MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 4

MUSAYAR ZUCIYA
 CHAPTER 4
“Aisha zo ki bawa yaron hakuri.” Tamkar bata jiba sai faman wasan ta take yi da k‘asar gurin da d‘an yatsan ta wanda alama ce ta baza ta bayar da hakurin ba ya kuma cewa. “Aisha ba magana nake miki ba kika min shiru..?!” “Malam  shine fa ya fara tono na kuma sai na bashi hakuri tafdi jam.” “Duk da haka ki bashi hakuri tun da kin yi mai ba dai-dai ba..” “Hu’…uhm.” Ta fad’a cikin k’asan mak’oshin ta, Abubakar yayi kamar zai wuce kawai yayi wuf ya damketa, nan da nan ta fara ihu har wasu malaman suna sake fltowa ya damketa ta bare baki tana ihu yaji wani sumumin wari ya flto daga bakin ta yayi saurin kawar da kai tare da hankad’a ta saitin Uba ta fad’i k’asa bata San lokacin da ta furta. “Allah ya baka hakuri Uba kayi hakuri kaji ka hakura..?l” “Eh.” Uba ya fad’a yana share hawaye malamai aka yi ta yiwa Indo fad’a akan karta sake yin fad’a da Namiji sannan aka sallame su. Ana tashi daga makaranta babu wanda Indo ta kula tayi wuce warta, ba gida ta wuce ba kai tsaye oflshin ‘yan agaji ta nufa tana zuwa ta sami ogan ya kalleta yace, “Yarinya ya aka yi aiko ki aka yi..?!” Tace “A’a shugaba k’ara na kawo dan ance shari’ar maita bata k’arewa toh wani malamin mu yaCe min banza maiya jaka, toh ban yafe bane shi yasa na kawo k’ararsa abi min hakkina.” “Au ke cema kika kawo k‘arar?” “Eh sabida ance nan ake kawowa kafIn akai kotu.” Sosai ya kalli lNdo wadda take faman turo baki tana taunar k’asan hijabin ta da hak’ori. 
“Toh naji yanzu shi malamin yana ina kuma a wacce makaranta yake koya muku duk da naga inifam (uniform) d‘inki na makarantar tsefawa ne…?!” Eh Shugaba acan nake kuma ma shi ba malamin mu bane d’ayan ne malamin mu amma kaga ya mareni, yayi min kutufo da k’afarsa sannan yace min Mayya, ance shira’ar maita baya k’arewa toh yazo ya fad’a a ina nayi maitar.”Shugaban ‘yan agaji na k’auyan ya sake kallonta sannan yace, “Ya sunan ki…?” Tace “INdo malam Hamza.” 
“Toh INdo yanzu abinda nake so dake nasan yanzu an tasheku ki bari gobe idan Allahu ya tahemu Iafiya kizo muzo ki nuna mana shi malamin kinji ko.?!” 
“Kai! Shugaba, ai tafiya yake yi kuma idan an gama jarabawa ba dawowa zai yi ba a hanyar gidan mu suke kayiwa Allah kayi ma ma’aiki kazo muje ayi Mai jan kunne ya dena ce min mayya da dak’ik‘iya.” 
“A’a bada ni zakuje ba zan’ saka wani yabiki suje yaji abinda ke faruwa.” Ya d’aga murya yana k’iran, “Awaisu! Awaisull, zo dan Allah kabi yarinyar nan ta kawo k’arar wani malamin su.” Awaisu na zuwa suka tafi suna taflya suna hira tamkar dama sun saba har suka k’arasa k’ofar gidan su malam Sadeeq wanda shigowarsu kenan dan sai da suka tsaya suka yi juyan bak’in mai. “Kika ce nan ne gidan k0?” INdo tace “Eh nan ne suna ciki.” Kwan-kwan-kwan, Awaisu ya fara buga k’ofar gidan yana kwad’a sallama. Malam Sadeeq ne ya fitO sanye cikin jallabiya ya kalli INdo sannan ya kalli Awaisu cikin rashin fahimta da 
kuma sanin dalilin zuwansu ya fara magana. “Laflya dai ko bawan Allah.” 
“Eh toh laf’lya ba lafiya, wannan yarinyar ce ta kai k‘ara cewar kana ce mata mayya. Toh bata yafe bane yasa takai mana k’orarka shine shugaban mu yace nazo naji dalilin da yasa kake fad’a mata wannan kalmar.” Mamaki da al’ajabi suka cika Sadeeq, sai yanzu ya k’ara tabbatar da hauka da rashin hankalin ‘yan garin ya kuma kallon INdo wadda itama shi take kallo yayi shiru yasan Abubakar ne dan haka ya tsaya yana tunanin abin cewa yaji lNdon tace. “Awaisu ka tambaye shi idan shine idan kuma ba shi bane toh d’ayan ne ya flto dan tagwaye ne.. 
Kallonta Sadeeq yayi ya sake tabbatar da lallai bata da kunya, shi kuma Awaisu sai d’aga kai yake yana kallon gidan ko zai ga wani ya fito amma ba kowa hakan da sadeeq ya gani ne yasa shi cewa. 
“Naga alamar baki da kunya Aisha, toh bazai fito ba ki shiga ki flto dashi fitsararriya kawai. Kai kuma SS ne ko d’an sanda ko soja k0 menene data dadd’ago ka kuka zo nan..?l” “A’a mu mune ‘yan kungiyar agaji na wannan kauyan kuma turo ni aka yi akan nazo naji abinda yake wakana dan tace bazata yadda ba.” CewarAwaisu Sadeeq yayi tsaki cike da takaici sannan yace, “Toh kaji abinda na fad‘a idan ba maita ba waye zai ciji mutum a mafltsara? Kuma ma wai fad’a mace da namiji dan iskanci.” “Haka ne kam malam kana da gaskiya ke lNdo baki da gaskiya dan haka zanje na sanar cewa ga abinda ya had’a dan haka sai ki tafi gida ki dena wannan halin.” Awaisu na gama fad’ar haka ya bawa Sadeeq hakuri sannan ya juya ya tafi INdo na kallonsa zuciyarta fal haushin sa. Da taga yayi nisa ta juya zata yi magana sai taga ashe shima 
Sadeeq din ya shiga ciki ta d’aga murya saitin k’ofartace. Kujini da kyau ni ba mayya bace sai dai kunemi mayya, kuma an dena zuwa bokon ai ba aikin Allah bane rawawul ni INdo na dena zuwa tsefawar yo dan banje ba ai ba mutuwa zanyi ba kuje ku cinye makarantar…” 
Sunajinta suka yi mata banza Abubakar ya shak’a iya shak’a Allah-Allah yake ya shirya yabar garin dan takaici. Ita kuwa tana gama fad’a tayi tafiyar ta gida tana zagin su tare da d’aura aniyar baza ta sake zuwa makarantar ba tunda ai sai taje zasu ganta har suyi mata maganar banza. 
K’arfe 3:34pm Abubakar ya idar da alwalar la’asar yanajiran Sadeeq su wuce masallaci dan da sunyi sallah yake son dawowa ya wuce gida. Jerawa suka yi suna tafiya suna hira abinsu gwanin ban sha’awa mutane sai kallansu ake yi. 
Sagiru dake tsaye a k’ofar gida ya hana lNdo fita ya tsaya yana kallonsu, ita kuwa INdo ganin yace baza ta fita ba yasa ta komawa cikin gida. Dai-dai katangar gidan zasu wuce kawai Abubakar yaji an cillo wani abu ya rufe mai fuska suka tsaya ya cire yana dubawa yaga hijjab ne yayi dik’il-dik’il dashi ya yarda shi, kafln ya kuma yin taku d’aya yaji an kwad’o mai wani abu a gefen wuyan sa ya kalli k’asa takalmi ne d’an madina silifas yasha d’aurin leda a wajan sanya d’an yatsa suka kalli katangar da ake yojifan kawai sai suka ga hannu hakan yasa ran Abubakar ya kuma baci sai ga k’afa can sai gata ta dirgo tim…Da sauri suka matsa inda take tana d’agowa ta gansu a tsaye a gabanta bata san lokacin da ta kurma ihu ba tare da juyawa zata kuma kama katangar ta koma gida Sadeeq yayi saurin janyo rigar ta mutane suka taru yayin da INdo ke faman basu hakuri. Gabaki d’ayan ta tsami take yi da zarni Abubakar ya tsinketa da mari tare da dungure mata goshi sannan Sadeeq ya sake ta Abubakar yace. 
“Baki da mutunci ko?Ke mara kunya kinga abubuwan tsummar da kika watsa min? Toh ki saita kanki idan ba haka ba kafin nabar garin nan sai naji miki ciwo idiot kawai sai zarni kike yi mai fltsarin kwance jibe ki dan Allah da wani billanki a goshi kamar zanan one…” Yana kaiwa nan yayi gaba yayin da Sadeeq ya harare ta shima yayi taflyar sa suka shige masallaci. Mutane kuma suka k‘arasa wajan INdo da tayi shiru tana kallon jikin ta. “Kedai lNdo wallahi kowa sai yace baki da kunya, suma bak’i har kin fara yi musu..” Cewar Rabi bala wadda makarantar su d’aya amma ita a js 3 take, INdo ta harareta tare da cewa. “Anyi d’in kizo kiyi kuli-kulin tara sisi dani munafuka kowa yasa dake..” “Ke lNdo dan ta gaya miki gaskiya shine zaki mata rashin kunya.” Wani yaro Bala ya fad’a ta kumajuyawa kanshi cikin masifa tace, “ji banza kai tun daga kan sunanka ansan kaI din bala’l ne banza Bala bala’l mtwww.” 
Nan da nan gurin ya kaure ita kad’ai su kuwa wajan mutum goma amma babu wanda ta ragawa, Sagiru k’aninta yajata suka shiga gida sai da suka kai har tsakar gida sannan ta ture shi. “Dalla can ni kyale ni banza.” Ruwa ta kindima a buta ta shiga band’aki shi kuma Sagiru ya kuma fita waje yana cewa, “Dama na barki sunyi miki shegen duka masifaffiya kawai.” 
Fitowa tayi jikinta sharkaf da ruwa wanda da alama wanka tayo amma ba a saka sabulu ba. Cikin d’aki ta shiga Inna tana sallah ita kuma taje ta sake kaya sannan ta d’an d’ibi man shanu ta shafa dama tana sato chuck ta d’auki d’aya ta daddaka tayi hoda da shi ta shafa tayi kwalliya jagirar nan har wajan kunne ta sanya kantakile a labbanta sannan ta d’aura d’an kwali tayi waje Inna na ta faman kiranta amma ko waigowa bata yi ba. K’ofar gidan taje ta zauna tana jiran su dawo, ana idar da sallah suka dawo gida tun daga nesa suka hangota kamar aljana dariya ta kusa kama Sadeeq ya daure yak’i yi a fili yayin da yace wa Abubakar. “Twinnie ga tanan fa kayi mata gorin wanka tayo tazo ta nuna maka.” Dai-dai sukaje k’ofa Abubakar ya kalleta wani takaici ya kuma kamashi INdo tace. “Gani yanzu kunsan abinda yasa bana kwalliya? Sabida mazan garin nan sun fiya kallona shi yasa amma ni bana zarni.” Ta fad’a tana bubbuga kanta tare da sosawa, mtwww “ke wai kinga sa’anki anan gurin ne?” Kallon shi tayi tare da kura mai ido tamkar zata cinye sa ya d’aga hannu kamar zai bugeta tayi saurin matsawa tace. “Yoo ni ina ruwa na wannan ai ba wasa bane kuma idan anyi duniya da manzo na dena zuwa makaranta wata za’a sake min irin ta ‘ya’yan gidan kansilan mu.” 
Mtwwww Abubakar ya ja tsaki tare da shigewa gidan, itama ta doka cinyarta ta kalli Sadeeq tace “Duk haka kuke babu me imani.” Sadeeq ya bita da kallo yana tunanin k’ila tana da aljanu yace. “Kije kiyi brush.” Abubakar daya fito da car key dinsa yace. “Bakin ta kamar kashi. Kinga yadda ake son aga hakora ba irin naki ba kamar kina shan d’orawa.” 
Ya fad’a yana nuna mata hak’orinsa fari kal. Wucewa yayi gurin motar sa Sadeeq yabi bayan sa dan suyi sallama, suna kallon sanda ta wuce tana sanya k’asan hijabin ta tana gage hak’orin. Sallama suka yi Abubakar na sake bawa Sadeeq shawarar ya k’arbi transfer ya k’ara da cewa. “Bazan sake zuwa garin nan ba sai dai na hakura har ka dinga zuwa can gida ma dinga had’uwa amma wannan garin beyi min ba.” “Insha Allahu doctor karka damu kayi min addu’ar abinda yafI alkairi.” 
“Toh amin ni na wuce.” Suka yi sallama ya tafi shima ya Shiga gida. Tunda ga ranar kuwa har aka yi hutu Sadeeq be 
sake ganin INdo a makaranta ba sai dai a unguwar su ya ganta suna wasa k0 da farantin tallah.. 
Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *