MISBAH BOOK 4 CHAPTER 5 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

ciki. ta dan datse lebanta tace *Baba Audi kin zo

Kenan?”

Cikin fara°a tace “Bahijjia an budi ido lafiya kai

Allah mun gode maka sannu fa.”

Murmushi tayi tace “Yawwa Baba Audi.” nan ma Hajiya tayi mata sannu ta amsa shi kuwa gogan hankalinsa yana kan jinin da ake kara mata fuskarsa kunshe da farin ciki yana gain jininsa yana shiga jikinta nan yaji zuciyarsa tayi sanyi yaji wani irin azababben sonta yana shigarsa.

Cira kai yayi suka kalli juna nan ya kara kanin tayi masa kyau fiye da koda yaushe duk da kuwa kumbura da fuskarta tayi. murmushi yayi mata yace Docter Bahijja barka da samun kai lafiya, kin ya haihuwa wannan irin fine Baby haka.” ya karasa fada yana murmushi.

Ta dan saki takaitaccen murmushi tace “nagode, ina Muhammad dina ko a gida aka baro min shi?” Bashi kadai ba Hajiya kanta sai da taji dadi yadda tana cikin wannan hali amma Jikanta na ranta nan take ta kara jin son Bahijja ya kamata.”

Cikin murmushi Hajiya tace “Ai dan ki tuni na barshi a gida hankalinmu a tashe muka taho

Ta dan yi murmushi tace “Haba Hajiya dan nawa ai dole a yi tashi gaskiya dai da an tasho min dashi ta kalli agogo tace gashi nan lokacin shan maganinsa ya kusa fa bai kamata kuma yaki sha kan lokaci ba. Cikin jin dadin kalamanta yace “karki damu yanzu zansa a kawo shi a kuma hado shi da maganinsa.

“Da ka kyauta min kuwa.” ta fada tare da sakin murmushi na farko da ta taba yi masa cikin son ranta da sakin fuska wani dadi ya kama shi. nan ya dubi Hajiya yace ya kamata muje mu nemowa

Baby kasyan sawa ko tunda munzo asibiti babu shiri.”

“Gaskiya ne” ta fada tana mai murmushi tare suka juya wa har likitan ya biya ya rubuta masa check na goran albishin dinsa har naira dubu dari biyu. nan likita ya shiga masa godiya sai da saka hajiya ta kara yi masa Hajiya tace babu komai likita duk mune da gode.

A nan yayi masa maganar

refunding din kudin CS da ya biya ba’ai bayace ya bari idan an kawo wata a yi mata amfani da kudin duk albarkacin Babynsu nan likita ya shiga dodiya ta sosai. suka fito abinsu.

A resting room kuwa Bahija ne da Baba Audi a dakin su kadai ta hadama Bahijja kayan tea mai kauri tana sha. baby na rike a hannun Baba Audi.

Bahijja tace “Baba Audi lokacin da kuka shigo ina wani tunani ban gamaba kuka shigo, Baba Audi na fara tunanin kai ma Deeni jininsa a cikin wannan kwanakin domin ya sani kuskure daya nayi da ban sanar da shi ina dauke da cikinsa bazan kai masa diyarsa dan na manta da shi da kowan irin DANGANTAKA a tsakaninmu ina son manta komai da ni da shi HAR ABADA domin ba zan iya rike masa jininsa ba ganinta a tare da ni zai ke yawan sawa ina tuno wani hadi da shi cikin rayuwata.’

Wani irin kallon Baba Audi tayi mata na kin haukace ne. sannan tace “Bahijja ban sanki da irin wannan rashin imanin ba yarinyarda ko awa bata yi a duniya ba kike son raba ta da ke baki bari taji dumin uwa ba har kike kokarin azabtar da ita haka Bahijja ina tunninki yake da tausayin uwa ga abinda ta haifa.”

Baba Audi tunda na rabu da dana lokacin da nake tsananin bukatarsa aka zo aka raba ni da shi tun ina jin ciwo har na zo na saba tunda na hakura to ita ma zan iya jurewa bana son sai na shaku da ita lokaci guda a zo a raba ni da ita kamar yadda aka raba ni da Muhammad don haka gudun kada haka ya kara faruwa da ni yasa na yanke wannan shawarrar domin mutanen cikin duniyar nan basu da kirki ina jin tsoran haka ya sake faruwa da ni.”

“haka ba zai sake faruwa da ke ba saboda babu wanda yasan kina da cikin Deeni a jikinki sai dai idan ke kike so hakan ya sake faruwa da ke. sannan maganar da kike fadi na cewa mutanen duniyar nan basu da kirki ban yardaba domin yau naga masu kirki fiye da yadda kika dauki mutanen duniya. naga so na gaskiya, naga tasanin kauna da KARAMCI, naga inda ake nuna kauna tsakani da Allah naga inda ake shiga cikin damuwa don samun lafiyar wani da farin cikinsa, naga inda wani uba yake saka takalmin wani uba ya hau ya zauna, naga yadda mutum yake nuna tsantsar damuwarsa ga mutumin da bai san yana yi ba, kuma duka cikin mutanen duniyar nan da kika fada.

Ko kinsa wannan jinin da yake shiga jikinki daga ina yazo to duk wannan abinda na fada miki a gurin mutum daya naga ya hada su, kuma ba kowa bane sai wannan bawan Allah da kike tare dashi Alhaji Umar Farouk. wannan jinin da yake shiga ilkinki nasa ne shine ya bayar a saka miki na jikinsa.

Don haka ina mai baki shawarar kada ki kara kiran mutanen duniya marasa kirki, akwai masu kirki akwai marasa shi, don haka babu abinda zai sa a barki ki rabu da yarinyar nan da bata da laifin kowa. idan kika ga na barki kin yi wani abu akanta to bani da numfashi ne, wanna shine iya abinda zan fada miki sai ki kara yin tunani akai.”

Jikin Bahijja yayi sanyi da jin kalaman Baba

Audi nan ta bi Karin jinni ta kalla wai jinin Farouk ne ke yawo a cikin jininta.

Baba Audi mai mutumin nan yake nufi da ni na fada masa ina neman taimako ne da zai yi hidima haka da ni, nayar da sun taimaka min sun kawo ni asibiti amma ban ce yayi wata hidima da ni ba don haka yaje ya dawo ya fada min duk iya abin da ya kasha min zan biya shi saboda bana bukatar taimako na kudi daga gurin kowa.”

Cikin takaici tace Bahiiia wai ke wace irin halittace da kike son ki aro wani hali daga baya bayan ba halinki bane kin kuwa ga  irin rudanin da bawan Allahn nan ya ya shiga da ya samu labarin an kaki asibiti.

Tunda muka zo ya shiga masallaci yana addu’a a akan Allah ya sauke ki lafiya da farko da aiki za’a yi miki shi ya saka hannu ya biya komai an nemi jinni ya kawo nashi ya bayar yanzu duk mutumin da yayi maka wannan kana da bakin da zaka iya tukararsa kace zaka biya masa na tabbata don

Allah yayi miki kuma ko ba ke ba ma na tabbata zai iya yiwa wani hakan ya nuna shi mutum ne mai alheri.

Bahijia ba zan bari ki ari halin da ba naki ba don wani yayi miki laifi sai ki dauki laifinsa kina hukunta wani da shi to ba zai yuwu baba zan laminta ba sam kin ji na fada miki.

Bahijja dole ki zama mai yafiya akan dukkan al’amuran ki idan kina hango laifin Deeni kina yiwa wasu hukunci da shi to baki kyauta ba, kowa ki barshi da halinsa sannan kowa ki hukunta shi da laifin da yayi miki wannan shine kin yi gaskiya.”

Baba Audi bani da wani buri da wani tunani na son mu’amala da wani danamiji nagama yinsa HAR ABADA bare har na bari yayi min wani laifin da zan hukunta shi a gaba”

Bahijja ni dai na fada miki kada ki kuskura ki tanka masa duk abinda yake miki sai ya daukeki butulu, kina yi masa kyakykyawan zato na tabbata domin Allah yayi miki haka, bana son ki nuna masa abin da zai sosa ransa kin ji na fada maki.”

Hmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *