NI DA PRINCE CHAPTER 15

NI DA PRINCE CHAPTER 15

Bangarensu suka karasa salman bai magana ba, toilet kawai ya fad’a yai alwala, bayan yayi sallah ya mike tare da kallan salma dake zaune akan kujera da alama tunani take, murmushi yai sannan ya karaso inda take, a gabanta ya tsugunna ya kamo hannunta da sauri ta kalleshi, yace me beauty take tunani haka? Salma tai murmushi sannan ta ran gwad’ar da kai gefe tace zaka skul ne? Yai tsaki yace eh, ta kankame hannunshi tace prince? Ya kalleta yace ya akai? Mikewa tai daga zaunen datake tad’an d’agashi, ya mike tare da kallanta, kujerar data zauna ta maidashi ita kuma ta tsugunna, salman ya kalleta da mamaki yace beauty menene? Takwanto da kanta kan cinyarsa sannan tace my prince in rokeka wani abu? Ya kalleta yace mene? Tai shiru dan tana tsoron abinda zata fad’a can ta daure tace yanzu muyi karatu, kaji? Ya kalleta yace muyi karatu? Ban gane ba? Salma ta kara gyara kanta tace karatun skul nake nufi? Muyi karatun da gaske kaga muna bata lokacin mu ne, sai alokacin salman ya gane me take nufi wato yadage akan karatunshi, ya kalleta tare da shafa kanta yace bana so😏 beauty, salma ta d’ago tace why? Hannu yasa a lebenta alamar tai shiru, yace beauty banaso inyi wani abun da zai birge Abba, yana kai nan ya mike yai hanyar toilet.+ Salma ta mike da sauri ta rungoshi ta baya, tace prince ba dan ka birgeshi nake nufi ba, dan ka gama ka huta nake nufi, salman ya juyo da ita gabansa yace beauty? Salma ta runtse ido tace please 👏🏻,salman ya kura mata ido ahankali ta bud’e idanta, salman yace inace banaso zaki daina min maganar? Salma tai shiru can tace a’a in kace bakaso yau, gobe zan kara tambayarka har sai nai convincing d’inka😕, salman ya kalleta yai shiru, salma idanta yai rau rau tace prince? Salman ya janyeta tare da shiga wanka. A gun ta tsugunna tai shiru, dolene ta taimaki mijinta, amma ta ina? Shiru tai dan itakanta bata da amsar tambayarta. Salman a toilet shaya kawai ya sakar ma kansa yai tsaye yana tunani, ruwa ne ke zuba ajikinsa, yasani maganar salma gaskiya ne, amma ina…..bayajin zai yi amfani da shawararta, ya dade a haka kafin yayi wankan ya fito. Inda yabar salma anan ya tadda ita, dasauri ya d’agota yace beauty meye hakan? Ta kalleshi batace komai ba, sun dade suna kallan juna kafin salman ya daure yace naji, I will think about it, salma ta saki wani murmushi tare da rungumeshi, salman ya d’agota tare dakai bakinshi cikin nata, sun dade suna kaima juna sakonni da harshensu kafin su saki juna, a hankali suka bud’e idanuwansu, salman ya rungumeta tsam a jikinsa wani shauki ke kamashi, salma ahankali tace Thanks, salman yace for? Tace kace zakai tunani at least bakai rejecting ba, salman ya shafo bayanta baice komai ba sannan ya d’agota, takalleshi tace yanzu zaka fitan ai ko? yace eh tace bari induba abinci kafin ka gama, tafad’a tare da dan matsawa, salman ya riko hannunta yace baki fitomin da kaya ba🙁 takalleshi tace ni😳? Yace tunda bakyaso bari na…..dasauri tace a’a inaso, bari ind’aukoma, yai murmushi. Itakuma ta bude drawer tafara duba kaya, kananam kaya ta d’auko rigar white ce anyi rubutu da dark blue a jiki sai wando jeans, salma ta kalleshi tace sunyi? Dariya yai yace in sun ma beauty nima sunmin, salma ta ajiye kayan akan gado tare da cewa godiya nake da wannan matsayi☺, tafad’a tare da yin waje. Fulani zaune itada farha da ishaq sunyi shiru can fulani tace ya kamata mu fito da wani plan, ishaq ya kalleta yace umma wai da gaske salma na ita ta wargaza plan d’in namu? Farha ta kalleshi salmana? Tab, fulani itama da kalmar ta b’ata mata rai amma ta daure tace eh mana, ni yarinyarnan ina mata kallan mara wayau ashe green snake ce? Farha tai kwafa ta tuno da marin da aka maka mata, sannan bakin cikinta d’axu da safe salman ko kallanta baiyi ba har yagama jawabensa ya fita, fulani ce ta katsesu da cewa kunyi shiru, ishaq yace kawai musa a kamashi akaishi can wani kauye mai nisa a cillar dashi, farha ta kalleshi tace me kake nufi? Fulani ta harareshi tace kai fa haka kake baka tunani kake magana, ishaq ya zuciya yace ni dama ba’a taba d’aukan shawarata ba😏fulani ta zuciya tace duk shawarwarin naka da basuda kan gado? Ishaq ya hade rai tare da mikewa yace ni zan wuce, fulani tace koma ka zauna dan ban baka umarnin fita ba, ishaq ya kalleta sannan ya harari farha yai fitarsa. Nace uhmmm🤔 Salma haka ta zauna har saida salman yagama cin abinci tana kalansa, daya ce taci sai tai murmushi tace ni ba yanzu ba, nafisan in kalleka har ka gama, yace in na kware fa? Tace bazaka kware bama in kuma hakan tafaru sai in baka ruwa😊 tai maganar tare da nuna mai jug d’in ruwa, dariya yai yacigaba da cin abincinsa, bayan ya gama ya mike, salma tace ina zuwa, ya kalleta da mamaki, d’aki tai da sauri, ta d’auko jotting book d’inta sabo ta duba rubutun ciki baifi 3pages ba dasaurI tasa hannu ta yage, sannan ta d’au biro ta makala a littafin ta fito da sauri.+ Salman na tsaye yana jiranta ta karaso tare da mikamai, yakalleta yace na menene? Tace na karatunka mana😉, salman yace what? Tad’an turo baki tace a class in anyi wani abun ai zakai jotting, salman yace wa? Ni? Salma tace kai my prince☹ irin wannan dizgi😢? Salman ya kalleta yai murmushi yace hakan ne dizgi? Ta juya baya cikin shagwaba tace eh mana gashinan☹, ajiyar zuciya yai ya juyo da ita sannan ya anshi littafin yace happy? Ta kalleshi cikin tsananin farinciki tace alot😊, ya sunkuyo yamata kiss a goshi ya fita, ta dade a tsaye tare da shafa gun kafin ta shiga ciki. Salman shikanshi a mota ya dade kafin yaja mota, yana isa gidan najib a waje ya tadda shi, bai fita ba najib ne yashigo, salman ya ja mota sukai skul, sai da sukai parking najib ya kalli salman yace yarima gaskita na yarda aure nacanza mutane😁 salman yace bangane ba? Najib yace da ace da ne da gudu zamu shigo muna tada kura amma yanzu baka gudu da mota nakula, ko dan……salman ya kalleshi yace kodan me? Yace ohh ka manta? First had’uwarku da salma ta hanyarne? Salman ya tureshi yace najib na kula kwanan nan gulma ke cinka dayawa, najib yai dariya yace Ango Ango, salma ya bud’e motar tare da ya fita, najib ya kalli kusa da inda salman ya mike ganin littafi da biro yasa shi wani tsananin mamaki, da sauri ya fito, sai dai baiga salman ba, can ya hangoshi yana tafiya, da sauri ya bishi. Salman sai dayaje kusa da theater d’in dazasuyi lectures ya tsaya, najib ne ya karaso yace kai wasa wasa kana da sauri, salman yace ina zan tsaya ka bayan kana ganin rana ake, najib ya kalleshi yace muje, salman ya kalli hannunshi yace wannan? Da sauri yasa hannu ya fizge, najib yasa dariya yace najib dagaske ne abinda nake zargi? Naka ne littafin? Lalai in nakane da alama za’ai ruwa da kankara, salman yace to parrot sai kai tayi, na matatane menene? Najib ya bud’e baki yace da alama naka ne da gaske😳 u? Littafi? Ha ha ha . Salman ya makamai littafin akai ya wuce ciki, to ba najib ba salman gani yai kowa na kallansa da sauri ya d’aga rigarsa yasa littafin a ransa yace yazanyi da beauty🤔?. Fulani zaune tayi shiru, ta kalli farha tace farha ki bani yau zuwa gobe zan samo mana wani plan d’in farha tai kasa dakai, itadai tafara tsoro sai dai salman ne batajin zata iya hakura dashi, farha ta mike tace to fulani Allah yakaimu goben, fulani ce tace farha kirami hindu( baiwar fulani ce) farha tace to, hindu ta iso tare da tsugunnawa, tace gani ranki ya dade, fulani ta kalleta tace kinsanar da ishaq d’in inasan ganinsa? Hindu tai shiru, fulani tace dake nake, hindu tace nafad’a mai amma yace kiyi hakuri bazai samu zuwa ba, kuma bayasa ran har zuwa gobe zai samu dama, fulani ranta ya kara baci,takalli hindu tace fita, hindu tace to dasauri tai waje, fulani ta rike kanta tace ni? Ishaq? Hannunta ta dunkule, aranta tace da alama sai na lalaboshi. Salman zaune a aji ana lectures, sai dai wayace a hannunsa yana dane_dane, najib yad’an zunguroshi yace yarima bazakai rubutu a littafin love d’in ba? Ga malan nata bayanai? Salman ya ture hannunsa yace kai rubutun kake? Najib yace yanzu nake tunani da alama gobe zan shigo da littafi tunda matar ka ta sa mu😊 salman ya makamai harara, najib yace kawo naku na love ni sai in muki rubutun, salman yace ka manta kana nufin littafin beauty d’in zan baka kamin jagwalgwalon rubutunka? Najib yace ahhh hmmm ayi hakuri, salman ya juya tare da kallan wayarsa jin karar text, dasauri ya bud’e ganin daga salma ne. STORY CONTINUES BELOW ” My prince please concentrate”. Ya kalli text d’in , yace ya akai ta sani? Wani text ne yakara shigowa. ” please ” Salman ya karanta tare da murmushi, sai kuma ya ajiye wayar yad’an d’ago ya kalli malamin amma dayake bai sababa haushi ya kamashi yaga ina… kifa kai yai akan desk d’in. Salma dake zaune tana breakfask ta kalli wayar tare da murmushi, tun daren jiya tasan yazama dole su kwaci kansu a gidan nan, kuma duk tunanin datai abu na farko daya kamata shine salman ya gama skul…….. Salma zaune take akan sallayar datai sallar la’asar suna waya da Abba, jitai ana mata knocking da karfi, tanaji tasan basu hanne bane, cikin mamaki tace Abba sai anjima tare da mikewa, ta bude kofar ta fita, farha ce, mamaki ya kamata ta kalleta cikin mamaki tace malama lafiya? Farha ta kalleta cikin gadara tace bake nake nema ba😏 salma tace wa kike nema kenan? Farha tace kinfi kowa sani ai, salma tai murmushi tace kinfi kowa sanin baya gidan ai da alamun yanda kika bugamin kofa, farha tace matsalarki, dama abinda yasa na miki knocking so nake kiban d’ayar number yaya na kira mtn d’inshi ya ki dauka. Salma takalleta baki bud’e tace ke da wa kike magana tukunna? Farha tace au mu 10 ne agun? Salma tace nakula marin jiya bai isheki ba, farha tai wata shewa tace toko zaki kara? Salma tai tsaki tace sai kuma aka samu matsala banda tym d’inki, ta juya ta koma d’aki tare da datsowa.+ Farha tai zauna akan kujera ta tuna magajarsu da fulani, datace ki nunamata bakya tsoronta, sannan bakya kara akan san salman, kishi zaisa ta mareki ko ta miki wani abun, ke kuma duk randa ta miki abu ki tabbatar ab’angarentane dan bayinta su gani, in ta mike sai ki kawo kara guna, nikuma sai insamu sarki infad’amai, dan salman na kulaki ta miki duka, wai soyayya kuke, ni dakaina zanba sarki shawara. Farha bayan tagama tunani tai tsaki tace yau plan d’in beye ba da alama sai na sake wani shirin, ta mike tai waje. Salma kam a d’aki tsakiwa tai ta rike kafad’a tace what? Number yaya? Lalai farha tagama rainata, ba shakka sai ta d’au babban mataki akanta. Salman sai bayan isha’I ya dawo, wasu bayi na biye dashi da ledoji manya guda biyu, a falo suka ajiye suka juya, salman ya d’au ledojin tare dayima salma knocking, da sauri takara shafa hoda tasa turare kad’an ta bude kofar tare da sakin murmushi, salman ya kalleta yai ajiyar zuciya, ta kalli hannunsa sannan ta anshi leda d’aya, yana shiha ciki ya ajiye kayan akasa ya jawota jikinsa ya rungume, ta shafa bayansa tace da alama prince d’ina ya gaji, salman yace kai I miss u beauty, jinai kamar na dade ban ganki ba, tai murmushi tace eh mama ka dad’e mana tunda tun safe ka fita☹ salman ya kara rungumeta yace gaskiya kam, ajiyar zuciya sukai a tare sai kuma suka saki juna sukai dariya duk hakoransu suka fito, salman ya zauna akan gadon yace ahh beauty da alama shiga zuciyata kike kima ganin abinda zanyi, tai murmushi tace au shiga ma nake? Nad’auka da a ciki nake🙄? Salman yasa hannu ya jawota ta zauna akan cinyarsa ya mata kiss a baki yace mantawa nai ashe a ciki kike? Salma tad’an mintsineshi a ciki sai dayai ‘yar kara tace ashe? Dariya yai shima yasa hannu a cikinta ta d’auka ramawa zai sai taji ya sa hannunsa a cikinta yana wasa dashi, motsi tafara tana ture hannunshi tace please ka bari, wanna fa wayon chakulkuli ne, dariya sukai so sai suka kwanta akan gadon a rigingine, salman ya mike yace beauty taso yafad’a tare da d’agota, ta mike tana kallanshi yace kaya ma siyo miki, tace haba? Yace jawo ki gani, nan ta jawo ledojin, English wears ne kala kala, riga da wando, riga da siket, riga iya gwiwa ta d’ago d’ayan ledar, duk mii siket ne da kanannan riguna wanda ko ciki basu rufeba, da sauri takalleshi tace naji wancan nawa ne amma wannan fa? Salman yace shima nakine 😉 STORY CONTINUES BELOW Ta kalleshi tace wannan? Tafad’a tare da d’aga kayan, salman yace eh kuma yanzu zaki kwada d’aya nagani ba🤔 salma tace naam? Salman yace ina jira, salma ta kalleshi ya had’e rai yaci wani magani, tace prince ai…..katseta yai yace in bazakisaba ki barshi, tace ba haka bane, tafad’ a tare da d’aukan d’aya harzatai toilet ta tuna da sauri ta dawo jikin kujera tafara kokarin cirewa, tanayi tana kallan salman, sai dai shi ta kula hankalinsa nakam wayar hannunsa. A hankali ta zura rigar ta kamata sosai, ga rigar bata gama rufe ciki ba, ta kalli siket din tasan ko cinya bazai gama rufe mata ba, takalli salman sai dai fuskarnan a had’e nan ta shiga sa siket, ya maseta d’am hips d’inta sun fito sosai ta kalleta tace kamar kiristiyana? Abinda batasani ba tunda tafara sa kayan salman ke satar kallanta ta gefe, ta tsaya tunanin kayan, batasan sanda salman ya karaso gunba, kanshin turarensa ne yasa ta d’ago, fizge zanin datad’an rufe yai tare da kallanta, yace Woooooo kai beauty kin ganki kuwa? Salma tad’an harareshi tace inafa zan ganni tunda an maidani kiristiyana😞? Salman yasa hannu sai jitai ya d’agata sama, tace prince? Juyi yai da ita sannan ya direta akan gado salma tai murmushi tace my prince? Salman yace umm, tace I am afraid😞 yace for what? Tai shiru can tace ganinake kamar I am too happy ya rungumeta yace bana fad’a miki ki daina wannan tunanin ba? Tace Allah in ina tare dakai mantawa nake da komai, ina tsoron kar farincikin danake ciki ya yanke, kallanta salman yai sannan ya sa hannu a gefen fuskarya ya shafo bakinta,ahankali yakai bakinshi nata, wani salo yake mata itama nan ta shiga maidamai, kan kace me? Duk sun fita hayacinsu, cikin wata murya salma tace i luv u dear, salman cusa kansa a rigarta a hankalI ya zagu mata siket…….nidai kam daga nan nai waje da d’an littafina, kafin salman ya bugo ni da sanda🚶🏻🚶🏻🚶🏻🚶🏻 Ishaq ne zaune a kam kujera ya had’e rai, fulani ta kalleshi tace haba ishaq nice fa? Ya kalleta cikin ko in kula yace nasani ai, tace to naji kayi hakuri, yace nahakura amma in an kiyaue abu biyu, na d’aya kidaina nuna salman ya fini komai, sannan na biyi duk cikin plan d’inmu kar akuskura a tab’amin salmata dan bazan yarda ba ehe, fulani ta tabe baki a ranta tace Allah ya raba bawa da wahala in banda rashin tunani me zakai da matar kaninka? Kanin ma makiyinka? Ishaq ya kalleta yace ke nake jira umma, tace nayarda zan kiyaye duka, mun shirya ai ko? Yai dariya yace yanzu a ina zamu tashi? ……………. Nace a inda kuka tsaya🙄😏aikin kawai Bayan sunyi wanka, suka sa kayan bacci suka kwanta, salma ta kwanto jikin salman sannan tace dear ya makarantar? Ya shafa kanta yace lafiya, tace kasanfa ba haka nake nufi ba, tafad’a tare da d’agowa ta kalleshi, salman yaja kumatunta kad’an yace beauty kenan, salma ta kalleshi batai magana ba, salman yai ajiyar zuciya, salma takalleshi tace badai bakai rubutu ko d’aya ba? Inbakai rubutu ba nasan kaji amma ko? yace badai haka za’a dinga min kullum ba ana sani a gaba ana tambaya, salma tai matso da fuskarta tace ah to, tun kafin in gano mijina bashi da kokari gwara ya nunamin, ko in dinga ma lesson? Salman yai wata dariya tare da mikewa ya zauna yace what? Baida kokari? Yimin lesson? Beauty nakula baki sani ba amma sanda nai karatu a paris bana wuce position 1 to 5, har nagama secondary na, zakice me? Salma tasa dariya tare da rufe baki, ganin salman na mata wani kallo, yace meke nan?baki yarda ba? In d’auko miki ki ganine😎?+ Salma takara dariya tare da toshe baki tace bafa haka nake nufi ba, ya had’e rai yace me kike nufi to? Ta daure tace nayarda dakai wallahi, kaima kasani ai duk abinda kafad’a ina yarda, na kuma sani basai an fad’amin ba, salman ya kalleta yace dariyar to tameye? Tace yanda kakeyi ne yasani dariya, yace kefa kika faro maganar, harda wani zancen lesson, salma ta gyara zama ta juya baya tare da rungume hannayenta a akirji, salman yace mekuma akai? Salma tace please kamaida hankali akan karatunka, salman ya kwanta tare da jawota, yace nidai abar maganarnan a d’auko wata, salma tace shikenan zan d’aura gobe, yai murmumushi tare da kara rungumeta, haka sukai tad’an fira kasa kasa,bacci me dadi ne yad’aukesu. STORY CONTINUES BELOW Yau watan su salman d’aya da dawowa, salma kullum sai ta tunama salman zancen karatu, duk da yana sharewa amma azahiri yanajin dadin yanda ta damu dashi, basa zuwa ko ina, tana gida, tayi sa’a kwana biyu farha ma bata shigo ba, salma najin dadi sosai rayuwarta da salman, wani irin so takema salman da ita kanta batasan yawanshi ba. Yauma tana zaune ya gama gyara d’akinsu dan ta hana kowa shigar musu turaka, ta gyara tsaf tai wanka ta d’auko riga da wando ta saka tayi kyau sosai, tai kama gashinta ta gefe, kallan gashinta tai a fili tace ya kamata in wanke kaina, waya ta d’auka tama salman text tanaso taje wanke kai, salman na gama karantawa ya kirata, ta d’aga tare da sakin murmushi, salman yace beauty ni zan kaiki amma ko? Tai murmushi dama haka take so, tace naga kai kana makaranta, yace mun gama ai, yafad’a tare da kallan malamin dake koyarwa, salma da mamaki tace da wuri haka? Yace hakan ne wuri? Tace shikenan in ka gama sai muje ko? Yace ganinan, salman na kashe wayar ya d’an bugama najib littafin dake gabanshi, yace shugaban sa ido, kai karatu da kyau ni zani gun matata, najib yace zan fad’a mata malam na aji kake fita😛, salman yace in ka samu dama kenan, yafad’a tare da fita ta kofar baya ko ajikinsa. Salma a baya ta d’ora akan kayanta ta nad’a mayafin kayan ta d’auko flat shoe tasa, agoggo ta duba tace ah why am I so excited? Waya ta d’auka tafara game, bata dade ba salman ya mata waya, da kyar tajira tai ringing biyu ta d’auka, salman yace matar salman ki fito, mijinki na jiranki, salma tai murmushi tace mijin salma ya jira matarshi kad’an gatannan fitowa, tafada’a tare da kashe wayar. Mikewa tai ta rataya karamar jakarta ta saka wayarta da wallet d’inta ta fito, a hankali ta karasa mota tare da bud’e gaba, ta zauna, salman ya kalleta yai murmushi, yace ahhh naji kanshi matata, salma tace kai prince😟 mota ya tada yace amma dai ba direct gun wanke kan zamu bako? Tace can zamu mana, yace ban yarda ba sai na d’an zaga da matata, tace to ina zamu? Yace ba ruwanki. Sun fita daga gidan daidai nan ishaq yazo shiga, da mamaki ya kalli motar, salma da salman ya kalla suna ma juna murmushi, wani mugun kishi ne ya turnukoshi, har ya shiga ya fito ya bisu. Salman kam a 212 yai parking ya kalli salma yace muje? Tace me zamuyi? Yace yunwa nakeji, tace ok, fitowa tai suka shiga salman yasa aka sa musu snacks a takeaway sannan yace asa icecream, nan aka had’a musu suka biya. Ishaq ya kalli shagon haushi ya kamashi, ganinsu yai sun fito da leda suna tafe kana ganinsu kasan sunyi matching da karshe ga wani farin ciki dake zaune a fuskokinsu, ishaq ya cika yai fam. Mota suka koma sukai can hanyar aminu kano, sai da sukaje gun fly_over sannan salman ya d’an gangara yai parking, bud’e kofa sukai, salman ya kalleta tare da cewa abani abu inci, nan salma ta mikamai chicken pie da lemo, daga d’an nesa kad’an taga wasu masu saida gurji, jitai yawunta ya tsinke ta kalli salman tace prince bari inje can, salman yace ina? Ta nuna mai gun mutanen data gani, yace inkaiki mana? Tace a’a da kafa zani, yace to nan ta fita, ishaq kam ya baya kad’an yana kallansu, ganin salma ta fito yasa yace da alama sunyi fad’a naji dadi. Salma kam takarasa gun masu gurji, ta siya, taga gyad’a dafafiya nan ma ta siya, har zata taho taga mai gwaza, tace abani gwaza, nan ta sisiya dadi ya kamata ta juyo tana murmushi, salman ganin yanda take murmushi daga nesa yasa ya fito ya tsaya yana kallanta,ishaq ya kallesu wato ba b’atawa sukai ba? Wani kishi ne ya d’ibeshi ya fizgo mota da gudu yai inda salman yake gadan gadan, salma dake tafiya ta kula da yanda motar ta taso, hannu take nuna ma salman ya matsa, shikam ya d’auka ko wani abun take nufi, tace kamatsa, salman yace naki, sai kin karaso, salma kam ganin yanda motar takusa zuwa inda salman yake yasa ta taho da gudu tare da jefar da ledojin salman ya kalleta ganin yanda take gudu a titi ya kalleta yace beauty? Ishaq yakarajin wani kishi lalai yau zai karasa salman, Kafin salman ya kara wani magana salma ta karaso haka motar ma, salma ta rukeshi sukai gefe, sai dai duk da haka sai da motar ta bige salma. STORY CONTINUES BELOW Ishaq baisan abinda salma take kokarinyi kenan ba, ganin ya bige salma yasa yai parking ya fito da sauri,salman kam suman tsaye yai jiyake kanshi na wainawa, salma ya kalla dake kwance a sume, ga goshinta ya fashe yana zubar da jini, masu gurji ne suka karaso gun ishaq ma haka, salman sai kallan kowa yake amma baisan meke faruwa ba jiyake kamar bashiba, ishaq ya karaso tare da kallan salma idansa ya ciciko, salman ya jijiga sai dai yakula salman baya hayacinsa, yace kai bakaga yanda salma take bane? Dalla malam…..gani yai salman ya rike kirjinsa da kansa wani irin kurkusus yakeyi, mai gurji tace ka kaisu asibiti mana, kar a samu matsala, ai kai kaja, kuna tafiya bakwa kula dana gefen titi? Ishaq ya kalli salma da sauri yasata a mota, masu gurji sukace saura shi, salman sai murkususu yake, nan wani mai rake ya karaso ya taimakamai aka saau amota, asibitin aminu kano yai dasu, shikanshi hawaye yake baiyi zatan abin zaikai haka ba yanzu ga salmarsa itace ba lafiya. Suna zuwa Aminu kano, akai emergency dasu, salman kam ya fita hanyacinsa dan ba maganinsa, likitocin sun dukufa akansu, ishaq kam kuka yake ya daure ya kira waziri ya fad’amai, sarki kam yanaji jiyai kamar yasa kuka,yana tsananin san salman in wani abun ya same shi yazaiyi?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *