NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 5 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Babu irin haukan da bai lika mata ba ta taso babu nauyi kuma cikin tashin hankali. Babu waya a hannun Adamu, sannan zai iya shallake kwanakin bikin yadda har za’a iya aura masa Husna baya nan kamar yadda aka aura masa Salma ba ya nan. Hankalin Salma da Sa’a a matuKar tashe yake da wannan, babu irin shan kai da shan cikin da Sa’a ba ta yiwa Alhaji ba don ganin ya soke auren nan amma sai ya ce mata shi fa ba Karamin mutum bane, ba zai yiwu mutane na ganinsa da daraja yaje ya tarbuda ta Kasa saboda jita-jita ba. Har ya Kara da cewa, .
Jiyan nan da safe fa abokinsa ya zo ya same ni dangane da wajen da za’a sa Amaryar, yayi min bayanin ccwa Adamu ya bar Sallahun a umarci Salma ta kwashe shirginta daga wadannan empty din dakunan” Wannan ya sanya Salma da Sa’a suka sake bazama.gidan bokansu wanda nan take ya tabbatar musu lallai za’a daurawa Adamu aure, amma su sha kuruminsu a ranar da ya dawo zai saki matar.
Sannan ya Kara da basu wani magani da zasu saki
ZAMU TASHI
kunamu a dakin Husna ko da an yi katari Adamu yaki sakinta har ya nemi shiga dakinta ya kwana.
Wannan zuwa wajen bokan ma an yi katari sun gamu da Tanimu wanda yaje domin wani kostomansu da ya saci kudin gwamnati aka fara bincike akansa, shi ne ya garzayo wajensu don su binne maganar har lahira, yaci musu_ alwashin zai biya kudin aikin da Www.bankinhausanovels.com.ng kaso daya cikn uku na abinda ya sata wanda ya kama milyan uku da doriya don kudin da ya sata milyan goma ne. Tanimu ya karbo nasa sihirin ya fito yayi kacibis da Kunduba ta kira mai ruwa tana siya, kasancewar ya san ba tasan shi ba ya bashi damar . kallonta sama da Kasa, kuma.da yake shi ma shakiyyi ne, murya Kasa-Kasa yace, “Wani lokacin fa kina da gaskiya matar nan, in ba da asirin ba da kyar za a samu mai aurenki”. Yana cikin yi mata kallon
Kurillar ne ya hango Sa’a na nufowa wajenta, da sauri ya juya baya ya cigaba da tafiya. Don ya san Sa’a dai ta san shi, don sun je gidan tare da Salmanu da Adamu. Aka yi Sa’a bata ganshi ba har ya haye . Www.bankinhausanovels.com.ng mashin dinsa ya tafi. Lokacin da ta Karasa wajen Salma jikin Salma Sanyaye take nuna Kurar Tanimu data Bace tana ce mata, An ya ba wancan mutumin ne mai kai wa Adamu rahoton ganinmu a nan ba, ina tsaye jikina na ba ni kallon Kurillar da yake min har zuwa lokacin da ya ganki naga ya tafi yana sinKe fuska”Ita ma Sa’a jiknta a sanyaye tabi Kurar
Tanimu da kallo, Babu mamaki, amma dai na so in ga fuskar algungumi don in ga ko na san shi, ke ba ki san shi ba Muryar Salma na rawa tace, Ban kalle shi sosai ba, na fada miki jikinana ne ya ba ni yana kallona”Sa’a ta yafice ta,“Zo mu tafi zai ci ubansa ne, ranar da muka dawo wajen boka zamu fada masa matsalarmu da shi”
***********
. Salmanu ne ya cigaba da kula da Husna ta bangarorinsa biyu, bokanta kuma abokin Adamu a lokacin da bayanan.Ya jinjinawa amanar Husna da riKon cikinta, idan ya shiga rigar Salmanu ko da wasa bata taba nuna akwai matsala tsakaninta da Adamu ba, duk furucinta da labarinta akan sa na yabo ne da boye masa aibu Irin wannan kan sa tausayinta kasa tsayar da gudu a zuciyar Salmanu, don ya haki kance na son Adamu yayi asarar farin cikin rayuwa gaba daya, mace mai kyau kuma mai kirki mai so don ‘ Allah ba tare da jiran raddi ko ta halin Kaka ba.
’ Shi yake daukar duk wata dawainiyar kawo-kawo da ke wuyan Ango lokacin biki, a waje daya kuma a rigarsa ta boka shi ke kwantar wa da Husna hankali Www.bankinhausanovels.com.ng yana Karfafa mata gwiwa da cewa, komai zai wuce, Adamu zai zabe ta ya bar kowa a duniya, zai fifita ta akan ko wacce mace, sannan in wuya ta wuce zata ji dadin zama da Adamu. Husna ta sa wa kanta tawakkali da shirin fuskantar ko wanne irin Kalubale da zai zo daga Adamu, kafin auren ko bayansa, don haka damuwarta ta taKaita, walwalarta kuma ta Karu. Satin Adamu biyu da kwana biyu aka daura aurensa da Husna, ba wani bata lokaci ranar auren _ duk da ango ba ya nan aka wanke amaryarsa aka _ kawo masa gida.
Salmanu da Tanimu da wasu daga abokansu ne suka wuce gaba a komai suke maye gurbin salmanu, bayan shigowar Husna gidan kuma ba mai iya cigaba da maye gurbin nasa ba, daga kai Kawayenta gida ko wannensu ya kama gabansa. Aka bar ta da uwargidanta Salma dukkansu suka yi kwanan fargaba da kunci. Salma kamar ta hadiyi zuciya ta mutu take jin kanta, Allah ne kawai ya kai ranta wayewar gari ta tashi da numfashinta kuma bata tashi da rabin barin jiki ba. Ta san Adamu bai rabu da Salmanu ba, amma ba ta taba kawo har yanzu suna da shakuwar da har Salmanu zai iya shige masa gaba bisa lamarin aure ba, tabbas ta tabbatar Salmanu ne ya dade yana mata mahangurba ba ta sani ba, kuma bisa nasa taurin kan da jajircewar ne ma Adamu ya auri Husna, to ta ina zata bi ta toshe wannan tasirin nasa a rayuwar Adamu? Nemo wannan amsar ce ya cinye kusan dukkan daren Salma, ta dinga jin Kullaci iri-iri na Salmanu da Husna, da za a yi mata rangwame a
Lahira, kuma a duniyar a bata dama da babu abinda
zai hana ta kashe wadannan manyan makiyan nata.
A daren dai Husna da fargaba ta ishe ta, sai fitowa ta yi ta yi alwala ta fuskanci gabas cikin kuka Www.bankinhausanovels.com.ng
da kushu’! tare da sakankancewa babu wanda zai iya
yaye mata damuwarta ya kuma tserar mata da mutuncinta sai ubangiji, ta roke shi manyan
abubuwa, muhimman cikinsu Allah yaji Kan iyayenta, ya shirya tsakaninta da Admu ya kore duk wata fitina a zaman nasu ya bar su da juna har abada. .
Safiya ta yi amarya ta yi tsuru-tsuru, tana zura idon ta inda wata rahmar Ubangiji zata bullo mata, don dai jiya kwanan yunwa ta yi, da alama kuma yau ma yinin yunwar zata yi, don me? Don dai gaisuwar je-ki da halinki sun yi tsakaninta da Salma, tana
kallon kuma Salma na karakainar karin kumallo, amma da ta gama sai ta ji ta shiru a daki, alamar dai kowa tasa ta fisshe shi. Har wajen sha biyu tana cikin tunanin yadda zata yi, “Ya’yan cikinta na juyawa tana ba su hakuri da baKin ruwa.
Salmanu yayi zaton haka zata faru, Karfe goma sha daya da rabi ya yiwa gidan tsinke, daga soro ya makale ya fara gurza sallama. Salma na wanka daidai lokacin ta fara wasi-wasin wanene? Husna kuwa da ta yi wa muryarsa farin sani sai gashi cikin farin ciki da murnar zuwansa ta bankado labile ta fito, Salmanu shigo mana” Salma taji hantar cikinta ta yi masifar kadawa, ba ta Kaunar Salmanu ko kadan kamar yadda ta fahimci shima ba ya Kaunar tata, sannan cike take da shakkarsa bare ta sami tsinin yatsunta ta soka masa a ido ya san cewa ita ba kanwar lasawa bace.
Tana wanka ta dinga jiyo kawarsa daga tsakar gida yana hira da Husna wadda ya sanya ta kawo masa kujera tsakar gida ya zauna, suna ta hira har take ji a bakinsa cewa gobe Adamu zai dawo. Suna ta hira da Husna hira mai alamar sun saba ta jiyo Husna nace masa, “Yakamata ka nemi wani abu ka kawo min Www.bankinhausanovels.com.ng
wanda zai iya dauka na zuwa gobe da jibi har ya
dawo, ban ci abinci ba jiya da dare, yau ma ban karyaba”Salmanu yana sane da hakan zai iya faruwa kuma yaji haushi amma haka ya basar da maganar cikin dariya yace, “Allah sarki Adamu, in ya dawo ya sami wannan labarin na san zan ci naushi, duk son da yake min ya sha ci min alwashin da kiyi Kwarzane gara ni na mutu ya huta”.Husna dariya take sosai ta ce, “Wannan raha ce Salmanu, don Adamu ya sha sanar da ni kana daga cikin mutane hudu na farko _ masu muhimmanci a duniyarsa, in ban manta ba ya sanar min kai ne na hudu…”. – Salmanu ya mike yana tare ta,Kece ta farko ko ta biyu?” . Ita ma tana dariya ta amsa, a,a “Hajiya ce..Salmanu ya tare, .
To ke ce ta biyu, Alhaji na uku ni na hudu, amma dai wani lokacin ina fin kowa Karfin iko a kansa,na yardadawannan…”Dariya kawai Husna ta yi. .
Ya sa kai ya fita yana cewa‘“Bari na ga abinda zan iya”. . Ya sa kai ya fice. a, Husna ta rafka tagumi a wajen cikin tausayin kanta har sai da ta ji motsin bude Kofar Salma daga bandaki sannan ta yi sauri ta janye tagumin.Salma ta fito bukudum-bukudum da alamun fishi ta doshi dakinta, Husna ta bita da kallo tana ganin beken Adamunta da abinda ya gani a wannan “Yar sukubar matar yace yana so.
Babu kudi wajen Salmanu sai da ya je can kabuga ya fitar da kudi a ATM sannan ya dawo, wannan ne dalilin da ya sanya ya jima bai dawo ba, har Salma ta gaji da fushinta ta yi kwalliyarta sannan ta fito ta fara shirin girkin rana. _ – Ta hada markadenta ta ajiye Kofar kitchen _ kenan tana jiran almajirinta ya zo ya kai mata ta ji sallamar Salmanu, yayi har sau uku tana sharewa, sai ma ta kada kai ta doshi Www.bankinhausanovels.com.ng dakinta. Lokacin Husna ta koma daki, tana tsaye jikin windo tana leken Salma na zungura baki idan Salmanu ya kwado sallama, har sai da Salman ta gaji ta shige daki sannan cikin mamakin rashin jituwar da ke tsakanin Salmanu da Salma tayo waje tana amsa Sallamarsa tare da yi masa izinin shigowa.
Ya shigo mata da katan din Indomi da na kifin gwangwani tare da kiret din kwai, sannan sai kayan shayi tare da su maggi da Karamar robar mai.Ya sa hannu a aljihu ya ciro dubu uku ya bata,
“Karbi kiyi maneji da wannan zuwa dawowar Adamu”.
Ta Ki karbar kudin,“Ba zan karbi kudi ba Salmanu, akwai kudi a wajena dama dan aike ne babu, sannan ba na son gulma mutan anguwa daga kawo ni yau na fara fita cefane.Salmanu ya mayar da kudinsa aljihu yana cewa, Eh da gaskiyarki, ai wadannan kayan duk masu saukin dafawa ne, ai kina da murhun dafawar ko?”.Ta ce,Eh babu matsala, ina da Gas…”.
Ya tare ta, , “Madalla, an huta”. Ya shiga nazarin kitchen din guda daya kacal, kasancewar yana bude, da ya lura sai ya fahimci Salma ta mamaye kitchen din, ya lura babu komai sabo da yayi kama da na amarya ne, ya mai do da ” ganinsa ga Husna,’ ,
Wai tsaya, kina ma da kitchen din?”. Murmushi kawai tayi tana girgiza kai. Ya sake bin gidan da kallo yana nazarin wani dan fili dake kusa da kitchen din Salma, ya zabura yace, – Ai kuwa zaki yi shi yanzun nan, bar girkin yanzu zan je na kawo miki Take away, zan zo kuma da ma’aikata da kwano a yau din nan su gina miki kitchen a wajen nan . Yana taka wajen da Kafarsa.Husna ta rangwada kai bata ce komai ba.Salma a daki ta zuciyo da jin bai kamata ta Www.bankinhausanovels.com.ng bar Salmanu ya cigaba da cin kashi a kanta ba, don me zaizo gidanta yana mata iko? Har da wani zai gina wa wata banza kitchen?
Ba ta cikin hayyacinta ta ganta a waje, tana ta faman huci ta tsaya a Kofar daki tana yi wa Salmanu kallon fusata.Ban fa gane ba, wai kai bisa wanne ikon zaka zo ka canja mana tsarin gida? Kai a su wa da zaka wani zo ka gina mana wani kitchen? Na ga ko shi Adamun ba shi da hurumin canjawa gidan nan tsari ba tare da yardar mai shi ba tunda ba nasa ba ne…”
Salmanu ciki yake.da haushi, da Salma namiji ce babu abinda zai hana shi shake ta, amma idon Husna ya sanya shi murmushi ya ce,
“To wai ke nan yabon Adamu kika yi ko zaginsa kika yi da kike tallata shi da cewa ba gidansa ba ne?… to bari naje na tambayo Alhaji mai gida, bisa alfarmarki da darajarki ya ba Adamu gidan ko kuma bisa darajar Adamu da tasa alfarmar?”. Ta Kara fusata, .“Anji, amma wallahi babu mai yi mana wani kitchen a gida”.
Ya sake wani murmushin,“Ki daina wani rantsewa, don ko Adamu bai isa ya dakatar dani ba bare wata shakatafi’Husna ta dan daga masa hannu, cikin mamaki da daureawar kai, cikin kwantar da murya ta ce, Salmanu ban da cin fuska, ka yi mata uzuri ka mutunta dalilin abokinka”. Salmanu yayi shiru, Salma kuma da ta cika ta fashe, . .
“Ban da ma mutum yana da rashin zuciya, ba nace kar naga Kafarka a gidana ba, uban me ka zo ” _Salmanu zai yi magana Husna ta sake daga masa hannu tana jinjina kai alamar roKo, Salmanu ya – sake girgijewa ya hadiye.Salma ta sake kwaso rantsuwa, Na rantse da Allah ka zo gina mana wani Www.bankinhausanovels.com.ng kitchen sai na debo maka ‘yan sanda…” Ai kafin ta rufe baki Salmanu ya mike, “Kin san Allah ki tafi ki debo min barikin soji kawai, na rantse miki da Allah mutuwa ce kawai zata dakatar da ni”.Bai saurare ta ba ita da Husna da ke faman kiransa cikin yanayin damuwa ya doshi hanyar fita, bai tsaya a nan ba sai da ya sa Kafarsa yayi fatali da – kayan miyan Salma da ke bakin kitchen ya. take bokitin kamar wani mahaukaci ya fice daga gidan. Salma ta dan razana. Amma bakinta bai fasa_dure-duren zagi ba. Husna tuni ta tashi ta gudu dakinta tana mamakin wannan_ tsattsamar dangantaka tsakanin Salmanu mutumin kirki da matar Adamu Abinda ya fi daure mata kai shi ne, Salma bata yi kama da mara kunya ba, Karfi da yaji take matsawa kanta rashin kunyar, kawai dalilin kishi, har take jin zata iya taka ta ta kwana lafiya, ita da ta taso da wasu kishiyoyin wato matan ubata, dalilinsu babu irin kalar rashin kunyar da bata koya ba. Ta kada kai bayan Adamu ya zo ranta, a fili ta ce, Babu komai, zata mutu tana cin arziKin Adamu”. Salma ta shiga daki cikin tashin hankali da kuka, barazana kawai tayi Salmanu ta manta dan ganye ne, kisa ma ya taba gwada aikatawa saboda haka shi ba baKon kotu da dansanda ba ne da zata yi masa barazana dasu. Da wanne Karfin gwiwar zata kira ‘yan sandan? Waye me tsaya mata? Jiki na bari ta janyo waya ta kira Sa’a ta kwashe mata labari, Sa’a tafi ta saiti, iyakarta durawa Salmanu zagi ta kuma ce,“Kar ki yi wani gigin kai shi caji Ofis ki janyo
mana fushin Alhaji, na san shi ma cewa zai yi abinda ya dace kenan a gina mata nata kitchen din, ki bar
kula shi kawai ki jira zuwan Adamu ya sallame ta _ Www.bankinhausanovels.com.ng mu huta in yaso shi sai yaje ya aure ta”Salma na kuka tace, “*Amma a gabanta naci alwashi na rantse fa Anti, zata dauke ni mai kuri.. Sa’a ta tare ta a fusace,“To dan kar ta dauke ki mai kuri, sai ki saka zare tsakaninki da dandaba ki janyo ya farde miki – ciki a gabanta, ko kuma maganar ta zo kunne Alhaji ya zo har gidan ya ci mutuncinki a gabanta ya kuma goyi bayan a gina mata kitchen din…Kawai sai Salma ta sake rafshewa da kuka. Salma na ji tana gani Salmanu ya zo aka ginawa Husna kitchen da sabon kwanon rufi, aka yi ‘mata kantoci, bai bar gidan ba sai dab da magariba a gaban idonsa Husna ta shirya kitchen dinta sannan , yayi mata sallama ya tafi. Amma: kafin fitarsa sai da ya yar wa Salma magana a tsakar gida, ‘Idan mutum ya isa’ mai hukunci ina jiran . sarKar da zata daure ni ta kai Bamuda triangle ta jefa ni a hadiye”
*************
Washe gari da safe Salmanu ya kira Husna a sigar bokanta,Yau mijinki zai dawo”
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE