NOOR ALBI CHAPTER 11 BY MAMUGEE

Kamar yanda Haj Anne ta sanar Masa da bayanin komai da Kawu saidu yayi Mata shiru yayi Yana sake juya zancen Dan kuwa Babu wani sauran abinda zai iya fada ayanzu tunda Anne tariga ta karba Auren Amma Kuma duk da hakan zai karba auren ne Dan taqaita maganar,
Zai karba auren Amma badan ya karbeta a matsayin Mataba,
Zai karba auren Dan inganta rayuwarta ta hanyar Bata ilimi Mai kyau da tsadarda zai iya bawa ‘yayan cikinsa da yanada,
Kar karbeta ne tamkar ‘yar riqo har zuwa lokacinda Allah zai bawa Amininsa nasa lafiya saiya sawwaqe Mata ayi Mata auren daya kamaceta,
Wannan shine abinda ya yankewa kansa da maganar auren
Dan kuwa bayajin har abada zai iya kallon ‘yar da Mahmoud da Zainab suka Haifa Amatsayin matarsa,
Macen da zai iya muamala ta daban da ita bayan ta uba da ‘ya.

Da wannan ya rufe maganar aka fara Shirin auren Wanda Babu Bata lokaci aka Sanya sati Mai zagayo ranar juma’a.

Wasu irin kudin gaske Aka aikowa Momy da Kawu saidu na hidimar Wanda yakusa haukata kawunan dangin momyn suka so cinye kudin
Dayake Kawu saidu shima idanuwansa a bude suke yace Babu wannan maganar shima Dole a fitarda na dangin uba abasa idan bahakaba zai fasa bada auren.

Wani irin murmushin bakada lafiya su Haj Karima sukai Masa
Alhaji Atiku kuwa Jin abinda Kawun Yafada yasashi kallonsa da kyau da hasaso irin dukan mutuwar dazasu saka Yan dabansu na shiyasa suyi Masa idan har ya kwatanta abinda Yafada din,
Umma Jamila kuwa cikin ranta fatar saukar masifar datafi ta Dan uwansa Mahmoud tai Masa.

Momy da har lokacin zuciyarta najin wani iri a al’amarin kallonsu tayi jiki a Dan mace ta rokesu akan subawa kawun haqqinsa na matsayin uba ko Dan asamu albarka a wannan auren.

Haka suka bawa Kawun saidu kudin dabai taba riqe irinsuba arayuwarsa hakama takamaimai baisan me zaiyi dasuba kawai dai yafison ya karba din Dan kuwa yagama ganin zallar kwadayin abun duniya da son zuciya a al’amarin dangin Zainab din.
(WAINDA SUKE RUDEWA DA SUNAN ZAINAB DANAKE FADA SHINE DA MOMY DA MAHAIFIYAR LAYLAH DA LAYLAH DUK SUNANSU ZAINAB,ITA LAYLAH SUNAN MAHAIFIYARTA AKA SANYA MATA BAYAN RASUWAR MAHAIFIYAR).

Sabuwar rayuwa Kawu ya bude a garin Dan kuwa tuni yasaka Abdullahi agaba akayo Masa manyan dinkunan bikin tareda huluna masu tsada da takarma harma dasu turaruka Kawun ya siya,
Dayake baida rowa har Abdullahi yabawa nasa kason kudi masu ‘yar tsoka wanda yasa Jikin abdullahi din yakuma sanyi da al’amarin yaji bazai iya boyewaba Dan Haka Ana saura kwana biyu daurin auren da daddare ya nufi gidan umma Jamila Dan ganin Sa’adah wadda ita kadai yasan zata fahimcesa sbd kaf kowa dukiyar tagama rufe idonsa
Shikuma yakasa danne al’amarin sbd sanin Auren Laylah da Turaki Kamar wani boyayyan burine Kuma Alqawarin Abba Wanda duk ranarda ya tashi yaga wannan sauyin bazaiji dadiba duk da itama Sa’adah din ‘yarsa ce Amma kamar sbd mahaifiyar Laylah yakeson Lallai laylance zata aura Turaki.

Babbar Sa’ar dayaci a zuwa gidan umma Jamila Bata Nan suna gurin hidimar bikin da aketayi duk da Turakin yasanar da cewan basason Ayada Dan kada Yan Media suji Amma zancen ya Dan firfita sbd sukam su Alhaji Qarami sunason asan Wanda suka bawa auren yarsu,sunason duniya tasan sun hada alaqa da ABUTURAB TURAKI Ko Dan matsayinsu da girmansu yaqaru a idon jama’a.

Lokacinda Anty Sa’adah taga Abdullahin ne Mai neman ta gabanta Saida yayi mummunan faduwa
Take jikinta yayi Sanyi sbd tasan tabbas kodai abbansu kokuma Laylah akwai Wanda wani Abu yasama.

Shigowa tayi dashi palon baqin gidan suka zauna takawo Masa ruwa tana kallonsa jiki mace muryarta na bayyanarda damuwarta tace”

Yaya Abdullahi Allah yasa lfy dai Dan nikam ganinka yasa jikina mutuwa.

Ruwan data kawo Masa ya Dan Sha Yana dauke idanuwansa daga kallonta ganin irin yanda ta sauya sbd zallar gyara da ake mata tayi haske sosai tayi fresh duk da ta rame Amma duk da hakan a idanuwansa ko ahakan batakai Laylah kyawu da haske ba.

Aje ruwan yayi tareda Dan kallonta kadan cikin nutsuwa yace”

Abba dai yananan yanda take hakama Laylah tananan da dama itama saidai Kam duk tayi wani iri sbd kadaici da rashinki ahakan ma dai aikin gidan yadawo kanta,
Saidai ba wannan ne yakawoniba.

Kallonsa Anty Sa’adah din tayi batareda ta iya cewa komaiba tana sauraron abunda zai fada.

Ya fuskanceta dakyau Yana tattaro nutsuwa yace”

Maganar auren Nan ne da za’a daura jibi nazo nafada Miki sbd naso daurewa nayi shiru nakasa hakan sbd Abba da Laylah dama ke din.

Ahankali ya zayyano Mata burin Abba  da babban qudurin nasa na Bawa Turaki auren Laylah tareda sanar da ita asalin abindaya faru ranarda ciwon na Abban ya rikice sbd shima Kamar yanda Momy taji komai yaji komai ganin momyn zata juyo tabar gurin yasashi barin gurin tun kafin tagansa ya fice daga gidan
Dan Haka ya Dora da cewa”

Sa’adah ke kadaice gatan Laylah ayanzu tunda Babu Wanda take nuna yasanda ita bare damuwa da rayuwarta,
Kece gatanta ayanzu da Abban yake kwance,
Kece uwa Kuma uba gareta hakama ‘yar uwa,
Idan kikayi auren Nan Kika tafi Amatsayin Laylah da wace daraja Turakin da Mahaifiyarsa zasu kalleki?
Hakama Abban duk ranarda ya tashi da wace darajar zai kalleki da Momy,
Hakama babban abindayake faruwa shine Turaki yasa ahada takardu da komai na lafiyar Abban za’a daukesa daga Nan zuwa wata qasar Kuma ansanar da Momy ta aminta da atafi dashi din Dan Haka bayan aurenki bana tunanin Laylah tanada wani sauran abinda yarage anan bayan kunci.
Nidai abindayasa nazo nafada Miki gaskiyar lamarin sbd kome Zakiyi karki manta da ‘yar uwarki Dan Allah,
Kamar yanda Kika dauko tallafar rayuwar marainiyar Allah kici gaba da tallafa Mata Dan Allah karki Bari ta  Shiga wani mummanan halin dayafi Wanda take ciki sbd nidai da antafi da Abba zuwana gidan nasan yaqare tunda dama dawainiyar Abban ke kaini…..

Dogon numfashin data saukene yasashi dakatawa Yana sauke nasa numfashin shima kafin ya kalleta ganin yanayinta ya sanyashi miqewa Yana kallon Agogo
Gwara ya tafi kafin umma Jamila tadawo ta taddasa gidan
Hardai idan tasan abin daya kawosa da Babu shakka saita Ari hauka ta Masa mummunan wulaqanci.

Bayan tafiyar Abdullahi Sa’adah na shiga gida tafara hada kayanta Dan kuwa ta yanke shawarar komawa gida ayau din,
Gwara Takoma gida kawai aqarasa komaima acan.

Koda umma Jamila tadawo agajiye take shiyasa Koda Sa’adah din Tai maganar komawa gida Bata kawo komai arantaba tasa driver yakaita Dan dama gobe za’a maida Sa’adahn gida sbd gobe su Haj Anne zasu iso
Dan Haka Kai tsaye tasa aka maida Sa’adahn gida da maraicen ta bugawa Mai hajiyar dasuka dauko ta musamman Dan gyaran Amarya waya cewa subi Sa’adah din can gida aqarasa acan na yau da goben.

Ko data iso gidan tsit kamar ba hidimar biki akeba Momy na Palo da baqi suna magana tashigo a natse fuskarta daukeda murmushi taqaraso gabansu cikin girmamawa ta gaidasu tana kallon Momy datake kallonta tana yaba kyawun datayi tace”

Momy kinata kallona
Na sauya Miki ne?

Murmushi momyn tayi tana cewa”

Dan sauyi kin sauya Kam kamar ba Sa’adah ba
Wannan hajiya Sa’adah shuwa Arab ce.

Dariya baqin momyn sukayi suna yaba gyaran na Sa’adah dake bayyane afili Dayar tace”

Momy ko Zaki bani numbern me gyaran Nan sbd auren sanah da zaizo qarshen watan Nan Dan Naga ta iya gyaran amare Kam gashi Sa’adah sai wani irin qamshi takeyi Mai Dadi.

*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902_* itace Mai wannan aikin na gyaran Amare tareda kayan qamshinda ko a anguwa za’a San ankawo Amarya,
Turarukanta na musamman ne Dan kuwa daga Chad suke zuwa ga kayan Mata na gyara masu kyau da inganci
08067558902.

Kai tsaye daki Sa’adah ta wuce inda ta tararda Laylah a dakinta zaune tana ninke kayan wanki datai na tarin tsoffin kayan Sa’adah da aka Bata akace gashinan ta ringa sakawa can gidan idan Sa’adah din taje da ita Dan karta ringa saka tsoffin kayanta dasuka Gama kodewa.

Tana ganin Sa’adah taji wani irin sanyin farin ciki harsaida fuskarta ta bayyanarda hakan
Fararen idanuwanta akan Sa’adah din tabude baki tace”

Anty Sa’adah kindawo tun yau ne?

Qarasowa Sa’adah tayi gabanta fuskarta daukeda murmushi tana kallon kayan da Laylah din ke linkewa tace”

Meyasa zakiyi wankin kayana tunda banananma ba sakawa nayi ba.

Kallon kayan tayi tana qarasa Nade rigar Dake hannunta tace”

Jiya Umma Jamila datazo suka bani itada Momy sunce Dani zakije na ringa sakawa acan.

Shiru tayi tareda sauke Kai tana jiran abinda anty Sa’adah din zatace ko tana buqatarsa kayan nata.

Shiru anty Sa’adah tayi cikin Dan takaicin yanda idanuwansu umma Jamila ke rufewa Akan komai,
Koda zata tafi da ita amatsyinta na wadda zata aura Mai Hali yakamata ace andinka Mata ko kala biyu ne na tufafi Amma shine za’a Bata tsofin Kayan da ita takashe taje dasu.

Wani murmushin takaici da baqin cikine ya kufce Mata,
Ita yanzu sun kore Mai aurenta da qarfi da yaji sbd zasuyi auren yaudara da ita
Gashi yanzu zata tashi a Babu tunda biyu Babu takamata.

Kallon Laylah tayi tace”

Aje kayan bazaki dasuba za’a Baki wainda Zaki ringa sakawa idan munje.

Ba musu ta ajiye kayan tareda dagowa ta zubawa Anty Sa’adah din idanuwa tana kallon sauyawar datai tareda tayata farin cikin auren dazatai din Babu babban farin cikinta irin tafiya da ita dazatayi Dan kuwa ita kanta da kanta tasan kanta yakusa qarasa juyewa sbd wasu abubuwan datakeyi wani lokacin.

Akwai gyaran yamma da ake Mata Dan Haka Koda masu gyaran sukazo Laylah tasaka suyiwa tace”

Kuyiwa qanwata gatanan itama da Dan sauya tunda da ita zani.

Momy dai batace komaiba ta qyale akaiwa laylahn sbd lallaba Sa’adah dasukeyi asamu ayi auren tukuna.

Fes Akaiwa Laylah wata irin dilka da wankan lalle tareda wasu gyaran da fatarta ta amsa atake sbd tanada Hasken fata sosai hakama tafi Sa’adah fata Mai taushi sosai shiyasa gyaran atake yaringa shiga jikinta tayi Dan Shar da ita
Abdullahi daya shigo yayi Ido hudu da Laylan tsinkewa yawunsa yayi Yana dauke Kai zuciyarsa na basa qwarin gwiwa da tabbacin Ana Gama bikin Sa’adah zai bayyanarda kansa a manemin auren Laylah din yasan Kuma zasu basa tunda neman Kai su umma Jamila keyi da ita kokuma ya lallaba Kawu saidu kafin yakoma yabasa aurenta basaima Sa’adah ta tafi da ita dinba Dan zata iya fin qarfinsa idan taje daular gidan Turaki ta samu sauyin rayuwa.

Da daddare duk maganin da aketa faman dirkawa Sa’adah Haka ta tattarosu ta bawa Laylah tasata ta shanye a sunan maganin rashin lafiyartane ba musu laylan ta shanye.

Washe gari da safe bayan angama gyaransu masu gyaran sun tafi umma Jamila tareda Haj Karima suka iso gidan da wasu irin Kaya na Alfarma da aka dinkowa Sa’adah din wasu manyan lace ne dasuka Sha maqudan kudi tareda gyalensa da takarmi aka Bata ta shirya tafito fes a Amarya sai qamshi take zubawa.

Kallon Laylah dake zaune gefe tana kallonta tayi tasaki murmushi jikinta amace tanajin inama aurentane na gaskia da Amana za’ai
Datayi farin ciki sbd ita kanta tanason tayi auren Dan ta tallafa rayuwar Laylah din Amma wannan aurene da ake Shirin ginawa Kan yaudara.

Fitowa tayi riqeda hannun Laylah Dake sanyeda doguwar rigar jallabiya sabuwa Navy blue da Sa’adah din tabata tasaka
Kanta nade cikin gyalen Abayar
Idanuwanta ki kwalli babu
Babu komai akan fuskarta sai asalin zallan kyawunta da Allah yabata duk da Babu wata walwala ko sakewa a fuskar tata Wanda Kuma hakan dabiarta ne tunda ahaka ta taso ba walwalar.

Kallonsu Haj Karima tayi kafin ta tsayarda kallonta Kan Laylah Dake rabe bayan Sa’adah din
Ta bude Baki zatai magana
Umma Jamila ta tareta da cewa”

Karma kiyi wahalar magana barta taje da ita din dan taurin Kan Sa’adah Ni har tsoro yakeban yanda kikasan kafiran farko Haka take da taurin tsiya akan wannan Mai Kama da ‘yar tsanar.

Shiru Haj Karima tayi tareda dauke Kai daga kallon inda suke din ta kalli Momy dake zaune tana kallon su Sa’adah din itama tace”

Gatanan gurin gaida uwar mijinta dasuka iso yau za’a kaita.

Umma Jamila ce ta karba zancen da cewa”

Ga abinci dasu komai can a mota duk ansaka.

Miqewa Haj Karima tayi dayake ita zata kaita suka fito bayan umma Jamila tasake bin jikin Sa’adah din da turarukan (AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902) masu qamshi.

Suna fitowa suka shiga babbar CR-V din Haj Karima driver yajasu zuwa masaukin Anne wadda ta iso aranar tareda jamaarta su biyu.

Wani babban makeken guest house din Turaki dake garin suka dosa
Tun a gate Sa’adah ke kallon koina zuciyarta a sanyaye har aka abarsu suka qarasa harabar gidan sukai parking suka fito.

Kallon Laylah da kanta ke sunkeye cikin sanyi Haj Karima tayi Kai tsaye tana cewa”

Kwaso kayan abincin,
Ki dauko da kyau karki barar kosu hargitse.

To” tace anatse tareda daukan kayan abincin tanabinsu abaya.

Wani babban palon dayake a tsare da komai na irin Rayuwar turawa akai musu iso suka zauna Kan milk and golden Royal set dake palon
Banda Laylah data tsaya da kayan abincin tana jiran afada Mata inda zata aje
Kafin suyi wata magana qamshin turaren Haj Anne yafara iso musu kafin ta fito cikin doguwar jallabiyar kuwait baqa Mai Fadi sosai kanta yane da mayafi Mai Dan girma sosai Wanda yasaka Hasken fatar datake dashi fitowa sosai duk da tsufa da manyanci Amma komai nata a natse yake,
Fuska dauke da Dan murmushi take qarasowa tana kallonsu ta iso ta zauna Kan 2 seater tana amsa gaisuwarsu a mutunce musamman Sa’adah wadda ke zaune gefn Haj Karima din…. Sauka Idanuwanta sukai Kan Laylah Dake tsaye har lokacin daukeda kayan abincin…

Dukkanin hankalinta da idanuwanta zubawa Laylah su tayi sbd ba shakka fuskar Zainab take gani akan fuskar yarinyar,
Babu abinda tabaro na zainab face yanayin jikinsu daya banbanta ita sirirya zainab Kuma ba siririya bace Amma kamanninta da mahaifiyar sunyi nauyi sosai take taji qaunar datakewa Zainab din kafin rasuwarta tadawo Mata sabuwa fil akan Laylah
da mamaki Kan fuskarta Tace”

wannan ‘yar Zainab ce basai nayi tambayaba.

Haj Karima wani juyi tayi tareda Yi kamar batajiba tasake dasa sabuwar gaisuwa da barka da hanya kafin tacewa masu aiki dasuke kawo musu kayan tarba su karba abincin.

Suna karba ta kalli Laylah zatai mgn Anty Sa’adah tariga cikin nutsuwa da cewa”

Laylah kixo ki gaida Mutane.

Sabone data taso cikinsa na idan ba umartarta akai da Abu ba Bata Yi sbd kaucewa laifi da matsala shiyasa Bata qaraso ta gaida Anne ba Saida Sa’adah din tayi magana
Ta qaraso ahankali cikin natsuwa batareda ta kalli Annen ba ta gaidata da muryarta Dake yankewa.

Kasa rike mamakinta Anne Tayi takai tattausan hannuwanta ta kamo hannuwan Laylah cikin tsananin kulawa tace”

Wannan ‘yar Zainab ce ko?

Eh itace” Sa’adah tafada kanta a qasa
Haj Karima kuwa kasa hakuri tayi ta miqe tana cewa”

Bari muje mukai wani sakon sainmu dawo mu dauki Sa’adah din daga baya Idan tagama gaidaki.

Cikin kulawa Anne tace”

Ba damuwa kuje tunda zaku dawo saina sake gaisawa da Laylah ko? Tafada tana kallon Laylan Wanda har lokacin itadai bayan gaisuwa batace komaiba kanta na qasa Wanda yasa Anne fahimtar Kamar Laylan nada matsala ko damuwa sbd sanyinta da rashin kuzarin yayi yawa.

Sa’adah datafi kowa farin cikin tafiyar Haj Karima da Laylah
Tana ganin Haj Karima taja Laylah suntafi sbd karsu bada damar da Anne zata qaunaci Laylah
Shi Turaki basama maganarsa Dan sunsan bazai taba ganin laylan ba saidai idan yaganta wata Rana a gidansa acikin Yan aiki.

Ajiyar zuciya Mai sanyi anty Sa’adah ta sauke tareda Dan dagowa kadan tanason magana Amma tanajin nauyi da fargaba saiga sakon zuwan Kawu saidu ya isowa Anne Ana neman ison shigowa dashi.
Wata irin Ajiyar zuciya anty Sa’adah ta sauke sbd tabbas wannan zuwan nasa wani aike ne daga ubangiji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *