NAYI GUDUN GARA CHAPTER 5

NAYI GUDUN GARA
CHAPTER 5
Kunna fitila tai, haske ya garwaye falon, sannan taje dining ta ajje food flask din, tayi hanyar sama, danjin jikinta take duk a mace, saboda gajiya, ga shi yau bata samu ta yi baccin ranar data saba yi ba. 
Ahankali take taka k’afafuwanta, harta kai k’arshen matattakalar ta shiga d’akinta, zubewa tai a gadonta tana mai da numfashi. Ganin kamar saura ‘yan mintuna a kira sallahr magriba,ya sanya ta mik’e ta cire kayanta ta fad’a wanka. Bayan fltowarta aka kira sallah, nan ta yi shirin sallah, tana idanarwa, ta tashi ta hau mulke jikinta da mai, sai zumudi take zaujin nata ya dawo, yau so take ta burgeshi, tana so tai abinda zai yaba mata ko sau d’aya ne taji dad’i. Farar fatarta ta kalla tasha kunshi, nan tai murmushi ta ci gaba mulke jikinta da mai, ta zizara kajal, ta gyara girarta, sannan ta d’ora jan jambaki a kyawawan lab’b’anta, dan su ne mafi soyuwa ga zaujin nata, daga bisani ta mulke fuskar tata da powder. Wata red d’in gown ta d’auko, wadda akai mata da material me silk, sai kyalli ya ke ta sanya, daidai jikinta akai mata d’inkin, tai mata das! duk da rashin k’ibarta ta san ko hasadun iza hasadan zaice ta yi kyau. Gashinta da ya kusa sauka kafad’unta ta baza shi baya, da yake a tsefe ya ke kuma agyare, nanta yafa sirirrin red d’in mayafl ya sauka kafad’unta, saboda rigar me hannun vest ce, haka ta bulbula turare ko’ina, ita kanta tasan ta yi kyau, ba ta san me yasa ba takejin tana san burge mijin nata ayau, kawai soyayyarsa da kulawarsa take buk’ata Nan ta sauka kasa ta kunna bunner ta zuba turare me kamshi, falon ya dinga fldda sihirttacen k’amshi, ta kunna tv tana kallon tashar televister da suke haska film din da ta keso. K’arfe takwas daidai taji dirin motarsa, nan ta lumshe ido harya shigo, ta mik’e ta isa ta gare shi ta amshi jakarsa,tana mai sannu da zuwa. So d’aya ya kalleta, ya yaba da kwalliyar tata sosai, amma fuskarsa bata nuna wai ya maga kwalliyar ba, ballantana ya tofa,wani abu kauda kai yayi ya ce: “Yasu karimar.” Tace “tana lafiya,” ta fad’a tare da nufar sama dan ajje jakarsa. Zama ya yi shi kuma akan kujera yana maida nunfashi, saida ta had’a mai ruwan wanka, sannan ta flto ta zauna tana satar kallonsa, idonsa k’irr akan tv. “Na had’a maka ruwan wanka.” “Saina hau zanyi.” ya fad’a ba tare da ya kalleta ba. Kallonsa kawai take tana son ta ji yace tai kyau, amma kamar bai san da zamanta awajen ba, runtse ido tayi jikinta ya yi sanyi,ji tai hawaye na neman zubo mata, da sauri ta maidaSU. 
Ji tai tana san canja tashar, sai ta tashi ta wuce ta gabansa, ta d’au remote ta koma tana satar kallonsa, ta gani ko zai kalleta ya yaba kwalliyar tata, caraf su ka had’a ido yana satar kallonta. Sai taji d’an sanyi aranta. ‘Maganar ce dai bazaiyi ba ta fadi  ‘a aranta, nan wani tunani ya fad’o mata ta mik‘e a hankali ta isa gabansa, ta tsugunna ta kamo hannunsa. taushin hannunta daya ji a nasa, ya sanya ya kalleta, sai tai murmushi ta shiga murza hannun, tana yi mai kallo k’asa-k’asa, murmushi yayi. “Ya dai Lad’ifa?.” Magana ta farayi cike da shagwab’a Shi kuma ya kafeta da ido. 
“Ba ka ce na yi kyau ba, bayan dan kai nayi.” Ta fad’a tare da langwab’ar da kai gefe da tarin shagwab‘a a fuskarta.Murmushi ya yi kawai ya ce. “Kinyi kyau.” “To amma mai ya saka da farko ba kace nai kyau ba? harsai da na tambaya.” “Lad‘ifa rigima kikeji yau, ko hutawa ban gama ba kin hau ni da surutai.” Girgiza kai kawai ta yi tace “Oh! ni lad’ifa! zauji na namin, rowar ya yaba kwalliyata.” “Dariya ya yi. ” Ni kawo mini abinci naci ba surutu ba.” Mik‘ewa tai tana murmushi. “Ko hakan ma na gode. Bari na kawo maka abincin.” Ta fad’a tare da juyawa,ya bita da kallo ya ayyana yanda rigarjikinta za tafl dacewa da budurwarsa laila. Food flask na abinci ta d’auko da filet da cokali, ta zauna. Shinkafa da miya ce ta fara zubawa, ya dakatar da ita.  Ba naci, kin san ban fiya san abincin da aka dad’e da dafawa ba..’ “To yanzu ya za ai zauji? ba,afa dad’e da sauke shi ba, aka zuba.” Tsaki ya yi “0h Lad’ifa problerm, kije ki had’o min abinci mara nauyi kawai.” Jiki a,sanyaye ta mik’e. 
Abinda ta ke zato dai shi ya faru, hawaye ta share zuciyarta na tsananin zafl, ita ta rasa wanne irin miji gareta, tayi kwalliyar ma bai gani ba, harsaida ta yada billenta, san nan ma ya tanka. Girgiza kai kawai ta yi ta had’a mai komai komawa falon tai ta zauna. Yana zaune sai chating ya ke, sai sakin murmushi ya ke, tare da shafa sumarsa, yana dad’a zamowa baya daga kujerar. Tunani ta shiga yi akan dalilin dariyarsa, me ya kewa kallo haka a wayar ya ke dariya.Ta fad’a aranta. “Zauji, zauji.” Sai da tai magana so biyu sannan ya kalleta. ” Ya dai baby.” “Ruwan wankanka fa zai salamce.” “Karki damu zan hau saman.” Hira take so su yi, amma ta kula wayarsa ta d’auke mai hankali. Bayan wasu mintinonin ta tashi ta shige kitchen, taliyar da taji vegetables har ta dahu, nan ta zubo mai ta kawo mai da lemon jinja. 
K’asan ya dawo ya zauna yana ci, amma still wayar na hannunsa yana dariya, so ta ke kawai taga me ya ke yi, amma ba dama. 
Bayan gama cin abincin nasa, ya mik’e ya shige d’aki, nan taji duk babu dad’i, runtse ido ta yi taji kallon ma ya flta akanta.Tsaki tai a hankali “sai kace masu gaba.” Ta fad’a a sarari. Shi kuwa yana shiga d’akin ya shiga toilet ya silllo wankansa, ya fito yayi duk wani abubuwan da yake gabatarwa indai ya yi wanka, ya haye gadonsa ya cigaba da chating da laila, da 
ke gaya mai kalaman da ke rikita shi, su ke sanya shi murmushin dole.
Kuma Ya kejin babu wata mace sai ita. 
Ji yake kamar ya Fito da ita daga wayar. Daga baya ya buga mata wayar, su kaci gaba da hirar, sai sakin numfashi suke., ganin goma na dare ta yi, d’akin nasa ta shiga dan taga me yakeyi
Wani takaici ne ya cikata da tarin kishin da taji ya baibaye ilahirin zuciyarta. Musamman ganin yanda yake murmushi, tare da maida magana. Nan ta ke zarginta, ya kuma tabbata akan lalle da mace yake waya. Cikin tarin kishi ta mik’e ta isa inda ya ke,ta haye gadon ta matsa gefensa ta shigejikinsa. Tana k’ok’arin amsar wayar. Yana jinta ya matsar da wayar gefe. “Me ye haka?.” Duminka na ke son ji, domin a yanzu nafi wayar da kake muhimmanci a gareka, gashi ina kewarka ayau..” 
“Kullum ba agida nake barinki ba, sai yau zaki ce haka?.” “Kawai ni yanzu ne naji ina son haka..” Ta fad’a zuciyarta na tafasa. “Dan Allah ki matsa, ba kiga waya na keba, ki koma d’akinki zan zo.” Harara ta sakarmai k’asa-k’asa. “Dan kana waya da budurwa sai ka hanani matsowa jikinka. To wallahi ba zan yarda ina zaune ana waya da wata ba, ita ai ta san kana da aure. Amma take biye maka, tunda ni baka maidani mace ba.” Ga ya mini kike ga abinda ya kamata nayi ko? Ni da gidana ba zan abinda raina keso ba ko? To kada Allah yasa ki bari.” Kuka ta saka. “Yanzu budurwa ta fini k’ima a wajenka kenan? wanda har k‘imana ta kai ka hofantar dani ka biye mata agidan aurena.” “Ai sai ki hanani,wa ya gaya miki da budurwa na ke waya?.” Ta shi tai zaune ta ce. ” idan har ba da ita kake ba ka ajje wayar man.” Wani kallo ya yi mata cike da fushi, “get out of my side, bana son shirme, na kula raini ya fara shiga tsakaninmu da ke.” Kuka ta kuma fasawa. “Wallahi ba zan flta ba, in har baka daina wayar nan ba.” Wata tsawa ya daka mata, da saida taji duk jikinta ya amsa, ta kalleshi cike da tsoro. “Ki fita na ce.” Ya fad’a fuskarsa a tamke. Kuka mai wuyar fassaruwa ne ya kufce mata, da sauri ta tashi ta fice ,ya bita da kallo tare da sakin tsaki. “Kawai kin zame mini liability..” Ba b’ata lokaci ya ci gaba dawayarsa, yaudararriyar muryar laila na dad’a shiga kowanne lungu da sak’o najikinsa.Hakan ya dad’a mantar da shi yanayin da lad’ifa ta fita. Lad’ifa kuwa, kuka ta ke na fitar hankali, ayau ta dad’a dana-sanin auren mijin nata, sam! babu farin-ciki a aurenta da shi, koyaushe matsala, ga shi duk irin tanadin da tai mai dan saka shi farin-ciki, duk ma a banza bai yaba ba, saima tarin bak’inciki da ya k’unsa mata. Cike da sanyinjiki ta isa gaban mudubi ta tsaya tana k‘arewa kanta kallo. 
‘Da me Allah ya rage ta ne? duk wani tofin kyau ta na da shi afuskata, wadda koyaushe cike da annuri da kyakkyawan murmushi ta ke, nan idonta ya kai ga jikinta. ‘kodan banda cikar k’irji da wadataccen mazaunai ne Garigiza kai tai. ‘Wannan duk magana ce, domin ita a hakan take ganin kyanta.Kuma mutane da dama na sha’awar yanayin jikinta. Me zanyi ne mijina ya tarairayeni ya soni ta fad’a aranta.‘ Share hawaye ta yi tabbas tatajarabawar kenan ta gidan aure, ashe! duk labaran da take karantawa na novel, ashe’. duk soyayyarda take ganin mazan novel na yi wa matansu ashe! A zahiri ba haka bane! ta d’auka idan tai aure za ta samu fiye da hakan, ganin yanda su ka sha soyayya da Ramdan kamar ba gobe. 
Tabbas ta k‘ara yarda da bambanci.Abin ba haka ba ne, zaman Aure makaranta ce mai fad’i koyaushe da kalar abinda Za ka tsinta. Babu abinda ta ke da bukata sai tattalin mijinta da yabonsa, tare da kulawa agareta, amma ta rasa, wanda duk ada kafin aure ya ke mata, amma yanzu sai maneji. “Allah ka bani ikon cinjarabawarka, tare da k’arin hak’uri.” Ta fad’a tare da zamewa ta kwanta, kayan ma ta kasa cirewa. Kishi sai nuk’urk’usarta yake,ji take kamar k’irjinta zai flto waje, nan ta shiga karanta lahaula wala k’uwwata illa billa. 
Ganin bacci na son d’aukarta, ya sanya ta mik’e ta shige toilet ta yi wanka ta fito tai shafeshafenta na mai da turarruka masu sanyin k’amshi, ta saka sleeping dress ta kwanta ta ja bargo, dan jin sanyi na d’an shigarta. 
Sai da suka kai sha-d’aya suna waya, sannan su kai sallama, yana ta murmushi, duk ta gama burkita shi, take yanayin sanyin da ake, ya sanya ya ji yana jin buk’ata, murmushi ya yi tuno hatsaniyar da su kai da lad’ifa. tsaki ya sanya. “lta ta so, taje can ta karata.” Ya fad’a yana mai bin lafiyar gadon. Nan bacci fa yak’i zuwa mai, ga kuma feeling da ke damunsa, dan ya kasa runtsawa. A gaggauce ya tashi ya yi d’akin Lad’ifa, a hankali ya tura k’ofar, idonsa k’yam! akanta ya k’arasa ciki. 
Gadon ya hau ya janyota, ya ji har lokacin ba tai bacci ba, nan ya shiga matsarta, tai mai banza,juyo da ita ya yi. “Na san ba kiyi bacci ba, ni kuma ina son hak’k’ina.” 
Wani k’ululun bak’inciki ne ya tokare mata wuya, take hawaye suka zubo mata, babu 
lokacin da yake nuna kulawarsa a gareta sai in yana da bukatarta. “Am so sorry ladifata, kece ki ka damen shi’isa nai miki haka.” “Ka koma wajen ta wayar, ni ka k’yaleni, tun da banda wani amfani awajenka, sai in kana jin buk’ata. Amma bayan haka ba ka d’aukeni da daraja ba. Komai na yi bana burgeka to nikam ai banga amfani ba.” “Haba ladifata, kin san fa hukuncin matar da ke hakan ko? ko so kike Allah yai fushi da ke? kan ki najayayya da mijinki kan hak’k’insa.” Kuka ta saka mai sanya zukata raunana, nan ya janyo ta, ta saki jiki domin tana tsoron Allah. Sai a lokacin ya ke yaba k’unshin da tai har da su lasar hannayen da tai kunshin, yana dad’ajaddad mata kyan da rigar nan tai a kunnenta, tanajinsa yana sumbatu amma ko d’ar, domin tarin bak’in cikin ya sanya ba ta jin buk’atar abin. Da yake ya san ta kanta, sai da ya san yanda ya yi ya lula da ita duniyar da ya shiga. Nan ta maida hankali, duk da zuciyarta acunkushe ta ke, haka ta zage ta biyama mijin nata buk’atarsa, duk wani abu da yake bid’a sai da ya samu. Shi kansa yasan ta yi k’ok’ari, domin a yanda yajita, bai saurara mata ko kad’an ba.Saboda abubuwan da kareema ta bata. Bayan komai ya lafa, ya juya yana maida numfashi, ita ko bacci ne ya kwasheta. Kallonta kawai ya ke, tabbas! ta ba shi farin-ciki ayau, shi kansa ya san yarinyar na hakuri da shi. Nan ya rungumeta shima ya fad’a baccin. Da safe ba ta tashi da wuri ba, saboda tsabar gajiyar da ya kwasar mata jiya. Tun bayan sallahr asuba ta koma. Yana zaune a falo yana jiran ta Fito,dan yayi breakfast ya ta fi office, nan ya mik’e ya shiga d’akin. Ladifa cikin bacci takejin amon muryasa, ta mik’e tana yatsine. “Wai baccin me kike ne haka? takwas har ta kusa! so kike na makara? ga shi ko break baki hada ba keda Allah yayi ki ba kya san yin komai da kuzari.” 
“Ka yi hak’uri zauji, wallahi kamar am mini duka haka na keji, na d‘auka ma ka dafa tea, naga ka iya, aida ka taimaka min.” Tsaki ya yi. “Aikina ne ko naki?.“ “Ya fad’a tare da tsare ta da idanuwa. Ganin yanda ya tsareta da ido, ya sanya ba tai magana ba, ta tashi cike da kasala ta fice, ya bita a baya. Da wuri ta dafa, tea d’in ta soya k’wai, ta had’a mai da bread ta kai ta ajiye. 
Sai da ya ci san nan ya tafl. Nan ta lumshe ido, ta zauna tana tunanin halayyar mijin nata, bayan itama ta karya ta koma bacci, saboda har alokacin bata dawo daidai ba. 
Murmushi tai bayan gama wayarta da shi,misalin k’arfe d’aya na rana. “Ramadan nawa,” ta fad’a tare da zamewa ta kwanta, ita kanta ta san tana sonsa kuma tana sha’awar aurensa.Tunani ta yi kan maganar da ya yi mata yanzu kan ta daure ta bashi damarya aikowa gidansu. Murmushi tai.tace “Zan baka dama Ramadan,amma ba yanzu ba.” Wajen biyu na rana, Ramadan ya buga wayar laila yaji a kashe, ya koma whatsaap ya ajje mata sak’o ya sauka. Da yamma da ya tashi daga aiki, ya kuma buga wayar still wayar a kashe, sai ya yi tunanin ko rashin caji ne. 
Zuwansa gida ya shiga falo bai taradda Lad’ifa ba, sai ya shiga kiranta, tana kitchen tana hada fruit salad, ta flto sanye da atampha mai kalar greeen da red, ko kwalli ba ta sanya a idanuwanta ba, saboda har yanzu abinda ya faru jiya na ranta, danji tai ma bata sha’awar kwalliyar saboda in ta yi ma ba yabawa ake ba. Kallonsa ta ke tana k’arasowa, tare da son ganin reaction d’insa akanta, ko zai magana ganin ba tai kwalliya ba, saboda ya saba zuwa ya tarad da ita da kwalliyarta tsab! Sai ta ga kamar yanda ya yi matajiya, hakan ce ta faru. Murmushi ta yi. ‘Wani aikin sai maigidanta.‘ Ta fad’a aranta. 
“Wellcome nawan, ta fad’a tare da shigewa jikinsa.” “Ya gidan? ya fad’a yana murmushi. Laflya k’alau,” ta amsa, ta karb’i jakar hannunsa su ka karasa d’aki, ta had‘a mai ruwan wanka ya shiga. lta kuma ta fito tana karasa ajje abincinsa a dining. Zama tai tanajiran ya fito, idonta na kan Tv tana kallon bollywood da ke haska film, wayarta da ke gefe ta tab’a, nan ta ciji leb’e, saboda takaicin fashewar da tai, da alama ba za ta moru ba. Fitowa ya yi yace ta kawo mai abinci, d’aukosu tai ta diddire agabnsa ta zuba mai, ta zauna a gefe tana d’an yi mai hira yana ci. Yau ta d’an kula da sassaucinsa. Nan ta dauk’o wayarta, tana jujjuyata tana satar kalonsa ta ga in zai magana, karaf! ta ji ya ce. “Me ya samu wayarki?.” “Wallahi zauji ina waya na fito,wayar ta sub’uce daga hannuna ta fad’o ta saman bene ta fashe.” Nan ya karb’a ya duba ya ce “gangancinki dai.” “Haba dai zauji, da gangan ba zanyi ba..” 
“To zauji za ka canjamin? dama fa ka dad’e da min alk’awarin sabuwar waya, ganin ta fara lalacewa, ga shi ko da alama ba za ta tashi ba..” Murmushi ya yi. 
“Lad’ifa kenan, akwai ki da k’orafl wallahi, to ki bari nan da wata biyu zani china, zan sayo miki wata acan.” Langwab’ar da kai ta yi, cikin shagwab’a ta ce “haba zauji na, idan a kai ta nema na kuma fa?.” “Sai kice ba ki da waya.” “To ka saimin k’arama k0 ‘yar dubu biyar ce kafin kaje chinar ka saimin babba.” ‘ “Zancen kike so.“ Sai kawai ta yi shiru, tana bawa zuciyarta hak’uri. Kwana biyu kenan ba ya jin laila a waya. Bayan fitowarsa daga aiki, ya biya ta gidansu laila, ya aika yaro ta zo. Tana  duk’e dak’al, dak’al da ita cikin datti  tana rizgar wanki. Tanajin aiken yaron, tai sauri ta shige toilet ta wanko fuska, ta shige d’aki ta mulka mai 3 fuska, ta shafa powder da man leb‘e ta canza zani, ta dora hijab, tare da feshejikinta da turare, nan ta fice tana zuwa soro ta canja taflya, yana hangota ya yi murmushi. “Yau da alama dai daga wurin aiki kake, dan na ga lokacin tashin bai ba.” Ta fad’a tana jifansa da kallo cike da lumshe su, wanda hakan ke dad’a narkar da Ramadan gareta. “Wallahi kamar kuwa kin sani, rashinjinki ne ya sanya ki ka ganni, ga missing d’in muryarki da ke addabata, wayarki kuma yau wajen 3 days a kashe.” 
Murmushi tai ta bud’e gaban motar, sanin cewa babanta ba zai dawo iyanzu ba, kuma layinsu ba irin me cikar nan bane, sai ka dad’e baka ga an gifta ba, shi,isa ta ke sheke ayarta wajen shiga motar samari. 
“Wallahi kuwa ,nima na yi kewarka my Ramadan nutsatstsun kalamanka da ke cike da taushi sunyi min nisa adan kwanakin nan, sai na keji tamkar na shekara ban jika ba..” “Allah ko?.” “Sosai.” 
“To yanzu ina wayarki?.” Sai da ta yi d’anjim! Cike da nuna alamar damuwa ta ce “wallahi tsautsayi dai, na yarda ita a adedeta ban sani ba.” Assha! ya fad’a da nuna damuwa. “Kuma na Buga a kashe 
Shiru ne ya biyo baya, can ya nisa ya ce . “lphone ce ko?.” E! Ita ce 7 ba.” 
“To yanzu ya ya za ai ne dear na? dan ba zan iya daurewa da rashin jinki ba, dan ina 
nishad’antuwa da sumammun kalamanki..” 
Murmushi tai, cike da yanga ta kalli gefenta. “To ya za ai? sai randa yayana ya dawo ya saimin wata, ka k’ara hak’uri.” 
“Kamar ba ki da gatan masoyi, meye amfani na? ai kawai zan siyo miki wata. Ko dai kud’in zan ba kine ki saya?.” Wani dad’i ne ya cika ta. “Anya kuwa ya kyautu na d’ora maka nauyi?.” Murmushin gefen baki ya yi. Ya kalleta “Laila anya kuwa kinsan wacece ke a zuciyata?.” Narkar mai idanuwanta ta yi. Ta ce “Ni kuwa na sani.” ” To ki amince, domin da kai da kaya ai duk mallakar wuya ne.” “Ramadan nawa.” Ta fad’a tana murmushi. “Gobe insha Allah zan kawo miki wata.” “My sweat Ramadan,” ta fad’a dajan maganar. Amma fa na gode.” Sun dad’e suna hira sannan ya tafl. 
Lallai ramadan dinnan anyi dan duniya
Ka kasa saima matarka wayar dubu biyar
Amman kace zaka saima budirwa iPhone
 Gaskiya ladifa na hakuri Hmm muje zuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *