MISBAH BOOK 2 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH BOOK 2 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Soyayya mai tsafta da tsananin shakuwa ya kullu tsakanin Deeni da MISBAHI, dukkansu suna son juna sosai so mai ban mamaki. Dukkan su kowa na aikinsa, sai dai wannan bai hana su bawa juna lokaci daga gidan gonar Deeni zuwa asibitin MISBAH ba, nisan sa bai wuce tafiyar kafa ba.
Haka wataran Deeni zai bar abinda yake ya je wurin MISBAII yana kallonta daga nesa ko da bata sani ba baya gajiya da kallon ta, haka kullum sonta karuwa yake a ransa. Tana masa wani irin kwarjini, ya dinga jin sonta yana tsuma

shi, yana godewa Allah da Ya hada shi da MISBALI, yana godiya da wannan shauki nata da yake ji, fatansa da burinsa Allah Ya bashi ‘ya kamar MISBAH
Ta bangaren Bahijja lokaci guda Deeni ya canja rayuwarta, ba ta taba zato ko tsammani zata tsinci kanta a wannan sabuwar rayuwar ba. Wani lokaci in ta tuna irin soyayyar da take yiwa Deeni hankalinta na tashi saboda tana tsoron kada wani abu ya shiga tsakaninta da Deeni, don kuwa tabbas tasan ba zata iya jure rayuwa ba Deeni ba. Don haka kullum ta sa goshinta a kasa tayi sujjada sai ta roki Allah da Ya mallaka mata Deeni matsayin abokin rayuwa, Ya mallaka mata Deeni da zuciyar sa.
Zaune take a (office) dinta idonta rufe ta tafi wani duniya tana hango rayuwar da za suyi da Deeni, tana jin son shi na tsuma ta. A lokacin ya shigo ya harde hannu a kirji yana kallonta yana murmushi, yana jin wani irin dadi a ransa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kamshin turaren sa mai kardi da dadin gaske ya dawo da ita hayyacin ta, ta bude ido ta ci karo da fuskar sa yana mata wannan murmushin nasa da take so fiye da komai a


rayuwa. Itama murmushin ta masa ta zuba masa
nata manya-manyan idanun, ta ce. “Har sakon zuciyar nawa ya isa gare ka?”
Ya fada murmushin sa, ya ce, “Wannan idanu suna kasheni da yawa, suna tsumani, suna gigita ni”.
Nan ta sake lumshe masa suta kuma bude su, sai da wani abu yaji ya tsirke shi har tsakar kanshi, yaji wani irin tsananin kaunarta da sha’awarta mai Karfi yana shigarsa. Zai yi magana yaji muryarsa na shakewa, da kyar ya iya furta maganar.
“Bahijja lokaci yayi da zamu ci moriyar soyayyar mu, Bahijja ina bukatarki kusa dani, ba zan iya jure yin nesa da ke ba. Ina zaune yanzu fitinar sonki ya hana ni sakat, na rasa sukuni, na rasa inda zan sa kaina.
Na yiwa Baba waya na ce masa Baba zan yi aure, ya ce in kawo duk matar da nake so a duniya zai aura min ita, na ce masa na samu mata, na samu uwar ‘ya’yana, Doctor Bahijja, Abokiyata kuma likita ta. Ya taya ni murna, yamin alkawarin mallaka min abinda nake so ko mene ne shi indai bai fi karfinsa ba.
Na ce masa bana son komai sai Bahijja, ita kadai zai mallaka min saboda yanzu Bahijja ‘yarsa ce, shi babanta ne, ‘yarsa nake so ya aura min. Na masa alkawarin rike masa ita da amana, don haka yau mamanki da babanki za su tambaye ki wa kike so? Ina fata za ki fito musu da gwaninki”.
Kalamansa sun ratsa ta kuma sun mata dadin gaske, wanda bata san yaushe ta fara hawaye ba. Tun tana ‘yar karama take buri da sha’awa ta ga soyayyar uwa da uba, ta ga kauna da gata daga iyaye kamar kowace yarinya, amma ta san wannan burin nata ba zai taba cika ba. Muslihu ya so ya cika mata wannan burin, sai dai hakan bai samu ba.
Bata san yaushe ta kifa kanta bisa hannayensa ba tana kuka. “Deeni ka gama min komai a rayuwa”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Burina kenan Bahijja in faranta miki, inga na cika kowane irin buri naki karami ko babba, duk da ke din ba mai buri bace”.”Burina guda in mallaki Deeni da zuciyar sa”.
Ya yi mata murmushi, “Burin ki ya cika my dear, ina jin dadin yadda kike sona Bahijja, yadda kike nuna damuwar ki da kulawar ki a gareni. Ina bukatar rayuwata”. wannan. har karshen
“Ka samu Deeni, soyayyata da kulawata naka ne”,
Ya yi murmushi, “Na gode, anjima Mama zata zo ta tafi da diyarta gida don mata shirye shiryen aure, saura kadan Abokiyata ta zama amarya ta”.
Murmushi tayi tare da ɓoye fuska saboda kunya, musamman da ta ga irin kallon da yake mata.
Da yamma Mama ta zo ta tafi da Bahijja
tare da Baba Andi gidansu Deeni, duk da tana jin wani iri da nauyin Mama amma ta daure saboda Deeni. Maman ta lura da haka, don haka tayi kokarin kawar mata da nauyin da take ji, ta cc.Bahijja ke diyata ce, soyayyar da kike wa Deeni shima yake miki ya sani sonki da Kaunar ki kamar ‘yata. Ina godiya ga Allah da Ya kawo ki rayuwar Deeni, don haka saki jikinki, nan gidanku ne, zan miki duk wani abinda uwa zata yiwa diyarta ko shakkar haka kar kiyi”. Alhaji ya shigo yana jinsu, shima ya matso
ya ce. “Haka zan miki duk abinda mahaifi zai yiwa ‘yarsa inshaa Allah”.Na gode Baba”.
Ta fada kai sunkuye yayin da taji hawaye na kokarin ciko idonta, wani (feelings) ne da bata taba jin irinsa ba, wani irin farin ciki na daban taji yana ratsa ta.
Allah abin godiya, Allah mai kyauta da kari, ya bata miji da iyaye lokacin da bata zata ba balle tsammani.
Alhaji ya zauna gefen Mama, ya ce, “Bahijja wane lokaci kika ga ya dace mu tsai da ranar auren ku?”
Kanta sunkuye ta ce, “Baba ai ku iyayena ne, duk ranar da kuka ga ya dace ku ka tsayar dai dai ne”. Alhaji ya ce “To Allah Ya miki albarka, ina so zan hada auren ku tare da na Lukman, shima ya samu matar sa, sai mu hada muyi nan da sati biyu masu zuwa. In mun hada ku mun hutar da ‘yan uwa masu zuwa daga nesa sau biyu, tunda mun shirya sai mu hada”.To Baba”. Ta fada kai sunkuye.To Allah Ya miki albarka”Nan ya
mike ya fice, Mama ta kalleta tace, Www.bankinhausanovels.com.ng
“To diyata za ta zama amarya sai a bawa asibiti hutu ko saboda a bawa jiki hutu da nutsuwa”. Tsananin kunya yasa Bahijja kife kai,
Mama na dariya ta ce. “Na fada miki ni mahaifiyar ki ce”.
Deeni dake tsaye yana kallon su ya tsinci kansa cikin wani irin tsananin farin ciki da jin dadi, son mahaifan sa da kaunarsu yaji yana kara karfi a zuciyar sa.
“Zan mallaki Misbah na nan da sati biyu inshaa Allah”.
A sati biyur nan Mama tayi hayar masu gyaran amarya na musmaman suka sa Bahijja gaba da gyara ba ji ba gani.
Mama ta fahimci nauyinta da Bahijja ke ji, wannan yasa ta damka ta a hannun masu gyara da kuma aminiyarta Haj. Amina da tazo bikin da kanwarta.
Ya zame mata dole ta yiwa matar Deeni gyara, Deeni gudan zuciyarta ne, zata iya komai don farin cikinsa, tunda Bahijja ce farin cikin Deeni ba zata yi wasa da ita ba.
Lokaci guda Bahijja ta canja, tayi wani iirin kyau da haske me ban mamaki, ta dawo tamkar wata Balarabiya, duk inda ta wulga sai kaga tamkar anyi walkiya saboda tsabar gaske da kyau da daukar ido da take.
Deeni ya kasa daga ido akanta duk inda tabi yana binta da idanunsa, yana jin Alfahari da samun mace irinta. Tabbas Bahijja ta ishe shi har iya karshen rayuwar sa, bashi da bukatar wata mace.
Ana saura kwana uku biki ‘yan uwa da
abokan arziki suka cika gidan wanda musamman Alhaji ya tura (ticket)
na jirgi wa mutanen Gombe da Kaduna don zuwa bikin dan gatansa.
Daya bangare na gidan aka warewa baki, yayin da bangaren su Hajiya sai aminiyarta da Kanwarta tare da su Farida da mahailiyarta.
Dakin Deeni shi ya koma dakin Bahijja shi kuma ya koma gidansa na (farm house) sai dai kullum yana makale tsakani idonsa kan Bahijja, bai iya jure rashinta ko na kankanin lokaci.
Bahijja ta kasa gasgatawa kanta sabuwar duniyar da ta tsinci kanta, gata da kauna da take gani gun mahaifiyar Deeni da ‘yan uwansa kadai ya isheta farin ciki, ballantana kuma uwa uba Deeni. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan sallar Juma’a jama’a da dama suka shaida daurin auren Deeni da Bahijja, aure yayi albarka, dumbin jama’a ne suka cika a daurin auren. Bayan nasu aka daura na Lukman da Amaryar sa Abida, duk a masallacin Juma’ar munguwar su aka daura.
Bayan daurin aure Mama ta shirya walima ta musamman, abinci ba irin kalar da babu tun daga gargajiya har Turawan. Wajen ya tsarus sosai, an gayyaci malamai mata masana da kuma ‘yan uwa da kowa in ya ci abinci ya tofa albarkacin bakinsa.
Haka a waje Alhaji ya shirya nasa da maza abokai da ‘yan uwa a waje, kowa ya ga Deeni wannan rana yasan yana cikin tsananin farin ciki. Wannan ya kara kayatar da kyan fuskar sa.
Cikin gida a daki Bahijja ta sha kwalliya da gyaru sosai, duk da shiga mai sauki tayi, doguwar riga mai tsadar gaske ta sa wanda Mama tayi mata (order) daga Dubai. (Blue) ce an mata kwalliya mai sauki da fararen duwatsu, ya matukar karɓar fatarta mai haske, haka ya dada fito da kwalliyar fuskarta. Ta tufke gashinta baki mai tsayi da sheki tare da lulluba gyalen rigar, ta sa (cover shoes) masu tsadar gaske da ya yi shige da irin (dressing) dinta, ta sa (bracelet) mai saukin kwalliya tare da zobuna guda biyu wanda suka yi matukar kayatar da dogayen yatsunta.
Bahijja mace ce doguwa mai kyakkyawar kira, shigar da tayi tai matukar kyau da bata taba ganin tayi ba, sai kamshi take. Mama ta shigo ta ganta ita kanta tayi bala’in mata kyau, ta dinga ganin duk yawan taron nan ba kamar surukarta Bahijja, tabbas ta amsa sunanta matar Deeni.Tayi murmushi, “Tabbas diyata tayi
kyau”.Ta ce, “Bari inje zan turo wacce zata zo ku tafi tare wurin walimar, duk an gama taruwa”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ita dai Bahijja kanta sunkuye har Mama ta fita, shiru taji gidan yayi alamar duk an fita wurin walima. Tana nan zaune shiru zuciyarta cike da tunani kala-kala taji motsin shigowa. Kamshin turarensa ya tabbatar masa da Deeni ne ya shigo dakin, nan tayi saurin daga kai suka yi ido biyu, yana mata wannan murmushin.
Ya zuba mata idanu itama ta kasa dage idonta a kansa, ya yi mata kyau sosai. Sanye yake da (blue) shadda kalar nata kayan ya sha aiki, shigar ta matukar kyau. Hular da ya kafa a kansa ta kara fiddo da kyan fuskarsa, gashin kansa kwance irin na Fulani sak, ga sajen da ya karawa fuskarsa kwarjini da annuri. Ji tayi tamkar ta je ta fada kirjinsa ta kwanta, amma sai ta kasa saboda kunya dukda

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *