NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 12 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

 NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 12 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

A Kufule Adamu ya tare Salmanu. Oh kai mata maza ne kake tunanin in ka je zai neme ka ko?” SO Shi kuma yana dariya ya-amsa masa, “Ko dai zai neme ka, ai kai zaka shirya ‘ yanzu ka tafi, Tanimu cigaba da ba _ shi bayani….’. De Kafin ya rufe baki Adamu yayi gaba yana cewa, . “Zan je amma duk bala’inku wallahi sai na yi baccin awa daya” “Dan raini wayo”. — In ji Tanimu. Salmanu ya tare shi bayan ya fara tafiya, “Kai ma ai wani dan rainin wayon ne, na ji kana kira mana Kananan alhaki wani besfa, ni ina da niyyar ta dalilin Honorable din nan duk sai mun je Kasa mai tsarki”. Cikin zumudi Tanimu ya ce, “Ka ga kuma tunanin ka yayi kyau”

******

Sa’a ita kadai ta je wajen Basaraken malaminta. Da farko ya so ya Ki bayar da ~ maganin ga Salma da ta Ki zuwa da kanta, sai da Sa’a ta matsa masa da magiya kuma dai da sabon da ke tsakaninsu ya sanya ya saurare ta, bayan ta . kwararo masa dogon bayani ya fara amsa mata da cewa, _ “Ai dama ta san da zaman wannan. yarinyar . Sa’a ta dubi Www.bankinhausanovels.com.ng malaminta da mamaki, tana jin haushin Salma don ta san malaminta ba ya Karya, Kai tsaye ya amsa mata da cewa, “Tun rana da ta fara zuwa da buKatar a. cusa sonsa cikin zuciyarta na sanar da ita cewa,

ZAMU TASHI 

yana cikin wata zazzafar soyayya, amma ba ta buKaci komai a kai ba”. . Sa’a ta zaro ido, “Ka san muguwar sokuwa ce, sai dai a taimake ta ba don halinta ba kawai, in ba haka ba na san waccan tana can tana Kugo mana asiri, har ni nan bata bar niba”.
Nan ma ya sake amsawa kai tsaye, ~ “Lallai dai kam, har wajen matsafa mun gano ta a can”. Sa’a ta gigice, shi kuma malamin ya cigaba da yi mata wani irin kallon maita, wanda ya sata ~ ke ta tsarguwa Www.bankinhausanovels.com.ng duk da ba yau ya saba yi mata _irinsa ba. Ta sha jin rade-radin ana cewa . ’ malamin nasu manemin mata ne, amma to yaya . zasu yi tun da a cikin malamai ana lalaubawa da _kyau kafin a sami me jan aiki irin nasa? Aikinsa kamar yankan wuKa ne, duk mutumin da ya dandana ba ya iya canzawa, don haka ake tafiya da shi tare da halinsa, to ita da aurenta ma me zai dame ta tunda in dai ba giya ya sha ba ai ba ya ce zai neme ta ba. .. , Kanta na

sunkuye tace, “Yanzu taimakon da muke so shi ne, lallai a fara hana auren, sannan ayi rigakafin faruwar Www.bankinhausanovels.com.ng
wani auren nan gaba, su rayu su mutu su kadai, a sace masa zuciya. fiye da yadda aka yi wa. Alhajina don shi wannan ya fi Alhajina hatsari, ‘wallahi ba don kai ba Malam ruwa ba zata sha ba mugun dan bala’! ne” Kafin ta rufe baki ya jefa mata wani Kullin magani mai kama da farin kwalli, Ki kai mata wannan”, ‘ – Sa’a ta dauka da sauri sannan ta nutsu tana sauraron bayaninsa. Yaci gaba da magana cikin yanayin Kasaitarsa, . “Kin san ludayin duma ko?”
Sa’a ta kada kai, Yauwa! Zata sami mai dan girma, ta nemi fararen goro guda uku ta sa a ciki, da dare sai ta yi fitsari a ciki ta tura KarKashin gado, a wannan ranar lallai ta tabbatar sun yi harkokin aure a kan -gadon. Da safe sai ta janyo goron nan ta fitar da shi daga cikin fitsarin ta shanya shi a rana, fitsarin ta zub da shi. Idan goron nan ya bushe sai ta hada shi da wannan garin maganin ta dake, ta dinga barbada masa a abinci yana ci, ina tabbatar miki in dai ta yi haka Adamu sai ya fi waina a tanda sauKin sarrafawa”Kamar Sa’a ta yi tsallen murna da ihu ta ke kanta, jikinta na Bari ta ce, . “Malam ni ma ko shi za’a ba ni?” Murmushi kawai yayi yana cigaba da
Kallonta, bai damu da amsar maganarta ba yace, “Ki fada mata, sharadin shi ne kar ta sake .ta shuri wani da Kafa” A sauKakKe kenan Malam, dama ta ce na sanar da kai kar a ba ta mai sharadin Kin cin wani abu, don muna zaton wancan maganin ya warware, ta karya doka taci nama”.Har yanzu idonsa na kanta, , –“Amma wannan da kike gani ma ba mai sauki ba ne, shuri ko ba tare da niyya ba kana iya yi baka sani ba, cin nama kuwa sai ka sa kanka – zaka kai bakinka’’. Cikin alamun kasa hankali biyu Sa’a ta kada kai, “Haka ne kuma Malam, yanzu ni ma ba zaa sam min ba? Kwanan nan Alhaji sai ya dinga sha min Kamshi gara a ba ni wanda zan hadiye shi duka”. Yanzu sha’awarta ta fara bayyana a. fuskarsa, muryarsa a dashe yana ta murmushi ya ce mata, .
Ai ko me zai hana a baki Sa’a? Babu abinda zaki nema a wajena ki rasa”Ya cilla mata Kulli daya. Jikinta a sanyaye ta dauka tana godiya. Kallonta kawai yake, don haka ta fara dokin tashi daga gabansa amma ya Ki sallamarta, ya kuma Ki cewa da ita komai sai uban kallon da yake mata. Ta muskuta ta sake debo wani batun, — . “To Malam wanne zaka ba ta wanda zai mata maganin kishiyar tata?” ,In an hana ta shiga gidan an yi daidai? Yanzu ta kasa jurewa wannan kallon nasa, kanta a Kasa ta yi saurin kada kai,“Anyi daidai Malam, mun gode”, – . Tana KoKarin ajiye abin sadaka. Yayi saurin dakatar da ita “Ki bar shi Www.bankinhausanovels.com.ng kawai…. Ta dauke kudinta jikinta na rawa. . Ya sake karkace kai ya dube ta ya ce, ° – “Sa’a haske na ga kina Kara yi,.ko kin yi , ciki ne?”. Sa’a ta ji dakin na juyawa da ita saboda tashin hankali, amma babu yadda ta iya haka ta ware baki cikin kunya tana dariya ta ce, A’a yanayin zafin nan ne ya sanya fatar mutane take ta gogewa, amma ai ban jima da _ yaye dana ba Malam”, —° “A’a ke dai kawai kina da kyan fata ne ° kamar ta larabawan masar, ko kina amfani da sinadaran Mangwaro?” – Yanzu Sa’a kasa magana ta yi, sai kada kai __ kawai ta yi. Bai damu da rikitarta ba ya cigaba da cewa, “Amma ko na yi mamaki, gaskiya kina da kyan fata ke komai ma kina da shi, in nine mijinki ba sai kin kai ni wajen kowa ba zan zama bawanki’’. ‘ Tana ta dariyar Karfin hali ta mike tsaye tana cewa,  “Na gode Malam, bari na wuce sai yaushe zamudawo” Shi ma dariyar yake bai kuma karaya ba, . “Duk lokacin da kika dawo ai ni mai maraba da kene, ga wani taimakon ma Ya cilla mata wani daurin magani, bai jira = cewarta ba ya bata bayani, . “Maganin dandano ne zaki zama fiye da = zuma, naki ne ke kadai idan Salma na bukata « tana iya zuwa ta karni nata”. Hannunta na karkarwa ta sunkuya ta dauka ta yi masa sallama sannan ta tafi cikin rakiyar idonsa. ’ Dai dai lokacin Adamu ya Karaso a babur, ya sauka ya fara tambayar mutane ana nuno masa  kofar shiga, ya fara hangen Kofar daga can sai ya hango wata na fitowa daga kofar da aka ce masa ta shigar mata ce kamar Sa’a, bai jima yana son tantancewa ba ya tabbatar da ita din ce.
Wani matsanancin tashin hankali’ ya fado zuciyarsa yana shirin halaka shi. Me Sa’a ta zo yi wajen bokan nan da aka ce Dan akuya ne? Ya tambayi zuciyarsa, wadda ta rikice, yadda ko ,,,,,,,,,-amsar ba zai zama ita zata lalubo ta ba.

**********

_ Adamu na kama hanyar Bunkure Salmanu ya kira Husna a waya ya ce mata maza ta zo yanzu.
’ Ko mintuna talatin ba a yi ba sai ga ta, jakarta cike da kyautar turaruka masu kyau da ta. kawo wa karrarmammen malaminta wanda ba ya Www.bankinhausanovels.com.ng
karbar kobonta, duk da bata ga wani malami da ya kai shi zafin aiki a duniyar nan ba, kai ko da tayi aka taya ta son Adamu ba ma wai a bude _ mata hanyar aurensa ba, ita har abada ba zata taba mantawa da wanda yayi mata wannan karar ba, . . ” , – Yau dai ba ta zo da buKatar komai ga.’ bokanta ba sai tarin godiyar da ta zo masa da ita. Gaskiya .a yau din nan Salmanu yaji tausayinta fiye da koyaushe, tana tsananin son . Adamu, ga matsiyaciya Salma na’ can cikin tsananin son raba su. — . _ Salmanu dai ya ga babu wata dabara wadda ‘ ta wuce ya fito fili ya sanyata a hanyar da zata ‘ Bullar da ita hanyar da zata dace, shi ba wani malami ba ne kuma ba mai yawan ibada ba ne, ” amma yana zama da masu yi, yana kuma ganin sun fi kowa bullewa idan sun kama turba. . ‘Saboda haka ya nutsu yace mata,“Akwai fa kalubale”. Husna ta yi tsuru tana kallonsa cikin dukan zuciya batareda tatankaba. Ya sake gyaran murya ya ce mata, “Kin sauke Kur’ani?” Da sauri ta kada kai cikin alamun rashin,,,,,,,, gabadaya ta fara jin karaya, amma ba ta san ta inda zata tattage tata
Kina zuwa islamiyya?” Nan ma ta kada kai da sauri
“To ki daure ki dinga hana idonki bacci kina neman tsarin Allah da dukkan masu sharri_ na fili da na Boye, amma magana ta gaskiya akwai makiya Allahn da suka tashi tsaye wajen – ganin bayan aurenku, magana mai kyau ita ce ayi rufdugu a nuna wa ubangiji su, in da gaske ne kina son Adamu to lallai ki nemo muku tsarkin rayuwa ta hanyar Allah”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kamar Husna zata yi kuka tana duban bokanta, ba taKi ta tasa ba, amma tana buKatar ya wayar mata da kai, abin ne ya Kazanta har ya – fi Karfinsa da yake ganin ba babu wata mafita sai dai ta addu’a ko kuma so yake ya ce ya gama taimakonta? ° Idonta na alamun zubar da Kwallah ta dubi Salmanu,
“Malam kaina ya rikice ban gama gane inda ka dosa ba”. A tausasaye Salmanu yayi fuska, Ke dai ki je ki yi abinda na ce miki, ki fuskanci Ubangiji da kushu’i, alkhairi kike nufi da Adamu, abinda ubangiji ke so kenan zai sanya hannu”. . . Husna ta ji wata ‘yar guntuwar nutsuwa ta keto ranta, ba ta saka ran zata sami Adamu ba sai dai sa ran rahmar Ubangijinta wanda kafin shigar son Adamu zuciyarta, ba ta da wanda take kai wa kukanta sai shi,-ta san shi ne mafi cancanta, ta hanyarsa ake riskar ko wannen irin tsira. Tana ta faman goge hawaye take wa Salmanu godiya. Sai ta Kara ba shi tausayi, ya dinga jin  tamkar ta karaya ne ko kuma tana son cire rai da Adamu, saboda haka ya Kwarara mata gwiwa,
Kije ki kwantar da hankalinki, tun kafin ki.zo gabana da buKatarki na ci alwashin in dai ina numfashi iyakar iyawata sai na taya ku harin burinku, da nace ki je kiyi addu’a ba wai ni zan – kwanta na manta ku ba ne, nima Zan taya ku add’ar kuma daidai gwargwado da aikina sai na ga abinda ya turewa buzu nadi’
Wani Kwarin gwiwar ya sake zuwa wa Husna ta shiga dariya.amma tana hawaye, a haka ta sake sauke kwandon wata godiyar sannan ta yi sallama ta tafi.
~~. Nan ta bar Salmanu fadawa tunanin ta inda bai iya taimakon Adamu ya raba shi da sharrin Salma Www.bankinhausanovels.com.ng Iyakar basirarsa ya Kure daya kasa tunano mafita.

***************

Karfe uku saura na yammacin ranar -Adamu ya shiga wajen sana’arsu wurjanjan. Kallo daya su Salmanu suka yi masa suka san lallai ba gajiyace kadai ta niKa shi ba, gajiyar ta damuwa ce me tasowa tun daga Kasan Zuciya. . Yana mika musu maganin da_ sauran bayanan ya. Kulle can ciki ya Kudundune ya kwanta, har sai da Honorable ya zo ya tafi suka ‘shigo suka tashe shi suna ta faman ihun sun yi kudi sun huta. ° . Salmanu ya daka masa duka -ya_ tashi zaune, SO “Kai wai aKafa kajene?” ; Saroro Adamu ya tsaya yana kallonsu, hakan ne kuma ya sanya Salmanu ya fahimci lallai akwai_ wani Katon abu da yayi wa Adamu mahangurba, nan da nan sai Salmanu ya shiga hankalinsa. , Ya gyara zama ya ce, Adamu me ya faru? Kar dai malamin nan ba mata kawai yake nema ba, na rantse da Allah in shi ya gigita ka daga kanka ba zai sake ba… Na rantse sai in zama ajalinsa sai dai duk abinda zai faru ya faru”. . “To sarkin ina da kisa”.Tanimu ya fada cikin mamaki da gajiya da halin Salmanu na yawan ambaton zai yi kisa, – amma ko KwakKwaran mari.ba ya yi, sai shegen Adamu ya tare shi yana murmushin Karfin—. hali,“Wai Sa’a matar Alhajina na hanga tana fitowa daga wajen bokan nan, sai rabewa nayi har ta bar garin…
– Tanimu da Salmanu suka dauko Hirji a tare suka sauke, Tanimu da mamaki, Salmanu komai_. ma ya hada. Duk sun kasa magana sai Tanimun ne ya WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG KoKarta yace, So,Zance ya baci”Cikin yanayin tausayawa kai Adamu yace, Ko kuma yana shirin baci ba, yanzu tashin hankalina shi ne, yaya zan yi in tabbatar Sa’a’ bata koyawa Salma bin malamai ba? Ka san ance goyo guba”, Salmanu ya kawar da kai wani shegen haushi na naushinsa a Kirji. Ai a duniyar nan duk wanda yayi maka sihiri ya juyar maka da lissafi ya gama da kai, wai sammatacce irin Adamu ne ke fatan matarda ta sammace shi. bata zuwa wajen bokaye, wannan kayan takaici da me yayi kama? Ga abin duka Adamu, amma babu dama. Tanimu dayake shi ma wani gabon ne kawai sai ya karkace kai yace,
“Yo Adamu wannan kundubar matar taka in ba ta je wajen boka ba, ta ya za’a yi ka zauna da aurenta? Ni wallahi ko da marsandi aka hada min ba zan zauna da wannan raka ni kashin ba, aiba ta da wani amfani in ba kashin tsakar dare ne ya rarako mutum yana tsoro kuma ya rasa dan rakiya…” Da dai Salmanu ya lura da cewa duk hararar da yake wa Tanimu bai kula ba kuma ba shi da niyyar diga aya nan kusa a kundin cin fuskar da ya budewa Adamu, kawai sai ya dauki wani kofin ruwa ya jefe shi da shi, cikin sa’a kuwa ya same shi a baki har ya dan yi masa jini.
“Ka ji ka nan wani banza, kai ko raka ni tusa kana da ita ne?”.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *