NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

           WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

MUN TSAYA 

kana ya Kara da wata Karyar cewa, -Sai kuma sana’ar da ya fara kwanan nan kuma ta zo masa da albarka, wato harkar sai da gidaje da filaye”’.Mahaifin husna ya dinga zura musu ~ albarka, sannan ya rufe maganar da cewa, In sha Allah goben nan zan dan bincikaka a unguwar, ina fatan babu laifi hakan?”. Cikin Karfin gwiwa Salmanu ya amsa, Ai in ba mu ji cewa zaka bincika din ba ne ma jikinmu zai yi sanyi Baba, mu ma binciken ai muka yi muka zo, bayan mun haKaKe mun zo gidan da aka karrama mutunci ake kuma ba shi hakkinsa”’.Mahaifin Husna ya Kara cika da jin dadi, fuskarsa ba ta Boye hakan ba ya cigaba da cewa,Na gode sosai, kuma wannan maganar , taka ta Kara tabbatar min cewa kun san abinda kuke”Salmanun ne ya sake tararsa da cewa, Mu ne da godiya Baba, sannan mu na – rokon cewa don Allah kar ka mantawa da bullawa unguwar tasu gobe, don Iyayenmu na shirin zuwa jibi’’. Zuciyar Mahaifin Husna daya ya ce,  wannan ai ba zai hana komai ba, su zo Allah ya sanya mana hannu a cikin nufin alkhairinmu”Daga nan suka datse tattaunawar, suka yi . KoKari ba wa Baba hasafi amma fur ya Ki karba. Sai kusan sallar isha suka bar gidansu

ZAMU TASHI 

Husna, a nan suka rabu biyu, Adamu ya tafi kai wa Alhaji kudi, Salmanu da Tanimu suka nufi gidan budurwar Tanimu mai suna Aisha.

*****

Kamar kullum Adamu ya silale daga gadonsu ya fice falo ya fara sallolinsa. Tun daga ranar da da salmanu ya tashe shi ya ce tuna masa. sallah zai yi, tun sannan bai Kara fashin sallar ba, _ kamar yadda Salmanun bai Kara saken tashin nasa ba, kullum zai tashe shi sai dai in ya tarar ya tashi su yi sallama su ajiye kawai. Salma ta kasa gamsuwa da yadda ranta ba ya son sallar daren ta Adamu, amma dai tana hana kanta rashin nutsuwar don kar Kazantar tata ta yi yawa, ga bin malamai

sannan ga hana mai ibada ibadarsa, to wai ma akan me sallar daren Adamu .zata dame ta? In hakkinta ne yana iya bata abinta farkon dare. Da ta cika bincikar zuciyarta sai ta gane_ cewa tana tsoron Adamu ya kai wa Allah – kukanta ya raba su, tun da ta dade da sanin_ Adamu in dai abu ya dame shi ko kuma yana . nemansa, akwai KoKarin addu’a. bayan wannna kuma sai ranta ke WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG raya mata kamar ma Kinta Adamun yake shiyasa yake raba kansa da ita ta hanyar share rabin dare a akan buzu, alhalin da rana ma in ya fice daga gidan tun sanyin safiya ba ta sake sanya shi a idonta sai duhun dare ya shigo. Yau ma a idonta ya tashi ya fice lokacin da aka kawo wuta Karfe uku daidai, ya yo alwa larsa _ya tayar da sallah zuciyarsa cike da nutsuwa da dayanta Allah, don karbar addu’arsa da yayi ya samar masa da son Husna.kuma ya bashi salamar aurenta. Tun kafin aurensa da Salma rabon da ya ji _ irin nutsuwar da yakeji a yau, tabbas yanayin da – yake ji yana masa kama da hango hanyar aljanna – a wangale tana jiran shigarsa, shi bayan wannan bai ga da wani abu da zai kwatantanta yadda yake jin shararriyar zuciyarsa mai tsananin jin farin ciki ba a yau. Daga farin cikin sai Husna su kadai suke ta faman shawagi a birnin zuciyarsa. Yana cikin salla Salmanu ya dinga kiransa a waya har ta katse, yana dab da sallame raka’arsa ta bryu Salmanun ya sake kira. * Salma na can ciki daki ta zaburo ta fito, dama tun tuni a tsarge take da me wannan wayar, – tana son ta san wanene me wannan wayar cikin
dare kuma me yake kiran Adamu ya fada masa? Yau da ta sami garabasar ba a kira wayar yana halin da zai iya amsawa ba ta yanke shawarar dagawa ta ji ma wanene. — – Amma kash! Tana fitowa Adamu ya janyo __wayar ya daga abarsa, kuma bai ko yi sallama ba kawai ya ce, . ~ “Kai na fa tashi Daga’can bangaren Salmanu na dariya yace,  “To wai meye na hasalar?”. Adamu ya amsa, . “Haushi nake ji, kai da Sallar farilla ma matsa maka na ke kana sauke hakKinta ba don yanzu da ka fara fahimta ta ba, wai kai zaka dinga tashina sallar dare?” Salmanu na dariya ya lce, “Ai dai an ce kar mu yi aiki da aikin Malam mu yi aiki da fadarsa ko? Na san Sallar daren zata yi maka amfani duniya da lahira, ‘ watakila nima ta silar tashin naka Ubangiji ya duba al’amarina ya shirye ni yayi min rahma…”. ‘ Adamu ya daga kai ya hango Salma tsaye tana yi masa kallon tsarguwa WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG hankalinta duk a tashe,sai kawai Adamu ya ji cikinsa yayi wani irin hargitsawa, gabadaya ya ji ransa bai masa . dadi ba. . Cikin karkarwar murya ya cewa Salmanu, Amin, kaga mu yi sallama kar ka tsare ni da surutu tsakar daren nan”, Salmanu bai fahimci komai ba a karkarwar muryar Adamu ya ce, To madalla, a roKa da ni don Allah”Bai jira cewar Adamu ba ma ya kashe wayar. Adamu ya kasa juyawa ya sake kallon Salma,.kawai sai ya ajiye wayar ya fara KoKarin tayar da sallah. .

Ita kanta Salma bakinta da zuciyarta karkarwa suke don shakkar abinda zai je ya dawo, idan ta fada wa Adamu abinda ya zo bakinta, har yanzu akwai shakkar Adamu a zuciyarta don ba ta gama gane kansa ba, a — saninta da shi mafadaci ne wanda kafin ka rufe baki daga yi masa batu ya mayar maka, to tun – bayan aurenta da shi ya canja, sai ta yi magana sau goma bai mayar mata amsa daya da fatar baki ba sai shiru sai gyada kai ko girgizawa.

Yanzu dai ta yi Kunan bakin. wake ta Kalubalance shi, ta dube shi cikin tsuke ido, “Adamu wai wa yake maka waya kullum cikin dare ne?”. Ya rasa da fuskar da zai juyo ya dube ta don tsoro, sai kawai ya dake muryasa a sanyaye ya amsa mata ba tare da ya juyo ya dube ta ba, “Wani abokinane” ‘“Abokinka?”. : Ta fada cikin kaushin murya da tsare gira, ~ Adamu dai ya sake ta maza ya amsa mata batare daya WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG dubetaba, ; “Abokina ne mana, baki yarda ba ne wai?”  Ta dan sassauta murya ganin shi bai dauki abin da zafi ba. “Amma abokinka sai tsakar dare zai kira – ka? Kusan kullum fa sai ya kira ka Yaya ~Adamu” “Baki yardabakenan”. Ya sake juriyar fada. Sa Salma ta rasa abinda zata ce, sai dai ta kada kai ta wuce tana sa wayarta a caji tana cewa,  “Gaskiya ni dai ba-na so ka sanar da shi ya daina kiranka a waya tsakar dare, wannan ma ai _ ba musulunci ba ne”. Adamu dai sai a zuci ya amsa, Kafirci ne”.
Yayin da a fili dai yayi KoKarin tayar da sallarsa ba tare da ya tanka ba. Ita kuma ta zaune wajen cajinta ta kunna wayar, amma ta kasa tashi tamkar tana jin in ta cigaba da zama Adamu zai sallame sallarsa ya tafi daki ya kwanta. Suna nan a haka har hudu ta kawo kai, Adamu na ta sallarsa Salma na zaman kare karofi ba rini ba matsa, illa a fakaice tana gadin Adamu. Hudu saura wayar Salma ta shiga ruri, a dan firgice ta daga wayar, sunan Antinta Sa’a da ta gani ya Kara rikita ta, a hargitse ta yafito Adamu, “Yaya Adamu ka ga Anti Sa’a ke kira na da tsakar daren nan, mun shiga uku me ya faru?”. . Daidai wannan lokacin niyyar Adamu ya kishingida bacci ko na minti ashrin ne kafin lokacin sallah ya cika, amma Salma na yi masa wannan maganar sai yayi kamar bai ji ba, da sauri ya mike ya tayar da sallah.  A firgice Salma ta kara waya a kunne babu ko sallama ta ce, -Anti Sa’a_ me ya faru, waye ba lafiya?”, Murya Kasa-Kasa Anti Sa’a ta ce, “Ke mai da hankalinki ki yi magana Kasa-kasa, idon Adamu biyu?”. Salma na jin haka da sauri ta doshi Www.bankinhausanovels.com.ng hanyar daki, sai da ta shiga ta turo Kofa sannan hankali a tashe ta amsa, “Na baro shi a falo, Anti me ya faru?”, Cikin azama Anti Sa’a ta ce, “Ya aka yi kika kashe wayarki tun safe? Ga wuta ta taso an rasa hanyar da za’a a ganki a dau hanyar magance ta”. – “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”. . Abinda Salma kawai ke iya maimaitawa ~kenan: . Anti Sa’a ta ce, Kin ga ba mu da lokacin da zamu bata,. meke faruwa tsakaninki da Adamu? Akwai wata ~ Baraka?” A tsorace Salma ta dinga kallon Kofar – shigowa falon tamkar tana shakkar in Adamun zai katse sallarsa ya zo ya ji me suke tattaunawa, sannan ba Karamin firgita ta yi da jin cewa wai ga wata baraka da bata san da ita ba ta bullo tsakaninta da Adamu wai har ma ita da take tare da shi ba ta san da matsalar ba sai dai ta ji a wani _ guri can da nisa. Gabanta na dukan uku-uku taceE “Baraka kuma Anti Sa’a? kawai dai cikin satin nan ya dan canja, walwalarsa da barin jikinsa ya ragu yana yawan zama cikin tunani,in_ kuma na dame shi da neman magana sai kawai ya tashi ya fara sallah, yanzun haka yana can yana salla..A dan tsorace Sa’a tace, _ “Kin yi amfani da maganin nan kuwa * daidai?”  “Nan da nan Salma taci laya, . “Wallahi Anti nayi…” Sa’a ta sake tare ta, “Har wannan na matsin da boka ya baki?”. – “Wallahi har shi Anti…“Kuma kin yi KoKarin kiyaye cin nama a lokacin da kike matsa maganin?” Salma ta dan yi dum! Sannan a sanyaye tace,  “Mantawar da na yi in tambaya har naman miya ba zanciba?”. . ‘ Cikin kaduwa Sa’atace,: -.. . “Kin ci kenan”. A tsorace Salma ta ce, “Bh wallahi naci naman miya Anti”. — – Cikin karaji Sa’atace, . . ‘ “Shikenan ai ga shi nan kwadayi ya sa kin ciyowa kanki kishiya”. A razane Salmatace, _ “Na shiga uku wacce irin kishiya Anti?” “Ba isasshen lokacin bayani, kawai dai _ lallai da safe ki zo mu koma wajen boka”. Sa’a bata jira cewar Salma ba ta kashe – wayar. Salma ta ji wasu manyan abubuwa masu ’ kama da WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG duniyar wata na son rakitowa su fada mata a zuciya da numfashi, ta yi nisa da hankalinta lokacin da take jiyo Adamu na bude Kofar gida zai tafi masallaci.

********

a Duk yadda Sa’a ta so ta yi dabarar hana mijinta su kai kudin auren Adamu gidansu Husna har su je su dawo daga wajen boka ta dabara abin ya faskara, ya nuna mata shi gaggawar cika umarnin Hajiya ne a gabansa, ya.ce mata, “Ban tanadi komai ba da zan kare kaina idan wani abu ya sami Adamu ta silar jinkirina _ ko fasa auren nan”Ta ce masa, “Ni ma ba nufina ba kenan Alhaji, wai ‘ kafin goben ko za mu iya shawo kansa kar ya tarkar wa kansa wannan nauyin da zai iya . wahalar da shi ko ya shafi iyalansa har wadanda zasu zo nan gaba”’, . Cikin gundura Alhaji yace, “Ki na da labarin cewa akan yarinyar nan Adamu ya Ki karatu don nace ba zan masa aure ba sai ya gama karatu? Yana fasa abubuwa muhimmai saboda ita kike tsammanin akan iyalan da bai gan su ba zai zabi ya rasa ta tsakanin yau da gobe?”.
Juya kai Sa’a kawai ta dinga yi ta kasa magana don takaici, ranta ba Karamin baci yake ba tamkar ita ce Salma. Alhaji da bai san dawan garin ba ya ci gaba da fadar abinda iyakar gaskiyarsa kenan. WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
Hajiya ma ta ce Adamu bai fara son yarinyar nan dan ya daina ba, ta san tarkacen abubuwan da yake iya fara so ya watsar, yarinyar ba ta ciki…” Sa’a ta kasa hadiye bacin ranta, “Kai da Hajiya wallahi kuke shagwaba Adamu, ku kuke taimaka masa yake samun duk abinda ya so samu ko da kuwa zai tafi da farin cikin mutane da yawa…Da hanzari ya kalle ta, ta shiga Bata rai tana hura hanci, ransa ya baci da abinda ta fada_ . amma babu yadda ya iya, sai ya tashi ya bar dakin yana ce mata, . “Ke kuma Allah yayi ki mai son tashin hankalin kai a abinda babu ruwanki, ta ina Adamu zai Bata ranki a nan?”’.
Da alama ba don ta amsa masa ba ya yi tambbayar ya fice tun kafin ya gama dire maganarsa
Wannan ya sanya ta dubi agogo da sauri wanda ya nuna Karfe goma da rabi, a hanzarce ta rarumo wayarta ta hau kiran Salma, “Wai ki yi ki fito mana ko har yanzu bai fita ba”. Cikin haki Salma ta amsa,
Na kusa Karasowa fa, shi ya fita tun kafin takwas”.
Bata yi mintuna sha biyar da ajiye wayar ba Salma ta Karaso, suka Kule can cikin daki tun – daga nan hankalin Salma ya Kara tashi, don ta tabbatar lallai lamarin babba ne.Bayan sun gaisa cikin murmushin yake Salma tace, Ban ga Alhaji ba, yau da wuri kenan shi ma ya fita”Kai tsaye Sa’a ta amsa,  “Eh, ya je kai kudin Auren Adamu, nan da dan lokaci ma zaki ga ya shigo, don ba nisa”.Zuciyar Salma ta kusa kwacewa ta Bare, amma dai ta yi Karfin halin tattaro ta cikin rashin azanci tana duban Sa’a,“Anti wanne Adamun wai? Sa’a ta san babu.abinda ke damun Salma sai tashin hankali. Don haka ta boye. tata damuwar ta amsa mata, “Adamunki, aure zai yi.zai auri budurwar da yake so, wadda ya bar karatu dominta, Hajiya da Alhaji sun yarda zasu aura masa ita don sunyi imanin bai fara sonta don ya daina ba”.Na shiga uku na lalace”. Cikin tausasawa Sa’a tace, “Ba ki shiga uku ba Salma, Aljanna kika shiga kika kasa fitowa. Ki bar su da ni suke maganar’
Gumi kawai Salma ke yarfewa yana Kara

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *