NI DA PRINCE CHAPTER 5
Tafe suke yana gaba tana baya, har suka isa kusa da motar najib ya fito da sauri yanacewa Amarya ansha kanshi, salma ta hade rai dan tagane shi, najib yace hmm salman Amaryarmu bata magana ne? Salman yai tsaki yace kaifa banza ne kamar bakasan munafircin wasu matan ba, najib yai saurin kauda maganar tare da cewa bismillah Ango ya budema Amarya kofa dan gimbiya ce😊 Salman yace wa? Nizan bude mata? Salma tace nima ban nema ba😏 ta zagaya ta d’aya bangaren ta bude ta shiga tare da rufo kofar da karfi. Salman ya kalli najib yace zakasha mamaki inkasan wacece najib yace naga itama ba sauki🤔 daga haduwa harkun fara fad’a? Da alama dai kunsan juna. Salman yace abar maganar shiga mutafi yafara kokarin bude gidan gaba najib yace yada haka? Ai a kusa da ita zaka zauna salman yace dalili? Najib yace naga an d’aura auran? Salman ganin baisan doguwar magana yasa kawai ya bude baya ya shiga, salma ta juyo ta makamai harara, yace ke wa kike harara? Tace wanda ya tsargu tafada tare da juyawa tana kallan window. Salman yad’auko waya yana dannawa, najib kam sai lekensu yake ta glass yana mamaki koda ace salman baisan yarinyar amma kyanta ai ya isa yasa yasota, shi jiyake inama za’amai auran dolen indai zai sami irin salma😜. Ba wanda yasake magana acikinsu sai najib dakebin wakar Aashiqui dake tashi a cikin motar, salma kam tunanin duniya ya d’auru akanta jitake kamar duk duniya ba wanda aka tsana kamar ita. A hankali najib yai parking, salman yace nifa natsani irin wannan gun na hayaniya😏najib yace haba salman ka hana ayi komai yanzu d’an dinner din ma bazaka bari ayi lafiya ba?salman Ya kalli salma dake cikin duniyar tunani yace ke tamai shiru yakara cewa ke limamiya! Ta juyo cikin bacin rai ta bugamai wani kallo kuma taki d’auke idanta, mamaki yakama salma yace ke who are u staring at? Tace in baxaka kirani da sunan da aka rad’amin ba kabarshi ya matso daf da ita har tanajin saukar numfashinsa akan fuskarta ya kai bakinsa saitin kunnenta dasauri najib yafita, salma kam numfashinta ne ya tsaya cak!! Salman yai wani murmushi yace how dare u talk to me like that? Dakyar numfashin salma yad’awo tad’aure tad’an turashi tace meye hakan? Yai murmushi yace u have to be careful bakomai nake d’auke ba. Yana fad’ar haka yai waje ta sauke wani numfashi tace wannan wani irin mutum ne? Najib ne ya kwankwasa mata glass a hankali ta zuru kafa ta fito, najib yace salman ku tafi atare plz? Yace kace ta matso, najib yace kid’an matsa ta matsa kusa dashi, najib yace dan Allah ku tafi a tare, salma ta kalli najib tace kacemai karyai sauri, salman yai wani murmushi wato tafi karfin tamai magana, itama aranta tace kaji ko da dadi. Ahankali suka fara tafiya sunje shiga aka ce su tsaya nan ‘yan yara da akama anko suka zo suka tsaya a gabansu kuyangi kuma suka fara zuba flower ahankali suke tafiya har suka isa masaukinsu. Abin ya kayatar da mutane ganin shima salman light blue din shadda, mutane sun yaba kyan salma sosai,ga salman ma ba bayaba abun nasu chakwas😜 Sukansu ‘yan uwanta dabadan sunsan itace Amarya ba da bazasu yadda salma bace ganin kyan datai. Anfara gudanar da shirye_shiryen da aka tanadar anyi gada, anyi kid’an gwarya sannan yan busa da kalangu, sai kuma DJ. DJ ya kira Amarya da Ango tsakiyar fili, sai dai duk maganar dayakeyi daga salma har salman ba wanda yake kokarin tashi, ganin haka yasa najib yazo kusa da salman yace hb salman so kake ka bamu kunya? Yai tsaki yace toshi Dj din cemai akai yakirani? Najib yace kayi hakuri plz, salman yace to kace ta taso, najib yakalli salma dake daf dashi yai murmushi shikanshi yasan ma’auratan kowa ba sauki amma yazaiyI? Haka ya juya yace Amarya kitashi kuje, salma tace kacemai yafara mikewa ai shine namiji😗 Salman yakalleta tad’auke kanta ganin mutane na kallansu ga dj ya saki murya sai kiransu yake yasa ya mike, ahankali itama ta mike suka nufi tsakiyar fili. Suna tsaye mutane sai barnar kudi suke suna musu liki, salma kam mamaki take sai kace takarda? Suna tsaye har dj yace su koma gunsu, ahankali suka fara tafiya zasu koma, tsautsayi yasa takalmin salma ya turgude tai baya luu zata fadi, da sauri salman yasa hannu ya tarota, nan suka kalli juna salman yace Will u stop pretending?dasauri ta mike tare da matsawa kad’an, ranta duk a b’ace. Nan mutane suka shiga tafi abin ya burgesu…… Nace hmmm 1 Takarasa ta zauna a kujera fuskarnan a hade, najib ya kalleta ya kalli salman yaga shima fuskarnan a hade, yace oh god yad’an matso yace hb prince kad’an saki ranka mana ‘yan jarida na kallo fa? Salman ya kakaro murmushin yake, sannan najib yakalli salma itama tad’an kakaro murmushi. + Angama shagali nan aka fara d’aukan hutuna kana ganin salma da salman sai kasan murmushin yake suke a hutunan, bayan an gama ‘yan uwanta suka mata sallama suka shiga mota, idanta ne ya ciciko ganin Asabe ta sata a motar da aka kawota sannan takalleta, tace salma kiyi hakuri, ki manta da kamal a ranki, yanzu ke matar wani ce dan haka ki kula da hakkinsa. Salma ta kalleta hawaye ya fara zubo mata tace Aunty meyasa kuka had’ani da salman? Cike da mamaki Asabe tace me salman din yai? Tace shikenan Aunty a bar maganar, Asabe tace koma dai menene ki rike mijinki, karki kuskura ki wulakantashi. Salma kam hawaye take ta rike hannun Asabe tace Aunty kicema yaya kamal……dasauri ta katseta tace salma me kike shirin yi? An fa d’aura miki aure, salma tai kasa dakai Asabe tace mun tafi sai munzo, Allah yabaku zaman lafiya. Salma ta bita da kallo hawaye na tsiyaya a idannunta,salman kam yanacan suna sallama da mutane sai can ya shigo shida kamal, lokacin salma kam ta hade kai da gwiwa tana zuba kuka, jin motsin bude kofa yasa tad’an sai_saita kukan salman yashigo ya zauna. Nan suka fara tafiya salma kam sai kuka take. Salman ne ya Kalli salma ta gefen ido dataketa shesheka tsaki yai yace malama dalla kimana shiru kin cikamana kunne, salma tad’ago ta makamai harara, ya juyo yakalleta tare dayin kwafa, najib ya ce salman hakuri zaka bata ba fad’aba. Salman ya kalleshi ta glass sannan yace ni? Yafad’a tare da nuna kansa, yacigaba ni wai kake nufi? Najib yace eh mana, salman yace over my dead body. Salma ta d’ago jajjayen idanunta tace kwantar da hankalinka nima I won’t let that happen. Daga nan kowa ya d’auke kai ita ta jingina kanta da window, shikuma yad’au waya. Najib yace oh god……. Sun isa gida sai dai a bakin gun sukaga su zeena a tsaye nan suka kama salma sukai ciki da ita, dakinta suka kaita su ka sata a gaba wai sai taci abinci, nan ta daure tad’anci kadan sannan suka mata sallama suka tafi. Mikewa tai tacire gwagwaron tai alwala tazo tai sallar ish’ai tana zaune agun ta zuba uban tagumi , salman ne ya shigo dakin tare da sallama ta amsa kamar bataso ya shigo ko kallan inda take baiyi ba ya bude drawer yad’au kayan baccinsa yashiga toilet din dakin. Ruwa ya watsa sannan yasa kayan yana fitowa ya fad’a gadonsa, salma ta kalleshi da mamaki tace malam meye hakan? Ya d’ago yace mefa? Tace anan zaka kwana? Yace da dakinki ne? Tace ba haka nake nufi ba amma tunda nazo nan aka kawoni, yace wannan matsalarkice sai kinemi inda zaki kwana ko ki kwana a kasa, tace what? Yace oho kardai ki kuskura kibar dakin nan dan bayi suna falo in baki kwana anan ba zasu fad’ama fulani dan haka dolene ki dinga kwana a kasa, tace dole? Yace yes kinada jaa ne? Tace mikomin bargo inshimfida a kasan? Yace bargo? Nikuma fa? Tace sai ka yaye bedsheet din ka rufa dashi. Salman yace kin ma rainan hankali ana sanyin zakice inkwanta na bargo? Ko in ja bedsheet? Ce miki akai zan iya bacci akan katifa zalla? Ran salma ya b’aci tace to ya kakeso inyi? Yace oho miki amma bazanyi abinda kikeso ba salma ta cika tai taf sannan tad’aure tace miko pillow, yace I can’t do that dan ni haka nake bacci in kwanta a d’aya in kuma rungume d’aya salma tai tsaki tace u are so selfish tana gama fad’ar haka ta mike tai hanyar kofa, dasauri salman yai dungure ya damko hannunta yace are u crazy? Tace mayb yace naga alama to ina zaki? Tace falo inje in kwana yace baki fahimci abinda nake nufiba kenan😡 tace ina zan fahimta? Yace go back yafad’a yana nuna mata cikin d’akin tace I can’t🤔 da karfi yasa hannu ya fincikota yai ciki da ita yasa makulli ya cire makullim yasa a aljihu. Salma ta fizge hannunta tace karka kara tab’ani😠yace ina kika ga jikin daza’a tab’a? Haushi ya isheta kawai tashige toilet, salman yai tsaki yace kawai za’azo a takuramin nida dakina😏 wannan aure ne ko takura🙄? Nace ba ka tambayeni ba salman katambayi kanka😏. Salma kam tsaye tai a band’aki kara karema bandaki kallo tai, aranta tace band’aki shine akama wannan kwalliyar oh, sai kuma tai tsaki tace wlh nikam an cuceni mezanyi da salman?fuskarta ta shiga wankewa a sink dan bazata iya wanka a gidan da batasan kanshi ba, tad’an dade kafin ta fito, salman tagani kwance ya rungume pillow yana narkar bacci…+ Haushi ya isheta ganin ko bargon baiyi karar ajiyewa ba takai hannu kamar zata dakeshi, tad’an daki iska sannan tace d’an rainin wayau ni da wannan ai gwara abarni ko shekara 10 zanyi a barni na jira kamal ko a had’ani da d’an garuwa😏. Ta koma kan sallaya ta tada sallah, ta dade tana nafila sannan ta d’aga hannu tashiga jero adduo’I tanayi tana hawaye, sai wajen 2 sannan ta mike dan kashe wutar dakin, ta kashe ta juya zata zauna taji ance I can’t sleep while light is off, dariya ma abin yabata a hankali tace dayake nepar a gidanku take😏 salman yace I can hear u, kuma ki kunnan wuta,tace gaskiya ni ban iya bacci da haske ba, yace wannan kuma matsalarki ne. Salman yace ki kunna min wuta ko? Dasauri ta matsa daga gun takaraso inda yake ta kunna yar karamar fitila ta dum light dakd side bed dinshi, zaiyi magana tai saurin juyawa zata koma kan sallayarta hijab dinta ya kamo ta baya yace ke! Ta juyo tace waye ke? Yace ke wannan hasken yamin kad’an,nida d’akina fa baki isa ki takuran ba😠 ta fizge hijab dinta tace sai kai hakuri da wannan inba hakaba ka bani makulli na fita🤔 tana kainan ta karasa kan sallaya ya kalleta taredayin kwafa. Itakam salma nan ta kwanta tare da takure jikinta, kan kaceme? Bacci yayi awon gaba da ita. Kamal kam tunda ya tsugunna a wajen nan bai tashi ba mahaifinsa yace kar wanda ya kulashi nan kowa ya watse aka barshi, sai wajen karfe 10 Abba yakasa jurewa yazo dakanshi ya d’agashi suka shiga ciki, sai dai kamal sam yakasa ko magana kawai idansa zaka kalla kasan yana cikin matsanancin bakin ciki. Da Asuba karfe 4:30am salman ya tashi,ya sauko yaga yanda salma ta takure dariya tabashi yace kad’an kika gani tunda ke kika ce ni kikeso, harzai samata bargonshi sai kuma yafasa yai toilet. Alwala yayi sannan ya fita, salma kam gajuya da rashin baccin wuri ga jikinta ba karfi saboda zazzaben datai agida yasa bacci mai karfi yai gaba da ita, sam bata farka ba lokacin sallah. Salman na dawowa ya kalleta tananan ayarda ya barta yai tsaki yace a waje kamar ustaziyar gaske amma ace mutum ko sallar asuba bai farkawa? Daga gani ba yau tasaba makara ba🤔 karasa wa yai inda take ya d’au sandar dake ajiye a d’akin yad’an zungureta dashi, cikin bacci tace Abba kafito? Salman ya tabe baki sannan ya kara zungura mata da karfi, cikin razana ta mike, sai dai me? Saman tagani ya harde hannunsa biyu. Haushi ya isheta tace wani sabon cin mutunci ne wannan? Bai mata magana ba ya juya ya hau kan gado takara cewa haka ake tashin mutum daga bacci?yace ke ni da sanyin safiyarnan bansan magana meye dan an zungureki?tace what? Kwanciya yai tare da juya mata baya, tai toilet batare data mai magana ba. Alwala tai sannan ta fito ta tada sallah, bayan ta idar ne ta kwanta wani baccin ne yasake d’auketa. Wajen karfe 9 sukaji anan knocking, salma ta mike da sauri ta bude kofar, wata baiwa ce tace ranki ya dade dafatan kin tashi lafiya? Salma tace lafiya, baiwar tace sunana Hanne baiwarki, salma tace baiwa? Tace eh zuwa nai nasanar dake karfe 10 zakuje gaida sarki, sannan karfe 12 baki zasu fara yimuku sallama. Salma tace toh😳 hanne takara kasa dakai tace karfe 9:30 zan kawo abinci, salma tace hmm to, nan hanne ta juya salma takoma ciki sannan tace nizan iya zuwa gun sarki kuwa? Tai maganar a fili, salman yace I can hear u, salma tad’an murguda baki tace mutum sai kunne kamar maciji? Yace inajinki fa? Tace oh ni😱 ta shiga duba drawer ko zataga kayanta sai dai kayan salman ne a jere tace oh wai nI ina akasamin nawa? Salman najinta amma ya shareta ya mike ya shiga wanka tabishi da harara. Tana zaune ya fito sanye da kayan daya shiga dasu yazo yad’au kaya a drawer yakoma toilet, tace ba laifi he has manner🙄 ta mike takara duba kayanta, sai dai bata gansu ba, salman ne ya fito sanye da wata dakakiyar shadda ya kalleta sannan cikin magana kamar bayaso yace ki duba akwatina, yanakai nan yaI waje ta bishi da harara wato yasan inda suke shine ya shareta, ta mike ta hau kujera ta janyo akwatin dake kusa aranta tace wad’annan akwatin masu kyau sune na lefen kenan? Cikin hanzari ta duba tarr da d’auko wani swiss less mai masifar kyau tace amma kayan sunyi kyau nan tashiga neman hijab dazata sa, sai dai babu da alama wanda tai sallah dashi shi kad’aine gashI na sallar irin burum din nan ne, kawai ta wuce tai wanka, tasa kaya sannan tazo ta shafa mai ta murza huda, nan taji an murda kofa ta juyo salman yace malama ki fito ga abincin anan, ta kalleshi shima kallan ta yai she is natural beauty haka yaji zuciyarshi tafad’a ya kauda zancen yace mekike shirin yi hakan? Ganin ta d’auko hijab din ta zura, tace me nake kuwa? Yace ki tambattar kin cire hijab din nan kinsa mayafi kalar kayan, yarinya sai kace a rigar fulani😏 Ta kalleshi tace waya sani? Ya juya batare daya amsa mata ba tai raurau da ido tace da ace mutumincan karami ne da sai na mai dukan tsiya💪🏼👊🏻 Nace hmm 😜 k