NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 7
Www.bankinhausanovels.com.ng
To bayan fitar su Zuby gidan su Lubancy suka zarce dake wata unguwa amma unguwar ba ta masu kudi can bace, kuma ita Lubancy iyayan ta sun rasu tun tana yar karama, a gurin kawun ta take, kasance war sa namiji ba ko da yaushe yake gida ba shiya yasa Lubancy ta zama abar da ta zama yanzu duk da matar kawun na kokari amma sam Lubancy ta raina ta bata jin maganar ta, ganin Allah bai bata haihuwa ba kar ta cika matsawa ace dan bata son zafin yara bane shiyasa ma yanzu ta zuba mata idanu, in dai duniya ce wanda bai zo ba ma jiran shi take.
Duk da sun sami matar kawun a tsakar gida, haka su ka wuce ta ba tare da sunyi mata sallama ba, da shigar su dakin Lubancyn suka wuce suna wani shan kamshi.
A cikin zuciyar ta take musu adduar shiriya dan baza tayi musu mugun fata ba kuma Allah na gani tayi iya bakin kokarin ta dan ta san abin da suke aikata wa ba abin arziki bane, ta bar ma Allah saboda duk zagin da mutanen unguwa suke mata yana dawo wa kunne ta a cewar su “dan ba yarinyar ta bace shiyasa ta barta tana yin abin da ta ga dama”. Amma ita ta san d’a a wannan zamanin ko kai ka haife shi sai kayi hakuri da shi.
* * * * * * * * *
To bayan sallar isha’i ne Daddy ya ce wa Momy “ta je ta kira masa yaran gidan zai yi magana dasu”. Ba tare da tayi musu ba ta ce mai “to”.
Falo ta fito in da ta kwalama Suwaiba mai aiki kira, nan take suwaiba ta zo tace “na’am”. Momy tace “haura sama ki kira min yaran nan, ki tabbatar kin fada ma ko wacce su”.
“To Hajiya”.
Suwaiba ta fada kana ta haura sama
Dakin Khadija ta fara zuwa in da ta shiga buka kofa ba ta wani bata lokaci ba Khadijan ta zo ta bude kofar ganin Suwaiba tsaye tace “Suwaiba lafiya?”.
Suwaiba tace “lafiya lau Hajiya ce tace “tana son ganin ku”.
To kice “gamu nan”.
Da “to”. Suwaiba ta amsa
sai da tabi duka d’akunan yan matan ta sanar musu, sannan ta sauko kasa inda ta tarar da Momyn inda ta bar ta take ta shaida mata gasu nan zuwa kana ta koma bakin aikin ta.
Ku san a tare Siddeeqah da Khadeeja suka sauko dan sun ruga kowa fito wa a lokacin falon babu kowa sai TV da yake a kunne yana karatun Al’qur’ani mai girma
Kusan tare suka zauna kan kujera kowa da abinda yake sakawa cikin ran sa, can dai Khadija tace “sister yau ba magana ne?”.
Ita Siddeeqah ba rufi ne da ita ba saboda haka ta mayar wa da Khadija amsar ta da cewa “yo gani nayi kina wani share ni nayi tunanin kina shigar ma Jiddah ne shiyasa ki ka ga ban kula ki ba, saboda na yarda na bata da kowa a gidan nan in dai akan kwatar yanci na ne”.
Bata karasa maganar ba Jidda ta sauko ganin Siddeeqah a zaune yasa ta ja dogon tsaki ta ce “sis Khadee me yisa ki ka zauna tare da wannan abar”.
Khadija tace “wa fa?”.
Nuna ni tayi da yatsa ba tare da ta jiwo ta kalle ni ba,
ganin haka yasa na mike cikin masifa na kama hannun nasa abaki na ganna mata cizo kana na koma gurin zama na kamar ba ni nayi ba.
ai kuwa ta shiga yin kuru-ruwa wanda yai sanadin fitowar su Daddy, Ummi ma da take sama ta ji ihun cikin sauri ta sauko har ta kusan tayi tun tube saboda ko gaban ta bata kalla ba.
Kafin su Daddy su ce wani abu yah Sadeeq ya shigo bakin sa dauke da sallama amma saboda ihun da Jiddah take yi babu wanda yaji sallamar.
Da ma-maki dauke a fuskar Sadeeq ya kara so cikin falon ya ma rasa wa zai tambaya abin da ya faru saboda haka ya jingina da bango ya harde hannayen sa waje guda
* * * * * * * * *
Bayan shigar su Zuby dakin Lubancy ta maida kofar dakin ta rufe da mukulli, kusan zan iya cewa Lubancy bata gajiya da da romance saboda haka ta shiga shafa jikin Zuby take ita ma tsigar jikin ta ya fara tashi nan take suka shiga cire ma juna kaya bayan sun gama suka fada kan katifar Lubancy suna nishi sama sama take suka fara tso-tse tso-tsan juna suna fada ma juna kalamai masu dad’i.
Wa iya zu billah Allah ka shirya mu kashir ya zuri’ar musulmai baki daya
* * * * * * * * * *
Sam sadeeq bai son hayaniya ganin Jiddah bata da niyar yin shiru ya daka mata tsawa, nan take tayi tsit kamar ruwa ya ci ta sai shash-sheka da take yi a kai a kai, sai a lokacin Daddy ya nemu guri ya zauna kana Momy ta zauna ita ma.
Da hannu Daddy ya nuna ma Sadeeq din Kujera alamar ya zauna babu musu ya zauna, an dauki kusan mintuna hudu babu wanda yai magana can dai Daddy yai gyaran murya yace ma Jiddah “ke! Tashi ki zauna”.
Saboda a lokacin Jiddah a duke take kan ta a kasa tana sash-shekarar kuka.
Ita ma babu musu ta nemi kan Kujera ta zauna kusa da Ummi sai murza idanuwa take yi.
Bayan ta zauna Daddy yace kafin na fara cewa komai “ku tashi muje muyi dinner”.
Gunin sha’awa zaune suke reras a kan dinning din ba ka jin sautin kowa sai karan cokula saboda Momy ce tayi girkin abincin ba karamin Daddy yayi ba jalof din taliya ce da kuma farfesun kaza ga farfesun kifi ga kuskus haka ban garen drink ta hada jus kala-kala dan Momy ba baya ba wajen iya abin ci.
Ina cikin ci Inna ta fado min a rai saboda haka na ijiye cokalin nayi tagumi kwalla na zubo min, Daddy ne ya lura da halin da nike ciki yace “A a mai gaskiya mai kuma aka miki?”.
Cikin kuka nace “Daddy Inna na tuna tun nazo banyi magana da ita ba”.
Yace “ai ba kuka zaki ba ko Sadeeq ki ka ce ma kina son magana da ita zai kira miki it maza dai na kuka bari mu kammala cin abinci sai a kira miki ita ko”.
Ya karasa maganar cikin sigar lallashi nace “to Daddy
Cigaba da cin abincin nayi ina jin dadi har cikin raina yau zanyi waya da inna, saboda zumudi ban wani koshi ba na mike daga kan dinning din+
Momy tace min “ina zuwa?”.
Naba ta amsa da “na koshi ne”.
Bayan na wanko hannu na falo nazo na zauna ina sake sake a raina
can shima yaya Sadeeq ya zo ya zauna, na kalle shi muka hada ido ya banka min harara nima na rama.
Yace “ke da ni ki ke?”.
Nace “nima dani kake?”.
Ganin ya taso nasan bugu na zaiyi na mike da gudu na nufi dinning ina kiran sunan Momy, ban kai ga karasa wa ba nayi kicibus da ita, da alamar ta tsorata da yadda nike kwala mata kira tace “ke lafiyan ki?”. Murya ta na rawa nike nuna mata Sadeeq da saura kiris ya damko ni Allah ya kawo ta.
Sai a lokacin ta lura a tsaye yake sai mazurai yake na rashin gaskiya.
Momy tace “Sadeeq Sadeeq wai sai yaushe zaka girma? To idan ka dake ta me zaka ji?”.
Yace “Allah Momy rashin…”.
Cikin sauri Momy ta katse sa da fadin “ban tambayeka ba Sadeeq ba tun yau ba nasan halin ka idan aka bibiya kai ne ka fara”.
Daddy ne ya zo gurin da muke yace “kai dai Sadeeq anyi katon banza abin kunya ka tsaya kana biye ma karamar yarinya sai kayi ai tunda kaima irin ta ne baka da hankali, ku wuce mu koma falo”.
Ya fad’a yana nuna mana hanya Momy ce ta fara yin gaba Daddy yabi bayan ta, ganin da gani sai yaya na kalle sa karaf muka hada ido ya galla min hara ra madadin na rama sai na kwashe da dariya ina yi mai gwalo nace “anji kunya giwa tana fada da shawo inba ga tsoro ba…”.
Ban karasa maganar ba ya damko ni ya toshe min baki ya tsats-tsare ni da idanu yace “ke dan uban ki yaushe zaki hankali dan kinga su Daddy na shigar miki shine zaki min rashin kunya dama na dade ina neman wannan damar gashi yanzu na samu zan ragar gaji bakin yarin ya”.
Tuni ido na ya raina fata gashi ya toshe min baki bare na basa hakuri
Ana haka sai ga Daddy ya zo wuce wa ganin Sadeeq matse da baki na yasa shi ma-maki dan takai ci bai ce masa komai ba illa da yace “bani guri na wuce”.
Kunya ce ta kama Sadeeq yana sosa keya ya sake ni kana ya matsa a hanya Daddy ya wuce ni kuwa ina ganin Daddy ya wuce na falla da gudu ina haki kamar wacce tayi gudun fan fa laki
Momy tace “keda wa kuma? A ina ki ka tsaya bayan mun taho?”.
Sai da na zauna akan kujerar da ke kallon ta nace “kedai Momy ki bari kawai kuna wuto wa ya damko ni ya shake min yuwa tare da toshe min baki, yanzu haka bacin Allah ya kawo Daddy da kashi na ya bushe”.
Momy tace “Sadeeq din?”.
Nace “kwarai kuwa”.
Zatayi magana kenan ya shigo yana dan so sa keya tace “ka kyauta ka nuna bamu isa da kai ba”.
Zai yi magana tace “za kai shuru ko sai na saba maka”.
Bai kuma magana ba ya nai mi guri ya zauna,
bai jima da zama ba sai ga Khadija da Ummi nan bayan wasu yan daki ku Daddy ya dawo hannun sa rike da na Umar can sai ga jidda nan ita ma fuskar nan tata a kwabe kollo daya nayi mata na kawar da kaina saboda dariya na so ta kama ni zokai zokai tazo ta zauna a kan kujera.
* * * * * * * * * *
Aban garen zuby kuwa bayan sun gama sheke ayar su, wanka suka kuma yi a gur guje kana suka fito kasan cewar a kwai taron da suke zuwa duk karshen mako, toro ne da manyan mata yan madugo suke sheke ayar su,
sun shirya tsaf cikin wata doguwar riga yar kanti daga kasan ta a yanke yake haka saman ta shara shara yake kuma hannun bes ne da ita yanayin rigar iri daya ce suka sa, sai dai kowa da kalar tasa,
Wani katon hijabi suka maka akan yar iskar shigan nan tasu dan ko undies basu saka ba kuma dama idan zasu taron ba a saka undies kashe wayoyin su suka yi kana suka daura nikab suka fito lubancy ta rufe kofar ta, alokacin tsakar gidan ba kowa
Sadaf Sadaf suka fice daga gidan dama kafin nan sunyi waya da drivern da yake kaisu duk karshen mako
Sun kuma ci sa’a suna fito wa yana karasowa ba su wani tsaya bata lokaci ba suka hau yaja su,
Bayan doguwar tafiyar da sukayi yayi fakin a dai dai get din wani gida mai girman gaske suka fito yaja motar sa yayi gaba saboda ya saba yana kawo su kuma duk karshen wata suna biyan sa kudin sa dan haka suka tsara dashi,
duk da bai san me suke aikata wa ba amma yana kyauta ta zaton ba alkairi bane,
Saboda tsaro ko mai gadi ma mace ce tsohuwar soja saboda basa son harka da maza sam
Bayan sun kwan kwasa an buda musu suka shiga gida ne mai girman gaske an kawata sa da ado irin na zamani sai da suka wuce gat biyu sannan suka samu inda ake toron mata ne a zaz zaune sun kai su tala tin ko wacce ka gani ba shigar ar zi a tare da ita,
Basu karasa inda matan suke ba sai da suka cire nikab da hijabin, suka tura cikin jaga dama ta kalmi mai tsini zuby ta saka take ta shiga tafiya tana gir giza ba bu abinda bai motsawa a jikin ta, gaba daya hankulan matan ya dawo kan ta a ka shiga tafa mata ana kiran sunan ta ana wasa ta kana ta sami kujera ta zauna lubancy tabiyo bayan ta
Sai da aka fara gabar da abinci suka ci suka sha tare da kayan marmari iri iri da madara bayan sun gama babbar cikin su mai suna Hajiya Turai ta tashi tana kwar kwasa shigar jikin ta bata da maraba da tsira ra Sai faman yauki take kamar kal kashi bata da tsayi kuma tana da dan jiki taci uban bilicin kan wani dakali ta hau tace “madugo”. suka ce “mu ne”. “madudo”.
“Mu ne!”.+
Ta cigaba da cewa “ba tare da bata lokaci ba kamar yadda muka saba ako wani mako yau ma hakan take a matsayi na na shugabar wannan kungiya ina mai kara farin cikin sanar daku yau ma akwai shagali dan mun yi sabon kamu”.
Raf Raf Raf suka dunga tafa mata ana ihu
Haka dai masu mukami a cikin kungiyar su kai ta futowa cikin shigar da bata da maraba da tsirara suna bayani kana su koma su zau na
A karshe dai ko wa ya tashi suka yi layi kana wata Hajiya turai tace “bari naje na kira manyan matan su zo su zabe ku dare na yi
ta wata hanya ta bi bata jima ba sai gata da wasu mata datti jawa da ganin su matan manya ne dan fatar su luwai luwai sai sheki take yi suma ba wata suturar arziki suka sa ba, bayan sun iso, Hajiya turai ta ce “to kun dai gansu nan gogag-gu ne a harkar ba abin da basu iya ba ku koma gefe zan dunga kiran su daya bayan daya duk wacce taga wacce tayi mata sai tayi magana amma baza ku zaba su wuce biyar ba”.
Take gurin ya kaure da ihu aka hau tafi Raf Raf Raf
* * * * * * * * * *
Daddy yai gyaran murya yace “Alhamdu lillah ina mai kara jad-dada godiya ta ga Allah ma daukakin sarki daya a ramin lokaci domin na kara tuna tar daku dan gane da wasu abububuwa da na lura suna faruwa a gidan nan,
Ya kalli Momy yace “ko kina da abin fada?”.
Tace “bani da shi”.
Yace “to madallah
yace to kai Sadeeq “Momyn ku tazo min da batun wai ka sama ma Matar ka makarantar kwana haka a kayi?”.
Ya karasa maganar yana kallon Sadeeq
Kamar da gaske Sadeeq yace “wallahi Daddy saboda na temaka mata ne, nayi tunani naga idan anan ne ba lallai ta maida hankali tayi karatun kirki ba amma acan idan bata ganin idan wanda ta sani sai ta fi maida hankali”.
Cikin gamsuwa da maganar Sadeeq Daddy yace “idan hakane kayi abu mai kyau, yaushe ne, zaka kai ta?”.
Yace “gobe ne daddy dan na gama shirya mata komai”.
“Ka kyauta Allah yayi albarka haka ake so”.
“Ameen ameen Daddy”.
Sadeeq ya ce
In banda faduwa ba abin da gabana yake yi sai na rasa me ke min dadi yanzu gobe wannan mugun zai raba ni da farin ciki na sosai nike jin kuna a raina nayi narai narai da ido ban san sanda kalla ta fara zubo min ba
Momy ta kalle ni tace “kiyakuri ki daina kuka ki kaddara tun kafin Allah ya halicce ki ya tsara miki yadda rayuwar ki zata kasan ce, ba kuka zaki ba gode ma Allah zaki da ki ka samu masu tsaya miki akan karatun ki dan wallahi wasu irin wannan damar suke so amma basu samu ba insha Allah zaki ga amfani karatun nan gaba”.
Naji dadin nasihar da Momy tai min saboda a rayuwa ta ina son nasiha kuma ina dauka sosai hawaye na na share nace “to Momy insha Allah zan jure”.
Daddy ya cigaba da cewa “na dawo kan ku, ke Jiddah”.
Ta dago kai ta kalle sa yace “da ke kuma Siddeeqah”.
bana son tone tone ba tun yau ba ina lura daku a cikin gidan nan bakwa ga maci ji idan nayi magana wa Momyn ku magana sai tace min ba haka ba, amma yan abu buwan da suka dunga faruwa a yan kwana kin nan yasa naji ba bu Daddy kuna yan kana nun ku daku kun iya fada har haka, a gaban mu kenan fa muna da rai, to idan kasa ta lullube fuskar mu ya kenan? Ku saura ra da kyau ku jini bana son na kara ganin irin haka a gidan nan ko naji labari zanyi mummunan saba muku kun ji ni?”.
Yai maganar yana kallon mu
Amma sai mukai shiru bamuyi magana ba
yace “ku tashi ku yafi junan ku kuyi ma junan ku sallama saboda Allah ya la’anci mai tada fitina”.
Yi mukai kamar ba muji abin da yace mana ba
yaya sadeeq da mun gama kai shi ban go ya taso da zafin sa zai dake mu Daddy yai saurin hana shi
Yace “ka bisu a hankali yara ne nasiha zaka musu yanzu sai suga muna takura musu ne”.
Ba dan ran Sadeeq yaso ba ya koma ya zauna
Nasiha daddy ya fara yi mana mai ratsa zuciya yana kara tunatar damu duniyar nan ba komai bace kuma duk mai yanke zumunta ba zai shiga Aljanna ba haka dai yai ta tuna tar damu! jiki na yayi sanyi matuka na gamsu da duk abunda ya fad’a saboda haka na mika ma Jiddah hannu babu yabo ba fallasa ta miko min mukayi musabaha
So sai Daddy yaji dadi dan ya nuna farin cikin sa yai ta samana Albarka
Khadija na zun buro baki tace “wai ni da Umar me mukayi? Daddy baka sa mana Albarka ba”.
Murmushi Daddy yai irin nasu na manya kana yace “ai ban ware ba Khadeeja Allah yai muku albarka gabaki dayan ku”.
Khadija na Dariya tace “amin Daddy”.
Fira muka shiga ta ba wa ina basu labarin kauye ana kwasar dariya can dana tuna banyi waya da inna ba nace “yaya”.
Bai dago ya kalle ni ba dan hankalin sa akan waya yake
Momy tace “baka ji ana magana ba?”.
Sai alokacin ya dago kai yace “lah wallahi Momy banji ba me tace”.
Tace “yo kace bakaji ba taya kasan ita tayi magana? Allah ya shirya ka Sadeeq”.
Siddeeqah tace “dama Momy so nike ya kira min Inna”.
Yace “Inna tayi bacci yanzu ki bari sai gobe idan Allah ya kaimu kan ki tafi zan kira miki ita ki mata sallama”.
Murya ta a dakile nace “to”.
Yace “Momy na manta ban fada muku ba nima gobe zan koma kaduna ana nema na a office din mu”.