MISBAH CHAPTER 13 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH CHAPTER 13 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kamar yadda ta kasance da su shamsu haka ta faru tsakanin farida da mahaifinta da mahaifiyarta. Tunda ya fara musu bayanin manufar sa bai kai ga karasawa ba ma farida ta mike ta tare shi da fadin .

    “Abba ba zan taba auren wani namiji a duniya ba inba deeni ba ,nayiwa deeni alkawarin kaina da zuciyata,zuciyata deeni take matukar so,don haka Abba kabar wannan maganar ta yaudara. So kake inci amanar deeni ? Kuma Abba bazan iya rayuwa da wani ba in ba deenni ba ,Abba ka taimakeni ,gara min mutuwa ta daa rasa deeni” 

      Mikewa yayi ya sharara mata mari sai data ga taurari.

   ” yarinyar banza mara kunya” ya fada yana huci. 

   “. Ke har kin isa kiyi jayayya dani ? Yaushe kika koyi rashin kunya ? Kin san me kike fada kuwa ? Har kina fadan mutuwa da iliminki da hankalinki ,kin san meye mutuwa da har kike ikirarin gara miki mutuwa ? Me aka miki me zafi a duniyar nan haka ? Kuma ko me ya miki zafi babban sabo ne kice kin gwammaci mutuwa . Miji dai nike da hakkin zaba miki shi ko ? Ba ke ba ,don haka na zaba miki shamsu ,inkin isa  in na daura miki aure da shi ki ki zama a gidansa ,sai in san ke cikakkiyar mara kunya ce ” Www.bankinhausanovels.com.ng 

        Ta durkusa har kasa tana kuka ,baba kayi hakuri don Allah kar ka rabani da masoyi na deeni,Abba deeni shi ne rayuwata ,ban taba tunanin wani a matsayin mijina in ba deeni ba,Abba ba zan iya biyayyar aure ga kowanne namiji ba sai Deeni “

    Ki daina bata yawun bakin fa, shamsu dai kin aurwshi kin gama “

      Ta mike , Abba bazan auri shamsu ba sai dai ka kashe ni “

 Ya kalleta cikin bacin rai ,ya ce

   Baki isa ba ,idan kinason zama a gidan nan matsayin diyata ,idan kinaso mahaifiyarki taci gaba da zaman aure a gidan nan kar ki sake musu dani akan maganar auren ki da shamsu””

     Maganarshi ta karshe ya mugun girgizata ,tabbas bazataso auren uwarta ya kare akanta ba . Ya kalleta,kina da zabi ,ko naki auren ko na uwarki,ina saurarenki”  Cikin tsananin kuka da bakin ciki tace ,Abba na amince ba don inaso ba ,sai don umma,” to banason sake jin komai ko wani musu akan maganar nan,munyi mun gama . Haka ko da wasa ban yarda idan kunyi waya da deeni ki sanar masa ba ,balle ya dawo ya daga mana hankali. Sai ki soma shirye shiryen biki” 

  Ya kalli mahaifiyarta da ta bude baki tana sauraron su cikin tsananin mamaki ,ta rasa abin fadi. Tabbas namiji halinshi sai shi .     Yace ,ki rubuto mun duk abinda ku ke bukata na bikin farida za’a siyo shi,cikin december za’ayi auren “

       Yana gama fadi ya juya ya fita ba tare da ya sauraresu ba,haka farida ta zauna a wajen ta sa hannu akai tana ta rusar ihu tamkar wacce aka cirewa ido ko ta rasa uwarta ko ubanta. 

       Mahaifiyarta dai bata da yadda zatayi sai lallashi da nasiha ,sai dai tabbas dole ta taya ‘yar ta kukan rashin babban masoyinta . Sannan karin tashin hankalin ma wai ta auri dan uwansa? 

     Nan ta rungumo ta a jiki tana lallashi ,tana mata addu’a.

    ‘Farida Allah zai maki zabi mafi alkairi”” tana fadi tana hawaye ,basu ankara ba sukaga jama’ar gidan duk sun cika falon kowa na tambayar meya faru ? Duk wanda yaji abinda ya faru sai ya tausayawa farida gami da juyayin wannan alamari,saboda kowa yasan karfin soyayyar dake tsakanin Deeni da Farida. Www.bankinhausanovels.com.ng 

   Haka farida ta wuni kuka ,ba ci ba sha,bakin ciki da takaici ya cika mata zuciya,tsananin kewar deeni da kaunarsa taji yana ratsa ta. Hankalinta ya mummunan tashi ,taji kwakwalwarta na juyawa tabdinga jin kamar zata yi hauka saboda kwakwalwarta ta kasa amince mata da hukuncin da mahaifinta ya yanke akanta,ta dawo tamkar wata mai jinni. 

          Ta mike da gudu ko dan kwali babu akanta ta nufi gidansu deeni,kai tsaye ta wuce dakin shamsu tana kwala masa kira.

    “. Ya shamsu”” ya shamsu ka taimake ni ” 

     Ta sameshi ya kasa tsaye ya kasa zaune yanata zagaya dakin ,shima abin duniya ya masa zafi. Bai ankara ba ya ganta a dakinsa ba zata tamkar an jehota ,ta sunkuya ta kama kafafunsa. 

  

     Ya shamsu ka taimake ni kace baka sona,kace ba zaka aure ni ba . Yaya shamsu kaima ka sani ko ? Kasan deeni nake so,kasan ba zan iya rayuwa da wani namiji ba in ba deeni ba . Ya shamsu ina son Deeni ,ka taimake ni ya shamsu ,bazan iya aurenka ba “” 

Kaka take tana ta surutai kamar mahaukaciya ,sai da shamsu ya rikota suka fuskanci juna.    Kiyi hakuri farida ,an fada miki ba dole akayi min ba ne kamar yadda aka miki ? Bani da yadda zanyi sai dai bin umarnin mahaifina,bani da yadda na iya,ya zame min dole zan ci amanar dan uwana . 

          Deeni ya bani amanar kula da ke kafin ya dawo,zai dawo ya samu naci amanarsa ,na auri macen da yake matukar so. Farida ba abu ne me sauki ba a gareni,duk kuka da rokona da zakiyi bani da ikon canja ra’ayin mahaifina ,yadda bazaki iya kin bin umarnin mahaifinki ba haka ba zan iya kin bin umarnin mahaifi na ba ;””

   Ta fashe da kuka, to ya kakeso nayi? 

 Kasan dai deeni nakeso ,Deeni ne rayuwata,please ka taimake ni ya shamsu ka taimake ni.

Mama ce taji hayaniyarta ,ta fito ta zo ta janyeta, yayin da shamsu ya lumshe ido hawayen bacin rai na zuba masa,yana jin kukanta na ratsa kunnuwansa,yana kuntata masa zuciya 

…..A daki mama tayi ta lallashi amma inaaa!! Farida kuma take ,bata ji bata gani,bata saurare,daga karshe ta tashi ta tafi dakin deeni,ta hau bisa gadonsa tana shakar kamshinsa,tana kuka tana fada masa irin tsananin son da take masa. Www.bankinhausanovels.com.ng 

    Farida bata gushe ba a gurin har sai data shide ta suma a wajen,mama da shamsu sukayi asibiti da ita a rude. Da kyar likita ya samu ta karfado,,sai dai zazzabi mai zafi ya lullubeta,haka nan bata bar kukan da take ba har sai da akayi mata allurar bacci,bacci me nauyin gaske ya dauke ta . 

        Mama ta zuba mata ido tana kallonta,tana matukar tausaya mata tare da mata addu’a a ranta ,tana maganar zuci.

    ” Yarinya karama ta hadu da kaddarar da ta kasa jurewa,ta kasa tawakkali,haka nan mahaifanta sun kasa ganewa.”” 

     Nan ta mike don zuwa tayiwa mahaifiyar farida waya ,,nan shamsu ya zauna ya zura mata ido,sai ya daina jin tausayin kansa se farida..  halin da ta shiga ya firgita shi,ya san suna matukar son juna da Deeni amma bai zaci farida na haukan son deeni haka ba. Shin taya zai rayu da macen da take matukar haukan son wani bata ji bata gani ? Taya zai iya rike amanar da mahaifinsa ya damka masa bayaan cin amanar dan uwansa da ya yi ? 

     Yana cikin wannan hali mahaifiyar farida da yan uwanta suka shigo,hakan yasa ya fita .

     Kowa dai bashi da ikon mata wani abu sai addu’a har kusan magriba ,mahaifansu maza
sukazo. Tabbas sun tausaya mata,amma hakan bai sa dayansu yaji yana da niyyar canja ra’ayi ba.

      Har faridan ta farka tana kuka tana rokon mahaifinta,amma sai ya kau da kai gareta,yace,intaga bata auri shamsu ba to dayan su ba ya numfashi ne ko ita ko shi mahaifinta,ko kuma shi shamsu din . Yana gama fadi ya fice abinsa. 

     Daga nana farida tasawa kanta dangana,sai dai ita tasan tabbas mutuwa zatayi inta auri wani da ba Deeni ba ,don haka ta soma shirin bankwana da duniya tana jiran ta Allah ta kasance akanta.

   *  * * * * * * * * * *

    Tun lokaci da aka kulla maganar auren shamsu da farida duk iyayen su suka hau shirye shiryen biki ,duk wanda yaji maganar aurensu sai yayi mamaki saboda kowa dai yasan farida da Deeni take soyayya ba da yayansa ba . 

    Tuni Alh umar ya siyawa shamsu da farida tsalelen gida na gani na fada,ba abinda bai sa musu ba na zamani mai tsadar gaske.

Hatta kayam daki bai bukaci Alh Ahmad da yayi ba dakin da bai sa kaya a ciki ba ,duk wani kayan 

Kyale kyale an sakawa farida da shamsu. Www.bankinhausanovels.com.ng 

   Ganin kara da kawaici da Alh umar ya masa yasa shima ya ce to ya bar wani maganar hada kayan aure ,haka nan shi ya dauki nauyin biya masa kudin sadaki. Alh umar baiki tayinsa ba ,saboda a fadinsa shamsu dansa ne.

     Ansa bikinsu a juma’ar farki na watan karshe.

    Ranar da Deeni ya bugowa mama  waya gaba daya rudewa tayi har ya so ya fahimci akwai matsala ,amma sai ta nuna masa ba komai,tana fama da hayaniya ne ana shirin auren yayun farida wani satin ,sannann shamsu ma zai yi aure.

     Ihu yasa mata na murna da mamaki ,ya ce 

    Mama ya shamsu zaiyi aure ? Mama kinsan ban taba ganin ya shmsu da budurwa ba sai kace me tsoron mata,amma nayi mamaki . A ina matar da zai aura take ? Unguwar mu ? 

     Mama tayi masa dariar da bata kai zuci ba ,tace. 

       Deeni kenan ,wannan tambayoyi haka,to koma dai yana nema ko baya nema ya samu ,yarinyar unguwarmu take ,” 

        Ayya mama,ina farida? Tna zuwa kuwa ? Kinsan nayi ta neman wayar ta a kashe,haka layin ummanta ma baya shiga ,ina jin dai hidimar bikin suke mama,yanzu da ina nan da har dani za a hada da auren yayun ta da yaya shamsu ayi,amma ba komai mu namu mu biyu zaayi mana special one ….

     Tuni mama taji ta rude ,ganin shamsu ya shigo tayi saurin mika mishi wayar. 

    Ga dan uwanka nan kuyi magana “”

  Jiki ba kwari shamsu ya karbi wayar yayin da mama ta koma gefe tana hawaye,tsananin tausayin danta ya ratsa ta ,tana tunanin ranar da deeni zai samu labarin  auren farida shamsu da halin da zai shiga ,bacin rai da tashin hankalin da zai shiga ne babban fargabarta . Tasan halin Deeni da zuciyar sa,in ta kule shi ba me kyau bane ……

   Oh Allah !!! Kayi mana maganin abinda ba zamu iya yiwa kanmu ba “”

 Tunda shamsu ya karbi wayar Deeni ke ta masa surutu yana zolayar sa,yana masa tsiya amma yayi tsit kamar ruwa ya ci shi. Deeni na tambayar sa yarinya da zai aura yar wani gida ce? Kuma meye sunanta? 

  Tuni yaji kansa ya sara,tambayar tayi masa kunci , ya rasa inda zai sa kansa.ya hau masa kame kame,yayin da deeni ya dauka zafin kan aure ne ya debe shi,don haka ya kyale shi,nan ya kawo masa zancen da yafi kowanne kunci. Www.bankinhausanovels.com.ng 

    Ina amanata da na baka ,farida ? Ina fata kana kulamun da ita ,ya take ,a wane hali take ? Kullum sonta da shi nake kwana ina tashi  ,bani da burin da ya wuce in gama karatu in dawo in auri farida…………

       Kafin ya kai ga ida maganar sa shamsu ya yi saurin katse wayar tare da kashewa ,saboda ba zai iya jurewa ba . Duk kunyar deeni ta ishe shi haushin kansa da tsanar kansa ya kama shi , bai san yaushe ya sa kuka ba………….     ¹⁹

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *