MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 27

MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 27
“Malam Sadeeq Kenan, ada kasanni ba yanzu ba.” 
Shareta yayi ya nuna tamkar ma bejita ba ta juya tana kallonsa ta kuma daukar wayarta daya cillo mata. Madubin saitin kujerarta ta bude tana gyara fuskarta ya girgiza kai dan shi dama yasan da wahala yarinyar tayi hankali sabida babu arabi ba boko yaja tsaki har kusan sau uku sannan INdo ta kallesa tace. 
“Babu kyau fa.” Yace “Ni zaki cewa babu kyau? Ko kin fini sanine da zaki cemin babu kyau?!” 
“Allah ya baka hakuri, cewa akayi idan kaji wani ko wata sunyi abinda ba kyau ka tuna masa, toni tuna maka nayi.” 
“Karki sake tuna min domin tun kafin kisan hakan nasani, ke karki sake yin magana har muje inda zan kaiki kina jina.?!” 
Bata sake kula shiba har sukaje danja masu tallar abubuwa suka dinga dago musu taga me alawar madara da sauri ta zaro dari biyu ta mika masa ji Sadeeq kawai yayi tana cewa. 
“Bani ta dika.” 
Aikuwa ransa ya kuma mugun baci Allah-Allah yake kam a gama miko mata ya figi motar amma danja batazo kansu ba harsai da aka bata tasa ajaka sannan aka basu hannu. Leda 
daya ta mika masa tace. “Malam Sadeeq bisimillah.” “Banasha.” 
Maidawa tayi cikinjaka ta bude leda daya tana sha har wani kunkuni takeyi irin na zakin nan idan ya gauraye kunne. Wayarsa ya dauka yasa earpiece tare da kiran layin Fateema, sai data kusa yankewa sannan yaji ta daga cikin sanyin murya tayi mai sallama. 
“Ohh babyna har yanzu jikin ne?!” Ya fada cike da damuwa, can barin Fateema tace. “A’ah kawai dai bacci nake, kun tafi ne?” 
“Eh muna hanya ma yanzu zan dawo insha Allah, amma ki tashi ko tea ne kisha zaki kuma samun relief.” “Toh Allah ya kiyaye hanya a gaida min ita.” Tana kaiwa nan yaji ta katse, ba haka yaso ba yaso suyi hira ta debe mai kewa amma tariga ta kashe ya cire earpiece din yana cigaba da tukinsa ba tare daya sake kallon koda inda take ba. 
“Malam Sadeeq dan Allah ka karba kasha, wallahi tayi dadi madara ce zallah.” Yayi shiru ta kuma cewa. “lnkaji dan Allah sha d’aya kaji.” 
A fusace ya juya yana kallonta shi har lokacin be manta yanayin ta na baya ba cikin bacin rai yace
“Wai dole sai na Shane? Idan dole ne toh sani insha dan Allah.” Ya fada tare da d’an kallon gabansa kafin ya juyo yana dankara mata harara, daya ta dakko da sauri ta danna mai ita a baki yayi saurin furzar da ita a kasa amma duk da haka sai da zakin ya shiga ko’ina na cikin bakinsa ya samu gefen titi ya tsaya tare da nuna ta da yatsa yace.
“Wallahi tallahi Aisha ki kiyayeni karkija wata rana na ballaki yasin. Kinga ina shiga sha’aninki ne? Toh ki kuka da kanki duk rashin kunyarki a tafin hannuna take..
Jan bakinta tayi ta tsuke bata sake cewa komai ba har suka shiga garin Sumaila, tana ganin barkono dama sundan tsaya sabida ana bada hannu batare da tayi mai magana ba kawai yaji ta bude kofarta fita tana cewa. 
“Bari na siyawa Inna barkono da gyada ko kwano daya-daya ne.” Kafln ya harzuka yayi magana ta karasa wajan, Sadeeq ya kifa kansa a steering shi kam ya shiga uku wannan wace irin yarinya ce tana ganinsu a tsakiyar titi amma ta balle murfin motar ta fita. Idan ta dawo sai ya mareta gobe bazata sake yi mai makamancin haka ba. Karasowa tayi wani yaro na biye da ita a baya da kaya ta bude gidan baya ya zuba sannan ta bashi naira hamsin ta shiga motar ta zauna tare da kallonsa tana gyara mayafi tace. “Malam muje na dawo, wallahi kuma da arha shi yasa na siyo mata kwano biyu-biy ….. 
Bata karasa ba taga ya d’ago hannu tayi saurin sunkuyar da kai tare da boyeshi tana sauke ajiyar zuciya cike da tsoro da mamaki. Fada ya fara yi mata kamar ya samu student dinshi har ya gama bata dago ba ya figi motar taji sun fara tafiya sannan ta dago tana kallonsa. 
Kasa yin magana tayi ganin yadda yayi kicin-kicin da fuskarsa dan haka ta share Sa har sukaje kofar gidansu. Mutane kuwa aka fara murnar ga lNdo ga lNdo, wadan da suka sanshi kuma suka dinga gaidashi yana amsawa da kyar tamkar beyi rayuwar garin ba. Kayanta ta kwasa tare da shiga cikin gidan su bata sake fitowa ba, shiru-shiru yaji babu wanda ya leko shi kuma jira yake su gaisa koda Inna koda Malam Hamza amma babu kowa daya fito daga gidan haushi da takaici suka sa shi ya tafi ba tare daya aika ankira wani ba. 
A cikin gidan kuwa lNdo cewa tayi musu ai ya tafi hakan yasa Inna bataje sun gaisa ba su kuma murnar zuwan lNdon yasa basu ma bari su ganshi harya tafi ba Har Sadeeq yaje gida be denajin haushin abinda INdo tayi mai ba, lokacin da yaje gidan a cike yake da ‘yan uwan Fateema hakan yasa shi juyawa yayi hanyar gidan su ba tare da ya shiga ba dan yasan akwai wadanda zasu yi mai kallon banza. 
Mama na ganinsa hankalinta ya kwanta tace. “Yauwa Sadeeq har ka dawo?!” “Eh suna gaida ku.” Ya fada yana kokarin zama a kujera, Mama tayi murmushi cikin jin dadi sannan ta shiga daki ta kawo mai abinci, beyi musu ba yaci dan yasan Fateema ba iya yi zatayi ba sabida ciwon marardaya barta tana yi. Yana gama ci ya fita yaje can gidan marigayi ya gano sannan ya wuce gurin abokinsa har sai da aka kira magariba sannan ya koma gidan. 
Bayan sati biyu Abba ya gaji da sanya mai ido da safe ya kirasa, yana zuwa sai daya shiga suka gaisa da Umma da Mama sannan ya shiga gurin abban. Gaisawa suka yi Abba ya kallesa tare da ajiye magazine d’in hannunsa yace. “Sadeeq yaushe zaka koma kwaran ne?” “Abba nan da kwana uku insha Allahu zamu koma.” “Kai dawa?” 
Sadeeq yace, “Abba da Fateema mana.” “A‘ah Sadeeq ya kamata ka farayi musu adalci tun yanzu, ina son tunda zuwan nan na karshe da Fateema kukayi toh wannan karan sai ku tafi da Aisha bana son ta cigaba da zama da auranka acan gidan su ina fatan ka fahimce ni.?!” Wani irin bacin raine ya ziyarci ran Sadeeq kansa a kasa yana danna yatsansa cikin zuciyarsa kuwa abubuwane kala-kala a cikinta. Jin yayi shiru ne yasa Abba kuma yi mai magana Sadeeq yace. “Abba ai tafiya ta da Aisha garin nan bazai yiwu ba sabida kaga su ba Hausa sukeji ba itama kuma ba yarensu takeji ba dama tanajin turanci ne da sauki amma gaskiya tafia da ita matsala zai jazamin wallahi, nasanta tun kafin Abubakar yasan ta.” Toh yanzu me kake nufi?!” 
“Abba kawai zan samu gida na ajiyeta anan idan yaso sai ta zauna a ciki har mu dawo.” Abba ya kallesa sosai kafin yace. “Kana nufin ta dinga zama anan har lokacin da zaka dinga dawowa yayi.” 
Sadeeq yace. “Eh Abba idan ba hakan ba wallahi bansan yadda zanyi da Aisha ba idan mukaje can, gashi ta raina ni sam bata ganin girmana tun sanda na koyar dasu a makaranta.” “Shikenan kafin ka tafi kaje ka daukota sai ta tare anan gidan Najib tunda naga ya 
Kammalasa kuma ‘yan haya zai zuba gashi dai-dai itane gidan.” Sadeeq yayi shiru tunani yake yana kuma jin takaici, kawai yana zaman-zamansa an dauko mai wani aikin, yanzu duk shekara sai ya bada kudin gidan hayar da lNdo zata zauna dubu dari da talatin. Mtwww yaja tsaki ba tare da yasan ya fito fili ba sai da yaji Abba yace. 
“Sorry kona shiga hakinka ne??”Da sauri Sadeeq ya hau kada kai alamar a’a sannan yace. “Toh Abba kuma ni zanje na daukota? Na d’auka kawo ta zasu yi.?!” “Eh toh kuma hakan dai yafi, amma ina son ka kara daga tafiyar ka harta tare sannan sai kutafi.” 
Dakyar ya iya amsawa Abba sannan ya tafi. Yau ya kuma yin Nadamar zuwa tsefawa secondary school domin zuwansa ne yasa Abubakar ya ganta harya aure ta gashi ya mutu shi anbarsa da alakakai. 
Yana komawa gida ya bawa Fateema labari tace Allah ya sanya alkairi, kallonta kawai yayi ya shige daki. Cikin kwanaki biyu tal Abba yasa Sadeeq aka kwaso kayan INdo na gidan Abubakar harda wanda duk shine ya siya aka kaisu gidan da INdon zata zauna a matsayinta na Matar sadeeq. Su Haleema Rukayya da Amina yasa sukaje suka kwaso kayan sawarta suka kai can gidan akajera mata sai dai babu dining area gashi INdo tana matukar sansa dan idan tana kaiji take tamkartana kusa da sharukhan. Sadeeq da Umma da Hawwa suka tafi d’akko INdo, hirarsu ce duk ta sashi mance wadda zasu je su dakko har suka karasa kofar gidansu INdo wanda yake cike da mutane wai ashe su biki suke yi wannan abun ya konawa Sadeeq rai sai kace wani sabon aure mtsssw. 
Sun dade a ciki kam a fito da ita su Uwani sai mata murna akeyi ta baro gidan dadi zata koma gidan dadi INdo taja tsaki ita kadai tasan gidan da zata shiga dan tasan sam basanta yake ba ta kuma riga ta shirya ma zama dashi a kowane irin yanayi indai bazai hanata abinci da fita yawo ba. 
A kusa da Umma ta zauna yayin da Hawwah ta zauna gefensa anata yi musu fatan sauka lafiya bayan Malam Hamza yazo sun gaisa dashi Sadeeq din ya kuma bashi amanar ‘yarsa sukaja mota suka tafi. 
Tunda suka kama hanyar komawa yaja bakinsa ya tsuke jin INdo ta zage sai suburbida hira take ‘tamkar ba amarya aka dakko ba, yaja tsaki ganin sam babu jan aji a tattare da ita. Suna zuwa a kofar gidanta suka sauke ta su Umma suka shigar da ita ganin amarya yasa makotanta suka shiga suma dan su ganta. Har kusan karfe shadaya na dare Sadeeq be shigo gidan ba, gidan yayi matukaryin kyau domin yasha tiles bangon da kasan ta ko’ina sai dai bekai girma da tsaruwar na marigayi Abubakar ba amma hakan be damu indo ba domin na iyayanta sam be kama kafar nasuba. Kallon agogo Hawwah tayi tare dajan tsaki tace. 
“Wallahi Yaya Sadeeq dan wulakanci ne, yasan fa munajiransa amma bazai zoba ga mijina can sai waya yake yomin.” “Kinga yaya Hawwah kiyi tafiyarki mu zamujirashi.” 
Haleema ta fada tana gyara kwanciya akan kujera hannunta rike da waya wanda hakan yake nuni da cewar chatting takeyi. “Ba haka mukayi da Abba ba, cewa yayi karmu bar gidan nan sai na tabbatar mai da shigowar Yaya Sadeeq.” 
“Toh saiki zauna gyara wani auran ke kuma ki ballo naki ba.” Waya ta zaro zata kira Abba sukajiyo sallamarsa a kasan makoshinsa. Tashi kowanne yayi yana sanya mayafinsa ya zauna a kan kujera. Toh Yaya Allah ya bada zaman lafiya.” 
Yayi shiru yana canza channel Hawwah tace. “Yaya ina muku addu‘a kayi shiru.” “Ke malama ku wuce kutafi gida bana son sa ido.” “Amin yayya Hawwah mun gode a gaida gida da abban siyama sai munzo.” Suka jiyo muryar INdo tana fitowa daga bedroom, hatta shi kansa saida ya kalleta ta gyatsina mai hanci tabi bayansu danyi musu rakiya. 
“Amarya kamar karmu barki wallahi.” 
“Allah sarki Aminatu idan Allah ya kaimu basai ku dawo ba.” “Zamu zo amma da yamma kinga gobe monday akwai makaranta.” Cewar Haleema INdo tace. “Toh koma dai yaushe ne sai kunzo a gaida Mama.” “Zataji.” 
Suka fada tare dajuyawa su shiga mota wanda driver na jiransu itama tajuya ta shiga ba tare da ta kulle gidan ba. Zama tayi a falon tana wakar Nas ya shareta yana kallonsa itama bata kulasa ba domin ba so takeyi ba daman. 
“Kejeki kwanta dare yayi.” 
Yayi maganar yana gyara kwanciya akan kujera. Itama ta gyara zama tare da daukar remote tana murmushi tace. 
“Wallahi malam Sadeeq banajin bacci.” 
Hade rai yayi domin yana son yin waya da Fateema ya rage mata dare yayi mata alkawari gashi wannan yarinyar zata samai ido. 
“Ke bakyajin magana ko? Kin tashi kosai ranki ya baci?!” 
Tashi tayi cike dajin haushi ta shiga bedroom, kan gadon Abubakar datake so shi aka sanya mata a daki dayan kuma dayake matsayin nata aka sashi a dayan dakin da ake nufin na sadeeq ne. Tana kwance kawai ya fado mata ta zura hannu karkashin filo wayam babu sweet dinsa da yake ajiyewa ta kalli agogo da yanzu suna tare kawai ta mike ta koma falon tana kikkifta ido. 
“Idan Zan iya zama ni daya a dakin Allah ya tsinen. Sadeeq dake manne da waya a kunnensa yaji ta fada. A hankali yace. “Babyna wait zan sake kiranki.” Kashewa yayi tare dajuyawa ya kalleta sai kuma ya juya ganinta sanye cikin riga da wando pink and white na bacci sun kuma zauna ajikinta das duk da basu kamata ba yace. “Toh kina son nazo mu kwanta tare ne.” 
“Malam Sadeeq k0 bakazo badai toh kabarni anan.” 
No baki isaba ko kuma ki kwanta anan din ni saina shiga ciki.” Zama tayi kan kujerar tare da cewa,. 
“Tunda waya kakeyi toh ka karasa anan idan ka gama sai ka tafi nasan sannan nayi bacci bazanji tsoro ba.” Mtwww yaja tsaki ta kwanta suna kallo duk sunyi jigum har wajan 1:45am duk ya gaji ita kuma sai a lokacin tadan fara lumshe ido ya zaro wayarsa ya lalibi Fateema amma abin mamaki switch off ya cillar da wayar gefensa yasan haushi taji be kiraba yanzu kila tana can tayi mai fassara kala-kala. Atakaice duk anan falo suka kwana, haka har yayi kwanaki biyu a gidanta washe gari Sadeeq da Fateema suka wuce kwara state cike da farin cikin su ita kuma lNdo aka turo mata Aminatu ta taya ta zama.. 
Hmm wannan zama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *