RAI BIYU CHAPTER 1

RAI BIYU





CHAPTER 1



Bana son na yi aure a gidan da za’a saka min gadon dubu ɗari biyu da hansin su riƙa girmamani suna ganin girman da ganin mahaifina yana da rufin asiri, na fi son na yi aure gidan da za’a saka min gadon miliyan uku su dinga ganin mahaifina talaka ne suna raina min wayo. Ma’ana dai har yanzu ina kan bakana na auren mai kuɗi fiye da talaka!” 2

Na yi dariya ina sauraren zance ko burin Jidda da ta saba nanata min a duk lokacin da muke zancen aure da ita.

“Ƙawata ba za ki taɓa ganewa ba, kin fiye maida zancena shirme Wallahi Nawwara rayuwar nan ɗa muke sam bata dace da mu ba”

Dariya na sake yi a karo na biyu kana na dube ta irin duban na nake mata a duk lokacin da nake son ta ɗauki zance na muhimmancin.

“Kina da yawan buri Jidda kamar yadda nima nake da shi, sai dai duk da haka na ki be kai nawa ba, gwargwadon rufin asiri Jidda kuna da shi, amman kina tsawwalawa rayuwarki akan son aure mai kuɗi, ba ko wane kuɗi ba ne na halak, ba ko wane mai kuɗi ba ne bane mutumen arziki, da da yawanzu basa darajanta talaka basa ganin girman iyayen matansu, basa kunyar taka kowa saboda suna ganin suna da kuɗi.

Wasu masu kuɗin maneman mata ne Jidda, ke da kike matarsu sai su wulaƙantaki musamman idan suka sa ke ɗin ba kowa bace, nafi sha’awar auren takala ɗan’uwana mai ilmi da ganin ƙimata, mutumen da zai taimake ni na gyara lahira ta, kuma na inganta rayuwar yaro na, ya mutunta iyayena ko da bayan raina, ni iya wannan ya wadatar da ni matuƙar yaƙar yana da halin da zai iya ciyar da ni”

Jidda ta dafani a lokacin da ta lura da hawayen da ya sauko daga idona ba tare da sani ba har sai da ta yi min magana.

“Share hawayenki Nawwara, nasan abunda kike ji, amman rayuwar nan da muke ciki ne bata da daɗi, ka tashi cikin talauci ka girma a haka kai ma kana son sauyin rayuwa, kana son ka taimaki iyayenka, karatu nan ma fa Nawwara ba zai yiyu ba idan babu kuɗi, idan baka da kuɗi kai ba kowa ba ne, yadda aka ga dama haka ake takaka, babu mai son takala sai Allah”

Na yi murmushi ita kuma ta amsa kiran da Mahaifiyarta take mata ta tashi. Na san yadda ƙawata take ji haƙiƙa rayuwar talauci babu daɗi, sai dai ni har yanzu rayuwar masu kuɗi bata burgeni saboda nasan yadda take, ba ko wace ƴar takala ce ke auren mai kuɗi ta jidaɗin rayuwaba, ko da kuwa ya aje mata banki ne a cikin ɗakinta.

“Kin gani ko kullum baƙin tuwon dawa sai na masara babu wani sauyi, ni Wallahi rayuwar nan ta isheni, ni ina tausayin rayuwar yarana idan nayi aure zasu tashi suna cin tuwon dawa duk suyi baƙi, ke Wallahi Nawwara da kwana ɗari da talaka ƙara kwana ɗaya da mai kuɗi” 1

Jidda ce take wannan maganar, yayinda take dire kwanon samira mai ɗauke da ƙatowar mulmular tuwon dawa da miyar kuka, agabana.

‘Allah sarki rayuwa ku har kun samu tuwon dawa’

Na faɗa a raina, a fili kuma sai na ce.

“Aifa sai ki yi mitarki kuma ki ci tuwonki dan ni dai a ƙoshe na ke”

Jidda ta wara ido tana min kallonta na iskanci wanda ta saba min a duk lokacin da aljannun rashin mutunci suka hau kanta.

“Maman Nura, Maman Nura yi sauri ki zo”

Nayi saurin kai hannu ina rufe mata baki jin tana kiran mahaifiyarta, nasan wata ƙulalliya zata ƙulla min.

“Jid”

Ban yi furucin ba sai ga Maman Nura a cikin ɗakin wato mahaifiyar Jidda.

“Maman Nura tace gida zata je da shi”

Jidda ta faɗa sai Maman Nura ta ce

“To bari a ƙara mata”

Da sauri na ce.

STORY CONTINUES BELOW


“Wallahi ƙarya take min Mama, ban ce ba”

Juyowa ta yi ta watsa min wata uwar harara kamar zata zo ta fanɗareni da mari, kana ta nuna ni da yatsanta.

“Kin gani Nawwara wannan halin naki yana ɓata min rai, kina rage ƙima idona, ko abu kika tarar a gidan nan ba zaki ɗauka ki kai gida ba, ni da Mamanki ba ɗaya ba ne ko? Allah wata rana sai na ƙwaɗa miki mari idan kina min irin wannan iskanci, fitsarriya”

Ta juya a fusace ta fice. Ni ko na kaiwa Jidda duka.

“Kin haɗa ni da ita kin jidaɗi”

“Ai nasan idan ba haka na yi miki ba, ba za ki co shi ba, marar mutunci, ni idan naga abu a gidanku tambaya nake ba ɗauka nakr na tsire ba”

Na girgiza kai ganin yadda take magana da tsire baki.

“Allah ya shiryaki Jidda”

“Amin Wallahi, idan Allah be shirya ni ba ai na shiga tara bama uku ba, Jidda ai sai Nawwara”

Bayan Maman Nura ta ƙaro min tuwon na taso Jidda ta rakoni ƙofar gida, a lokacin ana kiran sallah magariba. A bakin ƙofar gidansu ta karɓe tuwon.

“Kawo zan bawa Nura ya kai miki, kinga su idi can ƴan sa ido, ko Sallah ba zasu tashi su yi ba”

Ta taimaka min matuƙa, domin nima kaina ina jin kunyar fitowa da kwano a wani gida saboda ƴan sa’idon unguwa masu zaman kashe wando, zaman ƙirga atamfarki da kuma inda zaki je ki dawo. Sallama nayi mata tare da sai da safe sannan na kama hanya, bayan nayi nisa sai na hango Nura tare ɗauke da kwanon tuwon, sauri na ƙara dan bana son ya cin ma, nasan halin Nura zai iya cin min a hanya ya ce karɓi tuwonki.

Lokacin da na shiga gida har sai da na ɗan tsaya a bakin ƙofa jiransa, tuƙuna ya ƙaraso na karɓi tuwon yana mita ya juya ya koma, ni kuma na shiga gida ina doka sallama.

“Amin wa’alaikissalam Nawwara”

Ya faɗa yana aje butar da yayi alwala, sannan ya ɗauki tsohon rediyonsa da ke aje ya miƙa min.

“Shiga da wannan ɗaki”

“Tau Baba, Allah ya tsare”

“Amin, Amin”

Ya faɗa yana kallon kwanon tuwon da ke hannuna, kamin yasa kai ya fice.

A ɗaki na samu Inna ita da Habiba da Sakina, da mai sunan mama, wato Jamila da muke kira da Ummi.

“Wai Allah na”

Na faɗa ina ƙoƙarin zama kusa da Inna.

“Nawwara kin dawo?”

“Eh ga tuwon dawa Maman Nura ta haɗo ni da shi”

“Tau Allah ya saka mata da alheri, zuba ki ci tun safe rabonki da abinci Nawwara”

Na tada kai na kalli Inna.

“Ai ni matuƙar zaku ci, ko ban cin ba bana jin komai, amman idan na ci ku kuna jin yunwa hankalina ba zai kwanta ba, Habiba zuba ma Baba da Inna sai ku cinye sauran”

Inna ta ce

“Sai fa kin ci, ai ƙara su ma ɗazu Babanku ya samo naira hansi na basu suka siyo garin kwaki suka saka gishiri suka ci” 1

“Habiba zuba min kaɗan, ina Noor wai?”

Na tambaya ganin baya cikin ɗakin.

“Na aike shi ya samomin batir gurin Hajara wai mu samu na haskawa a fitila anjima”

Cewar Inna, ni kuma na amsa da

“Okay”

Tare da unƙurin tashi na cire hijab domin alwala. Ko kamin na yi alwala na gama, har sun cinye tuwon abun ka da masu jin yunwa.
Bayan na gama Sallah Magariba Habiba ta miƙo min ɗan tuwo can laƙe ga kwano.

“Gashi nan ke da Noor”

Karɓa nayi na aje a gabana. Sai ga Baba ya shigo yana faɗin.

“Bari naje gidan ciyaman na jirashi, ko Allah zai na samu wani abu, sai mu karya da safe”

Wani abu naji ya zo ya tsaya min a zuciya, wanda ya saba tsaya min a duk lokacin da Babanmu zai je yawon maula. Ina jin lokacin da Inna ta ce

“Allah ya tsare”

Habiba kuma ta ce

“Baba ga tuwon dawa”

“Ina aka samo tuwo?”

“Nawwara ce ta samo gidansu Maman Nura”

“Ku cinye, sai na dawo”

“Allah ya bada sa’a”

Da Amin ya amsa, sannan ya fice. Ni ko na aje carɓin da ke hannuna, na miƙe tsaye ina amsa sallamar Noor.

“Momy a ci abinci gidan Maman Hajara, tace na faɗawa Mama Habiba ta zo ta ɗauki tuwo, Momy har da kifi a miyarsu”

Duk dariya muka sa masa, daman Noor be iya cin daɗi ba, komai ya ci sai ya bada labari. Yasa hannunsa aljihu ya ciro batir ɗin ya miƙawa Inna, sai ya sake saka ɗayan hannunsa a aljihu ya fiddo kifi ɗan tsito ya miƙa min. 2

“Momy ungo na rage miki, ci ki ji”

Kai na girgiza masa.

“Cinye abun ka nima zan je can na ci”

“Yarinya ya ƙare ai”

“Ni ce yarinya?”

Na tambaya ina nuna kai na, sai ya sa dariya yana tsalle. Haka rayuwarsa take ba duk abu ne yake damunsa ba, ko da bai fahimcin inda duniyar ta dosa ba ne oho.Bayan mun yi sallah isha’i Inna take labarta min irin dukan da ka yi ma Noor a makarantar islamiya yau saboda rashin biyan kuɗin sati biyar. +

“Momy duba nan bulala ya kwanta min”

Ya faɗa yana nuna min hannunsa fafaren idanuwansa na cika da hawaye. Abun ka da farin mutun bulalar ta masa ja sosai kwanci jini ya kwanta a hannunsa. Hannunsa na kama ina murmushi.

“Ai lada kuke samu idan aka dake ku”

“Ni ba zan sake zuwa ba, Malam Usman azzalumi ne”

Ya faɗa yana taɓe pink lips ɗinsa. Sai na yi saurin rufe masa baki.

“Ba a zagin malami Noor kar na sake ji”

Habiba ta bige min hannu.

“Wallahi bar shi ya faɗa in ba zalumci ba miye na dukan ƙaramin yaro kamar Noor, ai dai yasan babu kuɗin ne da yanzu an bada, ji yadda ya bugar masa fatar hannu har ta yi ja, yaro ba a saba dukansa gida ba haka kawai wani ƙato zai dake shi”

Taja hannunsa suka fita waje ta shimfiɗa tsohuwar tabarma suka zauna, ni kan murmushi ne nawa, masifa ai Habiba ta iya ta har ta gaji musamman akan Noor duk wanda ya taɓa zai ga babu kyau.

Baba be shigo gida ba sai goma har da kwata a lokacin har Inna ta soma bachi, balle kuma Jamila da Sakina ba mota, daman su da anyi sallah isha’i suke bachi. Ni da Habiba ne kawai ba mu yi bachi ba, sai Noor da ke faman ƙirga taurariya, ina daga cikin ɗaki Baba yayi sallama, Habiba da Noor da ke waje suka amsa masa.
Motsin rufe ƙofar gida da Baba ke ƙoƙarin ne ya tashi Inna daga ɗan guntun bachi da ta fara.

“Malam ka dawo?”

Ta faɗa tana gyara ɗaurin ɗankwalinta, shi kuma ya amsa mata fuskarsa da damuwa sosai.

“Na dawo amman ban samo komai ba”

“Ciyaman ɗin be dawo ba ne?”

Inna ta sake tambaya.

“Ya dawo amman be fito ba kuma be ce mu shigo ba, sai kawai aka rufe gate” 1

Kai na girgira kana ka ce

“Ai ba zaku samu ba, zai ce kullum kuna zuwa kuma masa maula a ƙofar gida, wata rana wulaƙancin ma sai ya fi haka, ni Wallahi Baba da ma zaka ji shawarata da ka daina zuwa gidan kowa roƙo yana zubar da mutunci da ƙimar mutum take”

“Zuwan ne ai ya zame mana dole tun ba babu wata sana’ar yi mai ƙarfi, tsaran icce ne ba kullum ake samu ba, jarin kuma mun cinye rayuwa ta yi tsada yanzu, dole sai mun haɗa da haka indai kana gida babu wanda zai ɗauko ya aiko maka. Ga ɗari na ranto gurin Malam Sahabi, da safe a karya”

Ya ciro naira ɗari a aljihunsa ya miƙawa Inna. Baba yana da gaskiya ba ko wane mai kuɗi bane mai zuciyar tausayi da taimako mafi yawansu kansu suka sani.

Unƙurawa na yi na tashi, na nufi ɗakinmu da muke kwana a ciki. Ganin haka yasa Habiba ta shigo da Noor sai ta koma ɗakinsu Inna ta taso da su Jamila da Sakina.

WASHE GARI…

Bayan na yi sallah asuba na zauna ina askar na safe da na saba yi a duk lokacin da na gama Sallah. Misalin ƙarfe bakwai da rabi Jamila taje ta siyo mana koko na naira ɗari, aka rarraba haka nan aka sha gayarsa ba tare da suga ba muka sha. A lokacin ne Sakina ta yi ma Noor shirin makaranta, ta kama hannunsa shi da Jamila tana cewa sai sun dawo. Har ya tafi sai ya sance hannunsa daga na Sakina yazo a guje yayi min kiss a goshi, sannan yayi min bye-bye yana dariya suka fice. Ban san inda ya samo wannan dabi’ar ba, ni dai nasan ban taɓa masa sumba idan zai je makaranta ba, ban kuma saba masa idan zai fita ba, amman shi yana yawan min a duk lokacin da zaije Makaranta.

Sallama muka ji ni da Habiba dake saka wandon makaranta.

“Daga ji Malam Hamisu ne, yabi ya takura mana akan kuɗin haya da be taka kara ya karya ba, baƙin Azzalumin banza mugu mtsss”

Ta ƙarasa tana jan tsaki. Na tada kai na kalleta.

“Kowa a gurin ki Azzalumi Habiba, ina laifin mutumen yana ɗaga mana ƙafa dai-dai gwargwado ke kin san da wani gurin ne da yanzu an koremu, amman kowa ki riƙa kiransa da Azzalumin hakan be dace ba sam”

Kamar jira take sai tayi cikina da faɗa.

“Kowa Azzalumine Nawwara na faɗa, waya kula da halin da muke ciki har ya damu kowa dai kansa ya sani, na faɗa kowa na duniyar nan Azzalumi ne”

Tana kaiwa nan ta saka farin hijabinta ta ɗauki jakarta ta fice ina mata Allah ya shirya.
Bayan ta fita na tashi ya leƙa ɗakin Inna dan yi mata ina kwana.

“Lafiya ƙalau Nawwara Allah yasa dai kin sha kokon dan nasan halin fa”

“Na sha Inna, har sai da na raga”

Na faɗa ina dariya, sai ga Baba ya shigo.

“Baba ina kwana?”

“Lafiya ƙalau Nawwara an tashi lafiya”

“Lafiya ƙalau, ya lafiyar jikin”

“Alhamdullilah, Hamisu ne ya zo na ce yayi haƙuri har zuwa satin sama, sai dai ya ce daga wannan ba zai ƙara ɗaga mana ƙafa ba”

Ya faɗa yana zama kusa da tsohon rediyonsa.

“Allah gamu gareka, ka iya mana”

Cewar Inna tana sauke ajiyar zuciya. Ni kuma na miƙe tsaye ina faɗin

“Bari naje na shirya na koma can na gani dan jiya sun ce min na dawo da safe”

Baba ya ce.

“Sun ce zaki samu aikin ne?”

“Inshallah zan samu, saboda gurin Babansu naje kuma yana da mutuncin sosai”

“Wai aikin me ne?”

Inna ta tambaya tana daga kwance.

“Sharar ti’ti ne kuma kullum ake biya” 1

Ta yi saurin tashi zaune.

“Wane irin sharar ti-ti kuma Nawwara? Wannan sam ba mutuncin ki ba ne, Wallahi zaginki za a fara daman sun saba” 1

“Dukan masu zaginmu Inna babu wanda ya taɓa ɗauko Naira ɗari ya bamu ya ce mu siye wani abu, kuma na muku alƙawarin kare mutuncinna, Hijab zan saka idan har na samu aikin nan”

“Ba irin wannan aikin ya dace da ke ba Nawwara, ni nafi kowa dacewa da na yi shi”

“Baba ka san kana da Asma ba zai yiyu ka yi irin wannan aikin ba, kuma na maka alƙawari da zarar ka samu wani aikin zan daina wannan”

Ya girgiza min.

“Ba zaki yi ba Nawwara, sai dai ba zan hana ki bincikar wani aikin na daban ba, shi ma kuma kamin na samu wani abun yi”

Na ɗaga masa kai cike da ladabi.

“Tau Baba zan koma Candy Restaurant ko Allah zai sa a dace, amman Baba dan Allah ban da turin baron nan da ka taɓa yi kasan yadda zuciyarka yake idan ka ɗauki abu mai nauyi, ni Wallahi bana son kana dakon nan”

Na faɗa kamar na yi kuka, dan har ga Allah nafi tsanar dako fiye da komai a duniyar nan. Baba yayi murmushi irin nasu na manya sannan ya ce

“Nawwara kenan, ni dai ina jan hankalinki kan tsare mutuncinki da kuma na mu gaba ɗaya, Nawwara ke rai biyu ce mai maka da rai dubu a gurin mu, dukan abunda zai zubar da mutuncin ɗan ki da ni Mahaifinki karki kuskura aikata shi, ki riƙa tuna ke uwace, kuma ɗiyar wani wacce idan kika yi abun assha za a zagi Ubanki, ɗan ki kuma ayi masa jawabi, ni dai na san irin tarbiyar da na baku Wallahi ko cikin maza dubu zaki shiga matuƙar baki watsar da tarbiyar gidan nan ba, nasan zaki fito lafiya.

Ni da kan ɗan ki rai biyu ne a gareki Nawwara, abu kaɗan kika aikata zai iya saka zuciyata ta buga, ɗan kuma zai tsanake ni ya riƙa nadamar da kika kasance uwarsa, saboda haka ki riƙe mutuncin ki, Allah ya muku albarka”

Ni da Inna muka amsa da Amin.
Haka yake min a duk lokacin da zan fita neman aiki ko wani abu makamancin wannan, waɗannan nasihohin suna tasiri a gareni matuƙa, sukan katangeni daga duk wani tayi da wasu suke min na siyar da mutuncina, ko kuma musanya mutuncina da takarɗun aiki.Bayan na baro ɗakin Inna na ɗibi ruwa a shiga ban ɗaki na yi wanka. Atamfata ta sallar bara na ɗauko na saka, akwai da son saka gyale duk da kasancewar Baba baya son haka, daman ba ko waɗanne uwane suke son ƴarsu ta saka gyale ba, sai dai nawa gyalen ba irin na barbarɗaɗɗin ƴan mata nan ne ba, me zai kai ni saka ƙaramin gyale bayan ina da ɗa kuma ba budurwa ba ce ni, duk da yake wani lokacin Jidda da Habiba har da mutanen waje kan faɗa min babu wanda zai kalleni ya ce ni bazawara ce har sai idan ni na faɗa, wani lokacin ko da na faɗa ba a yarda har sai idan waɗanda suka san ni ne. +

Ina da kyau jiki dai-dai gwargwado wannan yasa mutane basa yarda idan har na faɗa cewar ni Bazawara ce har da ɗa, wannan baya rasa nasaba da auren wuri da aka min, a lokacin da nake ganin kamar ban isa auren ba, auren da ya gurɓata min rayuwa ya canja ƙaddarata daga mai kyau zuwa mummuna.

Atamfata miyan goro ce mai ratsin ja, hakan yasa na saka jan gyale saboda atamfar ta ƙara fita, talkamin Habiba na ɗauka na saka masu launin ja. Fes na fito sam baza kalleni kace ina da wata damuwa a wannan lokacin ba, idan ba ka birkice atamfata gaka ta roba bace sai ka ɗauka ni ƴar wani shegen mai kuɗi ce, ba laifi ni kaina ina sarawa kaina indai babin kwaliyana ne na iƴa fito kamar matar minister. 1

“Inna zan tafi”

Na faɗa ina tsaye daga jikin ƙofa, kai na jingine da ƙofar ina kallon Baba da ke unƙurin tashi.

“Tau Allah ya kiyaye”

Inna ta faɗa, Baba kuma sai ya ce

“Ni ma bari na shiga kasuwa na ga abunda Allah zai yi”

Salamar Maniru muka ji wato almajirin Hajiya Murja, maƙociyarmu masu babban gida, matar babban soja wacce bata taimako sai idan da dalili. Ni da Inna muka haɗa baki gurin amsa masa, Baban kan ya amsa masa da.

“Bata nan taje makaranta”

Domin yasan Jamila take nema, takan aiko kiranta a duk lokacin da wani aiki ya sha gabanta, domin kawai ta taya ta aikin sai ta sammata wani abu daga abincin rana ko dare da aka yi a gidan.
Bayan Maniru ya fita Baba ya haɗe fuskarsa saboda mu ɗauki zancensa da muhimmanci, ya saba mana a duk lokacin da yake hanin mu kan aikata wani abu ko kuma ba mu umarni.

“Bana son zuwan da Jamila take a gidan Manjo Faruku, kowa ya tsaya inda Allah ya aje shi”

“Ni kaima bana son zuwanta a gidan domin yaron gidan nan ba shi da tarbiya, sannan yunwa babu abunda bata sawa musamman ga waɗannan da suke yara”

Na faɗa cike da jin zafin tuna irin satar da ta taɓa ɗorawa Sakina a kwanakin baya.
Inna dai bata ce komai ba bayan ajiyar zuciya da ta sauke.

“Na tafi nidai ayi min addu’ah”

“Tau Allah ya bada sa’a karki daɗe dai, kuma ki kula.da irin mutanen da zaki yi hulɗa da su”

Cewar Inna ni kuma na amsa da tau na kama hanya ina addu’ar fita daga gida wato. _Bismillaahi, tawakkaltu ‘alallaahi, wa laa hawla wa laa quwwata ‘ illaa billaah._
_بِسْمِ اللَّهِ تَوَكَّلْـتُ عَلَى اللَّهِ، وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُـوَّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ_

Babu ko ƙwandala a hannuna ƙasa na kama hanya duk kuwa da kasancewar unguwar akwai ɗan nisa da ta mu. A bakin ti-ti na haɗu da Bilal wato abokina ko kuma na ce mutumen da muke mutunci da shi sosai har mutane suke raɗin-raɗin wai akwai soyayya a tsakanin mu.

“Nawancy”

“Bilal ya gida?”

“Lafiya ƙalau Wallahi Ina zaki je haka?”

Bana son faɗa masa ainahin inda zanje, ba kasafai nake son mutane su san ina zuwa aiki ba nafi son aji na samu aikin kawai, musamman Bilal da yake yawan nuna min baya son neman aikin da na ke.

STORY CONTINUES BELOW


“Nan zan je gawon nama gidansu wata ƙawata Zinatu”

Ya matso da mashin ɗinsa Honda

“Hau na sauke ki”

“A’a na gode”

Na faɗa ba dan bana son hawan ba sai dai bana son yasan gurin da zanje.

“Dan Allah ki hau mana, t-t ne balle ki ce kina jin kunya an mun fito cikin unguwar”

Bana da wata dabara ta da wuce na hau ɗin, babu tantanma idan har na zaɓi zuwa a ƙafa zan wahala sosai.
Abun ka da mai nema sai kawai na gyara zane na na haye mashin kamar na yayana ko kuma na ce na Ubana. Bilal ba baƙona ba ne hakan yasa na sake da shi sosai muna fira har muka isa bakin ƙofar gidansu Zinatu. Na sauka ina masa godiya.

“Am Nawancy na manta ban labarta miki wani abu ba, mun samu sabon shugaba a kamfaninmu kuma ya buƙaci sauye-sauye saboda yana da zafi sosai, kuma duk ya zubar da ma’aikatan gurin ya ce sabbi za a ɗauka, sai dai be faɗi rana ba, so ina fatar idan za a ɗauki wasu zaki yi applying”

“Kai ka ce kai ma kun tsallake rijiya da baya”

“Wallahi mun tsallake kan, domin mutumen akwai zafi sosai, gashi baya ganin kowa da mutuncin, ko dan yana kamfanin Mahaifinsa ban sani ba”

“Ai fa ka ji to mu da ba wani zurfin ilmi mukayi an ya zai ɗauke mu kuwa, Bilal kafa san SSCE ne kawai da ni”

“Abun sa’a ne Nawancy zaki iya shiga kuma ki yi sa’ar samu, ai kisan mataki mataki ne”

“Naga Babban kamfani ne Bilal”

Yayi wani abu da fuska yana matse hancin, irin yadda yake min a duk lokacin da zai zolayeni.

“Trust me girl zaki samu babu tantama”

Na yi murmushin da ya fitar da dimple ɗina, ina ƙara jan gyalena dan rufe jikina.

“Ni zan wuce aiki kar na yi latti ya kore, dan ya faɗa mana idan ka ƙara minti ɗaya zai koreka daga kamfanin”

“Tau Allah ya kiyaye na gode”

Hannunsa ya ɗaga min.

“Ina gaida abokina Noor”

Kai na ɗaga masa as respond na juya kamar zan shiga gidansu Zinatu, ina hango ya kama hanya, na juyo dan har ga Allah ba gidansu Zinatu zanje ba na san ma by this time bata gida, ko ma tana nan mi zanje na yi a gidansu yarinyar da bata ƙaunar zuwa gidanmu.

Miƙe ti-tin gawon nama na yi har na ɓullo ta gurin gidan Alu, wato tsohon gonnan, na miƙe na tsallaka babban titi na doshi Candy Restaurant.
Restaurant ne mai kyau da tsari ga tsafta, ba laifi ma’aikatan gurin suna na’am-na’am da mutane tun a farkon zuwana na lura da hakan. Kai tsaye na nufi gurin wanda na ke zaton babbansu mai sanye da riga orange an rubuta mata Candy Restaurant da fafaren harufa.

“Assalamu Alaikum”

“Wa’alaikissalam”

“Sannu ko ka gane ni?”

“Gaskiya ban gane ki ba, abun da yawa”

“Ni ce wacce na zo kwanakin baya ka ce min Khadeeja Candy bata nan”

“Ayya Allah sarki, sai kuma kika ƙara rashin sa’a yau ma bata nan”

“Dan Allah ko kasan yadda za’ayi ma sameta?”

“Gaskiya bata garin nan tana Gusau kusan yanzu a can take zama, ko tana garin ma da wahala ta shigo nan”

“Dan Allah ko zaka taimaka min da numberta?”

STORY CONTINUES BELOW


“Gaskiya ba zan iya baki numberta ta saboda matsala ta tsaro, amman ke zaki iya barin Number idan ta shigo gari sai na sanar da ke”

A take na rubuta masa Number Jidda domin bana da waya, kuma Baba ko Inna babu mai waya a cikinsu.

“Idan ka kira ka ce Nawwara kake nema”

“Tau Inshallah”

“Na gode”

“Yauwa a sauka lafiya”

Jiki ba ƙwari na juya na fito. Har ga Allah ban jidaɗin rashin ta tararda mai restaurant ɗin ba, ga kuma uwar hanyar da zan miƙe duk da yaƙe rana be yi sosai ba, sai dai ina jin kamar zan wahalar da kaina tafiya a ƙafa har zuwa unguwarmu. 3

“Allah ƙa zame min gata”

Na furta a fili ina busar da iskar bakina. Dabarar na je gidansu Zinatu ne ya faɗo min a rai duk da ban yi niyar hakan ba.
   Haka na kama hanya na miƙe na koma ta inda na fito har na isa ƙofar gidansu Zinatu. Har na kai hannu zan buga ƙofar gate ɗin sai mai gaɗinsu ya wangale gate ɗin gaba ɗaya daga can ciki. Zinatu hakince a motarta ta kunno kai da alama fita zata yi, har ta yi kamar zata wuce sai kuma ta tsaya ta sauke gilashin motarta tana kallona ta cikin baƙin gilashin da yake idonta.

“Khadija Musa Kafinta”

Ta kirani da sunan da nake amfani da shi a makaranta, nima kuma sai na kirata da nata.

“Zinatu Alhasan Hamshaƙi”

Ta yi wani shu’umin murmushi tana cire gilashin idonta.

“Nawwara ashe ana ganinki ko dai hanya ce ta biyo da ke?”

“A’a haka kawai yau na ce zan kawo miki ziyara”

Ta yi ƙis a ƙasan maƙoshinta wato ƙwafa na ƙasan maƙoshi.

“Aiko kin kyauta gashi kuma zan fita, ki shigo na saukeki gida kawai”

Na ji wani sanyi a raina daman abunda nake nema kenan.

“Okay”

Na faɗa sannan na buɗe motar na shiga. Jefi-jefi muke firar makarantarmu wato Nana Girl’s Secondary School, kamin na ɗauko mata zancen masters da naji ance ta fara yi.

“Wallahi ina nan ina yi yanzu haka kuma na samu aiki a wani babban kamfani this monday zan fara”

“Mashallah, Allah ya taimaka”

“Amin ai ke kin ƙi karatu ko?”

“Uhmm”

Na yi murmushi kawai ina danne abunda ke raina, yawancin mutane sukan faɗa min haka musamman abokaina wai na ƙi karatu bayan kuma karatun ne ya ƙi ni tun da komau sai da kuɗi, hawan napep zuwa da dawowa ma ai sai da kuɗi. Har ta sauke ni ƙofar gidanmu bata kalma bata sake fita daga bakinta, nima kuma ban sake ce mata wani abun ba.

“Na gaida Inna”

Ta faɗa lokacin da ta ga na buɗe mota zan fita.

“Inna zata ji na gode”

“Okay”

A bakin ƙofar gidanmu na tsaya ina kallonta cike da sha’awar rayuwarta, duk mutune da yayi karatu burgeni yake, balle ita da ta fara cin amfanin karatun a yanzu. Sai da na daina hangota kan kwanar gunguwarmu mai kwatannin sannan na shiga gida.

Inna na samu a tsakar gida tana shara, gyale na kawai na yaye ya karɓi tsintsinyar dake hannunta na cigaba da shara.

“Allah yasa dai an yi sa’a”

“Wallahi ba’ayi ba Inna wacce na je nema bata nan, amman na bada number wayata aje mata”

“Allah yasa mu da ce,  amman dai daga yau karki saki zuwa wani gurin ki haƙura idan ”

“Amin, inshallah nima zan haƙura indai da rabon na samu zan samu”

“Allah ya miƙi albarka”

“Amin”

Ta shinfiɗa tabarma ta zauna ni kuma na cigaba da sharar ina labarta mata cewar Zinatu ce ta kawo ni gida. Bayan na gam sharar na tattara na kwashe, muka ji ana sallama a ƙofar gida. Inna ce ta amsa ni kuma na nufi ƙofar dan duba ko wanene. Ganin mutun sanye da kakin ƴan sanda yasa gabana faɗuwa sosai.

“Nan ne gidan Musa Kafinta?”

“Eh Nan ne”

Na amsa murya na rawa.

“Musa Kafinta yana police station na guiwa locos, ana son a sanar da iyalansa ne kuma baya da waya shiyasa na zo”

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, miya faru?”

“Idan kika je can zaki ji”

Ya juya yayi tafiyarsa, ni kuma na juyo cikin gida idona na zubar da ƙwalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *