MY BESTIE’S HUSBAND CHAPTER 5 BY REAL FAUZAH TASIU
Www.bankinhausanovels.com.ng
Miqewa tayi ta gyara gurin ta shiga daki tayi wanka ta shirya cikin kayan baccinta ta sanya hijjab ta dauki hisnul muslum tana dubawa tana daukan addu’o’i ta Jima zaune sannan tayi addu’a ta kwanta, Shiru goma sha daya har daya bataji Motsin Ja’afar ba wayarta ta dauka ta danna numbersa ta kirasa har tayi ring Bai dagaba sake Kira tayi.
Taji an daga taja ajiyar zuciya tace “Allah yasa dai lfy kake najika Shiru….” Jitayi anyi murmushi sannan akace “dake zama kikayi kina jiran dawowar abinda aka baki aronsa to ai dama kwanciya kikayi kikayi bacci zaifi Miki sauqi Ja’afar kam yayi nisa saidai Kuma gobe idan naga dama na baki aronsa, sorry fah babie”
Qit aka kashe wayar taja numfashi tare da tashi tsaye cike da al’ajabi a ranta take tambayar kanta to dama ana haka kenan? Batada me Bata amsa hakan yasata ta koma ta sake kwanciya kishi na azalzalar zuciyarta hawaye nabin idonta tana karanto addu’ar annabi Yunus “ La’ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin” dahakadai daqyar bacci ya saceta itakam tana ganin rayuwa to me tayiwa Ja’afar haka ne daya fara juya Mata baya yana kantafi da mutuncinta.
+
Washegari har hudu bai shigo gidan ba batayi zuciya ba ta Kira wayarsa akayi rejected takaici ya kamata Amma saita dake saboda kullum Amminta tana fada Mata ibada batada sauqi aljanna ce me sauqi idan ka iya sarrafa zuciyarka tare da naiman daukin Ubangiji a duk lkcn da wani Abu ya kulleka.
Text ta rubuta Masa da zafafan kalamai da tasan zasuja hankalinsa Amma har dare babu reply hakan yasa ita da kanta ta fara zargin ko wani laifi tayi masa ta sake rubuta Masa saqon ban haquri ta tura Masa bai biyota ba har wayewar gari idan barawo ya rintsa itama ta rintsa.
Da sassafe saiga Hajiya Kaltume suka gaisa tace “ina me gidan ko ba anan yake bane?” Qaqaro murmushi tayi tace “Eh ba anan ya kwana ba” murmushi tayi tace “nikam Rafi’ah Anya bazan baki shawara ba a zaman da nayi dake na fahimci kinada tsayawa akan addini sosai alhmdllh Zaki dace a rayuwa Amma fah sai kin tashi tsaye, in baki wani lbr Mana surkarki da tatafi Damagaran bafa kowa take dashi ba neman asiri ta tafi na mallakarwa kishiyarki mijinku ta yanda da quruciyarki da komai zaki zama bora bance kiyi shirka ba Amma ki dan tashi tsaye ki tallafawa kanki rayuwarnan ta yanzu baa zama wlh duk wanda kikaga yana fantamawa to ya miqe”
Kallonta takeyi da rashin fahimta tace “ban gane ba Hajiya” miqewa tayi ta rufe qofa ta dawo ta zauna tace “saboda munafukai masu fakar ido am Rafi’ah da Hausa nayi Miki bayani ki miqe ki dage ki zama tauraruwa a gurin mijinki ta hanyar yan shige² nifa bance ki fita ba aa ki barmin komai zanyi Miki nidai hadin kanki nakeso”
Saurin girgiza kai tayi tace “astagfirullah Hajiya aa bazan iyaba nikam babu wanda nake dashi daya wucce Allah shine zai iyamin” Shiru Hajiya Kaltume tayi tana nazarin mgnrta kafin tace “Eh hakane kam kin Kama dahir Allah yasa mu dace” miqewa tayi tace “zan wucce kidai duba maganganuna akwai gyara a rayuwarki idan ba hakaba kinaji kina gani Zaki zama yar kallo” sallama sukayi ta tafi Rafi’ah ta tabe baki tace “dama Hajiya Innah ta fadamin ba Allah ne take kawoki ba kaji mace yar kalan masifa zata liqamin tsiya ta jamin raba tsaba da mahalicci na” shigewa tayi daki tayi duk abinda zatayi dare yayi tayi addu’o’inta kamar yanda ta saba ta kwanta tanajin cikinta yanata motsi tasan harma da yunwa kasancewar damuwar rashin mijin nata ta hanata cin abinci.
Ita burinta bai wucce ko a waya taji lfyrsa ba inda ya kasance duk Kira ana rejected haka ta wanzu idan taga dare yaqi tafiya takan tashi tayi alwala ta nufi mahaliccinta da, da yamma ta gama duk wani shirinta na karbar miji har dare tana tsara girkinta ta kashe lkcnta wajen shirya masa abinci tagama ta dauki wanka ta harde tana duba agogo takwai Tara goma sha daya Shiru.
Cikin tsananin mutuwar jiki ta dauki wayarta ta katsa numbersa gabanta na faduwa ta Kira cikin saa ya daga batare da yace komai ba taja fasali tace “barka da yini” qaramin tsaki yayi yace “inajinki” a sanyaye tace “lfyrka nakeson ji kwana uku bamu gaisa ba” wata qaramar dariya yayi yace “idan banida lfy nan nake jinya saboda haka indai Ina wajen gdannan kikajini Shiru to qalau nake” Shiru tayi maganganun nata suna hautsina nutsuwarta ta hadiye wani Abu me ciwo tace “ba nufina kenan ba gani nayi baka nemana idan na kiraka ma sai kayi rejected don Allah ka yafemin Best wlh nakasa tuna kuskurena gareka iyakar sanina dakai cikin watannin da mukayi baka iya barin Abu a ranka wannan ba dabi’arka bace tawace nima Kuma kullum Ina addu’ar Allah ya sassautamin nauyin baki saboda gudun kamuwa da wani ciwon akan matsalar da zan iya maganinta da harshena”
Maimakon yaji kalamanta sunyi tasiri a zuciyarsa saima tafasa da yaji zuciyar tasa tanayi yace “saime idan kin kamu da ciwon bake kika dorawa kanki ba kwanane yau ban shirya yinsa anan ba ni bama na Bauchi Ina Abuja Kira Kuma banaso ki daina idan kinqi kuwa ranki ne zai baci a banza sakarya kawai….”
Ajiye wayar tayi da sauri saboda a duniyarta takan hadiye kowacce irin damuwa Amma banda cin mutuncin iyaye shikuma ta lura hakan yafi Masa komai sauqi, zuciyarta suya takeyi sosai nadamar Kiran nasa takeyi da tasan abinda zai fada Mata kenan, kuka kam har saida taji jijiyar kanta na daurewa ta hqr tasha magungunanta ta kwanta zuciyarta nayi Mata wani irin zafi.
Abu kamar wasa tafiya sai qara miqawa takeyi daga sati antafi wata babushi babu alamarsa waya kam tun ranar da ta kirashi yaci mutuncinta take tsoron kiransa Amma ta wajabtawa kanta kullum saita tura masa saqon barka da safiya dana Saida safe shi kansa abin na damunsa sosai yarasa ya zaiyi ne wani sharadine Ni’imah ta gindaya masa wai idan ya kuskura taji lbrn yaje inda Rafi’an take sai tasa ya saketa shikuma tsoro ya shigeshi wani mugun tsoronta yakeji saiya daga waya zai kirata sai ya tuna cewa idan tasan ya kira Rafi’ah cin mutuncinsa zatayi hakan duk zafin kansa zai hqr ya share, wasa wasa har gashi da wata biyu a Abuja.
Yau tun safe ya tashi dajin wani qwarin gwiwa nason ganin Rafi’ah yana qissima watannin cikinta fitowa yayi daga daki ya tarar da hakimar tasa a zaune tanata fama da tuffa ya dubeta yayi mata murmushi yace “gimbiya yau watanmu nawa rabonmu da Bauchi ne?”
Dagowa tayi ta dubeshi a banzace tace “wata biyu da sati biyu mana wani abune?” Gabansa ne ya fadi yace “aa kawai dai na tambaya ne” yatsina fuska tayi tace “ok na dauka tunanin waccan yar iskar yarinyar kakeyi” dagowa yayi da sauri sosai kalamin ya tabashi Amma suna hada ido sai yayi qasa dakai yace “ah haba dai kawai dai tunanin cikin jikinta nakeyi”
Wani banzan kallo tayi masa tace “to ko zakaje ne” qasa yayi da kansa yana wasa da yatsunsa kamar wani qaramim yaron da yaje jiran umarni ta daka masa tsawa tace “tambayarka nakeyi ko zakajene?” Saurin girgiza Kai yayi tare da dagowa kawai sai idonsa ya ciko da qwallah ya miqe da sauri ya haye sama ta sheqe da dariya tace “sakaran banza da kace bakaji saura shegiyar baqar kadarar can labarinta ma saiya shafe a duniyar mutane daga ita har cikin jikin nata muga ta tsiya