NI DA PRINCE CHAPTER 17
Salman cikin zafin rai yad’an daga Salma daga jikinsa yai kan Ishaq, yanda Ishaq yaga Salman yayo kansa yasa yai baya yana cewa ” Salman tsaya kaji, ba abinda kake tunani bane, gani nai kamar matarka batada lafiya shine nakesan tai maka…….” ai kafin ya karasa jiyai an kaimai naushi da kafa a baki, jikake tim, Ishaq ya fadi, ga inda Salman ya bigeshi yafara jini, Ishaq ya d’ago cikin tsoro dajin zafin bugun ya kalli Salman yace ” Salman nifa yayanka ne? Me kakemin haka?” Salman ya matso inda yake ya shako wuyan rigarsa cikin b’acin rai yakara kaimai naushi, Salma kam tsoro ya kamata, karasawa gunsa tai ganin yanda yake naushin Ishaq, dafashi tai cikin hawaye tace ” Prince ka bari please.”+ Sai a lokacin hankalin Salman ya dawo jikinsa, ya kalli Ishaq da bakinsa sai jini yake, duk fuskarsa tayi jaaa da alama anjima kad’an gun zai kumbura. Mik’ewa yai daga kan Ishaq d’in sannan yasa hannu ya kamo hannunsa, yai hanyar waje dashi, sai daya fita dashi daga part d’insa yana zuwa kofar ya sakeshi ya nunashi da hannu, ya kuma kasa magana, da alama hannun kad’ai na kula yagama tsorata Ishaq, ga bayi da fadawa sai kallansa suke, suna gulmar abin. Salman ya rufo kofarsa da karfi yai ciki, Salma kam suna fita ta zube agun ta shiga kuka, meke faruwa kuma? Salman ya bud’e kofar ya shigo, ganinta a zube tana kuka yasa yaji zuciyarshi takara karaya, a hankali ya karasa inda take, yana zuwa ya zauna kusa da ita, ya jawota jikinsa, kuka takeyi shikanshi ji yake kamar yai kukan ga kanshi dake sara mai yana rike da ita yaji kirjinsa ya shiga zafi, ga yau harda bayansa, Salma gani tai yana kankameta da karfi ga sai durkusawa yake. D’agowa tai cikin tsoro, takalleshi, ganin yanda yake yasa ta rikece, tace “ciwon ne?” Magana take cikin kuka, Salman kam ya kasa magana cikin rud’ewa ta mik’e ta shiga neman maganinsa, sai dai ta rasa shi, a kid’ime ta matso tace ” Prince ina maganin?” Ganin kamar baya iya ma magana yasa jikinta ya shiga rawa, kawai tad’au wayarsa ta duba contact, number waziri taga an rubuta a jiki da sauri kawai tai dialing, waziri ya d’aga yace ” Yarima ya kake?” Salma cikin tsoro tace ” Waziri nice, ku turo likita d’an Allah Salman ba lafiya.” Yace ” ki nutsu Salma me ta sameshi?” Salma ta kalli Salman gani tai ya tintsiri ya kwanta yana murkususu, ai batasan sanda ta yarda wayarba tai kansa, tana jijigashi da jiran sunansa. Waziri da sauri ya kashe wayar, dama yana zaune kusa da Sarki ne, tunda Sarki yaji ana Salman ba lafiya duk ya rikice, kawai dai yana zaune ne amma gaba d’aya hankalinsa yagama tashi, waziri ya d’aga waya ya kira likitansu, suna gama waya ya kalli Sarki yace ” ko jokin ne?” Sarki ya kalleshi yace ” kai sauri kaje ka dubashi, amma me ya faru dashi haka?” Kafin waziri yai magana wanj bafade ya shigo yace waziri da matsala fa? Waziri ya kalleshi yace ” matsalar me kuma?” Bafaden ya kalli Sarki sannan yai kasa dakai, Sarki yace ” fad’i maganarka ba komai.” Bafaden da gulma ke cinsa yai kasa dakai yace ” Ranka ya dade tuba ina kunyar sanar dakai wai an kama yarima mai jiran gado, a d’akin Salman.” Cikin rashin fahimta Sarki yace ” ban fahimci me kake san fad’aba, an kamashi kamar ya?” Waziri daya fahimci me maganar bafaden ta nufa, ya kalleshi yace tashi kaba mutane guri dama can munafirci kazoyi, ka kuma tsumayi hukuncin abinda kai.” Waziri yana ganin mutumin ya fita ya kalli Sarki yace ” da alama Isahq ne dalilin tashin ciwon Salman.” Sarki ya kalleshi yace ” kana nufin d’akin da ake nufi ana nufin gun katar Salman ko me? Indai har ciwo ya tashi alamar ba karamar magana bace.” Waziri yai shiru, ganin haka yasa Sarki ya mike cikin tsananin tashin hankali yace “wani hauka da dabanci ne wannan?” Waziri yai shiru aranshi yace ” Salman kam ai yana ganin abu agun mutanen nan, badama nai magana ko na fad’ama, kar nima abu yashafe ni dan nasan halin fulani sarai.” Jiyai Sarki ya kalleshi cikin tsananin b’acin rai yace ” wato ba wannan ne abu na farko da akemai ba kenan? ” Waziri ya d’ago cikin tausayi yace ” yazanyi Ranka ya dad’e?” STORY CONTINUES BELOW  Jin haka yasa Sarki yai baya tare da girgiza kai zama yai a kujerarsa, a runtse ido, a hankali yace “Salman mena aikata gareka?” Waziri ya mik’e jiki a sanyaye yace ” bari inje gun Salman kila likitan ya iso.” Sarki ya mik’e yace “muje tare.” Salma kam duk tagama rud’ewa, banda kuka da rungume Salman ba abinda takeyi, Mik’ewa tai ta shiga duduba drawers tanayi tana hawaye, sai dai sam tarasa maganin Salman, jitai an kwakwasa d’akin cikin sauri ta bud’e, wani mutum tagani, da karamar jaka kamar akwati, ai bata tambayeshi ba kawai tai tunanin likitane tace gashi nan, cikin sauri ya shigo, ganin Salman a wani hali yasa ya shiga bashi taimakon gaggawa, Sarki da waziri ne suka shigo, Sarki yanda yaga Salman ranshi ya kara b’aci ya kuma ci alwashin ba Ishaq ba ko Fulani indai tanada hannu acikin abinda akema Ishaq wallahi bazai kyalesu ba. Likitan ya dade akanshi kafin Salman ya samu nutsuwa, bacci ne ya d’aukeshi, Sarki cikin tausayin d’an nasa ya matsa kusa dashi, Salma ya kalla dake zaune akasa jikin gadon idanta harsun kumbura jiyai idanunshi naneman kawo kwalla, ace d’anshi da matarsa suna cikin wannan hali shi yanacan akan kujera baisan meke faruwa ba? Kallan waziri yai yace “akira Ishaq da Fulani su sameni a fada, sannan a duba matarsa a tabbatar ba abinda ke damunta, sannan a kara kiran likitan da akace zai ma Salman aiki aji yaushe zai iso.” Likitan ya amsa da toh. Sarki ya mik’e har yakai kofa ya juyo yakalli Salma yace ” Salma taso inasan magana dake.” Salma ta amsa tare da mik’ewa. A fali ya zauna, itama taje tare da zama a kasa, ya kalleta yace ” Salma ki dubi Allab da matsayina agub mijinki na mahaifi, ki fad’amin meke faruwa tsakaninsa dasu fulani ko ince tsakaninku, tunda ance neman haik’e mike yaso yi.” Salma ta kalleshi hawaye ya zubo mata tace ” Abba bansan kezance ba, nadaisan kawai basa kyauata mishi.” Sarki yace ” hakan ma nagode tunda har baki karyata zuwan Ishaq bayau hakan ya tabbatarmin yayi abinda akace.” Salma ta share kwalla, ta daure tace ” Abba in zamanmu zai zama matsala anan ka amince mu bar nan gidan dan Allah.” Sarki ya had’iyi wani abu yace ” Salma bazan bari Salman yabar nan ba, dan kuwa shine magaji na, sai dai na miki alkwari ba abinda zai kara samunku daga ke har shi, kuma duk wanda yasan da hannunshi acikin abinda akamai ba shakka sai ya gamu da fishi na.” Ya mik’e tare dayin waje, Salma tabishi da kallo hawaye ya zubo mata. Duk sun fita sun bar Salma agun Salman, hannunsa ta rike kam tana kallansa, bayan magrib taga a hankali Salman yad’anyi motsi da hannunsa, ta matso ta kalleshi tace ” Prince!!!” A hankali taga yafara bud’e idanunsa cikin kuka kuka_ dariya dariya tace ” Prince are u alright? ” Salman ya kalleta tare da jawo hannun ta data rike nashi, daf tazo kusa dashi, Salman yasa hannu ya share mata hawaye sannan ahankali yace” wannan matar tawa akwai raguwa, tafiya saurin kuka.” Salma ta kalleshi sannan tasa d’ayan hannunta ta share kwallar data zubo mata tace ” bakasan yanda na tsorata bane.” Salman ya mik’e zaune sannan yasa hannu a wuyanta yad’an jawota suka matso daf da juna dan suna iya jiyo numfashin d’ayansu, a hankali Salman yace ” yanzu dai na warke ai sai adaina sa idanuwan danafiso a duniya sudaina zubar da hawaye.” Salma ta sa hannu ta rungumeshi, a hankali ya d’agota tare da tsotsen lebenta yace “I luv u Salmah.” Lumshe ido tai wasu hawaye ne zuka zubo masu sanyi, murmushi Salman yai ya tsaya yana kallanta, ahankali ta bud’e idanunta,wani kallo tamai da ita kanta batasan tayi ba, ajiyar zuciya yai yace “ahh lalai na yarda matatace vitamin A d’ina da alama har naji karfin jikina ya dawo, Salma cikin shagwaba tace ” kai Prince banda zolaya.” Salman yaja kunnenta da d’an karfi har saida tai kara yace ” wayace ki d’inga bud’ema kowa kofar d’akin nan?” Salma tace ” Prince dazafi fa?” Yace “nasani ai, Laifi kikai ake hukuntaki ai , dabanzo bafa? Wayasan me shashashancan zaiyi?” Salma ta riko hannunsa, ya saketa ta kalleshi tare da hararrar sa tace “ji kunnena fa yanda yai jaa.” Salman yace ” au bama amsa zaki bani ba?” Salma tace ” nafa d’auka kaine, to da aka kwankwasa kuma na duba banga kowa ba, nifa banma san sanda yashigo ba, sannan kai ina kaje?” Salman yace ” daga yanzu kidaina bud’ema kowa sai kinji waye.” Tace naji ” amma kai fa ina kaje?” Yace ” ina kuwa naje?” Ta mik’e tace ” anfa cemin kun fita da Farha? Ni ina nan na d’auka wani abu mai mahimanci kake ashe kanacan ka biyema Farha kuna yawo, duk sanda nakawo kaina damaka magana akanta sai naga kamar bazaka ji dadi ba, sai dai nafara tunanin kamar ina cutar kainane nayin shirun danake.”+ STORY CONTINUES BELOW  Salman ya kalleta yaga yanda ta had’e rai, yace ” oh ni Beauty kema fa ba sauki, irin wannan rufeni da fad’a haka? Kamar wanda nai wani laifi?” Tace “au wannan ba laifi bane Prince?” Tafad’a tare da mik’ewa, dasauri Salman ya ruko hannunta, ta fizge tare da cewa ” bari in d’auko ma ruwa kasha magani.” Salman ya bita da kallo, yasani sarai tamai kara sosai akan Farha, to amma bata tsaya taji ma ya maidata ba, yana zaune har ta dawo, ta bud’e robar ruwan ta tsiyaya a cup sannan ta b’allo magungunan ta mik’amai, yana kallanta ya amsa yasha, ta rufe rowan zata juya Salman ya riko hannunta, ta jiyo ta kalleshi ta kuma kasa magana, Salman ganin yanda ta had’e rai yasa kawai ya rike kirjinsa yace “ahh Beauty kirjina” Salma ta matso a rikice tace ” jikin ne? Nashina, ko inkira likitan? Wayyo ni?” Salman ya kalleta yai murmushi yace ” kin hakura?” Salma tace “what? Au tsokana ce? Pillow ta d’auka ta makamai ya rike pillow d’in yace ” patient ne fa?” Ta zauna tare da cewa “amma nikam Prince tunda kake ka tab’a cema wani sorry ko yi hakuri? Salman yai shiru yace ” badai saboda haka kike ta wani kara had’e rai ba?” Ta juya kai tace ” ni na fad’ama? Yai dariya yace ” dagaske kuwa saboda hakan ne” Salma ta mik’e tace ” nidai ban fad’aba, ammm mai martaba fa yazo.” Salman yace haba? Tace ” yazo naji kuma yace a kira Fulani da Ishaq.” Salma ya mik’e zaune yace ” bari inje Beauty. ” Tace to. Salman ya mik’e tare da fita. Sarki kam zaune yake shida Fulani da Ishaq, ya kalli yanda fuskar Ishaq tai luhu luhu dan duka, ya kuma kalli Fulani dan da alama itama yanzu taga fuskar Ishaq d’in ganin yanda taketa kallansa da b’acin rai. Sarki yai gyaran murya ya sallami kowa ya rage saura su uku, ya kalli Ishaq cikin d’aurewar fuska yace ” kai me kajeyi d’akin Salman, cikin ma d’akin matarsa?” Dasauri Fulani takalli Ishaq, d’akin matar Salman? Ishaq yai kasa dakai gabanshi sai fad’uwa yake, cikin in ina yace ” Abba ni ban tab’a zuwa ma d’akin Salman ba.” Sarki yace ” kai ni zakama karya? To dukan fuskar ka fa? Waye yamaka?” Ishaq yai tsuru_ tsuru yace ” uhm uhm….” Fulani tace ” haba mai martaba yazaka tambayi d’anka wai ko ya shiga d’akin matar kaninsa, yama za’ayi hakan tafaru? Ko gulma aka kawoma ai bai kamata ka yarda ba, inma ahi Salman d’in me ya fad’i haka to yayi karya dan kuwa Ishaq yafi karfin yaje kwartanci d’akin sa.” Ran Sarki ya b’aci wato dama duk wani so datake nunamai nasan Salman agabanshi karyane, Sarki ya kalleta cikin b’acin rai yace” kin tabbatar in nai bincike aka tabbatar da hakan duk hukuncin danamai sai ya shafeki, kuma ba matsala?” Fulani tai shiru ta kara kallan Ishaq zatai magana taji sallamar Salman, cikin kid’ima suka juya duk su biyun , Fulani ta had’iyi wani yawo, Ishaq kam jikinsa ya shiga b’ari, Salman ya karaso ya zauna kusa da Ishaq, ya gaida Abba sannan ya kalli Ishaq sannan ya kalli Fulani ya gaidata, ta amsa a d’am tsorace. Salman ya kalli Ishaq yace “yaya ya akai kaji wannan ciwon? Badai neman matar wani kaje ba aka ma dukan tsiya?” Ishaq ya kalleshi yana kif kif da ido yace” wani irin neman matar wani kuma?” Salman yai wani mugun murmushi sannan ya kalli Fulani yace ” Umma d’azu na kama wani yazo har cikin d’akina yana neman la lata da matata, banga fuskarshi sosai ba amma nasan namai bugu mai karfi, yaza’ayi? da alama sai an tara mutan gidan nan an nemoshi dan bama tunanin zan iya kyaleshi.” Fulani a tsorace ta kalli Ishaq sannan ta kalli Sarki ta kuma maida idanta kan Salman tace ” uhmm bai kyautaba kuwa ko waye.” Salman yace “good ashe kin gane umma, ke a tunanin ki ni namijin da zan yafe hakan ne?” Fulani ta kara had’iyar yawo da kyar tace ” a’a ammq ya kamata ka sassauta tun balle in wanda yama laifin d’an uwanka ne.” Salman ya kalleta yad’anyi murmushi yace ” inafa! Ai in d’an uwa nane ma shine bazan yafe ba, balle wanda ya shigo d’akin nasan shine wanda ya kusan kad’eni a titi matata ta tare.” Ai a tare zuciyarsu ta buga da karfi, Ishaq da sauri ya tsugunna yace ” Salman dama ka ganni sanda na kusa bigeka shine ka ki fad’amin ko? Sannan matarka wallahi tunda naganta naji……..” dasauri Fulani ta katseshi da karfi tace ” ISHAQ” STORY CONTINUES BELOW  Sarki kam Salman ya gama burgeshi, gashi ta hanyar sauki yasa Ishaq ya fad’i abinda ya aikata lalai ba shakka wannan inya zama sarki mutane zasuji dadi dan da alama bazai yarda da injustice ba kuma duk inda mutum yakai da boye abu zai sa ya sanar dashi ta hanya mai sauki, kallan Salman yai cikin tsananin so sannan ya kalli Ishaq da duk ya rud’e ya kuma kalli Fulani da ke hararar Ishaq ta gefen ido. Salman ya kalli Ishaq yace ” ahhh so matar kaninka kake so shine kaje d’akinsa?” Ishaq yace ” nifa ba haka nake nufi ba.” Fulani tace ” wai Salman meye hakan? Kasa yaro a gaba kanata bugar cikinsa, to bazan yarda ba, nasani sarai Ishaq d’ina bazaije gun wata matar ka ba mai kama da aljanna.” Salman yad’anyi dariya yace “Umma I feel hurt, wato ni ba naki bane bako?” Fulani takalli sarki tai kasa dakai tace “nifa ba haka nake nufi ba.”+ “Ohhhh nagane me kike nufi, amma umma bakya ganin bai kamata kice nasa yaro agaba ba? Yanzu kamar Ishaq a kira shi yaro? Yafa girmeni?” Salman ya fad’a yana mata wani kallo. Fulani kam ta tsani Salman yasata agaba duk ya rikitata haka, bare yau agaban Sarki tama rasa me zata ce. Ishaq yace” niba yaro bane, nasan kuma duk abunda nakeyi, yama za’ayi kid’inga kirana yaro agaban Salman?” Sarki yai gyaran murya hakan yasa kowa ya nutsu,cikin b’acin rai ya kalli Ishaq yace “kenan dagaske ka shiga d’akin Salman kaje neman matarsa?” Ishaq yace ” Abba ba haka bane..” “To ya ya ne? Ko inkira matar tawa ne? Ko kuma kanaso in kara maka dukan dana ma d’azu ne?” Jiyai Salman ya katseshi da wad’an nan kalmomin. Ishaq ya kalli Salman a rikice yakuma kalli Fulani datake makama Salman harara ta gefe, yai kasa dakai tare da runtse ido. Salman yad’an tab’e baki ya kalli Sarki, sannan ya kalli Ishaq yace ” nikam yaya waye ya kaimu asibiti ranan da mukai karamin accidents d’inan?” Ishaq cikin zumud’i ya d’auka wani abu ne yace ” nine mana, nina kaiku.” Fulani zatai magana Sarki yace ” kar inkuskura inkara jin bakinki anan tunda badake suke ba.” Salman yai murmushi yace ” Ayya yaya nagode, dabadan Allah yakawo ka ba bansan mezai faru da Salma ba.” Ishaq ya sosa keya cikin farin ciki yace ” ai duk lefinka ne, mezaisa ka bari Salma ta tarema, nifa kai……..” Kara Fulani ta saki, hakan yasa Ishaq yin shiru, Salman ya kalleta yace ” aya Umma ta shiga wani hali, yazakiyi Umma gashidai Ishaq yafad’i komai da bakinsa.” Ishaq ya kalleta yace “Umma inafa da wayau hauka nake zan fad’amai, karyar Salman ne kawai yana za’ayi yasan nina je bigeshi bayan bai kula ba? Sai dai in yau yake nufi, wannan kuwa ai shiyakamani…..” Fulani mik’e wa tai cikin b’acin rai ta zo kusa dashi ta haska mai mari, tace wlh Ishaq nikam banyi sa’ar d’aba. Sarki ya fusata yace ke Sakina! Ai duk fadar sai da kowa ya juyo, cikin sanyin jiki Fulani ta zauna Ishaq kam ido yai wuri wuri, Sarki cikin b’acin rai yace “banataraku anan bane kowa yai abinda yaga dama ba, kuma duk abinda kukama Salman dake da d’anki karkuyi tunanin zan kyaleku, ada na d’auka kina kula da Salman, a’a koma bakya kula dashi banyi tunanin zakuma ku had’u keda d’anki ku muzguna ma Salman ba, yanzu da sanda ya bige Salman ya mutu fa? Sannan ko kunya harya samu damar shiga d’akinsa neman matarsa? Gidana yakoma gidan dabobi kenan ko me? To wlh daga shi har ke dakike biyemai sai kun fuskanci hukunci mai tsanani.” Ishaq yasa kuka yace ” Abba d’an Allah kayi hakuri nasan nayi laifi, wlh ni tun ina karami da k’in Salman na taso, kullum umma zancenta d’aya ne kar in kuskura in bari Salman ya wuceni akomai.” Sarki ya kalli Fulani datai kasa da ido, da alama itama kwalla ke zubo mata. Sarki ya kalli Salman sannan ya kalli Ishaq yace ” na cireka a matsayinka na yarima mai jiran gado, sannan nakuma bama Salman wannan mukamin.” Fulani ta d’ago ta kalleshi cikin tsananin b’acin rai tace me kake nufi mai martaba? Ishaq shine babban d’anka a tunanina duk abinda yai zaka yafemai tunda shine magajinka kuma ni danake uwar gida, Fulani nice ya kamata d’ana yazama Sarki.” Jitai Sarki yace ” ahh namanta, gwara da kika tunamin kema ina sanar dake matsayinki na Fulani na cireshi daga yau…….” Salman yace ” Abba!!!” Sarki yace ” kamanta na sanarma bazan yafema duk wanda ya nemi kad’eka ba? Sannan ko kunya Ishaq ya nemi matarka? Kuma duk nasan lefin mahaifiyarshi ce.” Fulani cikin kuka tace” Alhaji ni zakawa haka? In ka cireni daga mukami na nida Ishaq alama ce ta mu mutu kawai, dama nasan ba sona kake ba, amma duk da haka bai kamata kamin haka ba.” Sarki yace ” kin d’auka shi kad’ai ne? Nasani sarai in na kauda Ishaq zakiyi tunanin saka Mannir ko wani daga cikin d’anki, bazaki tab’ajin kunyar abinda d’anki ya aikata ba, dan haka na yanke hukuncin dolene kibar nan gidan ki koma can karshen gida( inda ake kai iyayen sarki insun tsufa sosai ) anan zaki zauna.” Salman yace ” Abba? Hukuncin kamar yayi tsauri.” Sarki bai bashi amsa ba ya kalli Fulani dake kuka sosai tana bada hakuri, sannan ya kalli Ishaq yace kaikuma kashirya kaida iyalanka kubar nan ku koma kasar Egypt dazama kada kuma kadawo har sai in nina bada izinin hakan.” Abba yana gama fad’ar haka ya mike yai cikin gida, Fulani tasa kuka, Ishaq ma kuka yake sosai yana cewa “Salman d’an Allah kataimakemu, ni wlh duk Umma ce, laifina d’aya danafara san Salma wannan kuma Salman kasan ba laifina bane laifin zuciya ne. ” Salman ya kalleshi shikanshi tausayin hukuncin da Abba ya yankr yakeyi. Salman ya kalli Ishaq duk sai kuma yaji Ishaq d’in na bashi tausayi, Waziri ne ya shigo ya kalli Salman yace ” Yarima mai martaba yace ka ciga ciki.” Salman ya kalli Waziri yace ” Toh” mik’ewa yai ya d’an bugi kafad’ar Ishaq sannan ya kalli Fulani dake kuka yai ciki, Fulani tabishi da harara tare dacewa” niza’a wulakanta akan wani banza Salman? Wlh Sarki yayi kuskure.” Ishaq ya matso kus da ita ya riko hannunta yace “Umma kitaimakeni kisa abarni akasar nan, ni wlh na tsani wata kasar.” Fulani ta wafce hannunta tace ” wato kanka ka sani kad’ai ko? Ni baka tausayin inda za’a kaini? A k’alla in na zauna acan kila sai nayi wajen sati 3 zuwa wata kafin ‘ya’yana suzo su ganni.”+ Jisukai Waziri yace ” ku fito daga fad’a ba gurin hira bane, sannan kai yarima Ishaq katabbatar ka shirya d’an gobe zaka wuce, sannan Fulani au hajiya kema ki had’a kayanki yau dan gobe da safe zaki koma.” Yana kainan yai waje, Fulani ta zuciya tace “me? Au hajiya? Sai na ci*********, ” Ishaq ya kalleta yace ” nidai Umma yanzu ba lokacin wani zagi bane ya kike so nayi?” Fulani ta watsamai wani kallo tace ” duk ba kaikaja ba d’an rainin hankali, dalla matsamin.” Ta fad’a tare da wucewa. Ishaq ya dunkule hannu ya naushi bango, yace ” ni dai rayuwa ta gama b’aci, bansamu Salma ba, bansami mulki ba, garin muma yanzu ya fi karfina.” Shima waje yai jiki a sanyaye. Abinda zai baka mamaki kafin si fita zancen har ya yad’u agidan Sarki, suna tafiya bayi na kallansu suna d’an gulma. Salman zaune a gaban Sarki, Sarki yace” hukuncin baiyi ba kome?” Salman ya kara kasa dakai yace “a’a ba haka nake nufi ba sai dai ina ganin kamar hukuncin ya musu tsauri. ” Sarki yai murmushi yace ” mutanen da sukaso yin kisa? Da kuma hukuncin neman matar wani? Shine kake cewa d’an wannan hukuncin yai musu yawa? To ko kotu zan kaisu? Sai a banbance wanne yafi tsauri.” Dasauri Salman yace ” a’a Abba masan can sai yafi tsauri.” Sarki yace ” karka wani damu da wannan, ka maida hankalinka akan karatunka, inka gama kazo ka amshi mahaifinka.” Salman yai shiru….. Hakan yasa Sarki yace ” yaushe zaku fara jarabawa?” Salman yace ” saura sati d’aya.” Sarki yace ” good gwara ku gama kafin lokacin da likitan nan zai iso.” Salman yai murmushi tare da cewa ” amma Abba taron nad’in daza’amin a bari sai nagama ganin likitan.” Sarki ya d’aga kai yace ” hakan ma is a good idea.” Sunyi shiru kafin Salman yace “bari inkoma Abba, sai da safe.” Sarki ya amsa mai, nan ya mike yai waje. Mutane sai tayashi murna suke, shidai tafiyarsa kawai yake ba wanda ya amsawa, b’angarensa ya nufa, Salma na zaune a falo duk da ba kallo takeyi ba amma ta kurama tv ido, hankalinta nakan abinda hanne tace mata wai anba Salman yarima mai jiran gado, batama san sanda Salman ya shigo ba ya tura kofar tare da matsowa saitin wuyanta ta baya yace ” me Beauty take tunani?” Da sauru ta juya d’an tad’an tsorata, tace “haba Prince nafa tsorata. ” tai maganar cikin shagwab’a, shima kwaikwayar tata maganar yai yace ” nima na tsorata” yasa mata d’ariya tad’an d’akeshi kad’an ya rike hannun tare da d’agota tayo jikinshi, hannunsa yasa a k’ugunta yace ” bari mu gani ko Beauty tayi missing d’in mijinta sosai?” Yafad’a yana duba fuskarta, saurin rufe idanta tai, tace ” ta ina ake gane wa?” Yace in nuna miki? Ta d’aga kai. Batai auni ba taji bakinshi anata, sosai yau take maidamai sun shagala sosai, kafin su saki juna, ahankali suka bud’e ido tare dayima juna murmushi, Salman ya kamo hannunta yai d’aki da ita, suna shiga ya rufe kofar ya tsaya ajikin kofar, ta matso kusa dashi tace ” Prince baka fad’amin. ……jawota yai yakara kai bakinsa nata, nan suka kara tsundumawa cikin shauki, nikam har yanzu ban manta da korar da Salman yamin ba hakan yasa nai sumsum sum nai waje, tare da kara rufo musu kofar. Bayan sun gama Salman yad’au Salma ya kaita toilet tace ” au toilet d’inma bazan iya zuwa ba ko me?” Salman yace “banaso a wahalar min da baby na.” Tace uhmmm…..harzai fita ta riko hannunsa, ya kalleta tare da mata alamar tambaya, itama dakai ta nunamai, ya kara mata alama dakai na bai gane ba, murmushi tai tace ” muyi tare, ” shima murmushin yai yace “ahhhh yau naji dad’i na. STORY CONTINUES BELOW  Sunyi wanka sun fito, Salma ta wuce falo tad’an zubo ma Salman abinci kad’an a plate, ita da kanta tabashi, sai daya gama yasha ruwa sannan ta maida tare da hawa kan gadon, Salman ya jawota jikinsa yace ” Beauty akwai matsala fa? ” ta kalleshi tace name? Nan ya sanar da ita abinda ke faruwa. Tai shiru, kafin can tace”Allah yasa hakan ne mafi alkairi.” Salman yace “Amin, amma Beauty nifa banasan harkar mulkin nan, duk abi a hana mutum sakewa, ni dake fa sai lokaci_ lokaci ni kuma banasan hakan.” Gabanta ne ya fad’i tace “lokaci_ lokaci? Muna gida d’ayan?” Yace” hmm yanzu in akaban me jiran gado, nasan halin mai martaba abubuwa zai d’inga sani, kinga zama na dake dole zai rago.” Salma ta kalleshi jitake kamar tai kuka, sai dai tana tunanin ko bazata ji dad’i ba dolene ta karfafama mijinta, tace ” to menene baga waya ba? ” tafad’a tare da nuna wayarta, yace uhmmm, ta shige jikinshi tace ” bacci nake ji. Ta dade batai barci ba, har Salman yai bacci, tai shiru tare da kura mai ido itakad’ai tasan meke ranta. Ishaq kam da Fulani da matan Ishaq bana tunani sunyi barci dan dukansu ba wanda yake farinciki.