RAI BIYU CHAPTER 20

RAI BIYU




CHAPTER 20



Kaina ya yi nauyi sosai ta ya zan iya watsa kasa a gaban manyan mutane kamar wadannan? Mi zai biyo baya idan na ce ban amince ba? Wane irin fahinta Baba Sulaiman da Baba Dahiru zasu min?

“Ban zata zai aiko da wuri haka ba, shiyasa ban fada muku ba” 1

Na fada yayinda nake maida kaina kasa.

“Yanzu dai ba wannan ba, kin amince ko baki amince ba?”

Baba Dahiru ya tambaya. Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na amsa.

“Na amince” 1

“Al-hamdulillah, Allah ya miki albarka Nawwara kin ceci rai”

Abunda ya fito daga bakin Mahaifin Jibril kenan fuskarsa shinfide da farinciki.

“Tashi ki koma gida”

Cewar Baba Sulaiman, haka na taso kamar marar lakka a jiki na fito daga gidan na nufo gida, tun a hanya kuka ya fara kamani amman ban yarda na yi ba sai da na iso gida, ina shiga na fashe da kuka kamar an min mutuwa.

“Lafiya miya same ki?”

Inna ta tambaya tana rike da tsintsiya. Faduwa na yi zaune.

“Inna wai iyayen Jibril ne suka zo neman aurena?”

“Ban gane suka zo neman aurenki ba”

“Mahaifinsa ya turo da wasu mutane ya ce ni nace su zo, wai su nema masa aurena, shine Baba Sulaiman da Baba Dahiru da Baba Audi suka kirani suka tsareni suna tambayar wai na amince ko aa”

“To mi ya faru?”

“Na ce na amince”

“Shine kuma kika zo nan kina kuka”

“Ni bana son shi Inna ba zan aureshi ba”

Sai Inna ta nuna ni da tsintsiyar da ke hannunta.

“Wallahi kin yi kadan karyar karya take Wallahi, wato ni gani ice mai dadin zama shine zaki zo nan kina min kukan ba zaki aureshi ba ko? Ni da kika raina ai miyasa baki fada musu tun can ba”

“Baba Audi zai iya yanka ni”

Na fada cikin kuka.

“Oo to sai ni da nake rarrashin ki zaki xauna kina min kuka kamar yadda karamar yarinya ko?”

“Wallahi ko an daura auren nan ba zan tare ba”

“Tashi kije gasu can ki fada musu tun basu tafi ba, ko kuma ni na yafa mayafina na je na fada musu kina nan kina kukan ba zaki yi auren ba”

Jin haka yasa na yi saurin tashi na shige dakin Inna dan nasan duk Baban Audi ko Baba Dahiru suka ji wannan maganar na shiga uku yanxu bayan na ce na amince kuma na ce ban amince ba ai zasu ce ina musu wasa da hankali. Kuka na yi sosai dakin Inna rayuwar da zan yi gidan Jibril nake hangowa, taya zan rayu da mutumen da ya wulakanta ni? A yanzu ma zai iya kara wulakanta ni saboda yana ganin a bagas ya same ni kamar wacan lokacin, kuma zai yi ta tunanin ina son sa wanda hakan zai bashi damar sake wulakantani kuma na san har duniya ta nade Jibril ba zai taba sanin mutuncina ba.

Sai da yamma Baba Sulaiman da Baba Dahiru suka zo gidan tare da kwalaye minti da cingan da sauran abubuwan da ake kawo wa na baiko, suka labartawa Inna abunda ya faru, ta nan nake jin sun yanka sadakina dubu talatin abokin Abbah ya biya dubu dari kasa, kuma sun saka kwana shida da suka rage na aurena da Bilal sun maye gurbinsu da Jibril. Baba Sulamain har dadi yake ji wai yafi son haka ta yadda Bilal kawai da familynsa zasu ji an daura min aure. 1

A daren ranar kasa bachi na yi sai na kwana ina raya daren da sallah nafila da karatun qur’ane Allah na mikawa lamurrana har yanzu ban cire rai daga auren Bilal ba. 3

STORY CONTINUES BELOW

JIBRIL POV.

Tunda su Abbah suka kama hanyar gidansu Nawwara gabansa ke ta faduwa yana sauraren irin amsar da zasu dawo da ita, Abbah na kiranshi ya tsaya karanta addu’a sannan ya daga zuciyarsa cike da fargaba.

“Kana ina?”

“Ina gida Abbah”

“Ka zo gida ka same ni yanzu”

“Abbah bata amince ba ko?”

“Ta amince har mun biya sadaki kuma kwanakin da suka rage na wacan da bata aura ba aka maida da naka”

Rudewa ya yi yana tsaye ya zauna sai kuma ya sake tashi tsaye.

“Abbah are you serious?”

“Ah wasa na ke da kai? Ko wasa ake da lamarin aure?”

“No no i mean thank you gani nan zuwa”

Abbah ya kashe wayar yana murmushi. Sai Jibril ya fadi ya yi ma Allah sujudar godiyar, sannan ya mike tsaye yana wani irin dariya kamar mahaukaci har da jjjiga jiki, zuwa can kuma ya fara rawa takawa ya farayi a hankali a hankali kamin ya fara yi da karfi har da su kada kwankwaso, sai kuma ya yi tsalle ya fada saman kujera. 4

“Oh my God i just can’t believe this Al-hamdulillah Allah”

A take ya fara hango irin rayuwar da zasu yi da Nawwara idan aka daura musu aure, ya dade yana ta ayyana irin jindadi da gatan da zai nuna mata sannan ya tuna cewar Abbah yana can yana jiranshi kuma yau zai bar garin. Cikin hanzari ya fita gida, zuciyarsa fari kal saboda farinciki, har ya yi kamar ya kira Nawwara sai ya tuna da riske yayi mata sai ya fasa dan yasan tana nan tana fushi da shi. Ko da ya isa ya samu su Abbah na cin abinci shi kan ko ruwa kasa sha ya yi saboda farinciki, rabon da ya yi farinciki irin wannan har ya manta, kallo daya zaka masa ka gane yana cikin farinciki.

Wasu batutuwan Abbah ya tattauna da shi akan auren bayan ya fada masa yadda komai ya gudana. Sannan suka tsaya tsara yadda za ayi.

“Zan ba Hajiya ta hada mata kayan sawa na tufafi da komai da komai da ake, kai kuma sai ka bata kudin da zata yi hidima da wuri saboda kar lokaci ya kure, na fadawa iyayemta bama son komai, saboda haka idan an daura aure sai ka fara gyaran gidan kamin nan da wata daya ka gama sai ta tare”

“No Abbah a cikin week din nan ma za a iya komai a kudi ne matsalar kuma da an bada kudi za ayi komai a cikin lokaci, kuma ba dole sai furniture ba dole sai anyi order a abroad ba a nan ma Kano Kaduna ma za a iya samu na wajen, Abbah na fi son ana daura auren ta tare ranar gudun kar wani abu ya shiga” 3

Abbah ya dan tsaya kallonsa ya so ya fahimce cewar cilastawa Nawwara yayi sai kuma ya tuna da irin son da yake mata ko da ita din bata son shi ba matsala ba ne. Su yi maganganu sosai akan auren da kuma yadda za a tsara komai, ciki har da zancen da Jibril ya bijiro da shi cewar baya son a yi masa taso sosai gurin daurin auren domin ba kowa yake son a sanarwa ba. 2

Bayan sun gama Jibril ya raka Abbah da babban yayansu da kuma abokin Babansu da Kannen mahaifinsa airport suka hau Jirgin Abuja, shi kuma ya dawo gida.

Tun daga ranar Jibril ya fara shirye shirye, a bokansa na baya da baya ja a jikin saboda abotarsa da Siraj yanzu kan ya zubar da wannan halin yaja kowa a jikinsa, sai dai be yarda ya yi amini a cikinsu ba domin a yanzu ya wayance da duniya.

NAWWARA POV.

Tun da aka saka lokacin Inna ta cigaba da shirye shiryenta kamar yadda ta fara, babu yadda Jidda ba tayi ba akan na je gurin gyaran jiki amman na ki, duk wani shirye shiryen da amarya take idan an kusa aurenta ni ban yi ba, ban da rama da baki ma babu abunda na yi, ranar da step mother dinsa da yayanta da wasu familyn Jibril suka kawo lefe ma na sha kuka sosai, basu karbi komai ba, ni ban ma san za a kawo lefen ba dan tun lokacin da aka saka mana rana ban taba daga waya na kira Jibril ba, shi ma kuma be kirani ba ko gaisawar da yake da Noor sai ya daina. Idan har zai yi wata magana da ta shafi auren sai dai ya kira Baba Sulaiman, idan kuma ya bukaci ganin Noor sai ya aiko da direbansa ya daukeshi a akai masa shi.

STORY CONTINUES BELOW

Bilal kuma ban sake saka shi a idona ba, duk da ba fita na ke ba tun lokacin da aka saka min rana, Mama Turai ce take zuwa tana bani shike-shike na itatuwa da wasu abubuwa wasu na kan sha saboda fadan da take min, wasu kuma da na kafaici idonta sai na zubar. Ni dai bana shirin komai duk wani shiri daya danganci auren Inna ce take yi tare da Sakina da Jidda sai kuma yan uwnata da kuma yan Babban gida.

Ina jin yadda suke shirya za su yi walima ni dai Uffan ban ce musu ba, a nan naji cewar Jibril ya ce ranar da aka daura auren zan tare, ji na yi kamar na rabe biyu saboda bakinciki. Kallo daya zaka min ka fahimci cewar bana son auren. Ana sauran kwana uku a daura auren familyn Jibril suka kawo danyin abinci kama daga shinkafa da duk wani abu da za a sarrafa a ranar bikin, sannan suka bada kudi mai yawa na hidima. Cikin kudin ne Inna ta diba ta gyara gidan aka cike inda duk da fashe aka shafe gidan sam kai bama ka ce gidan mu ba ne.

Yau ta kama Assabar ranar da aka saka dauren aurena da Bilal, yau na tashi cikin damuwa da tunani, tun bakwai da rabi na safe Bilal ya turo min sakon da ya hanani sukuni.

_I love you so much Nawwara, na yi abunda na yi ne saboda ki samu farinciki, ni san Mama ba zata taba bari ki samu farinciki a gidana ba ina miki fatar alheri_ 3

Ina gama karanta sakon hawaye suka wanke min fuska, wani abu marar dadi ya zo ya tsaya min a zuciya.
Karfe Goma dai dai na safe aka daura aurena da Jibril, a lokacin ne na fara kuka kamar an min mutuwa a ranar sai da na fita ran kowa daga Inna har yan uwan babana da yan’uwanta duk suka kasa fahimtata, Mama turai ce ta yi min fada sosai hakan yasa na daina kukan na koma yin na zuci.

Da hudu na yamma aka yi walima a a Women development center, walimar da ta bawa kowa da mamaki saboda kayan da aka rana, ko da yake wasu sun riga sun ji cewar mai kudi zan aura, daman na san wasu gulma ce ta kaisu domin ni bana shiga mutane balle kuma biki amman aka taro sosai ga yan uwan Su Jibril suka yi nasu takeaway daban suka rabawa mutane. Malama Aisha ta yi nasiha sosai akan zamankewar aure da kuma hakuri da tsabta nidai duk abunda take fadi jinta kawai na ke dan ban shirya yi ma Jibril ko daya ba.

Misali takwas na dare ya aiko da motoci daukar amarya motocin har sun yi yawa, Jidda ce ta cilasta ni ta yi min kwalliya ba dan na so ba, ta dauko min wata farar farar atamfa na saka, bayan na saka Inners farare sannan na saka fararen takalmi da farin gyale, Inna na min nasiha tana kuka kamar yadda nima na ke yi, sai aka wuce da ni babban gida su Baba Sulaiman da Yakunbo suka min tasu nasihar sai aka saka ni a mota ina ji ina gani aka dauki hanyar Sama road da ni. Na yi zaton gidan kai tsaye za a wuce da ni ganin ni bazarawa ce amman sai da aka biya wani babban gida inda yan uwan Jibril suka sauka aka kaini gurin Step mother dinsa da wasu kanen mahaifiyarsa da gwaggonsa suka min nasiha sannan aka sake sani a mota. Ba mu yi tafiya mai nisa ba muka isa wani katon gida mai farin fentin da gate golden color, ko ina na gidan haskene kamar da rana.
Ana fitowa da ni daga mota na done kaina kasa ban sake dagawa ba har aka shiga da ni bedroom din gidan, da kafar dama na shiga kuma tare da bismillah. A tsayar gadon na zauna fuskata a bude hawaye kawai na ke ganin hakan yasa Jidda ta ja min mayafina ta rufe min fuska, yan uwansa suna ta daukata hoto wasu kuma na ta kokarin ganin fuskata sai Jidda ta hana.

Bayan kamar minti arba’in Jibril ya shigo tare da abokansa sai zolayarsa suke, a gafe gado ya zauna, sannan wasu daga cikin abokansa suka shiga yi mana nasiha daga karshe suka rufe da addu’a. Ina jin lokacin da suka fita tare da nawa yan uwan da kuma Jidda, suka bar mu mu kadai a cikin dakin. Mun kusa minti talatin daga ni har shi babu wanda ya ce da wani uffan, baka jin komai sai shesshekar kukana.
A hankali na ji ya kai hannunsa ya yaye mayafina ya dago fuskata, hawaye yake kamar yadda nima na ke yi.

“Ki yi hakuri Nawwara na san ba ni kike so ba, na san na yi miki kutsu a rayuwarki, amman ina da tabbaci zaki auri Bilal nan da wani dan lokaci kadan, da shi zaki yi rayuwa dawwamamma irin wacce kike so”

STORY CONTINUES BELOW

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya cigaba.

“Ada na yi tunanin idan an aureki zan kasance a cikin farinciki, amman wannan hawayen da na gani a idonki ya sani jin babu dadi kuma ya sani jin nadamar cilasta miki aurena”

“Ba zan taba son ka ba Jibril, ka rabani da komai nawa, idan har kana da kunya a idonka ba zaka taba kai hannunka ka taba jikina ba, jikin macen da ka hada hotonta da wani ka ce karuwa ce mai neman maza da aurenta, ka rabani da mutumen da yake so tsakani da Allah saboda kawai ka samu farinciki, to bari na fada maka, ka kara matsowa da mutuwarka da bakinciki da damuwa da nadama a kusa da kai” 22

Na fada ciki kuka. Sai ya yi saurin dauke kansa ya sauke wani numfashi da alama maganata bata masa dadi ba. Tashi ya yi tsaye ya cire Babbar rigarsa ya aje.

“Taso mu yi sallah”

Ya fada cikin muryar da ke nuna rashin jindadin da ke cikin ransa. Ban masa musu ba a nan na sauko saman gadon sai ya wuce gaba ya nuna min inda bandaki yake ya bude min, na shiga ciki na yi alwala ko da na fito ya shinfida carpet da alama shi da alwalar ya shigo.
Wardrobe ya bude ya dauko Hijabi ya miko min na saka sannan ya yi gaba ni kuma ina baya ya kabbatar sallah nafila.
Bayan mun gama ya yi addu’a nima na yi tawa addu’ar sai juyo ya rika goshina ya soma karanta addu’ar da annabi ya koyar da mu wacce miji yake rika goshin matarsa ya karanta saboda niman tsarin da zaman lafiya.

اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ

Allaahumma ‘innee ‘as’aluka khayrahaa wa khayra
majabaltahaa ‘alayhi wa ‘a’oothu bika min sharrihaa wa sharri maajabaltahaa ‘alayhi.

Na yi mamakin jin wannan addu’ar daga bakin Jibril lallai ba da wasa ya riki karatun qur’ane ba tun da har ya iya maida hankali ga yin addu’o’i ma. Bayan ya gama ya tashi ya dauko manyan ledoji ya aje a gabana tare da plate da cups. Ni kuma na mike tsaye na nufi hanyar da aka shigo da ni wato falo.

“Zo ki ci abinci mana”

“Bana jin yunwa”

Ita ce kawai amsar da na bashi na nufo falo na zauna, sai kuma na kasa yin kukan da na fito yi, haka na zauna a saman manyan kujerun alfamar ina ta kallon yadda aka tsara falon, ba dan ina ganin sha’awa ba sai dan na rasa abun yi zuciyata cike da tunanin Bilal. Har sha biyu ina zaune falon ni kadai kuma Jibril be fito ba. Jin na yi na tsallawa da kayan dake jikina kasancewar atamfar ta matseni sosai hakan yasa na tashi na koma dakin dan dauka wasu tufafin domin Jidda ta fada min inda ta aje min kayan da zan canja idan zan kwanta.

Aabunda na tarar ya tashi hankalina sosai, Jibril ne kwance kamar matacce ga jini nan gefensa da alama amai ya yi. A firgice na kai hannu na taba shi amman be motsa ba.

“Na shiga uku Jibril Jibril Jibril” 1

Shiru be amsa ba balle ya motsa, tun ina girgizashi kadan har na fara yi da karfi ina kuka, hannu na kai daidai hancinsa sai na ji baya numfashi hakan yasa ni fasa ihu na fito a firgice falo ban san lokacin da na fito harabar gidan ina ihu ba. Ban san da akwai mai gadi ba har sai da ya taso ya nufoni yana tambayar lafiya. 7

“Jibril ne ya suma ya ya ya mutu”

Na fada cikin Matsainancin kuka da tashin hankali. Tare muka dawo dakin da shi babu abunda ke fita bakinsa sai Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, yana girgiza Jibril tare da fadin

“Mai gida Mai gida”

Amman Jibril be motsa ba.

“Mi ya same shi”

Ya tambaya yana cigaba da girgiza shi cikin tashin hankali na ce

“Wallahi ban sani ba, ni ma ina falo ko da na shigo na ganshi haka”

Wayarsa ya ciro ya kira wani wanda ban san ko wanene ba, cikin kankanen lokaci mutumen ya iso a nan na gane direban da Jibril yake aikawa a gidanmu ne. Tare da taimakonsa suka saka Jibril a mota nima na shiga muka dauki hanyar asibitin One On One Special Hospital.
Muna isa aka karbeshi aka shiga dashi wani dakin suka shiga bashi taimakon gaggawa, sai direban ya dawo yana cewa na kira iyayensa na fada musu.

“Babu waya hannuna tana hannun Mamana”

“To ki kira line sai ki sanar musu idan kina da number a kai”

Ya fada yana mika min wayarsa. Cikin hanzari na karba na saka numberta na kira, sai da tayi ta ringing har ta katse na sake kira sai a na uku Inna ta dauka cikin muryar bachi.

“Assalamu Alaikum”

“Inna Nawwara ce ni ce, muna asibiti Jibril ba lafiya ya suma ko ya mutu”

“Wani abun kika masa ko?”

Na yi shiru na kasa amsawa sai kuka nake.

“To kin kyauta, kuma bari kiji na fada miki ko mutuwa ya yi karki kuskura ki dawo inda na ke, ki nemi wata uwar can ba ni ba fitsararriyar yarinya” 8

Tana fadar hakan ta kashe wayar. Sai na mika masa ina kuka kamar zan hadiye zuciya na mutu.

“Ki kira mahaifinsa ki fada masa”

Kuka da nake ya hanani fadin bani da numbersa numfashina har gargada yake. Shi da kasan ya kira Abbah ya fada masa, kusan a tare suka iso da Inna da wasu yan uwan Inna.

“Miya sameshi”

Shine abunda mahaifin Nawwara yake ta tambaya, ni kuma na kasa magana saboda kuka, Inna kan ban da hararata babu abunda take. Bayan likitoci sun gama bincikensu daya daga cikinsu ya zo yana ma Abbah bayanin cewar Jibril yana da heart attack kuma da alama an bata masa rai ne shiyasa wannan dogon suma.

“Zuciyarsa ta buga a yanzu, kuma an barshi ya dade ba a kawo shi asibiti ba, ban da Allah ya masa tsawon rai da yanzu ya mutu, da alama an bata masa rai ne ko kuma be samu wani abu da yake so ba ko ya rasa wani abu, so shawarar da zan baku ku yi kokarin kawarda duk wani abu da zai bata masa rai saboda in ta sake bugawa gaskiya zaku rasa shi yanzu ma sa’a ce kawai da kuma rabon shan ruwa a gaba”

“Mun gode likita zamu kiyaye”

Shine abunda Abbah ya fada, kallo daya ya yi min ya dauke kansa, ya nufi dakin da Jibril ya ke ya shiga, har su Inna suka shiga aka barni nan ni kadai tsaye kamar marar gata. Su Inna ne suka fara fitowa ban san ko karfe nawa a wannan lokacin amman tabbas dare ya yi sosai amman hakan be hana Inna da yan’uwanta bin daren au koma gida ba. Bayan Abbah da yayan Jibril sun fito tare da wasu yan uwansa mata na shiga, sai na tararda wasu yan uwansa a cikin dakin, sai dai ina shiga duk suka fita waje aka bar ni ni kadai.

Zaunawa na yi saman kujerar dake kusa da gadon ina hawaye, sai na dora kaina saman gadon da yake kwance ina kallon fuskarsa. Oxygen ne a bakinsa sensor na nuna yadda numfashinsa ke tafiya, tausayinsa ne ya fara kamani da kuma tausayin kaina a lokaci daya…
Ina biyu aka yi sallah asuba, sai na shiga bandakin da ke dakin na yi alwala da na fito sai na shimfida dankwalina already ina da Hijabi a jikina wanda na yi sallah da shi a daren jiya, sai kawai na kabbatar sallah. Dukanin addu’a ta ta nemawa Jibril lafiya, na tsorata sosai da yanayinsa ina tsoron na zama ajalinsa gashi mahaifiyata ta soma fushi da ni mahaifinsa kuma ba zai taba yafe min ba, duniyarta zata sake rikice har ma ta fi ta baya.

Idan har ban yi hakuri zama da Jibril ba duk abunda ya same shi a yanxu ni za a zarga, kuma nasan Bilal ba zai aureni a yanxu ba, ko da kuwa na kashe auren ne na fito. Saboda bakin jinina kowa ni zai dorawa laifi, addu’ah nake hawaye suna min xuba, mafita kawai na ke nema a gurin Ubangijina, ina rokon ya sassauta min zuciyata ya bani ikon mantawa da komai. Bayan na gama na dawo saman kujera na zauna ina ta kallon fuskarsa tashin hankali da zullumi cike a zuciyata. Misalin bakwai da rabi Mahaifinsa ya shigo ina ganinsa na sauka daga kan kujerar na duka har kasa na gaisheshi amman abun mamaki sai ya ki kallon inda na ke balle ma ya amsawa. Ban tashi daga duken da nake ba likita ya shigo ya kara duba jikinsa ya yi musu bayanin cewar jikinsa da sauki kuma zai farka nan da wasu yan awoyi.
Likitan na fita sai Step mother din Jibril ta shigo tare da wasu yan uwansa, su kan da na gaishesu sun amsa min har ma suka tambayeni mai jiki na ce da sauki. 2

“Hajiya kuje waje likita ya ce a barshi ya samu isasshen bachi, kuma akwai maganar da nake son mu yi da matarsa”

Shine Abbah ya fada abunda ya fadarmin da gaba, ba musu suka fice suna Allah ya sauwake, bayan fitarsu Abbah ya kalleni irin kallon nan na tsana ya ce.

“Bari kiji na fada miki duk da na ya mutu sanadiyarki kema sai kin mutu, ko wane ango aka kai masa amarya farinciki yake yana zumudi balle ma Jibril da yake jin kamar ya hadiyeki, amman daren da aka kai shi daren aka kwasoshi zuwa asibiti yan biki ko watsewa ba su yi ba, Wace irin macece ke wani irin kallo kike so duniya ta miki? Jaruma ko jajirtacciya? Duniya zata miki kallo wawuya ne marar hankali wacce ilmimta be amfaneta da komai ba.
Da kin san irin son da da na yake miki da ko ko da baki bari ya taba shi ba balle har ki bata masa rai, ban taba sanin cewar dana yana da heart attack ba sai yau, kuma na san saboda ke ne, idan kika kashe Jibril da wane ido zaki kalli Noor? Anya Nawwara akwai imani a zuciyarki kuwa?” 8

Zubewa na yi kasan guiwoyina ina kukan da ban san ta ina yake fito min, kukan da ya hanani cewa komai har su Inna suka shigo sai Abbah ya juya ya fita bayan ya gaisa da su. Inna kamar jira take ya fita sai ta hau ni da masifa ranta a bace

“Karkar kuka kike Nawwara, da kukan jini zaki yi, ba sakike kike so ba? Bari Allah ya bashi lafiya zan sa ya sakeki kije ki auri Bilal din mahaifiyarsa ta yi ta gasa miki garwashi a hannu ba ma gida ba, mutumiyar banza marar hankali wannan hakin naki ba haline na mutanen kirki ba, kuma duk mai irin rayuwarki ba zai taba jindadin zama duniya ba, ke baki ma Allah laifi ya yafe miki ne ko ke kin fi uban kowa ne, Jahila kawai ilminki ba shi da amfani Nawwara kin yi hasara jindadin zama da mutane indai haka zaki cigaba da rayuwa” 7

Babu bakar maganar da Inna bata fada min ba, ita da Mama Turai mutuwa ce kawai ban yi a gurin saboda kuka, amman har numfashina kokarin fita ya rikayi. Hakan be sa Inna ta tausaya min ba sai ma haushina da take ina kokarin rike mata zane ta buge min hannu ta fice a fusace, babu wanda ya tsaya ya saurari ni. Kuka na yi a gurin har sai da na gode Allah sannan na tashi na koma saman kujerar na zauna ba dan hawaye sun daina min zuba ba. Wata yar uwar Jibril ce ta shigo da kayan abinci ta aje sai ta dafani

“Adda Nawwara ki yi hakuri Yaya zai tashi Insha-Allah”

Uffan ban ce mata ba har ta fice, sai na maida kaina na kwantar jikin gadon na lumshe ido kaina na mugun ciwo kamar zai tsage.

JIBRIL POV.

Misalin goma da rabi na safe ya bude idonsa, ya dade yana gani dishi² sannan ya soma gani dai dai har ya gane asibiti aka kawo shi. A hankali ya maida dubansa gurin Nawwara da kanta ke kwance saman gadon idanuwanta a lumshe da alama bachi take amman sai shesshekar kuka take. Hannu ya kai ya shafa saman kanta, ya lumshe ido. Sai kuma ya kai dayan hannunsa ya cire oxygen din da ke bakinsa ya unkura cike da karfi hali ya tashi zaune, yana jin zuciyarsa kamar zata rabe biyu.
Hakan ne ya farkarda Nawwara daga bachin da take suna hada ido sai taga abun kamar mafarki saurin mikewa tsaye ta yi sai ta rumgume shi tsabar jindadin ya farka be mutu ba, sai ta fashe da kuka.

“Ka yi hakuri Jibril ba zan sake ba, ban zata abun ya kai har haka ba” 7

Rumgumeta ya yi tsantsan a kirjinta ya lumshe ido, rabon da yaji irin wannan sukunin da sakewa har ya manta, a take ya ji sanyi a zuciyarsa har wani kuzari yana rabarsa. Saurin sakinsa ta yi tana share hawayenta.

“Bari na kira likita”

Sai ya rike mata hannu ya bude ido a hankali yana kallonta da bakinsa da ya yi fari ya bushe.

“Doctor be da abunda zai min Nawwara, ki ce likita na komai za a min a duniyar nan ba zan warkeba matukar babu kulawarki da sonki a kusa da ni, babu ciwon da zai rabeni matukar kina kusa da ni, na san ba nine wanda kika so but please stay with me ko da na dan lokaci ne, i feel like rayuwata ba zata tsawaita da har zan hanaki jindadin rayuwarki ta nan gaba i need you”

Dawowa ta yi ta zauna bakin gadon da yake zaune, hannunta na cikin na shi fuskarta kuma na zubar da hawayen, dayan hannunta tasa ta jimke hannunsa a tsakiyar hannayenta.

“Har yanzu akwai son Jibril a zuciyarki, ki rantse min da Allah baki son Jibril, ba zan iya aurenki ba saboda zuciyarki Jibril take so ko da na aureki gangar jikin kawai na aura. Haka Bilal ya fada ranar ganina na karshe da shi saboda ya ga son ka a idanuwana, karya na ke na ce bana son ka Jibril kawai na kasa manta abunda ka yi min ne, amman yanzu komai ya wuce i promise you ba zan sake yin wani abun da zai tashi hankalinka ba” 5

Hawayene suka zubo masa hawayen da shi ma kansa be san na minene ba. Hannunsa ya dauka ya dora saman nata.

“Fada min wani abu Nawwara, ina jin kamar ba ke bace, wata kila saboda na kusa mutane ne kike so na yanzu” 4

“Daman can ina son ka nothing changed no one can take your place, da ace yau na rasa ba da na wayi gari cikin wata duniya mai rudani da rikitarwa, ban tabbatar da ina son ka ba sai da na ganka kwance a saman gadon nan, Jibril i love more than I did before” 12

Ido ya tsura mata yana ta kallonta, gaskiyar zancenta yake karanta a idanuwanta, kawai ya kasa yarda cewar Nawwara din ce, abunda ya dade yana jiran jin daga bakinta yau ya jishi. Hannunshi ta daga ta kai gefen kunci ta lumshe ido. 5

“Am sorry”

Ta furta cikin kuka. Sai ya matsa kusa da ita ya sumbaci goshinta ya sumbanci saman hancinta ya sumbanci lips dinta, sannan ya rumgumeta shima ya lumshe ido kamar yadda na ta idon suke a lumshe….Jihadin da na yi ba duk mace ba ce zata iya yinsa, zama da mutumen da ya nuna maka ba kaunarka, yanzu kuma ya dawo yana son ka kamar ya mutu.
Annabi ya yi gaskiya da ya ce mu yi so kadan kuma mu yi ki kadan domin wata rana masoyinka ya kan iya zama makiyinka ko kuma makiyinka ya zama masoyinka, har ga Allah ya yarda Jibril yana so na kuma i believe without me there is no Jibril. But for what Jibril did to me is unforgivable pain, hada hotona da hoton wani namiji shine abunda na ke gani a duk lokacin da na kalli fuskar mijina.
Ina cikin hada masa tea na ji hannayensa zagaye da kunkuruna ya dora fuskarsa saman wuyana yana goga min hancinsa a gefen fuskata. 2

“Karki wahalar da kanki gurin hada tea nan ba zan iya shan sa a yanxu ba”

Ya fada saitin kunnena kadan-kadan kamar mai rada.

“Saboda me?”

“Saboda ban wanke bakina ba kuma ban rama sallah da ake bina ba, kara ki bari kawai har muje gida”

“Fine zan je gida da kaina sai na dauko maka brush din da toothpaste”

Kokarin juyowa na ke amman sai ya ki bani dama saboda ya ji dadin yadda muke tsaye a haka.

“Kar wani ya tarar da mu a haka fa”

Ya sakeni sai na juyo na kalli fuskarsa yana murmushi sai ya dora hannayensa saman kafadata ya hade goshinsa da nawa.

“To miye a ciki haramun muka aikata?”

Har na bude baki na yi magana sai a turo kofar dakin aka shigo hakan yasa dukanmu muka tsargu ganin Abbah ne, bama kamar ni da nafi jin kunya, domin shi nuna yayi kamar be yi komai ba ya zauna saman gado yana gaisheshi.
Nima gaisuwar na mika masa ga mamakina sai ya amsa min sai dai fuskarsa babu yabo ba fallasa. Kofa na nufa da zimmar fice sai ya kirani hakan yasa na juyo ma dawo still kaina na kasa.

“Ki yi hakuri da abunda na fada miki, raina ne kawai ya bace amman dukan wani furuki da na yi agareki bana da nufin aikata ko daya kawai dai na ce ne dan an tsorota ki”

“Ba komai Abbah”

Na fada sai Jibril ya kalleni ya kalleshi

“Wani abun ne ya faru?”

“Lokacin da kake unconscious na fada mata masu Maganganun da basu da ce ba, saboda na yi tunanin ko da hannunta a abunda ya faru da kai ne”

“Aa ita ma bata san abunda ya same ni, domin na turata kitchen ta dauko plate kawai sai na ji jiri ya dibeni ban sake sani inda nake ba”

Abbah ya juyo ya kalleni.

“Amman Nawwara shine baki fada ba, kika kyale ina ta miki fada?”

“Ba lallai ne ka saurareni a lokacin ba, amman yanzu komai ya wuce, bari na je na dauko maka brush din”

Na karasa ina kallom Jibril sai ya kada min kai.

“Amman kisa direba ya kai ki karki hau Napep”

Da kai na amsa masa sannan na fice zuciyata cike da jindadi da kuma rashin jindadin da ban san na minene ba. Harabar asibitin na nufa inda aka faka motoci a nan na samu direansa da ban san sunansa ,bayan mun gaisa ya tambayani mai jiki sai na ce masa ya kai ni gida. Gida bayan na shiga shi kuma yana mazaunin direba kamar kullum.
  Ko da a muka isa gida wato sama road ina hawayen da bansan na minene ba. Bayan ya faka motar na bude na fito ina share hawayena na nan na samu damar kallon wani bangare na gida, irin tsarin nan na manyan masu kudi gurin faka motoci an kawata ko kna da furanni masu kyau da daukar hankali.  Babbar kofar shiga falon kuma tana da stairs biyar an kawata gefen karfen stairs din da furani kamar gidanjen turawa ko kuma na ce na indiya. 
  Ina shiga na samu falo kamar yadda na barshi, sai dai komai na falo fari kamar fentin gidan, ya kawata falon da hotuna na da na Noor sai kuma na Abbah da na Mahaifiyarsa, amman babu nasa ko daya. Lokacin da na shiga bedroom sai na manta da abunda ya kawo ni gidan kawai na hau gyara dakin saboda ya bace da jinin da Jibril ya amayar jiya da dare.

STORY CONTINUES BELOW

“Allah ka bani ikon jure komai”

Ya roka yayinda na ke dauke kazar jiya da har ta soma yauki, bayan na gyara ko ina na shiga bandaki na hada ruwa na yi wanka, sannan na fito na shafa mai na dauki atamfa maroon color na saka, gaban madubi ya zo na tsaya ina kallon kaina kitson da aka min ya kwanta a kaina sosai gashina ya yi baki kuma ya sauko har gadon bayana. Kamar a mafarki na hango mutum ta cikin madubi ya doso inda yake fuskarsa dauke da murmushi, saurin juyowa na yi na kalleshi.

“Ya aka yi ka zo”

“Baki ji mota ba?”

Ya fada yana muna min window.

“Sam ban ji ba”

“Hankalinki yana iya?”

“Yana can asibiti gurin mijina”

Goshinsa ya hade da nawa ya kama hannuna na dama ya shinsshina ya lumshe ido.

“Ya akayi aka barka ka fito? Na san dai babu likitan da zai sallami mai jiyanci irin a yau din na asibitin bayan kuma jiya da dare aka kai ka”

Be amsa min ba sai na ji kafarsa saman tawa yana goga min ita a hankali.

“Su Momi suna waje suna jiranki”

Ya furta sai ya sakeni ya yi baya baya yana murmushi har ya isa bandaki, sannan ya bude ya shiga. Ajiyar zuciya na sauke a hankali sannan na dauki mayafi na ya rufe kaina na nufi falo.

JIBRIL POV.

Zaune yake ruwan shower na dukan kansa, sai dai hakan be hana hawaye zubo masa ba, kuka yake kukan da be san na minene ba farincikin dawowar Nawwara a duniyarsa ko kuma bakincikin kwanakin da yake ji a jikinsa su suka rage masa, wanda hakam ba zai ba shi damar rayuwa irin wacce yake so a tare da ita mai tsowo ba? 1

Bayan na gama wanka yaje gaban madubi ya wanke bakinsa sai ya bude cabinet ya dauko maganinsa ya sha, sannan ya juya ya fito daga bathroom din. A gaggauce ya shirya cikin farin yadi marar nauyi sannan na fashe jikinsa da turare ya fito falo. Hajiya ya samu wato Step Mother dinsa tare da sisters dinsa a zaune suna ta fira da Nawwara sama sama. 
  A ranar wuni suka yi baki daga masu zuwa ganin amarya wandanda  ba su san an kwantar da Jibril asibiti ba, sai masu zuwa diba shi idan sun je asibiti ace musu ya dawo gida. Abbah dai tun asibiti suka yi sallama da shi Hajiya ce kawai ta jira taga jikinnasa kamin ita ta kama hanyar abuja gobe.

NAWWARA POV.

Sai kusan isha’i sannan kowa ya watse, muka shiga gyara gidan ni da Jidda da Sakina, sai da muka gyara ko ina muka masa tas sannan muka kunna turaren wuta gidan ya dauki kamshi.

“Gaskiya Nawwara kin da ce, ga mijinki yana son ki duk abunda kike so shi zai miki, yan uwansa ma ba baya ba suma na ga suna son ki”

Ta fada tana karewa falon kallo. Ni kuma na yi murmushi na ce

“Ni ko kin ga duk wannan dukiyar bata gabana, na rasa dalilin da zai sani na ji dadin zama a gidan nan”

“Aiko kara ki fara ji tun yanzu, domin wanda kike takama da shi ya yi aure rana daya da ke”

“What? me kike nufi”

“An daurawa Bilal aure da wata yar’uwarsa, Mamansa ta ce ba za a daga ranar ba tun da kowa ya san an saka rana kara kawai ya auri yar’uwarsa wata yarinya ce da ake riko a gidan”

Na ji babu dadi, dan nasan ba dan yana son ta ne ya aureta ba sai dan kawai mahaifiyarsa ta cilas masa.

“Hakika ta yi dacen miji mai kawaici da sanin ya kamata, miji mai gudun kukan matarsa mai son duk wani abu da zai faranta rai”

STORY CONTINUES BELOW

“Kuma ba ki ganta ba, ta ninka ki kyau sau ashiri”

“Ina ruwana”

Na fada ina harararta, ita kuma ta sa min dariya, sai da Jibril ya dawo sannan suka fice suka barmi cikin rashin dadin rai. Ina ta kokarin kawai da abunda yake zuciyata gudun kar Jibril ya zarge ni ko kuma damuwata ta saka masa damuwa, iya inda far’ata take na yi kokarin nemota na yabama fuskata. Bayan na fito wanka na hada masa nasa ruwan na fito daure da tawul da kuma Hijab a jikina. Tun da na fito daga bathroom din ya sakarmin ido yana ta kallona har na zauna bakin gado kamar yau ya fara ganina. Hakan yasa na soma tsarguwa.

“Ga ruwan wanka can na hada maka”

Murmushi ya yi sai ya bar jikin kofar dakin da yake tsaye ya nufoni ya zauna daf da ni ya kawo fuskarsa kusa da tawa har muna iya juyo mumfashin juna. Jin bakinsa daf da nawa yasa na runtse idona na dauki numfashi ina sauraren yadda yake watsa da yatsansa a gefen fuskata.

“I love you”

Ya furta muryarsa can ciki kamar marar kuzari, ji nayi yana huramin iska kamshin sweet candy a hankali daga saman goshina zuwa bakina. Lokaci daya na daina jin iska hakan yasa na bude ido sai na gashi tsaye yana kallona fuskarsa da murmushi. Hannayensa yasa ya tasheni tsaye ya rumgumeni tsantsan a kirjinsa.

“Ina son ki sosai Nawwara”

Ya furta yana kokarin ciremin Hijab din da ke jikina, ni ko gabana sai faduwa yake, hannuna ya rika ya dora saitin zuciyarsa, wani irin bugawa na ji zuciyarsa na yi da karfi har sai dai na tsorata, Dagowa na yi na kalleshi sai ya sauke idonshin cikin nawa yana min wani kallo mai wuyar fassara, hannunsa ya kai ya kama fuskata ya soma sumbantar bakina. Kasa kasa na ke saboda na kwaci kaina shi kuma sai biyoni yake hakan yasa muka fada saman gadon a tare. Dariya ya soma yi kamar yadda nima na ke dariyar, kunya tasa na yi saurin juyowa na kife fuskata cikin Bedsheet, sai ya dora kansa a bayana yasa yatsansa yana wasa da wuya. Sai da ya sumbanci kunnena sannan ya tashi daga bayana da dora kansa.

“Babe-Naj gaskiya wankan nan tare ya kamata mu yi shi”

Ya fada yana kokarin jan tawul din da nake daure da shi, hakan yasa na yi saurin sauka saman gado ina zare ido.

“Na fa yi nawa wanka kuma ka gani”

“Gaskiya ban gani ba”

Ya dosoni gadan-gadan hakan yasa na haye gado na koma can karshe ina ta kokarin rike tawul din dake son subucewa daga jikina.

“Ki sauko nan kawai Hajiyata”

“Aa gaskiya haka kawai na yi abuna kuma ka ce sai na sake wani”

Na fada ina turo baki, sai ya yi dariya.

“Fine”

Kokarin hawan gadon yake ni kuma na sa masa ihu.

“Tsaya tsaya zan sauko, amman Wallahi na yi wankan kwarai”

Tsayawa ya yi na sauko da kaina fuskata kamar na fasa kuka ina daga masa na ce.

“Dan Allah karka cilasta min wanka tare da kai Wallahi na yi wanka na kwarai”

Kyaleni ya yi har ya juya sai kuma ya juyo da sauri ya janye tawul din dake jikina, rudewa na yi na rumgume shi ina kokarin fashewa da kuka. Shi kuma sai ya fashe da dariya ya duka ya dauko tawul din ya daura min.

“Yi hakuri”

Kuka na ke da gaske har da hawaye domin na ji haushi kuma na ji kunya sosai musamman rumgumar da na masa. Sai ya nufi bathroom yana ta kyalkyatar dariyar mugunta kamar ba shi ba, ni ma har na soma dariyar kaina. 
Sai da ya shiga bandakin ni kuma na je na kulleshi daga waje.

“Sai ka fadi wanda ya aikeka ka yi min haka nan ko kuma ka kwana a bandakin nan”

“Yi hakuri idan na fito sai ki rama”

“Ni ba zan rama ta yadda ka yi min ba, sai dai ta wannan hanyar”

“Ashe ke matsoraciya ce ma, karki yarda na fito sai na miki abunda ya fi wannan yarinya”

“Waye yarinya?”

“Ke mana, kin san da auren kauye aka min da yanzu na haifeki”

“Sannu Baba”

Na fada ina dariya, da gangan na ki bude shi har na shirya cikin kayan bachi na nufi falo inda ya aje ledodin da ya shigo da su dazu. Zaunawa na yi a dinning din na ci abincina sai da na koshi sannan na bude freezer na dauko ruwa na sha.

“Al-hamdulillah”

Na furta ina mamakin yadda na soma sakewa a gidan kamar ba ni ba, ina kokarin maida ruwan na ji hannayensa kan kwankwasona, ba shiri na saki goran ruwan ya juyo da sauri ina ihu.

“Ya aka yi ka fito”

“Aljanine ni, waya ce ki ci amin abinci”

Shi ma kayan bachi ne a jikinsa irin kalar nawa sai dai na shi na maza ne nawa na mata. Hannayensa yasa ya daukeni kamar wata yar baby, ni kuma na dora hannayena saman wuyansa.

“Mrs baki da kunya, jiya fa aka kawo ki gidan nan amman har sakin tawul kike gabana”

Na yi saurin boye fuskata kirjinsa ina dariya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *