NAYI GUDUN GARA CHAPTER 13

NAYI GUDUN GARA 
CHAPTER 13
Koda Ramadan ya dawo ba ta nuna komai ba, saboda taJl hudubar mahalflyarta. Dan yinin rana, bakinta dauke ya yini da ambaton Allah. Saboda bata san shaidan ya nemi kawo mata nakasu, cikin ikon Allah kuwa sai zuciyar tata ta sanyaya, tana jin sanyi aranta, tanajin tsoron Allah na dada shigarta. Sai ta ji tana ma farinciki da auren. Duk wanda ya sanya Allah a lamuransa to saiya ga ribar hakan. Allah yana san masu hakuri. Duk wanda kuwa ya ke da hakuri to tabbas Zaku same shi da mik awa Allah lamuransa Da murmushi ta tare shi bayan dawowarsa. Sanye take ciki material pink me dan sharashara, anyi mata shi daidai jikinta, ya d’
au fatarta ainun!sai kamshin humra take mai matukar dadi. 
Da yake yana zuwa sama yayi wanka,ya sakko dan ya kwashi girki. Sai kokarin hada mai abinci take tana sakin dan murmushi. 
“Angon gobe ya gajiyan office habibi? Ta fada tare da zama gefensa. Kallonta kawai yake da mamaki dauke a zuciyarsa. 
“Ladifa ashe! har yanzu ni dan gatanki ne? amma naji fa dadin ganin ki haka, dama nasan babyna akwai kaifin hankali da fahimta. Wallahi na dauka zanzo na tararda kwandunan rashin kirki.” Ya fada tare da riko hannunta ya shiga murzarsu daddadan kamshinta na ta dukan hancinsa.
“Allah yayi miki albarka uwargidana ran gida,tabbas kwarin gwiwarki ya birgeni.” “hmmm! ci dai abincin zauji karya huce. So naga kwana biyu ba sosai kake cin abinci ba, saboda zumudin zuwan amarsu,gwanda amaryanmu ta ganka a nurmure.” Hancinta yadanja “kin ganki ko, ke kodan kishina ma bakya yi.” Sai ta saki murmushi. Kishi ai dole ne, soyayya da zan nuna maka itace na baka kwarin gwiwa. Saboda ina sonka dole naso abinda kake da mura din yi, koda kuwa abin ba mai dadi bane.” Sakin cokalin yayi ya kalleta yar albarka.Thank you. God bless you..Haka ake san mace ta gari.” Murmushi ta yi zuciyarta fess! Ko ba komai tasan albarkar mijinta za ta bita, koba komai ta sa yaji farin-ciki har zuciyarsa. Wanda tana da yak’in cewa Allah zai bata lada.Domin abinda ake ta bida kullum, amma yau gashi ta samu lallae ta gasgata maganar manya. Duk da cewar tanajin kishin amma hakan take dannewa. 
Nan sukai ta hira yana cin abincin har ya gama. 
Washegari da ya ke weekend ne bayan gama breakfast d’insu, ramadan ya kalleta, tana zaune gefensa tana mai tausa. “Lad’ifa, tabbas acikin mata ke ta daban ce ,wallahi idan wasu ne, wallahi k’arya nake na sha ruwa lafia, akwai wani abokina, da zai k’ara aure wallahi matar haka ta zame mai kamar dodo, karya ya ke ya shiga gida kalau, abinci kam sai dai yaje restaurent, duk wai akan zai kara aure duk ya rame.” 
Toya zami bayan Allah ya halatta mana.” “Hmm! tace ni dai zauji fatana kai mana adalci, kar amarya ta sanya ka manta dani.” 
“Baby ba zaki gane bane yanzu, ni dai zo muje mu kwanta. Ya fada tare da Kashe mata ido daya. Sai ta juyar kai, duk da cewar daurewa kawai take akomai idan ta kalleshi, takanji haushi, 
amma sai ta mike sukai sama. 
Karfe sha-biyu na rana, wayar ladifa tai kara, tana kwance ta tashi ta dauka, sunan salma ne akai. “Lalle Lad’ifa, sannu ashe! abinda Ramadan ya jajibgo kenan! wallahi sai jiya abdallah ke gayan. Wallahi ji nake kamarni za aiwa, jiya yini nayi yijikina asanyaye.” 
“Hmm kawai ladifa tace, ta kara da cewar. To ya za ai kinsan mazan nan ba,a saka su balle a hana su, har idan suka so abu.Hakuri ne kawai magani. 
Salma tace “taf wallahi na ga hakurin ki, yanda nake da kishin nan, ai ba zan iya ba, amma ta wani bangaren dai kin burgeni wallahi, dan kin yi abinda ire-irenmu ba zamu iya ba. Allah dai ya sanya ta gari ce ya baku zaman lafiya.” 
“Ameen lad’ifar ta fad’a.” Sai munzo dannar kirji.” Salmar ta fad’a tana dariya. Dariyar itama lad’ifar tare ta kashe wayar tana tunani. Wayarta ce ta kuma k’ara, ta daga, sunan babanta ne ajiki da sauri ta d’auka ta dan 
sunkwi da kai, tace “Baba ina wuni?.” Ya amsa yana “lad’ifa sai da hakuri kinji, karin aure ba illa ba ne, ta wani fuskar ma karin arzikine. Musamman in auren yazo da alkairai. Abinda zan jaddada miki ki kara hakuri, shi aure na Allah ne kinji. Bana son tashin hankali, duk dana sanki me hakuri ce ban lamince cutar da ‘yar uwarki ba, duk da nasan tarbiyarki a ingance take, to amma zamani a gurbace yake, dole sai an dada tunatar miki, banda daukar hud‘
ubar kawaye wajen kuntatawa abokiyar zama, komai ya shige miki duhu to ki kai kukanki ga rabbu, shine majibincin dukkanin komai kinji ‘yata. ALLAH yayi miki albarka. 
Tace amin baba. Ya kara da cewa, “Gobe su hassan za su zo, kayan dakinki za a canja miki, za a fidda nakin asayar acika asai miki wanda yafi kyau, ni dai fatana ki zauna lafiya da mijinki da abokiyar zamanki dan nan shine rufin asirinki.Dan haka ki sanarda maigidan naki. Haka ya yi tai mata nasiha mai ratsa zuciya, har taji hawaye na zuba, ta ji bata da sauran wani kalubale, ta ji duniyar ma ba kamai bace har idan ka zama mai da,a ga mahaliccinka. Ya kashe wayar. 
Godiya tai ta yiwa wa Allah da ya bata iyaye masu hangen nesa. 
Ita kanta tanajin dad’in yanayin da take ciki, babu abinda ya kai hakuri wahala, sai dai yana dadi har idan kajure mai. sai ka zauna lafia, babu wani abinda zai dameka, har idan ka mikawa Allah lamuranka. Kallon kanta tayi dan da ace ta sanyawa ranta damuwa, da tuni ta kojale ta rame. domin babu abinda ke ruguza jikin d’an adam da wuri, irin sanya abu arai da tunani da rashin kwanciyar hankali. Washegari kuwa su hassan suka zo suka cire tsohon kayan dakin nata Dan ta rigada ta gayawa Ramadan. 
“Ni kam laila banga amfanin sanya kayan matan nan agaba kina banka ba, wani ma bai dace ki shashi a yanzu ba, ki na matsayin budurwa ba.” “Ke gidan kishiya zan shiga. Gwanda na shiga da karfi na.” 
Anty hasiya yayarta, tace “wannan ba wayo bane, ai yanzu budurwa ta sha maganin sanyi shine gatanta, domin ita komai nata sabo ne, muddin tasan an saka aurenta. Shi zaki dage da sha, amma kina dirkar kayan mata. Ya kamata dai ki hakura da wadannannan, ki tasamma shan maganin sanyi Sara tace “gaya mata dai wallahi koni tun yanzu din nan da kika ganni ina shan maganin sanyi, saboda nai wa kaina gata tunkan bikina ma yazo, gwanda nai ta shan maganin sanyin ina shan fruit , idan naje gidan na sha na matan. Saboda wallahi sosai sanyi yanzu ke illata mata, dan wata sai tayi auren kuma suzo ana fuskantar matsala da oga, to watakil tana da sanyi yaci jikinta, kin ga zai iya ƙafar mata da ni’ima ma, domin babu macen da bata da sanyi, kuma sau da dama mace bata ganewa sai tayi aure. 
“Kyaleta dai, bikin khadijan anty ai taga yanda akai mata. “Ni dai ku kyaleni bani da wani sanyi.” 
“To ai shi kenan kanki. Cewar anty ta mike ta bar dakin. 
Sara tace “yanzu ni ki gama ki tashi muje mu amso kayan.” 
“To bari naiwa murabus waya, Sara ta kalleta “wai ke haryanzu ba zaki rabu da shi ba haba
Kallonta tai tana tauna cewgum, k’as! K’as, “an gaya miki zan sake shi a satin nan ne? shi ka daine ban saka ba a duk samarina, dan duk sauran na sallamesu, shi saboda ina so yayi hidimar kaini wurarene, shi,isa saboda kinsanni dajamaa.” Rike baki sara tayi “wallahi ni dai shawarata ki sallame shi, wai ma kin gaya mai za kiyi aure?.” “Har yanzu bai sani ba.” “Kai laila babu kyau fa, wannan ai yaudara ce.” “Ya ga zai iya, shi fa murabus dan wahala ne, wai shi bai yarda ba zai aureni,ba bai san yarfa shi nake ba, ba irin hannunka mai sandan da ban mai ba amma ya kasa ganewa.” 
“Hmm adai hankalta.” Dariya tai tace “Wanda yace zai iya had’iyar gatari ai sai ka sakar mai kota.” Hmmm ni dai tashi. Allah ya shiryeki babu dai kyau.” Tashi tai ta mike ta shige wanka dan mura ya kusa zuwa.
Ramadan ne zaune, lad’ifa na gefe yana mata bayani. “Ina so kinga falon nan na kasa ya zamo public, ke za ki koma sama, kujerun nan naki za a barsu a kasan nan su zama na kowa da kowa, ni kuma zan sayo miki sababbi sai a sanya miki a saman.” ‘ Daga kai tai alamar tana jinsa, sannan wancen babban dakin na kasan, zai zama na laila. Kusa da shi dama akwai wani sitting room babba ne sosai, to kinsan kofarsa awaje take, to za a maida matashi falo, sai A maido da kofarsa ta nan. Ta zamana kofar na cikin falon nan. Na yi hakan ne saboda ganin hakan zai fl.” “Amma ya kika ce?.” “Ni karn zauji dama kowa ya zauna gidansa da ban, misali ka kama mata haya.” Kallonta yayi yace “Aa bana son raba gida, ni kawai hakan za ai, yanzu ki gaya min duk abinda kike so kinji.” 
“Ai ka gama komai, kai da za ka sanya min sabbin kujeru.” 
Murmushi yayi yace “kin cancanci fin haka, domin kin bani hadin kai wanda ba kowacce mace za ta iya ba..” Kallonsa tai tare da yin yake “to in ban bawa mijina kwarin gwiwa ba, wa zan bawa, dole sai da hakan ai, kodan kwanciyar hankalinka mijin laila.” 
Cike dajin dad’in sunan. Ya ce “mijin ladifa da laila dai.” Sai ta murmusa. Tafiya tai tafiya, lokacin biki na ta kusantowa, dan yanzu saura sati biyu a gudanar da biki. Gyaran gida tukuru Ramadan keyi, yayinda abangaren ladifa ke dada ba shi kwarin gwiwa, ba karamin daraja ta samu awajen Ramadan ba, dan har dan shawara yake nema wajenta game da had’a lefe, takance ya sanya kaza ya sanya kaza, takance ya kara wancen, babu wancen. 
lta kuwa da yace zai mata na fadar kishiya, ta ce ta yafe, dan hidiman tayi mai yawa, dan har yanzu tana da kayan lefenta da bama ta dinka su ba. Sai ya dauki 100k ya bata, ta karb’a tai godiya. 
Abangaren samanta sosai ta shirya falonta da sabbin kujerunta.Wanda su kafi asalin nata kyau da tsada da tsaruwa. Ga labulaye da sauran duk kayan da yasai mata, lta kanta wannan auren gobaran titi
 zata ce ya zame mata kawai, ga sabon funitures da abbanta yayi mata, yau da ta sanya tsiya da sai dai ta zama ‘yar kallo. Tana zaune a sabon falonta na sama tana kallo, taji sallamar ya karima ce ta shiga falon rike da hannun ‘yarta, yarinyar ‘yar shekara biyar. Da murna lad’ifa tai mata sannu da zuwa. “Masha Allah ga wuri yayi kyau, ke kam wannnan aure da gata yazo miki.” Hmm kawai tace. Tana ma husna magana. Kayayyaki Ya karima ta hau fito dasu daga jaka. Ga sakon hajiya.” Ladifa ta kalleta “na meye yaya.” “Sai kinji bayani.” Ta zaro wata madaidaiciyar roba wannan na k’
arin girman kirji ne.” Hade rai Iadifa tai. “Nifa gaskiya yaya ba zan sha wani salala ba,jibi wancen da mukai ban kara da komai ba, kema fa kin sani.” Yaya zaki tunda oga naso.” Yanzu fa kishiya za ai miki, kina ganin tunda ya kwallafa ransa akan irinsu, zai auro wadda bata dasu ne? to ki dage fa atoh.” “Yaya nifa abu daya na duba, saboda Allah hakafa Allah yaso ya ganni, to akanne zan damu kaina. Allah ya gani na gaji, nayi iya yina kawai na barshi.” “To naji, amma dai kisha ko ba dan karin komai ba, shi abu ai dace ne in wadancan ba 
su karbeki ba, sai ki ga wannan yayi, kinga fa abinda akai da su shine: shinkafa ta tuwo,madara sai garin alkama, garin hulba,garin aya, garin plaintain,saijar gyada fa aka had’asu aka nuka. 
Dama shi zaki nayi, in yayi kamar kunu, saiki sanya madara ta ruwa ki sha. Ke ko kirjinki bai karu ba, to za suyi miki amfani su tada miki da komada.” Dariya lad’ifa ta sanya “ya meye komada kuma?.” 
Tsaki tai “ke fa dama in abu bai miki ba, haka kike sai ki wani rikice, ina nufi ki dada cikowa.” 
To zan yi” Yar takarda ta zaro “wannan jerin sunayen na ciki, su kuma indai kikajuri had’in su to zakiyi dumur mur kiyi kyau, kuma ba wai iyakiba zakiyu ba, ahhahh zaki murje komai naki su tasa, 
“Kinga ki samu wake, hanta, kifi sadin, tattasai, alayyahu, albasa, citta, man zogale da su maggi,jika waken zaki sa amarkado miki shi harda dusarsa, ki hada da hanta da albasa, ki sanya man zogale da su maggi, ki kulla aleda kiyi alala da shi, kwanaki kalilan, in zaki dimanci yi, to zaki ciko kiyi kumari, komai naki ya tasa, mai gida yaga kin mirje kin yi dumui -dumiu dake babu rama ko kashin wiya.” “Kai anty.Allah k0 mazan nan fa sai da hakan, balle ke mijinki mai ido atsakar ka.“”yaya wallahi maza ‘yan gata ne, yanzu dukdan ya samu nishadi . “Zauna nan,ke da za ai wa kishiya, duk ba dan hakan ya ke zumudin karin auren ba.” “Sai kuma me?.” Wadannan kuma su haddiyar zuma ne masu kyau, irin wadda kika sha rannan agidana, ai dai kinsan yanda take, sai kuma kayan marmari da zaki na sha sosai, Ki samu zogale ki markad’a shi ki zuba madara da zuma ki sha.Sannan zaki iya samun kankana ki bare samanta ki zuba kaninfari,madara da nikakken dabino ki hada ki juya su tsumu kisha. Ko ki samu dabino shi kad’ai tsura, ki jik’a shi ki dama ki shanye. Ko irin da yamma haka ki samu lipton ki jik’a shi sai yayi bak’i sai ki cire, ki fasa kwai d’aya akai ki kad’a ki shanye. Sannan ki na samun zogale d’anye bayan kin wanke shi tas! sai ki fasa kwai akansa, ki yanka manya -manyan tumatir a kai ki soya sama -sama da man zaitun hmmm! Ko su kika kama wallahi ba magana, ina fatan duk sun zauna akanki?.” “Ai ba kiga recording nake ba ma.” “Sannan akwai hadin kaza da zan miki, hmm ba magana,wallahi sai kin gode mini, ko ita kadai kika ci babu ke babu wani cushecushen kayan tarkace, dan zai ciko da ke, ba sai kinyi wani matse matse ba.Rufe ido lad’ifa tai, “kai ya ni fa kunyar ki nake.” “Zan mareki fa, ina wata kunya, idan ban miki ba, wa zai miki. Kinga husna ma tai baccinta nasan za ki ce kodan ita.Dan ban fara magana ba ma saida tai bacci.” Hadin kazar ke zaki yi min?.” “Eh zan yo a kawo miki.Sai kuma gyaran jiki da zaki fara yau.” “Yau kuma yaya”Yo me za ajira, ai gwanda amarya ta shigo ta ganki a kasaitacciya haba!. In kana da kyau ai ka kara da wanka. Yawwa kayan gyaran jikin ba mai wani wahala zamuyiba, kisamu lalle cokali daya, kwai daya,gishiri’ rabin cakali, kurkur cokali d’aya ki cakuda gaba: daya ki na shafawa da daddare idan za ki kwanta da safe ki murje jikinki da dilkar da kikajika, ki yi wanka. 
Ina so ki fara daga yau, dan duk kina dasu kurkur ne da dilka nasan zaki rasa, to ga shi nan na taho miki dasu. 
Sannan ga wannan turaren na ruwa ne dana gari, ki samu lalle ki zuba a ruwan wankanki, 
sai yayi ja! sai ki tace garin lallen, sai ki tsiyaya wannan turaren kadan,in zakiyi wankan. 
In kika fito kuma, sai ki turarajikinki da wannna turaren, za kiji kamshi ya manne ajikinki, karfa ki yi sanya.” “Kai yaya da kinsan da irin wannan haka, shine baki min ba, sai da za ai min amarya.” Ta fad’a cike da shagwaba. “Ke dallah! komai ai silarsa ke zuwa, yanzun kamawa tayi ne, saboda bana so a wulakantamin kanwa, kika san wacce zai auro, idan yaji abinda bai tabaji awajenki ba, ya samu awajenta ai sunanki sorry. Gwanda ko yaya ne kema ki bude wuta.” 
Dariya ta sanya “kawai ni dai Allah ya sanya sun kare hakan.” 
“Summa kare, kinga duk hajiya ce ta bada kudi aka sayo, itace ma tace duk abinda ya kamata in doraki akan hanya mai kyau” 
Rungume karimar tayi tace wallahi ina sonki yayata nagode Allah ya bar zumunci. Ameen ta fada tana mai cewa zata aiko mata da hadin kazar kan amaryya ta gama kwanakinta sannan sukai sallama ta tafi. ’ 
Ana jibi daurin aure, laila da sara nata kiciniyar rabon kati,ko,ina da nikaf take yawo. Suna tsaye a falon gidansu sara, ta kalleta “wai ni laila in tambayeki kin sallami murabus ne? Naga kojiya shi ya kaimu karbo d’inki.” Tabe baki tai “tun yaushe kuma,ai tun wajen sati daya nace masa biki zamuyi a maiduguri, nace mai sai nayi wata acan.Jiyan nan ya kawon dubu hamsin wai na anko ne? Wai kudin ma ranta yayi wurin kawunsa.” 
Rike baki sara tai “amma wallahi bai kamata ba, yaci ace kindai ce aure za kiyi.” “Wallahi kunyarsa nakeji, kinga dai duk cikin samarina shine bai da kudi k0, amma wallahi akwai karfin hali, ahakan karki ga yanda yake min hidima, shi,isa nakejin kunya na fada mai zan aure bansan me zai dauka ba.” Ni sai naga yafi ki gaya mai akan yaji daga baya, sai ya dauka dama yaudararsa kike.” “Shima ai yasan wasa ya ke,ni dinnan ai matar manya ce.” 
“Ai shikenan, sara ta fada suka ci gaba da harkokinsu.. 
Misalin takwas na dare ramadan ya shiga gidan, ladifa ta tarye shi cikin farin ciki, tana tsokanarsa angon jibi, murmushi yayi  ya kalleta ganin yanda fuskarta ke shining saboda tsabar gyara, in ya kalleta sai yaga ta kara kyau, fatarta ta dada smooth, daman kumatunta sai kyalli yake,ga lips dinta sai kyallin whitelips ya ke. Sosai yaga ta canja mai amma ya kasa fada. 
ita kanta tasan ta canja tunda ta fara gyaran da ya karima ta gaya mata, don taci sa a saboda zumud’in zuwan amarya, sam baya nemanta ma yanzu, shi,isa take shafejikinta da daddare da kayan dilka hankali kwance, ga turaren da karimar ta kawo ya fara zama ajikinta, ga kayan karin niema da take sha,da alalan da take yawaitawa ita kanta tasan tadan ciko kadan. 
Hmm yace “ladifa, kema fa kamar amaryar, na gafa duk kin canja, meye sirrin.” Dariya tayi kawai, ” me amarya har ya wani zuzuta uwargida, kai dai ai a jirayi amarya.” 
Babbar ledar da ya shigo da ita ya bude, ya zaro kayane kala biyar aciki,shadda ya zaro me kyau ready made,” ga kayanki.” 
Ta d’auka tana dubawa, shaddar anyi aikin pent work ajiki adon ja, tun daga sama har kasa, yayi kyau ga stone manya tsalli tsalli ajikin fulawar pent work din. Nan ya kuma zaro wata shaddar sky blue, ita kuma an yi mata bubana da surfani kadan agefe yayi kyau shima, sai wani dankareren less copee colour, an mata half gown da zani, hannu irin me fad’in bakin nan ne, an saka wani yadi silk
milk me kyalli ga stone copee birjik ajiki, sai gaban rigar ma, sai material black da atampha super exlusive, duk kuma adinke suke, sai mayafan kowanne kaya da takalimi guda biyu. 
“Wannan kayan fa nawanene?.” “Na kine kici biki.” “Au! Zan yi taro?.” “Haba dai ai na dauka su salma, da makotanki duk za su zo, ya karima,ga kuma lokacin kawo amarya duk sai ki sanya.” 
Jitai yayi masifar burgeta, sosai taji sonsa ya kuma ratsata, duk da cewa inta kalleshi tasan kishiya zai mata, takan ji haushi kadan sai ta danne. Cikin shauki ta fada jikinsa,‘ ‘nagoda habiby. Allah ya kara budi, ” ta fada tana mai shafar sumar kansa, ta kara da cewa “bansan wane irin godiya zan maka ba, ada na dauka a yayinda ka bijiron da karin aurenka za ka sanya ni a kwandon shara, sai kuma naga akasin haka nagode.” 
Janyota yayi ta kuma shiga jikinsa, ya shiga sinsinarta tare da kai bakinsa gefen wuyanta,dan kamshinta na dagulashi, tun bayan data fara gyaranjiki, yace “ai dole ne, nima kin farantamin, ban taba zatan zaki ba ni goyon baya ba kan aurena ba, duk da nasan ki da kishi, haka kike dannewa dan farantamin, thank you lad’ifata.Ya fad’a tare da juyo da fuskarta ya hade bakinsu waje d’aya ya shiga duniyarta.Atare suka saki ajiyar zuciya. Sun dad’e a haka ya saketa idonta alumshe tana jin zuciyarta na lugude, yace “ya dai?.” Ta dan kalleshi da alamar shagwaba “ni dai baruwana, kafa fara shiga hurumin amarya.” Dada mannata ya yi jikinsa waya fad’a miki haka?!’ Dan dukan wasa ta kaimai, “na sani kawai wasa nake, amma gwanda na barwa amarya huruminta tun yanzu.”Allah ko?.” Tace “Eh!Sai ya sanya dariya “naki wayon.” Ya fada tare da kuma hade bakinsu.Dan wani irin dadi ke kwasarsa in yana tsotsa. 
Washegari akai wa laila jere awajenta da Ramadan ya gyara, masha Allah komai daidai dan har karamin kitchen yayi mata, dan dai bai kai wanda na kayan ladifa ke ciki girma ba, sabida gudun hatsaniya, dan ko da ya gayawa lailan ba kitchen sai dai suna amfani da d’aya tace atafau! sai dai yasan yanda zai ya fitar mata da nata kitchen din.’yan jeren nata santin gidan da ladifar, saboda karamcin da tai musu na girki mai dadi, da nuna kulawa. Washegari ya karima ta zo suka tafi wajen kunshi, inda akayi yima lad’ifaja da baki tare da gyaran kai, aka dada kuma getta da gyaranjikin, kamar ka sace ta ka gudu, sai wajen hudu su ka koma gida. 
Washegarin daurin aure ita ta hada mai kayan da zai sanya, ta bashi kulawa sosai ya fito a ango, wanda sai karfe goma za ai daurin auren, ita ma alokacin tai wanka ta sanya shaddarta ta kafa d’aurinta, tayi masifar kyau, wani sai itace amaryar. 
Shi kansa kansa Ramadan idonsa ya kasa barin kallonta, sai ya dau wayarsa ya janyota jikinsa ya daukesu picture, yace “wanka yayi Ladifa sai na dawo.” Yana fita ta zauna a kan kujera ta saki kuka mai tsuma zuciya, shike nan yau za a daura, babu abinda ke bata haushi sai rawar kan da yake zai kara aure, dan ma dai yana ba ta 
kulawa ad’an  nan da bata san ina zata sanya ranta ba. 
 sallamar maman rauda makociyarta tasa ta bude idon. Maman Rauda tace wannan kyau haka? Wallahi kin burgeni da kika nuna babu komai, haka ake san mace da ta san kanta. Ba kiga mace za ai mata kishiya ba, duk ta haukace tabar kai duk daud’a.ba
Dariya lad’ifar tai ta ce “maman Rauda kenan zauna..“. Nan ta zauna Sukai ta hira tana d’ebe mata kewa. 
Karfe sha biyu salma ta dira, sai taji gidan yayi mata dad’i. Ba a dad’e ba sai ga ya karima da yaranta biyar, duk ta deb’e su, nan fa gidan yayi albarka ta ji dadi. “Kai Amma Auta zan baki kyauta, auta wallahi naji dad’in ganinki a haka.” Ladifa tace “to ai duk shirinki ne.” Salma tace “gaskiya naga kokarinki fa, ni innice akaimin kishiya, ai bansan yanda zan ba, dan ina da kishi.” 
Wallahi salma nima ina da kishi, ina ganin ma na fiki, wallahi kawai Allah na fawwalawa.” Ladifa ta fada tana mai jinjina kai. Maman Rauda tace “ya zaki kuwa in A kaddarar mijinki akwai ta Salma ta ce “ni fa banjin zan iya jurewa.” 
Karima tace “kina da aiki kuwa, domin wallahi mazan nan karka wani sanya hope na cewa ba za suyi maka ita ba, sanya a ranki ma koyaushe zai iyayi miki, sai ki zauna lafiya koda yayi nufin yi, ba za kiji zaFI sosai kamar ace kin sanya ranki ba zai miki ba.” 
Jinsu kawai ladifa keyi, dan zuciyarta na can na zullumi, kawai daurewa take. Kuloli da ya karima ta shigo da su shake da kalolin abinci, suka zuzzuba suka ci, ladifa ta kawo musu lemuka sukai ta bidirinsu, hakan sai ya ma mantar da ita cewa wai yau ake 
auren mijinta. Basu dad’e ba, sai ga anty hadiza nan da yaranta biyu mata, hasan da hussin sun rakota, da gudu ladifa ta rungume ta, sai ta saki kuka, yaya hadiza sai yau ko?.” To auta karki ban kunya man.” “Missing dinki ne fa ya sanya, aina dauka tunda ba anan garin kike ba, ba zaki zo ba.” Aa wace ni So kike hajiya tajuyan baya, ai ita tace nazo saboda miki,” “Ya karima tace “ai dole auta guda!” nan suka gaisa da maman rauda da salama. 
Haka gidan yayi albarka ga kayan cima, wajen uku saiga kannen Ramadan, zainab da wasu su biyu daga danginsu. Ba yabo ba fallasa su ka gaisa, dan su kan suna bayan sabon aure. Lad’ifa tace “Ai na dauka ma ba zaku ziba.” 
“Zainab tace “wallahi kin san hajiya, ita tace dole muzo itama can tana taro.” Nan tai musu sannu da zuwa. Take gidan ya dada karadewa, hassan da hussan su ka tafl. Acan b’agaren laila kuwa, karfe goma da rabi aka d’aura aure. Ramadan kamar an mai albishir, bakin nan har kunne, sai hidima yake da jam’a, gidansu amaryar suka shiga dan ai hoto, wani susucewa yayi ,da yayi arba da laila, tayi masifar kyau, musamman da akai mata kwalliyar zamani, sai walwali take, nan su ka dau hotuna yana jin kamar ya tafi da ita alokacin. 
Ita kuwa sai wani iyayi ake saboda kawayenta da keta santin angon, kan cewa tayi dace da handsome haka ga kud’i. Abinda take so kenan, in kaga mahaifinta da mamanta cikin farinciki suke, saboda abinda suke so ai kenan, su aurar da laila cikin mutumci gashi kuma burinsu ya cika.
 Haka su ka zarce da yininsu harzuwa karfe biyar, inda aka fara shirin mika amarya gidanta. 
Karfe shida daidai, motocin daukan amarya sun dade da wanzuwa a kofar gidan. Laila ta sha fada kala -kala, tana sanye cikin super holland kalar green da red, da babban mayafl sai risgar kuka take, don tun la’asar ta ji dukjikita yayi masifar sanyi. Adaddafe aka sanya ta mota akaja. ‘ 
….. 
Salma ya karima ya hadiza da kannen Ramadan su na zaune, su ka fara jin gud’a, nan fa duk suka mike, ya karima tai wajen ladifa dake kitchen tana kuka, sai ta kalleta “au so kike ki bar abin fada, maza, maza goge hawayenki. Dan karki bata kalliyarki. 
Janyo ta tai suka fita tana sanye da tsadadden lece din da Ramadan ya bata, rannan da mayafinsa, ta fita alokacin an ma shigo da lailan cikin falon, nan aka zazzanuna wata tsohuwa tace “to ga amana nan mun kawo, ina uwargidan ne?.” Salma ta nuna ladifa tace “masha Allah yarinya ce ashe! Sai dai na had’u nai muku fad’a,nan tsohuwartai musu nasiha sosai ta ce “ku rike amanarjuna, Allah ya hade kanku Aka amsa da ameen. 
Nan aka mika laila bangarenta. Wata daga cikin ‘yan kawo amaryar tace “cab! dama wannan ce uwargidan! gata yarinya, ga kyau dan ai tafi laila haduwa, gashi lailan ma zata girmeta ni sai ta bani tausayi ma.” 
Dayar tace shi ina ruwan namiji, ke ni yanda naga yana rawar kafa akan laila wallahi na dauka zanzo na ganta dagajaja dagaja ne! Hmm! Lalle namji. 
Hmm ke dai bar namiji, kuma dai mai daki shi ya san inda yake mai yoyo watakil kyan fuskar ne kawai..” 
Suka sanya dariya. Dayar tace wallahi kuwa ina ga hakan. Lailanmu ko ga iya daukan wanka ga komai. Bayan kowa ya watse a dangin amarya. Sai anty hadiza,salma da ya karima. Ta kalle ta “Kinji dai abinda na gaya miki ko?.” Tace E Nan su kai mata sallahma suka taFI. Zuwan angwaye itama salma abdallah ya kwasheta suka tafi gida. 
Hmm ya kukaga wannan CHAPTER din abinda wasu keta dakonsa yau ya wanzu sai kuma ajirayi CHAPTER na gaba yanzu wasan zai fara. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *