MY BESTIE’S HUSBAND CHAPTER 6 BY REAL FAUZAH TASIU

MY BESTIE’S HUSBAND CHAPTER 6 BY REAL FAUZAH TASIU

            Www.bankinhausanovels.com.ng 

Shiru ce ta ratsa gurin na dan wani dogon lkc kowa zuciyarsa na searching abubuwa da dama mabambamta, zumbur Ja’afar ya miqe ya nufi qofa zai fita Mai martaba ya rufa masa baya shima Jamal miqewa yayi suka fita daga gdan duk wani guri da suke tunanin rafi’ah sun kasa samunta wasa wasa sai ga lkc yanata tafiya har goma na safiya shikam Ja’afar ya zamana kamar wani robbot ko bakinsa bai iya budewa sai tafasa da zuciyarsa takeyi.

Mai martaba ne yace da Jamal su juya suje gdansu Rafi’ah sugani ko taje can hakan ce ta faru suka nufi gidansu Rafi’ah Mai martaba yasa akayi masa sallama da Abba dake asabar ce Abba ya fito ganin Mai martaba da kansa yasashi qarasowa da saurinsa yanayi musu sannu da zuwa yanda yaga dum jikinsu  a sanyaye ya fadar masa da gaba yace “meye yake faruwa ne naga kamar Kuna cikin damuwa?”

Ja’afar ne ya magantu a karon farko yace “Rafi’ah batazo ba ko Abba shikenan na shiga ukuna ta shiga duniya Ina zataje hannun wa zata fada…..” Jiri Abba yaji yana dibansa yayi saurin matsawa jikin motar yace “ban fahimta ba Ina Rafi’an ta tafi da danyan jego?”

+

Mai martaba ne ya zame rawaninsa ya goge gumi yace “wato yau mun tashi da wani iftila’i ne Alh Nuhu lfy Lau muka kwana da Yarinyar nan Amma da asuba sai ta tashi da wani yanayi me kama da samuwar tabuwar kwakwalwa hakan tasa mijinta yanke jiki ya fadi wai kafin a samu  a shawo kan tashi matsalar baa ankara ba ta sulale ta dauke danta ta fice munyi yawo sosai a garin nan tun asuba muke zagawa ko zamuyi katarin ganinta Amma Babu ita babu alamarta duk inda muka tambaya sai ace baa ganta ba to shine mukayi tunanin ko nan ta taho Kuma gashi alamu sun nuna batanan”

Durqushewa Abba yayi yana furta Hasbunallahu wani’imal wakil cikin mummunan tashin hankali miqewa yayi ya bazama gidan da sauri ya zaro wayarsa ya fito suka sake fita sune police station sune transport agent Amma Babu wani lbr me dadi saina godiyar Allah kawai ranar yini sukayi ko ruwa basusa a bakinsu ba Basu suka hqr ba sai taran dare suka koma gda kowa zuciyarsa cike da matsananciyar damuwa suna komawa gida Ja’afar ya shige bangarensa abin mamaki saiya tarar da Ni’imah a parlourn taci uwar kwalliya tana jiran dawowarsa.

Baikobi ta kanta ba ya shige ciki ya bude dakinsa tare da dauko key din daya dakin na Rafi’ah ya datse ya koma dakinsa ya haura kan gado ya hada tagumi yanajin wani zugi da radadin zuciya da bashi da misali baiji shigowarta ba saiji yayi tana wani shafa sumarsa ya dago idanunsa da suka kada sukayi jawur ya saukesu akanta take taji tsoro ya lullubeta Amma saita dake tace “we meye na tada hankalin hakane bafa wani hauka da takeyi tsabar iskanci ne dama ba sonka takeyi ba shine take neman hanyar rabuwa dakai cikin sauqi….”

Dagowa yayi ya sake saita injin idonsa akanta sosai take a tsorace Amma batason tabar zuciyarsa ta zauna kurum kamar yanda mahaifiyarta ta qyara Mata idan ya dawo tasan duk yanda tayi tasashi jin haushin Rafi’ah ta hanyar nuna masa tana sane ta Kama hauka don ta samu damar guduwar masa da dansa, hawaye ta dauke tace “na dade Ina jiye maka zuwan wannan ranar saidai Kai ka kasa fahimta Koda yake nasan bayin kanka bane asiri ne ke dawainiya dakai badon haka ba mema zakacj da Rafi’ah Ja’afar nidai Ina baka shawara ka cireta a ranka muci gaba da rayu…..”

Tsawa ya daka Mata tare da daga hannu zai dauketa da Mari sai Kuma ya fasa ya miqe tare da shigewa bathroom ya sakarwa kansa ruwa yana furzar da iska ya fito tana zaune inda ya barta yaja dogon tsaki ya dauki doguwar rigarsa yasa ya fice daga dakin ya bude Wanda ya rufe dazun ya shiga ya tada sallar nafila ya nata jerawa ba qaqqautawa bayan ya idar ya jima yanayiwa Rafi’ah da Mahir fatan fadawa hannu na qwarai.

Alqur’ani ya dauka fara karantawa zuciyarsa na karyewa sosai yanajin yanda ruhinsa ke ciwo tabbas yasan a zaman da sukayi da Rafi’ah wata ukune kawai sukaji dadinsu watanni biyar duk sun tafi a banza ne to ko watsin da yayi da ita da rayuwarta a lkcn da tana da cikin ne yasats yanke Masa wannan hukuncin na rabashi da kanta da gudar tsokarsa Mahir?

Tambayoyine da bashi da amsarsu hakadai ya rinqa zauniya Koda yayi abinda ya sawwaqa cikin karatun qur’anin saiya rufe ya rafsa tagumi yanajin yanda jikinsa ke daukar zafi alamun damuwa ta fara ratsa bargonsa ta zuba Masa ciwon gabobi da zazzabi me zafin narkar da nutsuwar ruhi.Zamewa yayi ya haye gadon ya kwanta yanajin yanda jijiyoyin kansa suke wani tartsatsin wutar azaba qwanyarsa tana neman tarwatsewa gashi Babu mataimaki sai Allah yaji sanda Ni’imah ke buga qofar yayi Mata banza saboda baisan meye yasa ba tunda ya dawo Azare ya barota a Abuja ganinta ma bayason yi idanma ya kalleta gabansa faduwa yakeyi.

STORY CONTINUES BELOW

**********

Baiwar Allah Rafi’ah kuwa lkcn data fita daga gidan sarautar da asuba ta yanki shara a guje gudu takeyi na wucce saa da danta qunshe cikin towel ta sake qudunduneshi da hijjab dinta haka taketa keta dajin batare dako takalmi a qafarta ba haka take gudu a jeji gar ta fita daga Azare gabadaya ta shiga wani jeji me surquqi ta rinqa gudu ba qaqqautawa tana cilla qafarta ko Ina qaya zafin Rana baisa ta sunkuya, babban tashin hankalin idan ta waiwaya baya sai taga wuta naci a bayanta ganga ganga tana lasota haka zata qara zabura ta kwasa da gudu tana abbaton ya Khaliqu yini tayi ranar tana gudu babu ci babu sha ga cikinta inda akayi Mata aiki daketa azabar ciwo Amma Babu hankalin ta tsaya Abu daya da ya kasa mantuwa a ranta shine tasan idan taji danta ya motsa ta qara matsesa hankalin ta bashi abinci kuwa babu.

Ba ita ta samu ta daina ganin wutar ba saita ta wucce dambam ta shiga wani dajin shima shikuma ruwane yake binta da mugun gudu yanason cinyeta haka suka rinqa tsere da ruwan sai dare Allah ya kaita rugar wasu fulani da farko da suka ganta sun tsorata ita kuwa tana zuwa taga wata dattijuwa tana matsar nonon saniya sun hadawa shanu wutar jin dumi aikuwa sai ta nufi dattijuwar nan ta tsaya akanta matar ta miqe da sauri a tsorace ganin mutum a kanta murmushi tayi kamar me hankali sai ta yaye hijjab dinta ta budewa Mahir fuska ta miqawa dattijuwar ta bude baki zatayi mgn abin mamaki sai bakin ha harde ta kasa mgn.

Tayi tayi tayi mgn ta kasa kawai sai hawaye ya wanke mata fuska ta zube a gurin tanata kakari a dole mgn takeson yi ta kasa Abu daya da idan ta dage take iya fada shine Mahir Ya Khaliqu bayan wannan komai ta kasa furtawa, nan fah gurin ya cika taf da mutanen rugar daidai lkcn da wata arniyar mota ta parkar a bayansu kadan an jima baa fito ba can aka bude aka fito wani kyakkyawan matashin attajiri ne a qallah zaiyi shekaru arba’in da biyar ya nufo rugar dauke da wata jarka a Hannunsa mamaki ya cikashi na ganin yanda mutanen rugar suka kewaye guri guda,

Hakan yasashi saurin qarasawa idonsa ya sauka akan Rafi’ah da ta hada uban tagumi tanata gunjin kuka so takeyi tayi mgn ta kasa hakan yasata dole ta Kama kuka tsayawa yayi daga baya kadan ya zuba Mata idanunsa a mamakance ya juya ya kalli wani mutum yace “Moddibo wannan fah daga Ina?” Dagowa Moddibo yayi yace “wlh bamu sani ba kawai yanzun nan tazo ta miqawa Gwaggo Hinde jaririn can tanata qoqarin mgn Kuma ta kasa” sake kafeta yayi da ido ya matsa gabanta ya tsugunna yasa hannu ya dago kanta Saida gabansa ya fadi ganin irin kyawunta da quruciyarta kawai sai ta fada jikinsa ta sake sakin  wani kuka tana shan zuciya tuni zuciyarsa ta karya ya cika da tausayin baiwar Allan tabbas yanayinta ya nuna ba daga qaramin ahli ta fito ba, haskata yayi sosai da fitilar wayarsa tana kwance a jikinsa ya dago ya kalli Gwaggo Hinde yace “Ina tunanin Jaririn nan dantane kijata ki kaita dakinki ki bata abinci da ruwa tayi wanka amma ta fara shayar da jaririn Nan akwai wani boyayyen qulli cikin lamarin yarinyar nan idan ta huta zuwa safiya zanzo zan dauketa na tafi da ita Gombe”

Tsalle Hinde tayi taja baya tace “Oye aradun Allah banni samkarta Niko shedai ka tahi da itan tun yau hakanan abuda munaji a gari ana yanke kawunan mutane nasani ko aikota akayi ta yanke kaina don anga zayayi tsada….” saurin kallonta yayi yace “haba Gwaggo da ganin yarinyar nan kinsan badaga qaramin gida takeba Kuma tana buqatar taimako idan kika taimaka Mata kema Allah zai taimakeki Kuma bakisan abinda Allah ke nufi ba ya kawota nan rugage nawa ta tsallake bata tsaya ba sai anan”

Sake ja tayi da baya tare da miqa masa jaririn tace “kaidai da kaji kana iyawa ka dauka nikam bani iyawa….” Alh Hashim irin mutanen nan ne masu zuciya kawai saiya Kama hannun Rafi’ah ya miqar da ita yace “ok ki zubamin danyar madara a kawomin mota Amma ki taimaki yaron nan ki bashi ko danyan nono ne dafaffe yasha akwai alamun bata Sami hayyacin bashi abincinsa ba” shima Hinde taso ta musa Saida Moddibo ya shiga mgnr sannan ta yarda ta dauko qaramin Kofi ta tsiyayo dafaffiyar madarar shanu Moddibo ya kawo Zuma akasa a ciki akayi kwakkwaro da ganyan ayaba aka zuba aka rinqa bawa yaron Allah Sarki bawan Allah har wata ajiyar zuciya yakeja yanasha yana lumshe ido.

Tausayi ya cika Alh Hashim yanda yaga Rafi’ah ta zubawa jaririn ido duk da kukan da takeyi Saida alamun murmushi suka bayyana a fuskarta tausayinta ita da yaron yasa baisan sanda hawaye ya rinqa zarya a idonsa ba yaron Yana gama sha taja wata ajiyar zuciya ta janye daga riqon da yayi Mata ta matsa ta karbi danta ta rungume a gurin babu wanda Bai zubar Mata da hawaye ba soyayyar da da mahaifi wato ko mahaukaci yasan jininsa kama hannunta Alh Hashim yayi yakaita motarsa ya bude yasata a ciki.

Shiga yayi yaja suka tafi tunda suka taho ta sunkuyar da kanta take ajiyar zuciya shima baice mata komai ba yaci gaba da tuqinsa yana saqa abubuwa da yawa yanzu ahalinta sunanan sunata nemanta ruwa a jallo shikuma gashi Allah ya bashi numfashi ya sauke sukaci gaba da sharara tafiya itai bacci ne ya dauketa batasan sanda suka isoba saida taji ana bugun kujerar da take Kai tayi firgigit ta farka wani abin mamaki sai ta bude baki da ambaton “A’uzubillahi minasshaidanur rajim” mamaki ne ya cika Alh Hashim ya dubeta da sauri yace “ya sunanki?” Zuba masa ido tayi tare da kallon yaron tace “Mahir” sai Kuma ta fashe da kuka jikinsa yayi sanyi ya miqa hannu ya karbi yaron ya bude Mata qofa ta fito saime?

Basai qafa taqi takuwa ba tayi saurin riqe cikinta ta durqushe tace “way…. Wayyohhhh cikina zaz….zai bude ahhhhhhh…..” Da sauri Alh Hashim ya iso gareta ya riqota ya sake sakata a mota suka Kuma ficewa daga gdan sai Gombe General Hospital shigar da ita akayi don har ta fice daga hayyacinta suka fara checking dinta da farko sun bata lkc Basu gano matsalarta ba sai suka bige a ciccire Mata qayoyi da kwalaben da ta tattaka a qafarta Saida suka gama wata cikin nurse din ta lura da rigarta data jiqe da wani ruwa me hade da jini jini ta daga rigar da sauri saiga bandege ya jike sharkaf da ruwan miki”

Nan fa suka fita suka sanar da Alh Hisham halin da ake ciki suka shigo tare suke fada masa sai an sake Mata gyaran aikin sabida alamu sun nuna ya balle Allah ne ma yayi da kwananta a gaba da tuni ta daina shaqar iskar duniya, nan take yasa hannu aka shiga da ita dakin Teather a lkcn dare yayi nisa waima don da sanayya ne dake ba boyayyen mutum bane shi a fadin Gombe a mota ya kwana da Mahir idan yaron ya farka sai ya lakata masa Zuma a bakinsa haka suka kwana shidai baiyi bacci ba ya lalace a kallon mahir yanajin dama ace dansane na cikinsa shi ko shegene goye abinsa zaiyi gefe daya Kuma yana tunanin yanda akayi mijin wannan baiwar Allah ya bari ta subuto daga hannunsa da danyen jegonnan tabbas ba banza ba bayan tiya akwai wata caca.

Tunanin abubuwa da yawa ya hanashi gane gari ya waye Saida aka qwanqwasa glass din motar ya dawo hayyacinsa ya dago ya bude Dr Zubair ne yace “ranka ya dade wannan baiwar Allah da alamun ta dan taba gushewar hankali alhmdllh ta dawo hayyacinta saidai fah kamar tayi loosing memory’s dinta na baya Abu biyu naji tana furtawa Mahir Ja’afar and tana buqatar kulawa sosai don Allah kada a qara bare ta fita qafafunta akwai ciwo don ba daidai ta koma ba Amma na’urorinmu sunkasa gano Inda ta samu matsala a brain dinta saidai abin bashida qarfi sosai idan ta samu kulawa ma zai gushe da Kuma addu’a”

Numfashi Alh Hisham ya sauke me qarfi ya dauki Mahir ya fito suka nufi masallaci ya sanya towel ya goye yaron ya dauro alwala yatada sallar asuba bayan ya idar ya saukeshi ya rungume a qirjinsa ya nufi dakin da Rafi’ah take hutawa ya bude ya shiga da sallama nurse din dake zaune kusa da ita ta amsa tare da gaisheshi ya amsa tare da miqa Mata yaron tasa hannu ta karba yace “bansan ya zanyi Masa wanka ba ki taimaka kiyi Masa wanka bari na dauko Masa kaya”
Karbarsa tayi ta nufi bathroom ta hada ruwan wankan tayiwa yaron suna fitowa shima yana shigowa da kayan ya miqa Mata tasa Masa kaya ta dago tace “amma Alh ya kamata abawa babie wani Abu yaci akwai alamun yunwa a yanayinsa Kuma kamar ma Bai cika lkcn haihuwarsa ba aka haifesa” Shiru yayi yana tunani can ya dago yace “ok bari asiyo mishi madara” ficewa yakumayi nurse din tanata kallon Mahir kyakkyawa dashi ji takeyi kamar ta saceshi haka dai tayita zaman kula dasu har Alh Hashim ya dawo ta hadawa Mahir madara tabashi yasha taci gaba da kulawa dasu.
Kwanan Rafi’ah biyar a asibitin tana samun sahihiyar kulawa inda Alh Hisham ya rasa ta inda zai bullowa Bari’ah matarsa da batun kawo Rafi’ah gdan da yaga yana neman haifarwa da kansa damuwa saiya share tunanin kawai yaci gaba da kulawa dasu domin ya daukarwa kansa alqawarin bazai taba bari Rafi’ah ta qara shiga wani gararin ba duk abinda Bari’ah zatayi saidai tayi.
+
Ranar da Rafi’ah ta kwana biyar ana gobe zaa sallameta da yamma ta farfado ta Jima tanajin kanta nayi Mata wani yammmm ta kasa bude idonta sai bakinta da take furta “la’ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin” sautinta baya fita sosai hakan yasa Alh Hisham bai lura da wuri ba Saida ta bude idonta taja ajiyar zuciya ta zuba Masa ido tana kallon yanda yaketa yiwa Mahir wasa, dagowa yayi da sauri ya sauke idanunsa akanta saiya miqe da sauri ya iso gareta yace “kin farka alhmdllh yanzu inane yake miki ciwo?” Zuba Masa ido tayi tanason tuno inda tasanshi Amma ta kasa zama yayi a gefenta yace “sannu ya jikinki Ina fatan dai Babu inda keyi Miki ciwo?”
Motsa bakinta tayi da niyyar yin magana Amma ta kasa maqogoranta ya kasa motsawa ya sake bude idonsa akanta tsoro da mamaki ya kamashi ya kwantar da Mahir agadonsa ya taimaka ya dagata ta jingina da bango yayi Mata murmushi yace “dama ba kowacce kalma kike iya furtawa ba kenan sannu Allah ya qara Miki lfy hakanma mun gode Masa” itadai idonta nakan Mahir dinta sai yaga tayi murmushi ta daga hannunta alamun a bata yaron, a hankali yaji tace “Ja’afar” sai ya juya da sauri ganin shi take kallo ya ankarar dashi shine take nufi Kuma ta Kira da Ja’afar numfashi ya sauke ya miqa Mata Mahir ta karbeshi tayi kissing dinsa ta fara kiciniyar fito da nononta tasawa yaron sai ya fice da sauri daga dakin
Bin bayansa tayi da kallo tanason tuna wani Abu Amma Babu hali da gaske ta rabu da ciwon hauka da qarfin addu’ar da iyayenta da mijinta da Hajiya Innah da kuma wacce Alh Hashim yasa akeyi Mata Amma fah ta kasa tuna komai Kuma bakinta ya kasa furta komai sai Mahir da Ja’afar sai addu’a da koyaushe take furta duk wacce takeson furtawa tana bawa babienta nono tana wasa da gashin kansa kyakkyawan yaron nata Kama yakeyi Mata da wani data sani Amma ta rasa tuna wanene Saida ya qoshi ta zare nononta taci gaba da kallonsa daidai lkcn da Nuraiba Nurse ta shigo tace “Masha Allah madam kin farka cikin hayyaci yanzu Alh yace kiyi wanka kafin su dawo bari nakai Masa Babien kafin mu gama”
Batace komai ba ta miqa Mata Mahir ta fita bata Jima ba ta dawo ta Dagota suka shiga bathroom ta rinqa nuna Mata yanda zata gasa jikinta tare da tayata sun Bata kusan awa guda sannan suka fito ta miqa Mata Mai ta shafa ta bude wani akwati da Alh Hisham ya hadawa Rafi’ah ta dauko Mata doguwar riga mara nauyi ta bulawus ta Bata tasa yanda bazata rinqa Sosa Mata aikin cikinta ba sannan ta hada Mata shayi ta rinqa Bata suna kallon juna Nusaiba tayi murmushi tace “meye sunanki?” Itama murmushin tayi tace “Rafi’ah” numfashi Nusaiba ta sauke tace “kinyi saar miji yanasonki tunda aka kawoki ya daina zuwa kasuwa balle aikin yananan tare muke jinyarki har kudi ya yankemin na kula dake da babienku nayi Miki murna wlh samun miji irin mijinki sai an tona Allah ya qara muku qaunar juna”Kallonta takeyi da rashin fahimta itama kallonta takeyi a hankali cikin sanyin muryarta tace “Ja’afar?” Girgiza Kai Nusaiba tayi tace “aa Hisham dai” sake itama girgiza nata kan tayi tace  “Ja’afar” to ganin bazata fahimta ba yasa Nusaiba binta da eh Ja’afar.
STORY CONTINUES BELOW
Shikam Alh Hashim gidansa ya nufa cike da fargaba yayi parking ya fito ya nufi cikin gidan rungume da Mahir a qirjinsa hadiman gdan sai kallonsa sukeyi da tsananin mamakin inda ubangidan nasu ya samo danyen jariri kafin ya Isa ciki har saqo ya ishe Hajiya Bari’ah cewar ga mijinta Nan dauke da abin al-ajabi hakan yasata saukowa daga saman ta zauna a qasa ya bude qofar ya shigo ya mayar ya rufe ya juyo sukayi ido hudu ta miqe da sauri qirjinta nabada wani daram.
Ya lura da yanayin data shiga shikuma sai yayi Mata murmushi ya zauna a kusa da ita ya bude fuskar Mahir ya dago ya dubeta yace “uwargida bani ruwa do Allah” jikinta a sanyaye ta nufi freezer ta bude ta sauko ruwa me Sanyi ya taba yace “yayi sanyi mara sanyi nakeso Mahir zanyiwa addu’a” batayi gardama ba ta sake daukowa da qaramin cup na glass ta rusuna ta bashi yaja ajiyar zuciya yayiwa yaron addu’a ya dago kansa ya guntsi ruwan a bakinsa ya hada Dana yaron ya rinqa basa a hankali Bai cire bakinsa ana yaron ba saida yaga ya shanye yayi hamdala yace “kinga wani kyakkyawan babe Bari’ah Yana burgeni sosai” numfashi tayi ta zauna qirjinta na dokawa tace “ina ka sameshi?” Murmushi yayi yace “ina ranar da naje Dambam karbo Miki magani to ranar Allah ya hadani da uwar yaron nan cikin wani mawuyacin hali abin tausayi da alamun sihiri akayi Mata aka kadota daga gdan mijin kinsanni da tausayi saina daukota muka taho nan har Nan gidan mun shigo fah nace ta fito kawai sai ta riqe ciki Ashe aiki akayi Mata aka cire wannan babien a cikinta Kuma aka samu azzaluman da suka haukatata hauka fah tuburan, so shine na dauketa muka tafi Gombe General Hospital anan aka rinqa kula da ita nikuma nasa malamai suka rinqa yimata addu’a har Ubangiji ya kawo sauqi yau yanzu haka ta farfado cikin hayyaci saidai fah ta manta kowa da komai sai danta kadai Babu abinda zata iya fada daya faru a baya”
Zuba Masa ido tayi ta kalleshi ta kalli yaron zuciyarta bata yarda da abinda ya fada Amma batason sanya Masa tuhuma da kanta zata tabbatar da abinda qawarta Rahila ta sanar da ita tagani a asibiti shirun nata ne yabashi damar cewa ki tsayar da zuciyarki Bari’ah bazan cutar dake ba kuma bantaba munafurtarki ba Am Baiwar Allan nan zatazo gidannan ta zauna kafin binciken da  nasa akeyimin ya bincikomin inda danginta suke na sadasu da ita so ki nutsu don Allah ki taimaka Mata wajen kula da yaron nan ta dalilin taimakonta sai muma kiga Allah ya bamu namu”
Jinjina Kai tayi tana qara kallon Mahir zuciyarta na Bata cewa Raina Mata hankali Hashim yakeyi fah yaje yayiwa yar mutanen ciki ta haihu iyayenta sun koreta ya dauko zai kawo Mata gidanta ko Kuma auranta yayi a boye yayi Mata ciki shine yanzu yakeson hadasu saboda idanunta daya rufe har Kama taga Mahir da Hisham sunayiMiqewa tayi ta shigewarta dakinta ya bita da sauri yana kiranta don dama ya hasaso faruwan hakan Kiran duniya ta bude taqi budewa bayason Bata Mata saboda itadin amanarsa ce Amma akan wannan jahadin saidai tayi duk abinda zatayi Allah shine zai fitar dashi.
Ya Jima cikin tunanin abinda ya dace kafin ya juya ya sake ficewa ya koma asibitin lkcn Rafi’ah ta samu bacci ya zubanta ido yana kallonta a ransa yanajin ninkin tausayin ta damuwar loosing memories ai ba qaramin abu bane dole tana buqatar kulawa ta musamman sake fita yayi ya samu likitan ya nema Mata sallama suka sallamesu tare da dorata akan magunguna sannan ya koma da Nusaiba aka had a kayan suka tafi yanata zuba mata sannu suka shiga gidan tanata bin gdan da kallo tana son tuna tasan wani Abu kwatankwacinsa Amma ta kasa Kama hannunta yayi har cikin gdan bangaren da yass aka gyara Nan ya kaita ya kwantar da Mahir yace “ki huta sosai sosai zuwa anjima sai nazo nabaki magungunanki” zama tayi ya juya ya fice ita Kuma ta kwanta bacci ya sake dauketa har yanzu akwai baccin gajiya akanta.
Ranar kwana sukayi shida Bari’ah suna rigima kuka takeyi sosai wai yaci amanarta Babu wani taimako matarsa ce Rafi’ah saboda yaga Bata haihu ba shine yayi Mata wannan sakayyar yaso fahimtar da ita Amma taqi ganewa shikam da yaji haushi ya dawo parlour yayi kwanciyarrsa cikin dare yaji Mahir na kuka yaso ya qyaleshi amma yaji bazai iyaba saboda qaunar yaron yakeyi da gaske ya miqe ya bude qofar bangaren a parlour ya tarar da Rafi’ah tasa yaron a gaba itama sai kuka takeyi.
Mamaki ya kamashi yayi dariya shi baitaba ganin wannan rigima ba ki haifi da a cikinki Yana kuka maimakon ki rarrasheshi Wai sai kema kisashi a gaba ki Kama kuka karbarsa yayi ya zauna yana hura Masa kunne har yayi shiru ya koma bacci ita Kuma Bari’ah ta fitto ta nemansa bata gansa ba zuciya tabata yana dayan bangaren ta nufa a fusace ta bude ta shiga sai tayi turus ganinsa kwance a parlourn farko Mahir na qirjinsa suna baccinsu cikin kwanciyar hankali qwafa tayi ta juya ta fice ta kwana zaune tana kuka Wai ya tsallaketa ya tafi gurin shegen dansa.
Da asuba ya farka ya miqe ya kwankwasa dakin Rafi’ah da take zaune tana lazumi ta miqe ta bude ta karbi yaron tare da jinjinawa alamun godiya yayi Mata murmushi ya fice, yana fita masallaci ya nufa lkcn daya dawo ya tarar da Bari’ah ta hade kayanta a akwatu tanata kukan Wai anaci Mata mutunci duk yanda yake tunanin shawo kanta ta dadi ya kasa qarshe yace  idan ta fita bai yafeba dole tayi hqr bata fitan ba Amma ko abinci ta rantse bazata rinqa bawa Rafi’ah ba bai wani damu ba hakanan ya amince kullum da kansa yake shigar kitchen yakewa Rafi’ah girki tea ne zai dafa Mata ya soya Mata qwai da duk wani Abu da yasan zata buqata har tayi sati uku a gidan lkcn tayi qwari sosai ta murje Amma Babu baki sai ido yanajin dadin yanda yaga ta saki jikinta dashi abu daya dake neman wargatsa lissafinsa shine yanda take mu’amalantarsa yayi Kama da tanayi masa kallon mijinta sannan taqi karbar sunansa Hisham kullum Ja’afar take kiransa
Yayi iyakar yinsa yaga ta gane ta kasa ganewa inda Bari’ah take qara samun hujja da yanda Rafi’ah take mu’amalantar mijin nata da Kuma irin son da yake nunawa Mahir kullum sai yayiwa Mahir shopping idan ya fita takanas Bari’ah da taga bashida niyyar saukowa ya sake Mata bayani tayi tattaki har gidan surukarta tana kuka ta fada Mata cewa Hisham ya kawo Mata mace gda ya ajiye Kuma harda ɗa a wata majiyar ma ance dansa ne yayi Mata ciki ta Haifa Masa shine iyayenta suka koreta shikuma ya aureta,
Sosai hankalin tsohuwar ya tashi duk da ta yarda da ingancin danta Amma mgnr Bari’ah abar dubawa ce dubanta tayi tace “kije zanzo anjima idan ya dawo” haka kuwa akayi da magariba ya dawo daga aiki yayi wanka ya zura doguwar rigarsa ya nufi bangaren da Rafi’ah take domin dauko dansa Mahir da ya qara kuɓulɓul dashi a parlour ya isheta tana sallah shikuma Mahir na kwance a kusa da ita yanata kallon sama yasa hannu ya daukesa ya zauna a kujera yana cillashi sama yaji an bude qofar an shigo ya dago da sauri sai yaga Hajiya Rakiya mahaifiyarsa ya shafa kansa tare da cewa “Ahhh Hajiya kece da daren nan?” Zubawa Rafi’ah ido tayi tana tunanin inda taso sanin fuskar yarinyar tana cewa “ashe haka ka zama Hashim dan shege a zuri’ar mu….” A gigice Rafi’ah ta dago ta dubi Hajiya Rakiya sai hawaye sharr a idanunta shima Hashim saurin kallon mahaifiyarsa yayi yace.
“Hajiya nasan cewa baki yanke hukunci da ka a mafi yawan lokuta ma baki amsar hujja saman yaqini wlh tallahi banida wata alaqa ta kusa da wannan baiwar Allan bayan taimako, Nan ya kwashe komai ya fada Mata tayi shiru tana nazarin kalamansa ita kanta Bari’ah sai jikinta yayi sanyi ya share qwallar idonsa yace “ke daga ganin nutsuwa da kamalar wannan baiwar Allan bata cancanci wofintarwa ba duk inda ahlinta suke sunanan suna haqilon nemanta jiya nabada hotonta a kafafen yada labarai da jaridu domin a cikitomin ahlinta ko Ubangiji zaisa a dace”
Jinjina Kai Hajiya Rakiya tayi ta dubi Rafi’ah ta miqe ta Isa gabanta lkcn ta idar da sallah ta zauna kusa da ita ta Kama hannunta kuka takeyi sosai, cikin yanayi na tausayi Hajiya Rakiya tace “kiyi hqr kinji yata Allah yasan komai Kuma shine yakeda maganin komai” kwantar da kanta tayi a kafadarta ta sake rushewa da kuka cikin yanayin da batasan ya akayi ya wanzu ba ta bude bakinta da cikin watanni hudun baya iya furta komai tace.
“Wlh banida wata alaqa da Hisham a baya ne ma yakemin Kama da uban Dana Ja’afar amma yanzun ya daina….” Miqewa Hisham da bari’ah sukayi tare suka Isa gabanta yakai hannu zai tabata sai ya tuna da mgnrta uban danta Ja’afar tuni ya dawo nutsuwarsa yaja fasali yace “dama bakinki Yana mgn kikaqi yimin mgn tsayin wata hudu?” Cikin kuka tace “aa yaune naji Ina iya furta wasu kalmomin sannan inajin kamar inason tuno wani abu game Dani Amma na kasa don Allah wacece ni ya akayi nazo nan Kuma inane nan?”
+
Hawayen tausayinta Alh Hashim ya goge ya fice daga dakin saboda zuciyar Mata ke gareshi abin kuka bayayi Masa wuya Kuma yin kukansa zai qara karya mawa Rafi’ah zuciya, zama yayi yana tunanin abubuwa da yawa da bashu da amsarsu bai ankara ba yaji Bari’ah nayiwa Hajiya Rakiya magiya akan kada ta tafi da Rafi’ah tayi alqawarin kulawa da ita tare da dauke Mata kewa taci alwashin taya mijinta ida wannan kyakkyawan aiki da yayi niyyar aiwatarwa.
Daqyar Hajiya Rakiya ta yarda tabar Rafi’ah a gidan tun daga wannan ranar zaman Bari’ah da Rafi’ah ya koma gwanin sha’awa komai tare sukeyi Bari’ah macece me surutu amma tanada hqr da Kuma sanyin hali wannan abin ya dawwamar da qauna tsakaninsu, yauma kamar ko yaushe suna parlourn sunata hirarsu Bari’ah tanayiwa Rafi’ah koken matsalarsu ta dubeta tace “akwai wani magani da wani Malamin mu ya sanar damu idan akayi amfani dashi indai da rabo zaa dace ki bani bero da takarda zan rubuta Miki mu fita pharmacy mu nemeshi insha Allahu idan kikayi amfani dashi Allah zai dubemu ya bamu babie”
Murna ce ta cika Bari’ah ta tashi ta dauko biro da paper Rafi’ah tayi rubuce rubucenta da rubutunta na likitawa mamaki ya cika Bari’ah ta dubeta tace “dama kinyi karatu ne Rafi’ah?” Murmushi tayi tace “jiya na tuna cewa Ina da medicine certificate a garinmu Amma na kasa tuna a makarantar da nayi karatu Ina takurawa zuciyata akan tuno wani Abu game dani nakasa kawai abinda brain dina take fadamin ni matar aure ce Kuma ni ba matar qaramin mutum bace”
Shiru Bari’ah tayi tana nazarin kalamanta kafin ta miqe tace “idan ance asiri akayi Miki aka haukataki aka baroki da garinku da Mijinki sai kice aa ke ba asiri bane Mijinki ya mutu Kuma a kalamanki kina bayyana ke matar aure ce na rasa wanne zamu dauka a ciki to Allah dai muke fadawa Kuma munsan zai amsa bari na Kira Yallabai idan yana kusa sai yazo yakaimu
Shigewa dakinta tayi ta canza kayanta zuwa doguwar riga tayi rolling mayafin ta fito lkcn da Alh Hisham yake shigowa ya dubeta ta rusuna tace “barka da dawowa” murmushi yayi yace “kun dawo dani ku dole da kukeso to Wai inama kuka samo sunan maganin?” Sunkuyar dakai tayi Bari’ah tace “gulma itane ta rubutamin….” Kallonta yayi da sauri yace “ina kika samoshi?”
Qasa ta sakeyi da kanta tace “akwai wani lecturer dinmu da yake yawan yimana bayani akan abinda ya shafi matsalar haihuwa dayake a bangaren daya shafi matsalolin Mata nayi degree na…” Shiru tayi Alh Hashim yana qare Mata kallo yasan daganan bazata iya sake tuna komai ba shi tausayi na sosai take bashi musamman idan tace Ja’afar dinta ya mutu. Ficewa sukayi kowa jikinsa Babu qwari suka inda suke sakaran zasu samu Basu samu ba sukayi Shiru a mota na tsayin lkc kafin yatada motar yace “na tuna a titin government house naga an bude wani sabon katafaren Pharmacy R&J naji ance na wani babban doctor ne Kuma kamar ance dan Bauchi ne akwai yuwuwar zaa samu acan”
Nufar Pharmacy din sukayi sukabar Rafi’ah a cikin mota Bari’ah na riqe da Mahir a hannunta yaron kyakkyawa dashi Masha Allah fari tass kamar ubansa ta ratsa jininsa ta fito yanda duk Wanda yasan ubansa yana ganinsa zai iya shaida hakan, suna shiga pharmacy din suka miqa takardar da aka rubuta maganin wani matashin saurayi da alamun shine mamallakin gurin ya karba ya dago ya sauke idonsa akan Mahir gabansa ya yanke ya fadi.
STORY CONTINUES BELOW
Miqewa yayi da sauri yana kallon yaron, itama Bari’ah sai tabishi da kallon mamaki kawai sai taga ya miqowa Mahir hannu duk qwuiyar Mahir da baya daukuwa gurin kowa sai taga ya miqa hannu shima yana bangale Masa baki mamaki ya cika Bari’ah da Alh Hisham sukayi murmushi a tare Alh Hashim yace “hukuncin Allah sai sauraro kiga maquiyacin yaron nan yanda ya wani miqa hannu gurin bawan Allan nan”
Murmushi yayi yace “fine boy Nima nayi maka kamar yanda kayimin ko?” Yaron da baifi 17 months ba ya daga Kai sukayi dariya mutumin ya zubawa yaron ido yace “wato Alh danaga yaron nan naku Saida gabana ya fadi tunda nake bantaba ganin kamantayyar halitta irin wannan ba tsananin kamarsa da yayana mamallakin wannan pharmacy din tasa gabana faduwa tare dajin qaunar yaron a raina”
Batare da sunba abin muhimmaci ba sukace “ai dama haka Allah yake ikonsa” Jamal da Dan banzan surutu ya sake dubansu yace zaku bani dama na dauki hotonsa duk da nasan Prince baya cikin nutsuwa Amma zan nuna masa yaron nan nasan zaiji dadin ganin me kama dashi wlh tallahi shi da kuke ganinsa kungansa can a hoto”
Nuna musu hoton yayi yace “ya rabu da matansa du daya ma ana kyautata zaton ta mutu dayar kuwa ranar daya samu lbrn mutuwar dayar ya saketa saki biyu so dama ya taba yanka Mata Kati sau daya yanzu haka baya qasarnan yana Canada sama da shekara daya babu Mata kullum mafarkinsa matacciya zata dawo”
Dariya yayi sosai yace “Allah Sarki Yaya yaci engine brain am mema zaa baku?” Miqa hannu yayi ya dauko maganin tare da rubuta yanda ake amfani dashi yace “amma likitan daya rubuta muku maganin Nan babban likita ne saboda ba kowa yasanshi ba indai Kuna da rabon qara haihuwa zaku samu kwanan nan Allah ya kawo twince”
Su dariya ma yake Basu duk ya susuce sai surutu yakeyi kamar zautacce Alh Hashim yace “nawane maganin?” Murmushi yayi yace “ah haba aini na zama dan gida in wannan ma ya qare ku dawo wlh kyauta zan baku albarkacin wannan zuqeqen yaron me kama da Prince am ni yama sunansa?” Alh Hashim yayi murmushi yace “Muhammad Mahir” wani ihu yayi yace “Allahu Akbar tudu biyu sunan ubana ne dashi Kai dole nayi maka kyauta kaida uwarka”
Bari’ah ce tayi murmushi tace “banice mahaifiyarsa ba qanwata ce tana mota yaro kayi uba a sama dama uwarka ta damemu da kukan Mahir maraya ne” nandanan tausayi ya cika Jamal yace “Allah Sarki buwayi yanzu uban wannan kyakkyawan yaron ya mutu sannu kaji dole uwa taka tayi kuka ni wallahi kayimin yaro ka samu sabon uba kaji?”
Kwantar dakai Mahir yayi a kafadarsa yana dan gwarancinsa saboda maganar Bata fita sosai a haka suka fito zuwa bakin motar Rafi’ah na tsaye tana danne danne da wayarta taji takunsu ta dago idanunta sanye da glass ta sauke idonta kan Jamal hakanan taji wata faduwar gaba ta sake saita idonta akansa shima abinda taji shi yaji tare da amsar wani rikitaccen saqo cikin sakanni numfashi suka sauke a tare itadai kallon sani takeyi Masa Amma takasa tuna inda tasan kamanninsa inda shikuma yake aika Mata da wani saqo.
Kawar dakai tayi tace “mamaki maquiyacin dana a hannun baquwar fuska ya akayi haka?” Murmushi Alh Hisham yayi yace “muma haka mukasha mamakin Nan” mota ta shige tana cewa “wannan ya tabbatar muku Dana Dan gayene baya jituwa da yan gaya shiyasa baya yarda da kowa sai an Gaye” dariya sukayi Jamal yana qara saita idanunsa akanta yace “inason yaronki mamana” da sauri ta kalleshi tace.
“Muryar dana sani Amma a Ina nasanta?” Kwashewa yayi da dariya yace “up ni a mafarki Mana tsuke fuska tayi tamai da kanta qasa shima baibi takanta ba ya matsa sukayi qusqus dinsu da Alh Hisham sukayi sallama ya leqo yace “hajiya ta zan kawo ziyarar gaisuwa gami da roqon iri inason nima asammin wannan kyakkyawan irin na yafa a gonata”
Wani dogon tsaki taja daya daki zuciyar Jamal hakanan Allah yayisu basa qaunar tsaki, itakam Bata kobi takansa ba Alh Hashim yaja mota suka tafi tunda suka taho take huci tana mita tana cewa “kowanne dan iska sai yace yanasona bayan na fadawa kowa ni matar aurece don mijina ya mutu Yana nufin dole sai nayi wani auren ne to ai banga gawarsa ba balle nayi takaba sudai Basu kulata ba saboda sun saba jin wannan tufka da warwarar tata tace mijinta ya muta ta dawo tace ita matar aure ce.
Suna zuwa gda ta fita a motar fuuuu ita a dole anyi Mata laifi Alh Hashim da Bari’ah suka kalli juna sukayi murmushi Bari’ah tace “wannan karon zanyi iyakar bakin qoqarina guy din ya hadu sosai da alamun zata samu nutsuwa idan ta amince dashi” fita sukayi suka rufanta baya kowa ya fara harkar gabansa bata ware ba sai washegari sukaci gaba da harkokinsu Bari’ah tace Mata zasuyi baqi yau suka kuwa bata lkc wajen shirya dinner itace harda zabar abincin da zaa girka duk Wanda ta zaba sai tace tasan Ja’afar dinta yanasonshi”
Basu gama ba sai yamma liqis ta nufi dakinta tayi wanka sukayi magrib ta dauki qur’ani tana karatu taji an turo qofar ta dago ta kalli Bari’ah daketa murmushi tace “Yallabai yace kizo ki gaisa da baqin kafin su tafi” lifaya ce a nade a jikinta kawai ta miqe ta fito ta nufi parlourn baqin tare da sallamarta gabanta ya qara faduwa ganin mutumin jiya me muryar Wanda ta sani ta kuwa daure fuska Alh Hashim yace “zauna Mana Rafi’ah” tsuke fuska tayi ta zauna tana wasa da yatsunta inda Jamal ya kafeta da ido ganin yau sai taga ya qarayi Mata kwarjini fiye da jiya.
Alh Hashim ne ya kawar da shirun da cewa dama haka Allah yake ikonsa qila dama rabon haduwarki dashine yasa tunaninki ya dawo kika tuna kinyi karatun medicine har kika tuna da maganin da yakamata ki taimaka Mana dashi kika rubuta mukuma muka tafi neman gaibu don Allah ya sani har mukaje pharmacy din farko ban yarda akwaishi ba saboda wani lkcn maganganunki suna sabawa da hankali Amma da mukaje akace akwaishi maganin sune dai nasu ya qare sai na samu karsashin daukarmu nakaimu R&j domin mu siyo kwatsam sai mukayi katarin haduwa da wannan bawan Allah so abinda nakeso dake Rafi’ah ki nutsu ki fahimcesa idan da hali ki buda zuciyarki kigani kozata karbesa kinji” qasa tayi da kanta tana matsar qwallah tace “amma Alh nasha fada maka Ni matar aure ce don Allah ku daina takurani nayi soyayya wlh bazan iyaba zuciyata shi daya takeso Kuma ya tafi yabarni idan bashi ba bazan iya rayuwa da kowa ba”
Mamaki ne ya cika Jamal ya miqe yana riqe da hannun Mahir ya matso gabanta ya tsugunna Alh Hashim ya miqe ya fice, ajiyar zuciya yayi yace “da farko nayi Miki kallon tuhuma dana sani Amma dana tuna wasu abubuwa saina cire tunanin komai araina nasa a zuciyata Kama biyu kikeyi min tabbas hakane Rafi’an Prince ta mutu kwana biyu da haukacewarta an samo gawarta data babienta a dajin Dambuwa Kuma ke ance Mijinki mutuwa yayi so karna jaki da nisa My Raf inasonki Kuma aurenki na daura dambar yi duk da kasancewata saurayi hakan bai dameni ba domin sunnah zan raya ma’aiki shine yayi mana nuni da hakan zan aureki Rafi’ah da gaske wlh tun jiya na afka ki bani hadin Kai bada sauri ba mu fahimci juna ke nifa idan kika amince dani zaki aureni gobe zantada hankalin Azare baki dayanta sai an dauramin aure dake….”
Wani Abu taji ya caki qirjinta da yasata dafewa tace “azare! Azare!! Azare!!! Kamar na tabajin sunan?” Dariya yayi yace “ya Kama babie kina qasar Hausa kice bakisan Azare ba ni dan sarautar Azare ne mahaifina shine sarkin Azare yayana daya namiji yana Canada shekara guda bashida lfy saidai yaji sauqi idan bege da shauqin rashin matarsa da dansa ya motsa Masa Kuma yayi kamar ba zaiyi raiba Ina tausaya masa sosai har kuka nakeyi Masa saboda magauta sun sashi a gaba kawai don ya kasance me jiran gado shi kansa anso haukatashi Allah Bai nufaba sai aka sa Masa tsanar qasar Nan gabadaya wannan dalilin yasashi komawa Canada dazama Amma dukiyarsa duka tana Nigeria duk wata jaha dake arewacin Nigeria idan kika shigeta zakiga R&J pharmacy mallakinsa ne sunansa ne da sunan matarsa marigayiya Rafi’ah…..”
Shiru tayi batare da tace masa komai ba ya zuba Mata ido yana jiran tace Amma taqi cewa sai ya miqe yace “kiyi tunani akan manufata ta alkhairi ce gareki dani baki daya idan kin yanke hukunci zan kiraki sai naji ya ake ciki saboda nasan mataki na gaba” tabe baki tayi ta miqe itama yabita da kallon mamaki tunda yake baitaba ganin birkitacciyar mace irinta ba tama saurareshi din babu dama.
Qwafa yayi daidai lkcn da Alh Hisham ya shigo suka qara gaisawa yace “yadai ta amince kuwa?” Murmushi yayi yace “aa batama cemin komai ba inaga barinta zanyi ta nutsu tukunna saita yanke hukunci” numfashi Alh Hashim ya furzar yace “haka takewa kowa bazatace maka komai ba saidai kawai zan baka dama ka turo magabatanka ayi mgn inaganin hakan zaisa ta samu nutsuwa”
+
Kallonsa yayi da sauri yace “da gaske?” Murmushi yayi yace “eh da gaske mana” hamdala yayi yace “Amma naji dadi sosai gobe kuwa zan tafi Azare zan sanar da Mai martaba abinda ke faruwa idan ya amince jibi ma zamuzo”
Jinjina Kai Alh Hashim yayi suka fita ya rakashi har gurin motarsa cike da kulawa inda yabar shirgin sha Tara ta arziqin daya hadowa mahir sun jima suna tattaunawa sannan sukayi sallama ya tafi Alh Hashim yana komawa gida ya Kira rafi’ah balbaleta da fada yayi abinda Bai tabayi Mata ba yana tuhumarta dalilin wulaqanta Jamal.
Hawaye ta rinqa sharewa tsayin lkc yana fadan nasa kafin ya sauko ya zauna yanayi Mata nasiha taci gaba da matsar hawayenta kamar tana daukar abinda yake cewa, Saida ya dakata sannan ta dago tace “bazanyi jayayya da abinda ka zartar ba Amma inason ki fahimceni wlh bansan komai game dani ba inaji a jikina Ni matar aurece Amma bana iya tuna komai so kuyi hqr ki qyaleni na rayu a haka har zuwa lkcn da Allah zai kawomin qarshen matsala ta tabbas akwai wani Abu da kullum zuciyata ke qoqarin tunawa ta kasa”
Shiru yayi na dogon lkc Itakam Allah yayi Mata baiwar saita kalami idan ya biyeta bazasu tsinanawa rayuwarta abin arziqi ba dubanta yayi yace “amma da sharadin zaki daina fita ko Ina don na gaji da mazan dakemin sinturi a gidana” saurin daga Kai tayi tace “na amince da hakan” dariya ma taso ta bashi saidai ya dake ya tashi ya shige ciki miqewa tayi ta shige ciki ta Kama danta suka kwanta ranar kwana tayi bata rintsaba ta takurawa kwanyarta son tuno abinda ya goge a cikinta hakan yake haifar Mata da matsanancin ciwon kai.
Kwanaki suka rinqa tafiya cike da abubuwa masu rikitarwa duk yanda Jamal yaso ta bashi hadin Kai taqi yaje ya samu Mai martaba da maganar auren shine yace masa ya fara samun soyayyar yarinyar tukunna gashi abinda yake tunanin bamai wahala bane yayi masa wahalar samu, duk da bata bashi damar soyayya ba Amma tana sakin jiki dashi suyi hira.
Abinka da abinnan da hausawa suke cewa me da Wawa soyayyar da yake nunawa Mahir tasa takejinsa a jikinta idan yaga haka yakan dauka fara sonsa tayi Amma da yayi mgn sai tace itafa uban danta kawai takeso bayanshi bata ra’ayin kowanne namiji a duniyaWannan kalma na Sosa zuciyar Jamal saidai bashida wata madafa shi s hakanma dadi yakeji  duk da ya zurma da yawa  yakan taushi zuciyarsa akam ta sassauta Masa kar yaje yayi saukon bukukuwa ya Gina zuciyarsa da qaunarta Rana daya ta juyansa baya Da wannan tunanin yake ragewa kansa shauqi game da ita
Al’amarin Ja’afar kuwa tunda Rafi’ah ta Bata ya shiga kwale²n masifa tun suna sakaran ji ko ganinta har suka fara fidda rai tsayin wata guda shikam yaqi lfy kullum cikin faduwar gaba da ciwon qirji yake, dadin dadawa Ni’imah da taketa qoqarin dole wai ita saita gogensa tunanin matarsa da dansa yakanyi Mata kashedi me qarfi game da hakan saidai taqiji wannan yasa suka rinqa samun sabani idan taje ta isheshi da mita wani lkcn idan takaici ya isheshi ya ware qwanji yayi Mata mugun duka ranar saidai ta kwana a bangaren Hajiya Fatsum.
Ana haka watarana ya zaneta cikin dare tazo ta isheshi aikuwa ba arziqi ta gudu bangaren Hajiya Fatsum tana kuka anan hajiyan take fada Mata tayi hqr bayin kansa bane aljani sukasa ya  cire masa tunanin Rafi’ah sannan ya batar dashi shine suketa fada da zuciyarsa da aljanin idan ya ciks takurawa ma haukacewa zaiyi shima, suna tsaka da wannan tattaunawa kawai sukaga wani jan haske ya keto bango ya nufosu gadan gadan take suka watse suka rinqa tsere Amma Saida ya cimma Hajiya Fatsum kawai saiji sukayi ta fasa qara ta fadi qasa Tim tundaga wannan Rana ta zama kamar mutum mutumin babu motsi babu magana babu komai a wannan ranar ne Kuma bakin Rafi’ah ya bude,
STORY CONTINUES BELOW
Sosai hankalin kowa ya tashi Amma banda Ja’afar da ya fara susucewa kullum cikin hada kaya yake ana riqeshi zaibar gari wata Rana da bazata goge ba cikin tarihin rayuwarsa yana kwance da dare kawai saiji yayi an qwala mass Kira ya miqe a firgice saijin murya yayi ana cewa dashi “Canada ka tafi Canada matarka da danka sunacan zaka ishesu acan”
Aikuwa batare da tunanin komai ba ya miqe cike da farin ciki ya dauki passport dinsa da master card dinsa da wasu takardunsa masu muhimmanci ya sace jikids qafa ya fice ta bsyan gdan saboda masifa ma ta katanga ya haura Hajiya Kaltume tana kallonsa tayi dariya tace “shege da kace bakaji ya tafi inda ajalinsa yake” tunda ya fita bai tsaya a ko inaba sai a inda zaiyi Visa ta tafiya kudi ya saki sosai akan cewa shifa tafiyar gobe gobe yakeso sunyi iyakar bakin qoqarinsu suka sama masa ta jibi daqyar ya hqr ya karba ya fice ya nemi masauki ya qarasa kwana washegari kuwa kashe wayarsa yayi Bai budeta ba Saida ya sauka a Canada ya nemi mazauni ya huta sannan ya bazama gari neman farin cikinsa duk Wanda yagani indai baqar fatane saiya tambayeshi inda zaiga Rafi’ah a qarshe ma mutane sukamai dashi mahaukaci kwana da kwanaki yana bilayi daganan zuwa nan a kwana na sha biyar ne aka kirashi a waya ake fada masa anga gawar Rafi’ah da danta a jejin Dambuwa daga tsaye ya yanke jiki ya fadi shine har yau Bai qara lfy ba.
Jamal ne ya biyosa yake jinyarsa kwanansa ashirin yaji sauqi sauqi aikuwa a ranar ya turawa da Ni’imah saqon sakinta uku harda qarawa da cewa “dama Ina zaune dakene arziqin Rafi’ah tunda na rasata kema dole kibarni nayi rayuwata ni kadai ki nemi miji kiyi aure Ja’afar na Rafi’ah ne ta mutu ta barni zan jira ranar mutuwata mu hade da ita a darussalam”  wannan saqo ya rikita Ni’imah ta rinqa kwarara ihu an dauka na iskanci ne Ashe qaiqayine ya dawo kan masheqiya tun ana daukan abin yanzu anjima har Abu ya tatura ta fara surutan tonan asirin kansu tashin hankalin da kowa ya shiga ba kadan bane aka rinqa Allah wadarai da halinsu.
Daqyar Abba ya rarrashi daddy Ni’imah ta koma gdansa Yana tur da Allah wadarai da halinta ita da uwarta aka rinqayi mata magani amma Babu sauqi Abu sai gaba yakeyi dole sai daki aka ware Mata aka rinqa Kiran malamai sunsyi Mata ruqiyya aljani kuwa yaci laya akan bazai barta ba tunda Rafi’ah tafi qarfinsa ai dama Saida sukayi sharadi shi baya zama hakanan batare da ya kada wani juji ba sukace sunji sun gani saboda haka Babu inda zashi Abu kamar wasa Abu sai gaba yakeyi takai tana tsigar gashin jikinta da kanta tana cinyewa kusan shekararta guda a haka sannan aka samu daqyar wani malami ya rabasu Amma me yana barinta ya koma kan Hajiya Fatsum.
Tashin hankali Ashe ga inda ake hauka can tuburan rawa da juyi takeyi tana yagar jikinta tunda akayi katari ta falle daga gdan sarautar har yau baaji duriyarta ba, inda Ni’imah take cikin tsananin nadama mabayyaniya son zuciya da zugar jahilan iyaye takaita ta baro gashi tayi uku babu babu mijin da take hauka akanshi babu aminiyarta babu auren Kuma babu mutunci da qima saima tarin tsana da qyamata da take fuskanta gurin mutane.
Tazamo kamar mujiya gurin dangi da mutanen gari daga ita har uwarta babu me musu dariyar rahama saidai habaici da shagube wannan abu nasata kukan tashin hankali takan dade tana tunano rayuwarsu ta baya da Bestienta da irin alqawuran da suka rinqa yiwa juna takanyi nadama tare da tambayar kanta meyesa tayi kaza meyasa ta yarda aka zugata tayi kaza ina zataga Bestienta da gaske Bestienta ta mutu ta sanadin mugun abinda sukayi Mata?
Tana tuna haka saita qara rushewa da kuka itace asalin asararriya mara gatan rahama data shiga tsakanin ma’aurata ta zamo silar sanyasu baqin ciki tabbas ta Debi kaya me yawan da batada me sauke mata, gabadayanta tayi sanyi bata iya komai sai kuka takan tuna a baya idan ta shiga mawuyacin hali Rafi’ah ke Bata shawara yanzu babu Rafi’ah waye zai bata shawara takanji dama hqr tayi da Ja’afar tun a farkon farawa kafin ya aureta data gane qawarta yakeso tabarshi ya auri aminiyartata da yanzu duk hakan bata faru ba Amma son kanta yasata qin gane kuskurenta Saida ta aikata kuskuren daya zarta kuskure.
********
A bangaren Rafi’ah kuwa shaquwa qara shiga tsakaninta takeyi da Jamal dole tasa ya hqr da mgnr soyayya ya dauketa kawai matsayin qawa mamaki yakanyi da wasu abubuwa da takeyi daya shafi harkokin lfy yakance Mata a Ina tayi karatun medicine sai kawai yaga ta fashe da kuka tace “tabbas nayi karatu Jamal Kuma mijina ma babban likita ne Amma na kasa tuna wani Abu daya shafeshi ko ya shafeni Jamal mijina fitaccen mutun ne fah Ina tuna kamar ya mutu kamar Bai mutu ba” bayason yawan furta masa mijinta mijinta da takeyi shiyasa yake basar da zancen ya aunata a abubuwa da yawa sai yaga ta wucce tunaninsa.
Yau tun safe yake tunanin meye yakamata yayi Mata Wanda zataji dadi, murmushi yayi yayi ya gama ayyukansa ya Isa gidansu tana harabar gidan tana wasa da danta Bari’ah daketa faman laulayi na gefe tanashan lemun tsami ya shigo ta tsaya da buga ball din yayi parking ya fito Mahir ya nufeshi da sauri yana kiran “Abba oyoyo” daukan yaron yayi yana cillashi sama ya zauna suka gaisa da Bari’ah ya dubi Rafi’ah yace “maman dana inason mgn dake” tsuke fuska tayi yayi murmushi yace “banan na nufaba hajjaju am ko kinada intereste akan aiki?” Saurin kallonsa tayi sai Kuma tayi dariya shima dariyar yayi yace “akwai sabon asibitin da Yaya Ja’afar ya bude anan jikin pharmacy dinmu Rafi’ah Memorial Hospital so muna buqatar ma’aikata shine nake ganin kamar kinada rawar takawa idan babu damuwa zan baki gurbi a asibitin kema kya rinqa rage kewa Amma me kika gani?”
Wani ihu tayi ta rungumeshi tana dariya shima dariyar yayi yace “kinqi aurena Kuma kina susutani meye yasa Anya kinamin adalci” nandanan ta hadiye murnarta tace “bazaa aureka badin ni ta mijina ce shishi kadai” kawar da zancen yayi yace “zan gama Miki komai ranar litinin ki fara zuwa aiki kawai” sosai taji dadi Kuma tayi masa godiya har ya miqe tace “amma Jamal banida takarduna a hannuna da mijina ya tashi mutuwa dasu ya mutu” dariya sukayi duka yace “bazan baki inda zakike aiki me wahala ba saboda gudun shirme ni inaji ma a lab zan barki” dariya sukayi ya kalleta yayi murmushi ya shiga mota ya tafi.
Binsa tayi da kallo Bari’ah tace “yana bani tausayi sosai Rafi’ah yaqi hqr da wahalta Miki ke Kuma kinqi hqr ki karbeshi don Allah ki bashi dama ko yayane” ajiyar zuciya tayi ta zauna tana matsa Mata qafa tace “uwar biyu bazaki gane ba ne kawai Allah bazan iya hada soyayyar wani data Abu Mahir ba ki barni kawai” sanin idan ta cika mgn fushi zatayi da ita yasata yin Shiru kawai sukaci gaba da hirarsu tna bayyana jin dadinta da aikin da Jamal yabata wannan kenan.
Hakan ce ta kasance kamar yanda Jamal ya fada Mata ranar litinin dakansa yazo ya dauketa zuwa asibitin da safe tare da bata takardun daukar aikin ta cike tabashi duk da baa bata wani bangare ba, tunda suka shiga asibitin gabanta ke faduwa har suka shiga reception din tanabin hotunan da aka maqale a reception din da kallo tana sauke ajiyar zuciya batakai ga gama kallon hotunan ba taji murya a bayanta ance Mata “sannu” gabanta ne ya sake bada wani dam har saida tayi kamar zata fadi yayi saurin Kai hannu ya riqota taja wata wawuyar ajiyar zuciya tare da zuba idanunta kan fuskarsa,
Murmushi ya sakar mata yace “wa kike tunani haka” numfashi ta sauke tare da janyewa daga jikinsa tace “ka tsoratani Jamal sainaji muryarka kamar ta JM dina” da sauri ya kalleta yace “waye shi?” Dago kanta tayi tace “Baban Mahir dina wani lkcn Ina tuna wasu abubuwa game dashi amma fah Raina yana fadamin ko ganinsa nayi bazan ganesa ba” saurin zama Jamal yayi saboda cikin kwanakin nan kalamanta suna sanyashi cikin tunani to Amma Alh Hashim yace itan qanwar matarsa ce to meyesa kalamanta suke Kama da wacce wani abunta ya Bata ne? Kullum tana saba lambobi idan an tambayeta sai tace JM dinta ya mutu Kuma idan tazauna sai take kalamin da suke nuna wani Abu sabanin haka.
Zuba idanunsa yayi akan hoton Ja’afar dake maqale qato a reception din ya zubawa Mahir ido yana nazarin wani abu hakanan yaji zuciyarsa na raya Masa wasu abubuwa duk da ya dade yana qoqarin bijirar dasu Anna sunqi barinsa miqewa yayi ya dubeta ga mamakinsa itama hoton ta kafe da ido ko qiftawa batayi Kama hannunta yayi yace “kinsanshi ne?” Numfashi ta sauke me qarfi tayi murmushin yaqe tace “aa kawai Dana kalli hotonsa sai naga yanamin yanayi da wani dana sani shekarun baya Amma fah nakasa tuna inda nasanshi qila ma a hanya na taba ganinsa”
Sake shiga rudani yayi bayan ya rakata office dinta ya koma nasa cike da tunani mamaki gamida zulumi wannan abin Yana bashi ciwon kai, wayarsa ya dauka ya lalubo number yayansa ya danna Masa Kira ring biyu ya daga muryarsa a kasalce yace “meye Kuma yake faruwa Jamal?” Ajiyar zuciya ya sauke yace “abubuwa da dama suna faruwa fah Prince kayi qoqari kazo 9ja gda ya rikice gefe Kuma da wani rikitaccen Abu da yake sani tunani da shiga zulumi” tashi yayi daga kwanciyar da yayi yace “jikin Barebarin ne ko kuwa wani abu ne daban?”
Shiru yayi na dan lkc kafin ya dago yace “Mai martaba ya matsamin nayi aure har yana iqirarin idan ban kawo ba zai zabomin so nikuma wacce nakeso taqi bani dama a qarshe ma ta dasamin kokwanto Yaya inasonta sosai Amma nafijin tausayinta tayi loosing memory dinta gabadaya bata iya tuna abinda ya faru da ita shekara uku baya saidai wani lkcn takan so tuna wani Abu Amma Bata samun dama a farko Ina dauka kamace kawai kakeyi da Mahir Amma yanzu na fara tantamar hakan inaji a Raina kamar ba Kama bace jinine Yaya don Allah kazo ka ganta ko ka ciremin kokwanto nima na samu salama”
Shiru Ja’afar yayi kamar bazaice komai ba sannan ya magantu da cewa “bana marmarin sake shigowa 9ja har qarshen rayuwata Jamal banida wani Abu da yayimin saura da zan kalla naji dadi komai na kalla damuwa yake qaramin am kaga ka manta da lamarin yarinyar ka nemi wata ka aura….” katseshi yayi da cewa “nifa ba hakanne damuwata ba damuwa ta  ka bani dama na gabatar maka da ita…” Katseshi yayi da cewa “dakata dallah malam idan ka gabatarmin da ita me zanyi Mata Kaine hakan ya Kama saboda Kai kake nema a gurinta ni bana shiga sharafin wani kayi naka nayi nawa kawai” qit ya kashe wayar cike da takaici.
Shima Jamal ransa ya baci sosai yana mamakin baqar kafiyar Ja’afar da gaske duk yamai dakansa majanuni  duk wani abu me amfani idan akazo Masa dashi sai ya Kama fada kamar ance masa shiga wuta”
Tun daga wannan ranar Jamal ya mayar da hankalinsa wajen bincike bisa lamarin Rafi’ah da kalamanta inda a gefe guda Kuma yake qoqarin samo wani Abu da zai tabbatar masa da zarginsa, yaudai tsoro ya cire kasantuwar asabar ce Rafi’ah batada aiki yasashi shiryawa ya nufi gdansu ya kuwa ishesu a parlour tanata tsokanar Bari’ah da cikinta ya fara girma Alh Hisham shima yana tayata.
Kasantuwar Jamal ya zama dan gda yasashi zama kusa da Rafi’ah yana duban Bari’ah yace “auntynmu ya nauyin jiki Kuma” harararsa tayi tace “gulmamme yaushe rabonka da kazo ka dubani” shafa kansa yayi yace “wlh abubuwa sukayimin yawa so banada lkcn kaina ko hajiyata?” Harararsa tayi yayi murmushi tare da kwantar da kansa a kafadarta yace “dan qara hararata kinji” dariya sukayi inda ita Kuma tayi murmushi kawai ya hadasu ita dashi da Mahir ya daukesu hoto yayi ajiyar zuciya yace “zuwa zanyi a wankeminshi nake kallonsa tunda kinqi aure na”
Itadai batace komai ba ta miqe ta shige dakinta zuwa yanzun tausayin Jamal yana neman yima zuciyarta illa kwanciya tayi ranta babu dadi ta rasa meye yakesata damuwa kwanakin Nan tanajin kewar mutane da yawa Kuma sunayi Mata gizo a idonta saidai takasa tuna su waye idan abin ya dameta sai tasa kuka kawai haka iyayen riqon nata zasuyita rarrashinta harsai tayi shiru to yauma duniyar data tafi kenan ganin kanta ya fara ciwo yasata tashi ta dauro alwalar La’asar tayi sallah taci gaba da lazuminta zuwa wani lkc me tsayi sannan ta tashi ta nufi kitchen ta dora musu abinci.
Sai bayan magrib ta gama girkin ta jera a dinning sannan ta koma dakinta tana duba wani littafi tanajin nishadin karatunsa wayarta tayi ring Saida ta katse sannan ta janyota aka sake Kira ta dauka taga number dake yawa àkan sensor din taja tsaki abokin Alh Hisham ne Alh Hassan ya takura Mata ya hanata sakat yo bandama abinsa taqi amsar saurayi saishi me Mata harda yara.
Kashe wayarta tayi gabadaya ta kwanta tanaci gaba da bincikenta bayan ta gama ta miqe tayi Isha ta fito parlour ta zuba abinci ta koma taci a dakinta sannan ta gyara kwanciya tana mamakin kanta a wannan kwanakin abubuwa sun cunkushewa kwanyarta da zuciyarta ta kasa Samo mafita sai addu’a da takeyi Allah ya kawo Mata mafita cikin rayuwarta.
********
Tunda asuba Hajiya Fatsum ta tashi jikinta da sauqi saidai surutan da har yanzu taqi ta barsu tana kulle a dakin da akabar Mata duk gidan babu me zuwa gurinta hatta yaranta Mata sunce bazasu iya ba sai Hajiya Innah da Jamal idan yana gari zuwa yanzu abubuwa ne suke damun zuciyar kowa da yake makusancinta musamman Jamal da subadadin surutun mahaifiyar tasa yake neman zautar da tunaninsa.
To yau dinma kuka takeyi tana Kiran sunan Bilkisu tana gunji tana cewa “nice na rabata da danta Kuma nasa aka kasheta a asibiti nice na rabashi da matarsa da dansa na haukatata ta shiga duniya mota tayi gori akansu nice, nice komai nice Amma bansan waye yayi masa farraqu damu ba bansan ya akayi ya daina Sona da tausayina ba Ja’afar kazo na fede maka biri…..”
Rufe Mata baki Hajiya Innah takanyi tace “zafin ciwo ne yakesata surutu shidai Jamal yashiga chakwakiyar tashin hankali domin kuwa yasan banza bata Kai zomo kasuwa tabbas inkaji gangami da lbr to yaudinma hakance ta faru tunda ta tashi take Kiran Bilkisu Ja’afar Rafi’ah kowa mamaki yakeyi to wace Kuma Bilkisu?”
Sai bayan sun gama gyarats sun fita Jamal ya dubi Hajiya Innah yace “wai wace Bilkisun da Barebari ke yawan kirane?” Numfashi ta sauke tace “bansanta ba kafin zuwana gidannan akayita ance ta  haihune ta haifi ya mace kwana uku da haihuwar aka shiga dakinta akaga tanata fitar da dafara alamun wani Abu ya faru nan akayi da ita asibiti ana zuwa asibiti aka gano guba aka bata a kunun kanwa so a wannan Rana dai Bilkisu Bata kwana ba shikuma Mai martaba lkcn yana tsakiyar gwasake Bai iya daukar mataki ba da akaso tsawaita bincike ma hanawa yayi shine aka dauki yarinyar aka bawa Hajiya Fatsum lkcn itama ta haifi Ja’afar don dama Rana daya aka haifi Ja’afar da yayarku Nafisa wannan dalilin yasa suka taso tare iyakar abinda na sani kenan”
Jinjina Kai yayi ya fice daga gidan Kai tsaye gidansa ya nufa yayi wanka yayi sallah ya dauki waya ya fara danne dannensa cikin saa kuwa ya tarar da yayan nasa a online suka gaisa ya tambayeshi mutanen gida Shiru ta dan ratsa dabara ce ta fadowa Jamal ya lalubo hotunansa da Rafi’ah ya turawa Ja’afar yace _“yaya ga surukarka kasa Mata albarka inajin yarinyar nan ko Bata amince ba zan aureta indai zata zauna dani”_ cikin Ja’afar ne ya kada ya miqe zaune da sauri cikin tsananin tashin hankali da mamaki ya Kira wayar Jamal ya daga yace “ina ka samu hoton Rafi’ah ta?”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *