NI DA PRINCE CHAPTER 16
Salman ya koma d’akin inda ya tadda Salma a kwance, Zeena ya kalla yace bacci tai? Yafad’a tare da kallan Salma, Zeena “tace Na fito daga wanka naganta akwance maybe baccine ya d’auketa.” Salman ya zauna a kusa da ita tare da kallanta, idanunta a rufe suke tanaji zeena tace bari taje waje zatai waya. Salman na gani ta fita ya matso daf da ita tare da sako fuskarshi daf da tata, yakai bakinshi gefen kunnenta yace “beauty nasan fa ba bacci kike ba” Salma ta shareshi, bakinsa yakai inda akasa mata plaster ya sumbata, salma a hankali ta bud’e idanunta, ta kalleshi.+ Salman ya d’ago idanunsa suka had’a ido, tace “har ka dawo?” Yace “Beauty ba inda ke miki ciwo dai ko?” Salma ta kalleshi har zatai magana ta fasa, can tace ” ka fad’ama su Abba ne?” Salman yace ” tun jiya nakesan sanar musu amma ina tsoron kar hankalinsu ya tashi.” Tace “gwara da baka fad’aba dama banaso susani, hankali Abba tashi zaiyi.” Da yamma hajiya karama da kanta tazo ta taho dasu Salman, ba shiri suke ba hakan yasa daga gaisuwa da dubasu ba abinda yakara had’asu har suka isa. Salman suna shiga ya kalli Salma yace “ina zuwa dear,” Salma tace to. Bangaren Fulani ya nufa, yana shiga ya wuce kilisarta, tana zaune itada Ishaq abin duniya ya damesu, jin sallamar Salman yasa suka kara shan jinin jikinsu, Salman ya shiga tare da neman guri ya zauna. Cikin murmushinsa dabazaka tab’a gane me yake nufi ba yace” Umma tunda ke kin kasa zuwa dubo d’anki shi gashi yazo da kansa.” Fulani ta shiga in in na tace ” Salman ba haka bane yanzu nake shirin fita, amma nikam ya akai hakan tafaru?” Tafad’a dan tabbatar da Salman yaga Ishaq Salman ya kalleta yace ” Hmmm to Nikaina bazance ga abinda yafaru ba, amma nikam kamar kana gun ko?” Yafad’a tare da nuna Ishaq, kan kace me? Ishaq ya rikice, jikinshi yafara rawa. Salman yai wani murmushi yace ” to ko ba kaina gani ba? Sai naga kamar kai ka taimakemu ka kaimu asibiti?” Fulani jin haka yasa tai saurin cewa ” shine mana, kasan halin Ishaq da rud’ewa, ya firgita ne ganin halin da kuka shiga.” Salman yace ” ohhhh naga alama, nikam ina Farha?” Fulani tace “tana d’akinta, hankalinta ya tashi dataji halin da kake ciki” Salman yace “nasani ai.” Yafad’a tare da mikewa, har yakai kofa yaji Fulani tace “Amma naji kamar ance kanada wani ciwo? Mai wuyar warkewa?” Salman ya tsaya cak, tare da cizen leb’e, ya juyo inda suke ya saki murmushi yace ” ba wani ciwo, kawai ganin matata tashiga wani yanayi ne yasa nima na shiga, ya akai? Kin shiga wani haline jin banida lafiya?” Fulani tad’an tab’e baki tace “sosai ma, Alhamdulila da abun ba serious bane.” Salman ya juya batare daya mata magana ba. STORY CONTINUES BELOW D’akin farha ya isa tare da knocking, ta budemai, sai dai ganin Salman ya sa ta saki baki, Salman ya karasa d’akin yana cewa “to ko ba’ayi farin cikin ganina bane?” Farha ta juya ciki da sauri tace “yayana, kaine?” Yace “me? Bakiyi farin cikin ganina bane?” Tace “inafa!!! Farin ciki yaimun yawa dai.” Salman ya karasa jikin madubi inda take yaga takardu, ya d’aga tare da cewa “badai anan kike ajiye passport d’inki ba?” Farha tace a’a takarasa cikin jakarta tare da cirowa tace “ka ganshi nan” Salman ya karasa ya ansa yace ” banyarda adinga ajiyeshi a jaka ba, dan haka nizan ajiye miki daga yau.” Farha ta rufe ido tace ” jinake kamar ka zama mijina yayana” Salman ya buga mata wani kallo sannan ya karaso daf da ita, yace “lokacine ai.” Farha kam kamewa tai a tsaye har Salman ya fita bata sani ba, Salman na fita ya d’aga wayarsa ya kira wani friend d’insa, yace ” zan kawo maka passport d’in gobe, please as soon as possible nakeso.” Ya kashe wayar tare da sakin wani murmushi, yace bazan bari ki kara canza hali ba anan garin. Salma kam d’akinsu ta shiga gyarawa, Salman ya bud’e kofar, tana tsaye jikin gado ta juyo ta kalleshi, Salman ya karaso tare da bud’e mata hannu, murmushi tai, takaraso ta shige jikinsa, riketa yai tsam yace beauty kamar munyi wata bama d’akin ko? Tad’aga kai, yace “ahhh naji dad’in ganin mu, mu biyu, Salman ta kara shigewa jikinsa, rikota yai ya zaunar da ita kan gado, tare da mikarmata da kafarta, yace “ki d’inga zama kina hutawa sosai, karki d’inga wahalarmin da babyna.” Salma ta rangwad’ar da kai tace “Prince gyaran d’akin ma wahala ne?” Yace “eh mana.” Tace ” to ai sai jikina yai tsami in haka ne.” Mikewa yai ya zauna a bayanta sannan ya kwanto ta jikinsa, yace “Beauty?” Tace “naam.” Yace ” nikad’ai nasan farin cikin danake ciki.” Tace “ummm to in haka ne abani gift” Yace “toh!! me Beauty na takeso?” Ta juya kanta tace ” exams dazakuyi this year, karka m’ika farar takarda.” Salman ya sakar mata murmushi yace “daga sanda naji kina da ciki, na d’au wannan alkwarin, bazan bari d’ana yataso yaganni coward ba.” Salma ta kai bakinta zata sumbaci kuncinsa, matsowa yai hakan yasa bakinta ya shiga nashi, tad’an d’ago ta kalleshi, hannu yasa a gefen fuskarta yakara jawota kad’an, shima ya matso, tare dakai bakinshi cikin nata, sun shagala sosai, salo suke ma juna, dukansu idanunsu a rufe, sun dade kafin su saki juna, a hankali Suka bud’e idanunsu, Salman ya had’a gushinsa danata, suka saki murmushi, tace thanks dear………murmushi ya sake mata. A ranta tace Allah nagode maka daka had’ani da wannan bawa naka. Farha kam tsalle ta daka, jitake kamar ranar auransu ta zo, waya ta d’aga takira mumynta, tace “mumy bana tunanin zan dawo yanzu, maybe ma kune zaku taho, bani ba.” Mumyn tace ” bangane ba” Farha tace ” kedai bari mumy, burina ya kusa cika.”tafad’a tare da kashe wayar, tace “hmm wayaga idanun Salma?”1 Salman yashirya tsaf, Salma dakanta ta d’aukomai kaya ya saka, suka fito dinning Salma ta zauna ta zubamai abinci, Salman ya kalleta yace “yauma nikad’ai zanci?” Tace “a’a tarw zamuci” yai murmushi tare da kallan su hanne, ya musu alama da hannu su fita, nan sukai baya suka fita. Salma ta sa spoon suka faracin abincin, Salman sai kallanta yake yana murmushi, suna gamawa ta d’auko mai littafinshi da mik’amai, yace “thanks dear” tace “Allah ya bada sa’a.” Salman ya mata kiss a kumatu sannan yai waje. Direct school ya wuce, a hanya yama Najib waya yace “nashigo, ka karaso?” Najib yace ” yanzu na shigo kana ina? Naji kace akwai magana.”+ STORY CONTINUES BELOW Salman yace mu had’u a inda muka saba zama, ya kashe wayae tare da karasawa. Sun had’u su uku da Amir, Salman ya kallesu sannan ya kalli agoggo yace “saura 5mins a shiga lectures, let me go straight to the point, daga yanzu no more play.” Najib da Amir suka kalleshi da mamaki, sukace yarima me kake nufi? Salman ya d’aga littafin hannunsa yace ” Nadaina submitting d’in blank sheet, na kusa zama uba, ba zan bari d’ana ya taso yaganni a haka ba.” Yana kainan yai cikin theater, suka bishi da kallo cikin tsananin mamaki, anya Salman ne kuwa? Sai dai Najib ya kalli Amir yace ” kamar cewa yai ya kusa zama uba ko?” Amir yace “haka naji.” Najib yai murmushi yace “wow da alama Salma ciki gareta.” Shima yai sauri ya shiga yana murna. Amir ya bisu da kallo, shikam sam baisan karatu, haka dai ya shiga ranshi a b’ace. Yan class gaba d’ayansu suka zuboma Salman ido, harda malamin, mamaki suke yau Salman ne ya shigo akan lokaci? Sannan kuma rike da littafi? Salman ko kulasu baiyi ba ya wuce ya zauna. Malamin ya saki baki, sai da Salman ya kulu yad’an daki desk kad’an, sannan kowa ya juya, malamin ya d’auko biro a aljihunsa a rikice ya d’auka maker ce, sai dayaje rubutu ya gani, yan class suka kwashe da dariya, sannan yai saurin d’auko maker ya fara rubutu. Salman rashin sabo yasa duk yaji ajin ya isheshi, yadaure sai gyara zama yake, yakai hannu kamar zai d’auko waya, Najib yace “ka manta ne baban baby?” Salman najin haka ya fito da hannunshi, har aka gama lectures kafin su fito. Yana fitowa yad’au wayarsa ya kunna, text ne ya shigo daga Beauty “My prince ya karatun?” Murmushi Salman yai sai dai maimakon ya kirata kawai sai ya kira wata number, yace “Asim ina zamu had’u? Na taho da passport d’in.” Sai kuma yace “alright” tare da kashe wayar. Najib ya kalleshi yace “badai honeymoon zaku kara guduwa ba?” Salman yace to baban sa ido, mun kusa fara exam inafa zani wani gun?” Najib yace “kai abin nan na bani mamaki.” Salman ya d’an bige kafad’arsa yace ” gwara ya daina ma baka, muje ka rakani.” Nan suka shiga mota suka fita. Farha zaune kusa da fulani da ishaq, Fulani tace “yanzu wace shawarar zamu b’ulo?” Farha ta kallesu tace “ni ba wani plan da za’ayi dani, dan yanzu yayana yana sona banason nasake wani abu dazaisa ya kara jin haushina.” Fulani tace ” ke yanzu kina tunanin Salman dagaske sanki yake.” Farha ta mike tace” ni ba abinda yadamen, abinda yayana Yafad’a dashi kad’ai zan d’inga amfani.” Takarashe maganarta tare da mikewa tai d’akinta. Ishaq yace “good haka akesan soyayya da confidence, da alama nima zan tari Salma in fad’a mata abinda ke raina, wayasani ko itama tana sona? Ganin na basar ne yasa ta share?” Fulani ta kalleshi shekeke, tace “lalai Ishaq baka da hankali, matar kanin taka zakace kana so? ” Ishaq ya mike yace “nidai nagaji da biye miki abubuwa na basa tafiya daidai.”shima ya juya yai waje. Tai tsaki tace “ace duk cikinsu bada wanda zakai shawara? Ga ragowar ‘yayanta maza bata saba irin wannan had’in dasu ba. Salman sai bayan magrib ya dawo, yana parking yaga wayar farha, tsaki yad’anyi kafin ya d’aga, cikin salo da kisisina take maganar, tace “yayana baka dawo ba?” Salman yace “ya akai? Kanwata ta damu ta ganni ne?” Farha tace “sosai ma.” Yace na shigo yanzu, anma zan tsaya gun mai martaba” Tace ” to sai ka gama.” Ya kashe wayar batare da ya amsa ba. Tsaki yakari yi, sannan ya kira Beauty, Salma ta d’aga tare dayin sallama, wani sanyine ya ratsashi, yace Beauty kinjini shiru ko? Tai murmushi tace ” eh mana duk ba dadi.” Salman yace “uhmmm lalai an damu dani dayawa, Me aka tanadarmin to?” Salma tace “komai ma, nidai ka dawo please” Salman yace ” amma dai ba inda ke miki ciwo ko?” Tace “nurse tazo d’azu ta dubani tamin dressing.” Yace “good, na iso ma, zan d’an shiga gun mai martaba ne” tace “tam a mikamin gaisuwata.” Yace “uhmm.” Ya kashe wayar tare da fitowa yai b’angaren mai martaba, yana isa, bafadan ya shiga yamai iso, Ishaq na zaune gun sarki, Sarki ya bada izini. Salman na shigowa yaga Ishaq, shima Ishaq din kallanshi yake, Salman ya d’auke kai, tare da shiga, yai kasa dakai sannan ya kwashi gaisuwa, ga mamakin Ishaq bayan Sarki ya amsa harda tambayar jikin Salma, cike da mamaki Ishaq ya kalli Sarki, bai kara shan jinin jikinsa ba sai dayaji Sarki yace Ishaq bamu guri zamuyi magana, cikin tsananin mamaki ya amsa sannan yafita, sai kuma yai tunani ko dai fad’a za’amai? to amma in fad’ane ai sarki bazai amsa gaisuwarsa ba, meke faruwa?. STORY CONTINUES BELOW Nace kaika sani………… 1 Salman ya dade sosai, da Sarki sai daya tirkeshi suka ci abinci tare, sannan yamai saida safe ya fito. Kana ganin fuskarsa zaka gane yana cikin farin ciki, yau ce rana ta farko daya tab’a cin abinci da mahaifinsa, bazai iya tunawa ba ko kila yana yaro, amma shidai a saninsa yau ce ranar farko. Bangarensa ya shiga da sauri, shi sam bai kula da Farha dake zaune a falo ba, zuciyarshi nakan yasanar ma Beauty abin farin cikin daya same shi, Salma kam, tayi kwalliya da riga iya gwiwa, da d’an wando pencil, ya d’ameta, ta fito daga toilet kenan, jin kamar zatai amai, sai dai taje ta kuma kasa aman, jitai an murd’a kofa ta juya dan tasan Salman ne, ganinshi tai ya shigo da sauri, yana shigowa ya sa hannu ya d’agata yafara juyi da ita, Salma tace “Prince? Wani abun ne yafaru?” Sauketa yai sannan ya rungumeta yace “Beauty kinsan me?” Ta girgiza kai alamar a’a, yace “yau tare mukaci abinci da Abbana.” Wani sanyayen farinciki ne ya bayyana a fuskarta tace” Prince? Naji dadi sosai” Shima yace “nima haka beauty.” Farha da kishi ya turnuketa ganin Salman ya wuceta yasa tabuga kofar da karfinta, Salma da Salman suka kalli juna, Salma ta karasa tare da bud’e kofar ta fita. Farha ta gani hakimce akan kujera, tace ” Yayana nake nema” Salma tace “haka b’atan kai kikai ko? Kin manta na hanaki shigomin guri?” Farha ta d’aga waya ta iira Salman, ya d’aga tace “yayana ina falo fa?” Tai maganar cikin shagwab’a, Salma tai wani murmushi tace wahalace bata isheki………maganarce ta tsaya a wuya ganin Salman ya fito, cikin mamaki tace “Prince?” Salman ya kalleta sannan ya kalli Farha yace “kinzo?” Ta makama Salma harara sannan tace “tun d’azu nazo fa, ina nan ka wuceni.” Salman ya kalli Salma data cika tai fam, ya kalli Farha yace “muje waje.” Tace ” to” sannan ta kalli Salma tace “inlaw Sai da safe.” Salma ai kasa magana ma tayi tana kallansu suka fita, bin kofar tai da kallo……. Mekenan? Abinda ke yawo akanta kenan. Salman suna fita ya kalli Farha yace ” gani neman me akemin?” Ta saki wani murmushin kissa cikin shagwaba tace ” nemanka kawai nake in ganka, jinake kamar na dade bam ganka ba.” Wani kallo ya mata da ita kanta batasan nameye ba yace ” idan bakya garin yazakiyi kenan?” Cikin rashin fahimta tace ” bangane ba yayana.” Salman yai murmushi shima tare da matsowa kad’an yace “just joking. ” Dariya tasa tace ” kai yaya har ka tsoratani.” Yace ” yanzu dai nagaji, muje in rakaki in dawo inkwanta, bacci nakeji.” Cikin salon shagwaba tace ” ba wani yaya so kake dai ka koma gun matarka.” Gani tai ya murtuke fuska ya had’e rai sosai yace” in muna magana karki kuskura ki kara sako matata, banasan haka.” Farha kam jitai jikinta yai sanyi, a hankali tace “kayi hakuri yayana.” Murmushi taga kuma ya mata, yace “ba haushi naji ba kawai banaso ne.” Tace “to yaya, zan kiyaye.”+ Nan suka fita ya rakata sai dai bai shiga b’angaren fulani ba yace mata ” nizan wuce, sai na ganki gobe.” Tace ” to yayana. ” Salman ya juya ya taho, itakam tana tsaye tana kallanshi har ya kule, kafin ta shiga gida, waya ta d’aga ta kira mumynta, yanda taji muryar mumyn da alama bacci take ma. Farha tace “Mumy natasheki ko?” Mumyn tace “ya akaine Farha?” Farha tace cikin rawar murya ” Mumy ina tsoro fa?” Tace “tsoron kuma me? Kamar ba ‘yata ba? Bansanki da haka ba.” Farha tace ” ina tsoron in na auri yaya Salman da kyar insamu soyayyarsa ko wata kulawarsa.” Mumyn tace ” baya sanki ne?” Farha ta share kwalla tace” Na kasa gane wa Mumy” Mumyn tace ” indai kinasan abu na dade ina fad’a miki ki tabbatar abin nan yazama naki, rayuwa d’aya ce ba biyu ba, kar kizo kiyi dana sanin abun.” Farha tace ” ai abun nan danakeso Mumy dole ne ya zama nawa, ko me mutane zasuce.” Mumyn tace “good, ke dama har kina wani tunanin soyayya? Bayan nasan kinsan komai, a yanda nasanki, ina tunanin ba namijin da bazaki iya karkato dakansa ba, amma kike shirin bani kunya?” Farha ta zauna akan gado tace ” mantawa nai mumy, gashi Salman d’in kwarjini gareshi, ina shirya a d’aki zanyi abu, ina fita sai in kasa.” Mumyn tace “to ko kinaso in ma yaya magana? Nasan dai zai duba maganata duk da ba uwa d’aya muke ba, inya duba hallarcin rike mai Salman danai, bazai ki ba” Farha tace ” haba mumy ni banaso inje gidan wannan ‘yar iskar matar tasa tad’ingamin wani kallo, nafisan in aureshi ta soyayya.” Mumyn tace shikenan sai naji good news tafad’a tare da kashe wayar. Farha tabi wayar da kallo tace ” shiyasa nakesanki Mumyna.” Salman kam yana shiga gida Salma ya gani tsaye a inda ya barta, baice mata komai ba kawai hannunta ya kama yai cikin d’aki da ita, suna shiga ya jawota jikinsa yace “Beauty me yasa zaki tsaya a falo bayan kinsan ba lafiya gareki ba.” Salma ta daure tace ” ina kaje?” Salman yace ” Beauty do you trust me? ” tai shiru can d’aga kanta, Salman yace ” in har kin yarda dani then please just trust me.” Salma ta d’ago ta kalleshi idanunta taf kwalla, tace ” I trust you Prince but I don’t trust that girl.” Salman ya shafo gefen fuskarta sannan ya tsaida hannunsa akan gefen fuskarta, ahankali ta d’ago ta kalleshi idanunta sun cika da kwalla, yace ” just trust me, kinji?” D’aga kai tayi alamar eh, nan ya kai bakinshi cikin nata, salon dasuke ma juna yasa suka gangara kan gado, sun shagala sosai da farantama juna rai, hakan yasa nikuma nai waje. Da safe wajen 10 Salman bayan ya shirya yace itama ta shirya ya ajiyeta a gida, murna agun Salma kamar me, itakanta tanasan zuwa, tana tsakiyar murnarta sai kuna tai kasa da kai, Salman yace ya akai kuma? Ta nunamai inda aka mata d’inki tace ” a haka zani?” Salman yace “zasu gani ko?” Salma tace ” banaso su zargi komai, inciwon ya warke na kirasu a waya.” Salman zaiyi magana wayarsa tai k’ara ya d’aga da sauri ganin Asim ne, yad’aga yace “abokina ya?” Asim ya sanar masa yayi ciko ciko dan haka karfe 5 akwai flight dazai tashi, yai murmushi tare dayin godiya ya kashe wayar. Salma ta kalleshi tace “wani abu ne?” Yace “is a secret bari inje gun mai martaba in dawo” tace to. Dasauri ya fita, yai fadar mai martaba, akamai iso ya shiga, sun gaisa cikin sakin fuska kafin Salman yace yanada magana, jin haka yasa Sarki ya bada umarnin abasu guri. Salman ya d’an matso kusa da Sarki, yace ” Abba akan Farha ne.” Sarki yace “nikaina inasan inma magana akanta.”Salman yace ” name?” Sarki yai shiru can yace ” d’azu da safe mahaifinta ya kirani akan wai Farha na sanka, kuma wai saboda kai tazo nan kasar.” Salman ya had’e rai yace” wannan zancensu ne, ni yanzu tunani nake yau zansa a maida ita kasarsu, dan nakula zamanta anan nema yake ya canza mata hali daga good zuwa bad.” Sarki yai shiru can yace ” bangane canza hali ba? ” Salman yace ” wasu suna amfani da ita akaina, nikuma nasan ta duk da she is not kind amma she is not bad.” Sarki yace ” su waye wad’anan mutanen?” Salman yai kasa dakai yace ” Abba abar maganar kawai.” Sarki yace ” shikenan amma da alama kenan baka san auran?” Salman yace ” Abba yarinyarnan kanwata ce, kuma koba haka bama ni bani da tsarin auren nace biyu. ” Sarki yai murmushi yace ” da alama d’ana yanzu yana fad’amin abinda ke ransa, naji dadi sosai, amma yanzu yazamuyi da iyayenta?” Salman yai wani murmushi yace ” ba wani abun bane ni zan fad’a musu” Sarki yace “good inasan confidence d’innan naka.” Salman yai kasa dakai tare da sosa keya. Kafin sallar la’asar Salman ya dawo gida, bangaren Fulani yai, tana zaune a kilisarta itada Ishaq, kallansu kawai yai yace Umma ina gaisuwa, Fulani haushi ya kamata, gashi agaban bayinta wannan ai cin fuska ne, Salman d’akin Farha ya wuce tare da knocking, ta bude da sauri dan yasanar da ita zuwanza, a kofa ya tsaya yace ” Farha hado kayanki mu fita.” Tace ” kayana kuma yaya?” Salman yace “eh wani gida zan kaiki.” Cikin rashin fahimta tace ina? Salman ya had’e rai yace ” in bakyaso mu barshi kawai, nad’auka zakifijin d’ad’in can da nan.” Farha ta riko hannunshi tace “ya hakuri yayana, bari na had’o” Salman ya jingina da kofa yana jiranta, Ishaq ne ya taho a zuciye, yace ” kai Salman wato dan rashin mutunci, umma kama haka?” Salman ya juya fuska sannan ya kara juyowa da murmushi yace “ahhhhh, dan nace ina gaisuwa?” Yafad’a tare da takawo zuwa gun umma, ya zauna sannan yai murmushi yace ” Umma ashe wai haushi kika ji?” Itama ta kakaro yake tace “haba Salman wani haushi kuma?” Salman ya mike tare da kallan Ishaq yace “kaji ko? Dama yama za’ai taji haushi akan wannan? Intaji haushi ai da matsala.” Ishaq ya kulo yace ” kaifa d’an rainin wayau ne.” Salman ya dafa kafad’arsa ya matso daf da kunnensa yace “rainin wayau ya wuce wanda kamin? Ka d’auka ban sani ba?” Yasaki wani murmushi ya wuce d’akin Farha. Jikim Ishaq ne ya shiga rawa, badai ya sani ba? Me ya ke nufi da kalamansa? Bai fito yace yaganshi ba? To me yake nufi? wad’annan tambayoyin su suka sa jikinsa ya shiga rawa. Sun fito shida Farha, ko kallansu bai ba ya wuce tare da cemata kisameni a mota, Farha ta fito janye da jaka, ta kuma rataya handbag d’inta, ta karaso kusa da Fulani tace “Fulani ni zan wuce, amma zan d’inga lekowa.” Fulani tace “ina zaki?” Farha tai shiru sai kuma tace ” nikaina bansani ba, yayana ne yace infito.” Fulani tai dariya tace “lalai Farha, kawai dan Salman yace ki fito shikenan sai ki fito?” Farha ta mike tare da kallan Ishaq tace ” na wuce.”cikin rawar murya Ishaq yace to.. Sannan ta kalli fulani tace “nagode sosai.” Ta juya tai waje Fulani ta bita da kallo tace “maza, hmmm Allah dai yasa ba hotel yake shirin kaita ba.” Sai kuma ta mike ta saki dariya ta matso kusa da Ishaq tace “Allah yasa hotel d’in zai kaita, da alama ya kamata ka tura mana wannan mai kula da harkokin Salman, ya tabbatar ya d’auko hotonsu inzasu shiga hotel d’in.” Ishaq ya kalleta yace ” Umma na kula baki damu da harkata ba, kawai ke kanki kika sani, burinki kawai inzama Sarki, baki damu da halin da nake ciki ba.” Fulani ta kalleshi tad’anyi siririn tsaki tace ” maganar Salma ce?” Ishaq yace ” har da ita.” Fulani ta dafa kai tace “oh God! Ishaq dan kanasan abu nizan je in jawo maka hankalin abinda kake so? Kaje kayi duk abinda kaga dama.” Tai maganar cikin gatse, Fulani ta d’auka zai bata hakuri, amma sai jitai yace ” yauwa Umma nagode kwarai.” Yanakainan yai waje da saurin shi, tana kiranshi ko kulata baiyi ba. Tace ” Oh God! mai yaron nan yake tunani?” Sun d’au hanya Farha sai jansa take da hira, shidai sama sama kawai yake amsa mata, can yace “Farha?” Jin yanda ya kirata yasa jikinta yin sanyi, tace ” Naam” Salman yace ” I won’t ask you to forgive me, dan nasan abinda nake shirin yi shine dai dai, koda kuwa zaki kulaceni, ki zageni, it won’t matter, nafiso na zama bad guy a kan harkata dake, bazan bari ina kallo halayenki su canza ba, bayan nasanki sarai.” Farha jikinta yai sanyi ta kuramai ido, tarasa mezatace, batai magana ba taga sunzo hanyar airport, kallanshi tai cikin tsoro da mamaki tace ” yayana nasani nayi ma laifi, bai kamata nayarda har nasama maganin bacci ba, amma yayana this is not right, karka wulakanta san danake maka.” Hawaye ne ya zubo mata ta share. Salman shikanshi tausayinta yake, yasani bai kyauta ba amma bazai bari yana kallo takoma su fulani ba. Baice komai ba ya shigaba da tukinsa, Farha kuka take sosai, ya daure yace” garin nakune bakya san zuwa kome?” Farha haushi ya kamata ta d’auka in tana kuka zai tausaya ya fasa tace” nikaine banasan na rabu da gani.” Salman ya sa signal, yace ” Farha kije ki nutsu kiyi tunani, me kikeso?” Farha ta share kwalla tace ” ni yarinyace? A iya sanina ko matarka na girmeta amma kace min ban masan me nake so ba?” Salman ya karasa ciki, ya kira abokinsa, Farha idanta yai ja, kana ganinta kasan taci kuka, Salman bai kara mata magana ba, itama haushin sa yasa taki mai maganar, sai dayaga sun shiga check out sannan ya juya ya hau mota. Waya ya d’auka ya mata transfer na kud’i 100 thousand, sannan ya ja mota yai waje. Ishaq kam bangaren Salma ya nufa direct, sai wani gyara kwalar riga yakeyi, yana shiga ya kalli bayin gun yace “Salma fa?” Hanne tace tana ciki. Ishaq ya kalleta yace ” an bani sako ku jira a waje bari in shiga ciki.” Yana shiga ya saki labulan falon ya fara kallon part d’in, randa yafara zuwa dayake fada ne yakawoshi bai kalla dakyau ba, amma irin nashine kawai dai ya kula furniture’s d’in nan sunfi nashi, d’akin daya tuna Salma ta fito daga ciki wancan zuwan ya karasa tare da yin knocking. Salma dake zaune tana gyarama Salman wardrobe yasa ta mike a hankali tai kofa, ta bude. Ganin ba kowa yasa ta fito falon sosai, Ishaq dake tsaye jikin labule yai sauri ya shige d’akin, Salma ganin ba kowa yasa ta koma d’akin tare da rufowa, sai dai batasa key ba. Tana zuwa wajen gado taji an rungumota ta baya, murmushi tai tace ” My Prince dama kaine?” Jin kanshin bana Salman ba gashi yayi shiru yasa cikin mamaki ta kai hannunta kan hannunsa dake cikinta, inaaaa ba hanun Salman bane, da karfi ta fizgeta juyo cikin tsananin tsoro. Wazata gani? Ishaq? Tsoro ne ya kamata cikin rawar murya tafara baya baya tanacewa ” yarima menene hakan?” Ishaq ya matso yace ” Salma please ki taimakenk, nikad’ai nasan me nakeji in na ganki, Salma zan mutu saboda ke.” Salma tace” me kake fad’a? Kamasan me kake fad’a? Matar kaninka ce nifa? Ko ba matar kaninka bace ni ai da kunya ka kalli mace kad’inga mata zancen banza.” Ishaq ya fara matsowa, Salma kam zuciyarta bugawa kawai take, wayarta ta hanga dake kan madubi ba damar kiran Salman, ganin yanda Ishaq ke tahowa yasa cikin tsoro ta d’au pillow ta tare gabanta, sai dai tana cikin matsawa sai jinta tai a bango, duka kawai take kaiwa da pillow cikin fad’a tana cewa “ka fita, zan sa ihu fa?” Ishaq kam sai daya karaso, ya rike pillow d’in tare da fizgewa da karfi ya cillar dashi, hannunta yariko da karfi, Salma ta kaimai cizo, amma ina ko ajikinsa, ihu tasa sai dai bataga kowa ba, ihu take sosai, ga Ishaq ya dage so yake yakai bakinshi nata, sai cemata yake ” Salma kitaimakeni kamar yanda Allah yataimakeki.” Salma ganin yakusa kai bakinshi nata yasa ta kwallama Salman kira da karfin gaske, jisukai an bude kofa da karfi kamar za’a balla, Isahq6 ya juyo dan yaga ko wani d’an rainin hankalin ne. Salma kam kuka take sosai, Salman ya tsaya a jikin kofa kamar zaki, idanunwashi sun canza kala, fuskar nan a murtuke, a hankali Salma ta bud’e ido, ganin Salman yasa ta fizge hannunta daga gun Ishaq daya zama gunki, jikinsa sai tsuma yake, itakam da gudu tai gunsa ta rungumeshi tana kuka. Salman kallan ishaq kawai yakeyi kallon dashi kad’ai yagama tsorata Ishaq jiyai har hanjinsa kad’awa suke, yama rasa me zaiyi, gashi bai cinma burins ba, amma ya d’auka hotel suka tafi da Farha.