NAYI GUDUN GARA CHAPTER 27

NAYI GUDUN GARA 
CHAPTER 27
Har karfe uku laila na daki tana kuka, wanda har saida taji kanta na ciwo, umma kuwa k0 
ajikinta, saida taga abin ya wuce munsherin, sannan ta leka dakin tace “Aduk lokacin da 
mutum ba zai ji maganar manyansa ba yana tare da wahala, tun dazu nake miki maganar 
sallah da abinci, amma kinyi burus ko, irin wannan gaddamar ne fa yajanyo miki halin da 
kike ciki. To wannan ne maganar k’arshe tsakanina da ke, kar Allah ya sanya ki tashi kuka babu wata tsiyar da zai miki.” 
Tana gama maganarta Fice. Sai alokacin laila ta mike tana tafiya a hankali, dan jinta take yi wata iri, ga zuciyarta data kasa sukuni da abubuwan da suka faru, wanda ramadan yayi mata, alwala ta je tayi ta koma tai sallah taci abinci, wanda bata tashi daga wurin ba, ta dau wayarta ta kuma latsa wayar ramadan, lokacin yana farfajiyar gidansa ta baya yana karanta jarida, wayar tana ta ring ya duba ya gani ya tabbatar laila ce sai yajuyar da kai. 
Alokacin kuma ladifa ta tawo da turtstsen cikinta dauke da kofuna biyu da lemon hollandia strawberry, ta karaso tai murmushi, sai ya kamo hannunta harta zauna gefensa. Yace “ya dai babyna.” 
“Hira nazo taya ka, ina can zaune ni kadai duk kadaici ya dameni, ga shi yau laila tun safe 
banji motsinta ba.” Wayarce ta kuma kara, ladifa ta mika mai, ba yanda zai yi, ya karba fuska a tamke ya danna yace “laila wai meye kike damuna ne ehe? kar ki kara bugo kin waya harsai sanda 
na nemeki.” Tana kwance ta mike tace “ka saurareni please habiby wallahi ba laifina..” “Ba na son jin komai. Allah ne ya toni asirinki,” ya kashe wayar. 
Sai ta sunkwi da kai ta shiga kukan zuci.ta shiga tsinewa murabus kamar babu gobe. 
Layinsa ta latso, lokacin yana cikin adaidaita sahunsa ya sanya kida yana bi, har dasu taka rawa irinta maza yana goge -gefen glass , daukan wayar yayi yace “hey.” 
Zafafan kalamar na raddi ta shiga maka mai tace “wallahi murabus tsakanina da kai Allah ya isa ban yafe ba, mugu azzalumi yanda kake neman kashemin aure, insha Allahu kaima ba zaka wanye laflya ba.” 
Wata dariya ya fasa, sai ta saki tsaki ta kashe wayar, ta kifa kanta gefen gado tana matsar hawaye. 
Lad’ifa ko bayan kashe wayar da ramadan yayi tace “zauji me ya faru ne da lailar?, ina ta tafi ne?.” 
“Tana gidansu,” ya ambata tare da kai cup bakinsa dake cike da lemon hollandia. Da sauri tace “subhanallah! me yafaru ne?.” 
Hannu ya daga mata “bana son ki sanya kanki cikin lamarin nan please, indai ba ranki kema kesan baci ba.” 
Sai ta ja bakin ta ta tsuke tare da cewa “Allah ya kyauta.” 
Gyara zama tai a kujerartana jin ranta ba dadi. Ko babu komai ba zata so ace hakan ya 
faru ga wata ba. 
Sai ta sunkwi da kai jikinta yayi bala’in sanyi, ganin hakan ya sanya ya matso da ita ya kwantar da kanta akan kafadarsa, ya shiga shafar bayanta yace “kinsan lamuran Iaila ne sai a hankali, ba wai rabuwa mukai ba, kawai na maida ita ne ta shakata agidansu na wani lokaci.” 
Idonta ta lumshe ta dagosu ta kalleshi tace duk da ban sandalili ba, amma banji dad’i ba.” Murmushi yayi yace “abar maganar baby bana sonta.” “To na barta dearna.” 
Baban Iaila bai samu damar magana da Iaila ba sai da safe. Wanda karfe bakwai na safe umma ta shiga d’akin dan tai kiranta. Lailar na tsaye da waya akunne. Ganin hakan ya sa uwarta ce “idan kin gama wayar babanki na kiranki.” 
D’aga kai lailan ta yi ta zauna gefen gado tana tryn, again taji wayar akashe tabbas! ta san iyanzu ramadan ke kunna wayarsa, amma taji akashe nan da nan tunaninta ya canja ya gano mata cewar ramadan na nan awajen ladifa dan tasan waye ramadan, tabbas tasan koda ciki ba zai sararawa ladifa ba. Wani irin turnikeken kishi ne ya tokare a wuyanta, tabbas! ramadan na tare da lad’ifa ayanzu, shi,isa bai kunna waya ba. 
Wani irin bakin-ciki ne taji ya dada mamaye mata zuciya, wani irin kishi ne ke shigarta ahankali tana jin zuciyarta na narkuwa cikin kakani-kayi na kishi .Dafe kirjinta tai ta fashe da kuka, “na shiga uku.“ Ta fada, Sai data tasha kukanta, sannan ta mike ta sanya hijab ta 
tafi falon babanta. Suna zaune da Umma suna hira yana karyawa. 
Laila ta gaidashi. a ciki-ciki ya amsa sai jikinta ya dada sanyi. “Me ya hadaku da megidanki harya maido dake gida..” 
Sunkuyar da kai tayi ta shiga wasa da gefen capet na d’akin. Umma tace “ana saurarinki. Kin wa mutaneshiru.” Sai ta daga kai ta ce “nima bansan dalilai ba.” 
Tsawa ya daka mata “ba zaki fad’i gaskiya ba, ko sai na tashi na farfasa mikijiki, in banda bakin halinki laila,ace aure wata takwas amma har kinyi abinda miji ya maido dake gida 
wannan ba abin kunya bane agareki? Duk cikin yayyunki mata dake gidan miji wacece kika ta taba yo ko yaji ma.” 
Kuka ta shiga yi “wallahi baba, ba laifina bane dan Allah kayi hakuri.” 
Girgiza kai ya yi yace “tashi kije, amma muddin naji gasiyar abinda ya faru ki kuka da kanki.” 
Kafafuwanta na rawa ta mike ta koma d’aki. 
A can police station kuwa ‘yan sandan nan ta lambar da ramadan ya basu suka shiga nemansa, inda suka kaiwa kamfanin layin da ya ke amfani dashi din. Inda su ka ce zasu duba aduk shashin da yake. 
Baban laila da kansa ya nemi ramadan yace yana son ganinsa, babu yanda ramadan zai yi 
haka yace mai zaizo bayan sallahr magriba. Bayan lokacin sallar magriba ramadan ya isa 
kofar gidan, yana cikin mota bai fito ba, har saida ya samu wani yaro ya aika, inda baban laila yazo, ramadan ya tsuguuna ya gaida shi kansa a sunkuye. 
Baban ya shiga yi mai magana akan abinda ya hadasu da laila 
Shiru ramadan yayi sai da baban ya kuma yin maganar sannan ya sanarda shi dukka halayen laila da abubuwan da take mai na rashin girmama shi, da kuma babban lefin da take soyayya da Tsohon saurayinta, wanda a wannan dalilin ya sanya yace tazo gida zai nemeta. 
Saboda tarin takaici baban ya kasa magana, sai jinjina kai ya yi, yace “kayi aikin hankali da bakai saki ba. Kayi hakuri da abinda ya faru ramadan ni nasan halin laila, bai kamata ace tana irin haka ba, me ya sanya baka zo ka sanar mana an tsawatar mata ba.” 
“Wallahi ban dauka abin zai ta‘azzara bane.” Ramadan din ya fad’a. Numfashin mai d’auke da takaici baba yaja yace “Amma babu komai ba zan tilasta maka na tafiya da matarka ba, amma ina baka hakuri akan abin, koni zanso ta zauna agida taji, tunda ita bata da nutsuwa.” 
Haka sukai sallama ya tafI, shi kuma ya koma gidan cikin fushi, falon umma ya Zauna yace 
“ina yarinyar nan ne saratu?” Umma tace “tana daki.” 
Kwala kiranta yayi ta fito ta tsugunna, nan fa ya farai mata fad’a kamar yaci babu, “wato laila duk irin fad’an da muke miki bakyaji k0? Wallahi wallahi! laila idan ba kibi mijinki ba, sai na sabar miki, ke idan ba kibi mijinki ba ban yafe miki ba wallahi, haka kika ga mahaifiyarki nayi? Mai yasa ba zakiyi koyi da ‘yan uwanki ba, Wannan Ban san ina kike koyo halayen nan ba, dan mu bamu koyar da ke haka ba, wai dan baki da mutumci shine kike soyayya da saurayi! dan baki san kimar aure ba k0? ba ki san darajarsa ba ko? Ina ilminki ya ke? Ko duk abanza ya tashi ne bakya aiki da shi?.” 
Ya fad’a cikin kakkausar murya. 
Kuka ta fashe da shi. Jikinta na rawa dan tsoron mahafinta take sosai “Wallahi baba 
shine..” Duka ya kai mata a baki sai ta sunkwi dakai tana kuka. 
Haka suka sanyata a gaba sunai mata fad’a kamar me, wanda ta ji gwandama ace dukanta suke akan fadan nan.
A karshe ya kalli umma yace “duk wani hukunci da zai saita ta, ki mata har ta hankalta.” Yana fita laila ta fasa kuka, “na shiga uku shi kenan, ba a sona ni.” 
Duka ta kai mata ta matsa da sauri, sai ta mike tai daki tana kuka. 
Da yake ramadan ya bada hoton murabus! wanda ya turo mai a waya amma ya cire na lailar, ya sanya ‘yan sanda sukai amfani da hotonsa da lambarsa, da taimakon kamfanin layin, suka gano inda murbus yake, ‘yan sandan ba su sha wani wahala ba sukaje, wanda alokacin da suka je ya bar wajen, a haka dai suna waya da ma‘aikatan na kamfanin wayar suna gaya musu sashin da murabus din yake ta amfanin da service, su ka taradda shi suka kame shi. 
Alokacin idon murabus ya raina fata, yayinda ramadan yace akulle mai shi saboda barazanar da yake yi mai a gidansa. Saboda tsabar zuciya murabus! ya dake yana tsuke baki, suna tsaye a police station din ramadan na jaddada kan su koya mai hankali, saboda irin rashin mutuncin da murabus yayi mai, da tozarta iyalinsa. Murabus ya kada baki yace “wallahi ko ta halin kaka sai na kwace laila. Meye ba muyi da ita ba.” 
Wani irin naushi ramadan ya kai mai wanda har saida hancinsa ya fashe, wani kurtu ya rike shi yace kar ya dau doka a hannunsa. 
Nan suka garkame murabus. Ramadan kuma yayi tafiyarsa. 
Laila duk ta damu kanta,kullum kuka, musamman yanda umma ke damunta da yawan fada kan ita tajawa kanta, abinda ke dada damunta kenan, ga aiki da take sanyata, kalakala, wanke -wanke safe da rana, girki na safe, rana, dare, shara ba daga kafa. Gashi ko kofargidan bata bari ta leka, idan tai magana uwar tace ba ta isa ba, ta kasa zaman aure 
dole tazo ita tai mata aiki.Ba kwanciya. 
Ga wayar ramadan inta kira ba ya d’auka.Tana zaune misalin karfe tara na dare tana chating, sai duba profile din ramadan take, da ya sanya wani picture nasa yayi kyau sosai! shi da wani abokinsa sunsha fararen kaya suna murmushi. Da alama magana suke aka dauka. 
Kura mai ido tai tanajin kewarsa na shigarta, sai ta aika mai sako, kuma yana online amma  bai duba ba. Sai ta kirawo shi. 
Shi kuwa lokacin suna zaune suna hira da ladifa yana mata tausa sakamakon jikinta dake ciwo, sai mai shagwaba take kala-kala, shi kuma ya biye mata, hakan ya sanya bai duba kiran ba, har sai da ladifarta ankare ta mika mai ya dauka, ya ga laila ya saki tsaki yayi ya ajje wayar gefe. 
Haka taita ring ladifa ta dauka ta danna wajen d’auka, ta sanya mai akunne kallonta yayi, sai tajuyar da kai. 
“Mene ne kike kirana ne laila.” 
“Gyara zama tai tace “habibyna dan Allah ka tsaya ka saurareni, wallahi ba laifi na bane, dan girman Allah kai hakuri.” 
“Kin gama..” Tace Aa sai ya katse. 
Kallon wayartaijin ta mutu. Kuka ta sanya ta wullarda wayar gefe ta shiga magana afili. “Na shiga uku, ramadan kasan ba zan iya rayuwa babu kai ba, amma shine kake guduna, laifin nan fa ban akaita da san rai ba. Wallahi ina kewar gidana, please ka amince na koma ramadan.” Ta fad’a da shashshekar kuka. Haka taita sumbatu tana kuka. Karshe ta shiga jawowa murabus Allah ya isah. 
Yau kwana hudu kenan murabus na tsare. Mahifiyarsa ta damu ainun! ganin baya nan kwana biyu. Suna zaune ita da ‘yarta sunyi tagumi tace “maryam wai haryanzu murabus ba kiji wani abu akansa ba. Allah yasa ba wani abun yayi ba. Ga Alhaji sule nata damum 
mu akan adaidaita sahunsa, ba na so ya kwace, dan shine rufin asirinmu.” Maryam ta ce “umma wallahi ni ban sani ba, amma dai naji d’azu nuhu yace wai zaizo yayi 
miki bayani.” “To Allah yasa muji alkairi,” tace amin. Washegari nuhu yazo gidansu murabus! nan yake sanarda umma duk abinda ya faru. Tafa hannu ta shiga yi “oh! ni wannan yaro meyake so ya zama ne? yanzu haryakai yana 
bibibyar matar aure dan ya kashe mata, ba shi da hankali ne! dan bai sameta ba. Sai yayi 
wannan aika aikarl.” 
“Wallahi mama babu yanda ban mai ba ya kyaleta, amma ya ce sai yayi, gashi kuma da naje sunki ba da belinsa wai sai mijin yarinyarya bada izini.” “To ni ya za ai, ba yanzu ba za,a bada belinsa ba ne? wallahi sun kafe, dan dama wai yayiwa Wani kurtu rashin kunya a wajen, abinda ya dada zafafa abin kenan.” 
Tagumi tayi tace “oh! Dan Allah ko za ka nemi gidan mutumin muje na bashi hakuri a sake shi?.” 
Shiru nuhu yayi na dan sak’anni ya ce “to zan san yanda za ai.” ‘ 
Mama ta ce “to an gode nuhu.”. Nan ya mike ya tafl. 
Da kyarda sid’in goshi nuhu ya samu kwatancen gidan ramadan a wurin yan sandan. Yaje ya sanarwa da mahaifiyar murabus. 
Yau ta kama lahadi dan itace suke tunanain samun kowanne magidanci agida. Ita da maryam da nuhu sukaje gidan, alokacin ramadan na kokarin shiga mota shi da ladifa zai kaita asibiti, dan ba tajin dad’i. Tsayuwa yayi ganin bakin da suke shigowa. Karasowa maman murabus tayi ita da maryam gaban ramadan. Sai ya sunkuya ya gaida ita ganin cewa babba ce. 
Mama tace “yaro kaine wanda ya kulle idriss ko?.” Ramadan yace “nine mama.” 
Sai ta dan sunkwi da kai tace “akan lamarin da ya faru ne naji komai, banji dad’in abinda ya yi ba, kuma kowanne dan adam me kishin iyalinsa dole ya d’au mataki. Amma ina rokonka Allah da annabi ka taimaka ka sake shi, shi kadaine namiji a wajena. 
Shine maija gaba wasu abubuwan na gidan,” sai ta sanya kuka. 
Nunfashi ramadan yaja! yajuya ya kalli ladifa dake saurarensu , sai ta dan yi alamar tausayin 
“Hajiya abinda danki yayi min ya batan rai, shi’isa nake ga gwanda ya gane shayi ruwane. 
“Ba danshi za kai ba, dan Allah da annabi za kai, kuma ka duba wallahi akwai wanda ke ta bibiyar babur dinsa dake awajensa kullum, bana so wani matsalar ta faru ne,” ta fada tare da kallon ladifa tace “ki sanya baki kinji ‘yata insha Allahu hakan ba zai k’ara faruwa ba.” 
Matsawa ladifa tai kusa da shi ya kalleta sai ta dan juya tace “mama karki damu, insha Allahu komai ya wuce Allah ya tsare gaba.” “Yawwa ‘yar nan mungode Allah ya saukeki lafiya.” Ramadan yace “amin insha Allahu anjima zan biya ta police din.” 
Godiya matartayi ta mai, har suka fita, ladifa kuma ta koma mota shima ya shiga ya kalleta yace “har da saurin yanke hukunci ko? ai naso ya kara kwanaki.” 
“Gani nai idan ba hakan ba baka da niyya, saboda naji tausayin matar,” suna hira suka ja motar suka fice. 
Sai da ya biya ta police station ya ce a sake shi, sannan ai musu tsakani dashi, kai ai mai tsakani da matarsa da shi kanshi, ko lambarta ya sake kira sai ya sani. 
Babu yanda murabus ya iya ya sanya hannu kan ba zai kara ba. Sannan suka sakeshi yayi cidin -cidin saboda tsabar rashinjin d’ad’in tsaron da akai mai akalla yau kwana bakwai. Koda ya koma gida ya sha fada wurin mahaifiyarsa, wadda har sai da ta sanya kuka tace wallahi in ya kuma kula yarinyar bata yafe ba, idan aure ya keso ga binta nan ‘yar kanwarta sai a hadasu. Ganin yanda uwar ke kuka ya sanya duk yaji babu dadi. Ya yi mata alk’awarin ba zai sake wani abinda ba taso ba. Ya yarda da kaddarar rashin lailar. Allah ya kaddara ba matarsa bace.” 
Bayan wata biyu. 
Laila ce tsaye tana shanya duk ta rame sai tai fayau da ita, ta kuma d’ashewa. Saboda tsabar damuwar da ta sanya aranta, duk ta yi sanyi musamman ganin yanda ramadan yayi blocking dinta a whatsap, ya sanya ta a black list a wayarsa, sam bata samunsa ta rasa yanda za ai ya fahimceta. Ga yawan fad’an da umma ke mata, abu kadan tai sai ta hau yi mata fad’a tana cewa ta yi ba daidai ba.Ko girki tai sai ta ce au! hakan kike yi ma mijin naki irin wannan girkin a gida na ganda. Komai ta yi ba tai daidai ba, bata da tsugun! kullum cikin aiki ta ke agidan, ga mahaifinta ya dad’a tsananta mata, ga yawan kuka da take inta 
zauna tana gayawa umma ta taimaka a bawa ramadan hakuri ya maida ta. 
Tana gama shanyar ta koma falo ta zauna tana goge gumin da ta kwaso ta kalli umma ta ce 
“umma.” Uwar ta kalleta ta ce “mene ne?.” 
Sai ta ce “umma baki tab’a tambayata fa ainihin abinda ya faru ta bangarena ba, tunfa da kukaji na ramadan shikenan.” 
“Au ke yanzu har kina da bakin magana, ko kin manta lokacin da mukai ta tambayarki ki fad’i gaskiya kika ki magana.” 
Kuka ta sanya ta ce “umma kinji fa abinda duk ya faru, kinsan dai ina da saurayi murabus mai adaidata, nan ta gargargaya mata duk gaskiyar abun. 
Uwar ta ja numfashi ta ce “naji kinyi kuskure laila. Ai na sha tambayarki ki fad’i gaskiya kika ki, kuma kinga duk matsalar da kike ciki kece kika dad’a rura ta, har abada wasu matan na cutar da kansu, idan matsala irin haka ta faru dasu, wai sai su yi shiru suki gayawa mijinsu, sai suyi ta boye-boye, wai dan kar yaji su shiga matsala, to idan ba ki fada ba ai shine matsalar, da ace tun darko kin gayamai, ai yasan mai zai yi, kuma zai tari abin da wuri, sannan k0 ta kwabe ba zai ce kece da laifi ba. To ina gaya miki ko nan gaba banda irin wannna dabarar, kuma akomai kika san in ta kwabe baki da mafita to fadi gaskiya.” 
“Umma nima nasan na yi kuskure wallahi, sai yanzu nake dana-sani, da na gaya mai komai. Sannan umma dama akwai hotunan da ya taba turowa a waya, ina so na je na kaiwa ramadan ya gani, ya tabbatar cewa fa ba nice mai lefi ba, dan wallahi duk ban goge chat din ba. Kiba ni dama naje inda yake aiki. 
“Ba kida hanakali ne?.” “umma bansan ina zan same shi ba kuma ba son zuwan gidansa.“ Shiru umma tai ta ce “ba zaki bafa, sai de kije gidan.” Shiru lailarta yi tace to. Washegari Laila shad’aya da rabi ta fesa wanka ta tsantsara kwalliya, wanda sai tace ta dade rabonta da yin kwalliya, tun bayan komowarta gida, wata doguwar riga ta sanya pink ta wani yadi mai kyau, an mai adon ratsin black ta sanya shi ta maka daurin kai irin mai style d’in nan, fuskar nan kamar za ta biki ta d’au mayafi da dogon takalmi black, dan ita duk takalmanta masu d’an karan tsine ne, ta dau black jaka. 
Kallon kanta tai a mudubi, ba tai ciko ba, amma sai taga ta yi bala’in kyau sallama taiwa umma ta fita zuciyarta na bugawa kar baba ya dawo ya ga bata nan. 
Direct wajen aikinsu ramadan Ta yi. Dan aganinta gwanda taje can, sai kallonta ake, sanarwa dan adaidaitan ta yi kan ya d’an tsaya idan wani ya fito za ta sauka. 
Dayar lambarta da ramadan bai sanya ta ablackliat ba ta buga, lokacin yana zaune yana kokarin shan ruwa. Wayarsa tai k’ara ya daga sai ta kashe murya tace “Ga ni a kofar ma’aikatarku.” 
Me kika zoyi?.” “Please habiby kazo.“ 
Kashewa yayi. Sai tai tsai tana Adduar Allah yasa ya fito. 
Ba,a dade ba sai ga shi nan ya fito yana waya. Sauka tai daga adaidaitan ta bashi kud’i ya tafl. Motarsa ya shiga yayi reverse, ya fito aka bud’e mai get ya fita. Tana tsaye agefen titi kusa da wata bishiya. Murmushi tai ta tako tana wata irin tafiya. Bude motar tai ta zauna suka hada ido. 
Bai magana ba yaja motar, sai da sukai nisa yayi parking daidai wajen da ba yawaitar mutane da motoci. Ya kalleta sai wani kashe mai ido take, cikin wani irin yauk’in magana tace “wallahi habeeby I missed you so much.”
Wani murmushi yayi iya labbansa ya juyar da kai, tare da shafar gefen habarsa.” “ “Meke tafe dake.” 
Dan jingina tai da kujerar tana cigaba da watsa mai salon kallonta. Cikin wata narkakkiyar murya a hankali ta kuma cewa “ina kewarka habiby. Dan Allah kai hakuri ka yafemin, kaji waallahi na saduda.” 
Shi kuwa kallonta kawai ya ke, dan harga Allah ta yi masifar yimai kyau ga yanda take wani karairaya yana shigarsa. Dan shi kam bayan son mace ‘Yar Duma-duma. Yana son mace kuma ‘yar kwalliya mai yanga da kwainane. Yana ganin kwalliyar laila da yangarta ke kwatarta a wajensa. 
Hade rai yayi yace “me ya kaiki zuwa har office dina?.” 
hanyar da zanji ko muryarka ne.” Sai ta sanya kuka na kissa “wallahi tallahi ba laifina ba ne,” tiryan -tiryan ta shiga rattaba mai. “Bari ma kaga wayar, nan ta dauko ta kunnata, ta shiga whatsap ta dubo lambar murabus ta bashi, ya karba ya shiga dubawa, ransa ne ya kumajin ya b’aci sai ya mika mata wayar. “Na gani kuma na fahimta.” 
“Ba kace komai ba, wallahi tallahi ban ci amanarka ba.“ 
“Na sani, kinga ai yanzu duk ya zame miki izina akan hakan, da duk mata irinki ma su yaudara, kusan hakan wasu na faruwa da su, kota’ina kin iya yaudara, ko ni ma kin yaudareni, to kinga duk wannan duk abubuwan da kika shuka ne, kinga ya zamo izna ga masu irin halayenki.” 
“Ni dai ka yafemin ka maidani ka amince na koma, wallahi zan zame maka mace abar alfarhri mai biyayya.” Murmushi yayi yace “da saura laila ki koma zan neme ki.” 
Kuka ta shiga rairawa, sai ya ja motarya barwajen. Har sai da ya kaita shashen unguwarsu. Sannan ya tsaya. Ya fita ya tarar mata Adaidaita ya biya kud’in yace ta fito ta shige. 
Share hawaye take yi har ta shiga, shi kuma ya ja yabar wajen yana tunanin dukkkan abubuwan da suka faru, tabbas! ya gane cewar lailar na da kamshin gaskiya, amma so yake ta dada nutsuwa da sauran halayenta. 
Gida ya tafi direct dan ya dubo lad’ifa.Kamar kuwa ya san ladifar na naiman me taimako, dan tana zaune dan tun bayan fitarsa takejin mararta na tsunkulinta. Daurewa kawai ta ke, tana zaune ta dan dafe gefen cikinta. Ta so ace ramadan ya barta ta koma gida. Dan tunda watan haihuwarta ya kama take cewa ya barta ta koma gida yaki. Kuma runtse ido tai dan 
jin marar tata na dada ci gaba da zafi. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *