MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 38

MUSAYAR ZUCIYA 





CHAPTER 38



Tunda Sadeeq ya koma gida be sanar da kowa zancen da suka yi da lNdo ba kasan cewar baya son duk wani abinda zaija ayi mata gori akai ba. Gidan kanwarsa Hauwa yaje suka yi magana hakan yasa duk abinda ya siyo ita yake kaiwa ga shirin gidan da ake yi mata wanda zata koma. 
Cikin kwana biyu ya gama had’awa washe gari ana sauran kwana biyu lNdo ta dawo yasa aka kai hawwa gidan su INdon takai kayan. Sosai aka dinga murna ana yiwa INdo barkar cewar mijinta ya fitar da ita kunya da kayan da babu wacce aka taba yiwa kowacce mace irinsa a kauyan. Shiri tayi sosai ciki da waje Rukayya ta kawo mata kayan INdo ta sake yin wani sassanyan kyau sam bata bari a sauya mata akidar da take da ita dan yanzu a kauyan akwai ‘yan matan da suke kwaikwayar shigarta da kwalliyarta har yafa mayafi ma. 
“Gaskiya Fateema kina da hakuri, ki duba ki gani a cikin shekara d’aya da auranku kishiyarki tayi zaman gidaje gashi yanzu mijinku d’aya amma zata koma wannan uban gidan na alfarma ke kina wannan duk da cewar shima yana da kyau amma nata yafi girma da kuma kyau ya kamata kema kiyi bori wallahi asan yadda za’ayi dake.” 
Cewar wata malama da suke kawance da Fateema tun zuwanta school d’in. Numfasawa Fateema tayi tana jin kirjinta na bugawa zuciyarta na zafi dan ta tabbatar da zancen aunty Hafsat gaskiya ne, gashi uwa uba ita bata haihuwa duk da bata fitar da rai da rahamar ubangiji ba a kan samun ciki. 
“Amma ni ina ganin ba wani abun d’aga hankali bane Hafsat ganin dama tun farko a cikinsa ta fara zama, karki manta gidan mijinta ne na farko kafin tazo mu had’e. Kuma a kishinkishin d’in da naji cewar an bashi gidan kinga dan ya mayar da ita ne baxan d’aga hankalina ba tunda itace ta fara zama a cikinsa.” 
“Lallai Fateema toh ai nan gaba na san zaki gane abinda nakeso ki fahimta.” 
Murmushi tayi kawai bata son nuna hassada akan lamarin tunda taga wanda ya narka kudin yayi abunsa Allah be barsa yaji dad’in daya tanadarwa rayuwarsa a cikin gidan ba. ldan ta tashi hankalinta akan abun itama Allah sai ya d’auke ta aga ta tsiya tunda kamar yadda Ummanta ta fada auran Sadeeq da Aisha Hadin Allah ne. 
Shiga yayi gidan ya tarartayi tagumi sam ba taji shigowarsa ba sai tsayuwarsa taji Sadeeq ya zauna a gefenta yana kallonta. Murmushi tayi mai sai dai iyakarsa lebanta kasan cewar ita kanta taga yadda yake rawar kafar dawowar matarsa dan yakan iya gaya mata zata dawo kusan sau biyar arana duk shigowa sai ya gaya mata hakan yake bata mamaki har take tunanin ko yanzu ya dena sonta ne, duk da cewar be sauya mata ba yana nuna 
mata soyayya fiye da tunanin me tunani. “Baby tunanin me kike yi haka?” “Babu komai baby kawai ina tunanin rayuwa ne.” 
“Hmmm da alama dai zaman kad’aicin nan ne yasa ki shiga tunani, toh na dawo kuma 
bazan fita ba yau ina tare dake soyayya zamuyi.” 
Yayi maganar yana rikota yana shakar kamshinta, ita ma tayi kok’arin Kawar da abinda 
yake damun cikin ranta. “Kai baka gajiya da aiki ne baby?” 
“Ehmm kinsan ai kedaya ce yanzu, kuma duka duka yaushe na dawo ai kinga nayi kokari baby.” 
Dariya tayi tana shafa kanshi ya lumshe idanuwa. Wato mata biyu Lafiya ne daga nan kayi nan babu fargaba bare tashin hankali dole maza suyiwa Allah godiya daya basu wannan damar. Sai gaf da magriba ya samu ya fita bayan sallan isha’i suka yi waya da lNdo sannan ya shiga gidan ba tare da Fateema ta gane sunyi ba. washe gari ya tafl Sumaila kauyan Sani yaje ya dakko matarsa. 
Yana zuwa ya buga mata waya ba’a d’auka ba sai gani yayi Sagiru ya fito, gaisawa suka yi sannan ya sanar masa cewar tana wanka Sadeeq yace ba komai sannan Sagiru ya koma gidan. Tana fitowa ta buga mai ya katse ya kirata da kanshi dan shine yafl can-cantar yin hakan ba itaba. 
“Cutie meye nayin wanka, da kin bari idan mun koma gida sai muyi tare.” 
“Hahaha..lallai a haka kake son na bar Sani zuwa cikin gari k0? Ban yadda ba gashi na fito kaya kurum zansa sai mutafl.” 
“Shikenan ai tunda abun ‘yar haka ne, ki turo a kawo min yaro na mu fara gaisawa nayi missingd’dinsa.” “Okey shi zaka fara gani ba niba ma ko?shi kenan bari a kawo shi sai ku tafi ni saina zauna a gidan.” 
“Wayyo cutie ki rufamin asiri I can die idan kika ki bina Zuciya ta zata iya shiga rudani zan iya rasa nutsuwa ta. Cutie kin zamo wani jigo a cikin rayuwata Ina sonki dan zan iya cewa nafi twinnie kaunarki Ina jin zuciyata na bugawa a duk lokacin dana tuna cewar bani na fara nuna miki soyayya ba but ki yadda cewar ni din ina wahala a cikin raina da rayuwata idan bake a kusa dani, please kiyi sauri ki fito mu tafi dan Allah.” 
“Gani nan fitowa barima a fara fito da kayan namu.” 
Tana fada ta ajiye wayan sannan ta Ieka tsakar gida ta kira su shehu suka fitar da kayansu. Tsab lNdo ta shirya Nafeesah ta shirya Ayman sannan ta fitar dashi, sai da suka gama 
shiryawa ta fita kallansa tayi ta glass din motar tare da cewa. 9 “One minute.” 
Makota suka shisshiga suka dinga yi musu sallama har sai da suka zagaye unguwar sannan suka koma Sadeeq ya gaida Inna sannan lNdo suka yi sallama da kowa na gidan suka shiga mota Sadeeq yaja zuciyarsa shar daya juya yagan su sai yaji wani farin ciki yana kuma ratsashi. 
“Cutie me dah, wai ke dan Allah bakya mamakin hakan?” 
“Bana yi, kai da ace fa marigayi bs dakko ni daga Saye ba da inajin yanzu ‘ya’yana biyu ko 
uku da wani saurayi na salele.” 
“Toh naji abar maganar waye wani salele ba ko dadin ji. Cutie nayi missing dinki amma ke da alama kamar bakiyi nawa ba.” 
“Abu Ayman kenan, karka fadi haka domin zaka zalince ni. Kawai ba yadda zanyi ne ko na nuna babu yadda zanyi tunda ko a gidan ka na zauna dole baka nan amma nayi missing dinka dan ma akwai Ayman ina kallonsa Zuciya ta na ganin kamar kaine shi yasa kaga banyi ramar rashinka ba.” 
Dariya yayi hannunsa na tabo kafar Ayman, haka suka dinga hirar yadda suka yi rashin juna har suka karasa kofar gidan marigayi wanda zata ci gaba da rayuwa a cikinsa. 
Kirjinta ne ya dinga bugawa Sadeeq yaje ya bude gate ya shigar da motar duk yana ganin yadda ta sauya jikinta yayi sanyi hannunta dafe da kirjinta idanunta a rufe. Hannunsa INdo taji a wuyanta hakan ya sake tayar mata da hankali kawai sai ta sakar masa kuka mai sauti. 
Ayman ya karba kafin yayi wani abun su Haleema sun fito suna musu oyo-yo kasan cewar suna ciki sune ‘yan taryar su. 
“Cutie ya haka? Kuka? Ohh ya subahanallahi danasan zaki kuka da wallahi baxan yadda na kawoki gidannan ba, cutie bakya sona k0? Please dan Allah kiyi shiru bazan iya barin ki fita daga motar nan ba alharin kina kuka dan kinga mun shiga nan gidan ba. Ki dinga sawa a ranki nine Abubakar Sadeeq gaba daya ki tuna cewar kina da irinsa kamar yadda nima nake ganinki a matsayinsa please.” 
Share mata fuska yayi sannan yasa hannu a baya ya dakko jakarta ya zare powder da kanshi ya shafa mata ya gyara mata fuskar ya sakar mata murmushi tare da cewa. 
“Kinfi ma kyau yanzu da nayi miki kwalliyar kin ganki kuwa Son Sadeeq kin wanda ya rasa zuki… 
Dariya yaga tayi sannan yayi unlock din motar su Haleema suka bude tana karbar Ayman tana cewa. 
“Wai toh me kuke yi a motar kuka dade aunty Humaira.” “Toh gulmammiya ina ruwanki bana son saka idofa.” “Sorry broth sannun da hanya.” 
Shareta yayi yana hararta lNdo dasu Aminatu suka shiga ciki shima yabiyo bayansu. Kujerun d’ayan falon na ciki wanda ba‘a shiga su aka dawo mata dashi falon farko kasan cewar da nata aka kai mata can gidan Sadeeq dining room d’inta yana nan tadal-tadal tayi fuskarta nason yin hawaye amma murmushi kwance a fuskarta lokacin da take tuno yadda suka yi rayuwa da marigayi,Sadeeq ya shiga tare da kama hannunta ya nufi bedroom su Haleematu suka zare idanuwa hannu rike da haba sannan suka tabe baki. 
Suna shiga ya jatajikinsa suka tsaya wajan madubi yana kallonta. Hannu ya dora saman k’irjinta yana wasa dashi bakinsa saitin kunnanta yace. 
“What happen to my cutie angel ne? Aisha I love you but naga ke haryanzu akwai marigayi a cikin zuciyarki kin kasa sanyani a ranki why.?” 
Numfashinta na sama-sama sabida yadda taji yana mata murya a sarke tana narke mai sabida yadda k’afarta take neman kasa daukarta tace. 
“Wa yace maka baka cikin raina? Shin duk yadda nake cewa kana cikin raina kazama ni nazama Kai duk a tatsuniya kake d’aukar su?” 
Juyo da ita yayi yana kallonta yace. “Na kasa ganewa but prove me now.” 
A hankali ta sanya hannu a wuyansa ta sargafo shi tare da had’e hancinsu guri guda cikin salo ta zuro bakinta cikin nasa Sadeeq yayi saurin karbar sakon tare da rikota shima. Kukan Ayman ne ya sanya suka tsaya da abinda suke yi jin kamar hanyar dakin aka yo dashi, sadeeq na matsawa sai ga Sajida da Ayman tana cewa. 
“Aunty Humaira wai kuka yakeyi inji yayya Haleema.” 
Karbarsa tayi sannan ta fita Sadeeq ya zauna a bakin gado yana cewa. 
“Wallahi munafurcin Haleematu ne dama naga take-taken su nasan ganin gulma.” INdo tayi dariya tana kokarin ba Ayman bra… Sadeeq ya mike yana cewa. 
“Bari naje na maida su gida bana son kinibibin yaran nan.” 
“A’a dan Allah ka rabu dasu kana ganinfa ko gaisawa bamu yi ba.” 
“Yanzu cutie kin fiSO su zauna akan ni na zauna?!” 
“A’ah ba haka nake ba, amma kaga ba dadi ka kyalesu basu yi niyar tafiya ba toh ka kyalesu dan Allah.” 
“Shikenan toh bari naje d’ayan gidan ai Fateema na nan.” 
Yana fada ya fita lNdo ta bishi da kallo, ai dole yace haka tunda ta dawo gurin sa. Tashi tayi ta koma falo wajan su haleema suka fara murnar dawowa da hiraryaushe gamo. 
Sai da akayi magariba sannan su Haleematu suka tafi ita kuma ta cigaba da gyara kayanta. Har kusan tara na dare Sadeeq be shigo gidan ba hakan ya batawa lNdo rai ganin ko dai ya dawo da itane dan ya fara wulakanta ta. Shirin bacci suka yi itada Ayman gashi ko gen ba’a kunna musu ba kuma bata damu ba domin a can gidan su ko wearing na nefa basu dashi, tana gamawa tayi kwanciyar ta zuciyarta na kuna ta janyo pillow ta rungume tare da rufe idanuwa. 
Sai wajan 10:15pm ya shigo hannunsa rik’e da ledoji, kayan ya ajiye a falo sannan ya fita ya tayar da injin taja tsaki tamkar yana gurin ta kuma rufe idanuwa dan ba karamin haushinsa takeji ba na watsar dasu din da yayi. 
“Cutie..! Cutie..!” 
Yaji shiru sai ya shiga cikin dakin, kwance ya gansu da alama sunyi bacci ya lallaba ya karasa kusa da ita yana son juyo da ita yaji tayi tauri hakan ya tabbatar masa da cewar idanunta biyu. 
“Haba cutie ba Oyo-yo shine zaki zo ki wani kwanta tashi muje falo.” “Sorry bacci nakeji ka koma inda kafi so.” “What..?!” 
Banza tayi mai ya kuma komawa wajan fuskarta yana matsa hannunta yace. 
“Amma ki bari sai munzo kwanciya sai muyi wannan wasan but yanzu dai taho muje falo.” 
“Nace kayi tafiyar ka wajan matarka, nasan dama can itace zabin zuciyar ka bani ba da aka lika maka, toh kaje katafi gurin Fateema daka fi so nabar mata kai. Banda mutuwa ma me fallasa ai da hakan bata faruba bare kamin wulakanci harda cewa toh kaima ka tafi wajan Fateema shine sai yanzu goma da wani abun zaka ce ka dawo in tashi.” 
Ta karasa maganar cikin kuka tare da tura fuskarta karkashin pillon da kanta yake kai. Ba karamin tashin hankali Sadeeq ya shiga ba jin abinda take fada, ya janyo ta yana lallashi kan ta sanar mai da abinda yayi mata amma taki, har zai rabu da ita yaji bazai iya ba sabida zuciyar da take tsananin sonta taki jin haushinta sai ma kara kaskantar da kansa da yayi yana cewa. 
“Kinga ba wai da gangan kika ga nayi dare haka ba no, ana yin sallahn magrib muka tafi gidan wani malami nida Abba bamu dawo ba sai bayan sallahn isha‘i naje nakaisa gida sannan nayo muku siyayya naje ko dadewa banyi ba a gidan Fateema nayo nan amma shine zaki min wulakanci k0? Shikenan tunda har kin fara yi min mumunan zato.” 
Yana fada ya fara kokarin sauka a gadon sai kuma yaji ta rikosa, itama bazata iya fushi dashi ba ya leka fuskarta ta kallesa sannan ya tashi tare da dagata suka nufi falo. 
“Cutie ki dena min saurin fushi bana so yana sani cikin damuwa da tashin hankali kinji?!” “Toh amma nima ka dena barmin gidan ka dade baka dawo ba tunda kana garin.” “lnsha Allahu.” 
Ya fada, kitchen taje ta dakko plate da cups ta dawo. Gashasshiyr kaza ce da aka sanya 
mata kwai tasha kayan lambu ga yajin tafarnuwa suka zauna suka ciyar da juna ranar sunyi 
kwanan farin ciki marar bayyanawa bare rubutawa. 
Satin lNdo uku da dawowa da kyar da nuna jajircewar shine mijin ba ita ba ta yadda zata bisa zuwa kwara state sabida ta kafe ita karatunta zata koma amma yak’i har kuka tayi suka yi fad’an kwana biyu amma yaki sakkowa dole ta hakura ta bisa suka tafl aka bar Fateema… 


Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *