MRS AMIDUD CHAPTER 3

MRS AMIDUD CHAPTER 3

Washe hakori tayi sannan tace. “Baffana! Ince idan nayi auren anan zan zauna!?” “Ai dole ma ki zauna a nan!” Alhaji Muhmood yace mata. “Toh Baffana waye min!” Tasaka hannu a habb’arta! “Eh toh! Nima ban san shi ba, sai Allah ya kawo miki.” Shiru tayi dan tunanin ta duk ya kulle, can tace. “Toh ita wancar doguwar waye Zata aura?” Shiru yayi yana kallon Mamie, girgiza kai tayi sannan tace mata. “Ai ita matar Yayan kuce!” Tura baki tayi kamar zatayi kuka tace. “Toh wallahi a nimo min mijina ko kuma na hanasu auren” Zaro ido waje suka yi, tare da jinjina kaurin kan Parih dakyar suka lallaba ta, ya bar falon.+ Bayan tafiyar Lamisah tayita mita, ita bata ga wani abin burgi a jikin Lamisah ba. “Haba ku baku ga yadda take ba mutum sai kace sanda rake” Babu wanda ya kulata haka ta gama mitarta har tayi barci a gurin. Bayan sati uku sai gasu Fahhamah da Fahmeedah, sun zo huta dake suna karatunsu ne a Jigawa. Anan suka kasa hakuri da Parih kullum sai sun maketa ita kuma ta lalata musu abinsu me kyau, idan suka yi magana Alhaji Muhmood ko Hajiya Adawiyah su musu fad’a, haka zasu zauna da Jalal suyita mita suna zaginta, idan tazo wuccewa suka ja mata tsaki d’aga kafada take tace. “Oho dai Allah kad’ai ke kaunar kura(🤷🏻‍♀️) haka zaku ganni ku barni sai ma nayi aure na barku da cizon yatsa” (💃)2 Tana gaya musu haka zata wucce ta Barsu da masifa. —– Yau tun safe ake gyaran gidan ana dafe dafe, ga shi sai sintiri ake, koda ta samu tayi sallah bata zauna a cikin gida ba, waje ta nufo tana tsaye a bakin gefe sai kallon mutane take, can ta juya taga Amrozia da Aarib sun wuccewa da Jalal abin karyawan shi, dan tana fitowa shima ya fito zai je aika, tana ganin sun koma ciki ta juya taga dandazon almajirai. “Ku almajirai! Kizo nan.” Da sauri suka zo tace. “Ku tsaya na kawo muku abinci ai kuma rabonku ne ya tsago” “Eh” suka ce mata, haka ta je har kofar Jalal ta dauko abincin da ta juye musu tass sannan ta mai da mishi kwanon ta rufe tayi cigaba da tsayuwar ta, dai dai lokacin da ya dawo bai ce mata komai ba sai ma Binta da yayi da ido, ta kuwa murguda mishi baki. Kauda kai yayi yana jin haushi a ran shi idan ya kamata sai ya mata abinda bazata manta da shi ba. Wani mahaukaci ne yazo wuccewa sai cewa yake. “Yesu! Yesu!! Yesu!!!” Sai da ta shiga cikin gidan sannan taje kofar Jalal tace. “Kai! Dukundukun angon tsaka nice na juyewa Almajirai abincinka.” A fusace tafito aikuwa ta arce waje da gudu, ya kuwa bita, makalewa tayi a bakin kofa, yana fitowa tace. “Yecuuuuuuuu!” Ai mahaukacin nan ya wulwula dutsen dake hannun shi sai goshin Jalal, sannan ya kuma biyo su, ta shige gidan a guje ta rufe shi a wajen mahaukacin ya rufe shi da mugun duka yayiwa Jalal Ni kuwa ina shiga na manta da wani can a waje, hayaniyar jama’a ya fidda Baba me gadi. Yaga irin ta’asar da akawa Jalal.1 Dakyar ya kimkime shi zuwa cikin gidan, daga nan aka wucce dashi asibitin rimi. Sai wajen biyar aka dawo dashi lokacin gidan cike yake da baki, Parih nacan dakinsu tana barci dan tunda ta dawo cikin gida takama barci, dakyar ta tashi tayi sallah, tana idarwa ta koma. Hayaniya mutanen gidan ya fidda ita, sanye take da riga da wando na barci sky blue, sai gashinta da suka yi tsage tsage. Ko kallon su batayi ba taje ta dauko abincinta, ta zauna a gabansu dan bata fahimci suwaye bane tana buɗe abincin taga kuskus, kallon Mamie tayi kamar zata yi kuka tace. “Allah bani cin tsakin nan, ranar haikeni yayi yau ma kuma naci Alkur’an mutuwa zanyi.” “Kije abaki tuwo!” Mik’ewa tayi can suka ji ihun ta, tana buga kafa a kasa tana cewa. “Wallahi bani cin wannan tuwon baki dashi.” Mik’ewa yayi yazo inda take ya kura mata ido, kafin ya yanke fuskar shi yace. “Dauka! Ki cinye ko na miki dukar da kika sa mahaukaci yayiwa Jalal.” D’ago kai tayi zata masa gardama yace. “Now!” Dangwara abincin tayi ta fita da gudu, zuwa waje. Tayita kurma musu ihu, tab’e baki Aunty Amarya tayi sannan tace. “Wallahi Son Yarinyar bata jin magana, kuma ana magana Alhaji yayi ta fad’a wai bamu ganin maraicin tane, shi yasa bana magana na zuba musu ido.” Jan waya caji yayi ya fita zuwa wajenta tana zaune ta cusa kanta a tsakiyar cinyarta. “Zaki tashi ko sai na zane ki” Ciro kanta tayi taga bulala, zaro ido tayi ta mik’e jikinta na rawa dan ba’a tab’a fuskarta ba, sai dai Iya kaka taja kunnen ta. Tsoron dukar ne ya rufeta dan dole ta koma tunda ta shiga daki, karshe zazzaɓi ne ya rufeta ta kwanta.2 Tayi kuka har idanunta na yaji. Tana yi tana cewa. “Mayye kawai mumuna dashi! Daga zuwan shi yasani kuka sai nagaya wa Baffana wani yazo ya sani kuka,har yace zai zane ni” Jan majinarta tayi abinta tana kuka tana jan majina har barci ya kuma saceta. …… “A’ah AMIDUD! bana so karka kuma kai idan da adalci yar Abtisham bata cancanci duka ba, koma meye tayi babu ruwan ka, taya zaka dauki bulala kace zaka zaneta gaskiya banji dadi ba.” “Kiyi hakuri Mamie! Amma kuma Mamie wannan abinda kike mata wallahi babu gata a cikin ta sai don kai taya zaki zuba mata ido, tayi abinda ta gadama yau badan Allah ya kare ba ai da mahaukacin nan ya kashe Jalal.” Sosai ya nuna musu basu kyauta ba amma mamie taki, …… Da dare da ake zo cin abinci a nan ne suka haɗu da Jalal, kallon shi tayi ta fashe da dariya tace. “Ka ga bakinka kamar an aunaka da danki! Himili guda! Ina ruwan rangwangwan sai kace budurwa jab’a” “Kee!” Ya daka mata tsawa, juyawa tayi ta kalle shi, da taga Baffanta a kusa da ita, komawa kusada shi tayi ta murguda mishi baki, tare da cewa. “Baffana kaga wannan d’azun bulala ya dauka zai zaneni! Ni dai ka kaini wajen Iyata” “Kul! Kar na kuma jin kince mishi Wancan shine yayanku Amiduddawlah! Kina ina ya dawo” Tashi tayi daga gurin cin abinci ta koma falo ta fasa kuka, diban Abincin Mamie tayi ta biyota har falon. Zama tayi kusa da ita tace. “Parih zoki ci abinci nasan baki ci na rana ba” Kallon Mamie tayi sannan tace. “Ina son ganin Babana! Nima” Jikin Mamie yayi sanyi ta hanyoyi jikinta, sannan tace. “Parih baki Son gaskiya! Idan an miki fada sai ki gudu baki san Abbanki bazai yi alfahari barin baya ba, Yayanku ne AMIDUD karki kuma ce mishi wancan, kuma ki daina tsokana kinga garin tsokanarki an fasawa Jalal baki har da kai” Dariya ta kyalkyala sannan tace. “Wallahi baki ga yadda bakinshi yayi ba kamar na saniya” 🤣🤣🤣🤣🤣😂 _Wannan yarinya ana yabonki sallah kin kasa alola_ Kallon Jalal kowa yayi suka fashe da dariya, musamman yadda bakin ya koma. Mik’ewa yayi ya bar cikin gidan yana nazarin me zai mata ya huce haushin sa akanta. “Toh kice mihi ya daina, kirar hansatu d’akin shi.” Shiru falon yayi kafin ta kuma buɗe baki tayi magana sai ji tayi an buge baƙinta, rikewa tayi tana kallon Mamie dan ta baya aka daki bakinta, juyawa tayi dan tana kirar kukanta ne ganin yanayin fuskar shi babu Annuri yasata kifa kanta jikin Mamie ta fashe da kuka, tana cewa. “Wayyo Allah na! Mama na! Wayyo Allah na! Abba na zai kahe Ni, Ni kan ku mai dani gurin Iyata.” Birkita musu lissafi tayi da bori na fitar hankali, tare da mugun rikici. Dama jikinta da zazzabi take ya kara tasowa, a jikin Mamie ta makale. Har lokacin barci yayi Buhayyah tazo ta rike ta suka kwanta. Bayan tafiyarsu ne Alhaji Muhmood ya juya ga AMIDUD cikin fada yace. “Bana son saurin hannu! Idan bata gani ba ai bazata fada ba, karka kuma dukar ta, bana so dan yau naji ba dad’i kaji tsabar dukar ya shageta tana kirar iyayenta” “Amma Daddy haka zaku cigaba da ganinta tana tab’ara son ranta, wallahi zata lalace.” “Idan masifarka bata lalata ba! Babu abinda zai faru kune kuke ganin illar abinda take yi Kuruciyar ta ce haka.” Karshe fada suka koma mishi, shi da yake ganin gyara. —- Cikin dare zazzaɓi ya hanata barci sai kuka take tana cewa. “Zan sha ruwa!!!” A firgice Fahhamah ta tashi zuwa d’akin Mamie sai gasu nan tare, dole suka tattara ta zuwa Asibitin Ni’ima, dake can new g.r.a, Suna zuwa aka amshe su, ba wani abu bane sai tsoro da ya haifar mata da zazzaɓi. Ruwan na karewa zuwa karfe biyar aka sallame su. Koda gari ya waye a bata tashi da wuri ba, sai karfe biyu ta farka dake D’akin Mamie aka kawota, tana tashi ta fito falo ganin duk suna hira sai wata ƙatuwar doll da ta gani ko nace Teddy, babba. Ihu tasaka tare da komawa ciki da gudu. “Parih! ” Buhayyah ta kira sunanta. Dariya Aarib yake “bakin mugu kawai ai nasan saboda ita kasaka a gurin kuma sai na gayawa Daddy, ai kasan bata da lafiya zata ji sauki tayi maganin ka kato ajebo” Tura baki yayi sannan yace. “Ke kuma tsinken biro kawai” Make keyarshi Amrozia tayi cikin fada tace. “Wawa kawai katon banza ina ruwanka da ita da zaka razana, kuma sai mun kona Teddyn.” Shigowa dakin da take suka yi suka ganta can kuryan gadon, zama suka yi suna bata hakuri, ban daki Buhayyah ta shiga ta haɗa mata ruwan wanka, sannan ta ce taje tayi. Dake bata jin dai dai, bata ce komai ba har tafito wankar. Kayanta Amrozia ta kawo mata ta saka sannan saka ta kuwa fito falon, kallon Aarib tayi ta kauda kanta. Dumamen tuwonta aka kawo mata, taci kadan a sannan Mamie ta sauko daga dakin Alhaji Muhmood tasa aka dauko mata maganinta. B’allo mata maganin tayi tare da mik’a mata, kallon maganin tayi tare da zaro ido tace. “Na higa uku! Ina zan tura su! Wallahi ina hain su mutuwa zanyi dan wancan rike min wuya zata yi” “Ke amsa bana ciki da sakarci” Mamie tace mata, “Wallahi bani shan su” “Buɗe baki na zuba miki” “Allah fasa min makoshin zasu yi” “Parih zan zane ki fa! Buɗe maza na saka miki” “Kwarankwatsa bani shan su!” “Ya ilahi! Kina da lafiya kuwa magani ne ai” Dariya tasaka sannan tace. “Ranar da muka je ruga naga Hard’o yabawa wata karsanan shi tasha Ni ba karsana nace Alqur’ani bani shan su! Kalan na koma Yar mataki” “Ke Buhayyah dauko min bulalar can na zane fitinanniyar yarinyar nan” “Allah Mamie karki zane Ni dan bazan iya had’iye dindinkeken maganin can ba, dama kananun ne” “Toh naji bari na jika miji!” Tura baki tayi tace. “Ni yar akuya ce da za a bani jikakken magani Allah Ni na tsani maganin naji sauki ma” “Assalamu alaikum!” Muryan shi ya gauraye falon, “Mamiena! Jika min nasha bani kuma miki gardama” Jika mata tayi maganin, tana kwalla tana komai, zama tayi yana kallon tv bai masana tana gurin ba, dan tunda yace. “Good Aftenoon Mamie!” Bai kuma cewa komai ba, mika mata kofin Mamie tayi sannan tace. “Lafiya lau! Ya gajiyar hanya” Karba tayi ta kalli maganin, ta kalli Mamie ta kuma kalli inda yake sai ta fashe da kuka tace. “Toh wallahi nikan ki dureni kawai dan bani iya shan su da hannuna” Dafe goshi Mamie tayi tana kallon ta, kafin tace.. “Yayansu! Don Allah bata ganin nan tasha” Idanun shi na kan tv yace. “Ayya Mamie ki karasa aikinki kawai dan Ni zan b’allo muku tekune kuma baku da abin tare wa.” Tashi tayi ta bar falon. Juyawa yayi sannan yace. “Kafin na kara karar tv nan naga babu komai a cikin kofin ko na miki dukar da sai kin had’iye kofin baki d’aya.” Jikinta na rawa ta dauka, ta kifa a bakinta, tana sha tana yunkurin amai, Ai kuwa tana shanyewa amai na zuwa mata, duk ta kwara mishi a jiki. A tsorace ta ja baya tana kallon kayan shi da shi kan shi Yadda ta jika shi da aman, wulla mata remote yayi ya bar falon. Dariya tasaka tace. “Dan gayu toh yau na ga karhen gayu tunda na zabga maka amai na kuma sai kayi yadda ka gadama dani”5 _Allah ka shirya mana haula! Amma Parih na bidar du’a’i 🤣😂_ Tashi tayi abinta ta bar falon, ta nufi kitchen, lek’awa tayi taga Baba talatu na saka kafi zabuwa. Rike baki tayi sannan ta juya sai da ta kusan fita daga gidan tace. “Iya Talatu ki daina mana barbad’e a cikin abinci” Kuma da karfi ta fad’a sannan ta ficce a gidan. Hanyar dakin Jalal ta nufa, yaji yana magana kasa kasa, lek’awa tayi ta hango hansatu bisar shi. Komawa tayi ta zauna tana kallon kofar dakin shi, har AMIDUD yazo ya wucce bai ce mata Komai ba, itama bata ce dashi komai ba, sai ma kauda kanta da tayi, tana kallon can gefen gidan. Har ya wuce sai yaji bai yarda da ita ba, dawowa yayi ya koma d’akin shi yaje ya zaro wayar rediyo, bata aune ba ya tsula mata a gadon bayanta, sai da ta fasa ihu tare da sosai gurin tana cewa. “Wallahi na tuba! Bani kuma leken su da maka aman da nayi”+ Da gudu ta bar gurin tana ihu sai ka rantse dukar mutuwa. Sai da kowa yafito a gidan, suna tambayar lafiya. Jikin Mamie ta shige tare da sake wani Irin kuka, me cin rai tace. “Mamie! Kice mihi bani kumawa, kar ya kuma dukana akwai zafi.” Dariya Aarib yayi cikin mugunta yace. “Madalla yau an kawo mana ƙarshen fitinar” ….. Bayan shigowar ta ne ya tsaya kallon kofar d’akin Jalal, bugawa yayi, a firgice Jalal ya ture Hansatu. Ya leko ta taga. “Waye?!” “Fito Ni ne!” Wandon shi ya dauka ya saka sannan ya janyo rigarshi ya zura, buɗe ban daki yayi yace. “Kishiga ban daki ina zuwa.” Shiga tayi ya rufe sannan yazo ya buɗe kofar dakin, shigowa AMIDUD yayi yana duba ko ina na ciki d’akin.. Sannan ya duba kasa, ganin inner wear duk sai jikin Jalal ya dauki rawa. Takaici ne ya kama AMIDUD ya gyara tsayuwar shi sannan yace. “Gatan da ya nuna maka ne ya lalata ka ko?! Me kake bukata?! Idan auren kake so ka sami Daddy da maganar ko kayi ƙoƙarin haka bai kulaka bane” Girgiza kai yayi tare da sunkuyar da kanshi kasa yace. “Wallahi Yaya na sami Mama da maganar ta hanani ta kuma gargad’e da kar na kuskura na gayawa Mamie ko Daddy, Ni kuma bazan iya cigaba da tsare kaina bane, muka fara sama sama da hansatu kuma gashi yanzun munyi nisa” Dafe goshi AMIDUD yayi sannan yace. ” Kacewa Ita Yarinyar ta fito taje tayi wanka, wanka kai ma kuma kayi kusame Ni da dare.” “Toh” yace mishi a sanyayye. **** Da dare sai da aka kai ruwa rana da Aunty Amarya kafin ta amince Da maganar Auren Jalal, dan tace bai isa aure ba.2 ……… Washi gari tana tsaka da barci aka tasheta, dakyar ta bud’e idanu hanyar ban daki Buhayyah ta nuna mata ta wucce koda ta shiga tafi minti arba’in a ciki sai da yazo ya buga tayi wanka tafito, Doguwar riga tasaka sannan ta lab’a mai wai tashafa sannan ta fito falo, tana fitowa ta nuna mata gurin cin abinci taje taci kamar zatayi kuka, tana idarwa ya nuna mata hanya suka fita, tun da tashiga motar ta kifa kanta har suka isa sunshine nan ya kaita aka mata tambayoyi, bata sani ba, karshe shi ya basu amsar ya kuma roki alfarma a bata aji hudu na primary, sannan suka mishi lissfin komai ya fito tare da ita, dan ya fahimci har da gudummawar jahilci yake haukata. Suna fitowa daga makaranta dake bai shiga da motar shi ba, ya yana gaba tana baya, kallon wani yaro yayi yasaka yara a gaba sai make su yake, a karanbana tana zuwa ta samu wani bulala ta fyada mishi a tsakiyar kai, sai ta ya fasa ihu, ta yar kamar ba ita ba, sai da take kusada me yalo ta tsaya tare da marairaice fuska tace. “Ayya! Bawan Allah bani mana guda d’aya.” Murmushi mutumin yayi ya dauki uku yasaka a leda ya mika mata, tana karb’a tace. “Nagode,” Ta zura da gudu dan har ya tadda motar ita yake jira, kallon ta yake da abinda take, shi ba me yawan magana ba, amma zuwan shi yarinyar nan tasa shi magana. Dole ya zaneta idan suka koma gida. Da gudu ta isa jikin motar ta shige, tana buɗewa ta shige tare da jan murfin motar girifffff. Manyan kenan, juyawa tayi ta kalle shi tare da washe mishi haƙora Tace. “Zaka ci?” Yadda ya tamke fuska ya sata shiga hankalinta, ta fara cin yalon kamar me cutar yunwa. Tana taunar yalon kamar tanayi a kunnen shi, tsaki yayi tare da buga mata tsawa. ” Zaki daina tauna nan ko sai na watsaki waje.” Cak tayi shiru tare da gayyato wasu fake hawayenta ta shiga cewa. “Don Allah! Karka wurgani waje yar kurkura ta take ni! Dan Iya kaka tace hine ya kahe min iyayena, kaga kai su Baffana da Mamie suna nan Ni kuma bani da.” “Zaki min shiru ko sai na wurgaki” “Uuuuu! Da gaske kake Yaya dan gayu” A fusace ya juya tare da zare mata ido. “Yo ai wannan zaro ido sai kace wanda aka tsikara maka allurai ba adadi”1 Make mata baki tayi, ta kuwa rike bakin kafin ta fashe da kuka, irin me cika kunne nan, suna isa gidan ya taka birni kamar zasu hantsila. “Yo ka hwasa min baƙi ma balle dunguren yar a kurkura, kawai ka buɗe min yar a kurkura ko nayi maka sayi a ciki.”+ “Idan baki da hankali kiyi mana” Tallahi zan yi” “Allah ya baki Sa’a sha-sha-sha” Kallon shi tayi kafin tace. “Alqur’ani bani ce shen me ruwa uku ba” Zaro ido yayi wato ba ita bace. Sha-sha-sha ba, Fita yayi ya je zargo bulala tana fahimtar yaje nima ai kuwa ta balle motar tafita da gudu, zuwa cikin gidan. Bata tsaya ko ina ba, sai gadon Mamie da takalminta ta haye. Jikinta na rawa dan bata manta bulalar da yayi mata ba. Dake ta wuce yan gidan a falo, basu samu da susan meke faru ba. Shigowar shi da bulala yasa suka fahimci shi ta tsokano. “Karka fara dukar min ita! Wallahi bani son mugunta! Haka kawai daga dawowar ka ka zaneta yanzun kana harin dukarta na biyu raina zai ɓaci matuka gaya.” “Mamie! Zagina tayi fa, nace mata sha-sha-sha tace min shen me ruwa uku!” Dariya duk suka saka a falon, “Uban me kukewa dariya” Tsit suka yi,. “Wallahi jeka zaneta Son! Karka raga mata.” Mamie zata yi magana! Aunty Amarya ta hanata, dan dole ta shiru ya shige dakin ya shiga tsulla mata bulalar, duka biyu yayi mata amma sai ka rantse zaneta yake kamar me, a na ukun ta daka tsalle. Ta cacume mishi riga, fuskarta na kan cikin shi, sai wani irin kuka take sakewa, sake bulalar yayi tare da tureta ta fadi. Fita yayi daga d’akin ran shi na kara ɓaci. Buhayyah da Allah ya daura mata kaunar Parih yana fita tana shiga dakin, ta sameta shame-shame. “Wayyo Allah Mamie kizo” Gaban Mamie ne ya fad’i, dole ta mike taje, tana shiga ta sami Parih sai nishi take zaka rantse wani mugun duka aka mata.1 Da sauri Mamie ta isa gareta, “Wayyo Allah na! Ni kam ku kai Ni gurin Iyata, Alqur’ani da ya zuba min bulalar shi cewa nayi an sake Ni da igiyar rama ce.”1 Kware cinyar ta tayi wanda suka yi jajjur sabida farin fatar ta. Rarrashin ta Mamie tayi sannan ta fita, ta same shi ya shigo daukar kofi, aikuwa ta shiga fad’a sosai. Shiru tayi tana gamawa yace. “Kuyi hakuri!” Wannan dabi’ar shi ce da zaran tayi fada ya bata hakuri (🙄🤔 Ban da yaran mu na yanzun kina musu fad’a suna kallon cikin idanun ki Allah ka shirya mana zuri’anmu tafarkin addinin Muslunci) Jikinta ne yayi sanyi dan itama yasan halin shi bazasu kuma kara cewa kome ba. …….. Rikicin da Parih tasaka musu ba iyaka, dan rigima take Sosai ita sai dai A maida ita Dabji, kuma abin dariya tana ganin AMIDUD zata had’iye kukan ta, domin kuwa tana tsoron kar ya kuma zaneta. Satin sa biyu aka kai tambayar niman auren shi da Lamisah, sai Jalal da Hansatu dan Daddy yace babu inda zai nima mishi Y’a sai dai ya auri wacce ya b’ata. Ranar monday dakyar Parih ta tashi daga, shima sai da Aka ce ga Ya AMIDUD shine ta tashi tare da bare musu baki tana kuka, a haka tayi wanka, da aka kawo mata abin karyawan taki ci wai ita bazata karya da taliyar Bature ba, ita gaya zata ci. Zan iya ce muku gabaki d’aya Parih ta hana kowa sukuni, sabida zata boko, da ya tuna inda zata kuma sai ta fashe da dariya, wai dan kar tayi rigima Mamie har da saka mata caferi son, da snack, koda aka kaita taga sun juya sun barta da ta rasa ihu, sai ga yara ƙanana suna mata dariya. Dakyar aka jata zuwa cikin makarantar. Ranar da babu abinda ta tsinana sai kuka, tasaka jakarta da aka bata tare da basket ɗin ta, tana kuka. Ana tashi sha biyu da rabi tazo gurin me yalo, tana zare ido. Ɗauka yayi ya bata, tana amsa tace. “Nagode! Baba me yalo.” Tana juyawa sai akan Idanun AMIDUD, sunkuyar da kai tayi tana motsa bakinta. Har ta shiga cikin motar juyawa yayi ya kwad’a mata rankwshi, har ta ɓare baki zata yi kuka, ya zaro wayar caji. Had’iye kukan tayi sukan tayi. Goge kwalla tayi suna shiga cikin gidan ta wurga da kayan tace. “Wallahi bani komawa makarantar arna.” Duk yadda aka so ta fahimta taki sai da Baffanta yasa baƙi, bata ga abinda aka samata a jaka ba, sai da aka zazzage nan taga kayan dad’i ta lakuci chocolat tasaka a bakinta tana lumshe idanu tace. “Yoh Mamie indai kullum zaku na saka min wannan abun Alqur’ani bani kuma cewa ban zuwa makarantar” Haka tayi ta surutu, tana gama ci ta tashi, tabi kofar baya, dan taji anata aiki a can inda Jalal da AMIDUD zasu zauna da matan su, tana shiga bata tsaya ko ina ba sai inda ya kayan motsa jikin shi, irin karafuna nan. Tana zuwa abinda ta fara, hayewa kan wani karfe, tayi nan ta tab’a can karshe dai sai da ta balla mishi wani karfe sannan ta mai da tare da barin gurin, bata tsaya ba ta nufi kofar baya wanda ya zagaya da ita dakin shi, tana shiga taga wayar shi da laptop din shi, dake akwai nasu Buhayyah suna game, tana zuwa ta shiga goge mishi files tare da ɗaukar wayar shi tana hoto ita nan, wango robar ice cream tayi, dira tayi ta bud’e ta fara sha, tana jin motsin ta sake robar ta bangaji mirror sai da turaren shi ya fado ya fashe. Tuni ta ficce tare da sake kofar garammmm.1 Jin motsin ya sashi fitowa daga ban dakin, yaga a min shi d’aya d’aya da daki, ga turaren shi a fashe. Ga Ice cream da aka bude sai wayarshi da take ya she a kasa, da ga laptop din shi a kune. Komai dai a wargaje. Zama yayi ya dade goshi Yace. “Parih! Dole na zane ki kai wannan yarinya ta zama fitina” Shiryawa yayi sannan ya fito, ta tsaye a kusada Jalal da yake waya da abokin shi, ta dauko macuci roba ta rab’a mishi, Zaro Ido AMIDUD yayi…. 🤔🤔🤔🤔😏😝 _Wallahi ayin mahaukaciya ce_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *