NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 6 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 6 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Tun daga wannan kumburin nasa Alhaji ya san ba zasu kwashe ta dadi ba, don haka shi ma ya kinkimo gizago ya makawa girar idonsa. Yaiyalin?”. .

Alhaji yayi fuska ya fara da wannan.Ba tare da Adamu ya daga kai ya dube shi ba ya daga hannu ya ce,  “Suna can gida”’. Alhaji ya hadiye haushin amsar ya ce, “To madalla”, Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yayi shiru Adamun kuma bai yi alamar . tankawa ba, dole sai shi Alhajin ne ya gyara zama ya debo abinda yatarasu, “Jiya ka tashi hankalinmu gaskiya, . musamman mahaifiyarka da ka hana runtsawa”.
Cikin daurarriyar fuska Adamu ya daga kai ya dube shi, amma bai ce komai ba. Alhaji yacigaba dacewa, “Cikin dare wallahi kasa bacci ta yi dole ta kira ni a waya ta ce na zo na ji danyen hukuncin dakazodashi’, .. Kawai sai Adamu ya daure gira ya sake yin Kasa da kai. oy . -Cikin fishi Alhaji yace,
Anya Adamu ba-zaka bar rayukanmu ni. da mahaifiyarka ya zauna lafiya ba, kullum mu kenan cikin saKa da warwarar yadda zamu ga ka , zama mutumin kirki kai kuma kana baudewa?___ Wai me ke damun hankalinka ne?”Adamu ya sake bata rai, murya a cunkushe,  yace,” “Ni wallahi ban san abinda yanzu nayi,,,,, Alhaji ya tare shi da sauri

ZAMU TASHI 

“Ba ka san abinda ka yi ba Adamu, ba ka sanma batun da kaje wa da Hajiya jiya dashi ba?” Kai tsaye Adamu ya amsa, “Ai na ji kana maganar ana so na zama mutumin kirki ina baudewa, na san jiya zancen zan yi aure na je mata da shi, sunnar Manzon Allah SAW, ni ban je da wani ta’addanci ba…” Eh, haka ne zancen aure ka je dashi,ko wata biyu da aure baka rufa ba ka tattago wani,wannan ba ta’addanci ba ne zama lafiyane, auren fari ma kai ka yi wa kanka ka nemi matsuguni kuma kana da sana’a ciyar da mata… duk wannan zama lafiya ne ba ta’addanci ba”. Adamu yayi dif! Zuciyarsa kamar ta kece da haushi da takaici. Alhaji ba abokin yin sa bane, amma da ya sha magana.

Kamar an jefo Sa’adatu ta shigo dakin da zummar kwashe kayan abincin Adamu, amma a zahiri Www.bankinhausanovels.com.ng tsegumi kawai ya kawo ta, don kiranda Hajiya ta yi wa Alhaji cikin dare ya tsaya mata a rai, gashi kuma Alhajin ya shafewa idonsa toka ya ki sanar da ita, ita kuma ta kasa rashin kunyar ta tambaye shi, kenan tana da yaKinin wannan zuwan na Adamu yana da alaKa da kiran Hajiya nacikin daren, – -Ta samu Alhaji na ta yi wa Adamu fada, .° don haka ta bi ba’asi shi kuma Alhaji ya kwashe komai ya Sanar mata. . Ba Karamin tashin hankali ta shiga ba da jin labarin, amma a iyakar filin zuciyarta kawai . rudun ya tsaya, fuskarta fal murmushi tashiga  maganar,

********

“Haba Adamu, kai kuwa ka dinga girma ~~ mana, nan da dan wani lokaci fa kai ma zaka. zama uban kanka, bai kamata ace har yanzu baa . dena zaunawa tattauna gyaran matsalolinka – ° ba. , Dama gabarda Adamu kenemakenan, .. wato inda zai sauke bacin ran da aka tara masa, Alhaji dai ya cika masa fuska, saboda haka Sa’adatu ta tari tsinin. Cikin kaushin murya ya tsattsare ta da ido yace, Ban gane ana zaman tattauna matsalolina ba…”. – Tunda Sa’adatu ta san hali saitatare shi – cikin rarrashi, ‘  “Ba ka fahimce ni ba, yanzu don Allah ba  tashin Www.bankinhausanovels.com.ng hankalinmu kayi ba, wata nawa da Kukutawa a yi maka auren zaka kinkimo wani ka kawo? Ko kai ka yi wa kanka aure Adamu bai kamata ko rufe wata biyu ba a yi.ba ka kuma tarko wani..Ya sake tare ta a zafafe yana fadan goggo  kofa, . . “Ni mamaki ake ba ni wallahi, don girman Allah wa na zo na tsugunawa naCe yayi min aure ko ya gina min gida in zauna ko kuma ya bude min shago? Dama duk an yi min wadannan ne don da nayi‘motsi a yi min gori. ‘Yanzu numfashin Alhaji neman daukewa yake saboda tsabar takaici, ya rasa inda zai ajiye tunani akan Adamu ya ji sanyi, tabbas ba roKarsa Adamu yayi ba yayi masa aure ko ya bashi abubuwan da ya bashi duk shi ya sa kansa, amma . ba yayi ba ne don cutar Adamu shi yayi ne don . ya faranta masa kuma ya farantawa Hajiya, yana kuma da tabbacin abinda yayi zai zama gyara ga rayuwar Adamun, amma ‘kaico! Ga yadda ‘Adamu ke kallon abin, ta ina zai fahimtar da shi? Ya ji kansa yayi masa wani irin nauyi kawai sai ya saki baki yana kallon Adamu suna tirzawa da – Sa’adatu. Sa’adatun ta cewa Adamu, “Gaskiya ka sake tunani Adamu, abinda _ Alhaji yayi maka godiya ya kamata ka mutu kana yi masa ba wai yana motsi ka ce ba rokarsa ka yi ba, na ga dai ai ba dole yayi maka ba da bakinka – ka fada masa kana son Salma…”. , A matuKar tunzure Adamu ya tareta, “Kin ga in zamu yi gaba mu bar wannnan zancen kawai mu yi gaba, amma kar ki Kara sako _ wata maganar ba dole aka yi min ba, in ma nina fada wallahi dole aka yi min na fada… ni ban taba mafarkin in auri Salma ba wallahi, wadda nayi mafarkin in aura ba a aura min ba, kuma ba a ‘ba ni dama na nemo kudin’da zan aura ba.. tamkar an halicci rayuwata ne domin komai ake zabamin.. Ba Karamin kaduwa Sa’adatu tayi da jin  wannan maganar ba, da Kyar ta takura kanta ta tsaya -kan doka da oda a filin fuskarta kawai, jikinta babu Kwari ta dora hannu a Kirji tace, “Ni nake zaba maka komai Adamu?…” . Alhaji da ya gama zuwa wuya ya tare ta“Kin ga ki bar shi ba da ke yake ba dani – yake”. – Adamu yayi fuska yaKi tankawa. Cikin rashin Kwarin jiki Sa’adatu ta bi kujera ta zauna don da tana tsaye tsakiyar dakin. Suka yi shiru tsawo wani lokaci kafin Alhaji ya yi gyaran murya ya dago kai ya dubi Adamu,. “Yanzu. wadda ka je wa Hajiya da – maganarta ita ka yi mafarkin aure?”. . , Kai tsaye Adamu ya_ gyada kai, har yanzu fuskarsa babu annuri., Cikin‘sallamawa Alhaji ya kada kai yace,
“To idan ka nemo kudin auren nata ko yau ka shirya ka kawo a kai mata kudin auren, badon turin haushi na yi haka ba kawai don ba nida kudin ne yanzu…”, o- Cikin barin ‘jiki Sa’adatu zata yi magana ; Alhaji ya dakatar da ita da hannu yana jiran . amsar Www.bankinhausanovels.com.ng Adamu. .__, Sai a nan Adamu ya dan saki rai, ya gyara zama yahaubayani.  “Yau zan dawo da dare na kawo maka, dama a gidansu ance in na wuce nan da jibi zasu bawa wani, kuma wallahi in na rasa yarinyar nan  na rasa rayuwar jin dadi ta har abada”. Zuciyar Sa’adatu na kamawa da wuta shi kuma Alahaji na jin kamar kansa zai tsarwatse, amma da yayi ta mazan kadawa Adamu kai yace “To babu laifi, ka kawo zamu yi KoKarin mu kai kafin jibin”. .
Cikin farin cikin da ya taso tun daga tsakiyar zuciyar Adamu ya duka yana yi wa Alhaji godiya sannan yayi musu sallama ya fice.
Yana fita Alhaji ya kawo gwauron numfashi sannan ya dora da fadin, . .Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”. A matukar Kufule Sa’adatu ta tsare Alhaji da ido tana cewa, “Alhaji zaka yi Hirji a abinda kake da ikon hanawa?’. . Da sauri ya tare ta cikin tara gira,Ni nake da ikon hana Allah yin ikonsa Sa’adatu? Kar ki manta da ina da iko tun farko ba haka na so Adamu ba, da ban canja shi ya zama abinda nake so ba?”. Har yanzu cikin zafin rai Sa’adatu ke kada
kai,“Alhaji in kace baka yarda yayi auren ba ai ba zai dora maka bindiga ya kashe ba, musamman ma da ya ce an ce nan da jibi ake Jiransa ya fito a gidansu yarinyar. Ni ban ce kai kake da ikon yin auren ko hanawa ba, amma__ ubangiji ya baka taka damar ta iko akan rayuwar Adamu…”Cikin bacin rai ya tare ta, “Da alama ke ma kin sha kayan mayen da ya sha Sa’adatu, Salma ma ba ni na aura masa ~ ba, Ubangiji ne ya hukunto cewa matarsa ce, idan wannan ma an rubuto matarsa ce wallahi ban isa na hana ba ko ina so ko bana so, kamar yadda na fada miki wallahi ba haka na so Adamu ya zama ba, amma tun da ba ni da ikon gashi nan yazama…. . Yanzu Sa’adatu ta fara KoKarin dawo da * hayyacinta ganin cewa tana Www.bankinhausanovels.com.ng Kokarin fitar da maitarta fili akan auren Adamu. 
Ta rausaya kai ta ce, . “Ka shawarci Hajiya, amma wallahi ni ban ga azancin ku bar Adamu yayi aure ba…”. – . Alhaji ya tari numfashinta tare da mikewa tsaye, .Ai sai kuma ki yi, Hajiya ba ta kira ni ba sai da ta yanke shawarar babu wata mafita sai ta barinsa yayi auren, ta roKe ni da cewa ko da wasa kar na hana shi” Sa’adatu ta ji wani irin tashin hankali da yake ruguzo mata a Kirji, babu fuskar wanda take
hangowa sai Salma wadda ta dauki son duniya ta dorawa Adamu, tana da tabbacin ba karamin ciwo auren Adamu zai mata ba, sannan tana da haKikanin matukKar sun bar Adamu ya sarrafa zguciyarsa da kansa, to kuwa ba zai taba iya yiwa Salma adalci ba.. Dole ma Salma ta sake lale. Ta dawo fagen daga ta neme Adamu da kyau, ba irin neman sassaucin da tayi masa ba, wai daga samun aurensa ta koma daki ta kwanta, ga sakamakon hakan nan ta gani ko wata biyu ba’a yi da auren ba ya kwantsamo kishiya zai kawo mata, kishiyar ma irin wadda yake ganin Kyallin gwal a goshinta. Kamar Alhaji na so ya _ gano_tashin hankalinta, don ya tsaya a kanta kawai yana ~ kallonta. Hakan ya sanya nan da nan ta wattsake ta dube shi ta ce, In haka ne to hirjin me kake? Ai kawai ka kwantar da hankalinka tun da Hajiya ta aminta, na tabbatar sai albarkata ta shiga lamarin”’. Alhaji ya ji wata .nutsuwar zuciya ta ziyarce shi, cikin jin dadi jikinsa a sanyaye ya amsa mata, Ni ma tun jiya da dare na ji nutsuwar hakan, bai kamata mu tare mu yi ta Bata mata raiba, maganar aurensa ni ta wuce a wajena, ina hirji ne don fargabar inda Adamu ya je ya nemo kudin auren nake yi, ko ke baki yi KoKarin tuna hakan ba?” Ta girgiza kai da sauri, “Alhaji zai wuce a ce jarin Www.bankinhausanovels.com.ng shagon zai — tattare?” _ Cikin murmushin Karfin hali Alhaji ya ce, “Amma dai Sa’adatu a bakinki na fara jin cewa Adamu bai damu da shagon ba, hasalima Salma ce me madafun ikon shagon, abinda ma – yakamata ki tuna shin, Shagon: yana samar da kudin da ya fice ciyar da su har ya tara kudin da zai aurar da me shi?” .Sa’adatu ta nuna sanyin jiki ne, kawai. Amma har yau ba ta gamsu da zafafa al’amarin da Alhaji ke son yi ba, ta dai rausaya kai ta ce, “Ya salam! Gaskiya akwai ayar tambaya”. Jikin Alhaji a sanyaye ya gyada kai ya fara KoKarin ficewa yana cewa,  “Allah ka dafa min, Allah ka ba ni ikon nuna wa yaron nan hanya kai kuma ka shiryar dashi kar ya zama daga cikin mutane tababbu”. . Sa’adatu ta biyo bayansa da sauri tana amsa masa, “Amin”.
Ta yi masa a dawo lafiya ya fice, sannan da sauri ta shige dakinta ta rarumo waya ta hau kiran wayar Salma amma abin takaici ta dinga samun wayar a kashe. Gabadaya nutsuwa ta Kaurace mata don ta tabbatar wata baKar Kaddara ta fadowa Salma, kishiya ai bala’i ce, wallahi ita da mijinta yayi aure gara mutuwa ta dauke shi ita a bar ta da jigilar marayu. Daga Adamu har Salmanu kai har ma Tanimu suna cikin farin ciki da yadda ta kasance, : da. yamma suka dau wanka dukkansu, suka fankaya gidansu Husna hira, bayan Salmanu ya danKawa Adamu kudin auren da zai kai har dubu hamsin. . Wannan zuwan ba Karamin dadi ya yi wa – husna ba, ta dinga share hawaye a Boye tana shi – wa Bokanta albarka bisa farin cikin da ya samar mata, ya kawo mata Www.bankinhausanovels.com.ng masoyinta rayuwarta alhalin . da ya nade Kafar wando yana shirin tserewa rayuwar tata, abinda zai janyo mata tawaya, babu abinda zata yi wa bokanta sai neman masa – gafarar ubangiji. Suka dinga hira da nishadi Husna da Adamu suka dinga jin kamar aljanna suka hango suke dosarta, yadda suke kwatanta farin cikin da zuciyoyinsu ke ji kenan. Har cikin gida husna ta ja su suka gaishe da matan mahaifinta, duk su ukun kuma babu wanda bai yi musu alheri ba.Bayan sallar magariba kuma mahaifinta ya dawo, shi ma suka je suka kwashi gaisuwa, mutum mai kirki da dattako ya karbe su da mutunci da girmamawa, sannan dayake yana da barkwanci sai ya dubi Adamu yace, a “Yanzu dama kaine wanda zaka iya sace . zuciyar Husna, duk ruwan idonta da ke hada ni fada da ita dama kai take jira? Gaskiya na gaishe ka”Duk suka yi dariya. Salmanu kuma ya shiga gabatar da Adamu a wajen Surukin nasa, Unguwar su Adamu da kuma gidan da ya fito Sannan da sana’arsa ta kanti Www.bankinhausanovels.com.ng kana ya Kara da wata Karyar cewa, -Sai kuma sana’ar da ya fara kwanan nan kuma ta zo masa da albarka, wato harkar sai da gidaje da filaye”’.Mahaifin husna ya dinga zura musu ~ albarka, sannan ya rufe maganar da cewa, In sha Allah goben nan zan dan bincikaka a unguwar, ina fatan babu laifi hakan?”. Cikin Karfin gwiwa Salmanu ya amsa, Ai in ba mu ji cewa zaka bincika din ba ne ma jikinmu zai yi sanyi Baba, mu ma binciken ai muka yi muka zo, bayan mun haKaKe mun zo gidan da aka karrama mutunci ake kuma ba shi hakkinsa”’.Mahaifin Husna ya Kara cika da jin dadi, fuskarsa ba ta Boye hakan ba ya cigaba da cewa,Na gode sosai, kuma wannan maganar , taka ta Kara tabbatar min cewa kun san abinda kuke”Salmanun ne ya sake tararsa da cewa, Mu ne da godiya Baba, sannan mu na – rokon cewa don Allah kar ka mantawa da bullawa unguwar tasu gobe, don Iyayenmu na shirin zuwa jibi’’. Zuciyar Mahaifin Husna daya ya ce,  wannan ai ba zai hana komai ba, su zo Allah ya sanya mana hannu a cikin nufin alkhairinmu”Daga nan suka datse tattaunawar, suka yi . KoKari ba wa Baba hasafi amma fur ya Ki karba. Sai kusan sallar isha suka bar gidansu

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *