MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 31
“Wallahi ni dai baza ni ba, haba-haba dafa bakin kafa kace wai ba zakaje dani ba sabida ni banajin turanci, toh wallahi yasin yanzu dakaji na faraji ba zan bika ba Allah kuwa.”
“Idan nace kuma sai kinje fa ya zaki yi?!” “Ai karka ma fad’a dan ba binka zanyi ba, kaje ku tafl da Fateema.”
“Aisha…!”
Ya fad’a cikin gentle mood wanda yasa lNdo saurin kallonsa cikin ido hudu, hannunta ya janyo yana kallon fuskarta a fili ya fara magana besan ma a fllin yake yi ba.
“Aisha My heart is filled with instantjoy, you give me everlasting warmth. Aisha your eye’s, your nose, your pretty cheeks your mouth, your chin, the whole of you all are sweet and so you are. Please Aisha ki bini wallahi babu abinda zan miki kinji na rantse.”
Kallonsa kawai lNdo tayi sam duk ta kasa gane abinda yake cewa hasalima dabarbarta ta yayi kwakwalwarta ta fara hasashe kafin tace.
“Dare nayi malam Sadeeq kaje ka kwanta nima kwanciya zanyi na gaji.” “Toh zaki bini mu tafi din..?!”
“A’ah wallahi bance ba.”
“Wai me yasa kike da taurin Kai ne Aisha?!”
“Malam Sadeeq wane kai ne me laushi?!”
Mtwwww yaja tsaki tare da sakin mata hannu yaje ya dauki mukulli ya tafi rufe gidan sannan ya dawo, yana dubawa ya tarar ta rufe d’akin ta ya san ko magana yayi ba bud’e mai zata yi ba kawai ya kwanta a falo. Washe gari yana yin sallah yabar gidan bayan ya ajiye mata 10k ya tafi gidan Fateema.
Yana zuwa ya tarar harta gama had’a mai kayansa ita kuma tana kokarin shirin zuwa gurin aiki. Sai da ta temaka masa ya samu relief sannan suka shirya tare suka fito ta samu napep shi kuma ya Shiga mota yayi gidan su dan yi musu sallama. Suna gamawa yajuya ya d’auki hanya bayan yasawa ransa cewar zai gwada musu shi d’in namijin duniya ne sai sun nemesa musamman INdo da bata ganinsa da gashi aka.
Bayan watannin uku.
12:30pm tana tsaye a makalejikin bishiyar darbejiya sai makaka ruwan sama ake yi, ta gaba da tsaya sai faman tangadi take tamkar ana tura ta, sam ba tayi tunanin ruwan zai yi yawan haka ba kafin ta karasa gida daga school. Hakan ne ya bata damar tahau napep tayi gidan Asma’u tsautsayi kuma yasa ta fito tace ita gida zata tafi.
Horn din mota taji amma batajuya ba sabida ko ganin hanya bata yi sabida karfin ruwan. Kuma yi mata horn yayi da nufin idan tana son temako idan kuma yayi mata sau uku toh zai rabu da ita ya kara gaba kila ba bil’adam bace.
Tana jin ya kuma yi ta fara laluben inda taji motar har Allah ya temake ta hangota, a hankali taje wajan kofar ta bude a she ta saitinsa ce sai ji tayi yace.
“Ke daga inama kike haka..? Ki zagaya ba ta nan zaki shigo ba.” “I am sorry sir…, I am Aishat Hamza by name so please don’t call me ke again…”
Ta fada tare da dan bude ido ta kalli motar, da sauri ta zagaya ta dayan gefen ta shiga ganin Sadeeq nejikinta sharkaf ya kalleta baki bude ta zauna sai ya kauda kai tare da
mika mata wani dan kyalle ta karba tana gage fuska dashi kafin shi kuma yaja motarsa suka fara tafiya a hankali kasan cewar ruwa ake yi sosai tamkar da bakin kwarya.
“Ke wai daga ina kike haka cikin wannan ruwa?” “Please sir I told you am not ke, kace min Aisha and daga school nake..” “K’arya ne ya aka yi banga students k0 d’aya ba sai ke kadai zaki tsaya yi min wani turancin banza.”
“Hmmm oga Sadeeq you don’t know justice is the best policy ko?!” “Kut..!” Ya fada ba tare da ya san ya fito fili ba sabida tsananin mamakin ta da daurewar kai jin abinda take ce mai. Juyawa yayi yana kallonta tana goge fuska ya cije lips dinsa na kasa har suka karasa bakin gate d’in gidan da, tayi niyar fita taji motar a kulle sai ta kallesa tace.
“Malam Sadeeq we are here fa, please ka bude min zan fita thanks for the help.” “Karki fito ki zauna a ciki na gaya miki.” Yafada tare da zarar mukullinsa na gidan ya fita da kanshi. Kallo tabishi dashi sai tayi murmushi lokacin ta tuno da Abubakar sam baya daure mata fuska tun lokacin da ya dakkota daga Saye, yakan yi mata duk abinda zai sa tayi dariya k0 ‘ayi farin ciki amman wannan gadai kaman nin sak amma zuciyarta banbanta.
Dawowa yayi cikin motar shima duk ya jike, shigar dasu yayi har parking lot da yake karami ne dai-dai mota daya INdo ta bud’e ta shige daki kasan cewar babu nisa befi taku hudu ba. shima yana gama parking ya shiga falo bata nan ya wuce bedroom d’inta, tsaye ya ganta d’aure da zani ta juya baya wanda da alama da taji motsinsa ne tayi saurin yin hakan.
A hankali ya taka yaje har kusa da ita ya tsaya, matsawa yaga tayi gaba shima ya matsa har takai karshe sannan yace.
“Go on..”
“Aisha you’re beyond my control ko meye dalili ne?!” “Because we don’t love each other.” “You dai but me….”
Yayi shiru yana kallon keyarta don har lokacin bata juyo ba sabida wani dalili nata da bata son ya gani. Ji tayi ya rungumeta tayi saurin rintse idanuwa jin yadda tsigar jikinta ta tashi yarrr yana kokarin dora hannun a saman kirjinta tayi saurin rike mai hannu.
“Please don’t touch me.”
Akan wane dalili Shin Aisha an hanaki yin yaren Hausa ne?
Tayi shiru tana kauce mai da sauri ya finciko ta suka fad’a kan gado harzanin da tayi daurin kirji dashi yana zamewa tayi saurin tashi a firgice shi kuma yasa hannu ya dawo da ita duk da cewar kayan jikinsa a jike suke. “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un malam Sadeeq ka takaita ni kil…“
Da sauri ya mike zaune jin abinda ta fada, itama ta mike cikin kidima ta sauke zanin kasa ya zamana bra ce kawai tayi saura daga cibinta zuwa sama, hannunta a saman cikinta daya dan fito wanda ba kowa yake gani ba idan ba kwance zani tayi ba ko kuma tasa t.sheet yaga tana shafar cikin bakinta a cune tana shirin yin kuka yace. “Aisha what’s going on.? Ciki gare..Ki..ne…!”
Bata bata lokacin ba ta daga mai kai sabida Asma’u tace mata kar tayi abinda zai sa cikin ya samu matsala yau gashi Sadeeq zai nakasa mata shi. A zabure ya dawo kasa idanuwa waje INdo na hawaye ta narkamai harara mai tattare da tsananin bakin ciki ya kalleta kirjin nan fam ya kuma yin kyau cikin in’ina yace.
“How come‘s daga yi daya…?!” “Ka kaini asibiti nidai, idan da bakayi ba da zaka ganshi ne yo ai gashi ka dauje ni.”
Ya akai haka daga one day wanda yasha matukar wahala ace mai tana da ciki ga Fateema
da suka dade tare ko batan wata bata taba yiba amma INdo nada Ciki..,ya kuma kallonta sai hawaye take yi bayan ta gyara daurin zaninta gashi har lokacin ruwa ake tsugawa Sadeeq ya koma kan gadon tare da zama a bayanta a hankali ya rungume ta tare da rintsa idanuwansa yana jin wani feelings har cikin kahon zuciyarsa. ” “Aisha Allah ne ya baki Abubukar a lokacin da zaku fara sabuwar rayuwa sai ya d’auke sa ba tare da kowa yasan manufar yin hakan ba, an hada mu aure ba tare da muna so ba sai dai ko wannen mu ya dauki hakan a matsayin kaddara. Aishi kiyi hakuri ki gafarce ni wallahi duk abinda nayi nayi tane cikin damuwa da tashin hankali amma ke babu abinda ya dameki why.”
“Nidai ka kaini asibiti kawai dan Allah.” “A cikin ruwan nan? Dama gashi kinje kin kaimin shi ruwa ya jibgeshi kilama kinja mata/masa mura.”
Sake rikota yayi sosai a jikinsa yana yawo da hands dinsa tayi dif, ganin haka yasa Sadeeq matsawa ya kwantar da ita kan gadon ya kura mata kyawawan idanunsa yana shafar cikin ta a hankali saitin kunnanta yace.
How many months.” lNdo ta kawar da kai tace “Ai bakaso ka dawo ka tarardani a raye ba malam Sadeeq, sabida tunda ka tafi ko please call me baka taba gigin yi min ba. A gabana kasha yiwa Fateema waya sabida ita ‘Son ranka ce’ ni kuma ‘Zabin iyayanka ne’ hakan yasa baka san komai daya danganceni ba. Duk surutuna wallahi danaga kana yin haka ka watsar dani yasa naki nunawa kowa ina da ciki sai Asma’u da Mama sune kawai suka sani, sai gashi Allah ya raya ni da abinda yake cikina cikin k’oshin lafiya. Baya sani wani laulayi yadda neke komai a baya haka nake yi har yanzu.
Malam Sadeeq baka sona sabida kasan cewa ta ‘yar kauye, matalauciya, marar ilimi. Karka manta Allah dayayo ka cikin wadata bawai yafi sonka bane, Allah dayayo ka hazik’i fasihi mai din bin basira bawai dan yana sonka bane ko kuma dabarar ka da iyawarka ba kawai hakan ma jarabawa ce sai gashi kana min gori akan hakan. Shin ka manta twinnie broth dinka duk ya fika wannan felekan amma da Allah ya tashi sai ya bashi ni, ya zamto a duniya ni yake so harya koma ga mahaliccinsa. Shine mutum na farko daya fara tsamoni daga kangin wahala da toshewar kwakwalwa Allah ya gafarta mai haka kuma har cikin
zuciya ta yana nan I will never forget him..never..never….” “Kiyi hakuri Aisha.”
Yayi maganar jikinsa a sanyaye, INdo ta share hawayen fuskarta tana cizon lips, ruwan da akeyi ne ya haddasa wani sanyi me ratsa cikin tsokar mutum hakan yasa INdo takurewa guri d’aya, Sadeeq na ganin haka ya xura kansa cikin wuyanta idanunta a lumshe yace. “Aishi kinyi hakuri kin yafe min? Namiki alkawarin maye miki wanda yafi Twinnie d’ina, bazaka sake yin kuka dani ba har nima lokacin da tawa zata kasance. Ina son ki bani dama na shiga cikin rayuwarki nima na dan yi miki koda rabin abinda Marigayi yayi miki ne, ina rokonki alfarma ko yaya ne ki bari muyi rayuwa tare.”