NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 3
Www.bankinhausanovels.com.ng
_______Na shiga uku ni Siddi’ka Yahyah D’an ‘kwambo anya su Daddy suna ‘kauna ta nasan kaf duniya babu wacce Sadeeq ya tsana kamar ni, amman wai yau ni ce zan zama matarshi+
“Kutashi kutafi Allah yayi muku albarka”.
Daddy ne ya fad’a haka
Sadeeq yariga ni tashi saboda ni jikina babu kuzari
“ji mana Sadeeq” Daddy yace “ka kira abokanan ka na kusa a waya ka shaida musu”.
Murya acan cikin ma’ko garo Sadeeq ya cewa Daddy “ba sai sun shaida ba”. Yana gama fad’ar haka ya fice
A masal-lacin juma’an dake garin buruku aka d’aura auran *SADEEQ ALIYU MAI GORO* da amaryar sa *SIDDI’KA YAHYAH D’AN KWANBO* d’um bin jama’a sun shaida d’aurin auren duk da kasan cewar babu ango da abokanan sa, Daddy ne yayi wakil cin Siddi’ka, inda d’aya daga cikin abokan Daddy da suka hallar ci taran, mai suna Alhaji Imran yayi wakilcin Sadeeq, auren da aka d’aura abisa sadaki dubu tamanin, lakadan ba ajalan ba, yayin da Alhaji Imran ne ya biya sadakin
A kwai ‘yan ‘kauyen Dande da dama, dasu ka samu halar tar zuwa masal-lacin, saboda su gabatar da sallar juma’a da yawan su mamaki suke saboda kowa yasan tsamar dake tsaka nin Sadeeq da Siddy amma wai yau ya zama mijin ta ko da shike daman ance idan zaka yi ‘kiyayya kada ka tsanan ta haka ma soyayyar
Da haka taro ya watse koda Daddy ya dawo gida anne mi Sadeeq anra sa kuma an kira wayar sa a kashe
Siddi’ka kuwa tun sanda ta shiga d’aki take raira kuka, rarrashin duniya anyi mata amma ta’ki barin kukan kamar ma dad’a zuga ta suke yi, haka suka gaji da lal-lashin ta suka zuba mata ido, saida Daddy yafa d’awa su Inna zai shigo dasu Alhaji Imran Sannan yaje ya shigo dasu, a falon Hajiya Inna suka zauna daman su Hajiya Inna sun girka shinkafa da miya Khadija ce keta hidama da ba’kin Daddy Sai da suka ci suka sha sannan Inna tazo suka gaisa
Suka yi mata Allah yasa alkairi anan Daddy yayi mata sallama yace su zasu wuce Abuja da a can jirgin su zai tashi izuwa lagos
“To bari na kira maka Aisha d’in ko”. Inna ta fad’a tana ‘ko’karin mi’ke wa
cikin sosa kai Daddy yace “ai na sallame su suma nan bada jimawa ba zasu wuce” mamaki ne yakama Inna saboda ita dai bataga sanda ‘karami yayi magana da Aisha ba
Hajiya Dady ya kira sunan ta “da mai sunan manya zasu tafi nayi maganar yar aikin za a nemu miki nanda kwana biyu”.
“Wace yar aiki! ‘karami duk yaran dake ci’kin Dande basu isa ba har sai an nemi wata, ai ko Ladiyo ‘kawar Siddi’ka na yiwa iya-yen ta magana tunda yarinyar ta iya aiki, kuma ta ma girmi Siddi’ka d’in,
Nasan baza ta ‘ki ba, sai ta dunga zuwa tana tayani d’an wanke wanke da shara tama dun ga d’ebe min kewar siddy d’in”.
Inna ta cigaba da cewa “Idan wata yayi kana yima ta d’an ihsani”.
“babu damuwa” Daddy yace yana mai ciro kud’i daga aljihun sa masu tarin yawa, ‘yan dubu dubu ya mi’ka mata
” ‘Karami kud’in wancen watan ma daka bani suna nan ban taba suba saboda duk abinda nike so akwai a gidan nan da ka bar shi kawai a gurin ka Allah yama albarka”.
Hannun ta Daddy ya kamo yasa ka yan bandir d’in 1000 guda biyu “haba hajiya ki karba koda sadaka ne kinayi dasu idan ki ka ga mai buka ta”.
Godiya Inna tai ta kwara rowa ‘Karami tanayi mai addu’ar Allah yatsare
“Ina mai sunan manyan take ne Hajiya?”. Daddy ya tambaya
“ai tun sanda ka fita ta shiga d’aki tana rusa kuka mun gaji da lal-lashi ne muma”.
STORY CONTINUES BELOW
“Wani d’akin?”.
“na can karshe”. Ta bashi amsa
Tashi yayi ya cewa abokan sa “minti biyar”.
A kan gado ya same ni kwance nayi rufda ciki
Siddi’ka Daddy ya kira suna na cikin sas-sanyar murya
Inaso kisan duk abinda ha’Kuri bai ba bawa ba a rayuwa rashin sa ma ba zai ba da ba, kuma wannan shine burin mahaifiyar ki tin sanda aka haife ki tace “idan Allah ya raya ki d’an ta Sadeeq shine mijin ki ko bayan baran ta mu cika burin ta, A halin yanzu bamu san awani hali Amina maman ki take ciki ba, zai iya yuyuwa tana nan a raye nesa damu, zai kuma iya yuyuwa Allah ya d’auki ranta, amma muna nan muna addu’a idan har Amina tana a raye Allah ya bayyana mana ita, nayi hakanne a yanzu saboda bani da tabbacin zan ‘kara wasu shekarun a raye, nasan ko bayan babu raina na cikawa kanwa ta burin ta za tayi alfahari dani, kiyi mana biyayya amatsayin mu na iyayen ki bazamu taba cutar da ke ba zakiga ribar abun nan gaba”.
Duk maganar da Daddy yayi na kasa d’ago kaina, Ko motsin kirki na kasa ina nan a yadda ya shigo yasa meni, jin shirun da nayi ne naji ajiki na ya fita daga d’akin, kaina na d’ago ina ‘karewa d’akin kallo Bansan mai nike nazari ba amma inajin kamar raina zai fita
Umar ne yashigo hannun sa d’auke da kular abinci har kan gadon ya hau yace “aunty Siddy please kada kicemin a a don soyayyar da kikewa goggo Amina ki tashi kici abincin nan nasan dai kina mutu’kar santa kuma duk ‘yar da aka ce tayi abu dan iya yen ta to indai tana son su za tayi”.
Jin Umar ya ambaci mahaifiya ta na tashi zaune saboda babu ‘yar da zata’ki mamar ta “mi ‘komin kular”. Nafad’a murya ta a dashe
Koda na bud’e shinkafa ce da miya har da nama a ciki, cokali nasa na fara cin abincin amma kwata kwata bemin dad’i ba ji nike kamar ba asaka magi aciki ba
“Umar wai haka abincin nan yake”. Na tambaye sa
“mai yayi” yace min
“naga kan infara ci yana ta zuba ‘kam shi yanzu kuma da nike ci wallahi ji nayi kamar inacin magani”.
Kallo na yayi muka had’a ido dashi yace aunty siddy inaga bakin ki ne domin kowa ya yaba girkin nan yadda yake da kamshi haka yake da dad’i abaki ma”.
“To iya magana”. Nafad’a ina tura masa kular abincin
“Kaddai har kin ‘koshi”. Yace yana kallo na
“na ‘koshi mana tashi kasa momin ruwa”.
“To” yace ya fice daga d’akin, jim kad’an sai gashi da ruwa a cup
yace “Momy” tace “kiyi wanka yanzu gata nan zuwa”.
“To”. nace
dama akwai bayi a d’aki na amma tsabar neman rigama yasa bana shiga, kuma da sabo dan munriga munsa ba da bayin tsakar gida tun kafin a maida mana gidan mu ginin zamani
Yaukam ciki na shiga wanda nike tsokanar ko sunan sa ma bana son inji ankira min
Ban wani dad’e ba na fito daka bayin kaya na tarar abakin gadon da alamar sababbi ne harda bra da fnt
Ina cikin mamaki sajga Khadija ta shigo fes da ita cikin wata tsaleliyar atamfa “cikin zolaya tace min amarsu har yanzu baki shirya ba Koda yake daman shirin amare ance yana da dad’e wa, sai kiyi kishir ya dan ke kad’ai muke jira”.
a kwati na na nufa saboda na d’auko kayan da zan saka,
da mamaki Khadija tace “Siddi’ka baga kayan ki nan ba akan gado”. Momy tace “su zaki saka”.
Hau shin kowa nake ji cikin masifa nace wa Khadija “naji to sai ki ban guri”.
Sai da ta ‘kyal-‘kyale da dariya sannan tace “amarsu kada in ‘bata miki rai naji ance ba’a san a ‘bata ma amarya rai, musamman ranar d’aurin auren ta, idan ni baki bud’e min ba zaki bud’e ma yayana”.
Khadija tagirme ni da 2 years nasan ba zata rasa sanin aure ba tunda ita abirni take kuma tana zuwa makaran ta, sa ‘banin ni da nike yawan gyad’a
Tana fita na rufo ‘kofar sai da na shirya tsaf sannan nafito sai ‘kam shin turare ke tashi
Da alamar kan a kawo min kayan sai da aka fesamusu turaruka masu ‘kam shin gaske da tsada
buga ‘kofar naji a nayi koda na bude Umar ne hannun sa d’auke da jaka da takalmi da gyale
Mi ‘komin yayi Momy tace “in kawo miki ki saka idan shirya ki fito”.
Kar ‘ba nayi takalmin irin mai tsinin nan ne ni kuma banason irinsa koda nasa tafiya d’aya buyu na turgud’e
Jakar tanada yar girma kalar dai ta amare a kafad’a na rataya gyalan ko ahan nu na ri’ke sa
Umar sai dariya yake min wai ahannu zan rike jakar ko sau raran sa banyi ba
A gaskiya ina son kwalliya a rayuwa ta saboda haka nike tafiya ina taku d’ai-d’ai duk da ban iya tafiya da takalmin ba zuwa zuwa ina turgu d’ewa Amman hakan bai hana ni yin yanga ba naman ta da wani lamarin aure
Afalo nasami su Momy duk sun shirya
“Momy wai ina zamu haka”. Na fad’i haka ne sanda nike zama kusa da Inna
“Abuja”. Momy ta bani amsa
zaro ido na nayi nace “Abuja kuma Momy shine zaku tafi da ni?”.
“Eh” kawai tace min narai-narai nayi da ido ‘kwalla na zubo min Daman koda nai wanka banyi kwalliya ba ko hoda ma ban shafa ba saboda haka na cigaba da yin kuka na ina share ‘kwallar da bayan hannu na
Inna ce ta kama hannu na tana matsar kwalla, ba tare da tace min komai ba
Cikin kuka nace “Inna kada kibari atafi dani mana Inna nasaba dake, bazan iya rabuwa dake ba nasan wannan tafiyar ba irin wacce na saba yi bane saboda haka jiki na ke bani, nidai gaskiya bazan je ba”.
Cikin sanyin murya Inna tace “to ba gasu Khadija ba acan kuma akwai su bilkeesu baki da damuwa zaki saba kuma duka ‘yan uwan ki ne”.
“Siddi’ka inaso na ingan ta miki rayuwa ne”. saboda ‘Karami yace min ” idan ban bar ki kinyi karatu ba nan gaba dani zakiyi kuka”.
Ina sharar ‘kwalla nace “Inna ni ba zanyi kuka dake ba ki yarda dani da iya gaskiya ta nike magana”.
Daga haka bata ‘kara ce min komai ba
Momy ce ta kama hannu na ta yima Inna sallama ina kuka ina kallon Inna haka na baro ta
daman driver mu yake jira a bakin ‘kofar fita naci karo da Ladiyo data ke ‘ko ‘karin shiga gidan mu
A d’an tsora ce ta kalleni sai tayi baya
Bance mata komai ba nashi ga mota idan ta naga ya kawo ‘kwalla kuma ta bani tau sayi,
ganin haka naya fito ta da hannu aikuwa da gudu tanufo ni
“Siddi’ka ina zaki haka ko sallama babu?”.
“Birni mana”.
“inda kike zuwa?”.
kai kawai na d’aga mata
“Amma shine wannan karan ko sallama babu?”.
“nima bansan da tafiyar bane ladiyo kuma karatu zanyi a can d’in ba yanzu zan dawo ba”.
“Karatu fa kika ce Siddi’ka, mai zakiyi da makaran ta?”.
“Nima bansan me zanyi da ita ba Ladiyo amma dai an cemin tana da mutu’kar amfani kuma nan gaba zai temaka min zanji matu ‘kar dad’in karatun”.
Cikin sanyin murya Ladiyo tace “to Allah ya bada sa’a Siddi’ka don Allah kada kimanta dani”.
Tabani tausayi sosai nasan kaf kauyen nan Ladiyo ba tada kama ta kuma nima banida kamar ta
Wata ran ma ni zanyi tsoka na amma sai inja mata duk da haka bai sa ta rabu dani ba
Nace “Bazan manta dake ba Ladiyo zan dawo gare ku Ina yi miki fatan alkairi kema”.
“Ki shiga gurin Inna kice injini taba ki kayan sawa na ga baki d’aya”.
“To” tace tayi min godiya mukayi sallama ta shige gidan mu
A lokacin su Khadija sun shiga mota driver yaja muka d’au hanya_______bamu wani tsaya akan hanya ba Dan Momy tace “duk mai uzuri yayi ha’kuri har sai munje gida saboda ance mata hanya babu kyau”. Da misalin ‘karfe 3:25pm muka isa garin birnin tarayya Abuja, tun daga unguwar zaki san ba irin unguwar nan ce ta kowa da kowa ba sai d’an wane da wane tunda ga wajen gidan Daddy zaki lsan gidan manya ne saboda ko fulawowin kansu da aka zagaye gidan dasu abin kallo ne, ba sai ka shiga daga ciki ba, ya wan cin gida jen un’guwar ginin gidan sama ne, idan ki kaga wannan sai kiga duk yafi kyau, amma kina ganin wani sai kice wancen bai kai wannan ba to haka dai gidajen unguwar suke, na wane yana wane na wane,+
Ba yau na saba zuwa ba amma har yanzu na kasa ri’ke sunan un’guwar Saboda ita kan ta sunan un’guwar na ‘yan gayu ne kuma da turan ci ne 🤔
Gidan su Khadijan ma yana d’aya daka cikin ‘ke rarrun gida jen saman dake un’guwar, shiyasa nike son zuwa saboda ina son bene a rayuwa ta
Driver d’in mu yayi horn adaidai bakin ‘katon get din gidan
Me gadi ne ya le ‘ko ta ‘karamar ‘kofa ganin motar Momy ne yasa shi saurin bud’e get motar mu ta sulala cikin gidan mai gadi ya maida get ya rufe
Daka bisani yazo da gudu ya bud’e wa Momy cikin ladabi yake yi mata sannu fuskar Momy a sake ta amsa masa “mun same ka lafiya?”. “Lafiya lau hajiya”. Mai gadi ya fad’a yana sadda kansa ‘kasa “masha Allah babu dai wata matsala ko?”. Momy ta kuma tambayar Habu mai gadi, yace “eh Hajiya babu wata matsala komi yana tafiya daidai”.
“A kwai kayan mu a bayan mota kashigo mana dasu ciki kaida Idi”. Da “to” suka amsa su duka
A kasalan ce muka fito daka cikin motar muka shiga cikin falo ko waccen mu tasan d’akin ta dan haka muna shiga ko wacce tayi inda tasan nan ne dakin ta yake
A sama d’akin danike sauka yake don haka na haura abina amma dana murd’a hannun ‘kofar sai naji a kulle yake gam
‘Da kin Khadija dake kallon nawa naje shima a kulle yake sai dai naji motsi da alamar ita tuni tana ciki ‘kwan-‘kwasa ‘kofar na shiga yi, daga can ciki tace “wace”.
“Siddy ce”. nabata amsa
Jim kad’an sai gashi ta bud’e ‘kofar jikin ta d’aure da tawul da alamar har ta cire kaya wanka zata shiga
“Khadija mukul-lin d’aki na nazo ki bani”.
“To” tace ciki ta komo sai gashi ta fito hannun ta rike da mukullin na amsa nayi gaba a bina
“Matar yaya a huce gajiya lafiya”. tace min, da gudu na na juyo dan na doke ta amma sai ta maida ‘kofar ta rufe tana dariya
♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
A bangaren sadeeq kuwa yana barin d’akin Inna bai zarce ko ina ba sai gidan abokin sa Farooq bai kirasa a waya ba amma yayi sa’a saboda ya same sa ne yana ‘kokari fita, nan dai ya bashi hannu suka gaisa Farooq yace “yanayin ka ya nuna kamar kana cikin damuwa, kuma ba ka saba zuwa gida na a irin wannan lokacin ba, kodai kai da mutuniyar taka ce? Saboda nasan labarin gizo baya wuce na ‘ko ‘ki, da fita zanyi na gaji da zaman gidan, amma tunda kazo mu shiga ciki ka fad’a min abinda ke tafe da kai”.
To bayan sadeeq ya shiga cikin bedroom suka wuce, saboda yanayin tsarin gidan irin me ciki da falo ne sai bayi da kitchen kuma duka haka gidajen kusa dashi suke saboda duka manyan ‘yan sanda ne wasu suna da 1 star wasu biyu wasu uku wasu kuma igiya ce gare su, da dai sauran su kusan unguwa ce guda aka bar ma ‘yan sanda ita, shi yasa da wuya kaji ance wani abu ya faru a cikin ta ko kamar ace anyi fashi ko an sace wani, saboda a zagaye take da masu tsaro kamar barikin sojo ji shima Sadeeq saboda ansan shine kuma akwai nasa ‘ban garan a ciki shiyasa da yazo ake bude mai get ya shigo abin sa
STORY CONTINUES BELOW
Kan gado Sadeeq ya fad’a yana maida numfashi, Farooq ya zauna a kan wata kujera dake bedroom d’in yace “ba ba kaifa nike jira kace wani abu mana ka wani baje a kan gado sai kace wata mace”.
Tashi Sadeeq d’in yayi ya zauna ya shiga jero ma abokin nasa d’anyen hukuncin da su Daddy suka yanke, Farooq ya san Sadeeq ba zai ta’ba yi masa irin wasan nan ba musamman ma da yasan cewa Sadeeq da Siddi’ka babu jituwa a tsakanin su saboda haka ya gyara zama yace “Alhamdu lillah gaskiya naji dad’in wannan had’in kuma da kace d’an yan aiki wallahi sunyi dai dai, Ko ba komai zaka daina tsangwamar Siddi’ka d’in kuma sha’kuwa mai ‘karfi zata shiga tsakanin ku, saboda haka ka tashi muje a d’aura auren da mu a kwai wata sabuwar shadda na da nasa aka d’inka min da niyar yau in sata to sai bayan na anso ta daga wurin taila na canza ra’ayi”.
Kwanciya Sadeeq d’in ya gyara a kan gadon yace “d’an iska mayen mata to ai sai kaje in yaso d’aurin auren ma sai ayi da kai, amma ni nan daka ganni babu inda zani wallahi, wai ni za’ama aure kamar wani ‘karamin yaro, arasa ma wa za a had’a ni da ita sai ‘yar ‘kara mar yarinya wacce ko gama sanin inda yake mata ciwo batayi ba”.
Dariya ce ta kama farooq saboda haka yay ta da rawa abin sa saida ya gama ya fara lallashin a bokin nasa akan ya tashi ya shirya suje d’aurin auren, amma Sam Sadeeq yace “bai san da maganar ba”. Farooq yana ji yana gani dole ya ‘kyale shi amma ba dan ransa yaso ba
Wayar sadeeq d’in ce ta hau ringing cikin hanzari ya d’auko wayar daga aljihun sa ganin sunan Haseem yana yawo akan screen d’in yasa shi jan dogon tsaki yace “kagani ko Farooq abinda nake gudu kenan yanzu haka kira na yayi ya cemin ashe nayi aure ko gayyata babu”. Kiran ne ya katse, yayi saurin kashe wayar gabaki d’ayan ta wannan dalilin ne yasa da Daddy ya kira wayar Sadeeq d’in yaji ta a kashe
Sadeeq ya ci gaba da cewa “ai ni yanzu na shiga uku Daddy ya gama jamin abun kunya a gari, ni ba mai laifi ba da sai na ringa yawo da abun fuskar da zan sauya kama”.
Farooq dariya harda ri’ke ciki yace “wallahi aiki ya ganka yanzu za ka fara nidai d’an kallo ne saboda ko na baka shawara ba lallai ne kayi amfani da ita ba amma bari na gwada baka”.
Sadeeq yace “wallahi Farooq na tsani yarinyar ne ji nike da ma na mutu na huta da dai nayi rayuwa da ita amatsayin mata ta”.
“Kana ruwa aboki na, to kai wai me yarinyar nan tayi maka ne haka da ka tsane ta”.
“haba Farooq wai har kana bu’katar ‘karin bayani, bayan komai a bayyane yake, kasan nafi san na auri wayay-yiyar mace mai aji da yanga wacce ta gama digiri dinta in so samu ne ma ta fara aiki koda kuwa wani iri ne sannan kuma kada shekarun ta suyi ‘kasa da 25 to ko bata da masifar kyau in dai tana da wa’innan abu buwan da na lissafa maka zan aure ta”.
Zai ci gaba da magana Farooq ya da katar dashi ta hanyar fad’in dakata malam “ai na d’auka ka bar wannan banzan tunanin da kasa a ranka zaka ro’ki Allah ne yayi maka za’bi mafi alkairi ashe ba haka bane, to ina so kasan har yanzu Siddi’ka yarinya ce ba a haka zata ci gaba da rayuwa ba ko kana da ya ‘kinin cewa baza ta canza ba? Ya fad’a yana kallan Sadeeq d’in”.
“Eh Farooq”. Sadeeq yace yana d’aga murya “bazata canza ba a haka zata gama rayuwar ta🤔 saboda irin zuciyar uban ta gare ta, kuma bugu da ‘kari rashin jin maganar ta yayi yawa, kaf ‘kauyen Dande babu wan da bai san ta ba ko ina idan na wuce ana kallo na saboda an san ni yayan ta ne, nasan ma dan suna jin tsoro na ne da tare ni zasu dunga yi, nafisan yarinya natsats-tsiya mai kunya”.
“Hhhmmmm Sadeeq nidai shawara ta anan ita ce kabi komi a hankali kada kayi gag-gawa, amma ni banga laifin Siddy ba rashin jin magana da kace yarin ta ce take damun ta, wataran idan akace tayi zata ce ba tayi ba, sharri ake mata”.
“Sa’ar Jiddah ce fa mai yisa Jiddah bata yin duk wa’innan abu bu wan da Siddi’ka keyi?”.
“To ai Sadeeq kasan yara kowa da kalan ‘kuru ciyar sa idan ka bibiya a kwai abinda ita Jiddahn ta keyi Siddi’ka kuma koda kud’i akace tayi ba zata yi ba kuma idan ka lura Siddi’ka goyan kaka ce duk abinda tayi sai ace daidai tayi ba a nuna mata tayi kus kure, amma da ina tabbatar maka da sai tafi Jiddah han kali”.
STORY CONTINUES BELOW
Ta’be baki sadeeq yayi yace “wallahi ina raga mata ne saboda gwaggo Amina, amma yanzu tunda ta shigo gona ta zan koya mata darasi😢 zan nuna mata tayi babban kuskure da Daddy yace zai aura mata ni bata ce A a ba”.
Kafad’ar sa Farooq ya daka sannan yace “Allah ya bama mai rabo sa’a”. Ya fice a d’akin
♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
*GARIN ABUJA*
Koda na bud’e d’akin na same shi atsaf tace kamar yadda nayi zato saboda duk zuwa haka nike samun shi
Da sallama d’auke abaki na, na shiga sannan na maida ‘kofa ta na rufe da d’an mukulli Kan gado na fad’a ina maida numfashi wash nagaji matu’ka
Baccin gajiya ya d’auke ni ba tare da nayi sallar la,asar ba daman sai da muka yi azahar agida muka taho
Hankali na kwance ni keyin bacci na na manta dawani auren yaya sadeeq da yake kaina
A cikin bacci na nayi wani mummunan mafarki wanda ban taba yin irin sa ba tun da nike arayuwa ta, ban fahimci me mafarkin ya ‘kunsa ba tsabar rud’a nin dake cikin sa,
A firgice na farka amma nakasa yin salati saboda ban saba ba, ina ta zaro ido na alamar tsoro nakasa firta koda kalma d’aya ina son in tuno abinda nagani acikin mafarki na amma na kasa, sai wani masifaf fan ciwon kai daya saukar min a lokacin daya, sosai tsoro ya shigar min har banason nayi motsi saboda sai naga kamar za a kama ni
Bugun zuciya ta ne ya ‘karu yana bugawa da sauri da sauri saka makon buga ‘kofa ta da naji anayi
Kara du’kun-‘kune kaina nayi a cikin bargo, daka waje naji ana fadin “Ummi ce ki bud’e”.
Jin muryan Ummi da nayi yasa nayi han zarin saukowa daka kan gadon jiki na ‘bari na bud’e mata ‘kofar ta shigo, rungume ni tayi tana ihu Bata lura da yanayin da nike ciki ba turanci ta fara su burbud’a min bayan tasan bawani ji nike ba amma tsabar iya yin Ummi takeyim shi Jin ban rungume ta ba kamar yadda muka saba yasa tasake ni, tana kallo na
tace “sisi kamar bakya hayyacin ki meke damun ki”.
“Bacci na tashi”. nace mata bansan maye dalilin ‘boyewa Ummi gaskiyar abinda yasa yanayi na ya sauya ba
“Haba koda naji”. ta fad’a tana kama hannu na, muka fito daga d’aki na, d’akin ta muka shiga wanda ya kasan ce a tsaki yar nawa da na Khadija
“Amma yakamata kiyi wanka sisi kican za kayan jikin ki kin ma yi kokari da kika yi bacci dasu a jikin ki ni yaushe zan iya”.
“Ai ke ki ka ce Ummi ni kin san na saba ko a kauye kayan da nasa dasu nike yin bacci duk sabun tar su bana sau yawa izuwa na bacci duk da ina dasu”.
Wata uwar ‘kara ta saki a razane na kalle ta “la fiyan ki ‘ka lau kuwa Ummi?”.
“lafiya ta lau sis naji kin anbaci kauye ne kinsan ni da ‘kauye amana don Allah yi ki fito wanka kizo ki bani labarin Dande”.
Ban kuma cewa da ita komai ba, na nufi bayin wankan ta masha Allah shine abinda na fad’a bayan na bud’e bayin naga ko mai na cikin bayin fari ne ‘kal kamar a zuba abinci a kasan a lashe saboda yadda kasan tayil din ke she’ki ga wani sihir taccen ‘kam shi da yake tashi,
A han kali na d’aga ‘kafa ta na shiga bayin duk da banyi addu’a ba amma na shiga da ‘kafar hagu cikin kwamin wankan na shiga na kun na famfon ruwan zafi da na sanyi na dad’e a cikin ruwan d’umin sannan na fara wanka ina gamawa na d’aura tawul din dana gani rataye a ayin na fito
Ina fitowa ana kiran sallar magriba saboda haka na koma ciki na d’auro alwala na fito
A gefen gado nasamu Ummi zaune tana buga game a laptop
Saida ta dube ni tace “gaskiya sis kin dad’e sai kace kina canza fata gashi kuma kina nan yadda kike”.
Ban kula ta ba na nufi durowar kayan ta saboda suna yimin dai dai, bayan na bud’e na ga wata doguwar rigar yadi mai laushi me run madara fitet ce ba tada wani kwalliya amma duk da haka d’in kin nada kyau,
ban wani damu da saka bra ba nafi sa haf bes, sif d’in haf bes din na bud’e na ciro d’aya sannan na bude na fant na d’auko sabo wanda na gansa da ‘yar takar darnan a jiki alamun ba a sa ba, da yake duk nasan inda suke harda na siket din ciki haka na fiddo duk abinda nikeda bu ‘kata
Sannan na nufi gaban madubi na zauna kan kujerar dressing mirror na fara shafa mai ina gamawa na d’auki tura rukan ta masu ‘kamshi da tsada na fesa a jiki da kaya na duk kuwa da wasu ba akaya ake fesawa ba amma saboda ni ban sani ba haka nai ta fesawa, saboda a lokacin Ummi ta shiga bayi, doguwar rigar na saka na dakko dadduma don rama sallahr da ake bina sannan inyi wacce muke cikin lokacin ta
Ina cikin yin sallar Ummi ta fito daman dad dumar na kar kata ta yadda mutane biyu zasu iyayin salla akai
Ko da na idar ban wani tsaya yin addu a ba na cire hijabin
Na sauko kasa na tarar da duka ‘yan gidan kowa yana nan harda Aunty Bilkisu da yaranta guda biyu Samahir da Shakran, Khadija da Umar ga Momy sai Jiddah da ke ta faman danna waya ko me take danna wa? oho ahankali na ‘karasa sau kowa daka kan benan gurin Momy naje na rungume ta nace “Momy ya gajiyar hanya”. Ina mai hawa kan cinyar ta na zauma
Tace “Siddi’ka rigima ni ban san yaushe zaki girma ba saboda wani abun idan kika yi ko Umar auta ba zaiyi ba”.
Momy nidai naji saboda bazan ta’ba girma da hawa cinya ba”.
“Sarkin san jiki” Aunty Bilkisu ce tafadi hakan
“La Aunty Balki bari inzo mu gaisa”.
“Wai bana hana ki cemin Balki ba suna na bil’kees”. Ta fad’a tana gyara sunan mu ka kwashe mata da dariya
Dai dai nan Ummi ta sauko muka dasa firan da ita Samaheer ce kan cinya ta ina yi mata wasa tana ‘kyal-‘kyala daria
Suwaiba mai aikin gidan ce ta shigo tace “Hajiya na kam mala yana kan dinning”.
“to” Momy tace sannan ta kallo mu
“Oya kutashi muje muci abinci dan nasan kowa anan yana jin yunwa”.
Kamar jira muke duk muka mi’ke muka nufi dinning kowa ya zauna muna ci muna d’an ta’ba fira taliya ce sai faten dankin turawa da yaji hanta sai farfesun naman kaza mai yaji, babu laifi Suwaiba ta iya girki dan idan Daddy baya nan ita take yin duk wani abu da za aci ko a sha, sa’banin idan yana gida Momy ke girka wa tace mu zo mu taya ta
bayan mun gama cin abinci muka dawo falo muka ‘kara dasa sabuwar fira har aka kira sallar isha’i duk da Jiddih tunda na sauko magana bai had’ani da ita ba saboda ita ta nada jin kai ga san nuna ita wata ce ni kuwa ba zan d’auki iskanci ba dama ba shiri nike da ita ba saboda abu kad’an ke had’a mu mu fara dambe kowa bai san raini____Bayan mun idar da Sallar isha’i wata firar muka cigaba da yi, idan Khadija tayi nata nima sai nayi nawa hakama Umar, yayin da Jiddah ke faman cika tana batsewa tana jan dogon tsaki, ko ita da wa oho,
_yanzu haka Umar ne ke bamu labarin wani_
_Almajiri daya shiga bara gidan wata amarya sai mijin_ _yace “almajiri kawo kwanon ka”. Sai amarya ta leko ta amsa, ta zuba masa abincin, Koda ta miko mai kwano sai ya amsa yatafi zauran gidan yana kuka, sai mijin amaryar yabiyo almajirin, ya tam bayesa meye dalilin kukan nasa “ko abincin ne ba zai isheshi ba?”. Sai almajiri ya girgiza kai, sai mijin amaryar yace “to maye kake ma kuka?”. Budar bakin Almajiri sai yace “shi ba komai ya sashi wannan kukan ba illah yana tsoran agama aure kyawa wan mata kafin lokacin su yai_
” Idan ke/kaine ya zaki/ka yi”, haka ya jefe musu tambaya aikuwa nan sukaita tafka muhawara suna shirme
♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Sadeeq kwan ce a kan gadon farook yana cikin Instagram sai kallon hotuna yake, kwatsam idanuwan sa suka sauka akan hotan wata yarinya, acikin zuciyar sa yace “daga ganin ta tanada aji kuma ba zaka ce mata ‘karamar yarinya ba domin zata iya kaiwa 25 years old da haihuwa”. Kara shiga account dinta yayi nan take hotunan ta da take dorawa suka bayyana sosoi Sadeeq ke kallon hotunan, sunan account din ta ya kalla yaga anyi rubuta kamar haka *Zuby officially*
“Wow” ya fada afili Suna mai dadi *Zuby* haka yaita maimaita wa bata da wani kyau a fuska kuma bawani haske gareta ba amma dagani ta ‘kara daman da yake sa hasken fata, ‘kirjin ta cike yake da dukiyar Fulani tana da dirin jiki
♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
*Abuja*
Ba muyi wata dinner ba kasan cewar bamu dade da cin abincin ba shayi Momy tasa Suwaiba ta hado mana yaji ni’inal da kayan kamshi, mukai ta kurba kamar wasu larabawa 😂
Bayan mun gama kowa ya watse amma nikam sarkin tsoro d’akin Ummi nayi tana ‘ko’karin rufe kofar nai saurin turawa
Da mamaki tace min “sisi yadai”. “Anan zan kwana” na fad’a yayin da nike shigowa ciki, ta maida kofar ta rufe
♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Ahaka rayuwa ta cigaba a gidan Momy, tsaka nina da Jiddah babu jituwa zan iya cewa tun nazo gidan magana bai shiga tsakanin mu ba, kuma babu Wanda ya lura a gidan saboda tun asali kowa yasan bama wani shiri,
Yau kimanin kwana bakwai kenan da aurena da Sadeeq amma har yau ban sashi a cikin ido naba gashi su Khadija har sun koma makaranta
Muna falo nida Momy a zaune sai Suwaiba dake faman zirga zirga ta kai ta komo tana kokarin hada abincin rana kafin su Khadija su dawo,
“dauko min waya ta a bedroom dina” cikin sauri na mike domin Momy batasan simi simi
Bayan na dawo nace “Momy gashi nasamu wayan ma tana ringing”. “Kawo mugani waye ya kirani” ta amsa tana shafa screen d’in wayar sannan ta kara a kunne
“Wa Alaikumussalam”. shi ne abinda naji Momy tace kafin tace “lafiya lau”.
Ta kara da cewa “wallahi Sadeeq zan cimaka mutunci fiye da yadda kake zato kasan dai yanzu ba kamar da bane kanada nauyi a kanka amma kayi burus da mu dama gwada ka nayi naga hankalin ka, to maza maza kazo gobe inason magana da kai na fada maka idan kuwa ba haka ba zanyi mummunan saba maka”.
Cikin fushi Momy tace “bazan sau rare ka ba Sadeeq baka da abinda zaka fada min na yadda, kaima kasani domin bakada wani uzuri kayi abinda nace maka kawai”.
Tana gama fadar haka ta kashe wayar
Jim kad’an saiga wani kiran ya sake shigowa daga yadda naga Momy ta daga wayar na gane yaya Mubarak ne d’an yayan ta, na sanshi sosai ya nada mutunci da yana nan ne da zama amma yanzu yatafi India saboda ya karasa karatun sa a can, kallo na tayi kana tace
“bani ruwa mana mara sanyi nasha”. “To” nace na mike cikin natsuwa koda na dawo har ta kammala wayan
____Washe gari da misalin ‘karfe 11am na rana a lokacin Su Khadija suna makaranta, Momy ma ta fita ma’kota gidan wata ‘kawarta Hajiya Nafisa, amma tace ba zata dad’e ba, zaune nike ni kad’ai a falo kan kujera ina kallon TV
Ya Sadeeq ne ya shigo bakin sa d’auke da sallama koda yaga ni ce zaune a falon sai ya gimtse bai ‘karasa sallamar ba ya d’aure fuska kamar bai ta’ba dariya ba, ni ma nayi kamar ban ganshi ba, tsawa ya daka min “dan ubanki baki iya gaisuwa bane ko nan d’in gidan uban ki ne? Ko da yike shima ubanki’ tarbiyar bata ishe sa ba bare kuma kema ya baki”.+
Inajin zafin gorin da Sadeeq yake mini har cikin raina a lokuta da dama
ya cigaba da cewa “idan ba mummunar ‘kaddara ba mai zanyi dake kucaka ki kalle ki, ki kalle ni, kin tafka babban kuskure da kika yarda Daddy ya hada auren nan zan shayar dake madarar azaba gida na zai zame miki tamkar kabari ke koda suna na ki kaji an ambata sai gaban ki yayi mummunan fad’uwa saboda bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane, ki fara tunanin yadda zaki rubuta littafi mai suna *NIDA YAYA SADEEQ* saboda irin zaman da zakiyi a cikin gida na ya ciki ki rubuta”.
Duka wannan maganar da Sadeeq yayi kaina a ‘katsa wasu hawaye masu zafi suna gan garo mini, narasa mai nayi wa Sadeeq da har ya tsane ni haka? Ban ta’ ba tunanin tsanar da yake ce wa yayi mini ta kai har haka ba,
Ban tanka masa ba illa mi’kewa da nayi na nufi hanyar sama na fara taka steps kenan ya da katar dani ta hanyar fadin “na tsane ki Siddi’ka na tsane ki, kuma bazan taba sonki ba a duk sanda ki kaji nace ina sonki to kada ki ta’ba yadda dani saboda yaudarar ki zanyi ba gaskiya bane”. 😭
Hawaye masu ‘kuna suka cigaba da gangaro min a haka na ‘karasa haura steps din, Suwaiba da ke faman dafa abinci a kitchen taji duk abinda ya faru tsakani na da Sadeeq
‘Dakina na shiga na fad’a kan gado, hawaye mai zafi yana zuba daga ido na, ni da kaina ina jin tausayin kaina saboda a sani na da yaya Sadeeq bai ta’ba cewa zaiyi baiyi ba duk abinda yace zaiyi to sai ya aikata sa
A cikin kukan na d’aga hannaye na sama na ce “ya Allah ka bayyana mahaifiya ta a duk inda take a fadin duniyar nan, ya Allah kasa tana a raye saboda inaso na rayuwa tare da ita, ya Allah kada kabama wani bawan ka sa’ar cutar da ita”.
Mama. Na fad’a haka yayin da na d’aga kaina sama ina kalla, “bansan maye dalilin ki na cewa ko bayan babu ranki a daura wa ‘yarki aure da Sadeeq ba, nayi alkawarin ni Siddi’ka zan zauna da Sadeeq koda kuwa hakan na nufin zai zama ajali na ha’k’kin ki ne nayi miki biyayya a sanda kike a raye da kuma abinda kika bani umarnin sa koda bayan ranki, Mama ta ina sonki”. Na ‘kare maganar da wani irin kuka mai tsuma zuciya
Allah sarki Siddi’ka ni kaina ta bani tausayi ban san sanda na saki waya ta tafad’i a kasa ba saboda ido na ya cika da hawayen 😭 tausayin halin da take ciki da ‘kyar na samu na daidai ta kaina na d’auki waya ta na fita daga d’akin naja kofar na rufe
Momy ce zaune ita da Sadeeq a falon ‘kasa, sai zazzaga masifa takeyi “Sadeeq kabi duniya a hankali ko ta d’aga ka zata aje ka, Wallahi Sadeeq ina guje maka ranar da zakayi ladama amma kuma ladamar zata kasan ce da ita gwamma babu saboda ka makaro, ka kasa d’aukar kaddarar ka a yadda tazo maka”.
Shi dai Sadeeq jin Momy kawai ya keyi amma baiga wata ranar ladamar da zata zo mai ba kuma ma ladamar ba akan kowa ba sai akan Siddi’ka yaji takaicin kalaman Momy, saboda har cikin ransa ya ke jin kiyayyar Siddi’ka
tace “dama akan maganar makarantar Siddi’ka ne yasa nace kazo tunda kai ba kayi hankalin haka ba kasan dai an koma hutu, so nike ka kaita makarantar su Khadija saboda akwai koyar wa sosai kuma kaga tana da saurin d’aukar abu bazata sha wuya ba”.
Yana sosa ‘keyar sa yace “Momy gaskiya ni boarding school zan kaita acan katsina nama gama komai yanzu haka ranar lahadi zan kaita”.
Momy bataji dad’in abinda Sadeeq ya aikata ba tare da ya nemi shawar ta kona Daddy ba saboda haka tayi mai fad’a sosai kuma tace “bata yadda ya kai Siddi’ka boarding ba”.
da yake Sadeeq ya iya dad’in baki kamar d’an siya sa yasan kalaman da zai fad’a ayi saurin yarda dashi, nan take ya siye Momy da da-d’a-d’an kalamai har ta amince masa
A zahiri Sadeeq ‘karya ya keyi saboda bai yi mata register ba dama yana da burin yin hakan saboda bai son ya kaita jeka kadawo yasan su Momy zasu takura masa amma boarding sai idan anyi hutu tazo, ko babu komai zai samu sau’kin abun
Bugu da kari yana san ya shigo da batun auren sa da Zuby nan bada jimawa ba, saboda a halin yanzu soyayya mai ‘karfi ta shiga tsakanin su sun aminta da junan su har sunyi alkawarin aure duk da basu taba ganin juba ba yau Sadeeq zaije ganin ta saboda itama anan garin Abujan take, saboda hud’uwar da zaiyi da masoyiyar sa ne ‘karfin zuwan nasa Abujan domin yana matukar ‘kaunar Zuby kuma yana da muradin ganin ta.
Momy ce ta katse shurun da cewa “kuma aji nawa za a sata?”.
“Momy yadan ganta da yadda suka gwada ta kinsan yarinyar kwata kwata ba tada ‘kwa-‘kwalwa yanda kika san dusa haka kanta yake Allah dai yasa ko JS1 ne su d’auke ta”.
“Js1 fa kace Sadeeq! Ina laifin 2 idan 3 bai samu ba, to ban lamun ce ba ban yarda ba kayi duk yadda za kayi ta gama prmry
School fa, kai kan ka shaida ne akan makaranta da ta gama, kuma kada na ‘kara jin kace bata da ‘kwa-‘kwalwa zan sa’ba maka”.
“Uhm” dai Sadeeq yace wa momy
Daga haka ya mi’ke “Momy ni zan fita a kwai wani aiki da zanyi zuwa anjima zan dawo zan kwana biyu anan kafin na koma “.
♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾