MISBAH BOOK 3 CHAPTER 13 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
zahiri kuma sai ta yi murmushi ta ce,
To ina jin ku Alhaj ya ce,
“Bahija ina so ki saurare ni da
kyan da kuma fahimta a kan abin da zan fada maki, ba na so ki yi mana rashin fahimta,
“Insha Allah zan fabimta Baba.”
ya ci gaba da ma maganar Deeni ne, Bahijja kin dauke mu iyaye,
Ta da girgiza kai kwarai Baba,
kin yarda
muna son ki kuma muna maki adalci tsakanin ki da Deeni.sosai Baba, alkhairi da mutunci da kuke mani ko iyayena ma sai haka, saì dai in yi ta muka addu’ar Allah ya saka muku da gidan aljanna.”Na ji dadin haka,
” in jì Alhajin ya ce,
«dama wani hukunci muka yanke, ina fata za ki ba mu goyon baya tare da hadin kai.
Iya dai yanzu bugun
zuciyarta ya fara tsamanta, haka nan ta dinga jin wani irin fargaba da tsoro na shigar ta, nan da nan ta fara addu’ a ta neman taimako a gun Allah ya ba
ta karfin zuciya da juriyar karbar ko ma wane
hukunci suka yanke ta ce,
“ina sauraron ku Baba.*
Ya ce Mun yanke hakuncin hada auren Deeni
da Farida.Ras! Ras! Ras! Taji kirjinta ya wani
mummunan bugawa hankalinta
ya nemi barin
jikinta, amma sai ta daure ta cije, kanta sunkaye cikin natsuwa ta ce,
“To Baba ai duk hukuncin da
kuka yanke daidai ne, Allahya sanya alkhairi
Hajiya Aisha tayi saurin karba da cewa
“wannan ba hukuncinmu bane mu kadai har da Deeni da kuma hukanci da kaddara irin
na Ubangiji, ina so ki karbe shi hannu bibbiyu ba tare
da wani tashin hankali ko hatsaniya ba, ba na so ki daga wa Deeni hankali a kan abin da yake so kuma
a kan abin da Allah ya halatta masa, ina son ki
masa adalci, in har kina sonsa, ki bar shi ya samu abin da ya dade yana so yake muradi.
«Farida wata halitta ce da Deeni ya so fiye da
komai a rayuwarsa wanda Allah bai nufa zai
mallakaba har sai yanzu mun yi magana da Deeni
yana son Farida yana son auren ta amma yana
gudun rigimarki don za ki daga masa hankali a
banza, wanda in kin yi haka baki masa adalci ba,baki yi wa ‘ya ‘yansa da mu kanmu iyayensa adalci
ba. Kin kuma so kanki da yawa in kika hana shi
abin da zuciyarsa ke so da abin da Allah ya halatta masa.
Babijja ta ji zuciyarta na zugi da zafì tare da wani irin radadì mai kuna, tabbas akwai tashin hankali ga mace in ta ji za a yi mata kishiya, amma fiye da
wannan shine irin ta inda Deeni ya bullo mata ya hada ta da iyayensa, ya ci amanarta ya yaudare ta
da zuciyarta, lokacin da yake gigin nemanta da son
ta, ya mata alkawarin karya ya munafurce ta ya
cutar da ita da zuciyarta, ya sa ta karaya, a kan
kanta da rayuwa ma gaba daya.
Idanunta suka kada suka yi jawur cikin tsananin kunar zuci da bacin rai ta daga kai za ta yi magana,Deeni ta gani tsaye a wurin suka yi ido biyu, haka
ta dinga ganinsa wani baki kirin, ya yi mata
tananin duhu, ta ji ya fice mata a zuciya, ba ta
kaumar ganisa, ba za ta iya jure kallonsa ko da na minti daya ba.
Saboda tsananin kinsa da ta ji a ranta ta yi saurin
kau da kai daga gare shi, tuni ya rude ya susuce ya
rude maganar iyayensa sun firgita shi matuka sun kara ruda zancen sun kara dagula al’amura da ruruta
wani rashin fahimtar tsakaninsa da Bahijja, ya
dawo gida saboda su yi magana su samu fahimta ya
samu labarin zuwan iyayensa, bayan ya iso gida ya
yi saurin zuwa asibitin zuciyarsa cike da tunani
kala-kala.
“Maganar ta yi zafi har haka, da ya sa iyayensa
tasowa su zo. Nan jikinsa ya ba shi za a samu
matsala, ga shi kuwa yana shigowa ya tarar da zancen da ya dagula komaì. Wanda bai san ta yaya
zai soma gyara shi ba, zufa ya ji yana fito masa ta
ko’ina a jikinsa. Tuni ya jike sharkaf saboda
tsananin tashin hankali. Bahija ta mai da kallonta
kan Hajiya Aisha tuni, ta Maida zaciyarta ta dake ta ce,
“mama ai kuwa Deeni ya min rashin fahimta, niba
zan taba shiga tsakaninsa da farin cikinsa ba ko da
abin da yake so, saboda ni dai mai kaunar Deeni ce
da zuciya daya, don haka ina maraba da duk abin
da yake so da kuma farin cikinsa koda kuwa ni ya saba wa nawa farin cikin.
‘”Dan haka na muku alkawari ba zan taba daga
wa Deeni hankali a kan abin da yake so ba, in dai
Farida abar sonsa ce farin cikinsa ce to, ina maraba
da ita, na yi alkawarin ba shi hadin kai ya aure ta,in dai daga wurina ne ba zai taba samun matsala
ba, ina maraba da Farida da kuma zuciya daya.Alhamdulillah» Alhaji
ya fada yana
murmushi tare da fadin
‘Allah ya yi maki albarka
da kika fahimce mu, kika dubi girmanmu da
darajar son da kike yi wa danmu, kika kawo komai
cikin sauki, Allah ya maki albarka ya ba ki abin da kike nema na alkhairi duniya da lahira, yau na kara
ganin girmanki da kimarki Bahijja.”
Hajiya Aisha ma kalaman Bahija sun sa duk
wani zafi da ta danka ta nema ta rasa, sai ta ji
kaunarta da kuma tausayinta sun shige ta saboda ance ciwon ya mace dai na mace ne, dan haka ta
yaba da namijin kokarin da Bahijja ta yi na yadda
ta amine ta karbi maganar cikin sauki tare da
saukaka lamarin, duka ta ce,
“Allah ya maki albarka Bahijja yarda kika faranta mana, ke ma
Allah ya foramta maki.”bahijjah tayi murmushi a takaice tace Ameen mama
tunda munyi maganar sai mu je gida ku huta sosai
ku kuma yi magana da Deeni a kan auren da
lokacin da za a yi shi.”
“To, insha Allah.
” in ji Alhaji, ya fada suna
kokarin mikewa, sai a lokacin suka ji motsin
Deeni, kasancewar sun ba shi baya, Babijja kawai
ke kallonsa ta kofar shigowa, ya kalli iyayen nasa ya Ce,
“Baba ban amince da hukuncin da kuka yanke
ba, ba ni da ra’ayin kara aure ko yin mata biyu ko ra’ ayin auren Farida, rayuwata ta riga ta ci gaba
yadda baya ba za ta dawo ba, haka dangantakata da
Farida ba zai dawo ba, babu Farida ko soyayyarta a
zuciyata yanzu.
Mama ta yi masa wani mugun kallo ta ce,
“InA wacce kake gudun bacin ranta da tashin hankalinta
ta ce ba ta da matsala, kai meye naka, kana son
Farida ko ba ka sonta, wannan ba na bukatar ka fada min saboda na san meye a zuciyarka game da
Farida, kar ka nemi ka raina mana hankali, ai ba
mace daya na haifa wa kai ba, zan ganì da matsayin
uwarka da na matarka wanne ya fi muhimmanci,
UMARNI na baka da ka auri Farida
Durkusawa ya yi a gaban maman zai yi magana
Bahijja ta yi murmushi ta ce,
“‘mama matsayinki ya wuce na kowa,
matsayinki ya wuce
wasa,
matsayina bai kai rabin naki bama balle har na
fiki, Deeni zai auri Fanida insha Allah, wannan
alkawari na maki,
damuwa da natsuwa, alamar ta riga ta sallama wa
zuciyarta, ta shirya kuma ta karbi wannan hukuncin
daga Allah, ta yarda da kaddarar ta Deeni kuwa ta
sallama shi HAR ABADA ba za ta sake bacin rai ko wani shiga harkokinsa da rayuwarsa ba, illa
iyaka ta sauke hakkokinta na aure a kansa da Allah
ya dora mata, ta fuskanci rayuwarta domin wannan tashin hankali da matsalar kam ta kau da shi daga
rayuwarta insha Allah, ta fada a ranta.
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe