MIJIN DARE CHAPTER 4 BU R.HUSSAIN
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
_BANYI DON CIN ZARAFIN WANI KO WATA BA,IDAN KINGA WANI ABU WANDA YA DANGANCE KI, TO ARASHI NE🙏_
*SADAUKARWA GA ƳAN ƘUNGIYAR ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION,☀️🌟*
*PAID BOOK #300*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
F~Page 7/8
_________Ta na shiga gidan su Hafsat ta yi sallama, “Assalamu alaikum” Hajiyansu Hafsat na tsakar gida tare da almajirinta Sulaiman, gaisawa su ka yi Inteesar ta ce”Hafsan na ciki ne?” Hajiya ta ce ” ta na nan, ki shiga mana”
Hafsat da ta ke zaune ta na chat da Mijinta, ta jiI shigowarta. “aunty Khaleesat ke ce tafe sannu da zuwa”
Ta faɗa ta na fara’a Inteesar ta ce, “wallahi ni ce zaman gidan ne ya ishe ni kawai na ce bari na ɗan yawata haka”
Hafsat ta ce ” lallai kin ji daɗinki ki je duk inda ki ke so, amma mu yanzu ba bu dama” Inteesar ta ce” ai kuwa dai kuna ƙoƙari ni ina zan iya zama kwana nawa a ce wai ban fita ba ina ba zan iya ba, ƴar da ta haifa Hafsat ta ɗauko mata, kamar ta ga kashi, Inteesar ta matsa “a’a ki barta ni bana ɗaukan jarirai ai” cike da mamaki Hafsat ta ce” kamarya ba kya ɗauka, lallaima aunty
Inteesar shikenan lokaci dai watarana ke ma za ki haifa” hira su ka ɗan taɓa ta tashi ta fice dan jin ta gaji da hirar,sallama ta yi wa Hajiya ta fita.
Sulaiman ya kalleta ya ce” wai ke aunty Inteesar yaushe za ki yi aure?” da wa Allah ya haɗa Inteesar in ba da shi ba “Ubanka na ke jira ya zo sai muyi” Yaron da bai fi sa’an Imran ba take ta yiwa wannan tijarar,shi ba da wani abu ya faɗa ba kawai so ya ke yaga tayi auren,ganin neman dukansa ta ke ya sa Sulaiman tashi a ƙofar gidan ya shiga gari.
Ranta ne ya ɓaci ta koma gida, ko sallama ba tayi ba ta shige ɗakinta, banko ƙofa ta yi ta kwanta, ga shi an kusa kiran sallar magriba, bacci ne ya ɗauke ta har akayi sallah ba ta ta shi ba, Umma ce ta shigo ta ta da ta, ” to asararriya za ki tashi ki yi sallah ko kuwa?” cikin jin haushi ta tashi ta na ɓata rai, daman ta saba shiga bayi kai ba ɗankwali buta ta ɗauka ta nufi rijiya ruwa ta zuba ta shiga bayinsu mai bala’in duhu ba addu’a ba komai ta je ta yi fitsari ta fito alwala ta yi sai fushi ta ke yi ita kaɗai ta shige ta yi sallar magriba alhalin ba azahar ba la’asar tana idarwa ta yakice mayafin ta fito tsakar gida, “Umma ina abincina?”
Salma ce ta ce” ya na kitchen aunty in ɗauko miki?” Inteesar ta danna mata ashar ” ƴar….ke na tambaya” ta shige ta ɗauko ba laifi yau kuma sandararriyar jalop ce, wacce ba wani wadataccen kayan haɗi ba mai, ɗaukowa ta yi ta hau ci a dole ba wani daɗi tsire ta raya aranta ta na so, kaɗan ta ci ta wanke hannunta, ta tashi ta koma ɗaki, tun da ta shiga ta ke jin ƙamshin tsire ba tare kuma da ta ajiye ba, ganin leda ta yi a ƙasa, a haukace ta buɗe ledar ganin irin tsiren Amadu mai nama tayi,ta ke kuwa zuciyarta ta raya mata ai Baba ne ya shigo da shi, shine da tayi bacci aka ajiye mata nata, zama ta yi ta na ci tana jin waƙa sai da ta gama ta ture ta yi miƙa ta kwanta sai bacci, kamar ko da yaushe MIJIN DARE ne ya bayyana, “hahhhahhhh sai ni arne uban arna,sai ni maƙiyin Allah duk mai son Allah ba na sonsa, sai ni shaɗani uban shaianun bil’adama hahhhh” nu ni ya yi ga Inteesar take ta koma tsirara girgiza ya yi ya rikiɗa ya zama mutum sosai sai dai fuskarta ta aljani ta na nan, sarrafa ta ya shiga yi hakan ya sa Inteesar ta ta shi, ba a hayyacinta ba, gigita juna su ka yi sannan MIJIN DARE ya shiga haƙarta tamkar ya sami aikin yi, sosai Inteesar ta ke ƙara ba shi haɗin kai, da za ta iya buɗe idonta ta yi arba da shi babu abinda zai hanata haukacewa tsabar munin halittarsa, daɗi ta ke ji sai tanɗe baki take ta na fitar da sautin nishi tamkar wacce ta ci yaji, mummunan bakinsa ya ɗora a kan nipple ɗinta ya hau tsotsan boobs ɗin ta bai sauka akanta ba sai da ya ji Baba ya buɗe gida ya fita masallaci, su Irfan da Imran ma sun fito, Umma ta zo ta fara buga mata ƙofa nuni ya yi ga kayanta sannan aljanin ya ɓace.
“Ke wannan Ƴa naga ranar da kiran sallah zai dinga ta da ki a bacci, ki tashi ki yi sallah” Inteesar da ta ji haushin tashin da Umma ta yi mata ta na tsaka da jin daɗinta ta ja tsaki “mtsww aikin banza burar uba sai mutum ya na bacci a wani tashe shi sallah idan nayi sallar Allah ya tsine min”ta juya ta koma baccinta, MIJIN DARE da ya ke laɓe ya fashe da dariya sannan ya ƙara mata nauyin bacci dan karta yi sallar asuba ya tafi.
Su Irfan na dawowa daga masallaci ya sa ƙannensa a gaba,su ka shiga karatu kowa ya na biya ƙarin da aka yi musu a makaranta,dan yau akwai boko, a bacci ta ji sun cika mata kunne tamkar a makarantar allo kowa akwai inda yake karantawa, cikin ɓacin rai Inteesar ta ja tsaki gami da janyo filo ta rufe kunnenta, ta na son komawa bacci amma karatun ƙannenta ya hanata.
Umma ce ta fito ta fara ɗorawa yaran ruwan wanka a murhu, karfe bakwai saura suka yi addu’a su ka tashi kowa ya fara shirin makaranta Yaya Irfan shi ma zai je makaranta, kafin takwas kowa ya fice neman iliminsa, sai da Umma ta gama komai sannan Inteesar ta fito ta na botsare-botsare, ko kallonta Umma ba ta yi dan idan da sabo ta saba da halin ƴartata, ruwan wankan Baba ta juye ta shiga bayi tayi wanka, Inteesar akwai son wanka, jin mararta ta na ɗanyi mata ciwo sama-sama ya sa ta fito, ta nufi ɗakin Umma ta na hawaye, “Umma,Umma” ta na kiran Umma dan ta ba ta magani tun yanzu,Umma da ta ke gyaran wake ta ce”me ne ne,ki ke min kira kamar wata makauniya ko baki ganni ba ne?” Inteesar ta ce”marata ce ta ke min ciwo” cikin tashin hankali Umma ta ce” subhanallahi sannu, ba ri a nemo magani kar ya yi yawan da ya saba, kin karya kuwa?” Inteesar da hawaye ya fara sharara a fuskarta ta ce”ni ba na jin yunwa” magani Umma ta ɗauko jikinta na rawa ta bawa Inteesar ta sha, ta koma ɗakinta ta fara murƙususu, tun tana kuka har abun ya ci tura. Haka Inteesar ta ke fama da tsananin ciwon mara na iska, dan har suma take yi, Umma duk ta bi ta damu sai sannu ta ke mata, kamar ko da yaushe sai da ta sume sa bo da azaba, asibiti Umma ta ke so ta kaita, ta zari hijab ɗinta ta yi gidansu Hafsat ko Haidar na nan ya taimaka ya kaisu Shakata hospital, “assalamu alaikum, Hajiya ina kwana” Umma ta faɗa a gigice Hafsat da ke tsakar gida ta amsa “waalekumussalam Umma lafiya?” Hajiya ce ta fita da sauri ta na cewa, lafiya kuwa Laure?”
Umma ta ce” dan Allah ko Aliyu ya na nan ya kai min Inteesar asibiti, wannan ciwon maran nata ne ya tashi” Hafsat ta ce”ayya dama har yanzu ta na fama da wannan ciwon, Allah ya ba ta lafiya” Hajiya ta fara kiran “Yaya zo maza ka kaita asibiti” Haidar da ya na jinsu, ya ce” kawai na san wahalar da ni za’ayi haushin zuwan Umma nan nake ji, na san wannan Inteesar ɗin muguwar raguwa ce, ta na sane ta ke yin hakan sai ka ce ita kaɗai ce mace wacce ta ke menstration period” ya na mita ya na fitowa.
“yauwa ku je ka kaita asibiti”Hajiya ta faɗa, Umma ta koma da sauri, Haidar ya ce”na yi late fa Hajiya kuma ina da aiki da yawa a office” Hajiya ta ce ” sa bo da rashin Imani ko idan matar ka ce a wannan halin ya za ka ji, za ka wuce ko kuwa” Haidar ya fita ya na ce wa na tafi” Allah ya tsare ya ba da sa’a” Hajiya ta yi masa addu’a ya fita ya na mitar “Allah ya kiyaye Mata ta ba irin wannan ƙazamar ba ce, wata mummuna da ita”.
Malam Ayuba da ya dawo daga sarin kayan miya ya ga Umma ba ta nan, ganin Inteesar ya yi a sanƙame ya sa hankalinsa ta shi, (ashe dai kana sonta duk da baƙin jinin nata Baba Ayuba) a lokacin Umma ta shigo Baba ya ce” ciwon ne ya tashi Laure?” Umma ta ce” shi ne Malam yanzu na roƙi arziki Ali zai kai mu asibiti, ka ba ni kuɗin magani” Baba Ayuba ya fito da aljihunshi ya na ce wa” yanzu fa na dawo daga kasuwa na saro kayan miya da kuɗin hannu na, ki ranta min do Allah akai Yarinyar nan asibiti” Haidar ne ya shigo ya na ce wa” ku fito mu je Umma” Baba ne ya cicciɓota a sume aka sa ta a mota Baba ya ce ” Aliyu dan Allah ka taimaka ka aramin ɗari biyar akai ta asibitin alƙur’an ka ganni nan ko sisi ba ni da shi, dan Allah” inda sa bo Haidar ya sa ba , cikin girmamawa ya ce ” ba komai Baba Allah ya ba ta lafiya” Umma ta hau su ka tafi asibitin, dan dama sun saba zuwa har likitocin sun sa ba da Umma.
Irfan ne tafe ya na ta faman hamma yunwa ya ke ji, tun safe da ya shiga school ya ke ta zirga-zirga har yamma sannan ya dawo, tafe ya ke a hanya ya na riƙe da handout ɗinsa a hannu,
Wata rantsattsiyar mota ce ta wuce ta gabansa cikin sha’awa Irfan ya ce” Allah ka yi mana arziki duniya da lahira” ya na bin motar da kallo, da tunane tunani ya nufi gidansu, sallama ya yi ya tarar da su Salma da Imran a gidan, “Yaya sannu da zuwa” Salma ta fara yi masa, sannan sauran suka yi masa, ya ce “ina Umma?” Imran ya ce” ba ta nan, ta kai aunty asibiti tun safe Hajiya ce ta faɗa mana”
Irfan ya ce “Allah ya sauwaƙe ba ri in yi wanka in bi su” Na’ima ce ta ɗauko masa taliya ta kai masa ɗaki, duk sunyi tagumi su na son aunty Inteesar duk masifarta ba sa so ta yi rashin lafiya.
Haidar na kaisu ya ba wa Umma dubi biyar ya na yi mata Allah ya sauwaƙe ya juya ya tafi aikinsa, nurse ne su ka ɗauko Inteesar aka shiga da ita dan ita ta zama customer, allura aka yi mata ta farfaɗo ruwa aka sa mata shiyasa su ka kai har yamma ba su dawo ba.
* * *
Wasu Samari ne zaune a bakin hanya, su na shaye-shaye ɗaya daga cikinsu ya ce” kai ɗan Malam ka da ka sha tayi maka yawa, ka sha kaɗan dan ni bazan kai ka gida ba Malam ya ganni, wanda ake kira da ɗan Malam ya ce” kai dallah ware yanzu zamanin mu ne dole mu yi abinda muke so, wai kunsan san ma me ne kuwa?” abokan nasa su biyu Anas da Lurwan su ka ce “a’a sai ka faɗa” Umar(ɗan Malam) ya ce” wai jiya kamar ni Malam zai sa wa mari” cikin mamaki su Anas su ka ce “haba dai yawane wallahi me ka yi?” Ɗan Malam ya ce” wannan Adamar mana ƴar rainin hankalin Matar tsohon mana ita ce ta kai masa gulma ta” Lurwanu ya ce” kut ka ce kishiyar Baba ce, ai wannan matar ko ba dan Ali Zaki ba ko alkur’an da sai na kwantar da ita” Ɗan Malam ya ce” kawai ku share, kai ba ni madarar nan in ɗan watsa kai na ba chaji…
Gidan MALAM KABIRU MAI ALMAJIRAI…….
DOMIN KARANTA CI GABA DANNA WANNAN LINK DIN👇
https://arewabooks.com/u/rhussain
*Zinariya ce✍🏻*