NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 1
_______A zaune nike a kan tabarma cikin baranda isaka na kad’a bishiyar mangwaron da ke tsakiyar gidan mu Ganyen ta na fad’owa ‘kasa gunin burgewa Dambu ne a gabana cikin wata ‘yar samira inaci ina sud’e yatsun hannu na saboda dambun yayi min dad’i banason ya’kare
Kawata Ladiyo. Ce ta shigo gidan mu hannunun ta rike da goshin ta yana zubar da jini koda na d’aga kaina na kalle ta bance mata komai ba Na maida kaina kasa na cigaba da cin dambu na, Saida na cinye dambun tas Sannan na kora da ruwa, Baki na bud’e iya ‘karfi na Nayi wata katuwar gyatsa tarashin mutunci, Irin wacce idan yaya Sadee’k ya na guri nayi yake buge min baki.+
Kallan Ladiyo nayi Na ta’be baki nace “Ladiyo lafiya kika zo ki ka tsaya min a kai ko aiko akayi?”.
Ladiyo. Dama jira take in tambaye ta, saboda tasan in bani na tambayeta ba tana iya fad’a min na bata kunya tana kuka take fad’a min abinda ya faru.
Tace “Kinsan yaron da jiya muka barar mai da markad’e ai Dazun Umma ta ta aike ni gidan su Zulai anso mata kud’in zubin a dashi,bayan na anso kud’in na had’u da yaron akan hanyata ta dawowa Ni bansani ba a she nan ne layin da yaron yake, shine yayi taimin ruwan duwatsu tako ina har wasu abokan sa suka taya sa Allah ya temake ni Baban
Ramma Yazo wucewa sai yaga abinda ke faruwa, nan take ya tsawatar musu shine suka ‘kyale ni amma wallahi inaga da sai dai a d’auko gawa ta saboda jifan da suka min bana wasa bane Ko gida banje ba nayo nan saboda ya bani sa’ko”. Yace in fad’a miki “wallahi kema saiya fasa miki goshi”.
Nace “Kan uban_nan yanzu dama acikin’ kauyen nan a kwai wanda zaija dani har ni zaice zai fasama goshi To wallahi kaf kauyen Dande. Banga mai fasamin goshi ba amma tunda yace haka muzuba ni dashi shege ka fasa kafin ya fasa min ni zan fara zuwa gidan su in fasa na Babar sa inya so kinga yaji dad’in fasa min nawa da hujja”.
Inna da fitowar ta kenan da Buta ri’ke a hannun ta da alama daga ban d’aki ta fito Tace “ke da wa siddi’ka. Ki ke yin wannan ashar d’in kamar bakya zuwa islamiya”? .
Nace “yo Inna bakiga Ladiyo bane?”.sai alokacin Inna ta lura da Ladiyo da ke a tsaye gindin rijiya ta d’ora hannun ta a kai. Inna Tace “na ganta sai akai yaya”?.
Cikin ‘kosawa da tambayar da Inna take min nace “yo wai ke Inna bakiga goshin ta bane a fashe jini yana zuba?”.
Inna tace “na gani mana. tunda ta’ki rabuwa dake ai tana tare da wahala gashi ta zama lusara bata iya ta’buka komi Se tsokana fal cikin ta tsokana kuma tame ‘karfi ce”.
Nace “yo Inna wanda yafasa mata goshin ne nima” yace “zai fa samin duk sanda muka had’u shine abin yabani dariya da takaici Har kika ji nayi wannan ashar d’in Idan duka ‘kauyen nan gatansane wallahi se naci ubansa duk abinda ze faru ya dad’e be faru ba Besan wace ce Siddi’kar Inna ba shiyasa amma ko yaran goye aka amaba ta masa suna na Nan take jikin sa yake fara rawa saboda karo dani babu dad’i”.
Banyi aune ba naji anbige min baki Da masifa na d’ago kaina dan naga wani mara kunyan ne ina magana ze bigen baki.
Amma sai mukayi ido hud’u da yaya Sadeeq Turo d’an ‘karamin baki na nayi. Yayin da shi kuma ya kashemin ido d’aya.
Yace “saidai ke ki ci uban ki, kamin shi yaci nasa, yau ina gida bazani gurin aiki ba Saboda haka kema babu inda zaki fita sakarya da’ki’ki ya kawai ba arabi babu boko se yawan gad’a a dan-dali ke a cikin matan ‘kauyen kin fita zakka saboda kinfisu wauta da tuma sanci.
Inna na daure miki gindi kina yin abinda kika ga dama ko Kina ganin kamar gata take yi miki To kisani inna ta riga da ta gama cin kasuwar ta Ke kuma yanzu kika fara taso wa. Dan baki san komi game da rayuwa ba. kwata kwata ma nawa kike? ko 14 years old baki kaiba amma kin addabi mutanan gari kullum ana cikin kawo min ‘karar ki ina bada ha’kuri”.
Yace “ke yakike da suna ma? Ladiyo yake nunawa da d’an yatsan sa manuni ya
Ladiyo dake a tsaye hannun ta akan goshinta, tace ” “sunana Ladiyo”.
Yaya Sadeeq yace “oho koma dai maye sunan naki maza tashi kibi nan yai mata nuni da hanyar fita gidan.”
Yakuma cewa “ko a ‘kofar gidan nan idan kika bari na kuma ganin ki to kashin ki ya bushe. Bare kuma in ga wa’innan ‘yan ‘kafafuwan naki a cikin gidan nan. Allah sena ‘ba’b-‘ba’bla ‘kafa fuwan. Ina fatan kinji abinda nace miki idan kunne yaji gan-gar jiki ta tsira.
Yace “oya maza zo kibi nan tun muna sheda junan mu”
Ladiyo jiki na ‘bari ta bar gidan mu. A d’ari da hamsin.
Kallo na yayi muka had’a ido da shi ya wurgo min hara-ra Nima na rama ina ‘kun’kuni ciki-ciki nace “nima idan ido ne ba a fini ba bare ayimin bara zana dasu kuma mu zuba ni da kai d’in.
Yah Sadeek yace “ke me kike cewa?”.
Inna tai saurin cemai ba da kai takeyi ba tafi abinka”.
Yah Sadeek yace “Inna kiba ta abinci na takawo min”.
Inna taja dogon numfashi tace waini Garba me yarinyar nan taimaka ne haka? daka tsaneta. banason haka fa tun ba yau ba nasha fad’a maka Amma dake ka rainani bakajin magana ta. Ko kad’an saboda ni kaka ce To alhaji karami na nan zuwa wata ya kusan ‘karewa idan kai ban isa da kai ba shi na isa dashi. Kuma shine mahaifin ka Idan yafad’a maka wata ‘kila kaji nasa tunda ka ‘ki jin nawa ni”.
A sakarce yaya sadeek ya kalli Inna yace “haba hajjaju makkatun mu karrama ranki shidad’e Ki dad’e kiyi ‘kar’ko kiyi shekarun bishiyar dabino Ni na isa in raina ki duk da cewa nike aurenki amma ke ke bada umarnin Kuma yadda Kiki ce haka za ai nadena daga yau babu ruwana da ita.”
washe baki inna tai tace ” ko kaifa Garba shikenan ya wuce amma da kasa ka ‘yar mutane a gaba se ramewa take shiga ciki yanxu zansa ta kawo maka abincin naka
💋💋💋💋💋💋_________Inna tace, “Siddi’ka daure ki tashi ki kaiwa yayan ki abincin sa ya dawo daga aiki ya gaji ga yunwa”. ‘Daure fuska ta nayi ina turo baki nace, “ni dai Inna bazan kai mishi abinci ba duka na zeyi, baki ga yadda yake kallona ba kamar wani tsohon maye, kwana biyu be samu ya dakeni ba, kinsan halin muguntar sa ba se nayi masa laifi ba, yana iya rufo ‘kofa idan na shiga kinsan shi kullum cikin jin haushi na yake”.+
Inna tace, “Garba ko kunnan ‘kashi ne dashi baze dake kiba nayi masa magana kuma a gaban ki akai, idan ko ya ta’ba ki sena had’ashi da Alhaji ‘Karami. Tashi maza kije ki kai maisa yar albarka
Nace, ” yo ina abincin nasa yake Inna?”.
Inna tace, “yana kitchen mana inda kika d’auko naki”.
koda na ‘dauko abincin a saman kaina na d’orashi ina d’igir-gire. Inna tace “A’a fa kada tsautsayi yasa ki zubar mai kinga yana cikin fushi babu abinda baze iya miki ba”, nace “haba Inna baze zube ba sedai idan kece kike so ki zubar dashi, amma ai ba yau nikeyi ba kuma be ta’ba zubewa ba”, Inna tace “Allah ya bada sa’a ta shige d’aki abinta” nace “amin hajiya Inna”
Ina tafe ina ‘yan wa’ko’ki na ina tafa hannu, hanyar d’akin yaya sadeeq na nufa saboda yana daga hanyar waje ne. Koda nazo ba’kin d’akin ban tsaya yin sallama ba kuma ban buga kofar ba duk da yasha yimin gargad’i a kan inde nazo d’akin sa kada nashiga se nayi sallama ya bani izinin shiga ko kuma na buga masa kofar. Ina tura ‘kofar na bankad’a labule nakutsa kaina ciki. Yanayin da naga yaya Sadee’k yasa nasaki wata uwar ‘kara, har saida kular abincin kaina ya fad’i murfin kular ya bud’e dambun ciki ya watse.
A fusace yah Sadee’k ya nufo ni kamin in Ankara ya wanka min kyawawan maruka. Haske nagani wal a idona. Har saida gani na ya d’auke na wasu ‘yan da’kiku, babu riga a jikin sa kirjinsa a kwai yalwa taccen gashi baki sid’ik dashi kwance luf-luf banta’ba ganin namiji a haka ba tunda nike a rayuwa ta, ja da baya na fara yi yah Sadee’k kuma yana nufo ni, na furgita dashi matu’ka. Saboda haka na fara ihu iya ‘karfina yadda Inna zata ji tazo ta cece ni. Takaici na ne yakama ya Sadee’k cikin zafin nama ya ‘karaso inda nike belt din jikin wandan sa yaciro se alokacin nai yun’kirin guduwa daga d’akin. Amma caraf yakama hannu na sannan ya maida ‘kofa ya rufe harda samata kye da sakata, Duka na ya fara yi kamar Allah ya aiko shi, kota ina zabga min belt d’in yake yi. Ihu nikeyi da duka murya ta, saboda naga so yake ya kashe ni tun kamin lokaci na yayi.
Inna da dake cikin d’aki tajiyo ihuna da gudu ta fito tazo bakin ‘kofar d’akin sa buga ‘kofar tafara yi tana kiran suna na da’karfin ta. Ganin ba kiran suna nane mafita ba yasa tafara kiran sunan yah Sadee’k, Garba Garba kada ka kashe yarinyar mutane na shiga uku, dan Allah kaya’kuri ka ‘kyaleta haka nan kome tai maka ai tada ku bazata ‘kara ba daga yau insha Allah”.
Tun ina iya jiyo muryar Inna tana magiya har nadena jiyo ta nasan ta tagaji ne saboda bata jure yawan magana yanzu se hawan jinin ta ya tashi. Sadeeq kuwa kunnen uwar shegu yayi kamar bashi Inna kema magiya ba, tuni Inna hawaye sun fara zarya a kan kuncin ta saboda tasan yah sadeeq zeyi d’anyen aiki,
STORY CONTINUES BELOW
Ni kuwa har muryata ta dashe ko sautin ihun nawa ya dena fita, hawaye ne kawai suke zubar min. Kuma har yanzu be dena duka na ba saida yaiwa jikina rud’u rud’u. Sannan yacemin “shiiiiiiii” yana wani irin huci kamar yayi dambe da ‘kartai.
Murmushin mugunta yayi, Nikuwa a cikin raina nace, “mugu burin ka ya cika kaci zalina” wata doguwar ajiyar zuciya naja kamin na fara sauke numfashi da sauri da sauri”. Yah Sadee’k yace “idan na’kara jin kinja ajiyar zuciyar nan wallahi saina sako miki farkon dukan nan koma nayi miki mafiyin wanda nai miki yanzu”. Ya cigaba da cewa “so nake kiyi shiru kamar bakya gurin nan ko numfashin ki kar inji saukarshi. Hakan ne kawai idan kikayi zaki temaki kanki, kifita daga d’akin nan lafiya da ‘kafa-funki batare da anzo an d’auke kiba”.
Nasan halin yah sadeeq sarai ba ‘karamin mugu bane, saboda haka nayi Kamar yadda yace nayi “haka nayi shuru kamar wacce ruwa yacita” numfashina na neman d’auke wa ina ta ‘ko’karin dawo dashi ba tare da inason yah Sadee’k ya gane ba. jinike kamar ana so a zare min raina saboda azabar dukan dana sha, gaba d’aya jikina rad’a-d’i yake min, ga kaina da nike jinsa kamar ze bar gangar jikina ya fad’i’ kasa.
lura da yanayin yadda nike ciki ne yasa yaya Sadee’k cewa ” kad’an namiki ma wallahi saboda batun yauba nasha fad’a miki kidena shigo min d’aki kamar d’akin arna, bama d’akina kawai ba duk inda zaki shiga kishiga da sallama a matsayin ki na musulma, Amma dayike kunnen ki na ‘kashi ne ina gama fad’a miki kike watsar da maganar anan, to wannan shine na ‘karshe wallahi idan aka’kara ai koki baki sallama ba kika shigo zakiga abinda zan miki”.
Yace, “Tashi kiban guri na gaji da ganin wannan mummunar fuskar taki gashi kin tsura min ido kamar sa’anki ne yake miki magana”.
Tashi tsaye nayi Ina layi ina bin bango har na iso bakin’ kofar na bud’e. Ina fitowa naci karo da inna dake faman sintiri. Kamar wacce tayi ‘karya. Cikin sauri Inna takomo ni. zubewa nai a jikin ta babu numfashi ihu inna tafara tana kiran ya sadeeq da karfinta Garba inalillahi wa innah ilaihi rajiun shikenan ka kashe ta. Garba ka kashe ‘yar mutane, bazaka fito ba mukaita asibiti ina magana kayi shuru. ya sadeeq yana jin Inna amma yai banza da ita kasan cewar yasan halin inna da zuzuta abu shiyasa ya’ki fitowa. Can dayaji ihun nata ya’ki karewa yasanya rigarsa jallabiya me ruwan madara Yafito. A zaune yaga inna dirshan, ni kuma ina kwance a jikin ta kamar matacciya, yayin da Inna keta faman jij-ji-gani tana sun batu kamar wacce tafara ta’buwa.
bece wa Inna komi ba yawu cemu cikin gida yashiga ya bud’e fridge yad’ibo ruwa me sanyi acikin kofi, koda Inna tagan shi da kofi batasan meye aciki ba, ta bud’e baki kenan zatai mai magana
ya antaya min ruwan duka ajikina harda mugunta, wata doguwar ajiyar zuciya na sauke ina ‘kan-‘kame jikina ina ‘kara shigewa jikin Inna, ta kaicin yah sadeeq yahana Inna magana. amma ganin ina motsi yasa tadanji sau’ki aranta. Tace “siddi’ka sannu, haka Inna taita kiran suna na tana min sannu, sedai na kalle ta da ido kawai saboda bazan iya magana ba.
da’kyar na iya d’aga han-nuna na mikawa Inna saboda na gaji da kwan-ciyar so nike in tashi, Inna ta fahimci nufi na saboda haka ta kama hannun nawa. Tana fadin “sannu Siddi’ka sannu kinji, Allah zesaka miki, se a lokacin na iya magana cikin wahalal-liyar murya nace “Inna zan mutu inaji ajiki na karshena yazo” nafad’a ina rushewa da wani irin kuka me ban tausayi, itama Inna kukan tasaka, tana fad’in “bazaki mutu ba ‘yar Inna saidai shi yamutu zaki tashi Insha Allah” hannun Inna na kama na d’ora a ‘kir-jina nace “Inna nan d’ina kusa da zuciya ta zafi yake min”.Inna tace “ciwo yake miki?” nace, “eh Inna, Ji nake yi kamar ba ajiki na yake ba”.
yah sadeeq da yake a tsaye tun sanda ya kwara min ruwa na far fad’o yake jin diramar damukeyi. Bakaramar dariya muka bashi ba amma yasan babu halin yin dariya yanzu se abin yayiwa Inna yawa. Dabara ce ta fad’o masa. Saboda haka yaje d’aki ya dauko wayar sa yazo yake mana video. A cewar “sa idan yashiga d’aki ya kalla abinsa yayi dariyar sa san rashi”.
Cikin muryan kuka Inna tace, “garba ashe rashin inanin ka ya kai haka. Kayi mata dukan mutuwa be isheka ba kazo kana d’aukar ta hoto. Bakomi kana lokacin ka”. Ta kuma fa shewa da kuka tace, “yanxu Garba bazaka zo kafad’a min yadda zanyi da ita ba?. Ko tunda ka illata ta shike nan burin ka ya cika?. to kiramin ubanka awaya nasan duk inda yake yaji ina nemansa zezo yanzu da gau-gawa. Idan kuma baya garin ze turomin Wanda ze share min hawaye”.
‘Dan ta’be baki yah sadeeq yayi, Sannan yamatso inda nike, ya tsugun-na han-nun-sa ya d’ora a kan wuya na, yaji da zafi sosai
Ya cewa Inna “ki d’auko mata hijabi inkaita asibiti naji jikin ta ya d’anyi zafi”. Inna tace “au ya d’anyi ne ko Garba Allah ze saka mata mugu, kaje d’akin ta ka d’auko mata kowani irin hajabi ne”. Yah sadeeq yace “Inna bafa dake zani asbitin ba a gida zan barki”. Inna na salati tana tafa hanna-yenta tace. “Garba me kace? na d’auki yar mutane na baka katafi da ita kai kad’ai kaje kai mata wani abun nasan saboda tsabar ba’kin halinka ko gawarta ma bazamu gani ba. To ban yarda katafi da ga kai se ita ba. Kafata kafar ka maza shiga ciki ka taho min nima da maya fina”.
kallon mamaki sadeeq yabi Inna dashi sannan ya ta’be baki yace, ” bari na fara fidda motar waje senazo na d’auko muku”. Inna tace “da dai yafi maka saboda bazan bari kaje ka kuma cin zalin ta ba, Nima se Allah ya tambayeni”.
Fita daga gidan yaya sadeeq yayi.
Ina kuka nace, “inna wallahi banasan zuwa asbitin nan”. Inna tace “ya zakiyi Siddik’a daurewa zakiyi dama ba a zuwa asbiti se idan ba’ada lafiya. Duk ni naja miki da dakika ce bazaki ba na rabu dake ai da haka bata faru ba”.
Yah sadeeq ne ya dawo yatar da Inna tana shere ‘kwalla. Be ce mana komi ba ya wuce cikin gida se gashi ya dawo da hajabi na da maya fin Inna. Yana zuwa ya mi’kowa Inna yace “dan Allah ni kuna ‘bata min lokaci ina da abin yi kisaka”
Amsa Inna tai bata kula shiba saboda ya gama kaita bango. Saida tayafa maya finta sannan tafara ‘ko’karin d’agani amma ta kasa, saboda shekaru sunja kuma tun ina jari-riya a cikin tsumma na take d’awainiya dani, saboda haka tace ma yaya sadeeq “.
Temaka ka d’aga min ita nasaka mata hijabin. Yi yai kamar beji abinda Inna ta fad’a ba. Kome ya tuna oho. Se gashi yazo ya dagani sama ta yadda fiskata zata kalli Inna. Saka min hajabin tayi, yasan Inna baza ta iya d’auka taba saboda haka ya ajiye ni a ‘kasa amma be sakeni duka ba. Yace “Inna muje ko,’ko’karin fara jana yakeyi, Inna tai saurin daka mai tsawa tace” wai Garba lafiyan ‘kalau kuwa?”
Be ce mata komi ba yasa’ba ni a kan kafad’ar sa, Saboda yayi min mugun ta yazuro kaina ‘kasa sosai. jini na se dawo min kai yakeyi, a haka muka isa bakin motar, a gidan baya ya ajeni sannan yashiga gurin zaman direba. Inna ma baya tashigo tana mita. domin Allah ya mata mita koda yiki yawanci tsofaffi sunada wannan mitar, kaina nadora kan cinyarta ina matso kwalla bawani bab-ban asbiti ya kaini ba illah asbitin dake cikin ‘kauyen mu asbitin shi kadai ne asbiti. kuma babu wasu kwararrun ma aikata acikin sa.
_________Asbitin gaba d’ayan sa a lala ce yake saboda ginin jar ‘kasa ne wani ‘bangaren ma duk ya rushe, d’a kunan da ake kwantar da marasa lafiya guda 4 ne kawai, Sai office 1 da ma aikatan asbitin suke zama a cikin sa, gabaki d’aya asbitin gado biyu ne kawai a cikin sa,+
a bakin asbitin yah sadeeq yayi faking, Asbitin bashida kofar shiga ko ta ina shiga a ke saboda ba a ke waye yake ba, ya d’auki kusan 10 seconds a cikin motar, kafin ya kashe ya fito,
Saida yafara bud’ewa Inna murfin ‘motar ta fito, san-nan yazo ya bud’e bangaren da nike yad’an zuro jikinsa ciki ya mi’ko hannu ya janyo ni, Inna na fad’in “kabita a hankali ba tada cikak-kiyar lafiya”.
‘Dauka ta yayi irin d’aukar da a kewa jari-rai cikin Asbitin ya nufa dani,
Inna na biye dashi a baya,
Da yike yah sadeeq sanan-ne-ne a gari bama iyaka kauyen mu kad’ai ba harda burni. Saboda babban d’an sanda ne
wata nurse ce ta han gomu da sauri ta ‘karaso inda muke, cikin rawar jiki tace “yallabai cikin wancen d’akin zaka kaita zatafi hutawa babu mutane da yawa a cikin sa”. Tafad’a haka tana nuna mai d’akin da yatsan ta manu-niya, “alright” shine abinda yah sadeeq kawai ya fad’a.
‘Dakin da a kace yah sadeeq ya kaini shine d’akin da ake ji dashi a cikin asbitin saboda a kwai siminti da gado guda d’aya tak a cikin sa, mun tarar da mara lafiya a kan gadon kwance, saboda yah sadeeq ya d’ora ni aka sauke mara lafiyar gunin ban tausayi gashi masu jinyar ta basa kusa,
“yalla’bai d’ora ta a kan gadon”. A cewar nurse d’in data sa aka sauke mara lafiyar
Yah sadeeq beyi ma-maki ba saboda ya saba kawo ni asbitin kuma irin haka ne take faruwa.
‘Dora ni yayi akan godon, yana d’orani ya fice daga d’akin,
Nurse d’in ma tabi bayan shi tare da wa’inda suka cic-ci-‘bi marar lafiyar da aka sauke a kan gado,
be jima ba saiga shi ya shigo tare da wata nurse, hannun ta rike da wani d’an karamin faran tin silba, kan wani teburi na katako ta ijiye tiran silban, sannan ta matso kusa dani, ta d’ora hannun ta a kan wuya na, “a kwai zafi a jikin ta yallabai, zazza’bi ne ya kamata”. Nurse d’in tafad’a tana duban shi, amma ko tanka mata beyi ba sai yayi kamar ba dashi take magana ba,
“meke damun ki?”. Nurse ta tambaye ni,
nace “duka jikina ciwo yake min, amma kirji na yafimin ciwo”.
Fuska ta ta kalla da kyau sai taga shatun hannu tace “kamar dukan ki akayi ko, domin shaidar hannu ya bay-yana a kan kuncin ki rad’a rad’a”.
Na bud’e baki zanyi magana kenan yah sadeeq ya wurga min hara ra,
Ya kalli nurse d’in yace “ke maye aikin ki?”.
“Duba mara lafiya”. Ta fad’a bakin ta na rawa,
saida ya d’aure fuskar sa babu alamun wasa a tat-tare dashi yace “to kiyi aikin ki wannan be shafeki ba kiyi abinda yadace”.
Cikin in-ina tace “to ranka shidad’e na tambaya ne saboda nasan irin maganin daya dace na bata, amma kaya ‘kuri naga kamar ranka ya ‘baci”.
Be kuma bi ta kanta ba yafi ce daka cikin d’akin, tasha fama dani sosai kamin na bari tasoka min allurar da zata samin abin ‘karin ruwa, shima saboda naga yah sadeeq ya dawo d’akin ne.
STORY CONTINUES BELOW
Banfi minti 25 da samin karin ruwan ba, baccin wahala ya d’auke ni,koda na farka bayan wasu awanni da bazu wuce 2 ba
Naga momy zaune a kan wata farar kujera, da alama daka gida aka zo da kujerar mamakin ganin ta ne ya kamani, na mi’ke zaune na jingi na da filo a baya na, kallon ta nikeyi ina muts-tsuka idanu na, ban gama mama ki ba saida naga Khadija, tashigo d’akin hannun ta d’auke da kular abinci, da kwano, Umar, na biye da ita a baya,
tashi Momi tayi tamatso da kujerar ta kusa da gado na ta zauna tana kama hannu-na “sannu kinji Allah ze saka miki ya jikin naki”. Momy ta tambayeni muryan ta d’auke da damuwa
mada din na bata amsa sai nace “wai momy yaushe kuka zo kuma waya fad’a muku banida lafiya?, Inna dai bata da waya yah sadeeq kuwa nasan ko mutuwa nayi baze kiraku ya fad’a muku ba”.
Momy tace “Babu wanda ya fad’a mana, daka kaduna muke hutun makarantar su Khadija ya ‘Kare zamu koma Abuja, shine muka biyo tanan, can gida muka fara zuwa bamu sami kowa a ciki ba,kun bar ko ina abud’e, hakan ne yasa naji a jiki na ba lafiya ba, shine nakira yayanku sadeeq awaya.
shine ya shaidamin “bakida lafiya ne ya kawo ki asibiti”.
Nace “mai wani asbiti?”.
“Asbitin Dande”. yabani amsa daga haka muka yi sallama na kashe wayar.
Sanda mukazo hajiya Inna ke bani labarin abinda yafaru tana kuka, gaskiya sadeeq bai kyauta ba,
Momy tace “Na kira sa a waya nayi masa kaca-kaca, kuma nakira Daddyn ku a waya, na fad’a masa, ya ce “muzau na anan Danden nanda kwana 2 zaizo”.
Ina ‘Ka’ka lo hawaye nacire hajabin jikina, nace “Momy kalla kigani fa wallahi babu abinda nayi masa yayi min wannan dukan kuma”. Yace “kad’an yayi min”.
Salati Momy keyi tana tafa han-naye “yanzu sadeeq ne yayi miki haka?”. Momy ta fad’a tana ri’ke ha’bar ta,
gyad’a kaina nayi alamar eh,
tace “kiyi ha’kuri Daddyn ku ze zo nan da kwana biyu insha Allah,zai d’auki mummunan mataki yanda koda kud’i a kace sadeeq ya dake ki baze dake kiba”.
Khadija da tunda ta shigo ta aje kular hannun ta, ta sami gefan gado na ta zauna, sai alokacin tace min ” sannu Siddi’ka yajikin naki da sauki dai ko?”.
“Babu laifi dai zance amma wallahi na daku gurin wancen ba’kin mugun”. nace mata,
“ina ke miki ciwo yanxu to?”. Khadija ta kuma tambaya na,
Nace “Babu sai d’an abinda baza’a rasa ba”.
“Alhamdu lillah” momy tace
yayin da Umar yace “aunty Siddi’ka yajikin naki?”.
“Dasuki” itace amsar dana basa,
ina mi’ka mai hannu alamar yazo kusa dani, ai kuwa ba musu yakama han-nun nawa, zaunar dashi a d’ayan gefen gadon nayi suka sani a tsakiya,
dayi ke lokacin da nike bacci ruwan da ake ‘kara min ya ‘kare nurse d’in tazo ta cire min.
zubamin abincin Khadija tayi, tana fad’in “sister Siddi’ka daure dan Allah kici wannan babu yawa”. Tamiya ce fara da mai da yaji
nace “na’koshi”
da ‘kyar Momy ta lal-la-‘bani naci abin cin d’an kad’an, na ture kwanan
nace “nifa na ‘koshi Umar zo kacinye sauran”.
Sai alokacin na lura babu Inna, “ina Inna wai?”. na tambaya ina kallon Khadija,
takoma gida nasaka driver ya kaita nace “zan zauna dake har sanda zasu sallame mu”. A cewar Momy
STORY CONTINUES BELOW
“to Momy muko ma gida mana na warke”. Nafada ina sauka daka kan gadon kamani khadija tai tana fad’in “wannan wani irin ciwo ne Siddi’ka?,🤔
Koda yike kedaman haka kike bakyason asbiti”.
“haba khadija ai kwata kwata natsani asbiti wallahi inba dole ba me mutum zaiyi” nabata amsa da haka
Nace “momy kira driver d’in Allah da gaske nike na warke”.
Momy tace “bari a fara kiran likita idan tace zamu iya tafiya gida sai subaki sallama”.
dariya ce taka mani sosai nike ‘kyal-‘kya-tawa,
“Lafiyan ki kuwa Siddi’ka”.Momy ta tamba yeni,
nace “wallahi momy kece ki ka bani dariya, baki karewa asibitin kallo bane halan to wannan asbitin da ki ke gani ba a sallamar mutum,
idan aka kawo mutum yaji sau’ki ka wai tafiya zeyi. Idan kaga dama ne ma sai kace musu zaka tafi, basa saida magani wasu magunan kirki, kuma basa wani rubuta maka koda zaka siya wani gurin idan su basu da shi, idan ma sun rubata to abu 2 ne kawai fanadol sai farasitamol”.🤣na’kara sa fad’a ina ‘kara ‘kyal-‘kyala dariya
Na cigaba da cewa “nifa momy wallahi a gani na duk basu san aikin su ba, gwara gwara ma Aliya wannan tad’an I ya aikin, itace ma tasamin ruwa, idan fa aka kawo mutum bata nan sunan shi sorry ba’kara min ja-gwal-gwalo mutum ze sha ba”.
sosai khadija ke dariya tace “ai ni ban zata ma asbiti bane domin sam baya kama da asbiti”.
“‘kwarai ma kuwa”. Nabata amsa
Nace “kefa da a ka kawo ni wata a ka sauke a kan gadon a ka d’ora ni, nason don sunga yah sadeeq ne duk sanda ya kawo ni gado suke bani”.
cikin mamaki momy tace “wata fa ki ka ce aka sauke”.
“eh mana Momy” nabata amsa
“to ina suka kaita?”. Momy tayi tambayar,
Nace “wallahi Momy ban sani ba lokacin ina fama da kaina”.
cikin hanzari momy ta fara lalu bar jakarta tana fad’in “da gaskiyar ki Siddi’ka bari na kira driver yazo ya kaimu gida kamin kema a sauke mana ke, tunda sadeeq d’in ya tafi”.
Ina dariya nace “hhhhmmmmmmm Momy da zamu shekara anan babu wanda ze sauke ni”.
“saboda me? Yaya ko?”. Khadija ta tamba yeni tana kallon idona
Nace ” eh, nifa mutane har mamaki suke bani yadda naga suna tsoran yah sadeeq kamar wani mala’ika”.
Momy tace “nidai duk da haka gwara mu koma gida, ko wani asbitin na kudi a canza miki ban yarda da wannan ba za a iya bawa mutum maganin da bashi yadace ba”.
Nace “momy nifa na warke babu wani asbitin da zan sake koma wa”.
‘Dau kar wayar ta tayi ta latsa nombar Idi driver, bugu d’aya ya d’auki kiran
kamar tana gabansa cikin ladabi yace “Hajiya na kawo Inna tun d’azun”.
Tace “yayi kyau muma kazo ka d’auke mu ta sami sau’ki mara lafiyar”.
Yace “to Hajiya”.
sannan takatse kiran
Ba a fi 15 minutes ba saiga Idi driver yazo
dayake d’azun har dashi aka zo yasan asbitin har d’akin da aka kwantar dani ya shigo,
ya kwashi tarka cen da khadija tazo dasu yayi gaba,
Sannan mumu muka fito, da Aliya muka ci karo A bakin fita asbitin tana Murmushi tace “mara lafi sauki yasamu kenan”.
Nace “eh”. Tace “to bazaku sai magani bane?”.
“muna da irinsu dayawa agida” nace mata
“to shekenan Allah ya’kara sau’ki” ta fad’a yayin da takai duban ta ga Momy tace “Hajiya ya me jiki?”.
Momy tace “da sau’ki”. Daga haka muka mata sallama muka futo cikin asbitin, muka shiga cikin mota Idi driver ya hau titi
umar ne ke bamu labarin ban dariya a mota sai ‘kyal-‘kyala dariya muke yi kamar wasu za-rarru Momy dai saidai tayi Murmushi idan taji ya fad’i abin dariya,
yanxu ma wani labarin bafullatani yake bamu
Yace ” wai wani ba fullata ni ne, ya siyo lemu, shine aka samai lemun aleda, sai yasa ka lemun a bayan keken shi koda ya fara tafiya a kan kwalta, sai ledar lemun ta ‘bule, lemu d’aya yafad’i a kan kwalta, koda ba fullata ni yaga abinda ke faruwa lemun sa ya fad’i kan kwalta, amma se gudu yake yi, sai ya sauka a kan keken yatsa ya d’auko sauran lemun da suka rage a cikin ledar, ya watsar kan titi”, yace “a kin banza a she ku kuna ma tafiya kuka bani wahala, to muhad’u a gida”. 🤣
________Sosai muke dariya Khadija harda rike ciki, ni kuwa ba a magana don har tsalle nikeyi, a haka muka iso gida cikin farin ciki da nishad’i na manta da wani yah sadeeq saboda ganin su khadija
+
“Inna Inna”. Na shiga ina ‘kwala mata kira buta ce a han-nun ta da alamar ban d’aki zata, mama ki ne ya bay-yana ‘kara ra a kan fiskar Inna,
rungume ta nayi ina fad’in ya dai tsohu wa ko baki murna da gani na bane, “ja ira”. Inna tace tana jan dogon hanci na “banyi murna daganin kiba zaki ce nida nafi kowa san kisa mu lafiya, mamaki ni keyi saboda sanda naba roki baki san wake a kanki ba”.
dariya nayi nace “yo Inna ikon Allah ai ya wuce gaban komi”.
“haka ne Siddi’ka ya jikin” Inna tace min Nace “jiki yayi sauki wallahi”.
Inna tace “haka akeso wancen mugun kuma Allah ze saka miki kinji”.
“To”. Nace yayin da nike nufar cikin falo, ina shiga na zauna a kan kujera ina maida numfashi, kamar wacce tayi gudu saboda al’ada tace,
can sega khadija tashi go
“ke haka ake tarban baki?”. tace min
“ina ba’kin suke?”. na tambaye ta
“gamu” tanu na kanta, duka nakai mata sannan nace “to ki godewa Allah domin na kar-rama ku”.
“A hakan”. Khadija
tace min “eh”. Nace mata
“bakida kirki Siddi’ka”. khadija tafad’a tana zama kan kuje rar danike kai, nace “danayi me?”.
Tace “bakisan me kikai ba ko”
nace “eh man”. “shike nan ya wuce tunda kin manta”.Ta fad’a tana share zancen,
ta’be baki nai nace “kinsan wani abu khadija?”.
“A a”. tace min na d’ora da cewa “wallahi yaya sadeeq bedaki banza ba zan rama bashi yaci, domin ni ba kanwar lasa bace”.
Mi’kewa Khadija tayi alamar razana tana dafa kirjin ta, “zakiye me”. Ta kuma tambaya ta. “ramawa”. Nace mata
Tace “ke kuwa ta yaya”. Nace “kedai kitsa ya kiyi kallon ikon Allah”.
da ido ta bini da kollo irin bakida hankali yarinya
Nace “kinamin kallon banida han kali ko to zan tab-batar miki da a cikin hay-yaci na nike amma tabbas yaya be daki bulus ba”.
“hhhhm”. tace tana cire gyalen ta, ta ajiye a han-nun kujera
Umar ne yashigo bakin sa da sweet yana tsotsa, la Umar zo kasam min”. Na fad’a ina mi’ka mai hannu na, yace “za kisha ne?”.
Nace masa “eh”. Yace “nakawo miki naki, bari naje na d’auko miki yana d’akin Inna”.
Nace “to”
“nima katawo min dashi”. Kadija tafad’a
beda d’eba saiga shi yakawo mana, nan ya zauna mukai ta shirme daman idan muka had’u a guri babu dama
Ana idar da sallar magriba ina sula lewa nabar gidan ‘yar kasuwa nanu fa ina tafe ina gad’a ni kad’ai, a can na iske kawata Ladiyo, kaf kauyen Dande banida kawa sai Ladiyo saboda nafi san a kullum nice shugaba, bana son raini ko kad’an sauran duk nayi fad’a dasu saboda halin mu be zo d’aya ba, itama Ladiyo tana da hakuri ne kuma kome zan mata batayin fushi
Ladiyo nakwala mata kira daka nesa saida nasake kiran ta, ta na waige-waige tajuyo inda nike baki washe ta nufo ni, tafawa mukai alamun munji dad’in ganin juna
“Ai nazaci bazaki futo ba”. Ladiyo tace min”.
“Saboda me”. Nace mata
Tace “saboda abinda yayan ki yace d’azun wallahi na tsorata bazan ‘kara zuwa gidan kuba”. Wani dogon tsaki naja mastssttt
Nace “kefa sakarya ce bakida wayau, yo saiki yarda da maganar sa, shi ba mala’ika ba ba kowa ba, abinda ma yasa baki ganni da wuri ba banida lafiya ne saida aka kaini asbitin bakin gari”.
Ladiyo tace “Siddi’ka baki da lafiya fa kika ce” d’aga mata kai nayi alamar eh
“meke damunki nidai banga alamar rashin lafiya atare dake ba”. Tace min
“Ke wallahi kuwa”. Nace mata “yah sadeeq ne yaimin dukan mutuwa saida akai min ‘karin ruwa”. Ido tazoro waje tana dafe kirjin ta tace “dukan mutuwa fa kika ce”.
Tsaki nayi nace “dube ta kamar ita a kaima dukan duk ta firgice”. Tace “yo dole na firgi ce, d’azu fa da yana min magana wallahi ba’kara min tsoro naji ba, saboda dana bar gidan ku kafin inkai gidan mu nayi fitsari gurin sau uku, kuma kinsan d’an Sanda ne, mugunta babu wacce be iya ba domin rannan tsallan kwad’o naga yasa wasu yara a layin ku zanzo gurin ki, zuwan da banyi ba kenan”. duk Ladiyo ce tayi wannan bayanin
ta’be baki nayi sannan nace “hhhhmm kinsan be daki banza ba ko domin wallahi bashi yaci abinda ma yasa nafito kenan neman mafita domin yau ba tsoka na zanyi ba”.
Tace “ai kuwa naji dad’in ganin ki domin bakiga yadda su Mariya da Harira suke tsokanata ba wai inyi magana suyi min dukan tsiya tunda bakyanan”.
“Me kika cemusu”. na tambayeta
“babu komi”. Tace min
kwafa nayi sannan nace “bari na gama da yah sadeeq sai na juyo kansu”.
“Yanzu nidai fad’a min me zanmai na huce”. Na kuma tambayar ta
Shiru Ladiyo tayi a lamun tana nazari can tacemin “a dake dai baze dakun miki ba saidai muyi masa mugun ta dai-dai da dukan daya miki”.
“mugun ta kuma?” nace mata
“eh”. tacemin “kawo kun- nen ki kiji yadda zamuyi”.
A kunne tarad’a mun aikuwa naji dad’in shawar ta domin nasaki raina tunda nasamu mafita, nayi tsokana iya tsokana se gurin tara na koma gida, a d’akin Inna nasa mesu a nata fira da sallama na shiga,
Da ido kowa ke bina, “wai Siddi’ka ina ki ka jene haka, gurun muta ne biyar suka kawo ‘ka ranki, Aisha ke basu hakuri da d’an kud’i”. Inna ce ke wannan maganar
cikin
in-ina nace “Inna daman naje….”.
“Daman me” tace min
Nace “waye yakawo ‘karata ban sani ba”. ta’be baki nayi nace “wai haka momy ankawo Kara ta”.
Momy tace “Hajiyan ‘karya zata yi miki, wai Siddi’ka yaushe zaki girma ne kiyi hankali, kina girma kina ‘Kara rashin wayau, Allah ya shir yaki”.
“Ameen” nace “ina abinci na?”.
“yana kitchen umar” yace “nima banci abincin ba” nace “sai kin zo” to yayi d’auko mana muci me aka girka na bukata,
Yace “fatan doya ne Momy ta girka”.
Nace “maza d’auko mana”. munaci ina bashi labarin inda naje da kalar tsoka nar da nayi, sai cizon yatsa yake yi yana fad’in wai meyi sa baki min magana ba, sanda zaki tafi, wallahi da dani za’ayi, da yanzu ba labari kike bani ba saidai ni na bada,
Nace “yo kaya’kuri bansan ai zaka ba na d’auka kai ma irin Khadija ne me tsoran tsiya”. wa’ni Umar yafad’a yana nuna kansa Allah ya kyauta ina namiji intsaya tsoro sai kace mace”._________Bayan gama cin a bincin mu da Umar na mi’ke ina hamma alamar bacci nike ji,+
Khadija ce ta kalle ni tace “ba dai bacci za kiyi ba”. Nabata amasa da “eh kwanciya zanyi”.
“Dawuri haka” ta tambaye ni
Da “eh”. Na bata amsa
“yo in banda abinki khadija ai Allah kad’ai yasan inda Siddi’ka taje bayan fitar ta gida kinga ko dole ta kwanta da wuri”. duk Inna ce ke wannan maganar, ta’be baki na nayi nace “Momy zan kwanta saida safe”.
Wayarta ta kunna ta kalli a gogo ‘karfe goma saura na dare, kallon Khadija Momy tayi tace “kitashi kibita dare yayi goma saura”. Umar ma tashi yayi ze bimu amma Momy tace “bata yarda ba tare da ita zai kwana saboda ita batasan kwana ita kad’ai”.
A kwai d’akin da idan sunzo suke sauka acikin sa, duk wani abun bu’kata Daddy ya zuba a ciki
saida safe muka ‘kara yimu su Khadija ta rigani yin gaba, daka baya na bi bayan ta,
Jinayi kamar na taka ‘kafar mutum dayike lungun d’akin a kwai duhu ‘kauyen dande babu wuta, janna-reto muke kunnawa zuwa ‘karfe goman dare a kashe, to yau yaya sadeeq be kunna ba,
ban tab-batar da ‘kafar mutum bace a gurin nataka hakan yasa na ‘kara d’ora kafata a kai na murza, ‘yar ‘kara naji anyi alamun mutum ne, koda na waiga inda nike tsammanin zan sami Khadija wayam babu ita ba alamar ta, zaro ido na nayi da kyau gabana ne yafad’i saka makon ba’kin mugun da nagani, yana wannan Murmushin nashi na mugunta,
A d’an tsorace nace “la yaya”. Ban ‘karasa maganar ba ta ma’kale,
Saka makon bige min baki da yayi, ya sha’ke min wuya,ya had’ani da jikin bango
Yana fad’in me hali be fasa halin sa gwara na kasheki kowa ya huta,
Da iya ‘karfin sa yasha ‘kemin wuyan ina son inyi ihun neman d’auki amma na kasa, cikin ikon Allah saiga Momy da Umar, sunzo wucewa hannun ta d’auke da hasken fitilar wayar ta, tana haskawa, mai zata gani wani ‘kara ta saki saida wayar ta yafad’i a ‘kasa
Inna da khadija rige-rigen fitowa suka yi saboda ihun Momy da suka ji,
Umar tuni ya das-kare a gurin, jikake tas tas ‘karan marin da Momy ta wanke yaya sadeeq
Amma duk da haka ya’ki sakina don haka ta ‘kara mai wani saida tayi mai mari biyar amma ko gezau, beyi ba dayike yah sadeeq namijin duniya ne, “to idan baza saketa ba sadeeq zan cireka cikin ‘ya’ya na”. Momy ta fad’i haka fiskar ta babu alamun wasa
jin wannan lafazin na Momy yasa Sadeeq yayi jifa dani ida nuwan sa jajur kamar Wanda yasha wani abun, huci yake yi sosai
Kasa nafadi shirim jikina babu ‘kwari ina fitar da numfashin wahala Inna da Khadija takaici ya hanasu magana, hawaye ne ke gan-gan garowa a cikin Idanuwan Momy, ta kasa magana han-nuna ta kama muka wuce d’aki na, su Inna na biye da mu abaya
Kan gado ta d’orani, na kwanta yaraf kamar gawa, ruwan fridge me sanyi khadija ta d’ibo min ta d’aga kaina ta bani nasha ina maida numfashi,
Babu Wanda yatam bayi me ya had’amu, duk kuwa da cewa zuciyoyin su cije take da tamba yoyi, daga haka kowa ya tafi ma kwancin sa,
STORY CONTINUES BELOW
a raina sa’ka yadda zan wula’kan ta yaya sadeeq nikeyi, domin wallahi bashi yake ci wani mugun tsanar sa naji ya ‘kara da d’uwa a zuciya ta,
da wannan tunanin bacci ‘barawo ya sace ni
Kiran sallar asuban fari a kunne na akayi, banida nauyin bacci, tashi nayi na zauna gaba d’aya jikina ciwo yake min amma wuya na yafi min ciwo,
Tashi nayi tsaye ina mi’ka ko salati banyi ba, ba kuma dan ban iyaba saidan tsabar shagala, da wasa da yayi min yawa,
tsakar gida nafito babu kowa d’an Murmushi nayi saboda zanyi abinda zanyi babu wanda zai ganni a irin wannan lokacin ya Sadeeq ke fitowa yayi alwala, kamar yadda Ladiyo ta tsara min haka nayi, a binda kuwa Ladiyo tace min a kunne shine “na zuba masa karara aruwan alwalar sa, da na wanka, nayi na’am da wannan shawarar da tabani, saboda nasan tanan ne kawai zan iya ramawa,
sad’a-d’awa nayi ‘bangaren sa inda yake ajiye butar sa na nufa, “Alhamdu lillah”. na fad’a yayin da na hangi butar sa, a jiye a gurin, da hanzari na ‘karasa gurin
d’aga rigata nayi na war-ware siketin jikina, na ciro ‘kullun ledar karara da nasaka Ladiyo ta sato min na Umman ta da take saidawa
Murmushin mugunta nayi, yayin da na d’aga burar naji ta cije da ruwa, bud’e murfin butar nayi, na zuba sannan nasaka hannu na na kar kad’a ruwan
Yaya Sadeeq baya barin sai zaiyi anfani da abu yanema yana tanadar sa ne tun kamin lokacin amfanin sa yazo saboda bayason bata lokaci
A jiyar zuciya nayi nabaro lungun, a hankali nike tafiya kamar mara gaskiya, Inna na hango idon ta akaina ‘kyar da buta a gaban ta, da alamar alwala ta gama, Murmushi nayi na’kara sa gaban ta nace “Inna kin fito kenan?”.
“eh na fito, daga ina ki ke?”.ta tamba yeni
“daka waje le’kawa nayi, alwala na fito sai yanayin garin ya bani sha’awa shine na le’ka waje” na fad’a mata haka kamar da gaske
“Amma mai yatada ki daga barci” Inna ta tamba yeni a karo na biyu,
wallahi Inna baccin ne ya’ki zuwa min sai naji an kira sallah shine nace “bari nayi sallar sai na kwanta”.
Tace “to ya jikin naki?” nace Inna da d’an sau’ki amma na kasa bacci, dana rufe ido sai na dunga ganin kamar zai zo ya sha’keni”. Saboda yace “saiya kasheni”.
Inna na salati tace”yanzu Garban ne yace saiya kashe ki!?”. Eh Inna shi fa ai ba ‘karamin mugu bane”. Na ‘kara maganar ina yin hanyar ban d’aki,
Na bar Inna da mamaki
Bandaki nashiga nayo fitsari, na fito nazau na a kan kujera, nafara alwala kenan saiga Yaya Sadeeq nan, nayi kamar ban ganshi ba, na cigaba da yin Alwala ta, ta gaba na yazo ya wuce, bayan shi nabi da kallo ina Murmushi, a cikin zuciya ta nace “zaka bawa yan garin ku labari, zaka san kayi da ‘yar halak”.
bandaki yashiga yajima aciki, can saiga sa ya fito, a lokacin nagama Alwala ta amma ban tashi a gurin ba,
Tashi nayi na koma d’an nesa da inda ya tsugun na
Alwala yafara yi ganin ya manta beyi kus kuran baki ba naji sanyi a raina, d’aki na koma na tsaya a bakin hundo, ina kallon sa,
yana wanke fuska ne naga ya mike kamar wanda aka tsungula gabansa yakama yana murzawa🤣 bansan sanda daria ya kwace minba can kuma yafara kifta ido se yanzu yake tunani tabbas yaji ruwan wani iri lokacin dayeke shakar hanci, abinda yasa baiyi wani tunani ba yaga butar sa ce shi kad’ai babu wanda yake amfani da ita, sosai yake murza idonsa ati shawa na biyo baya haka yaita fama 💃 d’aya hannun rike da gaban sa yana murzawa 🤣
Dariya nike ina tsalle abin nema yasa mu sosai Yah Sadeeq yazama karamin mahau kaci gashi har an shiga masallaci amma shi ko alwalar be samu ya gama ba
Sosai abin ke damun sa musamman gabansa yafi sosa gurin, a haka Momy tafito ta same sa, watsi tayi dashi kamar bata ganshi ba, jin motsin da yayi ne yasa ya d’an bude idon sa, saboda yaga waye, wata a zaba ce ta ‘kara shigar masa ido har saida ya saki ‘yar ‘kara, tsaki Momy taja tagama abinda za tayi nan tabar sa tanai masa kallon mahaukaci, 🤣
Khadija Khadija yah Sadeeq ne ke ‘kwala mata kira, barci take yi, ganin yana kiran ta nayi saurin zuwa bakin gadon ina dukan ta,da magagin bacci a idon ta “lafiya?”. Tace min ‘yar dariya nayi nace “yah Sadeeq ke kiran ki”. tashi tayi zaune tana zaro ido kamar ba me magagin bacci ba “yana ina?”. tace min “tsakar gida”. na bata amsa
Nace “amma fa kiyi a hankali don naga kamar yasamu ta’bin hankali”
jin yana ‘kwala mata kira dakarfi yasa ta fad’uwar gaba babu shiri ta sakko daga kan godon, tayo waje, yadda taga yaya sadeeq d’in a tsakar gida ba ‘kara mar kunya yabata ba, gani Yaya tafad’a sanda ta ‘karasa gansa,
“d’auko bokiti a d’aki na ki zuba min ruwan wanka, ki kai min ban d’aki”. Sadeeq ya fad’i haka.
Da “to” tabi shi kamar yadda ya umar ceta haka tayi, a binda khadija bata sani ba ina la’be lungun bayi tana aje ruwan nazuba mai karara nai fitowa ta, tsaye na ganta gurin tana cemai “yaya na kai maka ruwan”.
“Kama hannu na to” yace mata, hannun na sa takama har bayi ta kaisa, sannan tafito
Idanun sa a rufe suke har yanzu cire jalla biyar jikin sa yayi, sannan ya laluba yaji babu sosan wanka, kiran sunan Khadija yafa rayi nikuwa daman ina kusa da bayin, khadija kuwa tayi alwala ta tafi d’aki sallah, “kawo min sabulu”. Yace
daman Yah sadeeq bai wanka da so so ko kadan sai sabulu kawai, Murmushi nayi naje na dauko mai sabulu wanda na badeshi da zallan tarugun dana ga Inna ta daka sa ta shanya asama jiya,
hhhmmmm nace “ai wallahi tunda ka ta’bani sai kayi da ‘ya, taka kujera nayi naje fa mai sabuln cikin bayi
Komawa gefe nayi na zauna inajin raina fes banida wata damuwa,
har gari yafara wayewa babu sadeeq babu labarin shi nikuma na’ki tashi domin ko sallah ma banyi ba
Ya sadeeq kuwa yazama abin tausayi cikin bayi yarasa wannan wani irin bala’i ne, shida yayi wanka domin yasa mu sau’ki amma sai a kasin haka, susar jikinsa yake iya ‘karfin sa duk da idan yasosa yanajin wani mugun rad’ad’i a jinkin sa, amma bashi da wani zabin da yawuce susar,
har 7 am be fito ba Inna ce zata shiga bayin na kalle ta nace “Inna fa da mutum”.
“Waye?” tace min “yah Sadiq ne” na bata amsa,
Inna tace “me yake yi agidan har yanzu da bai fita gurin aiki ba, naga da an idar da sallar asuba yake tafiya”.
Nace “to Inna kika sani ko anyi musu canji ne kinsan ana canza su ai”.
“haka ne” Inna tace min, d’an matsa wa nayi kusa da ita, sannan nace “Inna amma fa yau yah Sadeeq wallahi kamar mahaukaci, domin tun asuba yake abayin nan, kafin yashiga ya dad’e anan tsakar gida yanayin wasu a bubuwa masu kama da na mahaukata”. Zaro ido inna tayi
na d’aga mata gora, nace idan baki wa yarda ba, Ki je tambayi Khadija ko Momy saboda dukan su sun ganshi a cikin yanayin,
♾️♾️♾️♾️♾️