NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 11 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 11 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

bayan sun barbade da garin lalle kadan. Hannun jimmai na bari ta janyo Koko, da taga yawan kunun gashi da zafi sai da gabanta ya fadi, ba tare da ta iya daga ido ta dubi boka Salmanu ba tace, . “Duka zan shanye MAlman?” Ya amsa mata, Duka zaki shanye”.Nan ta. daga kai ta fara sha ba ji babu gani, da farko Www.bankinhausanovels.com.ng dandanonsa da zaKinsa ya dada ta da Kasa, amma kafin ta gama shanyewa sai da ta ji babu bala’in da ya fi wannan a duniya, ta dinga jin kamar zata amayo da zuciyarta wadda yawan kunun ya danne, amma dai haka ta daure ba ta bayyana komai sai yamutse fuska. Tana ta faman numfarfashi ta ajiye Koko – tana cewa, . . _ “‘Malam na shanye”Salmanu kamar ya fashe da Www.bankinhausanovels.com.ng dariya saboda gaba daya ta fita daga kamanninta, sai uban gumi take hadawa. Ya dube ta ya Kara yin fuska yana nuna mata KoKon kunun aya da aka barbade shi da koren magani, Ki dan huta sai ki sha wannan, yau duk

ZAMU TASHI 

zasu sha ukuba, in an ce su sake shiga rayuwarku tsinannu ne su”
Wannan alwashin nasa ya sanya ta jin _Karfin gwiwa, ta dan huta kadan, duk da ta fara hargitsewa sai ta kinkimi Kokon kunun aya ta fara maka, amma kafin nan ta fara yunKurin amai, sai Salmanu ya ce ta bar shi haka ta ja gefe ta fara jiran aikidacikawa. Ta kuwa .ja_ gefen tana ta _ faman numfarfashi, shi kuma Salmanu ya mai da


hankali ga hira da Baba yana ta faman bugar
ciknsa, a nan ya ji yawancin sirrrinsu, abinda ya Www.bankinhausanovels.com.ng sanya ya Kara tsinewa Jummai, don ya sake gane._ta gama tatike mahaifinsa tsab! Yanzu ba shi da komai sai tsumman rigunan jikinsa, wannan matar ko kashe ta yayi yana jin yayi abinda ya kamata, don fasiKa ce mara imani da tsoron Allah. Kimanin mintuna talatin tuni hanjin cikin Jummai yayo hayar ganguna ya fara kadawa ita kuma tana ta faman murKususun ciwon ciki. Ba mijinta da ke kusa da ita ba, hatta Salmanu yana daga nesa da ita yana jiyo kade-kaden. Nan fa nasa aikin ya tashi. Da zarar cikinta ya debo Kara Kuuuuuu! Sai Salmanu ya saki ihu sannan ya shiga lissafin wasu kwanaki da Karfe kaza an turo aljani wane ya kawo ajiya Kaza, idan yayi shiru cikin nata ya sake debo wani Kugin sai salmanu ya sake bayar da wani bayanin Anan ma sun share sama da muntuna _ashirin, daga Jummai mai wahala biyu ta – lalacewar ciki da bakin labarin da suke samu har Maigidanta mai tausayinta da yawun bakinsa har bushewa yayi. saboda roKon Boka Salmanu ya turawa makiyansu sharrin da suka turo musu. a Daga Karshe Salmanuya bata ruwan gishirin da ya jika tuni da sunan shi zai markade  duk sammun jikinta da aka ajiye mata. Bayan shan ruwan cikinta ya rage rugugi sai ita kadai take jin yawon abinta, babu abinda: ta ke so irin zuwa gida ta hau Shadda. A gaggauce Www.bankinhausanovels.com.ng Salmanu ya sallame su amma ya sanya musu ranar dawowa Juma’a, ya san mahaifinsa babu inda yake zuwa ranar Juma’a saboda yana hidimar masallaci a ranar, Sai gashi kuwa ya gabatar da Uzuri, “Amma kuwa ranar juma’a Malam_ ina da uzuri…”. ; . Karaf Jummai ta tare shi, “Don dai rana guda Malam ai sai ka haKura, ko aikin albashi ne ai ana fashi”. A dan sanyaye yace mata,“Aikin lada ma bai kamata a yi fashi ba…” a . Salmanu ya tare shi, Oh an sanar da mu kana hidimar masallaci ko? To madallah .ai ba sai kazoba, ita sai ta zo a ranar, dama aiki bai dawo kanka ba”. Wannan maganar ta Salmanu ma sai da ta Kara siye imanin iyayensa, tunda yana iya sanin – duk halin da mutum ke ciki ta ya ba zai iya magance masa ba? Hankalinsu kwance sun amince. masa sannan suka nemi sanin cajinsu, nan take Salmanu yayi fuska Dubu talatin zaku. bayar a sai kayan aiki, don aikin naku babba ne”. . Duk yawan dubu talatin din cikinsu babu ~ wanda ya damu da ita. . Jummai ta kwance jaka ta ciro masa dubu -goma tare da bayar da haKurin,.in zata dawo zata ciko ragowar.  Mijinta ya ja ta suka tafi tana ta faman nishe —nishe, Allah-Allah take su je gida ta samu ta juye duniyar wahalar da ke cikinta. Bayan tafiyarsu su Adamu suka fito suka hadu suka yi ta dariya kamar yadda suka saba, in sun wahalar da mutum sannan sun wanke shi. Sannan Tanimu yayi-yayi Salmanu ya fada masa abinda ake shirin yi da iyayensa ya ki fada, cikin barkwanci ya cewa Tanimu,  “Daka kwantar da hankalinka Tanimu ba zan fada maka abinda zan yi ba, na ce ma wannan aikina ne kawai zaku gani a Kasa”. Suka yi dariya kawai. Sai dab da magariba suka fice daga gidan, Tanimu ya tafi tasa sabgar Salmanu da Adamu kuma suka doshi gidansu Husna, har Karfe goma da rabi suna can. –

Ba da son ran. Salmanu ba suka yi mata ~ sallama, saboda idan akwai abinda Salmanu ya tsana bai wuce Salma ta kebe da Adamu ba har ta sha kansa ta cuce shi.. Amma ya san ba shi da wannan damar ta hana su kebewar duk da yana kan tunanin hanyar da zai bi ya hana din.  Wannan ya sa ya dinga rakitar Adamu cikin daren nan suka dinga yawon gidan abokai, har Karfe sha biyun dare. Kafin Adamu ya isa gida sai daya saura, lokacin Salma ta gama cika da kuka da damuwa, don haka ko magana kasa yi masa ta yi. Www.bankinhausanovels.com.ng Tana kallonsa ya dinga sanda yana shirin kwanciya har daga bisani ta ji shiru bai shigo dakin ya kwanta ba. Ita ma ta yi sandar ta Isko shi a falo sai ta gan shi yayi kwanciyarsa kan kujera, da alama baccin har yatafidashi. – Ranar nan ta yi kwanan azabar kuka da damuwa, ji take kamar zuciyarta zata babbabake
da bakin ciki, ina zata iya daukar wannan Kaddarar ta kai? Tun ma kafin amaryar ta zo Adamu ya fara juya mata baya, ‘yan tsokokin naman miyar da ba su fi a Kirga ba da taci su Suka jawo mata wannan tawayar? To shin babu asirin da za’a iya yi mata wanda ba za’a a kafa mata dokar cin nama ba? Wannan azabar ta  sanya ta dokin zuwan safiya ko zata samu ta je gidan bokanta ya fitar da ita.Amma me? Da safe Adamu sai yayi fuska  ya sake hana ta fita. Kamar ta dora hannu aka ta kurma ihu
Saboda tashin hankali, kallon Adamu kawai take saroro tana mamakin in ma shi ne Adamunta da ta sani a kwanaki kadan da suka wuce, wanda ko hada ido da ita ba ya son yi balle yayi mata musu, ita yake shigowa gida tsakar dare ya kwana sallah sannan ya doka wa sammako ya fice? . Da ta ga bai damu da kallon tuhuma da tausayin kai da take masa ba sai ta bude baki a – marairaice ta ce masa, Yaya Adamu wai don Allah gadin gidanka kawai nake ne? da Kyallin rana ba na . sanya ka a idona, ka dawo ka kwana kana sallah, da sanyin safiya ka fice, yanzu in ka bar ni na yi ziyara na ji sanyi sai ya zame maka aiki?”
Ya Ki dubanta lokacin da yake amsa mata,
In dai ba sallar ce ba kya so in yi ba ni ban ga abin kawo maganar sallah nan ba, na san dai duk muradunki ba su isa cinye lokacin sallah ta ba, in kin takura kina iya magana a baki mintuna a cikin na sallar…”Salma ta dafe baki tana ambaton, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!”Yayi fuska ya Ki tankawa, Cikin hawaye ta ce, “Yanzu yadda ka mayar da maganar kenan Yaya Adamu?”  Ya sake kawar da kai, “Ni ban ga abin dumi ba”. Kawai sai kuka ya Kwace mata. Ya juyo yana kallonta, don tsakaninsa da Allah shi bai ga abin zafi a maganarsa ba, sai dai idan dama tana da niyyar kukanta. Yayi KoKarin yayi mata magana ya rasa abinda zai ce, kawai sai ya kada kai yayi ficewarsa. Ita kuma cikin kukanta ta dira Www.bankinhausanovels.com.ng gaban wayarta takira Sa’a. Yau ma ya hana ni zuwa Anti…”. A matuKar Kufule Sa’a ta ce,  “Ki ji min dan iska! To ki bar ni da shi, ni ~ zan je miki yau, gobe in ance ya kuma kallon idonki ya hana ki fita ba zai fara ba”. Salma ta hadiye wani jin dadi da farin ciki mukut! Ji take kamar damuwarta ta yaye an gama. .
Muryarta na rawa ta ce, . “Amma Anti ki ce kar ya sake ba ni mai sharadin Kin cin wani abu, kin san sharrin shaidan, ko baka son cin abu idan aka hana ka sai ka ji duk duniya babu abinda kake so irinsa” “Kar ki damu duk zan masa _bayani, Adamu da wancan shegiyar yarinyar wallahi na yi alKawarin sun rasa farin ciki har abada”. Salma ta sake cika da murna har ta rasa da bakin da zata gode, amma duk da haka tayi togaciya,  Anti ban da Adamun dai”Www.bankinhausanovels.com.ng

***********

Adamu na shiga harabar gidan da sanyin safiyar nan ya hango Salmanu da Tanimu tsaye cirko-cirko, yanayinsu na nuna ba lafiya, saboda haka ya Karasa wajensu da sauri, “Malamai lafiya kuka yi mana tsaiwar jiran kawo gawa?”’  “Ta kacame ne Adamu” Ya ji wani irin haushi ya Kule shi, duk ya . hada su’ yana zabga musu harara: da tsaki, ya fara KoKarin wucewa yanacewa, “Ko kuma mayar da allura garmarku ba, mutum ya baro damuwa ya zo ya tarar ku ma wata damuwar ce, Orijinal ma…”. “Ka tsaya ka ji, in kuma kai ne damuwar sai mu san ta inda zamu magance ta” Salmanu ya tare shi,  Ba a son ran Adamu ba ya tsaya yana kallonsa kawai, Ka san jiya aka zaben cikin gida na jam’iyyar hOnorable ko?” Kada kai kawai Adamu ya sake yi, To jiya tsakar dare Honorable na kuka wiwi ya kira Tanimu, wai mun yaudare shi ba aikin kirki muka yi masa ba gashi nan har an hamBare shi…”Adamu ya tare shi cikin tsaki,
“Ku da Honorable din na rasa wanda ya fi wawanci, ji nake an ce masa ban da sa turare, kai Tanimu ina karuwarsa da muka bata kudi ka kai  mata ka sanya Www.bankinhausanovels.com.ng ta fesa masa turare?”“Na fa kai, kuma ta tabbatar min rannan ta fesa masa, ai na sanar da ku…Adamu Www.bankinhausanovels.com.ng ya sake tarewa a tunzure, To ku bar dan iska ya zo ya tuhume mu mana, turare muka ce kar ya sake ya fesa shi kuma ya yarda wata ta fesa masa..“Anjima ai zai zo”. Salmanu ya amsa masa, sannan ya cigaba_ – da cewa, Tanimu ya tsara shi da kyau, zai zo da maKudan kudi shi ne muke tashin hankalin yadda zamu ci kudin da dadin rai, sai dai nima na kawo shawara”.
Cikin zumudi Adamu ya tari numfashinsa,“Ka ce me?”.
Salmanu ya amsa,“Za mu yi masa aikin sabatta juyatta, mu karbi aiki da makudan kudi a wajensa, mu je mu sami bokan gaske mu biya shi kudi yayi masa aikin, wani abokina da ya koya min wannan_! sana’ar ya sanar da ni ana haka’” Da sauri Adamu ya ce,
“To ba shikenan ba an sami mafita, kuma zaku zauna ku ishe mu da fuskar shanu?” Salmanu da ya gaji da jarabar Adamu sai ya kai masa bangaza, . “Kai mu fa ba matar da ka baro a gida bane zaka zo ka ishe mu da dumin kai, muna lissafo maka matsaloli kana mana hayakin kai, wallahi zan daki hancinka Adamu…” “Don Allah kar ka fasa”Adamu ya fada bayan shi kuma ya  cukwikuyo kwalar Salmanu. Tanimu ya shiga tsakani yana dariya, Salmanu ku bari,. yanzu ba lokacin game dinku ba ne, mutumin nan da yamma zai zo duk inda zamu samo asiri mu samo mu bashi mu karbi kudinmu, in ya so sannan idan ma kofin – kokawa zaku sa mana sai mu shata muku layi a yi, amma yanzu dai a san na yi, a wannan zuwan. nasa yakamata Www.bankinhausanovels.com.ng dukkanku ku sami Besfan hawa, ni kuma in fara tara kudin sayan mota…” “Ko kuma jirgin sama ba In ji Adamu ya saki kwalar Salmanu yana hararar Tanimu kuma. __. . Tanimu bai kula shi ba ya cigaba da. bayani, . “Akwai wani Basaraken boka da na ji labarinsa, na kawo shawarar a je wajensa, yana can cikin Kauyen Bunkure, an ce aikinsa tamkar dauki ajiye ne, duk abinda ka nema-sai ka — samu…” ‘“‘Matsalarsa kawai manemin mata ne…”. -Inji Salmanu. a ‘ A Kufule Adamu ya tare Salmanu. Oh kai mata maza ne kake tunanin in ka je zai neme ka ko?” SO Shi kuma yana dariya ya-amsa masa, “Ko dai zai neme ka, ai kai zaka shirya ‘ yanzu ka tafi, Tanimu cigaba da ba _ shi bayani….’. De Kafin ya rufe baki Adamu yayi gaba yana cewa, . “Zan je amma duk bala’inku wallahi sai na yi baccin awa daya” “Dan raini wayo”. — In ji Tanimu. Salmanu ya tare shi bayan ya fara tafiya, “Kai ma ai wani dan rainin wayon ne, na ji kana kira mana Kananan alhaki wani besfa, ni ina da niyyar ta dalilin Honorable din nan duk sai mun je Kasa mai tsarki”. Cikin zumudi Tanimu ya ce, “Ka ga kuma tunanin ka yayi kyau”

******

Sa’a ita kadai ta je wajen Basaraken malaminta. Da farko ya so ya Ki bayar da ~ maganin ga Salma da ta Ki zuwa da kanta, sai da Sa’a ta matsa masa da magiya kuma dai da sabon da ke tsakaninsu ya sanya ya saurare ta, bayan ta . kwararo masa dogon bayani ya fara amsa mata da cewa, _ “Ai dama ta san da zaman wannan. yarinyar . Sa’a ta dubi Www.bankinhausanovels.com.ng malaminta da mamaki, tana jin haushin Salma don ta san malaminta ba ya Karya, Kai tsaye ya amsa mata da cewa, “Tun rana da ta fara zuwa da buKatar a. cusa sonsa cikin zuciyarta na sanar da ita cewa,

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *