MISBAH BOOK 3 CHAPTER 21 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 21 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

 

 

 

lokaci yara na dawowa daga makaranta karfe hudu bayan sun gama lesson haka Farida wata ran takan kai shida wani lokaci biyar.

Bahijja ko koda ta gama aikinta da wuri takan

wuce gidanta a cikin asibiti tayi ta aikace-aikace da rubuce-rubuce duk da tayi bankwana da rubutun  soyayya takan zabi wani bangare na rayuwa tayi rubutu akai hakanan ta bude wani blog a sirrance mutane masu matsaloli sukan aiko mata da tambayoyi game da matsalolinsu wasu akan

lafiyarsu wasu akan wani kunci na rayuwa da suka tsinci kansu tana basu shawarwari iyakar iyawarta. Deeni kuwa wataran sai karfe goma yake dawowa kafin ya wuce bangarensa zaije ya leka bangaren Bahijja dan tabbatar da lafiyarta a kullum yaje tana barci wanda har ya fahimci salon gudunsa take hakan ya kara masa jin haushinta. Da tsananin fushi akan yadda ta mai da shi shi da babu duk daya,haka nan suka kasance suna jin haushin juna tare da fushi da juna soyayya na rikidewa yadawo kiyayya ban tabaji da gani ba sai akan Bahijja da Deeni wanda hakan yayiwa Farida dai-dai da dadi. Hutun yara yazo dai-dai da hutunsu Farida dan haka Hajiya ta basu shawaran ya kamata suzo gida

hutu wato Kaduna Bahijja bata iya tsallake

maganar Hajiya dan haka itama ta dau hutun ta damka asibitin a hannun sauran likitocin da suke kula da asibitin tare haka Deeni ma duk suka tattaràa sai garin Kaduna. Gida ya cika da yara da jikoki wanda hakan ba karamin dadi yayiwa Hajiya ba musamman yadda ta

lura akwai zaman lafiya ba kananan magana ba gutsiri tsomi haka bata ji wani yayi korafi wani ba sai dai ta lura ba wani walwala da sakewa sosai tsakanim Deeni da Bahijja ba kamar da yadda ta saba ganinsu ba.

Sai dai hakan bai daga mata hankali ba saboda yanzu da Farida a tsakaninsu satinsu biyu a gidan Hajiya suka koma nasu gidan wanda nan ma kowa da nasa bangarensa,haka suka dinga ziyarar

‘yan’uwa kamar yadda suka saba da in sunzo sai dai wanna karon kowa da hanyarsa.

Deeni yakan tafi da Farida da yara yayinda

Bahijja in ta tashi ta kanje tayi nata ziyaran ita

daya,duk wani abin da zai hada ta da Deeni da Farida ta kan guje masa saboda hakan shine zaman lafiyarta,domin kuwa taci alwashim yakar duk wani abu da zai daga mata hankali ya hanata zaman lafiya.

Wanna tsari da ta dauka ba karamin dadi yake

mata ba wanda a yanzu har ta saba da wannan rayuwar in dai anji muryar Bahijja tana magana sosai to tsakaninta da marasa lafiya ne,wani lokacin har kyakyata dariya za’aji tana yi a cikinsu musamman yara sai kuma Baba Audi itama takan zauna su yi hira ta dinga bata shawarwar cewa ta saki ranta ta

daina zama cikin kunci,ta kanyl murmushi ta kalli baba audi ta ce “Baba Audi bana bakin ciki,kunci, na godewa Allah da yabani karfin hali da Karfin imani na kaucewa kuncin rayuwa

da karfin addu’a da ayyukana Baba Audi,babu wani abin dani a rayuwa duniyar nan da har in karasashi zaka shiga cikin tsananin kunci,rayuwace in wani ya faranta maka

wani zai bakanta maka babban nasarar da dan-Adam zai samu a rayuwa shine kusancinsa da mahaliccins kaji tsoron Allah ka kiyaye ibada,riko da gaskiya da amana kuma duk abin da za kayi ka

yi shi dan Allah in kayi haka zaka samu natsuwa a rayuwa,karka tsammaci komai a gurin kowa sai Allah mahaliccinka duk dan Adam mai rauni ne karka tsammaci wani abu daga gareshi Baba Audi dai ta saba ji ire-iren wadannan maganganganun gurin Bahijja sai dukda hakan bai sa ta fasa mata masiha ba data saki ranta ta dinga walwala hakan nan ta lura da wani boyayyen damuwa a cikin zuciyarta wanda ta rasa na

menene.

wance take a kangadonta kanta na

kallon sama bata san lokacin

da hawaye ya gangaro mata ba ya Allah

ka sake sani cikin wata jarrabawar a kullum

ina kwana ina tashi da kewar dana

Muhammad, yaya yake a wani hali yake ban sami ba ba kuma bani da ikon zuwa inda yake ya yake ya kamanninsa yake a yanzu ban sani ba nayi hakuri

na jure da fatan Allah ya sadamu da Alkhairi ko a duniya ko a lahira rabuwa da da alkwai ciwo sannan

yanzu a daidai lokacin da nake son nesanta kai danake son nesanta kai na bawaDeeni na cire shi a raina na bashi dama yayi rayuwarsa yadda yake so da wadda yake so sa Ya Allah, sai. Kuma gani dauke da cikin Deeni yanzu kuma wajan, wata shida ina kokarin boye shi kar kowa ya sani amma yaushe zan boyeshi dole sai ya bayyana kansa a lokacin da nayi nacin son na samu cikin da haihuwa da Deeni ban samu ba sai yanzu da na sallama Deeni ya bar nì da ajiyar dansa a cikina.

Wanda hakan na nufin sake kasancewa da

Deeni wanda bana jin sa a raina Ya Allah nice

uwa ta farko da ta tsinci kanta cikin kunci ta dalilin dan dake cikina maimakon nayi farin cikin na tsinci kai na cikin tsananin bakin ciki.manta fashe wani irin kuka da karfi wanda bata san tayi yi shiba.

Da sauri ya iso gurin ta cikin tashin hakali don

duk tashin hankalin da suke baitaba ganin ta cikin wanna yanayin ba macece mai juriya da karfin hali tare da fuskantar matsalolin rayuwa komai tsananinsu. Yau ganinta cikin rauni yasa

zuciyarsa ta raunana tsananin tausayinta da son ta suka dirar masa a zuci yayi saurin rikota da rungumota a jikinsa sosai ya dinga jin son ta na ratsa shi rabon da ya jita a kinsa haka har ya manta tabbas yayi kewar Bahijja sosai.

Ya jima yana kallonta a wurin yana sallama

amma bata amsa ba hawayen da ya gani na zuwa  a fuskarta da yanayin da ya ganta a ciki ya tausaya mata,tabbas Bahijja tana cikin tsananin kewa duk da kuwa ta nuna bata bukatasa da kowa a rayuwarta yasan tana bukatarsa. fashewa tayi da wani irin kuka tare da kankameshi karo na farko da ta tsinci kanta cikin tsanamin tausayin kanta, da gaske ashe ba za ta iya rayawa ba tare da (Support) din Deeni ba a she tana bukalan

kafadar da za ta kwanta.Bahijja ta fada a zuciyarta kada ki bari Deeni ya raunanaki, karki rauni baki da bukatar Deeni bakya bukatar taimakonsa nan tayi karfin hali ta

janye daga jikinsa tare da juya masa baya tana share hawaye ta ce kana bukatar wani abu ne ta fada murya kasa kasa

Yayi saurin matsowa gabanta yana fuskantarta yace Menene Bahija?”

ta sake kan da kai saboda

bata son ganin  fuskarsa ma balle taji haushi har

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *