta rasgar kuka, Alh ibrahim hankali tashe yake tambaya lafiya? Cikin kuka saleh yace albishirinka Alh amina ta kam d’a namiji,ta haifa wani irin murna ne Ya kama Alh |brahim tare da fadin zan baka goran albishir in mun koma Gida Toh amma wannan kukan fah?saleh yace ni tawa matar ta rasu ita da abunda ke cikinta, salati Alh Ibrahim yayi tare da jajanta mishi ranan aka sallami amina inda aka sallaci gawan matar saleh aka birneta a gidanta na gaskiya, duk da anyi mutuwa saida akayi shagalin suna amma sun kira shi da sadakan bakwai amma irin abubuwan da akayi da kashe naira kaman babu gobe ya isa Ya nuna maka murna suna ake ga amina Anci kwalliya Sosai ansha gwala gwalai, anyi ma yaro Huduba da suna Umar faruk, tun daka lokacin mutuwar matar saleh yake kwana gidan Alh Ibrahim inda amina tace ma mama ya kamata Ya zauna dasu saboda kadaici, mama ta amince tunda gidan babban Gida ne akwai dakuna da yawa Sosai, Dan dama Alh lbrahim yayi tsarin gidan ne wanda zai iya zama shida yaranshi maza sai gashi mata Allah yake ta bashi sai yanzu Ya sami d’a namiji, duk wani kayan wasa in Alh |brahim ya gani saiya siyo ma faruk khairat tana son wasa da kayan amma babu dama, gaba daya duk wani abu mai muhimmanci akwai inda Alh Ibrahim ya ware Dan ajiyewa harda kudi koda wani abu ya taso baya nan, key din dakin yaba mama, inda mama ta bama amina key din dakin amina yanzu an kara zama babban mace sai abunda tace Idan ummi na bukatar abu wajanta zata.
Yau ummi na zaune limam yazo gidan Wanda Ya riqe ummi Bayan rayuwan iyayenta yace mata zai Koma kano da zama wajan danginsa ummi nata kuka haka dai sukai sallama da Idan yaje can zai kirata, haka rayuwa taci gaba ma ummi cikin rashinjin dadi da walwala ga Amina taita sa ummi aiki Kala Kala in ummi ta gama wannan tace tayi wannan haka dai kullum suke ummi bata da lokacin hutu in zarah na Gida shine take taya ta in kuma bata nan taje skul ita takeyi, hindu kanwar Alh |brahim mijinta yayi hatsari ya mutu itama ta dawo gidan haka suka hade Kai ita da amina suna wahalar da ummi …….. Hmmm mai
karatu yanzu Labarin zai soma kudai kuci gaba da bina sannu a han kali tare da suburbodo comments dan shine zai bani karfin gwiwan yi muku posting akan Lokaci.