NI DA PRINCE CHAPTER 1
Mikewa tai azabure tare da kallan agoggon bango na dakin dasauri tamike ganin takusa makara, mamaki take yanda bacci yadauketa akan sallayar datai sallar asuba, kaya ta cire tai saurin fitowa tsakargida taja ruwa a rijiya tafada toilet, wankan minti 5 tai tafito tafada daki tazura doguwar riga baka tasa hijab fari tare da daukar nikaf dinta da jakar makarantarta, dama ita sam kwalliya bata dameta ba. Dakin ummanta tashiga azaune taganta tana ninke kaya tashiga da sallama tare da gaidata ta amsa cikin daure fuska Salmah kam tasaba da wannan hali na ummanta dan yanzu abin baya damunta, mikewa tai tare da cewa umma banga Abba ba koya fita ne? Kara hade rai umma tai tace ki wuce kigaida Goggo dan shikam ya fita tadan tabe karamin bakinta tare da karasawa dakin goggon ranta duk ba dadi, sam batasan matar.+ Sallama tai Goggo dake kwance ta amsa mata cikin gadara salmah tashiga tare da gaida ta goggo ta amsa tare da cewa yawan banzan za’a tafi? Salma tadaure tace goggo nidai makaranta zani😞. Goggo tai tsaki tace oho dai tunda ke da kamal kunfi karfin iyayenku ai sai kuyi tayi tace goggo yaza’aikifadi haka? cikin zafin rai goggo ta mike zaune tace karya aka muku? Wayasani ma ko kamal din yamanta dake yayi auransa acan kasar dayake ke ya barki nan kina yawon nuna jiki😏? Idanun salma suka ciciko da kwalla tadaure ta mike tace natafi makaranta goggo tace ke kika sani munafuka mudai kika kuskura kika dauko mana abun kunya sai kinsha mamaki, Salmah tai saurin yin waje tana share kwalla umma tagani a tsakar gida alamar duk zancen dasukai taji dasauri ta wuce dan tasan umma baxata taba sa baki a wannan maganar ba, nikaf ta daura takarasa waje. Titi ta fita tasamu bus din dazatai Buk tahau, acikin mota kanta kawai ta jingina a kujera tana tunanin wannan al’amari wai ace tsakanin ta da mahaifiyarta bawata shakuwa? Wai ‘yar fari😟? Ita atunaninta tin yaushe aka dena wannan abun? Intayi magana sai Abba yace mata uwarta ai bafullatanace tai wata ajiyar zuciya tare da dauko hoton kamal cikin jakarta takuramai ido aranta tace yaya yaushe zaka dawo? I really miss you, lissafin kwanan wata tashigayi yaci ace yaya kamal yadawo dan ayanda yafada mata randa sukai waya saura 3wks su taho to yanzu gashi taga harda durin kwana 5 😞 lalai yaya kamar bai matsu yaganta ba? Rabonsu da juna tun shekara 3 dasuka wuce, maida hoton tai ganin sun iso tafito daga motar ta shiga makaranta. Lalai yau tayi late cikin hanzari tafara tafiya sam bataji motsin mota a bayanta ba sai da motar tazo daf da ita dasauri ta juyo cikin razana tare dayin gefe amma ina motar gudu takeyi gashi kamar dan koyo ne ke tuka motar sam ba’a seti take tafiya ba motar sai data gogi jikinta hakan yasa tafadi kasa tim🙆🏻 Tabi motar dakallo idanta taf da kwalla dan mutane sun taru suna kallanta abin haushi bawanda yataimaka mata, ahankali motar tafara yowa baya sai alokacin takalli number motar Prince 1 ne rubuce a jiki. Sai da motar tazo daf da ita dan harta runtse ido tadauka murkusheta za’ayi jin shiru yasa ta bude idanta ahankali kafar mutane uku tagani ahankali tafara dago idanta har ta dure su akan nagaban wanda tasani shine Prince Salman dan tanaganin rashin mutincin dayake yi a school din wani wahalalen yawo ta hadiya. Salman yakashe mata ido sannan yace limamiya bakya gani ne? Aranta tace limamiya? Yacigaba kosai muntaimaka miki da glass ne? Salmah tamakamai harara sannan tadaure tace ku bugeni maimakon kubani hakuri sai kuce me? Amir dake baya yai wata dariya yace hakuri? Oh prince kagane metake nufi ai😆? Salman yace ohh ai kaji halin talakawa sannan yaciro bandir din dari biyar yacilla mata yace sune matsalarki I know😏 Najib dayai shiru abaya dan shi yake koyon tukin motar azahiri shikam baijin dadin abinda ke faruwa amma yazaiyi? Salma tai wani murmushi tare da daukan kudin sannan takaraso kusa da Salman ta mikamai ganin yaki amsa ta daura akan motar sannan ta matso kusa da salman tace maza irinku masu daukan mutane banza sannan suke tunanin kudi na maganin komai suna matukar bani tausayi😏 tana gama fad’ar haka ta juya tafara tafiya, mutanen dake gun suka shiga gulma, ran salman yagama baci yamaimaita afili Tausayi? Sannan yakalli kayan jikinta yaga gaba daya kayan datasa basu wuce kayan 2000 ba amma takalleshi tace yanabata tausayi? Dasauri yakara kusa da ita ta baya ya fizgo hijab dinta, jikintane yafara rawa ganin bata taba shigowa makarantar ba nikaf bama bare hijab ahankali hawaye yafara gudu a idanta salma yadawo ta gabanta dasauri ta tsugunna tare da kankame jikinta, ya firgita ganin yanda Allah yamata kyau amma rashin mutuncin dake idananunsa sun rinjayeshi yatsugunno kusa da ita sannan yace tausayi? Nidake yanzu waye mai kalar tausayi? Hawaye kawai takeyi yai wata dariyar mugunta sannan yace banza ‘yar tallakawa ya mike yafara tafiya tace kai da kake d’an masu kud’i fin wasu kai? Tsayawa yai chak sannan ya juyo yace ke kinsan niko waye ma? Tace why should I know? Yace be careful dan zan iya ruguza miki rayuwarki mark my word ya juya ya tafi. Amir yashiga tafamai yace woo Man kana burgeni, salman yai tsaki yafada mota yace najib zokaja cikin sanyin jiki najib ya shiga. Salma kam suna tafiya tadau hijab dinta tasa da nikaf dinta tamike tare da kallan agogon hannunta shikenan tayi missing lectures dan kusan 40mins kenan dashiga class ahanakali take tafiya tana jin wata muguwar tsanar salman jitake daza’a bata wuka ace anmata uzuri takashe mutun daya data tsana a duniyarnan to lalai ba shakka salman zata lumawa wannan wukar😡. Salma kam yaci alwashin sai ya nunamata shi basa’an yinta bane dan tunda aka haifeshi bawanda yataba fadamai maganar banza irin wannan banzar yariyar dabai masan ta ba, Amir yakalla yace adubomin ko ita wacece, Amir yace wannan yarinyar? Salman yace yes I can’t live her like this. Amir yace angama prince….Salmah kam karkashin wata bishiya tasamu tazauna dan tarasa dalili tunda ta taho ake binta da kallo, cikinta taji ya murda tasani yunwace ke damunta hakan yasa tadauko jakarta tabude tashiga irga kudin ciki ~N~350 ne aciki ta ciro dari ta mike tai hanyar shop, har alokacin mutane na binta da kallo cikin rashin damuwa takarasa tare da mikama mai shop din kudi tace abani buns sai dai me? Kafin mai shagon ya amsa taji an wafce kudin ahankali ta juyo dan ganin wannan rainin hankalin wani saurayi tagani cikin mamaki ta dauriya tace malam mekenan? saurayin yace indai kinasan siyan abu anan to lalai ne ki kwabe wannan munafikin abinda kikasa muga mai kika nunama prince har ya tsugunna kusa dake tace me kake nufi da kalamanka? Yace oh kindauka bamusan manufarki ba? Salmah ta runtse ido tadaure ta juya batare da ta amshi kudin ba, jitai an mazan gun sun kwashe mata da dariya, ahankali take naga kafarta dan jin kafar take tamata nauyi. + Sai datai tafiya mai nisa sannan tasamu guri tazauna kwalla ya cika mata ido, tunda tafara zuwa makarantarnan bata tunanin wani yasanta banda mutanen datake gaisawa dasu yau gashi anjayo mata duk inda ta wuce ana binta da kallo😰hoton kamal tadauko tafada afili yaya kamal kadawo plz😔 jitai ance lalai salmah soyaya har a skul? Tadago danta gane mai muryar tace zee ashe kin shigo, zee tazauna tare da cewa salmah meya hadaku da prince? Tace au kema harkinji? Zee tace hmm ni fa muna zaune munajiran Professor mannir kawai wani ya shigo class da gudu yace yan class kunsan salmah ai kawar zee? Sukace eh mai nikaf yace to tanacan ana show itada prince ya cire mata hijab da nikaf😂 nan yan class sukashiga dariya tundaga nan nafito nemanki banganki ba, Salma tai murmushin yake tace zee kodai inhakura da makarantarnan? Injira kamal yadawo inmunyi aure sai inkarasa. Zee tace haba salma akan wani can zaki durkushe rayuwarki? Kinsan prince yakai 2yrs a skul din nan kuwa? Tace haba? Zee tace hmm amma kinsan me? Haryanzu fa a level 200 yake salma cikin mamaki tace haba dai? Baya jaa ne? Zee ta kwashe da dariya tace inafa? Ance blanksheet fa yake submitting😝. Salma tace blank? To ya akai ya wuce level 100 zee tace ance wai da shugabar makarantar taso tadinga bashi mark sai dai shi dakanshi yace mata bayaso karta karamai haka, salma tace meyasa😳? Zee tace oho ba wanda yasan dalili, tadan tabe baki tace shiyasani zee tace waje iskanci cikin fanko😜nan sukasa dariya. Salman kam bai dade a skul ba ya wuce yawansa dan dama ba lectures yake shiga ba sai wajen magrib ya shiga gida ya ajiye mota yai bangarensa bayi nata gaisuwa yana isa daki yai wanka yazura doguwar riga yafito tareda bayinsa dake kuladashi yai bangaren fulani zuciyarshi taf take da bakin ciki suna isa harabar gun yacema bayin su jirashi yashiga, ahankali yakarasa kofar dankin bayin dake kula dagun suka budemai yashiga sai dai bakowa a kilisar da fulanin ke zama yai shiru zuciyarshi na bugawa da karfi. Wata baiwa ce tazo tace tana daki bari insanar mata, yace a’a bari in karasa tace to ranka ya dade, ahankali yakarasa dakin yakai hannu zai kwankwasa yaji maganar Ishaq (yayansa ne agun mahaifinsu) yanacewa yau ma dai kamar kullum salman yawansa yaje, fulanice ta saki dariya tace ka tabbatar dai kana kula da takunsa dukda kaini dan sarki nafarko bai zama lalai ka gaji sarki ba ehe. Ishaq yace haba ummi yaxakina fadar haka ke kina tunanin wannan shashashan Abba zaiba mulki? Yaranda banda yawo ba abinda yake? Haryanzu yakasa gama karatu? Tai dariya tace kasan sarki na tausayinsa ganin bashida uwa, ishaq yace tab aikin banza kenan to sau nawa yana zuwa gaida sarkin amma baya amsawa? Ahankali salman yafara yin baya idanshi yakada yayi jaa dakinsa ya koma yai saurin dafa kansa da kirjinsa jiyake kamar zai mutu dasauri ya bude drawer yad’auko magani ya hadiya yashiga karanta *INNALLILAHI WA INA ILAIHI RAJI’UN* ahankali yafara jin nutsuwa tana zuwa mai. Salmah zaune a tsakar ta zuba tagumi ga kwanukan wanke wanke a gabanta da alama shi takeyi tashiga tunani, abinda salman ya mata take tunani tai ajiyar zuciya aranta tace da yaya kamal nanan munyi auranmu da duk haka bata samen ba jitai an daka mata dundu a baya tadago cikin mamaki goggo tace kinci gidanku, wanke_wanke zakimana ko tunanin wancan dan iskan? Salmah tace goggo wai meyasa kika tsani yaya kamal? Ba dan uwan Abba bane? Tace oho ko dan uwa nane mai yadameni? Kedai kinji asara kannenki duk sunyi aure ke kinfi karfin iyayenki, salma tace nima da yaya kamal nanan ai…jitai an kwabe mata baki goggo tace mara kunyar banza kawai ke baki da aiki sai zancen kamal duk mutanen dasukazo neman auranki kim koresu shima Alhaji ai duk laifinshine aikin banza, tana zuwa nan tai gaba salma tabita da ido itakam bakomai zatajira kamal dinta 😗.Motsin bude kofa taji salma ta mike da sauri dan tasan Abba ne takaraso inda yake ta rusunna tare damai sannu da zuwa ta amshi ledar hannun sa, cikin murmushi ya amsa yace andawo? Tace eh Abba, nan yakarasa daki itama tana biye dashi.+ Falo yashiga itakuma tai dakim goggo ta mika mata ledar sannan tai falo gun Abba, azaune taganshi umma nakusa dashi, Abba yakalleta yace salma ya akai? Tace Hmm Abba dama……tafad’a tana kallan fuskar umma, Abba yakalleta sannan ya kalli umma yace ko in fito? Tad’anyi kasa dakai, Abba yamike umma tad’aure tace hb Alhaji? Yace ke kinjiki ai yarinya nasan magana da mahaifinta, menene a ciki? Abba ya fito salma ta biyoshi tana kallan umma na harararta suna fita tace Abba kunyi waya da yaya kamal? Yai murmushi yace jiya daddadare dai ya kirani😊. Salma tasaki murmushi tace Abba yaushe yace zai dawo? Yace hmm lalai salma tadamu yayanta yadawo tunda harta fara tambaya, salma ta rufe ido tace Abba karatu yafara tsauri inaso insamu mai koyamin ne🙈….. Abba yai murmushi yace hmm banyarda da wannan wayan ba nida nakeso yana dawowa musha biki😀 dasauri tad’ago sai kuma ta ruga daki da gudu, yabita da kallo tareda murmushi yana san yarinyar duk cikin ‘ya’yanshi yafi shakuwa da ita kasancewar uwarta bata shiga harkarta hakan yasa shine ke zama abokin hirarta tun tana karama. Salma kam gado tafad’a tashiga ajiyar zuciya na farin ciki itakanta takosa tai auren nan ko dangin mahaifiyarta zasu daina mata fad’a. Shekararta 22 amma tarasa dalilin dayasa idan kowa yake akanta kodayake kannanta 2 sunyi aure suna gama secondary, kaninta namiji kuma na makarantar kwana ta Gezawa. Wahsegari ta shirya yanda tasaba tafito ta tafi makaranta, 12 suka fito daga lectures itada zee wajen wata kujera suka zauna, zee tafara tambayar salma akan karatun dasukai yanzu, salma sosai tashiga yima zee bayani wani guy ne yazo yace wai ana magana da limamiya, cikin mamaki zee tace limamiya? Antaba kiran macce limamiya dama? Yace haka akacemin nidai taje inji prince, yana kaiwa nan yai waje. Zee takalli salma tace don’t tell me ke ake nufi? Salma tai tsaki tace dalla share d’an iska, zee tace salma karfa asamu matsala dan prince inya tsani mutum har korarsa yanasawa ayi, Salmah tai tsaki tace keni duk wannan abun bai damenba menamai wai? Shine yaci mutuncina? Zee tace tashi mubar gun nan daga gani yaganmu ne. Mikewa sukai suka fara tafiya, salmah jitai an ja mata hijab dasauri ta juya tare dacewa wani irin iskanci ne…..kalamanta sun katsene ganin mazan jiya su uku Amir na rike da hijab d’inta, cikin zafin nama ta fizge sannan tace meye hakan kakeyi? Amir yace tambaya kike? Tace eh laifi ne? Mena muku wai? A tunanina kune kuka min abu amma na nuna ya wuce to why are u bothering me? 😠 tafad’a tana hararra salman duk da cikin zuciyarta taf yake da tsoro amma ta riga tasa aranta bazata juri wulakanci ba. Zee kam tagama tsorata ahankali tafara ja da baya, prince ne yakaraso inda take daf da ita hakan yasa tad’an matsa dan tanajin sautin numfashinshi, kara matsowa yai kusa da ita , zuciyarta sai bigawa take sai datakai jikin bango ya kara matsowa tadaure tace me kakeyin hakan? Yace dazu kin tambaya me kikayi shiyasa nake kokarin baki amsa, tadaure tace to d’an matsa yace in naki fa? Tai shiru. Salman yace abinda kika fad’a jiya shine dalilin dayasa nadawo yau kikace maza irinmu nabaki tausayi? Mamaki ya kama salma itakam sam ta manta ta fad’I haka to meye inta fad’a karya tayi? Jin salman tai yace meye abin tausayi agareni? Bayan ubanki ba d’an kowa bane? Ta dago ido cikin b’acin rai tace arziki shine komai kake tunani? Yace ke yar gidan Amadu mai gini kishiga hankalinki sannan kiyi gaggawar janye kalmarki ta tausayi agareni wannan shine last warning dina…… Salma mamaki yakamata wato bincike yasa ayi akanta? Tadaure tace kalmace bazan janyeba tunda ba karya nai ba😏gini kuma da mahaifina ke ye ai baiwace wani sana’ar yi ma bashi da ita🙄 tuni zuciyar salman tagama dugunzuma ba abinda yatsana a duniya irin ace ana tausayin sa jiyai kansa yafara sarawa, hannu yad’aga alamar zai mare ta dasauri ta runtse ido ko meya tuna sai yafasa tare da juyawa dasauri. Salma tabishi da harara Amir ya nunata da hannu sannan ya nuna idansa da hannu tasan meyake nufi wai they are watching me tace oho aikine bai isheku ba. Salman kam toilet yashiga dasauri ya dafe kirjinsa ya d’auko maganinsa ya had’iya ahankali yafara jin numfashinshi na fita dai_dai……..