NI DA PRINCE CHAPTER 18 KARSHE
Da safe Salman yace Salma ta shirya yakaita gida, bayan ya kaita ya gaisa dasu Abba sannan yajuya ya koma gida, sam bayasan Salma takasance a gida arana irinta yau da gidan zai kasance a hargitse.+ Waziri da wasu fadawan ne sukazo suka tsaya a b’angaren Ishaq har sai da matanshi suka gama had’a kaya, kana kallan fuskokinsu kasan tabbas suna cikin bakin ciki. Fulani kam kuka sosai tai cikin dare sai dai da safe tana zaune tana kallan bayinta na had’a mata kayanta, ita kad’ai tasan bakin cikin dake damunta ga rabuwa da d’anta, matsayinta sannan korarta da akai, kana kallanta kasan bakin ciki ne fal zuciyarta. Salman yafito yai b’angaren Ishaq, ganin su waziri a tsatsaye yasa shi mamaki, karasawa yai suka gaisa ya tambayesu meke faruwa yagansu haka? Waziri yace” mai martaba ne ya umarcemu da mu tabbatar mun tsaya harsai Ishaq ya bar gidan nan ya shiga jirgi.” Salman ya kalli Waziri yace ” haba a tunanina ko ba’a tsareshi haka ba zai tafi dakansa tunda yasan umarni ne ba shawara ba.” Jiyai Ishaq yace ” Salman inasan magana dakai.” Salman ya juya ya kalleshi duk ya canza a kwana d’aya, binsa yai suka d’an keb’e, Ishaq ya kalli Salman yace ” Salman nasani tunda kadawo kasarnan nake muzguna ma, bana kunyar yimaka sharri ko agaban mai martaba ne, ko ba’a fad’aba nasan bai kamata inma d’an uwana haka ba, amma azahiri kai kasan duk inda gidan sarauta yake to tabbas akwai hassada, kyashi da kuma san kai a ciki, sai dai bazan nemi yafiyar ka akan sharrin dana maka ba, dan nasan ko kaine ba shakka hakan zakayi, sai dai zan nemi yafiyarka akan abu biyu, na d’aya bigeka danaso yi, sannan neman matarka danai.” Yana kai nan yai ajiyar zuciya idanunsa suka cika taf da kwalla. Salman ya kalleshi cikin tsananin tausayi, ya runtse ido sannan ya bude tare da cewa” Mubar zancen nan, dana yanzu dana da banasan adinga tunowa, abu d’aya nakeso kasa aranka, a duk inda kake kazama mai so wa d’an uwanka abinda kake sowa kanka, karka manta wannan kalmar hadisi ne sahihi, duk wani abu daya shiga tsakanina dakai nayafe ma.” Ishaq ya kalleshi cikin hawaye ya riko hannunsa cikin kuka yace “Salman please take care of my mother, nasani she is so greedy, amma tunda nake da ita bata tab’a bani shawarar neman Salma ko kad’eka ba, duk da batasanka.” Salman ya dafashi yace ” karka damu I will take care of her, amma inkaje can me zakayi?” Ishaq yace ” ban mayi wannan tunanin ba.” Murmushi Salman yai yace ” u have to make plan, dan karkaje kawai kace zama zakai kaga dai zama ne bama shekara ba, mayb inka tafi ba dawowa zakai ba.” Ishaq yace ” nagode Salman.” Salman dakanshi yakaisu airport da azahar suka tashi, baiji dad’in yanda Sarki ya had’ema Ishaq rai ba dayaje masa sallama. STORY CONTINUES BELOW  Yana dawowa gida yatadda Fulani har ta tattara ta koma, yai ajiyar zuciya yace ” why am I feeling so empty? ” Salma kam taji dad’in zuwa gidan nan tayi mamakin yanda aka gyara gidan, sam bazakace gidansu ne na da ba, goggo sai janta a jiki take, sun sha hira da Abbanta, nan ya fad’a mata ai kamal ya kusa komawa kasar waje d’an yin masters d’inshi, takalli Abba tace ” Abba zanma Salman magana, akwai naga mutanen da ake d’eba na scholarship a gidan Sarki, duk da dai naga ‘yan uwane yawanci amma nasan in namai magana zaisa sunanshi” Abba yace kina ganin ba matsala? Tai dariya tace ” yasan komai Abba ba wata matsala. ” Salma duk yanda taso suyi hira da umma amma abin ya gaggara hakan yasa ta hakura ta koma gun Abbanta. Sai bayan magrib Salman yazo, sun gaisa da Abba sai daya shigo yaga gyaram gidan da akai lalai komai yayi kyau, Abba ya kara mai godiya sosai sannan yagaudasu umma da goggo, sannan suka fito. A hanya ne Salma ta sanar dashi zancen kamal, Salman ya mata wani kallo yace ” tsohuwar zuma ce ta motsa?” Dariya tai tace ” ai kafi kowa sanin ba wata tsohuwar zuma araina, daga sabuwae har tsohuwar mutum d’aya kawai nasani.” Kallanta yai yad’an d’age gira yace “mutum d’ayan dai ko ba’a fad’a ba nasa nine.” Tad’an murgud’a baki tace “irin wannan confidence haka?” Yace “kinsan nayarda dakaina, no doubt. ” Tace “ahhhh namanta ne, but what can we do? Sai kuma yakasance bakai bane Mr self-assurance?” Salman ya kalleta yace “ban gane ba?” Tad’an langwab’ar da kanta batace komai ba. Salman cikin b’acin rai yai gefe da motar yai parking, ta guntse dariyata tare da maida kanta tana kallan window, Salman yasa hannu ya juyo da fuskarta, yace ” Beauty magana nake.” Juyowa tai ta had’e rai tace ” inaji Mr self-assurance.” Yace ” me kike nufi da kalamanki?” Tace ” me nake nufi kuwa?” Yace ” karkisa naje na fasama kamal baki wlh, dama inajin haushi banine first love d’inki ba kar ki kara b’atan rai.” Dariya ta kwashe dashi tace ” Prince kanada abin dariya wlh, ni fa matarka ce banasan mud’inga zancen wani kamal inbadai aharkar ‘yan uwan taka ba.” Yace ” to ai kece kika zo min da magana abaibai.” Salma tace “uhmm nad’auka Mr Prince duk abaibai d’in danai magana zai gane, tunda dai shi ya koyamin.” Salman yace ” ohhh dama saboda ni kikai? Band’auka kema kin koyaba ai.” Tace “ina zaune dakai ai dole ne.” Kunnenta yad’an ja tace ahhh, yace ” ramawa nai……dariya sukai atare, nan suka wuce gida. Yau Salman sun gama jarabawa kuma a yau akesa ran za’a kwantar dashi a asibiti danyin treatment, dan yau da yamma akesa ran zuwan Dr Bilal da matarsa Dr Ilham. Salma ta had’a musu kayansu a akwati, duk yanda akaso a hanata zama acan saboda larurarta amma taki, hakan yasa sarki yace akyaleta, Fulani kusan kullum sai tayi abun marmari ta aikoma Matar Munnir dake da ciki da kuma Salma, Salma kam tsoron ci takeyi sai dai ganin mai kawowar bata take ta zab’a kafin takaima matar munnir yasa ta fara rage kokuntan ko magani ne a ciki. Farha kam mahaifiyarya taji bakin cikin korota da akai, sai dai yazasuyi? Da Mumyn ta kira Sarki dan tai fad’a sai ya gwaleta yace ” yama za’ayi ace yarinya takai shekara 25 amma ba zaku mata aure ba? Sai dai tai ta yawo a gari, wannan dalilim yasa tama daina kiran Sarkin. Bayan Shekara 3……….. Salman zaune akan dinning shida d’ansa Salim, Salma tazo kusa dashi ta zaune tace ” Prince dagaske kake wai?” Salman ya kalleta sannan ya shafa kan Salim yace ” Beauty wai dole ne sai naje wani matriculation? Ni yaro ne?” Salma tad’an had’e rai tace ” yara ne ke zuwa?” Salman ya kalleta zaiyi magana wayarshi tai kara yad’aga tare da cewa ” Najib ya akai?” Najib yace ” malam Yarima mai jiran Gadon Sarki bawai dan anaso Sarki ya mutu ba sai dan hakan Al’ada ta tsara.” Saki yai yace ” kafara ko? In roko ka fara to zan iya taimaka maka da kalangu.”+ Najib ya kwashe da dariya yace ” kaii mutumin akwai iya fad’ar bakar magana, yah zaka shigo kuwa? Su dad zasuzo fa.” Salman yace ” kai fa banza ne, meyasa baka sanar dani da wuri ba? Gashi nikuma banda niyar hallatar taron.” Najib yace ” haba yarima kafasan yanda Director yabada umarnin kaje saboda akwai kyauta dasuke san baka.” Yai wani murmushi yace” kyalesu so suke suyi neman suna gun mai martaba, ko an fad’a musu ban sani bane.” Najib yace ” to yanzu ya za’ayi?” Salman yace” zanzo bayan an gama sai mu gaisa dasu Dad d’in.” Nan sukai sallama ya kashe wayar. Salma ta kalli Salim tace” Ma boy jeka akaika gun Fulani tun jiya take aiken nemanka.” Cikin murna yace to. Yana fita Salma ta harari Salman tai d’aki, murmushi yai tare da mik’ewa yai d’akin, tana zaune akan gado, yana zuwa ya kwanta akan cinyarta, tare da sai ta fuskarshi kan nata, yace ” Beauty muje yawo?” Salma tace ” indai bazaka ba shikenan, dama bansan mai martaba yaga baka hallarci taron bane. ” Salman ya shafa cikinta yace ” Baby na kinga Mumynki na neman tilastama mahaifinki abinda baya so ko?” Salma ta shafa kan Salman tace “kaima kasan ba haka bane Abba nasan Umma bazata ma haka.” Tai magana amatsayin wai babyn Ajiyar zuciya yai yace ” Babyna I wish mace ce mai kama da Beauty na kinga sai in mata rival, ni dama ban tab’a ganin magajin Sarki da mata d’aya ba sai ni.” Salma tai dariya tare da manna mai kiss a kumatu tace ” na daina tambayar tunda an fara zancen rival.” Shigewa jikinta yai tad’an mai shakulkuli ta ciki tace ” kar ka matse mana babyn mu.” Yace 3mnt ko? Tace yeah Turata yai kan gadon tare da jawota jikinsa, yace ” Beauty wai sai naje?” Ta girgiza kai alamar a’a tace ” Ur choice. ” Ahankali ya kai bakinshi nata………… Ya shirya tsaf ya kalli Salma yace ” Zan wuce.” Tace sai ka dawo, Allah ya bada sa’a.” Yace amin “amma taso muje tare indai kinaso naje.” Murmushi tai ita kanta tanason zuwa, gyara fuskarta tai, Salman yakalleta yace ” ni fa banasan zuwa dake gun taro, maza suyi ta wani kallanki, narasa meyasa Abba kwanakin nan yai ta sakamu hallarta taro tare, haushi duk ya isheni.” Dariya tai tace” to ko inzauna?” Yace ” yau ni nakeso muje tare saboda nasan kinasan zuwa, koba yau zee zata gama ba itama? Sannan inaso kiga matar da Najib zai aura.” Nan suka gama kintsawa suka fito. Wata had’ad’iyar Motarsa mai masifar kyau suka shiga, sam yanzu anhanashi fita shi kad’ai, hakan yasa dole akwai mota d’aya da akesa fadawa suke rakashi inda zashi. Yafara tuki tare da kallan bayanshi ya kalli motar haushi ya isheshi, yai kwafa yace ” Who am I?” Salma tace” The Prince!!!!!” Yai wani mugun murmushi yace ” Sa belts dear.” Tasa tare da cewa me za’ai? Ya kalleta yai murmushi tare kara gudun motar, nan yadinga shiga cikin d’an lungun hanya daya gani, sun rikece suna binshi, sai dai ina, salon da Salman yake musu yasa sun rasa inda yai. Sai dayaga ya b’acemusu b’at sannan yai wani murmushi, Salma ta tafa mai tace ” irin wannan salo?” Yace “inama ni ba d’qn sarauta bane, da mota zan koya miki mud’inga fita bayan gari muna tsere.” Dariya tai tace ” stop Imagine, nikam kuna waya da Dr Bilal?” Salman yai murmushi yace ” guy d’in nan da matarsa sunyi, ba sa’idan kowa akansu, rayuwarsu free.”1 Salma tai shiru, can tace” amma fa ance aunga rayuwa, sai dai naji dad’in yadda yawarkarmun da My Prince.” Murmushi sukai Salman ya wuce skul d’in dadinshi d’aya bai fad’a ma fadawar inda zasu ba, kuma a iya saninsu bazai je makaranta yau ba. Anyi taro lafiya Salman an kirashi ya amshi kyauta amma yanajinsu ya sharesu, sai Mannir ne ya amsar mai a matsayin sa. Salma tayi farin cikin ganin zee, sunsha hira nan Zee take tambayar Salma labarin Kamal, Salma tace yana can naji Abba yace ya samu aiki acan, zee tace lalai. Ishaq kam yanzu rayuwa tazama saisa saisa, duk da ana tura musu kud’i kuma yana karatu, amma yanzu ya koma shiru shiru, sam bayasan garin, amma ya zai yi? Fulani kam an shiryu kusam kullum sai ta nemi akai Salim da kuma ‘yar gidan Mannir( Zulfa) sun tayata hira. Farha kam anata shirin bikinta, Salman yace zasuje shida Salma…. ……….. After 6years……….. Salman zaune akan kujerar mulki, yana karanta korafe korafen mutane, wazirinsa na yanzu shine ya kalleshi yace “Ranka ya dad’e bai kamata ace har yanzu matarka d’aya ba.” Salman ya bugamai wani kallo yace” in na kara auren kai zaka rik’emin matar? Ko kuwa mutanen dakesan in aure ‘ya’yansu suke turoka su zasu zaunamin da ita? .” Waziri ya had’iyi yawo yace” ya hakuri ranka ya dade ba haka nake nufi ba.” Salman yace ” ko ma me kake nufi, sannan ban fahimci wannan takardar ba.” Waziri ya kalli takardar, yace ” eh wani babban d’an kasuwa ne yakeso kad’an taimaka mai da sa hannu.” Salman yai tsaki tare da wurgo takardar yace ” ina sa mai hannu sai yaje yai ta shigo da kayan da basu dace ba yace nine na bada izini ko?” Waziri yace “ba haka bane, zai d’inga aiko da kud’aden da kadarori masu yawa ai.” Salman yai murmushin sa yace” bama bukatar kud’insa in bazai abu dan Allah ba ya barshi, sannan kar in kara ganin takardu shigen wannan anan gurin.” Waziri yad’an tab’e baki a zuciyarsa yace ” wannan wani irin mutum ne? Yaza’ayi mu tara arziki in baya….. Salman ne ya katseshi yace jeka na sallameka, waziri ya mike yana fita yai ajiyar zuciya yace” kaiii!!!!!! Haka zan d’inga fama kullum?” Salman kam yana ganin waziri ya fita ya kira Salma, tad’aga da sauri tare da cewa “My Prince gaskiya I miss u.” Yace “mee too dear, ina Swty na?” Tace gani nan. Yace ” not u new nake nufi, murmushi tai tace gatannan tana barci.” Yace shafamin kanta….tace yaushe zan ganka? Yace yau da aiki amma zan tsagaita inshigo, tace sai na ganka….. Nan sukai sallama tabi wayar da kallo, ga shi dai yanzu arziki itada ‘yan uwanta ba’a magana, ga matsayi na Fulani an batan ga yaransu guda Uku, 1 namiji, 2 mata, sai dai tarage zama da mijinta sosai, yazatai haka rayuwa take ba’asamun komai dole in an samu d’aya a rasa d’aya. *ALHAMDULILA NAN NAKAWO KARSHEN LITTAFINA MAI TAKEN ‘NI DA PRINCE’ BANSAN IYA YAWON GODIYA DA ZAN NUNAMA D’UNBIN MASOYANA BA, NAGODE KWARAI DASO DA KAUNAR DA KUKA NUNA MA LITTAFINAN, ALLAH YABARMU TARE……..