MISBAH CHAPTER 15 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH CHAPTER 15 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wani lokacin haka zata ta dinga mata fada da nasiha akan ta rungumi abinda Allah ya bata hannu bibbiyu ,idan ta nuna halayya na kin amincewa hakan ya nuna bata yarda da abinda Allah ya bata ba,don haka ta hore ta da tayi hakuri ,tayi juriya ta saka soyayyar shamsu a zuciyarta,saboda shine mijinta yanzu,don haka ba karamin zunubi bane ta mayar da tunanin wani namiji da sunan so balle har taji sha’awar sa. Ya zame mata dole ta danne son zuciyarta,ta fi karfin zuciyaeta ta rungumi abinda Allah ya bata hannu bibbiyu ,ta gode masa.

    Nan ta girgiza kai tare da fadin , naji mama,nagode ,insha Allah zanyi duk yadda kika ce..”Www.bankinhausanovels.com.ng 

     Mama tace ,”Akwai wani aiki a gabanki ,nasan bakya son shaamsu,haka shima baya sonki,amma fa yanzu ya zame miki dole ki so shi,kuma dole ki ja hankalinsa ya so ki a matsayin ki na matarsa. Yana da kyau ki kama zuciyarsa,ki jefa soyayyar ki a zuciyar sa kafin ku kai ga fara zaman aure.

   Sunkuyar da kai tayi kunyar mama ta kama ta ,hakan yasa mama ta mike tace. 

   To zan fita amma ga kaya nan ki ahirya kiyi kwalliya ki fito ,shamsu na falo yana jiranki ,na hada muku dinner zakuyi tare.

   ” To mama “

 Ta amsa murya kasa-kasa .

Bayan fitar mama ta mike ta kalli kayan,,wani jan material ne mai kyau da tsadar gaske ,sai kamshi yake. Ta sa a jikinta,doguwar riga ce mai sharpe ,dinkin ya kamaa jikinta tamkar don ita akayi material din ,fatarta mai haske tayi matukar karbar kayan.

Nan ta tsaya tana kallon kanta a mudubi,ta tuno yadda take bata lokaci da tana kwalliya don ta burge Deeni,amma in ya zo sai dai ya yi ta mata daria da gwalo yana cewa bata yi kyau ba . Da kanshi yake tayata ta gyara yana koya mata yadda zata yi kwalliya,in yaga ya kalleta ya mata murmushi yace

  “. Kinyi kyau mrs Nuruddeen duk duniyar nan ba macen zata kai matata farida kyau a wurina_

   Ta kanyi murmushi ta boye fuska ,amma yau da ikon Alkah tana kwalliya don ta burge wani ba deeni ba,wani namijin da bata taba noticing dinsa ba a matsayin namiji ,bata taba kula da shi ko ta bashi muhimmanci ba ,asali ma ita yaya shamsu tamkar bako ne a gareta ,shi ne yau ya zamo mijinta. Lallai Allah shi ya barwa kansa sanin abinda ya lullube . Www.bankinhausanovels.com.ng 

     Tana cikin wannan tunanin mama ta dawo ta ce.

    “Har yanzu farida,ina ji dai sai na sa miki hannu . Farida sarkin tunani ,na ce miki ki rage tunani amma ba kya ji ko ?

      Murmushi kawai tayi ta sunkuyar da kai. Ta ce ‘ kinyi kyau kuwa,kayan sun karbe ki. Bari in miki daurin tunda naga ke bakya son yi..”” 

   Nan kuwa ta ajiyeta ta mata daurin da ya kara fito da kyan fuskarta,ta taimaka mata wurin sa dan kunne da abin wuya da dai sauran kayan karau. Ta bata takalmin da ya dace da kayan ,sannan ta fesa mata turare mai kamshin da dadin gaske.

     Ta ce ,yauwa ,yanzu ‘yata ta fito a amarya sak,sai gun ango ko ?

   Kanta sunkuye tayi saurin rufe fuska.

     Mana tace to na tafi tunda kunyata akeji ,amma fa inna fita ki fita ,kinga tun dazu yana jiranki..”

” To mama ” ta amsa murya a kasa.

  Bayan ta fita itama ta bi bayanta ,tana tafiya cikin nutsuwa da hankali tamkar mai tsoron kasar ko tausayinta.

   Tun kafin ta iso turarenta ya rigata isowa,hakan yasa ya dago kai a zatonsa ta iso falon. Hango ta yayi tana tahowa ,ta zuba kyau,tana wani taku tamkar wacce take filin gasar sarauniyar kyau. Yarintarta da cikarta ,budurcinta ya bayyana a zahiri,nan ya tsinci kansa da kallonta ya kasa kau da kai daga gareta . Sai sheki take tana kamshi,bai ankara ba har ta ta iso dab da shi. Nan yayi saurin kau da kai.

   Ta ja kujerar dake kallon sa ta zauna itama ta kasa dago ido ta kalle shi,kanta a sunkuye ta ce . 

   Yaya shamsu ina wuni?

  Muryarta me dadi da sanyi ta daki dodon kunnensa ,yaji ya taba zuciyarsa.

   Ya amsa,” lafia farida ,ya kike? Ya fada cikin kau da kai .

   Ta amsa kai sunkuye ,”lafia ” Www.bankinhausanovels.com.ng 

 Mama ta shigo tace ,To ko waye ake kawar wa da kai da sunkuyar da kai ban sani ba. Shamsu ,farida halal dinka ce fa,farida shamsu mijinki ne,kina da damar kallonsa ko menene abin sunkuyar da kai ban sani ba . Ni zan wuce bangaren babanku,ki tashi ki zubawa mijinki abinci, kuma ina so ku saki jiki da juna kuyi hira,” 

    To mama” suka amsa a tare.

  Bayan fitar mama farida ta kasa daga kai,yayin da shamsu ya yi karfin halin dago kai yana kallonta kanta sunkuye tana wasa da yan yatsunta.

  Nan yayi kokarin kawar da shirun ta hanyar cewa. 

 Tunda bazaki zuba min abincin ba bari ni in zuba miki,”

   Nan ya bude kular abincin fried liver with potatos ne,ya zuba mata hade da juice ya mika mata . 

    Ta dan kau da kai ,” Da ka barshi  zan diba da kaina ” 

  Ya yi murmushi yace,”Naki na barshi”.

  Ya fada cikin muryar tsokana da kwaikwayonta ,hakan yasa ta dago kai ta kalleshi. Gabanta ne yayi mummunan faduwa saboda yadda ya yi sai taga ya bala”in yi mata kama da Deeni,yadda yake murmushin sa da yadda yake zolayarta. Bata san yaushe ta saki murmushi ba ,murmushin da yasa shamsu yaji ya tsaaya masa a zuciya,ya tsinci kansa da kasa dage idanunsa daga gareta har sai da ya ga ta dago. 

 Ya yi saurin mikewa,” Ni zan wuce naga dare yayi “

   Cikin sanyin murya tace,ya shamsu kaci abincin mana,kar ka kwanta da yunwa”=

 Ya tsinci kansa da kasa musa mata. 

  Sun ci abinci tare ,sai dai sunyi zaman kurame,dukkansu sun kasa sakewa da juna yayin da suke kallon juna a sace,,har mama ta dawo ta same su a haka. Ita ta zauna a wurin ta kau da shirun tana kokarin jansu da hira tare da sa su yin magana da juna . Da Shamsu ya zo tafiya mama ta sa farida tayi masa rakiya har kofar dakinsa da ke gidan ,suka yiwa juna murmushi tare da fadin ” sai da safe ” ta juya. Www.bankinhausanovels.com.ng 

  Shamsu ya bita da kallo yana jinjina takunta da yaba halittar da bai taba mai da hankali ya lura ba,yayin da farida taji hankalinta ya tashi da ta hango kofar dakin Deeni wanda suke kallon juna da na shamsu . Ta sawa kofar dakin ido,hawaye suka zubo mata,soyayyar sa da kewar sa taji yana ratsa ta. Shamsu ya tsinci kanshi da zuwa inda take,ya lura da yanayin da take ciki idonta lumshe hawaye na zuba ,bai san yaushe ya jawota jikinsa ba ya mannata da jikinsa gami da shafarta yana lallashi.

     ” kiyi hakuri farida ,nasan ba abu ne mai sauki ba ,sai dai tuna baya ba abinda zai baki sai bacin rai.”

   Nan ta fashe masa da kuka ,ya zanyi ya shamsu? Ya zanyi da soyayyar Deeni da ke cina yana azalzalar zuciyata? Ya shamsu ina son Deeni ,ina cikin tsananin kewar sa. Ina son kasan cewa da Deeni”

     Nan ta dada kankame shi tana kuka,tun yana lallaahi har ya daina ,shi kadai yansan
me yakeji a jiki da zuciyarsa.

   Tabbas abinda bai so ba abin da bai zata ko ya tsammani bane ya faru da shi,wato ya tsinci kansa da jin kishin dan uwansa,hakan yana nufin Www.bankinhausanovels.com.ng soyayyar farida ta shiga zuciyarsa kenan ? Ya ci amanar dan uwansa da tushe ,ya bari zuciyar sa ta kamu da son farida lokaci guda.

    Addu’a ya dinga yi a zuciyarsa,tare da kokarin sharewa farida hawaye.ya ja hannunta ya kaita har kofar dakin mama tare da kara bata baki,har sai da ya ga ta saki ranta tayi murmushi tare da masa godiya.

       Ta shige ciki ta samu mama suka dan yi hira kadan sannan tayi shirin bacci. Duk yawanci hirar tasu ta kare ne a nasiha da misalai da mama ke bata game da yanayin irin  mata data shiga ne …………..

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *