QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 4

QADDARAR SUMAYYAH






CHAPTER 4




Sati guda da kammala gyara gidan ranar wata litinin mukhtar ke gaya mata ran laraba masu kafin amarya zasu zo,sai da taji wata faduwar gaba da bata san ta mece ba “Allah ya kawo su” ta fada kawai kana tayi shiru tana dubansa yana rubuta lissalin kasuwa cikin wani qaramin excercise book. Jin shirun yayi yawa ya sanyashi dago kansa ya dubeta,sai yaga littafi take kallo,ya sanya tsinin biron ya dan mintsini cinyarta,sai ta dago tana dubansa fuskarta dauke da murmushi tana sosa gurin ”Yadai ‘yammata?” Kai ta girgiza tana murmushi ‘Babu komai ….. cewa nayi ai za’a yi musu girki ko,tunda naga ana yi”,rai ya bata,don yasan yanzu zata fara soko masa zantukan da baiso,ya tabbatar sumayya danya ce shakaf,domin da wata macen ce aka yi mata zancan kishiya da tuni yanzu gidan ya dade da zama dan qaramin sansanin yaqi,ya tabbatar ba qaramin dauki ba dadi za’a yi ba,duk da quruciyarta ma ya tabbatar da gudun mawar qarin tarbiyya data samo daga gida,tunda ko a gidansu bata taso taga mamanta da kishiya ba,da wata ce wannan kadai ya isheta mafaka. ” ba da kayan abinci na ba,kuma kema ban lamunce kiyi ba,idan kunne yaji ….. ” sai ta ja bakinta ta tsuke,don bata son yayi fushi da ita irin na baya kan zancan fenti da lefe.
Washe gari ranar talata gefen magariba lokacin dawowarsa,ta gama komai kamar yadda yake al’adarta,gidan nata qamshin turaren tsinke,tana tsakiyar yaranta ta siyo madarar ruwa ta musu iloka ta rarraba musu suna sha,wani yaro dake bayan gidansu yayi sallama dauke da akwati wasu yaran na bayansa. ‘Wai gashi inji yaya mukhtar” ya fada kamar yadda yaji matar gidan na gaya masa,sai mamaki ya kamata don bataji alamar shigowarsa k0 qarar babur dinsa ba,tashi tayi ta bude masa labulen falonta suka shiga da su,akwatunane guda shida rlmasu kyau duka iri daya uku set daya uku set daya.
Suna fita ya shigo yana dauke da baqar leda,duka yaran suka masa sannu da zuwa suna qoqarin tafiya gida,ya bibbisu da alawa kamar yadda al’adarsa take sannan suka bi sumayya da
‘Anty sai da safe ….. anty sai gobe” “To Allah ya bamu alheri” ta amsa musu suka fice ta rufe gidan sannan tabi bayan mukhtar da tuni ya shige falon. Murmushi ta sakar masa kamar yadda ya sakar mata “Kinyi kyau sumayya kanta ta sunkuyar cikin kunya tana murmushi Na gode yaya na,sannu da zuwa” ta fada tana cire masa hular kansa da bai samu cirewa ba “Ya kasuwar” ta sake fadi tana qoqarin ajjiye masa ruwa mai sanyi “Kasuwa alhamdulillah …… kinga ai my sumy abinci zaki kawomin don yunwa nake ji’,ta dan zaro ido tana dubansa ” da wuri haka yau?,na zaci sai ka dawo daga sallar magariba”,shafa cikinsa yayi yana murmushi “Salla bazata yiwu cikin nutsuwa ba ina fama da yunwa,taimakeni ki bani sumayya magan’nar da sauran lokaci,idan na kammala ko masallacin sun idar mayi jam’in da ke” “To” ta fada tana miqewa zuwa kitchen.
Bayan ta gabatar masa da komai tuwon semo ne miyar kuka sai qamshin daddawa take duk da babu nama amma tayi dadi qwarai,tasa bismillah sannan ta koma gefansa ta zauna.
Sai da ya kai loma biyu sannan yace “Ga kayanku nan ki duba kiga” ya fada yana mata nuni da akwatunan dake jere gefe,da to ta amsa masa sannan sannan ta sauka qasa ta janyo akwatunan ta soma dubawa. Tana dubawa yana zuba mata santin tuwo,yayin da itama ke santin kayan,komai yayi kyau,sai data kammala tas,lokacin har ya gama cin twon ya jngina da kujera yana kallonta tana ta daga kayan tana yabawa,ta rurrufesu yadda ta gansu sannan ta dubeshi. “Nayi zaton ma kai kayan ne naga lokaci ya qurato” “Um um” ya fada a taqaice ‘Sunyi kyau sosai ya mukhtar Allah ya qara budi,saidai komai naga bibbiyu ka saka kala daya,nufina kayan dake cikin akwatin kayan sawa sune a daya akwatin,under wears da
mayafai ma“
“Eh,akwatin uku naki ne uku nata”, idanu ta zaro a firgice tana dubansa ” ni yaya ka manta ka yimin lefe na tun sanda zaka aure ni?” “Na fiki sani,kayan fadar kishiya na miki”. ‘
Tsoro ne sosai ya kamata,tsoron su yaya yahanasu,ina zata sa kanta idan suka ga wadan nan kayan,komai iri daya ita da amaryarsu,hatta da man lebe iri daya ne?,tabdi lallai ya mukhtar so yake ya janyo mata bayan lallabawa takeyi.
gaskiya ya mukhtar ba’a haka,itafa amarya ce ya zaka hadamu kayi mana abu iri daya? bayan kayan kitchen da kayimin,ka sauya min kayan kallo,kasan su yaya yahanasu sai sunce wani abu idan ma basu ga laifina bato sun zargeni ba”
“Eh,saboda kin fiye min ita,ke din zabi na ce,kuma raino nace,tun kan kisan ciwon kanki kike zaune da ni,tun ana ciyarda mu bana daukar nauyinki,ita din ban santa ba,bansan halinta ba bansan ko zata iya irin zaman da kika yi dani ba,sannan idan su yaya yaha da kike zance ai basu suka yimin ba,da kudina nayi balle a ce don me?,kudina ne kuma iyali nane,saboda haka bana buqatar ki sake cewa komai”. Tun asali ita ba mai musu bace da ya mukhtar din ba,girmansa take gani,kallon yaya take masa saboda haka cikin sanyin jiki tsoro da sanyin murya tace ” hidimar ce naga kamar taso tayi yawa,na gode Allah ya saka da alheri,Allah ya jiqan magabata ya basu aljanna madawwamiya”cike dajin dadin yadda ta yiwa mahaifansa addu’a yace “Amin,Allah yayi miki albarka” “Amin ya mukhtar na gode sosai”.
Tun qarfe takwas washegari ta kammala komai saboda da wuri mukhtar yace zai fita
saboda masu jere,qarfe tara ta sallameshi,har ya fita ya dawo ya dubeta 
” idan kinga babu dadi zaman gidan,na baki izini kina iya tafiya duk inda kike so.idan yaso idan sai kimin waya ki gayan inda kike,idan na taso daga kasuwa sai na biyo na daukeki”murmushin yaqe kawai tayi,don hakanan tunda ta tashi yau take jin fargaba da bacin rai “Babu komai ya mukhtar zan iya zaman ma,me zai hana” “Kada dai ki takura kanki idan ba hali kiyi ficewarki” 
“To, a dawo laf’lya”,ya amsa mata da ” Allah yasa”ya saka kai ya fice. 
Tayi wanka ta shirya tsaf cikin atamfarta da abbanta ya dinka mata ita kwanaki,dark brown ce da adon mint green ajiki,sosai ta mata kyau dinkin ya zauna mata das a jikinta,falo ta koma ta zauna,jikinta a sanyaye bata san dalili ba,gidan ya mata shiru kasancewar ‘yan hirar tata duka ana makarantar boko sai sha biyu da rabi suke tashi. 
Ganin akwai wuta ya sanyata jona kayan kallo,tashar arewa 24 ta kama,cikin sa’a suna maimaicin shirin agent ragab,tana son film din sosai,kusan shi ya dauke mata hankali har sha daya da rabi. 
Gamawarsu yayi dai dai da bugun qofa da ta somaji,ta miqe ta fito tana tambayar waye tare da nufat soron,tun kafin ta kai ga budewa taji cikin kakkausar murya 
“Malama ki bude bana son salo kin wani kama qofar gida kin rufe,bayan kinsan akwai wadanda zasu zo,dadin abun saura ‘yan kwanaki naga ta iyayi” da sauri ta qarasa bude qofar domin tuni ta dauki muryar wacece,yaya bara’atu ce sai fadima tsaye a bayanta,dai sauran da bata san su waye ba,tasan dai ba zasu wuce dangin amaryar ba tunda ita daga amaryar har ‘yan uwanta babu wanda ta sani,iyaka dai tasan cewa amaryar ‘yar aminiyar yaya yahanasun ce. 
Saura kadan yaya bara‘atun tayi gaba da ita badan tayi gaggawar matsawa gefe ba ta wuceta saura suka biyo bayanta suka bar mazan da zasu shigo da kayan katakon da kujerun. 
Bata qosa ba tabi bayansu zuwa dakin da aka bawa fa’izan wanda tuni yasha fentin farar qasar data siya tayi da kudinta,babu komai a dakin a share yake fes kasancewarta gwanar tsafta ce,tun kafin tace wani abun yaya bara’atun ta galla mata harara yayin da sauran suka mata caa da ido 
“Uban me kuma kika biyo mu ki mana?” Ta tambayeta tana huci,qasa tayi da kanta saboda yaya bara’atun ta girme mata nesa ba kusa ba cikin ladabi tace “Zuwa nayi mu gaisa ne” 
“Riqe gaisuwarki bama so” “Uhmm,wallahi kuwa” fatima tayi carafta karbi zancan 
“Allah ya baku haquri” ta fada sannan ta juya ta fice kai tsaye falonta ta shige taci gaba da kallonta. 
 Miqewa tayi zata dauko wayarta dake uwardaki tana ringing ta hangosu suna kici kicin bude kwadon dake rufe da dakin ya mukhtar wanda da kansa yasa ya rufe ya tafi da abinsa,da taga a kulle yake sai ta saka tana fadin 
“Lallai,kaddai yaya mukhtar daki daya ya bayar,tabdi lallai,yana nufin ita a falle daya zata 
zauna waccar tana da ciki da falo….haka ne….mu shirya mata kayan idan muka koma ma sanar da yaya yahan”,bata ce uffan ba don ba mas’alarta bace,ko tata din ce ma basu sako da ita ba. 
Ya mukhtar ne ya kira yana tambayarta komai lafiya ko tace eh sannan sukayi sallama ya kashe wayar. 
Kafin wani lokaci gidan nasu ya cika da ‘yanjeren,ko ina sai shewa ke tashi da qananun magan ganu,take tsoro ya cika sumayya,ta dinga kiran lambar maman naana kan ta shigo ta tayata zama amma wayar a kashe take,ta dinga leqe ta window dinta taga k0 akwai hanyar da zata ratsasu ta fie. 
Bata samu sararin gurin ba sai da suka fara daura alwalar sallar azuhur,tayi hanzarin shiga uwar dakanta ta dauko hijabinta tare da padlock ta sanyawa qofar dakin nata ta fice. 
A qofar gida ta tarad da su naana suna tsaye,suna ganinta suka nufota da sauri,ta dubesu tana cewa 
Me kuma yau kuke tsaye a qofar gida?”bilkisu ce tace “Hanamu shiga anty akayi?” “Waye ya hana ku shiga?” “Masu jeran amarya”inji nana,take taji ranta ya baci,sam bata son abinda zai taba mata yaran,ba zata juri haka ba sam,bata ce musi komai ba sai ” kuzo muje,qila fitina zaku shiga kuyi musu shi yasa suka hanaku shiga don kada ku bata masu kaya” “Wallahi anty a’ah” inji aysha “Shshshshah” sumayya tace da su,sun san me take nuf’l ko batayi magana ba,bata da son su kawo mata hirarwani dama. Gidan mamam naana ta shiga,ta taras da ita tana kwashe abinci cikin kula “Ina zaku haka ke da gayyar yaran naki,ina kika baro baqin naki,ai yanzu nake shirin shiga kinga girki ya tsayar dani ina so na kammala na turasu islamiya sannan na shigo” murmushin yaqe tayi ta ja kujera ‘yar tsuguno ta zauna daga bakin qofar falon maman nanan,yaran nata suka zazzauna kusa da ita “Eh wlh,na gaji da zama ni daya nace bari na leqo” 
“Banda abinki sumayya aiko baki aiko na shigo miki ba kyayi waya a turo miki halima da zainab ko su tayaki zama” “Wallahi maman naana bansan haka akeyi ba ai” murmushi tayi tana tausayawa sumayya da quruciyarta “Ai shikenan,Allah ya bada zaman lafia,ya kade fitina tsakaninku” 
“Amin” sumayyan ta fada cikin faduwar gaba. 
Duka yaran ta zubawa abinci suka ci sannan ta tura kowa ya tafi gida saboda ganin lokacin tafiya islamiya yayi,ta shirya su naana ma suka tafi sannan suka daura alwala sukayi sallar azahar ita da sumayyan. Shinkafa da miya harda salad da kifl abinda ta dafa ta zubo musu cikin plate 
“Sauko sumayya maza muci” kai ta girgiza don a cunkushe takejin cikinta babu space din abinci 
“Na qoshi maman nana” tausayinta ya kamata amma ta dake tayi murmushi 
“Sauko muci akwai abinda nakeson gaya miki” bata da jan doguwar magana saboda haka 
ta sauko ta sanya hannu suka soma ci. 
Cikin hikima maman nanan ke kwatantawa sumayya dabarun zama da kishiya,qissa dabara da wayo kala kala,ta dora da yi mata nuni da haquri,kau da kai kara da alkunya,gaskiya da amana,zama na tsakani da Allah,sai gashi sun tashi da abincin tas,har sai da hannayensu ya fara bushewa da miya saboda sun kasa tashi a gun darussan maman naana sunqi su qare,saiga sumayya na kwasar dariya saboda wani abun idan maman nanan na gaya mata kunya ce ke kamata ko mamaki. Harararta maman nana tayi dariya itama nason qwace mata itama amma ta dake saboda yadda taga sumayya na dariya wani abu da ta gaya mata ne”Au dariya ma nake baki ko?,zaki ci gidanku wallahi idan baki dauke duk abinda nake gaya miki ba” cikin dariyarta dafe baki Tayi
“Yi haquri maman nana,abunne wallahi” ta kuna saka dariya,kada kai maman nana tayi itama dariyar ta kwace mata,ba shakka sumayya danyace har yau,ta miqe ta dauke plate din da suka gama cin abincin ta fice da shi. 
Basu ankara ba sukaji ana kwala kiran sallar la’asar,nan suka tashi sukayi,maman nana ta dubeta tace “Ba zaki koma gida kiyi girki wa mukhtar bane” 
“Ina som in koma maman nana amma ina zaton haryau basu tafi ba,bari na kira ya mukhtar din naji mai zai ce”. 
Koda ta kirashi cewa yayi tayi zamanta kawai idan ya dawo din ya kirata ta dawo,a nan tayi zamanta suka ci gaba da hirarsu har su nana suka dawo daga islamiya,sai qarfe shida kiran mukhtarya shigo wayarta,ta yiwa maman nana sallama ta wuce gida. 
Kaca-kaca ta tarad da gidan tun daga qofar gidan tamkar bata taba Shara ba,kwalaye da ledojin abubuwan da sukajera duka ko ina a gidan,ga kwanukan abinci nan nata har da sabbi da bata taba amfani da su ba,da alama ma girki sukayi saboda kitchen din na bude zasujerawa amarya nata kayan a ciki,mukhtar na tsaye a tsakar gidan riqe da qugu cikin bacin rai,da alama ransa ya baci da irin abinda sukayi,ga abincin da suka dafa din ma basu iya cinyewa ba sun kuma lalata bare a bawa wani,zai soma sababi ta shige jikinsa ta soma lallabashi,sai da ta sauke masa temper dinsa sannan ya tayata suka fara kintsa gidan fes. 
Kafin su kammala anyi kiran sallar magariba,ruwan wanka ta dora musu sannan sukayi alwala sukayi sallah,bayan sun idar ta juye musu ruwan sukayi wankan tare,ta shirya tsaf tayi kwalliya cikin qananun kaya,zata dora musu girki yace ta barshi kawai ya zura jallabiyyarsa ya fita. 
Cikin minti a shirin ya dawo da ledoji a hannunsa,ya ajjiye kan kujerar yana cewa “Dauko faranti kijuye mana wannan,ki hado da cups,hala ma yau duka bakici abinci ba” murmushi tayi sanda take fita daga falon tana cewa 
“Naci mana ya mukhtar a gidan maman naana” ,ta dawo dauke da plates din ‘tajuye abinda ke cikin ledar. 
Tsire ne da zafinsa sai zuba qamshi yake,sai rabin gasashshiyar kaza Ja bude dayar ledar,lemon roba ne na fanta sai maltina wanda tasan ta mukhtar din ce tunda ita bata dameta ba. A nutse suke ci suna hirarsu jifa jifa kamar babu wani abu dake damunsu. 
Suna tsaka daci wayarsa ta dauki qara,sumayya ta miqe ta isa inda take chargy ta ciro masa kana tazo ta miqa masa,baquwar lambace,yayi kamar bazak daga ba amma yadda kiran keta nacin shigowa ya sanyashi dagawa ya kara a kunnensa. 

Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *