RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 4 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA 2/4
Mun tsaya
Daga nan sai aka ce Ango ya zo ya ba matanshi abin sha ko naci. ‘Yammata masu sanye da kaya iri daya su uku, su ne suka zo suka kawo wani dan tire. a rufe, daya da ‘yan kofuna guda uku, dayar kuma da hankici na share baki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta bude dan tire din, nakiya ce guda uku, ya dauki daya ya ba Aliya ta gutsura, aka yi tafi gami da rangada guda.
Mai kofunan ta matso, ya dauka madarar shanu ce wadda ba a jima da tatsowa ba, ya kurba mata, sannan me hankici ta kawo ya dauka ya share mata. Duk su ukun hakan ya yi musu.
Shima haka aka umarce su su ba shi daya ta bashi nama, daya ta ba shi ruwa, daya ta ba shi tataccen ‘ya’yan itatuwa.
Tsarin bikin ya birge mutane sosai, daga nan aka shiga daukar hotuna. Tsakiyar Aliya da Amna ya zauna, sannan ya rungumo su duka. Ya sake dawowa tsakiyar Amna da Nafisa, ya sake rungumo su. Sannan yayi da kowacce rungume da ita. Daga nan kuma aka shiga ci da sha na abinci. Ana cikin haka sai ga gara tazo daga gidan su
Nafisa mota guda, kayan abinci da kuloli, da
zannuwa, da shaddoji.
Sai ga ta Amna ta linka ta Nafisa sau biyu, aka ce wannan ta iyaye ce, ta Ango an kai can gidan shi. Aliya ta rude, nan ta dauki wayarta ta yi wa Aisha kawarta text cewa taje gidan su ta ce a kawo garar nan, a basu duka har nata din. Can kuma sai ga shi an kawo, haka aka dire gara
kashi uku. Salma ta sake yiwa Allah godiya da
wannan rufin asiri da ya yi mata, ta ma daina jin
haushin Hajiyar
Karfe hudu biki ya tashi, aka ce da an yi sallah za’a kai Amare gidansu. Nan kowace Amarya ta koma gurinta don kimtsawa.
Salma ma ta tashi da gudu don komawa samanta, wani abin mamaki har karo suka yi da Hajiyar a
Halima Abdullahi K/Mashi
kofar falo, cikin sa’a bata gane ta ba, sai ta ce “Wannan ‘yar waye haka ki ke gudu, tafi a hankali mana.
Salma dama bata waiwayo ba, sai ta tafi saf-saf ta haye sama ta fada kan gado.
Ko minti shida bata yi da shigowa ba, taji an turo kofar, a zatonta Badi’atu ce, don haka ta taso da ‘yar fara arta zata bata labarin karonsu da Hajiya, kawai sai taga Angonsu.
Ta sauko cikin tsoro ta ce, “Don Allah Yaya ka fita, kar Hajiya tazo ta sake marinka.” Ya juya ya murda makulli, sannan ya dawo cikin tausayi. Ya ce, “Kiyi hakuri da zaman wuri daya, yanzun za ki fito, don yanzun za a kai ku.”
Tayi murmushi, “Ai na fito. Badi’atu ta ce in fito
in yi kallo. Naga kun yi kyau sosai da matanka.”
Kalamanta suka sa tausayinta ya sake tsirga mishi. Ya ce, “Dama kina kallon mu shi ne ba ki zo .gurinmu ba?” Ta ce, “Tab! In zo in ɓata muku
abinku! Hajiya ma zata yi fada.” Yayi shiru yana kallonta. Ta ce, “Kun yi kyau da
ku ka dauki hoton nan, ashe gaske ne mu hudu ne? To a cikin su wa ka fi so?”
Yayi ‘yar dariya, “Ke barda ke?” Ta ce, “Ai ni na sani ka tausaya min ne ba na cikin su.” Ya ce, “Ni
Www.bankinhausanovels.com.ng
dai kina cikinsu kuma nafi son duk wadda ta fi sona.
Ta ce, “To wa ce ta fi sonka a ciki?” Ya ce, “Ban sani ba tukunna sai mun zauna.” Ya ciro wayarshi, “Kema ki zo mu dauka.” Ya zauna a kan kujera, bata ankara ba sai taji ya kamo ta ya dora a kan cinyarsa.
Ya rungumota ya daga waya yana daukarsu. Wani abu take ji yana ratsa mata jiki, ta yunkura zata tashi, ya ce “Ki tsaya mu kara daya.” Ta ce, “Ya yi haka?” Ya yi dariya “To mu dauka a tsaye.” Ya sake kwantowa ta bayanta, ya matseta a jikinshi ya dauke su.
Wayar ta shiga ruri ya daga tare da fadin “Munnir ya ce kazo mana mun fa idar da sallah.” Ya ce, “To bari ni in yi tawa in fito.” Ya shiga bandaki yayo alwala, a nan yayi sallah.
Ya ce ta shirya. Ta ce, “Kayanta ne kawai da ta
cire.” Ya bata wata leda ya ce ta sa a ciki. Ya fita ya
bar ta tana sallah.
Amna su ne suka fara tafiya saboda da motocinsu a hannu. Duk an kwashe Amaren saura Salma a sama. Shatima ya kira Anty Momiyo ya ce, “Ki ce ma Hajiya don Allah Salma a sama wai ga motar daukanta.”
Halima Abdullahi k/Mashi
Momiyo ta ce, “Tab! Ni na ma manta da ita, to ta ci abinci ko?” Ya ce, “Ban sani ba Anty, in kun yi ki sa ai kayi bayani.”
Da sauri ta nufi gurin Hajiya, tana fadin “Hajiya
‘yar mutane a sama. Sai da Shatima ya ce a fito da
ita sannan na tuna ko abinci bata ci ba.”
Hajiya taja tsaki, “Nasan ba zai barta haka ba. Da zai ce a fito da ita wa zai fito masa da ita? Sauran ba danginsu ne suka fito da su ba! Ta sauko su wuce.”
Hajiya Saliha ta ce, “Yanzun dai kin hana ayi wa yarinyar nan budar kai?” Hajiya ta ce, “Ai har abin da ya fi budar kai ita ya yi mata, domin jiya har biyun dare yana dakin.” Nan suka dauki salati, ita kuma ta nufi dakinta tana fadin “Ba ni da lokacin su.”
Anty Momiyo da kanta ta hau sama, samu Salma tana zaune a kan abin sallah. Ta ce, “Au! Har da kaya ki ka canza? To taso ku je, kin ci abinci ko?”
Salma ta ce, “Eh naci, domin na sakko kallo, da ana ba mutane nima aka bani na ci.” Anty Momiyo ta kalli Salma, “Lallai wannan yarinya ce, komai nata a kuruciya. Ji yanda take magana, iyakar gaskiyarta kawai take fada.
Shatima yana tsaye Salma ta shiga bayan sabuwar motarshi, har ma sai da tayi mishi
Www.bankinhausanovels.com.ng
murmushi. Ya zo bakin kofar, “Ke kadai ce ko za a bi ta gidanku a dauki wasu?”
Ta ce, “A’a, ai ina zaton fa duk suna Kaduna din gurin jere.” Ya ce, “Ina zuwa.” Ya shiga cikin gida ya kira Badi’atu ta fito. Ya ce, “Ke ba za ki ba ne?” Ta ce, “Zan je tare da su Anty Momiyo zamu je, in an tashi Dinner kuma mu dawo.”
Ya ce, “Dinner da za’a tashi sha biyun dare, karfe tara za’a fara. Sai dai ku kwana. To ki zo ku zauna da Salma kuje tare, don Allah ki taimaka mata gurin kwalliya, don har da ita a dinner tunda wannan na abokaina ne.”
Badi’atu ta ce, “To bari in kwaso kayan da zan yi amfani da su.” Shima ya koma gurin Salma ya ce, “Ina kayan da na ce ki dinka su za ki sa a Dinner?”
Ta ce, “An dinka suna gidan mu.” Ya daga waya ya kira Auwal ya ce, “Ka amso min kayan Salma yanzun ka kawo min gidanmu.” Auwal ya ce, “Ai an tafi da Akwatunanta duka can Kaduna din.” Shatima ya ce, “Yauwa, hakan yayi.” Badi’atu tana fitowa suka kama hanya.
Kowace Amarya tana gefanta da danginta suna kara kintsa mata guri, amma fa na Amna tun kafin ka shiga za ka hangi bambanci wanda iyayenta suka mata, har da wata Rumfa suka aje mata irin ta zamani kusa da na ginin don ta aje motocinta.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Rumfar zata ci a kalla mota biyar. Sannan ga furanni na zamani da aka jera mata. Nafisa da taji ana labari, har ta zo iya wuya, wato ita don ‘yar masu kudi ce shi yasa yake bambanta komai.
Haka da su Shahida suka shiga gurin Amna din suka ga duniya a tsire suka fito a rude suna labari. Suka ce, “Hatta fentinku na ciki ba iri daya
ba ne.” Nafisa ta ce, “Ai ni na sani sai yafi sonta, kuna fadin ba dole ba ne ya zama haka.
Salma kuwa suna tafe tana kallon ‘yan kauyukun da ke tsakanin Zariya da Kaduna, har tana tambayar Badi’atu “Nan ina ne?” Badi’atu ta ce, “Wai ba ki san Amarya shiru take yi ba?”
Usman da ke gaban mota ya ce, “Ai wannan Amaryar ta daban ce.” Salma ta ce, “To kuma an ce tambaya mabudin ilimi ce.” Ya ce, “Haka ne.” Badi’atu ta ce, “Ba ki taɓa zuwa Kaduna ba?”
Salma ta ce, “Tab! Ban taba fita daga cikin garin
Zariya ba.” Suna shiga cikin Gate din gidan Salma ta bi gidan da kallo, har kofar falonta motar ta tsaya. Su Yaya Hadiza suka fito suka tare ta zuwa ciki.
Badi’atu ta wuce neman gefen Nafisa, Salma tayi ta kallon ko’ina, har suna ce mata wai ba ta da kunya, tana leka ko’ina.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Kujerun sun yi tsurut! A falon saboda girmansa, ga kujeru uku rak! Ta shiga dakin gadon yafi kyau. Sauran dakunan dai ba komai, sai dan tarkacen da aka sa mata.
Kicin kuwa shima a rame. Amma dadi ya cika zuciyar Salma, tana ganin kamar babu macen da ta kai ta sa’a a duniya, wai nan gidanta ne.
Kafin lokacin zuwa Dinner duk Amaran suna
cikin shiri, domin Ango da kansa ya kira kowace ya
ce ta zama cikin shi. Salma ce dai da bata da waya ya kira Badi’atu ya ce ta shiryata da kyau kafin karfe tara.
Ya zaci Amna zata yi masa gaddama tunda ta ce, “in dai ‘yan’uwanta suna nan sai ya ji ta ce za su shirya da wuri.
Salma tayi matukar kyau cikin riga da siket na
pink din material. Kayan sun kama ta tsam! Duk da
ba ta da kiba ko kadan, ‘yar singila. Badi’atu ta daura mata dankwali, sai tayi matukar kyau, tana ta kallon kanta a madubi. Mota daya aka so a dauke su, amma Amna ta ce a’a ita tana da motarta.
Nafisa ta ce ba za ta zauna da kowa ba. Shatima ya kira Aliya a waya, ya ce za a dauko su da Salma ta ce ‘To.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Shahararren Hotel ne in da za’ayi Dinner. Hall din kuma mai kyau da tsari, ba’a bari kowace Amarya ta shiga ba, sai da suka zo su duka.
Fuskar Nafisa tam babu fara’a, Amna kuwa zuciyarta cike da tambayar wannan wacece a cikinsu? A tare suka fito, shi ne a gaba sai Amna da . Aliya, Nafisa da Salma na biye da su, kowace da kalar shigarta.
Kujerar su biyar aka zagaye tebur din da aka jere musu abin sha da tsotsa a kai. Can gefe ga dogon cake wanda aka yi surar mata guda hudu a jiki da namiji guda daya a tsakiyarsu.
Bai zauna ba sai da yaga duk sun zauna, sannan ya fara nazarin inda zai tsoma nashi duwawun. Ya dauki kujerar shi ya sa ta tsakiyar Nafisa da Salma, sannan ya zauna. Amna da Aliya suka kalle shi, sai ya daga ma
Amna gira, Aliya kuma ya kashe mata ido daya.
Sannan ya ce, “Hasken fitila yana kashe min idone?”
Aliya tayi dan murmushi. Amna ta dan saki fuska, sai dai shi ba don haka,,,,,,ba, yana gudun kar Amna ta tambaye shi wace ce Salma, sannan kuma zai ke kallon fuskar Nafisa wadda tayi murtuk da rai.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ma su kidan turanci ne irin wakar nan da ake yi cikin nutsuwa da sanyaya rai. Tun daga bude taro da addu’a har zuwa jawabin maraba da baki duk abokanshi ne suka yi.
Abokai da ‘yan uwa suna ta zuwa suna daukar hoto da su. Daga nan aka zo batun yanka cake, duk suka je gaban cake din suka tsaya. Mai abin magana ya ce, “Wannan dangatan
Ango ne, ga shi ga kyawawan matanshi. Yanzu za su
saka hannu su duka don su yanka cake din su.”
Duk suka sa hannu, Salma tsawonta bai kai ba don dogo ne. ya ce da Nafisa “Dan koma in da Salma take.” Salma ta dawo kusa da shi. Ta kara daure fuska, sannan ta koma. Da zata koma ta zauna nema, sai dai tayi ta maza ta cije.
Duk da haka karshen wukar hannunta ya taba.
Suka yanka ana yi musu tafi tare da murna. Me abin
magana ya ce, “Yanzun Ango zai yanka cake ya ba kowacce daya-bayan-daya. Sannan suma su ba shi, yanzun zamu ga wadanne irin mata ya samu.” Shatima ya yanko ya soma baiwa Aliya, sannan ita ma ta amsa ta ba shi tare da risnawa, aka tafa. Me abin magana ya ce, “Uwargida mun gano cewa me
ladabi ce, saura me bin uwargida.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Amnah kuwa daya Ya yanko zai bata sai ta amsa ta sa a bakinta, sannan ta kamo fuskarshi da hannuwanta biyu, ya gutsira a bakinta. Nan tafi da ihu ya cika gurin.
Mai abin magana yana fadin wannan ta soyayya ce. Nafisa kuwa bayan ya bata da zata ba shi, har da hawaye don kishi.
Me abin magana ya ce, “Wannan kuwa tana da tsoron Allah. Yanzu sai ‘yar autar Amare.”
Salma ta girgiza kai cikin yanayi na shagwaba, tare da fadin “Yaya ba zan iya ba.” Ya rusuno da kunnansa daidai bakinta “Me ki ka ce?”
Ta ce, “Tsawona ba zai kai ba.” Ya ce, “Zan taimaka miki.” Ta matso ta dan yanki kasan, ta kalle shi a zatonta zai durkuso ne tasa mishi, sai kurum taji caf! Yayi sama da ita, ya rike kugunta.
Ta kalmashe kafafunta tamkar masu rawar
turanci, sannan ta saka mishi a baki. Gurin ya dauki
sowa. Maimakon ya dire ta sai kurum ya shiga juyi
da ita. Guri kuwa ya dauki ihu da sowa.
Sannan ya sauke ta, kowa ya koma mazauninshi, aka shiga ci da sha. Ba a tashi ba sai sha biyu da mintuna.
Tun da aka dawo daga Dinner Salma ke zaune a barandarta, ga makulli a hannunta amma bata iya bude kofar ba, don tun kafin su Yaya Hadiza su tafi suka kulle suka bata makullin tasa a jaka.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG